Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a samun masoyiya a wannan duniya.Nan take kyakkyawar ta ajiye farantinan abincin a gaban jarumi Darusi tayi masa waniirin kallo wanda dole ne ya dimauta dukkan 'da namiji tace lale marhaban da babban masoyi,ban taba zaton cewa mafarkina zai tabbata gaskiya ba,kullum sai an nuna mini dawowarka garin nan a cikin barcina,ashe kuwa kana tafe,ka sani cewa jina da ganina sun zama naka,tafiyata ta zamana da kwanciyata,duk begenka ne babu wata kalma dake fita daga cikin bakina face sunanka.Shin yanzu a wannan karon zaka ceci rayuwata ka amsa mini tambayar da nayi maka kayi mini alfarmar nan dana nema a wajenka?Kayi hakuri idan na takura muku daga zuwanka na dameka da surutu ko hutawa da cin abinci ba kuyi ba.Koda kyakkyawar budurwar tazo nan a zancenta sai Jarumi Darusi ya budi baki cikin sanyin murya yace yake GIMBIYA SUZAINA me kike ci ne na baka na zuba? Shin kin manta ne na gaya miki cewa zakiji amsar tambayarki amma sai bayan na kammala aikin daya kawo ni wannan nahiya taku,haka ma wannan alfarma da kika nema a wajena bazan iya yi miki ita ba yanzu sai bayan na dawo daga kogon Taskar Ajali.Koda jin haka sai fuskar budurwar ta juye izuwa tsananin damuwa tace gaskiya zuciyata da jikina ba zasu sake iyayin wannan dogon jira ba,ka sani tuni na roki sarki akan cewa indai ka dawo tare da ni zaka wuce kogon taskar Ajali kuma ya amince mini saboda mana sami damar koyon ilmin bautar ALLAH nima na dawo na sanar da sauran yan uwana mata.Baya ga haka kaima ka sani cewa zan iya taimaka maka a cikin wannan MUGUWAR TAFIYA mai hadarin gaske.Yayin da Gimbiya Suzaina tazo nan a zancenta sai hankalin Jarumi Darusi ya DUGUNZUMA yace saboda me abbanki zai yanke wannan hukunci alhalin baiyi shawara dani ba?Koda jin wannan tambaya sai Gimbiya Suzaina tayi murmushi tace Abbana ya yanke wannan shawara ne saboda yasan cewa yin bazai cutar dakai ba ni kuma zai ceto lafiyata da rayuwata daga vutar dana kamu da ita ta yawan begenka da tunaninka a kullum da koyaushe DARE da RANA.Koda jin wannan batu sai Jarumi Darusi ya gyada kai cikin mamaki yace da Gimbiya Suzaina wai ke akan wane dalili zaki kamu da SO na alhakin ma baki taba ganin fuskata ba?To idan kuma ni mummuna ne fa ko kuma ina da wata illah a fuskata?Koda jin wannan batu sai Gimbiya Suzaina tayi murmushi tace ai mu a zuci mukeyin SOYAYYA,koda ban taba ganinka ba,bansan yadda kake ba muddin a ka bani labarinka naji cewar haka kake kamar yadda na gani da idanuna tofa shikenan na kamu da matukar SON ka.Koda jin wannan batu sai Jarumi Darusi da Mujahid suka dubi junansu cikin matukar mamaki sannan Darusi yace to ni din yaya nake?Suzaina tace kana da tausayi,hakuri, kunya,kawaici gaskiya da kuma son Al'umma.Duk macen data sami namiji mai irin wadannan halayen to koda yafi gaba dayan mazajen duniya muni da talauci tafi dukkan mata samun dacewa saboda zai iya zama da ita a cikin kowane irin yanayi take kuma zai bata cikakkiyar kulawa,uwa uba zai bata soyayya dari bisa dari,shi kuwa SO na gaskiya wanda babu algus a cikinsa yafi dinare da lu'u lu'u daraja saboda su abubuwa ne da kowa ke iya samunsu amma SO na gaskiya ba'a samunsa a gun kowa.Na rantse da girman UBANGIJIna ba MUSULUNCI koda fuskarka ta dodo ce zan zauna da kai a haka.Koda Gimbiya Suzaina tazo nan a zancenta sai jikin Jarumi Darusi yayi sanyi matuka kuma nan take yaji ya kamu da tsananin SON Suzaina fiye da koyause duk da cewa dama can a wancan zuwan farko da yayiwa birnin nasu yaji ya kamu da SON ta amma saiya danne shi a can karkashin zuciyarsa.Nan take Jarumi Darusi ya dubi Suzaina yace shikenan ki gayawa Abban naki kicewa na amince zanyi wannan tafiya tare dake,koda jin haka sai Gimbiya Suzaina ta kamu da tsananin farinciki taji kamar ta rungume Jarumi Darusi amma saita mike tsaye zumbur ta fice daga cikin dakin da gudu tana tsalle da rawa tamkar wata karamar yarinya.Fitarta keda wuya sai Jarumi Darusi yaga Mujahid ya daga kansa sama yana tunani kuma idanunsa sun kafe tamkar ya zaman gunki. TASKAR AJALI Littafi Na Shida (6) Part D Tamkar ya zama gunki.Al'amarin daya dan razana Jarumi Darusi kenan ya kama kafadun Mujahid ya girgiza.Take Mujahid ya dawo cikin haiyacinsa,Darusi ya dubeshi yace wane irin mugun tunani kakeyi haka wanda yasa ka zama tamkar gawar da babu ruhi a jikinta?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid ya kawo gwauron numfashi ya ajiye tamkar wanda ya farfado daga dogion suma sannan ya dubi Darusi cikin murmushi yace yakai abokina kayi sani cewa ba komai ne ya jefani cikin wannan hali ba face tsananin mamaki bisa ganin babban dace da kayi.Duk da cewa banyi yawo a duniya sosai ba,iyakata nahiyarmu kuma ni ba masanin labarai bane,amma na tabbatar da cewa wannan budurwa data fita yanzu daga cikin dakin nan wato gimbiya Suzaina a duniya kaf a halon yanzu dai babu mace mai kyanta,amma kuma gashi ta kamu da tsananin sonka kuma irin son da babu dukiyar da zata iya siyansa.A yanzu da nayi arba da ita kuma naji irin kalamanta sai na gane cewa sauran mata sun kasance tamkar rakota sukayi a wannan zamani babu wani sarki ko attajiri ko matsafi ko kuma jarumi dayake da irin wannan mace.Waishin ma idan Yazirina da Sarila sukayi arba da Suzaina ya zasuji?Na rantse da girman iyayena sai sun raina kansu domin bambancin kyawunta da nasu tamkar an ajiye hoge ne a gaban tsauni.Sa'adda Mujahid yazo nan a zancensa sai Jarumi Darusi yayi murmushi yace ai kuma inda kasan daya baiwar da Allah yayi mata daka dada tabbatar da cewa Gimbiya Suzaina daban ce a cikin mata,kai ko a cikin mazan ma samun mai irin wannan baiwa sai an tona hatta ni kaina dinnan kuwa.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Mujahid yace wannan wace irin baiwa ce take da ita?Darusi yace baiwace ta jarumtaka da sadaukantaka,ba zan iya baka labarin Jarumtakar Suzaina da baki ba sai ka gani da idanunka,ni kaina da muka fafata na gane kurena kuma saida na nemi taimakon Allah sannan na sami nasara akanta,ga yadda na sami labarinta ita kadai take tare ayarin fatake ta tarwatsa su komai yawansu ta kwace dukiyarsu ta kame matansu da samarinsu a matsayin bayi kuma tun da takeyin gumurzu ba'a taba yi mata rauni ba kuma ba'a taba kaita kasa ba.Nine Jarumi na farko dana taba fitar da digon jini a hancinta kuma na kaita kas,abinda ya fara burgeni da ita shine a duk gwagwarmayar fashin da tayiwa fatake bata taba kashe mutum ba saidai ta karya shi kuma bata taba mata,yara da tsofaffi.A yanzu data musulunta idan ma ta tuno da abubuwan da tayi baya na zalunci kuka take yi da nadama.Gama fadin hakan keda wuya sai sarki ya shigo,koda ganinsa sai Jarumi Darusi da Mujahid suka mike tsaye da sauri don girmama shi amma sai yayi sauri ya ruke hannun Darusi ya mayar dashi zaune ya dubi farantin abincin da Suzaina ta kawo musu sannan ya dubi Darusi yace me yasa baku ci abincin ba alhalin nasan cewa irin wannan abincin ka fiso a garin nan musamman gimbiya ta shirya maka shi.Koda jin haka sai Jarumi Darusi yayi murmushi yace ai gimbiya ce ta jamu da hira yanzun nan bata jima da fita ba kai kuma ka shigo.Koda jin haka sai sarki yayi murmushi yace to ni dai ba hira nazo muyi ba dama nazo ne na shaida muku cewa gobe da safe akwai GASAR JARUMTAKA ta karshen shekara wacce muka sabayi a kofar fadata.Na sanar da abokan tafiyarku Sarila da Yazirina cewa 'yata Suzaina ce ke ruke da kambun a hannunta shin a cikinsu akwai wanda yake sha'awar shiga cikin wannan gasa?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid yayi caraf yace nidai ban kasance Jarumi ba don haka zan tsaya ne na more kallon wannan gasa na baiwa idanuna abinci.Koda jin haka sai Sarki yayi murmushi yace ai kai dama bakayi ruwan jarumai ba kafi kama da masu son samun kudi a banza,kai fa BABBAN JARUMI?Ina fatan zaka shiga wannan gasa saboda ina da matukar sha'arwa sake ganin gumurzunka da 'yata saboda gumurzu ne mai ban al'ajabi da ban sha'awa.Koda jin haka sai Jarumi Darusi yayi murmushi yace zan shiga wannan gasa amma bazan karbi kambun ba,gimbiya nake so ta lashe gasar saboda ta nunawa abokan tafiya girman jarumtakarta akan tasu.Ya shugabana na roke ka da kada ka gayawa gimbiya cewar zan bata dama ta lashe gasar.Waishin Sarila da Yazirina sunga Gimbiya kuwa?Sarki yace a'a basu ganta ba,ai wani bangare dabam a cikin gidan nan nasa aka kaisu nesa da inda turakar gimbiya take.Koda jin haka sai murna ta kama jarumi Darusi yace yauwa dama nafiso sai a filin gasar suyi arba da ita inda zasu ga irin tsananin kyawun da Allah ya bata da kuma baiwar jarumtakarta domin su san cewa kome mutum yake takama dashi akwai wanda ya fishi.ME ZAI FARU A WANNAN GASAR JARUMTAKA DA ZA'AYI A BIRNIN ARNAN DAJI WADANDA TUNI SUN KARBI ADDININ MUSULUNCI A WAJEN JARUMI DARUSI? WACE IRIN MASIFA CE TAKE ADDABAR MUTANEN BIRNIN ZAMRAS KUMA ME ZAI FARU IDAN SU DARUSI SUKA ISA BIRNIN? INA LABARIN SARKI DAMNASH WANDA YA TAFI DA YANKAKKEN HANNUNSA GUDA? SHIN ZAIYI WANI SHIRI NE NA DAUKAR FANSA A KAN DARUSI DA KUMA NEMAN KOGON TASKAR AJALI? YAYA KARSHEN KIYAYYAR SARILA AKAN JARUMI DARUSI ZATA KASANCE? WACE IRIN ALFARMA CE GIMBIYA SUZAINA TAKE SON DARUSI YAYI MATA KUMA YAUSHE NE DARUSI ZAI BUDE FUSKARSA KOWA YA GANI? Mu Hadu A Taskar Ajali Littafi Na Bakwai domin Jin cigaban Wannan Kasaitaccen Kayataccen Labari.TASKAR AJALI Littafi na Shida 6 Littafin Abdulaziz Sani m gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI Littafi na bakwai 7 Littafin Abdulaziz Sani m gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com KASHE GARI tun da duku dukun safiya kafin haske ya baiyana mutanen birnin daji suka rinka tururuwa a kofar fadar sarkinsu saboda murna da dokin gasar jarumtakar da za agabatar wacce kambunta ke hannun gimbiya suzaina yar sarki kafin rana ta bude tayi haske'' Fadar ta cika ta batse da bil'adama duk inda ka hanga baka ganin komai face kawunan bil'adama. Yazirina , sarila, mujahid da jarumi Darusi tuni suma sun halacci filin gasar tun da farkon safiyar shi ma sarki da fadawansa da dukkan jama ar gari maza da mata sun halacci filin gasar amma har sa 'o'i biyu suka kara shudewa ba a fara gabatar da wannan gasa ba sarila yazirina da darusi na tsaye a cikin filin gasa tare da sauran dakarun da zasuyi gumurzu kimanin mutum arba'in nan fa kowa ya kosa da yaga an fara wannan gasa musamman sara da yazirina cikin alamun fishi sarila ta dubi darusi tace wai shin wa ake jira ne har yanzu da ba za a fara wannan gasa ba ga shi rana na dada budewa an shanyamu a cikinta saikace tsummokara? Koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi yayi murmushi yace ba kowa ake jiraba face jarumar jarumai mai rike da kambun wannan gasa wato gimbiya suzaina'' koda jin wannan batu sai sarila da yazirina sukayi tsaki a lokaci guda tamkar hadin baki sannan sarila tace kawai don ta kasance yar sarki shine zata wulakanta mutane tayi ta bata mana lokaci to ai kuwa yau saina wulakantata a gaban jama ar ta nayi mata dukan kawo wuka na ragargaza sassan jikinta da takobina in yaso naga ta girman kai jarumi darusi yayi murmushi sannan yace '' Tabdi jan ai gimbia ta wuce zatonku domin ba kanwar lasa bace ku sani ita rijiyace gaba dubu kowa ya shigeta ba zai iya fita ba ta kasance barkono duk wanda ya shaketa saiya zubar da hawaye da majina amma banda Al amin Guyson ehm bugu da kari ita hadarice duk inda ta so nan take sa gabanta kuma ta cika mace mai dakawa maza gumba a hannu koda jin wannan batu sai sarila ta bushe da dariyar mugunta kuma ta murtuke fuskarta tace ai idan kaji ana cewa gaki gudu to sa gudu ne baizo ba inda ba kasa a nan ake gardamar kokawa tunda dai ga fili kuma ga doki zamuga karshen tika tiki tik! Kafin sarila ta gama rufe bakinta tuni an buga tambari kuma an busa algaita koda jin sautin tambari dana algaitar sai fadar ta rude da shewa tafi gami da jinjina nan fa maroka da mawaka suka shiga yiwa gimbiya suzaina kirari tsawon kusan dakiku dari da ashirin ana tayin sowa amma gimbiya suzaina bata fitoba Al amarin daya kara fusata sarila kenan ta dubi yazirina tace ai wannan ma shirme ne da kauyanci yaza ayi ka kuranta wacce take tsoron fitowa ta tunkaro dodannin da suke jiranta hm guyson. Koda jin wannan batu sai yazirina ta yi ajiyar zuciya sannan ta dubi sarila cikin alamun karayar zuciya tace ke yar uwa nifa jikina ya fara yin sanyi tun daga lokacin da naji darusi ya kuranta wannan yar sarki na fara ji a jikina cewa lallai ta cika jaruma yanzu kuma danaji yadda mutanen garin nan ke tsananin sonta dayi mata jinjina saina sake samun karayar zuciya cikin fushi sarila ta tare numfashin ta tanamai daka mata tsawa tace wai shin kema matsoraciyace haka ban saniba yaya mu da muka ragargaza maza har ya mace yar uwarmu zata baki tsoro ni na sani cewa karya ne a sami wannan mace a doron kasa wacce zata fini karfin damtse iya yaki da karfin sihiri idan ke kin karaya ba zaki iya fafatawa da ita ba to ki janye daga cikin wannan gasa kikoma gefe daya ki zuba ido kiga yadda zanyi da ita gama fadin haka keda wuya sai ga gimbiya suzaina ta shigo cikin filin gasar ta yafa wata kyakkyawar alkyabba a jikinta wacce akayita da shudin alhariri sai sheki da walwali yake alkyabbar ta lullube gaba dayan jikinta A kanta akwai hular sarauta ta zinare dogon gashin kanta mai tsananin sheki da walwali ta daureshi ya zuba a gadon bayanta har izuwa kan duga dugunta takalmin dake kafarta kuwa na fatar damisa ne wanda akayi masa ado da zaren zinare wohoho da baiyanar gimbiya suzaina a cikin filin gasar sai jama a suka dimauce ba wai maza ba wadanda suka kama yin kwalla saboda sunsan wutsiyar rakumi tayi nesa da ksa mata ma miko hannayensu suka rinka yi domin su sami damar taba jikin suzaina subar abin tarihi amma ina damar hakan bata samu ba saboda dakarun dake takewa suzaina baya sun kewayeta sun hana kowa rabarta hatta sarila da take ta faman cika baki tana yin arba da suzaina saita kame kamar gunki bata san sa adda ta wangame baki ba ta kura mata ido saboda tsananin mamakin ganin kyawun fuskarta wanda a duk lokacin da tayi murmushi sai kyawunta ya ninka kai fatar jikin suzaina kadai ta isa ta dimauta mutum domin ta fita daban da ta kowa a duk fadin garin babu mai irin launinta kuma ko ido idan mutum ya dubi fatar yasan cewa a fagen taushi ko auduga albarka ehm guyson ma ya kyasa fa Ashe sarila bata ga komai ba domin lokacinda gimbiya suzaina ta iso tsakiyar filin gasar sa adda jama a keta shewa da tafi ta haukan wani dogon mumbari sai ta cire alkyabbar dake rufe a jikinta Tayi cilli da ita sama ai kuwa sai maza yan kallo suka daka tsalle sama suka sawa alkyabbar wawa kowannansu na shinshina kamshin dake jikin alkyabbar koda jama ar sukayi arba da gimbiya suzaina a cikin shigar datayi sai suka dimauce suka fita hayyacinsu nan take samari da yawa suka rinka shidewa suna zubewa kasa saidai kaga ana yayyafa musu ruwa ana dauke su daga cikin mutane mata kuwa yan uwanta kuka suka kama yi saboda bakin cikin rashin samun irin surarta wohoho wadansu bakaken tufafi fari gimbia suzaina ta sanya rigar ta kasance yar karama kuma mai yankakken hannu iya cibiya wandaon jikinta kuwa gajerene iya guiwarta shima ya matseta ainun don haka dukkanin surorin jikinta sun bayyana suzaina ta kasance doguwar mace mai matsakaicin kaurin jiki dai dai misali kwankwasonta yana da fadi sosai kuma mazaunanta suna da tudu kirjinta a cike yake fal kuma duk da cewa bata sanya rigar rufe kirjinta ba a kumbure suke a tsaye tamkar balanbalan aka hura'' cikinta a shafe tamkar bata taba ciko shan wani abuba idanunta manya ne dara dara kuma farare kal tamkar madarar shanu tana da dogon siririn hanci tamkar alkalami bakinta dan karamine ga kyawawan labba kamar zanen wuka kaicon maza koda namiji zai zamo shine yafi kowa talauci a duniya indai zai rinka bude idanunsa yana ganin suzaina a matsayin matarsa ta aure to kuwa har abada ya daina takaici da bakin ciki rataye a bayan suzaina wadansu gajerun adduna ne wadanda akayi su da zallar karfen lu'u lu'u koda ta zaro suta gyara tsayuwarta sai kyawunta ya sake bayyana nanfa mazan da hankalinsu bai gusheba gaba daya suka rinka fashewa da kuka suna ta zubar da hawayen bakin ciki fiye da shekaru baya samari da yawa sun rasa rayukansu bisa tsananin kamuwa da son ta a cikin wannan birni domin duk wanda ya doshe ta da batun so sau daya ba zai kara marmarin sake son ganinta ba ma domin kashedin ransa zata yi masa wasu tsananin tunanin da begentane ya sanya musu cuta ta zamo sanadin ajalinsau lokacinda sarki yaga masoya sunata fitowa don neman aurenta amma taki ta fitar da gwaninta sai ya kirawo ta ya kadaita da ita a inda babu mai jinsu sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace yake yata menene dalilin daya sa kikaki fitar da gwani guda daya daga cikin masoyanki ya zama cewa kwata kwata ma bakya yin soyayya ki dubi yadda samari da yawa a wannan kasa tawa suka hallaka saboda soyayyarki ki sani cewa wannan abu yana damuna matka tamkar kina zubar mini da kimata ne mutuncina lokacinda sarki yazo nan a zancensa sai idanun gimbiya suzaina suka ciko da kwallah ta dubeshi tace yakai abbana kayi sani cewa duk da namijin da zaizo yace yana sona sai dai fa yasoni saboda dalili guda uku amma ba dai yasoni sona gaskiya ba wanda babu algus a cikinsa kodai yasoni saboda tsananin kyawun da allah ya bani ko kuma ya soni don matsayina na yar sarki mai jiran gado ko kuma yasoni saboda irin jarumtakar da nake da ita ranar da duk na rasa daya daga cikin wadannan abubuwa guda uku shikenan saina fita daga ransa ya daina sona ba zan taba son wani da namiji ba face na sami wanda na tabbatar da cewa bai damu da duniya ba sannan kuma dolene ya kasance ya fini jarumtaka kayi hakuri ya abbana na sani cewa abune mawuyaci na sami irin wannan miji amma tabbas indai ban sameshi ba to na hakura da yin aure har abada ( hm ga Guyson nan ai Indai jarumtane ko Sarki sahibul hairi na sarkin sarakai bai kaini ba ) Al amin guyson ke magana ka gafarceni idan wadannan kalamai nawa sun bata maka rai na barka lafiya koda gama fadin hakan sai gimbiya suzaina ta mike tsaye ta fice daga cikin turakar shi kuwa sarki saiya bita da kallo cikin alamun tsananin mamaki gami da takaici saboda tsananin son da sarki yake yiwa gimbiya suzaina tun daga wannan rana kawo iyanzu bai sake yi mata maganar aure ba har saida itada kanta tazo masa da batun cewa ta zabi jarumi darusi a matsayin abokin rayuwarta nan take sarki yakamu da farinciki mara misaltuwa saboda murna a ranar kasa yin bacci yayi lokacin da yazirina ta dubi sarila taga yadda ta dimauce bisa ganin tsananin kyawun suzaina da kyawun surar jikinta saitasa hannayenta biyu ta kama kafadunta ta girgizata da karfi nan take sarila ta dawo cikin haiyacinta sarila ta dubeta tace kada ki bamu kunya mana shin kin manta ne cewa mu ma kyawawa ne babu kamarsu a garin nan face wannan gimbiya? Koda jin haka sai sarila tayi yake cikin alamun borin kunya tace kenifa ba wani burgeni tayiba kawai mamakine bisa ganin yadda mutane suka rude a kanta dajin wannan batu sai dariya ta kwacewa yazirina tace haba yar uwata ai komai hassadarki dolene a ce da mijin iya baba a ko ina cikin duniya sai an jinjinawa wannan yar sarki ke a gaskiya ma ni ina ji a jikina cewar babu wata ya mace mai kyanta a wannan zamani kuma ga dukkan alamu jarumtakarma dolene a samu a tare da ita saboda akwai alamun hakan shikuwa jarumi darusi koda yaga irin shigar da gimbiya suzaina tayi sai ransa ya baci ya daka mata harara sannan ya kauda fuskarsa ga barin kallonta da ganin haka sai guyson yaci gaba da kallonta shi abinsa hm. Da ganin haka sai suzaina tayi murmushi itama ta kau da kai ta daina kallonsa saboda tasan cewa tabbasa tayi laifi to amma da gaiya tayi hakan domin ta nunawa su sarila cewa ruwa ba sa an kwando bane nan take alkalan gasa suka shigo cikin filin gasar ya fuskanci jama a lokacin da filin yai tsit yace yaku jama ar wannan birnin namu mai albarka ina mai yi muku barka da zagayowar wannan rana ta gasar jarumtaka wacce muke gabatar da ita a karshen kowace shekara kamar yadda aka saba bisa al ada tun da idanuwanku ga zakarar gasarmu mai rike da kambu a tsaye a tsakiyar fili wato gimbiya suzaina sannan kuma ga jarumai goma daga cikin mutanen birninmu Akwai kuma bakin jarumai guda uku mata saikuma jarumi darusi wanda kunsan shi ba bako bane kuma ya karbi kambun daga hannun gimbiya suzaina amma sai ya maida mata da abinta to wannan karon dai ya sake shiga gasar ina mai sanar muku cewa wannan karon gasar ta sauya launin domin gimbiya ta bukaci ta fafata da gaba daya jarumai goma a lokaci guda sabanin dacan da take yi da mutum dai dai ragowar mutum ukun kuwa zata fafata dasu daya bana daya ne kuma duk a yau dinnan take son ayita ta kare ko da jama ar sukaji wannan tsari sai suka kamu da tsananin mamaki saboda sun san cewa ba karamar wahala suzaina zata sha ba a ce tayi gumurzu da manyan zaratan jarumai su goma a lokaci guda sannan kuma tazo ta fafata da wadannan bakin jaruman mata wadanda suma da ganinsu sun taki wani abu kuma ga uwa uba jarumi darusi wanda kowa ya tabbatar da cewa yafita jarumtaka domin a wancan gumurzun da sukayi tasha wahalar gaske a hannunsa batare da bata wani lokaci ba aka buga gangar fara gumurzu nan take alkalan gasar , sarila yazirina da jarumi darusi suka fice da sauri daga cikin filin gasar suka bar gimbiya suzaina tare da zaratan jaruman goma a tsaye sunyi mata kawanya kowannansu na rike da zabgegen makami abin kwatance su dai wadannan jarumai guda goma ana matukar ji dasu a wannan birni domin ko yaki za a dasu ake fita sune a kan gaba saboda sadaukantakarsu gami da kwarewarsu a yaki A tarihin yake yakensu ma ba a taba yi musu rauni ba a filin daga kuma duk yakin da suka jagoranta sai an sami nasara ba a taba samun akasi ba amma gaba dayansu suna shakkar gimbiya suzaina amma a yau da sukaji cewar suzaina ta yarda su hada karfi su goman su yaketa sai suka yi murna saboda lokacin ramuwarsu tazo domin suna ganin cewa farat daya ma zasu gama da ita dama wadannan jarumai goma suna matukar jin haushin gimbiya suzaina saboda babu wanda bai nemi ya aureta ba har daya daga cikinsu ta wulakanta shi kuma ga shi ta dakusar da kimarsu da daukakarsu a idanun jama ar tunda duk ta kaisu kas a yayin da suke fafatawa nan take jaruman goma suka fara kewayeta suna jujjuya makamansu cikin zakuwa da mugun nufi ita kuwa suzaina ko motsawa batayi ba daga inda take tsaye rike da addunanta guda biyu kuma a natse take bata waigen komai idanunta ma kasa suke kallo kawai saboda tsabar yarda da kanta amma ta kasa kunnuwanta sosai tana sauraren sautin motsin kafafuwan jaruman goma kwatsam sai jaruman goma suka afka mata gaba dayansu a lokaci guda sukayi mata rubdugu suka rinka kai mata sara da suka tako ina cikin bakin zafin nama da dukkan karfinsu kaico ciwon ido sai hakuri hakika idan allah ya baiwa mutum baiwa tofa babu yadda makiya zasuyi da shi wanda ya iya ya huta nan take jama a sukaga abin al' ajabi domin suzaina bata gusa daga inda take ba taku guda a haka ta rinka kaucewa sara da sukansu tana karewa da addunanta ba tare da ta maida martani ba sai dai kaga tana sunkuye da kauce kauce gami da tsalle tsalle a waje daya su kuwa jaruman goma su kayi ta sara da sukan isa har tsawon kusan rabin sa a ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikinta ba bisa dole sukaja da baya sukayi cirko cirko suna haki gami da kallonta kawai cikin alamun tsananin mamaki suna tunanin irin salon yakin da yakamata su sauya A wannan lokacine yan kallo suka kaure da yiwa suzaina tafi suka rinka yi mata jinjina a dai dai wannan lokacine yazirina ta dubi sarila tace yaya kikaga takun hannun suzaina? Sarila ta tabe baki cikin alamun raini tace '' eh to babu laifi ta cika jaruma amma ai kada mage ba yanka bane kuma sai miya ta kare sannan ake sanin maci tuwo kafin sarila ta gama rufe bakinta sai taga gimbiya suzaina tayi nuni da danyatsan hannunta na dama ga dukkan jaruman goma tace tunda dai na baku dama ku cutar dani amma kun salwantar da damar bari na jarraba amfani da tawa damar koda gama fadin hakan sai suzaina ta yafito jaruman goma da hannunta cikin alamun raini tana mai kiransu dasu zo a fafata koda ganin haka sai jaruman goma suka fusata suka rugo izuwa kansu aka ruguntsume da azababben yaki nan take suzaina ta sauya salon yakin ta hada da kai musu naushi da bugu da hannu da kafa kuma ta rinka tsalle tsalle da kwance kwance a tsakiyarsu wani lokacin har shawagi takeyi a samansu tamkar ta kasance tsuntsuwa mai fuka fuki nan da nan kuwa ta fara hada musu jini da majina tana kulle musu ciki Al amin Ahmed Guyson Ke magana.. Al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan cikin kankanin lokaci suzaina ta rikirkita dakarun goma kuma ta kuntata su har ya zamana cewa basa iya kai mata hari sai kokarin kare kai ba zato ba tsammani sai akaga suzaina ta daka tsalle sama tayi wata irin katantanwa a sama tamkar an murza mazari kafin ta diro kasa ta yanke gaba dayan dakarun goma a kan kafadunsu da kaifin addunanta kuma ta doki kirazansu da kafafunta su duka suka zube kasa suna masu dafe raunikan kafadunsu hatta sarila bata san sa adda tayiwa suzaina tafi ba bisa ganin wannan gagarumin jarumtaka da tayi ta ban Al ajabi Ni kaina Guyson me baku labarin saida na kame kuma dakyar na cigaba da rubutun.. Sai bayan tayi tafin ta lura da cewa baikamata ta nuna ta burgete ba nan take ta murtuke fuskarta a wannan lokaci ne filin gasar ya rude da sowa a ka rinka yiwa suzaina tafi da jinjina fiye da wadda akayi mata a farkon shigowarta filin gasar, nan take aka fitar da dakarun goma daga filin da sauri cikin hanzari alkalan gasar ya rugo izuwa cikin filin gasar ya dubi suzaina cikin girmamawa da risinawa yace ya shugabata shin kina da bukatar hutawa ne kafin kici gaba da yin wannan gasa? Koda jin wannan tambaya sai suzaina ta dakawa alkalin gasar harara tace shin kaga alamar na

Chapter 10 of 14