sai Jarumi
Darusi yayi caraf yace ai na ukun
nasu shine mata
ko ba haka bane?Yazirina ta
murtuke fuska tayi
shiru,Ita kuwa Sarila sai ta bushe
da dariya tace ka
tona mana asiri ai kamata yayi
kayi shiru da
bakinka amma yanzu da ka fadi
zaka iya sawa
wasu su tsorata damu suyi taka
tsantsan kuma su
ki baiwa mace yardarsu ko
cikakkiyar SOYAYYAr
su a garemu.Koda jin wannan batu
sai Jarumi
Darusi yayi murmushi yace ai
kukan kurciya ma
jawabi ne mai hankali ke
ganewa,yana gama fadin
hakan saiyaje ya kama dokinsa ya
haye sannan ya
dubesu su duka yace wata bakwai
fa ba kwana
bakwai ba ne saboda haka sai kuzo
mu kama
hanya domin himma bata ga rago
ba.Gama fadin
hakan keda wuya sai Darusi ya
kada linzami
dokinsa yayi gaba.Cikin sauri
Sarila,Yazirina da
Mujahid ma suka hau nasu
dawakan suka bishi.
Nima ganin sun hau dawakansu
yasa na dakata
nan.
Suka hau nasu dawakan suka
bishi.Mujahid sai ya
zaburi nasa dokin da gudu ya riski
Jarumi Darusi
yace waishin me kake nufi ne da
kukan kurciya
jawabi ne mai hankali ke ganewa?
Koda jin wannan
tambaya sai Darusi yayi masa
murmushi yace kada
ka damu yakai Abokina da sannu
zaka
ga abinda
wannan kalma take nufi da
idanunka.Kawai sai
Darusi yayi shiru bai kara cewa
komai
ba ya
cigaba da tafiya.Duk wannan
magana
dasu Darusi
sukeyi Sarila da Yazirina basuji ba
domin suna
bayansu da kimanin tazarar taku
biyar
sun jero
bisa dawakansu suna tafe suna
hira,inda Yazirina
ta dubi Sarila kawai ta bushe da dariya,koda ganin
haka sai Sarila ta dubeta a fusace
tace
menene
kuma abin dariya a fuskata har da
zaki kalleni ki
kama kyakyatawa?Daji n wannan
tambaya sai
Yazirina ta nutsu tace ba wai wani
abu na gani ba
ya bani dariya a fuskarki kawai
mamaki ne ya
turnuke ni bisa ganin yadda wai
yanzu ni dake
muka jera muke tafiya har muna
hira
cikin
kwanciyar hankali da nishadi
alhalin
mun kasance
abokan gaba masu FARAUTAR
RAYUWAr juna.Wai
dama ashe akwai ranar da za'a
sami
wannan sulhu
a tsakaninmu?Koda jin wannan
batu
sai itama
Sarila ta bushe da dariya sannan
tace
ai wannan
sulhun namu na dole ne saboda
idan
ba muyi shi
ba dukkaninmu zamuyi asarar
abinda
muka fito
nema.Ni babban ma abinda ya
daure
mi kai shine
yanzu dai ga taswirori biyu a
hannunki kuma ni ma
ga tawa a jikina amma duk sun
zama
na banza
domin tun dama ba da su zamuyi
amfani ba.Kai
lamarin wannan bakon jarumi
akwai
al'ajabi,to
waishin ma ta yaya akayi yasan a
inda
kogon
Taskar Ajali yake alhalin mahaifina
ya
boyeshi
yadda babu mai iya gano shi face
da
wannan
Taswirar guda uku?Koda jin haka
sai
Yazirina ta
numfasa tace bakiyi mamakin irin
tsananin
jarumtakarsa ba sai mamakin
yadda
ya gano inda
kogon Taskar Ajali yake?Ni bama
wannan ba akwai
abu guda da nake tsoro,wai shin
bayan ya kaimu
kogon taskar ajali idan kuma
kikayi
kokarin
shammatarsa don ki kashe shi kika
kasa fa?me
kike tunanin zai biyo baya?Dajin
wannan tambaya
sai Sarila tayi murmushi tace ta
yaya
ma haka zata
faru?Ai da ganin Jarumi Darusi
mutum ne mai
yarda da mika amana saboda haka
bazai taba
tunanin cewa zamu ci amanarsa
ba.Yazirina tayi
ajiyar zuciya tace to shike nan
wannan abu dai
mace ce da aiki ba'a san abin da
zata
haifa
ba,akwai wani abu da nake tunani
waishin bakya
tunanin cewa manyan sarakuna
suna
nan sunyi
mana kwanton bauna?Ke kin sani
cewa ba zasu
taba zuba mana ido ba kawai suna
ji
suna gani
har mu mallaki wannan dukiya
muzo
mu mallaki
komai nasu.A yanzu haka inaji a
jikina
cewa suna
biye damu a cikin wannan tafiya
ba
tare da mun
sani ba.Koda jin haka sai Sarila ta
busje da dariya
tace saboda me zaki damu kanki a
kan abinda
baikai darajar sauro ba a nauyi
akan
tafin
hannunki,kin sani cewa inda
sarakunan duniyar
nan kaf gami da gaba dayan
bokayen
duniya da
jaruma duniya zasu taru a nan
domin
su yake mu
ni kadai zan iya kashe su a cikin
kankanin
lokaci.Koda jin haka sai Yazirina ta
jinjina kanta
tayi shiru bata kara cewa komai
ba.Haka dai su
Yazirina suka nausa cikin dajin
sukayi
ta tafiya
basa tsayawa face idan jarumi
Darusi
zai gabatar
da sallah ko kuma idan dayansu
nason ya kawar
da wata bukata wato dole a tsaya
shi
kuma duk
inda mutum zai zagaya domin
kawar
da bukatar
tasa sai an caje wajen an tabbatar
da
cewa babu
wani abu mai cutarwa a wurin
amma
banda jarumi
Darusi domin shi komai duhun
waye
da
surkukinsa kawai kunna kai yake yi ciki yana
karanta addu'ar neman tsari a
cikin
zuciyarsa.Muhaj id da Yazirina da
Sarila kuwa suna
matukar mamakin yadda jarumi
Darusi keyin
ganganci da rayuwarsa
haka.Abinda
basu sani ba
shine ya dogara ne da ubangijinsa
dari bisa dari
yayi imani cewa zai kareshi daga
dukkan
abinki.Saida su jarumi Darusi suka
share kwanaki
uku suna ratsawa ta cikin mugayen
dazuzzuka ba
tare da sun hadu da wani mugun
abu
ba,abinda ya
daurewa su Yazirina kai shine
ganin
yadda Darusi
ya rinka kurdawa dasu ta cikin
surkuku iri irin
kuma kafin aje wani a sai ya gaya
musu cewa za'a
riski abin dake wajen,idan yace
akwai
tsauni a nan
gaba tafiyar kimanin rabin sa'a na
isa
wurin kuwa
sai suga tsaunin.Hatta girman
tsaunin
da
yanayinsa saiya shaida musu
hakama
tsirrai ko
fadama ko dutse ko kogi,Darusi
yasan
komai dake
cikin dazuzzukan tamkar a rubuce
suke cikin
kwakwalwarsa.Al 'amarin da yayi
matukar basu
mamaki kenan.A ranar kwana na
uku
ne daf da
faduwar rana suka iso wani wuri
mai
yanayi iri
daban dana sauran dukkan
dazuzzukan da suka
wuce a baya.Wurin fili ne fetal cike
da
yashi
tamkar sahara.Akwai tsirarun
bishoyoyi a wajen a
can gaba kuma kamar tazarar
zara'i
arba'in da
biyar akwai wani katon dutse
wanda
kasansa kogo
ne kuma gaba daya dutsen a
lullube
yake da
bishiyoyi masu rassa da ganyaye
don
haka wajen
yayi matukar duhu mutum bai isa
ya
hango abinda
ke wajen ba ko cikin kogon dutsen
dole sai mutum
yabi ta gefen wannan kogon dutse
sannan zai iya
wucewa izuwa kan hanyar da zata
kaishi daji na
gaba.Kawai sai su Mujahid sukaga
Jarumi Darusi
yaja linzamin dokinsa ya tsaya
sannan
ya sauko
daga kan dokin nasa,koda ganin
haka
sai duk su
ukun suka ja linzamin dawakan
nasu
suka
tsaitsaya.Mujah id ya dubi Darusi
cikin alamun
rashin fahimta yace me yasa ka
tsaya
anan?Darusi
yace dalili na farko shine lokacin
ibadata ya
gabato,dalili na biyu kuma inason
na
baku dama
ne kuyi duk irin shirin da kuke
ganin
zakuyi domin
fuskantar bala'in dake cikin
wancan
kogon dutse
domin baku isa ku iya wucewa ta
gaban dutsen ba
batare da kun fafata da abinda ke
ciki
ba.Koda jin
wannan
batu sai cikin Mujahid ya duri ruwa
tsoro ya
baibaye shi ya ce ka sani cewa ni
ba
jarumi bane
don haka kada ka barni da
karfina.Koda jin haka
sai jarumi Darusi yayi murmushi
yace
ai babu wata
kariya da zan baka a yanzu tunda
ba
kayi imani da
ubangijina ba,kamar yadda na
fada da
farko ba zan
taimaki dayanku ba face naga
muraran zai rasa
rayuwarsa.Kada ka manta da cewa
kai
shahararren
barawo ne mai karfin sihirin tsafi
daka
gagari a
kamaka a wannan nahiya saboda
haka
kayi amfani
da karfin sihirin nake anan ka cece
kanka.Koda
gama fadin hakan sai Darusi ya
dauki
butar
alwalarsa daga cikin jakar
guzurinsa
ta nufi gefe
daya ya tsugunna domin yayi
alwalar,Mujahid ya
rugo gareshi ya durkusa daf dashi
yace wace irin
masiface a cikin wannan kogon
dutsen?Darusi yace
nifa kuna bani mamaki yaya ni da nake bako a
cikin wannan nahiya taku ace na
fiku
sanin sirrin
dazuzzukanku,ka tuna fa cewa ba
wani nisa mu
kayi ba a cikin wannan tafiya daga
cikin birninku
tafiyar kwana uku kacal ce.A
matsayinka na
gawurtaccen barawo ya kamata
ace
kasan komai
dake cikin dazuzzukan da suka
kewaye ku.Mujahid
yace ai ni ba dan fashi bane,ba mai
buya a cikin
daji a cikin gari nake satata inda
ya
gagari barayin
daji shiga.Koda jin haka sai jarumi
Darusi yayi
shiru yaci gaba da alwalarsa.Koda
yazo zaiyi
shafar fuska saiya juyawa su
Mujahid
baya ya
wanke fuskar tasa sannan ya
hattama
alwalar tasa
ya dauko buzunsa ya tayarda
sallah.Adaidai
wannan lokaci ne Sarila ta yafito
Mujahid da hannu
yazo garesu,ita da Yazirina,Tayi
masa
wani irin
kallo cikin murmushi mai dauke da
alamar
tambaya(?)ta bude baki da nufin
tayi
masa magana
amma sai Yazirina tayi wuf ta sha
gabanta saboda
kishi ne ya turnuke ta ta dubeta
tace
bana son
naga wata alaka na kulluwa
tsakaninki da
Mujahid.Koda jin haka sai Sarila ta
bushe da
dariya tace saboda Mujahid mijinki ne
ko kuwa
saboda ya kasance dan uwanki ne?
Yazirina tace
babu daya cikin biyu kawai saboda
ban yarda dake
bane domin a ko yaushe zaki iya
yaudararmu ki
cutar da dayanmu.Sarila tayi
murmushi tace ba
gaskiya kika fada ba kishi ne kawai
ya
turnuke ki
saboda kina ganin cewa nima ina
son
sa ko?Dajin
haka sai kunya ta kama Yazirina ta
dan kau da kai
ita kuwa Sarila sai ta cigaba da
bayani
tana mai
cewa kada ki damu ni a rayuwata
soyayya da aure
basu zame mini dole ba ina iya
kawar
dasu daga
raina nan take.
Hmm Nine Jarumi DarusiIna iya kawar dasu daga cikin raina nan take.Kai Mujahid waishin me kake tattaunawa ne kai da
Darusi wannan shine kadai abinda nake son na
tambaye shi,koda jin haka sai Yazirina ta dan saki ranta tayi guntun murmushi.Mujahid yace ya gaya mini cewa muyi shirin tunkarar masifar dake cikin wancan kogon dutse dake gabanmu kuma dana
tambayeshi ko wace irin masifa ce sai yace dani wai zamu ganta da idanunmu.Koda jin wannan
batu sai Sarila ta bushe da dariyar mugunta tace yanzu akan haka ne naga duk ka wani firgice,to koma dai kai bazaka iya yin komai ba ai ka sani cewa ni da Yazirina ba zamu taba barin wani abu ya cutar da kai ba.Gama fadin hakan keda wuya
sai suka ga Jarumi Darusi ya idar da sallarsa ya shafa addu'a.Nan take ya mike tsaye da sauri ya nannade buzunsa ya sanya shi cikin jakar
guzurinsa ya hau dokinsa ya dubi su Sarila ya ce kuzo mu cigaba da tafiya.Kafin dayansu yayi wani yunkuri tuni Darusi ya kada linzamin dokinsa kuma ya zare takobinsa ya nufi inda wannan kogon dutse yake yana karanta wata addu'a ta musamman a
cikin ransa,ita kuwa Sarila sai ta bishi da kallo cikin harara ta daka tsaki tace nifa na tsani wannan
mutumin.Baya magana sosai kamar kurma baya yi mana bayanin komai ya barmu a cikin duhu
sannan kuma yaki yarda muga fuskarsa nidai ina kyautata zaton cewa shi mummuna ne na kwarai
shi yasa baya son muga fuskarsa.Tana gama fadin hakan sai tayi sauri ta kama dokinta ta dane kuma itama ta zare takobinta tabi bayan Darusi.Take Yazirina ta rufa mata baya,Mujahid ne na karshe kuma kana kallonsa zaka gane cewa a tsorace yake domin akwai alamun firgici akan fuskarsa.Lokacin daya rage saura baifi taku goma ba tsakanin
kafafun dokin Darusi da wannan kogon dutse sai ya rage saurin tafiyar dokin nasa kuma ya kura
idanunsa sosai akan kofar kogon dutsen,suma su Sarila sai sukayi koyi dashi,saida Darusi ya dan gifta kofar kogon dutsen kadan sannan wata
katuwar macijiya mai KAWUNA SABA'IN DA DAYA
ta jeho kawunan nata gaba daya waje daga cikin kogon dutsen,amma sai kawunan suka tsaya cak
kuma suka kurawa Jarumi Darusi idanu aka fara
kallon kallo tsakaninta dashi.Sarila,Yazirina da Mujahid kuwa koda sukayi arba da wannan maciya mai tsananin girma da munin fuskoki guda saba'in da daya sai suka firgita ainun domin ko a labarai basu taba jin labarin irin wannan macijiya ba.Duk da tsananin jarumtakar Sarila da Yazirina basu san sa'adda suka ja linzamin dawakansu ba sukaji
kamar su ruga da baya,shi kuwa Mujahid jikinsa ne gaba daya ya kama karkarwa yayi wuf ya matsa kambunsa na tsafi domin ya bace amma sai sihirin tsafin nasa yaki yayi aiki.Al'amarin da yayi matukar kara razana shi kenan ya saddakar da cewa lallai yai dai kam ranar AJALINsa ce.Saida Jarumi
Darusi ya wuce gaban wannan macijiya har ya bata yar tazara suna kallon kallo ita bata kawo masa wano hari ba shima kuma baiyi wani yunkurin ba na kai mata hari.Hakika masu iya magana sunyi
gaskiya da suka ce BABBAN GORO sai MAGOGIN
KARFE.Tsakanin wannan Macijiya da Jarumi Darusi KAR TA SAN KAR ne domin a wancan karon sunyi
bakin gumurzu tasha bakar wahala a wajensa
shima ya wahala amma shi ya sami damar hallaka bai kasheta ba ita kuwa kasa hallakashi tayi.A yanzu tana ganinsa ta shaidashi don haka ne taki cutar dashi.A wannan lokaci a akwai tabon
raunikan da Darusi yayi mata a sassan jikinta sunfi guda dari,shi kuwa rauni daya ne tayi masa da
kaifin hakorin bakinta guda a lokacin data kawo masa wani mugun sara ya goce cikin bakin zafin nama.A wannan lokaci da farko saida suka shafe sama da sa'a guda tana kawo masa duka da
jelunanta kuma tana kawo masa sara da cizo da
bakunanta duka yana gocewa cikin bakin zafin nama yana kadesu da hannayensa da takobinsa da kuma kafafunsa.Darusi yana wannan jarumtaka ne da zallan karfin damtsensa da kuma zafin
namansa,ita kanta wannan muguwar macijiyar tayi matukar mamakin Darusi saboda wannan ne karo
na farko data hadu da wani mahaluki daya
gagareta kashewa a cikin dakika biyu walau
MUTUM KO ALJAN ko kuma dabba,shi kawai
Darusi ransa ne ya baci da yaga KAIFI DA TSINI basa tasiri a jikin wannan macijiya domin duk
sa'adda ya sareta koya soka mata takobinsa sai yaga jikin nata ko kwarzanewa bayayi saidai
tarwatsin wuta ya tashi amma kuma naushin da
yake gabzawa macijiyar akan fuskokinta da
hannayensa da kafafunsa suna dimautata domin ji take kamar dutse yake maka mata.Nan da nan
yasa idanunta suka rinka kumbura fatar gefen
idanuwanta ya rinka durar ruwa kafin shedewar
sa'a guda macijiyar ta jigata ainun ta fara wani irin nishi na wahala.Babu shiri macijiyar taja da baya tana haki kamar ranta zai fita suka sake kurawa juna idanu a lokacin da Darusi ya gyara
tsayuwarsa kuma ya ruke takobinsa da hannayensa biyu ya fara karanta wata addu'a ta musamman a cikin zuciyarsa.Ita kuwa macijiyar saita fara tattaro dukkan dafin dake cikin cikinta izuwa hakoranta kuma ta dago gaba dayan kawunan nata sama
kawai so take ta kawowa sassan jikin Darusi sara da dukkan kawunan nata a lokaci guda.Cikin
shammace gami da amfani da dukkan zafin
namanta sai macijiyar ta kawowa Darusi sara da kawunan nata kawai sai gani tayi Darusi ya daka tsalle sama da baya tamkar wani tsuntsu ne ya
sureshi kawunan nata suka doki kasa gaba
dayansu,take kasar wajen ta daddare wata bakar mugunyar kumfa ta jike kasar wajen tamkar bakin shuni aka zuba har wani irin tururin zafi ya rinka tashi a wajen,ba komai ne ba wannan face masifar fitar dafin macijiyar.Shi kansa Darusi daya kalli wajen da Macijiyar ta sara da bakunan nata bai san sa'adda
™Abubakar Haleefah Physicist™
ya yiwa Allah godiya ba a cikin ransa saboda ya tabbatar da cewar inda jikinsa bakunan macijiyar ya sara da tuni tasa ta kare.Koda macijiyar taga jarumi Darusi ya tsallake wannan mugun hari data kawo mai sai ta firgita da al'amarinsa ta dubeshi ta bude bakinta na tsakiya guda daya tace yakai
wannan hatsabibin bil'adama kai kuwa waye
bokanka a cikin wannan duniya?Da wane irin tsafi kake yin aiki kuma wanene ya baka horon yaki?
Koda Darusi yaji macijiyar ta bude baki tayi wannan magana sai ya gane cewa ba dabba bace
lallai aljana ce ta rikide izuwa wannan siffa don haka saiya dubeta a fusace yace yake wannan
shaidaniyar aljana ke kuma menene dalilinki na rikida izuwa wannan mummunar siffa kuma akan
wane dalili kike kokarin hallaka ni?Sai kin bani amsar tambayata sannan nima zan baki amsar
tambayar da kikayi min.Koda jin haka sai macijiyar ta bushe da wata mahaukaciyar dariya mai kama
da saukar kwarankwatsa wacce babu dadin ji
sannan tace yaro kabar hanin munyi gumurzu har na tsawon wannan lokaci ban sami nasarar hallaka kaba,to ka sani cewa shirina babbane yanzun nan kuma zan nuna maka hakan domin ni MURUCIN
KAN DUTSE ce ban fito ba saida na shirya.
Turkashi sai Mu hadu a Littafi Taskar Ajali Na Biyar (5) domin jin cigaban wannan kasaitaccen
kayataccen labari.
DONE FOR TODAY.
SAI KUMA NEXT TIME.
HALEEFAH A ABUBAKARTASKAR AJALI 4
Littafi na hudu 4
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
TASKAR AJALI 5
Littafi na biyar 5
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
K
afin Darusi ya budi baki yace wani
abu sai
Macijiyar ta dako tsalle daga inda
take ta kawo
masa mugun hari irin na dazu a karo
na
biyu,maimakon Darusi ya dala tsalle
da baya sai
yayi gaba a sama ya dira akan
tsakiyar kan
macijiyar ya hau kawunanta da
jelunanta da sara,ai
kuwa sai gashi yana daddatsa su jini
na tsartuwa
da feshi,babu shiri macijiyar ta rinka
kurma uban
ihu da kyar ta samu tayi dungure da
jikinta a kasa
tayi wurgi da Darusi can gefe daya
kawai sai ta
rikide izuwa ainihin siffatar ta
Aljana.Tunda Darusi
yake ratsa manyan dazuzzuka a
rayuwarsa bai
taba yin arba da Aljana mai tsananin
girma da
muni ba kamar wannan Aljanar.Siffart
a kala biyu ce
ta Aljanu da dodanniya,da yawan
mutane idan
sukayi arba da ita a cikin wannan siffa
take suke
faduwa kasa matattu,yan uwanta ne
Aljanu suke
zautuwa ko kuma su kamu da
matsananciyar
rashin lafiya.Kai faratan hannayenta da kafafunta
ma wadanda suka kasance zara zara
kuma cako
cako ba kyan gani sun isa su firgita
mahaluki.Koda
Jarumi Darusi ya dubi Aljanar yaga
yadda yayi
mata raunika a jikinta kaca kaca,jini
na ta zuba
kuma tana numfashi sama sama
kamar ranta zai
fita sai yaji ya kamu da tausayinta
duk da cewa
taso tayi masa KISAN GILLAH.Aljanar
ta budi baki
da kyar d wannan kai dake tsakiyar
gangar jikinta
tace yakai wannan gawurtaccen
jarumi kayi mini
rai kada ka kashe ni yanzun nan zan
amsa maka
tambayar da kayi mini.Da farko dai ni
sunana
Marwisa Bintu Hazmir,na kasance
shugabar
hadiman Bokan daya kirkiri Kogon
Taskar Ajali,ina
rikida ne izuwa wannan halitta ta
macijiya domin
na yaki duk mahalukin da yake da
niyar zuwa
kogon Taskar Ajali na kashe shi koda
kuwa zaije
ne ba da niyar dauko dukiyar
maigidana
ba.Maigidana ya ajiye kuma babu
wanda ya isa ya
tsallake sharrina face yana dauke da
wadansu
taswirori guda uku masu nuni izuwa
hanyar da
zata isa can kogon na Taskar Ajali.Mai
gidanan
nawa kafin ya bar duniya ya shaida
mini cewa ya
boye wannan dukiya ne domin yarsa
ta cikinsa ta
mallaki komai da kowa dake cikin
wannan duniya
kuma ko itace tazo nan gabana ba
tare da
taswirori uku ba kasheta zanyi haka kuma idan
tazo da taswira biyu babu ta ukun
kasheta zanyi
wannan shine umarnin da mahaifinta
ya bani kuma
a kansa nake daga nan har mutuwa
ta,bisa
binciken da yayu babu wanda ya isa
ya hada
wadannan taswirori guda uku face ya
cancanci ya
mulki wannan duniya.Abinda ya kasa
ganowa shine
shin yar tasa ta cancani ta mulki
duniyar?Lokacin
da Aljana Marwisa tazo nan a batunta
sai Jarumi
Darusi ya tari numfashinta yana mai
daka mata
tsawa yace dake da bokan naki duk
kuna kan bata
mabaiyani,MULKI da ARZIKI duk
Allah ke bada
su.Mai gidanki bai isa ya iya hana
wani ba
MUTUWA da RAYUWA duk wanda yayi
nufi zuwa
kogon taskar ajali face idan kwanansa
ya kare,nazo
ne wannan nahiya taku domin na
nuna muku cewa
addinin da kukeyi na bautar gumaka
da sauran
abubuwa da kuma imani da tsafi da
kukeyi duk
karya ne kuma bata ne mabaiyani,ke
a kanki yanzu
kinga misali tunda gashi kin kasa
hanani wucewa
izuwa kogon taskar ajali,gaba daya
sarakunan dake
wannan nahiya taku sunyi imani da
cewa duk
wanda ya mallaki wannan dukiya ta
mai gidanki sai
yafi kowa karfin arziki kuma saiya
mulki duniya
gaba dayanta kuma wai a ko ina sai
anyi fari da
talauci a karsa ne kadai ba za'ayi
annoba ba.To ni
na karyata wannan tsafi kuma sai na tabbatar
muku da hakan bazan kashe ki ba
yanzu amma
zan koma da baya naje na nemo
wadanda ke
dauke da wadannan taswirori guda
uku nayi musu
rakiya izuwa can kogon taskar ajali
amma sai
bayan naje can kogon naga duk irin
masifun da
mai gidanki ya zuba akan hanya don
hana shiga
kogon,idan kin gama jinyar jikinki kin
warke in
yaso ki sake tarata a dawowata ko
kuma idan na
dawo karo na biyu.Koda gama fadin
hakan sai
jarumi Darusi ya juya ya cigaba da
tafiya abinsa ya
nufi hanyar da zata kaishi can kogon
na taskar
ajali ko sau daya bai sake juyowa ba
ya dubi
Aljana Marwisa har ya kule a cikin
dajin lokacin
data bishi da kallo kawai tana
mamakinsa.Saida
Aljana Marwisa ta shafe wata shida da
kwana
ashirin da daya tana jinyar raunikan
da Jarumi
Darusi yayi mata sannan ta warke
amma tabon
raunikan basu bace ba a jikinta.A
ranar dataji
karfin jikinta Jarumi Darusi ya dawo
daga can
kogon taskar ajali kuma yazo giftawa
ta gaban
kogon dutsen da take cikin nutsuwa
da takama ba
tare da shakkar komai ba.Yana isowa
kofar kogon
dutsen yayi arba da aljana Marwisa
tsaya a cikin
siffarta ta macijiya amma ko kallonsa
batayi ba sai
ta koma cikin kogon dutsen ta
kulle,shi kuwa ya
wuce abinsa,wannan shine abinda ya faru a baya
tsawon watanni takwas da suka shude
tsakanin
wannan muguwar macijiya da jarumi
Darusi.Lokacin da Jarumi Darusi yaga
ya wuce ta
gaban Macijiya Marwisa lami lafiya
saiya dubi Su
Sarila ya yafito su da hannu yana mai
yi musu
nuni dasu tawo su wuce ta gaban
macijiyar.Koda
ganin haka sai Sarila,Yazirina da
Mujahid suka
dubi junansu dukkaninsu sai suka
noke aka rasa
wanda zai fara shiga gaba.Al'amarin
daya fusata
jarumi Darusi kenan ya daka musu
tsawa yace
yanzu a hakane kuke tunanin cewa
zaku iya zuwa
har can kogon taskar ajali alhalin
gashi tun a
matakin farko kun razana da abinda
baifi somin
tabi ba a cikin tsaro dake kan
hanya.Idan har kun
karaya da dukkan jarumtakarku da
karfin sihirin
tsafin naku kunyi imani cewa ababan
dogaronku
ba zasu iya tserar daku ba to ku karbi
addinia
mana.Na rantse da girman ubangijina
indai kuka
karbi addinina yazu take zan kaiku
kogon taskar
ajali a cikin abinda bai wuce rabin
sa'a ba kuma
ubangijina zai
™Abubakar Haleefah Physicist™
kareku daga sharrin duk masifun dake
hanya.Koda
jin wannan batu sai hankalin su Sarila
ya
dugunzuma ainun kuma jikinsu ya
kama bari take
sukaji dukkan tsoro yakau daga cikin
zukatansu,kawai sai Sarila ta fara
sakarwa dokinta
linzami tayi gaba sannan Yazirina ta take mata
baya shi kuma Mujahid ya
bita.Kaico!!!Ma i rabon
shan duka sai ya sha shi domin ita
kazar wahala
indai aka yankata tofa dole ne a
figeta,Koda Aljana
Marwisa taga su Sarila sun durfafota
zasu wuce ta
gabanta sai ta kame cak tamkar gunki
ta dauke
numfashinya a zatonsu Sarila yadda
jarumi Darusi
ya wuce lafiya kalau haka suma zasu
wuce.Yazirina ce kadai zuciyarta bata
amince mata
da hakan ba don haka hannunta na
dama na kan
kufen takobinta kuma idanunta na
kan kawunan
macijiyar guda saba'in da daya da
kuma dukkan
jelunan nata ko kiftawa batayi.Saida
su Sarila suka
iso daf da gaban Marwisa saura kiris
su dan gota
ta sai ta yunkura cikin bakin zafin
nama ta kawo
musu mugun sara da kawunanta
uku,cikin
tsananin zafin nama Yazirina ta daka
tsalle sama ta
kade kan macijiyar daya kawo mata
hari da
takobinta kuma ta take kafafunta a
sama ta doki
Sarila da Mujahid suka fado daga kan
dawakansu,ai kuwa sai bakunan
macijiyar biyu
suka sari gadon bayan dawakan Biyu
na Sarila da
Mujahid.Take hakoran macijiyar suka
datse gangar
jikin dawakan biyu tamkar da adda
aka saresu
kuma dafin macijiyar yasa jinin jikinsu
ya daskare
sukayi bakin kirin tamkar a cikin wuta
aka babbaka
su nan take.Ai kuwa sai dokin Yazirina
ma ya
firgita ainun ya ruga izuwa cikin daji da gudu yana
haniniyar doki.Cikin tsananin firgici
Yazirina,Sarila
da Mujahid suka mike tsaye zumbur a
tare suka
kama ja da baya baya tamkar su ruga
da gudu
amma babu damar hakan saboda ita
ma macijiyar
tunkararsu tayi tana shawagi da
kawunanta da
jelunanta a samansu.Ko yaya dayansu
yace zaiyi
yunkurin gudu sun san cewa kawai
jefa masa
bakinta zata yi guda ta lankwameshi
ko kuma ta
cafko shi da jelarta guda ta maka
shi,ba shiri
Sarila da Mujahid ma suka zare nasu
takubban
kuma suka cigaba da ja da baya
macijiyar na biye
dasu tamkar mai kaya ya taso barawo
akan
gaba.Koda Macijiyar taga Sarila sun
kusan izuwa
inda Jarumi Darusi ke tsaye sai ta
zubo musu
kawunanta gaba daya ta rinka kawo
musu
sara,nanfa aka kacame da azababben
yaki ya
zamana cewa suna kade hare haren
nata da
takubbansu da dukkan zafin namasu
da iya
yakinsu.Babban abinda ya dugunzuma
hankalinsu
shine duk sa'adda takubabban nasu ya
hadu da
jikin kawunan macijiyar saidai suji
kara kal!na
tashi tamkar karfe da karfe ne suka
hadu gami da
tarwatsin wuta kuma ko kwarzanewa
jikin kawunan
macijiyar bayayi.Duk sa'adda kuma
suka kaucewa
harin kawunan macijiyar tofa duk
abinda bakunan
macijiyar ya sara walau bishiyoyi ko duwatsu take
suke ragargajewa su farfashe kai kace
a cikin turmi
aka dake su.Al'amarin da yai matukar
dugunzuma
hankalinsu kenan musamman da suka
gane cewa
ko alamar gajiya babu a tare da
macijiyar su kuwa
nan da nan jikinsu ya fara
amsawa.Lokacin da
macijiyar taga jaruman uku suna
.atukar kokarin
kare kansu daga hare harenta sai ta
kara da jeho
musu jelunanta ta tinka kawo musu
duk dasu ta ko
ina tana neman ta galabaiyar
dasu.Koda ganin
haka Sai Sarila tayi girgiza ta zama
guda arba'in
kuma kowace sarila da takobi a
hannunta tana
kare hare haren macijiyar tana maida
martani.Duk
da cewar takubban Sarila ta tsafi guda
talatin da
tara basa iya yiwa macijiayr illa saidai
karfin saran
nasu ya zama lugudan duka a
gareta.Nan take
macijiyar ta fusata ainun ita ma tayi
girgiza
kawunanta suka kara girma suka
ninka da sau uku
haka ma jelunan nata kuma ko ina a
jikinta yayi
mugun santsi,babu shiri duk su ukun
suka
dimauce damar data samu kenan ta
mammake su
da jelunanta.Saril a,Yazirina da
Mujahid suka yi
sama suka gwaru a jikin kogon dutsen
take kan
Sarila ya tsage ta fado kasa
sumammiya,Mujah id
ya karye a hannu ita kuma Yazirina ta
karye a kafa
kuma duk su biyun suka fado kasa a
matukar
galabaice suna numfarfashi ko kyakyawan motsi
babu wanda yayi a cikinsu batare su
sami damar
iya tashi.Nan take Aljana Marwis ta
nufo kansu su
ukun cikin matukar farinciki da
mugun nufi domin
tayi musu KISAN GILLA.Ba zato ba
tsammani sai
kawai taga Jarumi Darusi ya dako
tsalle ya dira a
gabanta ruke da takobinsa.Cikin
razana Marwisa
taja da baya sannan ta rikide izuwa
ainihin siffarta
ta dubi Darusi cikin alamun tsananin
tsoro da
kaduwa tace saboda me zaka hanani
kashe su
alhalin ina kan aiki nane na cika
umarnin
maigidana?Koda jin haka sai Jarumi
Darusi ya
daka mata tsawa yace saboda me
zaka salwantar
da sauran kwanakin rayuwarki a
banza kina cika
umarnin matacce wanda yanzu haka
ya dade da
rubewa a cikin karkashin kasa?Ki sani
cewa dake
da mai gidan naki duk kuna kan bata
ne
mabaiyani,ina mai umartarki daki
ajiye wannan
tsohon addinin naku na tsafi ki karbi
addinin
gaskiya wato addinin musulunci in ba
haka ba
kuwa yanzun nan zan kasheki na
kawo karshen
zaluncin ki a cikin wannan daji.Koda
Darusi yazo
nan a zancensa sai Aljana Marwisa ta
takarkare ta
bushe da dariyar mugunta lokaci guda
kuma saita
murtuke fuskarta ta dubi Darusi a
fusace tace kabar
ganin inajin tsoronka kayi zaton zaka
iya rabani da
addinin iyaye na da kakannina,akan na bar gadon
gidanmu gwara na rasa
rayuwata,kawai kayi
addininka nima nayi nawa.Kafin
Marwisa ta gama
rufe bakinta tuni Darusi ya tari
numfashinta yana
mai daka mata tsawa a karo na biyu
yace wannan
sulju ba zai taba yiyuwa ba tunda
nasan cewa har
abada ba zaki daina wannan zalunci
ba,idan na
barki na baki dama ki fada mini
hukuncin da kika
yanke na
™Abubakar Haleefah Physicist™
karshe zaki karbi addinin gaskiya ko
kuwa kin zabi
ki mutu ne?Koda jin wannan tambaya
sai Marwisa
tace waishin wanda ya mutu zai dawo
ne,ra'ayina
bazai taba sauyawa ba ina nan akan
addinina...Kafi n Marwisa ta gama
fadin abinda ke
bakinta tuni jarumi Darusi ya dako
tsalle cikin
bakin zafin nama da shammace ya
soka mata
takobinsa a makoshinta.Take takobin
ta faso bayan
wuyanta ta durkushe kasa bisa
guiwoyinta yayin da
jini ke kwaranyowa kasa bisa kirjinta
ta kame
kamar gunki domin tuni an zare ranta
ta zama
gawa.Koda ganin wannan al'amari sai
Mujahid da
Yazirina suka kamu da tsananin
al'ajabi duk da
cewar suna cikin mugun yanayi saida
suka
yunkura da kyar suka mike tsaye suka
kurawa
gawar Marwisa idanu suna mamakin
yadda kayi
Darusi yayi mata wannan kisa na farat
daya.Duk
wannan abu dake faruwa Sarila bata
farfado ba
daga suman da tayi,koda hankalin
Darusi yakai
kanta kuma ya dubi halin da Yazirina
da Mujahid
ke ciki ya tabbatar da cewar ba zasu
iya bata wani
taimako ba saiya dimauce bai san
sa'adda ya ruga
da gudu izuwa kanta Sarila ba ya
tallafo kanta ya
dubi raunin wanda baiyu zurfi ba
sosai a saman
kunnenta na hagu amma kuma bai
daina zubar da
jini ba.Cikin hanzari ya mike tsaye ya
ruga inda
dokinsa yake ya dauko jakar
guzurinsa ya budeta
ya fiddo zare da allurar dinke rauni ya
kama dinke
mata rauni sannan ya shafa wani
magani akan
raunin duk da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 14