Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
dajin amma shiru bata ga su Mujahid ba ko alamar su bata gani ba.Haka tayi gabas da yamma,kudu da arewa ta karkade ko ina a cikin dajin bata ga ko wane abu dazai nuna alamunsu ba.Kawai sai Sarila ta tsuguna a kasa ta daga kanta sama tana mai wangame bakinta ta kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba daya da amsa kuwa,sautin ihun saida yakai har cikin ko ina a birnin na Yamein,kuma ya firgita duk wani abu mai rai tamkar zaki ne yayi ruri a tsakiyar kasuwa.Ba komai ne yasa Sarila tayi wannan mugun ihu ba face tsananin bakin ciki bisa ganin cewa su Mujahid sun bace mata da gani kuma bata san a inda zataje ta same su ba.Kawai sai Sarila ta fashe da kukan takaici kuma ta shiga tunanin abinda ya kamata tayi. *Al'amarin Mujahid kuwa lokacin daya shigo cikin wannan sarkakiya goye da Yazirina a guje yana waigen bayansa cikin tsananin tsoro sai kawai yaji kafarsa ta zurma cikin wani rami take ramin ya karawa kansa fadi suka fada cikinsa shi da Yazirina tamkar an je fasu a cikin RIJIYA mai zurfin kamu DUBU don haka bai san sa'adda ya kurma uban ihu ba saboda tsananin razanar da yayi kuma yadda yaji suna ta cigaba da fadawa cikin karkashin kasa.Ashe suna fadawa cikin wannan ramin sai ramin ya cike da kansa daga sama,ciyawa mai huduwa tayi tofo a daidai inda ramin yake,Sarila tazo ta wuce ta kansa da gudu bata ma san cewa rami bane a wajen.Kwatsam sai Mujahid yaga sun fado tsakiyar wata kasaitacciyar fada amma babu kowa a cikin fadar face wata mace yar kimanin shekaru talatin da shida zaune bisa KARAGAR MULKI fuskarta cike da ANNURI.Kallo daya mutum zai yiwa matar ya san cewa ta cika hatsabibiyar bokanya,matar ta dubi Mujahid cikin murmushi a lokacin da yake tsaye bisa kafadunsa goye da Yazirina wacce har a sannan bata farfado ba daga dogon suman da tayi kuma jini bai daina diga ba daga jikin raunin kanta dana kirjinta,tace,Lale marhaban da sarkin barayin wannan zamani kuma yaro DAN BAIWA Mujahid Ibin Assudusi,kayi sani cewa rayuwar abokiyar tafiyarka na cikin mugun hadari sakamakon raunika biyun da Sarila tayi mata amma zan iya ceto rayuwarta a yanzu idan ka amince da sharadina.Cikin rawar jiki da rawar murya Mujahid yace ni bama sainaji sharadinki ba na amince kawai ki hanzarta ceto rayuwarta.Koda jin haka sai matsafiyar ta bushe da dariyar murna nan take ta tafa hannnunta sai ga wadansu kuyangi guda hudu sun shigo cikin fadar.Da zuwansu sai suka kama Yazirina suka sauketa daga bayan Mujahid suka yunkura zasu tafi da ita izuwa cikin daki amma sai Mujahid ya tsaida su yace dole a tafi tare dani duk inda za akai Yazirina.Koda jin haka sai Matsafiyar tace shin ka manta ne cewa Yazirina bata son wani da namiji ya taba jikinta bare yaga tsiraicinta.Dole ne a cire gaba daya rigar dake jikin Yazirina kafin a iya yi mata magani.Mujahid ya numfasa yace zancen yaushe kuma tunda na goyata ma a bayana tsawon lokaci ina gudu da ita bata ma san a halin da take ba,idan har kin matsa baza aje dani daki da za ayi mata magani ba to ina son na cire jakarta ta guzuri daga jikinta na ajiye mata har izuwa lokacin da zata dawo cikin haiyacinta.Koda jin wannan batu sai matsafiyar ta tuntsire da dariya a karo na biyu sannan ta nutsu tace ai babu abinda zanyi da taswirori biyun da take cikin jakar Yazirina tunda kamar ka bani tuwo ne babu miya.Duk wanda ya mallaki wadannan taswirorin guda biyu ba tare daya mallaki ta ukun ba wacce aka zana akan gadon bayan Jaruma Sarila tamkar an bashi kyautar mutumin mutumi da bazai iya yi masa aikin komai ba.Toofah!!!Wata sabuwa su Yazirina sun fada hannun wata Matsafiya.Nima dai mamakin yadda wannan matsafiya ta gina fada a karkashin har ta ceci su Yazirina ta kubutar dasu daga Zaluncin Sarila yasa nace bari idan tsaya anan saboda al'ajabi.Bazai iya yi masa aikin komai ba.Samun wannan Taswirar dake bayan Sarila yafi komai wahalar samu a wannan duniya a yanzu,zamuyi maganai mai muhimmanci nan gaba bayan Yazirina ta dawo cikin haiyacinta kuma zaka iya daukar jakar guzurin daga jikin Yazirina.Take Mujahid ya dauki jakar ya rataya ta a kafadarsa su kuwa wadannan kuyangi hudu sai suka tafi da Yazirina suka shigar da ita cikin wani daki suka kwantar da ita akan gado sannan suka shiga aikin gyara raunikan jikin nata saida aka dinke raunikan duka biyun sannan aka shafa mata magani a kansu.Bayan nan sai kuyangin suka mayar da rigar Yazirina izuwa jikinta suka suturceta suka fice daga cikin dakin suka barta ita kadai.Da ma Mujahid na zaune a fadar tare da matsafiyar an kawo masa abinci da abin sha na alfarma yana ci kuma suna hira.Koda yaga wadannan kuyangi hudu sun fito daga cikin dakin da suka kai Yazirina sai ya dubesu yace shin zata rayu kuwa?Shugabar kuyangin da dubi Mujahid cikin murmushi tace ka kwantar da hankalinka mun tsayar da jinin dake zuba a jikinta kuma mun shafa mata magani,nan da cikar kamar sa'a biyu zata fardado.Koda jin haka sai murna ta kama Mujahid ya koma kan kujerar da yake zaune ya dubi matsafiyar yayi mata godiya sannan yace wai shin menene sunanki kuma menene dalilin da yasa kika gina fadarki anan cikin karkashin kasa? Tabbas na gamsu cewa kin cika hatsabibiyar bokanya tunda har Sarila ta kasa gano nan din,da ace ta gano da tuni yanzu ta shigo ta gama damu gaba daya ta karbi abinda take farauta a wajen Yazirina.Koda Mujahid yazo nan a zancensa sai matsafiyar ta kyalkyale da dariya sannan tace da farko sunana Muznaira bin Salmara.Nima 'yace a wajen marigayi Boka Salmara mahaifin Jaruma Yazirina.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya mike tsaye zumbur cikin tsananin mamaki ya dubeta yace ya akayi kika zama yar boka Salmara alhalin ance bai taba aure ba kuma bai taba haihuwa ba,ita kanta Yazirina har ya bar duniya bai san da cikinta ba.Koda jin wannan tambaya sai Hawaye ya zubowa Muznaira tace tabbas abinda ka fada gaskiya ne amma ka sani cewa kafin Boka Salmara ya fara neman Basma mahaifiyar Yazirina saida ya nemi mahaifiyata da tazarar shekaru ashirin tun sa'adda ma yake matashin saurayi babu yadda mahaifiyata batayi ba akan Salmara ya aureta amma sai yaki.Karshen ma da duka da wulakanci irin na rayuwar bariki suka rabu a takamaimai ma saida yayi mata dukan KAWO WUKA ya farfasa mata jiki ya barta a kwance jina jina yayi tafiyarsa.A zatonsa ma tuni ta dade da shekawa Barzahu.Saboda bakin cikin wannan abu da Boka Salmara yayi matane yasa bayan ta kwana talatin da uku a kwance tana jinya tayi hijira daga garin ta koma wata nahiya dabam,shi kuwa Boka Salmara daya daina jin duriyarta sai yayi zaton cewa ta mutu an rufe bakinta.A can nahiyar birnin Hindu mahaifiyata ta sauka a gidan wani attajiri ta kama yi masa aikin bauta,dama attajirin ya taba haduwa da zaluncin Boka Salmara ya kwaci dukiya mai yawa a hannunsa sa'adda sukayi wani kasuwanci bisa wannan dalili ne attajirin ya tausayawa mahaifiyata kuma ya cigaba da kyautata mata.Bayan sati biyu ne mahaifiyata ta gane cewa tana dauke da juna biyu na Boka Salmara,Al'amar in daya jefata cikin tsananin bakin ciki kenan ta fashe da matsanancin kuka.Koda Attajirin ya dawo gida yaga halin da take ciki na bakin ciki sai ya tambayeta dalili,ba tare da boye komai ba ta sanar dashi cewa ta gane tana dauke da juna biyun boka Salmara kuma lallai sai ta lalata wannan juna biyu.Koda jin wannan batu sai Attajirin ya bushe da dariyar farin ciki.Lokaci guda kuma ya nutsu ya dubi mahaifiyata yace ai ba zaki zubar da wannan ciki ba saboda shine kadai makamin da zaki iya yakar Boka Salmara dashi ki DAUKI FANSAR abinda yayi miki,nima nayi RAMUWAR GAIYA,kiyi sani cewa binciken danayi akan Boka Salmara duk matar daya sadu da iya indai ta sami juna biyu dashi sai ta sami duk irin sirrikan tsafin dake jikinsa haka ma abinda zata haifa zaizo duniya ne a tsume cikin irin TSUMIN TSAFInsa.Lallai zamu reni abinda zaki haifa har izuwa lokacin da za kwashe gaba daya dukiyar da Boka Salmara ya tara wacce a halin yanzu babu wani attajiri da yake da kamarta a cikin gaba daya fadin wannan duniya,idan har muka sami nasarar hakan tofa sai bakin ciki ya kashe Boka Salmara.Da ransa yana ji yana gani zai dawo matsiyaci kuma yalaka fitl wanda bashi da abinda zai ci sai yayi bara.Yayin da Attajirin yazo nan a jawabinsa sai farin ciki ya lullube mahaifiyata har ta kaisu ga yin aure a cikin kwanaki kadan.Don haka lokacin da cikin mahaifiyata ya tsufa aka haife ni sai jama'a suka dauka cewa ni 'yar wannan attajiri ce.Tun banfi shekara shida ba a duniya gaba dayan mutanen birnin hindu suka tsorata da al'amarina bisa gani irin abubuwan al'ajabi da nakeyi na tsafi,sai dakai cewa hatta sarkin Hindu na wannan lokaci wato mahaifin Sarauniya Iklaira bin Aslam ta yanzu yana matukar tsorona yana y mini biyayya kuma yana aiko mini da dukiya mai yawa a karshen kowane wata guda.Attajiri da mahaifiyata kuwa kullum suna dorani a kan TAFARKIn kassara Boka Salmara suna nuna mini cewa bani da makiyin daya fishi a doron kasa.Bisa binciken danayi a hallarar tsafina ne na gano cewa bazan taba iya sace dukiyar Boka Salmara ba har sai bayan mutuwarsa kuma sai yar uwata Yazirina ta baiyana mun hada kai NI da ITA mun kashe Jaruma Sarila mun kwafe taswirar dake bayanta mun hada da ragowar taswirorin dake wajen Yazirina.Koda Bokanya Muznaira tazo nan a jawabinta sai Mujahid ya sake kamu da tsananin mamaki gami da fargaba ya dubi ™Abubakar Haleefah Physicist™ Muznaira cikin alamun firgice yace ta yaya kike zaton cewa Yazirina zata yarda da duk wannan labari da kika bani yanzu kuma ta yaya zata amince ku hada kai domin ku mallaki wannan dukiya tare?Ashe kenan RABA DAIDAI zakuyi tunda dai kinason sace dukiyar ne domin ki dauki fansa akan Boka Salmara saidai ki hakura tunda babu sauran DAUKAR FANSA akan matacce.Koda Mujahid yazo nan a jawabinsa sai Muznaira taja dogon numfashi gami da ajiyar zuciya sannan tace banda batun daukar fansa wadda ke gabana akwai batun tunanin ceto rayukan miliyoyin jama'a.Idan na bar Yazirina ta mallai wannan dukiya dake can TASKAR AJALI ita kadai zatayi irin zaluncin da sauran sarakuna da sauran matsafi keson yi ya kasance su kadai ne da makusantansu kejin dadi a cikin wannan duniya.Ni burina shine jin 'KAI,TAUSAYI da TAIMAKO kamar yadda kai ma zuciyarka ta kansace mai imani,inai mai tabbatar maka da cewa Yazirina bata da wani wabi wanda yafi ta hada kai dani domin inda da abu na biyu wanda take nemansa ruwa a jallo.Koda jin haka sai Mujahid ya sake kamuwa da mamaki yace ke kuwa menene wannan abu? Muznaira tayi murmushi tace bazan fada kome nene basai a gaban Yazirina dake kwance domin bana son ta farka bata ga jakar guzurinta ba a kusa da ita don zata iya yi min hauka a cikin fadata idan bata ganta ba.Koda jin haka sai Mujahid yayi murmushi ya mike tsaye ya nufi cikin dakin.Da shigar Mujahid cikin dakin sai ya duro kofar dakin ta kulle sannan ya zauna akan wata kujera dake daf da Yazirina ya kura mata idanu.Nan take yaji ya kamu da tsananin sonta saboda dimaucewa dayayi da ganin kyawun da Allah ya bata.Abinda ya daure masa kai kenan shi kansa domin a rayuwarsa bai taba gani wata 'ya mace da yaji yana son taba sai ita.Saida Mujahid ya dauki lokaci mai tsawo yana ta kallon Yazirina har ya tafi duniyar tunani inda ya tsinci kansa a cikin wani kasaitaccen lambu tare da Yazirina a zaune suna hirar soyayya cikin nishadi.Kwatsam sai yaji tarin Yazirina ta farka a firgice a razane tana mai mikewa zaune.Koda ta bude idanunta tayi arba da jakar guzurinta a kafadar Mujahid sai yai wuf ta suri jakar ta bude ta leka cikinta,kawai sai tayi ajiyar zuciya cikin alamun samun nutsuwa sannan ta dubi gabas da yamma kudu da arewa ta dubi Mujahid kuma ta shafa raunin kanta taji an dinke shi ta shafa raunin kirjinta shima taji an dinke shi kawai tace ina ne nan kuma ya akayi muka zo?Kafin Mujahid ya budi baki yace wani abu sai sukaga an turo kofar dakin an shigo,ba wani bane ya shigo ba face bokanya Muznaira.Koda ta hada idanu da Yazirina sai Yazirina ta mike tsaye zumbur ta kura mata idanu cikin mamaki ba don komai ba sai saboda ganin yadda suke matukar kama da junansu.Nan take Muznaira ta gabatar da kanta a wajen Yazirina ta kwashe labarinta kaf ta zaiyane mata sannan ta kwaye hannun rigarta saiga kambun tsafin Boka Kaisu Bin Alkama,Muznaira ta dubi Yazirina tace yake yar uwata na sani cewa kina neman wannan kambun tsafi na boka Kaisu ruwa a jallo saboda shi ne kadai abinda zai kare ki daga sharrin jaruma Sarila to nafi wata biyu da sato shi a can fadar Boka Kaisu,ina mai tabbatar miki da cewa ni kadai ce zan hada karfina da naki mu sami nasarar kashe Sarila mu kwafi wannan taswirar dake kan gadon bayanta sannan mu tafi izuwa TASKAR AJALI mi debo dukiyar ubanmu Boka Salmara.Idan har kin amince zaki hada kai dani bisa aminci da alkawari lallai burinmu zai cika,koda jin wannan batu sai idanun Yazirina suka zazzaro suka kama kallon juna ita da Mujahid ta rasa abinda zatace. SHIN YAZIRINA ZATA AMINCE TA HADA KAI DA MUZNAIRA SU TAFI ZUWA TASKAR AJALI TARE...? WACE IRIN MUMMUNAR BARNA SARILA ZATA CIGABA DAYI A KOKARIN NEMAN YAZIRINA? WANE IRIN MATAKI SAURAN BOKAYE DA MANYAN SARAKUNAN DUNIYA ZASU DAUKA AKAN SARILA DA YAZIRINA? WAISHIN MUJAHID NE BAKON SAURAYI DAN BAIWA DA ZAI IYA TAIMAKON YAZIRINA KO KUWA WANI NE DABAM WANDA BAI BAIYANA BA? YAUSHE NE ZA'A TAFI IZUWA KOGON TASKAR AJALI KUMA WADANNEN IRIN MASIFU DA BALA'I NE AKAN HANYAR? SHIN MUJAHID ZAI NUNAWA YAZIRINA SOYAYYARSA A GARETA? IDAN YA NUNA MATAN ZATA KARBESHI KUWA? Mu hadu A Taskar Ajali Littafi na Uku don jin cigaban wannan labari.Amma mene hasashen ku? Nima da wannan nake ce muku sai mun hadu a Littafi Na Uku.TASKAR AJALI Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI 3 Littafi na Uku 3 Na Abdulaziz sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com Lokacin da Yazirina ta kama raba idanu tsakanin Bokanya Muznaira da Mujahid ta rasa abinda zata ce bisa hadin kanta da Muznaita.Koda Muznaira taga haka sai ta kyalkyale da dariya a lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta ta dubeta cikin nutsuwa tace yake yar uwata kiyi sani cewa baki da wani cikakken lokaci nayin dogon tunani bisa wannan al'amari kuma baki da wata mafita a cikin wannan matsala face ki bani hadin kai tunda a halin yanzu rayuwarki na cikin mummunan hadari,ki tuna cewa Sarila na farautarki haka kuma manyan bokaye da manyan sarakunan duniya suna farautarki ruwa a jallo.Ba karamar sa'a kikayi ba da kuka fado hannuna ba amma da tuni taku ta kare,na baki tsawon kwanaki uku kiyi tunani da shawara keda abokin tafiyar taki,da gama fadin hakan sai Muznaira ta juya ta fice daga cikin dakin tana mai jan kofa ta rufeta.Faruwar hakan keda wuya sai Yazirina ta dubi Mujahid tace me ka gani don game da al'amarin wannan matar? shin ka amince mu hada kai da ita?ka sani cewa ni a halin yanzu duk fadin duniyar nan mutum daya ne jal zan iya bashi yardata.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya dubi Yazirina cikin mamaki yace wanene wannan mutum wanda zaki iya bashi yardarki? Sa'adda Yazirina taji wannan tambaya sai tayi dan gutun murmushi ga Mujahid tace shine wanda ya ceci rayuwata daga hannun Sarila a yau din nan,in ba don shi ba da tuni yanzu na zama tarihi.Koda jin wannan batu sai Mujahid yayi murmushi yace a'a ba ni bane na ceci rayuwarki yar uwarki ce Muznaira ta cece mu gaba daya ta zukomu izuwa nan cikin gidan da karfin sihirin tsafinta.Yazirina tace amma ai ni ba don ka goya ni ba a bayanka kayi wannan azababben gudu ba na ban al'ajabi da ita ma bata sami nasarar cetonmu ba yakai abokin tafiyata kuma amintaccena,kayi sani cewa duk da Muznaira ta kasance yar uwata zuciyata bata aminta da ita ba domin ina ganin cewa a karkashin zuciyarta akwai wata muguwar nufin wadda tasa lallai take son mallakar wannan dukiya ta mahaifinmu shi yasa take neman hadin kaina,ni yanzu babban tashin hankali na shine bansan iyakar adadin rayukan da Sarila zata salwantar ba a kokarinta na farautata,kaga kenan buyana a wani wuri dominta bazai haifar da komai ba face karin asarar rayuka da dimbin dukiya,ya kamata lallai musan hanyar da zamubi mu fuskanceta domin muga karshenta mu kwafe wannan taswirar dake zane a kan gadon bayanta.Koda Yazirina tazo nan a jawabinta sai hankalin Mujahid ya dugunzuma ainun ya dubeta cikin alamun tsananin tsoro a lokacin da idanuwansa suka zazzaro yace haba ya shugabata wace irin magana kikeyi ne haka kamar wacce ta zautu,ta yaya kura zata ce ta taro zaki da fada?Ke kanki kinsan cewa Sarila tafi karfinmu ta kowace siga kuma indai zamu tareta gaba da gaba cikin dakiku kadan zata gama damu,ni ina ganin cewa baki da wani zabi wanda yafi ki hada kai da wannan yar uwata taki Muznaira.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta murtuke fuskarta cikin alamun tsananin bakin ciki a lokacin da Mujahid yabita da kallo kawai zuciyarsa dauke da matukar damuwa.Kawai sai yaga Yazirina ta durfafoshi fuskarta a murtuke,al'amarin daya razana shi kenan ainun.Tana isowa daf dashi sai ta kama kafadunsa a karo na farko ta girgiza shi ta dube shi cikin fushi tace,idan zaka dawo cikin haiyacinka ka dawo amma abinda kake fada ba zai taba yiyuwa ba,idan kuwa ka dage akan hakan saidai mu raba hanya ni da kai,ka sani cewa tun a farkon haduwata dakai zuciyata ta bani cewar kaine saurayi dan baiwar da aka bani labarin cewa zai iya kubutar dani daga sharrin Sarila,dari bisa dari zuciyata ya aminta da hakan saboda me zaka bada mini kasa a fuska? Koda Yazirina tazo nan a zancenta sai jikin Mujahid yayi sanyi a lokacin ne ta saki kafadunsa ta koma izuwa kan gado ta kwanta tana mai kallon rufin dakin cikin tunani mai zurfi.Nan take idanunta suka ciko da kwalla sakamakon tunowa da tayi cewa ba kowa bane ya haddasawa mutanen duniya wannan mummunan tashin hankalin ba face mahaifinta BOKA SALMARA.Nan take Yazirina taji bakin ciki ya turnuketa data kasance tsatson boka Salmara kuma taji ta tsane shi ta tsani kanta.Nan take hawaye ya kwararo daga cikin idanunta ya kama zuba bisa kumatunta.Al'amarin daya karya zuciyar Mujahid kenan yaji ya kamu da tsananin tausayinta don haka bai san sa'adda ya taso daga kan kujerar da yake zaune ya dawo kan gefe gadon ya zauna shima a karon farko sai ya kama hannunta ya ruke suka kurawa juna idanu yace,ya shugabata ki gafarceni hakika yanzu na gane duk irin abinda kike tsoro da tunani a cikin ranki kuma nayi miki alkawarin cewa duk wuya duk rintsi zan cigaba da taimakonki koda kuwa zan rasa rayuwata har izuwa lokacin da bukatarki zata biya amma fa akwai matsaloli guda biyu.Matsala ta farlo itace ni kaina bansan ko ni waye ba,abin nufi shine bani da tabbacin cewa nine wannan saurayi dan baiwa mai sa'a da rabo da zai iya kubutar dake daga sharrin Sarila.Matsala ta biyu itace bansan hanyar da zamu iya rabuwa da maigidan nan lafiya ba har mu sami nasarar sace wannan kambun sihiri dake hannunta wanda zai taimaka mana wajen tsira daga sharrin Sarila.Koda jin wannan batu sai Yazirina taja dogon numfashi sannan ta zuke hannunta daga cikin na Mujahid tana mai daka masa harara tace wanene ya baka ikon ruke hannuna?Koda jin wannan tambaya sai shima ya murtuke fuska yace wanene ya baki ikon kama kafaduna dazu har da girgiza su kuma me yasa kika bari na goyaki a bayana har nayi gudu mai tsawo dake a lokacin da ba kya cikin haiyacinki?Baki tambaye ni dalilin yin hakan ba sai a yanzu kawai dana rike hannayenki. ™Abubakar Haleefah Physicist™ Koda jin wannan batu sai Yazirina ta kyalkyale da dariya sannan ta kamo Mujahid ta rumgumeshi a kirjinta gaba daya tace hakika yau ka burgeni dakayi ta maza ka kawar da dukkan tsoro kuma daga yau ka zama cikakken abokina.Lallai kafin dare ya raba inason kayi tunani akan hanyar da zamu sami nasarar fita daga cikin wannan gidan bayan mun sace kambun sihiri.Ai dama sata idan ta saci sata ba laifi bane.Koda gama fadin hakan sai Yazirina ta janye jikinta daga cikin na Mujahid ta koma kan gadonta ta kwanta tana mai juya masa baya,shima saiya mike tsaye ya koma kan kujera ya zauna kuma ya daga kansa sama ya fada sabon kogin tunani.Wannan shine abinda ya faru tsakanin Yazirina da Mujahid bayan sun tsallake harin Sarila na farko sun fada hannun yar uwarta boyayyiyar bokanya Muznaira. *A can cikin birnin Yamein kuwa saida aka gama wannan bakin gumurzu tsakanin Sarila da Yazirina bayan gidaje da yawa sun rushe,mutane da yawa sun hallaka sannan Boka Matawus dasu sarkin yaki suka iso wajen.Koda sukaga irin mummunar barnar da su Sarila suka aiwatar sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka gane cewa lallai Sarila da Yazirina ba kananun annoba bane.Nan take cikin hanzari Boka Matawus ya fiddo madubin tsafinsa ya shafeshi da hannun hagu domin yaga a inda Sarila da Yazirina suke a sannan.Nan take yaga hoton Sarila tana tafiya a cikin Birnin Yamein a wani bangare daban tana waige waige da dube dube,duk inda taje saidai kaga jama'a nata guje guje da iface iface ana rugawa izuwa cikin gidaje ana rufe kofofi.Babban abinda ya dagawa Boka Matawus hankali shine hanyar da Sarila ta durfafa babu inda zata kaita face Gidan Sarautar birnin wato inda Sarki Ubaiyu yake.Boka Matawus ya sake shafe madubin tsafin ko zai ga inda yaro dan baiwa yake wanda shi suka fito nema amma sai hasken madubin tsafin nasa ya disashe izuwa tsananin duhu.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalonsa kenan ba shiri ya dago kai ya dubi sarkin yaki da ragowar dakarun dake biye dasu yace rayuwar sarki data iyalansa na cikin mugun hadari domin can Sarila ta nufa,yanzu kuzo muyi sauri mu koma can domin mu kai masa dauki.Koda jin haka sai sarkin yaki Ya dubi Boka Matawus cikin alamun firgici yace to yaya batun yaro dan baiwar wanda shine kadai zai iya ceto rayukan al'ummarmu da dukiyarsu?Boka Matawus yace na kasa ganinsa a cikin madubin tsafina,ka sani cewa bamu da lokacin neman wannan yaro a yanzu,kuzo muyi sauri mu koma fada in ba haka ba kuwa fadarma gaba daya zata tashi daga aiki.Koda gama fadin hakan sai Boka Matawus ya kada linzamon dokinsa baya ya zabureshi da gudu izuwa ga hanyar da zata mayar dashi fada.Cikin hanzari sarkin yaki da sauran mukarrabansa suka rufa masa baya,nan fa suka ci gaba da yiwa dawakansu kaimi suna tsala gudu.Aikuwa suna isowa kofar gidan sarautar suka iske dakarun dake gadin kofar shiga a kwance a kasa sun zama gawa kimanin su dari uku,ita kanta kofar shiga gidan sarautar wacce ta kasance katuwar gaske ta bakin karfe mai matukar kauri da nauyi an jijjigeta daga jikin gini an yarda ita kasa.Koda ganin wannan mummunar barna sai hankalin su boka Matawus ya dugunzuma ainun suka karawa dawakansu kaimi suka nufi hanyar da zata kaisu fada kai tsaye.Nan fa duk inda suka wuce basa ganin komai face gawarwakin dakarun gidan sarautar gidan gaba daya yayi tsit tamkar babu sauran mutum daya a raye a cikinsa.Koda ganin wannan al'amarin sai boka Matawus yaga bazai iya jiran dokinsa ya karaso dashi fadar ba domin zuciyarsa bugawa takeyi da karfi sakamakon fargabar tunanin cewa babu mamaki tuni Sarila ta gama da sarki Ubaiyu.Bisa wannan dalili ne Boka Matawus yayi girgiza ya bace bat daga kan dokin nasa bai baiyana a ko ina ba sai a cikin fadar sarki Ubaiyi.Yana baiyana yayi kicibus da gawarwakin dakarun dake tsaron sarki da kuma gawarwakin tsirarun fadawansa da hadimansa.Acan kuma karagar mulki kuwa sai ya hango sarki Ubaiyu a zaune ga wani mummunan sara a kafadarsa jini na zuba yana numfashi sama sama Sarila na tsaye a kansa ta daga takobinta sama tana shirin ta karasa kashe shi.Koda yayi arba da Boka Matawus wanda ya kasance dogon mutum mai kirar sadaukai kuma duk jikinsa a cike yake da layu gami da guraye na tsafi sannan kuma taga ya durfafota kai tsaye ba tare da shakkar komai ba sai ta dan sha jinin jikinta ta fara tunanin cewa lallai abinda yasa ta danyi shakkarsa shine yanayin shigarsa iri daya ne dana Boka Salmara domin shiga ce irin wadda ba zata taba mancewa da ita ba duk da cewa tun tana yarinya rabonta da ganin irin shigar. Tun tana yarinya rabonta da ganin irin shigar.Koda ya rage saura baifi taku uku ba tsakanin Boka Matawus da Sarila sai ya tsaya cak a gabanta suka fuskanci juna ya dubeta a fusace cikin tsananin fushi har fuskarsa na gatsinewa yace,wannan wane irin haukan banza ne haka kizo kina kashe mana jama'armu a banza har ma sauran kiris ki kashe mana sarkinmu saboda kawai kin nemi Yazirina kin rasa?Shin baki san cewa muma abokan gabar Yazirina bane?Koda jin wannan batu sai ita ma Sarila ta fusata ta dakawa Boka Matawus tsawa hakan yasa yaji har saida hantar cikinsa ta kada amma saiya dake yaki ya nuna tsoransa.Sarila tace da Yazirina da dukkan sarakunan duniya da irinku bokaye duk abokan gabata ne tunda nasan cewa dukkaninku kuna son ku rigani mallakar taswirar dake hannun Yazirina guda biyu domin isa kogon Taskar Ajali.Bani da wani zabi wanda yafi na kashe ku gaba dayanku domin na daina fuskantar wata barazana.Boka Matawus yace ai kuwa wannan shine babban kuskuren da zaki aikata kuwa domin dole ne ki hada kai da wani kafin ki sami nasarar hallaka Yazirina har ki rabata da wadannan taswirori guda biyu kamar yadda ita ma a halin yanzu ta hada kai da wata yar uwarta ta jini domin ganinbayanki.Ko da jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Sarila tace yanzu dama Yazirina tana da wata yar uwa a duniya bayan ni dana kasance mun sha nono daya?Boka Matawus ya numfasa yace kwarai kuwa.Nan take sai Matawus yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango sai ga hoton Boka Salmara ya baiyana shida mahaifiyar Muznaira tun daga farkon haduwarsu kawo izuwa lokacin data haife Muznaira har izuwa rabuwarsu da yadda akayi Muznaira ta zamo gawurtacciya matsafiya har ta gina wannan gida nata dake karkashin kasa kawo haduwarta dasu Yazirina.Koda Boka Matawus ya fuskanci hakan sai farin ciki ya lullube shi ya dubi Sarila yace abinda nake so dake shine yanzu ko kwantar da hankalinki in kaiki masauki ki zauna ki huta.Nayi miki alkawarin zan taimake ki yadda zaki kai ga samun nasarar abinda kika sa a gabanki cikin ruwan sanyi amma bisa wata yarjejeniya.Ki sani cewa gaggawa ba zata kaiki ga wata nasara ba face akasinta.Koda gama fadin hakan sai Boka Matawus ya kwalawa wadansu kuyangin Sarki kira.Take wadansu kyawawan kuyangi su uku suka shigo fadar a guje jikinsu na tsuma saboda tsananin tsoron Sarila.Da zuwansu sai suka zube kasa a gaban boka Matawus shi kuma saiya dubesu ya daka musu tsawa yace ku kwantar da hankalinku kuyi sani cewa Sarila ba zata taba cutar daku ba a yanzu domin mu da ita mun zama daya.Maza ku kaita babbar turaka inda aka saba saukar manyan baki ku kaita kewaye kuyi mata wanka sannan a gyara mata jikinta kuma a shirya mata abinci mai daraja.Koda jin wannan umarni sai kuyangin uku suka hada baki sukace an gama ya shugabana.Nan take kuyangin suka mike tsaye sukaje suka kama Sarila tamkar wata karamar yarinya suka fice da ita daga cikin fadar suka nufi wani bangare daban na gidan sarautar ba tare data yi musu gardama ba ko tayi yunkurin cutar dasu.Tafiyarsu keda wuya sai Boka Matawus yasa akaje aka kirawo likitan sarki Ubaiyu cikin gaggawa da zuwan likitan ya shiga aikinsa ya yiwa sarkin magani.Koda Sarki Ubaiyu ya dawo cikin hayyacinsa sai ya dubi Boka Matawus cikin murmushin karfin hali yace yakai dirkar birnin Yamein ina godiya a gareka bisa ceton rayuwata da kayi,tabbas ba don kai ba da tuni yanzu na zama gawa,to amma fa ka sani cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba.Ta yaya kake zaton cewa zaka iya sarrafa wannan mahaukaciyar Jaruma?Duk naji maganganun da kukayi yaga samun nasara a kanta da kuma batun Muznaira daka nuna mata wanda bata san dashi ba,inda tayi yunkurin hallaka ka ba zaka iya tsira daga sharrinta ba.Nasan kaga irin mummunar barnar da tayi mana a cikin gidan sarautar nan

Chapter 4 of 14