samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
TASKAR AJALI 4
Littafi na hudu 4
Na Abdulaziz Sani m gini
Ebook creat by Shuraih Usman
Ebook publish by www.hausaebooks.cf
Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai
Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com
L
OKACIN da aka ruguntsume da Masifaffen Yaki
tsakanin Sarila dasu Yazirina ya zamana cewa sun kasa mai da mata da martani sai kokarin kare
kansu kawai sukeyi sai kare kan nasu ma ya
gagara.Shi kuwa Boka Matawus da sauran
dakarunsa na yaki sai suka zama yan kallo kawao suka tsaya suna ta kyalkyala dariyar farinciki.Shidai Boka Matawus hankalinsa dana dakarunsa ne ya
kwanata suka cika da dimbin farin ciki tunda sun tabbatar da cewar sun fita daga tarkon Sarila gashi ya cika alkawarin dake tsakaninsu ya kawota inda su Yazirina suke.Lokacin da Sarila taga ta kuntata Yazirina da Aljani Lafwas sai ta shammace su ta daka tsalle sama ta gabza musu wawan naushi da kafafunta biyu akan fuskokinsu saboda karfin
naushi saida kowannansu yayi katantanwa a tsaye sau uku suka kama layi zasu kife kasa,kawai sai Sarila ta sake gabzawa Aljani Lafwas mummunan
naushi a ciki ya sunkuya ya furzar da gudan jini daga bakinsa sannan tasa takobinta ta fille masa kai ya badi kasa matacce ko shurawar kirki bai yi ba.Ita kuwa Yazirina data fadi kasa magashiyan sai Sarila tasa kafarta guda ta take kirjinta ta dubeta tace maza ki gaya mini inda taswirorin nan guda biyu suke ko yanzun nan kema na karasa kashe
ki.Adaidai wannan lokaci tuni Mujahid ya fara zubar da hawaye bisa ganin halin da masoyiyarsa
Yazirina ke ciki domin numfashinta ma sama sama yake fita ga jini na yoyo ta hanci da bakinta,kawai sai sukaji Yazirina ta bude baki cikin matukar karfin hali ta bushe da dariya.Lokaci guda kuma ta
turbune fuskarta ta dubi Sarila tace ashe ma na cika wawiya mahaukaciya idan na gaya miki inda na boye wadannan taswirori guda biyu tunda
nasan cewa koda na fada miki ko ban fada ba
kashe ni zakiyi.Da jin wannan batu sai Sarila ta
sake fusata ainun tace aiko baki gaya mini inda kika boye su ba sai mun gano wajen da karfin
sihirin tsafi don haka idan ma kina da wata wasiya ta karshe ki fadi yanzun nan zan zare miki ruhin numfashinki.Yazirina ta sake bushewa da dariya a karo ba biyu tace wasiya ta kawai itace zan mutu da farin cikin sanin cewa na boye wadannan
taswirori a inda babu wanda zai iya daukosu har abada bare ya iya zuwa kogon Taskar Ajali ya
debo dukiyar mahaifina.Ba tsafi ba kome zakuyi kun rasa su kenan har abada kamar yadda nima
na rasa su.Koda jin haka sai zuciyar Sarila ta kama tafarfasa kamar zata kone kuma nan danan
idanunta suka kada sukayi jajur,kawai saita kwarara uban ihu mai tsananin firgitarwa ta daga takobinta sama ta kaiwa Yazirina mummunan sara da nufin
ta tsinke mata kai!Tuni Mujahid ya kurma uban ihu ya fashe da matsanancin kuka,kawai sai gani akayi wata takobi ta kare saran da Sarila ta kawo,wanda ke ruke da takobin kuwa kamar daga sama aka
jehoshi ya dira a gaban Sarila.Wani jarumi ne a cikin koren tufafi ya rufe fuskarsa da rawani
idanunsa kadai ake gani.Koda haduwar takobin
tasa data Sarila sai tartsayin wuta ya tashi gami da hayaki,babu shiri Sarila ta ja da baya tana mai gyara tsayuwarta kuma ta kura masa idanu suka
fara kallon kallo.A wannan lokaci ne Yazirina ta mike tsaye da kyar ta tofar da jinin dake cikin bakinta ta koma bayan bakon jarumin ta tsaya.Shi kuwa Boka Matawus kasa motsawa yayi saboda
kaduwa da mamaki domin a zatonsa duk duniya a
halon yanzu babu wani jarumi dazai iya gangancin tarar Sarila gaba da gaba.Mujahid kuwa daya ga Yazirina bata mutu ba saiya bushe da dariyar farin ciki.Bayan anyi kallo tsakanin Sarila da bakon jarumin sai ta dubeshi ta daka masa tsawa tace kai kuma waye kuma daga ina ka fito har da zaka zo ka shiga fadan da bai shafeka ba?Maza ka baiyana kanka ko yanzun nan kaima ka sheka
Barzahu.Kafin Sarila ta gama rufe bakinta tuni bakon Jarumin ya tari numfashinta yana mai cewa sunana Darusi Bin Sardus mai yaki da zalunci
kuma mai kokarin tabbatar da gaskiya bisa
karya.Burina shine haske ya mamaye dukkan
duhu,mutane su farga su daina bautar gumakan
banzan da shaidanun aljanu su koma bautar Sarki guda daya mahaliccin komai da kowa.Kuyi mini
bayanin makasudin wannan yaki a tsakaninku
domin nayi muku sulhu na baiwa mai gaskiya
gaskiyarsa.Koda jin wannan batu sai Sarila ta
bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ta
murtuke fuskarta ta dubi bakon jarumin a fusace
tace baka isa kasan komai ba dangane da wannan rigima kuma tunda dama na fuskanci kazo mana
ne da bakon addini to tabbas bani da makiyin
daya fika saboda haka yanzun nan zan gama dakai sannan na gama da wannan shashashar dake
bayanka.Sarila na gama fadin haka sai ta dako
tsalle a sama daga inda yake ta kawowa bakon
jarumin mummunan sara a kafadarsa da nufin ta
tsargeshi gida biyu.Cikin bakin zafin nama na
gaban kwatance sai gani akayi ya daga takobinsa ya kare saran,nanfa suka ruguntsume da
azababben yaki cikin matukar jarumtaka da
gwaninta ya zamana cewa suna kaiwa junansu
hare hare.Ko dakika ashirin ba'ayi ba da fara
wannan gumurzu Sarila ta fahimci cewar lallai yau ta gamu da gamonya domin kuwa kafin ta kaiwa
bakon jarumin sara guda daya shi ya kai mata uku kuma zafin namansa ya ninka nata sosai.Nan
danan ya fara kuntata mata domin sau uku yana
kadar da takobin hannunta ya tsirata da tasa amma sai yaki kasheta ya kara bata dama ta dauki
takobin tata su ci gaba da fafatawa.Da dai Sarila taga cewa tabbas ya fita iya yaki sai ta fara amfani da karfin sihirinta ta huro masa wata irin iska mai karfin gaske domin ta sure shi sama ta makashi da jikin wani dutse amma sai taga iskar ta kasa
daukarsa ta juya izuwa kanta ta sureta ta makata a jikin wata bishiya.Sarila ta fado kasa tim!a lokacin dataji kamar-
™Abubakar Haleefah Physicist™
kashin bayanta ya karye amma bata daddara ba
saita mike tsaye zumbur ta cigaba da watsawa
bakon jarumin mugayen abubuwa,saidai kaga
bishiyoyin dajin suna tunbukowa daga cikin kasa har jijiyoyinsu suna faduwa akan bakon jarumin.A lokaci guda sama da bishiya arba'in ne suke
tahowa da gudu izuwa kansa zasu makeshi amma
sai aga ya tashi sama ya bubbuge su sun ratattake sun zube kasa.Kai bama bishiyoyi ba har manyan duwatsu Sarila ta rinka watsa masa masu mugun
kwari da nauyi amma sai gashi bakon jarumin
yana naushin duwatsun da hannayensa da
kafafunsa suna farfashewa suna tarwatsewa tamkar da guduma ake bugunsu.Saboda tsananin
mamakin wannan jarumta ta bakon jarumi Boka
Matawus,Yazirina,Mujahid da wannan dakaru dubu na birnin yamein basu san sa'adda suka wangame bakunansu ba,idanunsu suka zazzaro kuma suka
kame tamkar gumaka.Lokacin da Sarila taga ta
jefawa bakon jarumin bishiyoyi da duwatsu domin ta hallakashi amma duk ya ragargajesu sai kuma ta watsa masa kibiyoyin tsafi masu dauke da mugun
dafi sama da guda dubu a lokaci guda,kawai sai bakon jarumin yayi amfani da takobinsa yayi dan tsalle sama kadan ya harde kafafunsa ya
tankwashe su tamkar a kan shimfida yake zaune
kuma ya rufe idanunsa ya rinka karkade kibiyoyin tsafin suna zubewa kasa a kakkarye ko guda daya bata taba jikinsa ba kuma bata samu damar
wucewa ba ta gabansa.Ita kanta Sarika saida ta razana bisa ganin wannan gagarumar jarumtakar
da yayi ta dan ja da baya a tsorace a lokacin da kibiyoyin tsafin nata gaba daya suka gama zubewa kasa.A sannan ne jarumin ya diro kasa bisa
kafafunsa har a sannan fuskarsa na rufe bai bude ta ba daga cikin rawani,kawai sai ya dubi Sarila cikin murmushi yace kin yakeni da makami bakiyi nasara ba,kin yakeni da sihirinki na tsafi
ubangijina ya bani kariya,yanzu kuma menene
sauran abin dogaron naki?Koda jin wannan
tambaya sai Sarila tayi jifa da takobinta kuma ta gyara tsayuwarta tana mai dunkule hannayenta
tace yanzu kuma zan jarraba tsagwaron karfin
damtsw na akan naka.Koda jin haka sai Jarumi
Darusi yayi murmushi yace ina mai shawartarki
daki gaya mini matsalar dake tsakaninki da
wadannan mutane da kuke yaki domin na sulhunta ku nayi tafiyata amma tabbas na zaki iya yin
galaba ba a kaina ba.Sarila ta girgiza kanta tace ai sai an gwada sannan ake sanin na kwarai.Kafin
Darusi ya kara cewa wani abu tuni Sarila ta dako tsalle daga inda take tsaye cikin shammace ta
kawowa Darusi naushi a fuskarsa da kafarta
guda.Cikin sa'a kuwa ta gabji bakinsa yayi baya taga taga kamar zai fadi amma saiya tsaya cak
lokacin dayaji dan radadi a kan lebensa na
kasa.Koda Darusi ya shafa leban nasa yaga jini saiya dubi Sarila yayi mata dan guntun murmushi kuma ya gyara tsayuwarsa ya yafito ta da hannu alamar cewa idan ta isa ta sake kawo masa
hari.Kash!rashin sani yafi dare duhu,tabbas inda Sarila tasan abinda zai biyo baya da batayi
gangancin sake kawowa Darusi hari ba domin
koda ta sake dako tsalle a sama ta kawo masa
wani wawan naushi da kafa sai a kaga yayi farat ya ruke kafartata da hannu daya take ya wulwulata a sama yayi mata hajijiya sannan ya makata a jikin wani dutse.Take hannunta na hagu ya karye ta
fado kasa sumammiya ta baje.Faruwar hakan keda wuya sai jarumi Darusi ya dubi Boka Matawus da dakarunsa yace ku kuma fa zaku jarraba naku
karfin ne a kaina?Dajin wannan tambaya sai Boka Matawus ya juya da sauri ya kama dokinsa ya
haye ya juya da baya ya zabureshi da gudu,take
suma dakarun nasa sukayi koyi dashi aka rufa masa baya.Adaidai wannan lokaci ne jarumi Darusi ya karasa inda Mujahid ke tsaye a daure cikin
sarkar tsafi,koda Mujahid ya shafi sarkar saita zagwanye ta zama ruwa,cikin kaduwa Mujahid ya
tsugunna kasa ya kama godiya amma ko kallonsa
Darusi baiyi ba saiya juya ya dubi Yazirina yace maza kije ki duba hannun wannan jarumar da tayi yaki dani ta karye ki gyara mata karayar.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta dubi Darusi cikin
matukar mamaki tace saboda me zaka ce naje na
taimaki abokiyar gabata wacce takeson ta hallaka ni?Me yasa kai ba zaka taimaketa ba da kanka?
Darusi yace mutum baya sani waye masoyinsa ko
makiyinsa muddin zuciyarsa na son
kowa,makiyinka baya daina kinka face ka taimake shi,dake da ita duk kuna cikin bata ne mabaiyani saboda haka inason na taimake kune na sanyaku a kan tafarki madaidaici.Watakila idan ta fardado daga suman da tayi zuciyarta tayi sanyi kuma ta cire duk abinda ke zuciyarta na mugunta a kanki saboda haka inason ki hanzarta yi mata magani
kamar yadda na umarceki.Koda jin haka sai
Yazirina ta dubi Mujahid shi kuma yayi mata
inkiyar tabi umarnin.Yazirina ta karasa inda Sarila ke kwance takai hannunta domin ta duba hannun
Sarila amma saita fasa ta waigo ta dubi Jarumi Darusi tace har yanzu baka bani amsar tambayata ta biyu ba,menene dalilin da yasa kai ba zaka
gyara mata karayar ba da hannunka?Kuma menene
yasa har yanzu kaki ka nuna mana fuskarka muga irin kamaninka?Lokacin da Jarumi Darusi yaji
wadannan tambayoyi guda biyu sai yai dan guntun murmushi sannan yace ni a addinina haramun ne
namiji ya taba jikin macen da bata kasance
muharramarsa ba face bisa lalura,abinda yasa
kuwa kiga naki baiyana fuskata a gareku shine
ubangijina yayi mini wata baiwa wacce ke kawo
matsala ga wasu jama'ar idan sun kalle ni,zaku iya ganin fuskata a wani lokacin anan gaba idan mun sake haduwa,maza ki gyara karayar hannun yar
uwarki kafin hannun ya kumbura?Koda jin haka sai Yazirina ta duba hannun Sarila da sauri take kuwa taga ashe lallai karyewar tayi,cikin hanzari ta umarci Mujahid yaje ya saro yan kirare sannan ta gyara
™Abubakar Haleefah Physicist™
karayar aka shafawa hannun magani kuma aka
daureshi da kararen.Gama hakan keda wuya sai
Darusi ya karaso garesu ya tsugunna dag dasu ya karanta wata addu'a ya tofa a kan hannun Sarila sannan ya dubi Yazirina yace da izinin ubangiji na
wannan karayar zata warke a cikin kwananki uku kacal kuma ba zata sake jin wani ciwo ba a
hannun.Koda gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya koma can gefe daya ya dauko wata sarewa ya
busata sau daya.Faruwar hakan keda wiya sai ga wani Doki daga nesa ya taho da gudu har saida
dokin yazo gaban Darusi sannan ya durkusa bisa guiwoyinsa,Darusi ya shafa kan dokin yace an
gaisheka Haidimul Dini,kawai sai Darusi ya bude wata jakar guzuri dake kan dokin ya dauko butar alwalarsa ta duma gami da farin buzu ya koma
gefe daya ya zauna ya kama yin alwala,bayan ya idar da alwalar sai ya hau kan farin buzun ya tayar da sallah,duk wannan abu daya faru wato Darusi yayi Yazirina da Mujahid sun kura masa idanu
kawai suna kallonsa cikin matukar mamaki.Ita
kuwa Sarila har wannan lokaci bata farfado
ba.Lokacin da Darusi ya fara sallah ne Yazirina ta matso daf da Mujahid tace yanzu menene abinyi?
Ga Sarila a sume har yanzu bata farfado ba shi kuma wannan bakon jarumi ya kama yin wata irin ibada wacce ni ban tana ganin irinta ba,ko waige bayayi bare ya kallemu yaga abinda mukeyi,baka zaton cewa zamanmu anan a haka yana da mugun
hadari?Ina ganin cewa zaifi mana alheri mu gudu kafin Sarila ta farfado ta kashe mu sannan ta
kwashe wadannan taswirori na jikina.Koda Yazirina tazo nan a zancentsa sai Mujahid ya girgiza kai alamar cewa bai yarda da shawarar ba da tazo da ita don haka saiya dubeta yace yanzu idan muka gudu ina zamuje?Babu inda zamu iya zuwa face
gidan yar uwarki Muznaira kuma kinsan laifin da mukayi mata mun sace kambunta na tsafi kuma
gashi an kashe shugaban dakarunta Aljani Lafwas a sanadiyyar mu,babu wanda zai iya karemu face wannan bakon jarumi.Duk inda muka shiga sai
Sarila ta kure mana gudu ta kashe mu kuma ta
dauke wannan taswirar taje ta cika burinta.Ni ina ganin cewa zaifi kyau mu jira jarumi Darusi ya gama ibadar tasa mu sanar dashi gaskiyar duk
al'amarin dangane da Taskar Ajali da dimbin
dukiyar dake cikinta wadda a kanta ne yanzu kowa hankalinsa ya raja'a domin yaga ya mallaketa.Koda Mujahid yazo nan a zancensa sai Yazirina ta daka masa harara tace amma dai bansan cewa baka da
basira ba sai yau,Kai wane irin wawa ne zaka
sanar da irin wannan gawurtaccen jarumi mai
tsananin karfin sihiri sirrin wannan dukiya ta mahaifina,ai yana jin komai shike nan ya sami
tsuntsu daga sama gasashshe.Abinda nakeso
dakai shine mu lallaba shi mu yaudare shi mu
numa kamar muna sha'awar wannan addinin
nasa.Kai idan ta kama mu karbi addinin nasa ma sai mu karba har ya rakamu izuwa can kogon
taskar Ajali,ina da tabbatar da cewar zai iya
karemu daga dukkan sharrin dake cikin dajin kuma kaga zai bamu kariya daga sharrin Sarila har
hannunmu yakai kan wannan dukiya,kawai sai mu
shammaceshi mu kashe shi.Yayin da Yazirina tazo nan a jawabinta sai Mujahid yaja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya sannan yace a rayuwata nayi karya sau ba adadi nayi yaudara da cin amana yafi sau dubu ba tare da shakkar komai ba amma
wannan karon ina tsaoron nayi karya ko yaudara ga wannan bakon jarumi,gaskiya ni zan karbi
addininsa bisa gaskiya kuma bazan yaudareshi ba amma idan ke kina ganin zaki iya tofa ban hanaki ba.A iya rayuwata ban taba ganin matsafin dayayi irin gagarumar jarumtakar da yayi ba a yau,lallai jikina ya bani cewa shi ba matsafi bane kuma lallai wannan gagarumar jarumtakar tazo masa ne daga
karfin da yafi karfin tsafi.Koda jin wannan batu sai jikin Yazirina yayi sanyi tayi shiru batace komai ba daga can kuma saita cakumo kwalar rigar Mujahid tace ka sani dai cewa wannan dukiya dake Taskar Ajali tawace nice kadai na cancanci na gajeta
saboda haka ban yarda ka sanar da wannan jarumi inda take ba koda kuwa zaka sanar dashi
komai.Mujahid ya gyada kai yace to shikenan nayi miki alkawari bazan sanar dashi ba to amma kuma idan ba'a sanar dashi ba ta yaya zai rakaki can din har ya kareki daga sharrin abubuwan dake kan
hanyar da kuma sharrin Sarila wacce ita ma na
tabbatar da cewar ba zata taba janye manufarta ba akan mallakar wannan dukiya ta Taskar Ajali?Koda jin wannan tambaya sai Yazirina tace kada ka
damu ai hanyar kashe makahon kare ba wuya
gareta ba ni nasan abinda zanyi kawai ka zuba
mini idanu.Gama fadin hakan keda wuya sai Sarila ta farfado daga dogon suman da tayi,koda ta bude idanunta ta tsinci kanta kwance a kas a gefe daya ga hannunta na dama a daure cikin karare alamar cewa ta kuma ga Yazirina da Mujahid a can gefe daya sun kura maya idanu.Jarumi Darusi kuma na zaune bisa buzu kusa dasu ya idar sa Sallah yana shafa addua'a sai takaici ya turnuketa ta kamu da tsananin bakin ciki ba don komai ba sai saboda yaune karo na farko da'a ka sami jarumin daya
samu lagonta tundaga ranar data fara gumurzu da mazaje.Nan take kwallar takaici ta ciko a cikin idanunta ta yunkura ta mike tsaye da kyar ta tako kafafunta tazo gaban jarumi Darusi,kawai sai ta sake yunkurawa da nufin ta dokeshi da kafarta
amma sai taji kafar tata ta sage wani irin mugun
zugi ya shigeta bata san sa'adda ta kwalla ihu ba ta fadi kasa.
Bata san sa'adda ta kwalla ihu ba
ta fadi
kasa.Al'amarin da yayi matukar
baiwa su Mujahid
mamaki kenan,shi kuwa Jarumi
Darusi bai ma san
abinda takeyi ba har saida ya
gama shafa
addua'arsa sannan ya juyo.Koda
yaga Sarila ta
farfado harma ta zo kusa dashi sai
ya dubeta yace
to yake wannan babbar jaruma
shin kece zaki fara
yi mini bayanim abindake
tsakaninku da wadancan
abokan fadan naki ko kuwa sune
zasu fara.Ni
yanzu alkali ne kawai a tsakaninku
mai son yi
muku sulhu.Koda jin wannan batu
sai Sarila ta
dubi Darusi cikin irin murmushi
wanda yafi kama
dana yaudara tace tsakanin ni dasu
duk wanda ya
fara bayani daya ne babu laifi
kawai dai abinda na
sani shine dole ne ko ni ko su a
sami wanda zaiyi
maka karya alhalin kuwa na
fuskanci cewa kai
baka karya kuma baka son muyi
karya.Darusi ya
gyada kai yace tabbas abinda kika
fada gaskiya ne
kuma nayi matukar jin dadin
bayanin naki to amma
ki sani cewa su alkalai Allah ya
basu ilmi na
fahimtar gaskiya da akasinta da
izinin ubangijina
daga bayananku zangane wanda
ya fadi gaskiya da
wanda yayi mini karya don haka
yanzu zan fara
sauraron naki bayanin saiki
fara.Sarila tayi gyaran
murya tace Da ni da waccan duk a
hannun Boka
Guda muka taso ni tsintata yayi ya raineni ita kuwa
'yarsa ce ta cikinsa,kafin
mutuwarsa ya adana wata
dukiya mai tsananin yawan da
babu kamarta a
cikin wannan duniya a wani
boyayyan wuri kuma
ya zana taswira ta zuwa wannan
wuri har guda uku
kuma dole sai an hada wadannan
taswriro guda
uku a waje guda sannan taswirar
zatayi
aiki.Taswirar ta farko ya zanata ne
a kan gadon
bayana barima ka gani.Koda fadin
haka sai sarila
ta yunkura zata cire rigarta amma
sai Darusi yayi
sauri ya rike hannunta ba tare
daya tanka ba yace
a'a dakata ba sai na gani ba cigaba
da
bayaninki.Sarila tayi murmushi
tace ragowar
taswirorin guda biyu akan fatar
dabba ya rubuta su
kuma yanzu haka suna hannun yar
uwan nan tawa
Yazirina ta boye su,dani da ita da
dukkan manyan
sarakunan duniya bamu da burin
da yafi muje inda
wannan dukiya take mu mallaketa
saboda duk
wanda ya mallaketa tamkar ya
mallaki duniyar nan
ne kaf,bisa wannan dalili ne take
so ta kashe ni ta
kwafe taswirar dake zane bisa
gadon bayana ni
kuma nakeson na kasheta na
kwashe taswirorin
dake hannunta,na gama nawa
jawabin saika
saurari nata sannan kayi mana
hukunci bisa adalci
amma kafin nan inason na roki
wata alfarma guda
daya a wajenka.Alfarmar kuwa
itace bayan kayi
mana shari'a kafin mu rabu inason ka bude
fuskarka domin naga kamannin
jarumin daya fini
karfin damtse,iya yaki da karfin
sihiri saboda har
abada bazan taba mancewa dakai
ba kuma sa na
zana fuskarka da kirar jikinka na
ajiye a cikin
kundin tarihin rayuwata.Lokacin da
Sarila tazo nan
a zancenta sai jarumi Darusi yace
bazan iya
baiyana fuskata ba ga kowa a
wannan nahiya taku
face na kammala abinda ya kawo
ni.Koda gama
fadin hakan saiya juya ya fuskanci
Yazirina yace to
kinji bayanin yar uwar taki yanzu
kuma kece zakiyi
naki bayanin kin kuma amince da
duk abinda yar
uwar taki ta fada gaskiya ne babu
gyara,ba sai
kince komai ba kawai zan zartar
da hukunci
nane.Caraf sai Yazirina tace a'a
abinda ta fada
akwai karya da yawa a cikinsa da
ita da manyan
sarakunan duniya suna son su
mallaki wannan
dukiya ne saboda kawai su ci gaba
da zalunci a
doron kasa,ni kuwa wannan dukiya
tawace gado
nane zan mallaketa ne don
amfanin kaina ni
kadai.Koda jin haka sai Jarumi
Darusi yace ai
kema ba adala bace kin zama
azzaluma
kamarsu,duk dan adam din da
yake son dukiya mai
tsananin yawa irin wannan don
amfanin kansa shi
kadai bazai taba zama mai tausayi
dajin kai
ba.Waishin abin tambaya anan
shine shi kansa
mahaifin naki ta yaya ya tara
wannan dumbin
dukiya?Koda jin wannan tambaya
sai jikin Yazirina
yayi sanyi ainun tayi shiru ta kasa
cewa
komai.Jarumi Darusi yayi gyaran
murya sannan
yace shari'ar da zanyi muku itace
daga yau na
hana yaki a tsakaninku tunda a
kan taswirar zuwa
kogon taskar ajali kukeyi.Indai
kogon Taskar Ajali
kukeson zuwa ni nasan hanyar da
za'a bi aje can
din kuma ina mai tabbatar muku
da cewa na shiga
har cikinsa kuma na fito da raye
cikin koshin lafiya
ba tare da wani abu ya taba
lafiyata ba.Koda jin
wannan batu sai Sarila,Yazirina da
Mujahid suka
zazzaro idanu suka kurawa Darusi
idanu cikin
alamar rashin yarda.Koda hanin
haka sai Mujahid
yayi murmushi yace na fuskanci
cewa baku yarda
da wannan labarin dana baku ba
tunda kuna
mamakin cewa na sgiga cikin
kogon taskar Ajali
na fito a raye.To me yasa bakuyi
mamakin irin
abubuwan danayi ba na jarumtaka
da al'ajabi a
gabanku ya zamana cewa sihirin
tsafinku ya kasa
tasiri a kaina?To ku sani ni
ubangijina ne yake
bani taimako da kariya a kan
dukkan al'amarina ni
ba dukiya ce a gabana ba ko mulki
abinda yake
gabana kawai shine ubangijina da
addinina,kuyi
mini alkawari cewa zaku karbi
Addinina idan na
raka ku har cikin kogon Taskar
Ajali kuka sami
wannan dukiya.Koda jin wannan
tambaya sai Sarila
da Yazirina suka kalli junansu
sannan suka kallo
Mujahid aka rasa wanda zaice wani
abu.Darusi
yace idan kun yarda da hakan
akwai sharadi guda
daya,sharadin kuwa shine zaku ceci
kanku da
karfin damtsenku,iya yakinku da
karfin
sihirinku,bazan taimake ku ba face
naga zaku rasa
rayuwarku ko dukiyarku.Koda jin
wannan batu sai
Sarila ta numfasa tace bari muyi
shawara tukunna
tana gama fadin hakan saita mike
tsaye ta karasa
inda Yazirina da Mujahid suke ta
jasu izuwa gefe
daya.Sarila ta dubi Yazirina tace
yaya kike gani
shin kin yarda da tayin da Darusi
yayi mana?Idan
kin yarda akwai matsala daya,
matsalar kuwa itace idan har muka
karbi Addinin
Darusi tofa zamu mallaki wannan
dukiya ne kawai
amma ba zamu sami sihirin dake
jikinta ba na
mallakar duniya gaba
dayanta,saboda tsafi da
addinin Darusi basa haduwa a waje
guda.Koda jin
wannan batu sai hankalin Yazirina
ya DUGUNZUMA
tace to menene amfanin duk
wahalar da mahaifina
yasha kenan wajen tara mini
wannan dukiya da
sihirceta,yayi ne domin na sami
daukakar da tafi ta
kowa a duniya bana bakin ciki
kema ki amfani
wannan dukiya tunda baki san
kowa ba a duniya
face mahaifina,shine uwa da uba a
gareki to amma
ta yaya zamu ci gajiyar wannan
gagarumin aiki da
mahaifina yayi mana idan har
zamu karbi addinin
wannan bakon jarumi?Koda
Yazirina tazo nan a
zancenta sai Sarila ta dubi Mujahid
tace kai meye
shawarka?Mujahid yace ai ni
tuntuni na nuna
muku ra'ayina akan wannan bakon
jarumi daga
yanzu zuwa ko yaushe zan iya
karbar addinin
nasa.Koda jin haka sai Sarila ta
murtuke fuskarta
ta dakawa Mujahid harara tace kai
ba abokin
shawarar mu bane bamu wuri nayi
shawara da yar
uwata.Cikin sanyi jiki Mujahid ya
tafi ya
barsu.Tafiyarsa keda wuya sai
Sarila ta dubi
Yazirina tace zamu jefi tsuntsu
biyu ne da hoge
daya,zamuje Taskar Ajali da
taimakonsa kuma
zamu yaudareshi a matsayin zamu
karbi addinin
nasa,da zarar mun isa can din
saimu shammace
shi mu kashe shi kinga kenan ba
zamu bar aikin
baba ya tafi a banza ba.Duk da
newa nice gaba
dake a shekaru nayi miki alkawarin
cewa indai
muka sami wannan nasara zan
zama karama kece
babba kuma zan zamo mai
biyayya a gareki.Koda
Sarila tazo nan a zancenta sai
Yazirina tayi shiru
tana tunani da nazari har izuwa
tsawon yan dakiku
sannan ta dago kai ta dubi Sarila
tace na amince
da hakan amma bisa sharadi
guda,sharadin kuwa
shine ni ba zan sa hannu akan
batun kashe
wannan bakon jarumin ba ba bar
miki komai a
hannunki.Sarila najin haka sai ta
kamu da tsananin
farinciki tace na yarda da
hakan.Nan take su biyun
suka dunguma sukaje wajen
jarumi Darusi Sarila ta
dubeshi tace mun yarda zamu
karbi addininka
muddin ka kaimu Taskar Ajali.Koda
jin haka sai
Shima Jarumi Darusi ya kamu da
matukar farinciki
kuma ya amince akan su ci gaba
da yin wannan
tafiya gaba daya tare.Ba tare da
bata wani lokaci
ba kowa ya shiga shirin tafiya,saida
kowa ya
kammala tsaf sannan Sarila ta dubi
Jarumi Darusi
tace tunda kai ne kasan hanya sai
ka wuce gaba
kayi mana jagora amma inaso ka
gaya mana yanzu
daga nan zuwa can kogon taskar
ajali tafiyar
kwana na wace?Koda jin wannan
tambaya sai
Jarumi Darusi yayi murmushi yace
ai ba batune na
kwana nawa ba saidai kice na wata
nawa ne,a kalla
sai mun shafe wata bakwai muna
tafiya ta cikin
mugayen dazuzzuka,manyan
birane kuwa guda
uku ne a gabanmu kuma a kowane
birni akwai
wata mummunar masifar data
addabesu,dama na
kudurce a raina cewa zan
taimakesu basai na
dawo saboda dama nasan cewa
burina bazai taba
cika ba a wannan nahiyar face
nazo na riske
ku.Koda Jarumi Darusi yazo nan a
zancensa sai
hankalin Sarila,Yazirina da Mujahid
ya dugunzuma
ainun ba don komai ba sai bisa jin
doguwar tafiyar
dake gabansu har ta kimanin
tsawon watanni
bakwai da irin masifun da zasu
fuskanta a kan
hanyar tasu,uwa uba kuma sai
batun garuruwa
ukun da sukaji cewar dole sai sunbi
ta cikinsu
kuma akwai bala'in da yake
damun garuruwan uku
wadanda jarumi Darusi keson
magance su.Cikin
alamun tsananin damuwa Yazirina
ta dubi Mujahid
tace kai ni fa na fara sarewa wai
shin ma menene
tabbacinmu cewar zamu tsira da
rayukanmu a
cikin wannan tafiya,lallai kowa yaci
zomo yaci gudu
kuma babu wani abu da mutum
zai samu a
saukake a cikin wannan duniya ba
tare daya sha
wuya ba,ni kam sai yanzu na gane
cewa mahaifina
ya yanka mana KAZAR WAHALA
wacce gata ta
zame mana dole mu figeta.Hakika
duk wanda bai
damu da abubuwa uku ba a cikin
duniya daya
gama morewa,abu na farko shine
mulki,sai
Dukiya,sai kuma na ukunsu wanda
ba sai na fada
ba.Koda Yazirina tazo nan a
zancenta
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 14