Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duka nice na shayar dasu ina kallonsu a matsayin 'ya'yana.Koda gama fadin hakan sai Basma ta kurma uban ihu sannan ta fashe da matsanancin kuka na bakin ciki,ita kuwa tsohuwar sai ta shiga rarrashinta tana mai cewa babu yadda zakiyi da kaddarar rayuwarki tunda baki da ikon sauyata.Haka dai tsohuwar tacigaba da rarrashinta har izuwa lokacin mai dan tsawo sannan ta shawo kanta ta daina kukan.Daga wannan rana kuyangin suka ci gaba da kula da Basma ya zamana cewa juna biyunta ya dada Girma har watanni tara suka cika,da tsakiyar dare nakuda ta zo mata kuma a cikin dakiku kadan ta haife santaleliyar 'yarta.Da kwanaki bakwai suka cika aka radawa yarinyar suna Yazirina,nan fa Basma da kuyancinta suka cigaba da renon Yazirina har takai shekaru shida a duniya kuma tun a sannan ne aka rinka ganin abubuwan al'ajabi a tare da Yazirina domin tana iya sarrafa komai da karfin sihirin tsafi domin komai nauyin abu data dauke shi da hannu sai ta daga shi sama takai shi inda takeso ta ajiye.Tana da shekaru shida ne akaga wadansu zakakuron aljanu suna zuwa suna bata horon yaki,tun a wannan lokaci Basma ta sanar da Yazirina komai dangane da rayuwarta da kuma gagarumin aikin dake gabanta nan gaba idan ta cika Budurwa.Koda Yazirina taji cewar an sameta ne bata hanyar aure ba sai bakin ciki ya turnuketa yayi mata kututu a cikin ranta domin saida ta kwana ta yini tana kuka baci basha.A sannan ne taji ta tsani Basma kuma ta tsani Boka Salmara,kai saida ma tayi yunkurin kashe kanta da kyar aljanun gidan da kuyangin dake kula da ita suka rarrasheta ta hakura amma duk da haka saida ta kwana uku bata yiwa Basma magana ba,kuma bata zuwa,Basma na zaune a cikin turakarta ta hada kai da guiwa tana tunani da kuka bisa ganin yadda yar cikinta ta tsaneta,lokaci guda sai kawai taji an turo kofar dakin,koda Basma ta dago kanta sai tafa ashe Yazirina ce ta shigo idanunta sunyi sharkaf da hawaye,cikin sanyin jiki Yazirina ta karaso gaban Basma ta durkusa a gabanta bisa kafafunta ta sunkui da kanta kas tace,yake ummina kiyi mini aikin gafara domin nayi babban kuskure dana nuna kiyayyara a gareki tunda bani da kamar ki ko inaso ko banaso ban isa na sauyawa tuwo suna ba.Koda jin wannan baty sai mamaki da farinciki suka lullube Bsma domin bata taba zaton cewa yarinya yar shekara shida kamar Yazirina zatayi irin wannan tunani ba.Nan take Basma ta rungume Yazirina suka fashe da kukan farin ciki tare.Daga wannan rana Basma da Yazirina suka cigaba da zama cikin farin ciki har Yazirina ta cika shekaru goma sha biyar a duniya.A wannan lokaci ne kyawun surar jikinta ya baiyana sosai kuma ya zamana cewa ta sami horon yaki mai tsanani yadda tana iya tarwatsa gungun dakarun yaki na aljanu ma.Wata rana da safe sai Yazirina taga gaba daya yanayin Basma ya sauya,alamun cewa hankalinta a tashe yake domin ta kasa cin abinci kuma idanunta sun kada sunyi jawur alamar cewa tasha kuka a boye.Koda ganin haka sai hankalin Yazirina ya dugunzuma ainun ta dubi Basma cikin alamun tsananin damuwa tace yake Ummina ina dalilin sauyin yanayi haka a tare dake alhalin an gaya mini cewa baki da wata damuwa a gidan nan.Sa'adda Basma taji wannan tambaya saita mike tsaye daga kan gadonta maimakon tace wano abu sai kawai ta kama hannunta ta jata suka fice daga cikin turakar suka nufi wani bangare daban na gidan.Wani lungu suka shiga mai zurfin gaske kuma yana da dan duhu.Tun daga tasowar Yazirina kawo izuwa girmanta ko sau daya bata taba shiga wannan lungu ba saboda ganin cewa gaba dayan hadiman gidan ma bata taba ganin wanda ya shiga ba don haka tun tana yarinya taje tsoron lungun bisa mamaki sai taga Basma sai dada kutsawa take cikin lungun ba tare da wata fargabar ba saida sukayi doguwar tafiya a cikin lungun tamkar bazasu isa karshensa har saida Yazirina ta kosa sannan suka iso wani daki wanda bashi da kofa.Da isarsu gaban dakin sai Basma ta dafa garun dakin da hannunta na hagu.Take garun ya tsage gida biyu ya bude musu hanya suka shige ciki suna shiga sai bangon ya koma ya hada.Babu komai a cikin wannan karamin daki face akwatuna na gilashi sama da guda miliyan daya,wata kan wata,gaba daya akwatunan a rufe suke kuma babu kofa ko murfi a jikinsa wanda za'ayi budewa ko a zura hannu ciki don dauko abindake ciki kowacce akwatu na dauke da abu guda daya ne jal mai muhimmanci.Kai tsaye Basma ta nufi wata akwatai mai dauke da wani Allon Katako da isarta gaban akwatin sai ta dafata da hannun hagu take akwatun ta dare tamkar an yanka tsakiyar tuffa.Ba tare da tsoron komai ba Basma ta zura hannunta cikin akwatun ta dauko wannan allon katako.faruwar hakan keda wuya sai akwatun ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen Basma ta mikawa Yazarina allon ta karba sannan ta sake zura hannunta cikin aljihun rigarta ta dauko jemammiyar fata ta sake danka mata tace wannan abubuwa biyu dana baki ba komai bane a jikinsu face zanen taswirar izuwa taskar ajali wanda mahaifinki yabar miki gado amma kiyi sani cewa ba zasuyi amfani ba har sai kin tafi farauta yar uwarki Sarila kin kasheta kin kwafi taswirar dake zane a kan gadon bayanta kin hada da wadannan guda biyu dake hannunki.Kamar yadda na gaya miki a baya yanzu ne zaki shiga sabuwar rayuwa ta biyu wato zaki bar wannan daji ki shiga cikin duniya domin farautar Sarila ki sani cewa nice na shayar da Sarila don haka na dauketa tamkar yar cikina don haka bana son dayanku ta cutar da yar uwarta.Ina rokonki alfarma guda daya idan har akwai hanyar da zakibi ki kwafi taswirar dake kan gadon bayan Sarila ba tare da kin kasheta ba to kiyi hakan.A yaune zamuyi bankwana ni dake ki shiga cikin duniya kuma bani da tabbacin zamu sake saduwa bisa wannan dalili ne kika ga yanayina ya sauya gaba daya domin tun jiya nake ta faman shara kuka da bakin ciki bisa ganin cewa lokacin rabuwarmu yazo.Koda Basma tazo nan a jawabinta sai hawaye ya zubowa Yazirina ta rungume Basma suka fashe da kuka tare.Saida suka dan jima a kankame da juna sannan Yazirina ta janye jikinta daga cikin na Basma suka dubi juna a lokacin da hawaye ke sartu akan kumatunta tace,yake ummina kiyi sani cewa babu maganar sassauci ko tausayi ko kuma jin kai tsakanina da yar uwarta Sarila musamman idan kikayi la'akari da yanayin yadda halayenta zasu kasance na rashin tausayi da kuma zalunci.Duk danaji ance sai ta ninkani a karfin damtse dana sihirin tsafi da kuma iya yaki ni bazan ji tsoronta ba kuma ba zan fasa tunkararta ba ko da kuwa zan rasa raina,saboda ni a rayuwata babu mutumin dana tsana sama da azzalumi.Da wannan furuci nake yi miki sallamar karshe gami da bankwana amma nayi alkawari cewar bayan na cika burina na dauko dukiyar mahaifina dake can Taskar Ajali zan dawo nan na rabaki da wannan gida mu koma cikin gari muci gaba da rayuwa a lokacin da zan zama sarauniyar duniya.Koda gama fadin hakan sai jaruma Yazirina ta juya ta fice daga cikin wannan daki tana waigen mahaifiyarta ta su duka suna zubar da hawaye.Lokacin da Boka Matawus Bin Ashshahab yazo nan a labarin da yake baiwa Sarki Ubaiyu sai kowa dake cikin fadar ya kamu da tsananin mamaki gami da tsoro musamman sarki Ubaiyu wanda hankalinsa ya dugunzuma ainun fiye da kowa.Hankalinsa ya tashi Ainun fiye da kowa.Cikin kaduwa sarki Ubaiyu ya dubi Boka Matawus yace yanzu ina dabara?Ka gaya mini cewa idan har daya daga cikin wadannan yan mata walau Yazirina ko Sarila ta sami nasarar zuwa Taskar Ajali ta dauko dukiyar Boka Salmara saita mulki duniya gaba dayanta.Gashi a yanzu mun kasa kama Yazirina kuma kace Sarila ta fita hadari,yanzu shi kenan babu matakin da zamu iya dauka domin mu magance wannan matsala.Koda jin wannan tambaya sai Boka Matawus yayi doguwar ajiyar zuciya gami da sunkui da kansa kas ya na tunani.Daga can kuma saiya dago kai ya dubi Sarki Ubaiyu cikin alamun tsananin damuwa sannan tace ya shugabana akwai hanyoyi guda biyu kacal wadanda za'a iya amfani dasu wajen magance wadannan yan mata biyu wadanda suke neman su zamewa duniya ANNOBA.Koda yake daya a cikinsu ta gari ce wato ita Yazirina,ita kuwa Sarila muguwa ce wadda a halin yanzu bata iso nan cikin duniya ba tana can tsibirin Jannatul Duniya amma daga yanzu zata iya baiyana a koyaushe kuma tana baiyana sai duniya gaba daya ta san da baiyanarta.Hanya ta farko da za'abi a ga bayan Sarila Da Yazirina shine dole ne manyan sarakuna guda hudu na kasashen da babu kamarsu a wannan nahiya su hada KARFI DA KARFE su yake su su kawar dasu daga doron kasa,kafin daya daga cikinsu ta hada taswirorin uku na zuwa Taskar Ajali a hannunta.Wannan sarakai hudu kuwa ba wasu bane face sarkin kasar Sin da Sarauniyar Birnin Hindu sai kuma Sarkin Misra da Sarkin Kisra,kuma kowanne sarki dole ne yayi aiki tare da babban bokansa.Hanya ta biyu da za'a iya ganin bayan wadannan takadiran yan mata shine akwai wani bakon sarauyi dan baiwa mai tsananin sa'a da Baiwa shine kadai zai iya hallakasu ta hanyar hikimar ba wai da makami ba.Koda Boka Matawus yazo nan a zancensa sai ran sarki Ubaiyu ya baci bai san sa'adda ya dakawa boka Matawus tsawa ba,kuma ya mike tsaye zumbur daga kan karagarsa ta mulki ya dubeshi a fusace yace wannan wace irin maganar banza kake yi mini ne hala alhalin kasancewa ban san a inda wannan bakon saurayi yake ba,ban san ta yadda zan iya shaida shi ba kumaka gaya mini cewa sarakunan kasashe hudu a halin yanzu tuni kowannensu ya baza dakarunsa izuwa kowanne bangare na duniya domin suyi farautar Yazirina da Sarila su rabasu da taswirorin zuwa Taskar Ajali.Kaga kenan babu dayansu da zai yarda a hada kai saboda son kai da son zuciya gami da kwadayin duniya.Lokacin da sarki Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai Boka Matawus yace ubangiji Kartus ya huci zuciyarka ya shugabana kayi sani cewa wuya itake sawa ayi gudun dole idan lokaci yayi halinsa ya zamana cewa kowa yaji a jikinsa to dole ne a nemi mafita.A wannan lokaci ne wadannan sarakuna hudu zasu nemi hadin kan junansu na dole domin magance wannan matsala amma ba yanzu ba ni yanzu shawarar da zan baka itace duk yadda zaka yi domin ka mallaki wannan bakon saurayi da zai baiyana ya kasance yana tare dakai domin idan daya daga cikin wadannan manyan sarakuna hudu ya sami taswirar zuwa Taskar Ajali har yaje ya debo dukiyar Boka Salmara to gaba daya ku sauran sarakunan duniya sai kun zama bayinsa. TURKASHI SAI MUN HADU A CIKIN LITTAFI NA BIYU DON JIN CIGABAN WANNAN LABARI. TASKAR AJALI 1 Littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI Littafi na biyu 2 Na Abdulaziz sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com KODA jin wannan batu sai idanun Sarki Ubaiyu suka zazzaro ya dubi Boka Matawus cikin razana da firgita yace waishin a kan wane dalili zamu zamo bawan wanda ya mallaki wannan dukiya dake Taskar Ajali?Koda jin wannan tambaya sai Boka Matawus yayi murmushi yace,yanzu kayi tambaya mai matukar muhimmanci ya shugabana kayi sani cewa daga ranar da aka sami mahalukin daya debo waccan dukiya ta Boka Salmara dake can Taskar Ajali ya kawota kasarsa to daga wannan rana sauran kasashen duniya zasu shiga cikin fari,fatara da munin talauci saboda babu wata kasa da za'a iyayin noma a kanta face kasar garin da aka ajiye wannan dukiya.Babu inda za'a iya siye da siyarwa face wannan kasa,kai hatta abinci saidai a rinka fataucinsa daga birnin da aka ajiye wannan dukiya ana kai shi izuwa sauran kasashen duniya kuma inda duniyar zata taru domin ta kwace dukiyar daga hannun mai ita ba zata iya ba,kaga kenan dole ne sauran sarakuna su zamo almajirai a gaban mai wannan dukiya domin su tsira daga yunwa da talauci su da jama'arsu.Ka sani cewa ko akan hanya yan fashi basu isa su iya kwace irin dukiyar garin da aka ajiye wannan dukiya ba ta Boka Salmara.A takaice dai duk sarkin da ya sami nasarar debo wannan dukiya sai ya zamo kadagaran bakin tulu kuma saiya zama kangarau maganin gagararru.Koda Boka Matawus yazo nan a jawabinsa sai sarki Ubaiyu yaja dogon numfashi cikin ajiyar zuciya gami da karayar zuciya ya dago kai ya dubi Boka Matawus yace na baka ragamar nemo wannan bakon saurayi dan baiwa da zai baiyana kuma sarkin yaki da dakarunsa ne zasu taimaka maka wajen yin wannan aiki,kudi ko nawa ake bukata zan bayar dasu don ganin wannan aiki ya cika.Ni kam na cire raina daga kan tunanin mallakar dukiyar Boka Salmara amma inason lallai na mallaki wannan saurayi dan baiwa domin ya kawar mini da duk wani mahaluki mai son yaje ya debo wannan dukiya ya janyowa duniya gagarumar annoba wacce take daidai da GOBARA DAGA KOGI wacce bata da magani.Koda jin wannan batu sai fuskar boka Matawus ta fadada da murmushi yace tabbas yanzu kayi tunani da shawara mafi alheri a garemu baki daya ya shugabana.Gama fadin hakan keda wuya sai Boka Matawus ya dubi sarkin yaki yayi masa wata inkiya a lokacin daya juya ya nufi kofar fita daga cikin fadar.Cikin hanzari sarki yaki da mukarrabansa suka mike tsaye da sauri suka takewa Boka Matawus baya,wannan shine abinda ya faru a fadar sarki Ubaiyu na birnin Yamein. *Al'amarin Jaruma Yazirina da Barawo Muhajid kuwa bayan ta dafa kafadarsa sun bace bat daga wannan wuri inda ta fafata da dakarun sumamen,basu baiyana a ko ina ba sai wata unguwar daban dake nesa sosai da inda akayi gumurzu kuma agefe hanya suka bayyana inda mutane ke wucewa.Baiyanarsu keda wuya sai Yazirina tayi sauri ta dauko mayafi daga cikin jakarta ta guzuri ta lullube jikinta yadda idanunta kadai ake gani,kawai sai ta dubi Mujahid a lokacin da taga har yanzu jikinsa bai daina bari ba domin gani yake kamar a ko yaushe shugaban wadannan dakarun sumamen zai iya baiyana tsulum a gabansa,ta dafa shi tace kai matsoracin banza kwantar da hankalinka kayi sani cewa babu wani makiyi da zai riskemu anan yanzu ka nemo mana gidan da zamu kwana domin ni bana son na kara yin magana da kowa kuma ban son aga fuskata.Koda jin haka sai Mujahid yayi murmushi yace kada ki damu ya shugabata zo muje wani wuri dake can gaba kadan na san ida zamu sami mai kyau.Koda gama fadin hakan sai Mujahid ya wuce gaba ba tare da fargabar komai ba kuwa Yazirina ta bishi a baya kai kace miji da mata ne.Yar gajeriyar tafiya sukayi suka iso kofar wani gida mai tsananin shiru tamkar babu kowa a cikinsa,da zuwansu sai mujahid ya kwankwasa kofar gidan har sau bakwai,cikin alamun fushi Yazirina ta dubi Mujahid tace wannan wane irin shashancin banza ne haka zakayi ta kwankwasa kofar gidan mutane haka har sau bakwai ko kuwa kurame ne a cikin gidan.Koda jin wannan tambaya sai Mujahid yayi murmushi yace dadi na da dan adam kenan ya cika garaje da mantuwa,ashe har kin manta ke da bakin ki kince babu inda ban sani ba a cikin garin,wannan kwankwasa kofar da kikaga nayi har sau bakwai to inkiya ce na yiwa mai gidan domin ya gano wanda yazo.Ai kuwa kafin mujahid ya gama rufe bakinsa tuni sunji karar zare sakatu uku dake jikin kofar sannan kuma sai sukaji an sanya kuba a cikin kofar an murde har sau uku sannan aka turo kofar gidan ta wangame sai ga wani dan gajeran mutum mai katon ciki ya fito.Daga shi sai gajeran wando a jikinsa iya guiwa sai wani mayafi daya rataya a kafadarsa gashi baki ne sosai fuskarsa babu gemu kuma kansa yasha askin kwarya molo.A hannunsa na hagu akwai dan karamin tulu na giya yana kwankwada kuma a cikin maye yake don haka baima lura da Yazirina ba wacce ke tsaye a gefe daya lullube cikin mayafi.Koda gajeran mutumin ya dubi Mujahid saiya bushe da dariya irin ta yan giya sannan yace kai shegen duniya lallai yau ma dawa tayi nama kenan,ina akaje akayi aiki mai riba haka har da akazo neman hayar gidana mai tsaada..?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid ya doki kafadar mutumin yace kai Andalu tsohon kwallon duniya,dubi bayana da kyau ka gani tare nake da..Kafin Mujahid ya karasa abinda yakeson fadi sai Yazirina ta tari numfashinsa tace ni matarsa ce daki nake son ka bamu mafi kyau a cikin wannan gida.Koda Andalu yaji sautin zazzakar muryar Yazirina sai ya bangaje Mujahid daga gabansa ya kura mata idanu duk da cewa gaba dayan jikinta da fuskarta a lullube yake sannan ya juya ya dubi Mujahid yace wai kai wane irin yaro ne DAN BAIWA haka mai tsananin sa'a da ™Abubakar Haleefah Physicist™ rabo,ba'a taba kama ka ba a wajen yin sata ko ayi maka rauni yanzu gashi ka auro dalleliyar mace wacce muryarta kadai ta isa ta debe kewa koda tafi kowace mace muni a duniya.To gaskiya dakin daya rage babu kowa a gidan nan shine mafi tsada sai kun bani dinare dubu uku,kafin Andalu ya gama rufe bakinsa tuni Yazirina ta bude jakar Guzurinta ta fiddo da kullin dinare guda,sannan tace kaimu dakin naga yanayinsa.Batare da wata gardamar ba kuwa sai Andalu ya ratsa ya baiwa su Yazirina hanya suka wuce cikin sannan ya janyo kofar gidan ya rufe ya maida sakatun kuma yasa kuba ya dada kulleta yana mai murda kubar har sau uku kamar yadda yayi a farko.Yazirina na shiga cikin gidan ta tsinci kanta a cikin wani babban falo,ashe mutane ne da yawa a zazzaune maza da mata ana ta shaye shaye na giya,lemo iri iri wasu kuwa hayakin taba suke ta faman busawa,kallo daya zaka yiwa gaba dayan mutanen gidan ka gane cewa dukkaninsu yan bariki ne muma dukkanin matan karuwai ne babu mutuniyar kirki gaba daya a cikinsu.A gefe daya kuma teburin yan caca ne suna tayin cacar tasu,daga can bangaren yamma kuma sai suka hango wasu majiya karfi mutum biyu zaune a kan wani tebur sun hada hannaye suna gwada yar kwanji jama'a sun kewaye su suna yi musu tafi da shewa kowannensu ya dage iya karfinsa domin yaga ya sami nasarar danna hannun dan uwansa izuwa kasa.Koda Yazirina ta dubi mafi girman surar karfi daga kartin biyu sai taji bata yarda dashi musamman datayi la'akari da irin kallon da yayi musu ita da Mujahid amma sai ta basar suka wuce ta gabansu suna bin Andalu a baya yayin da suka hau kan wata matattakalar bene suka hau can sama inda dakunan gidan suke burjik har suka iso kofar wani daki dake can kuryar karshe.Take Andalu ya zaro wata kuba dake cikin aljihunsa ya mikawa Mujahid,Mujahid na karbar kubar saiya zurata cikin kofar ya kunna kai cikin murna.Ita kuwa Yazirina saita waigo tana mai lekawa kasan benen,akawai sai taga ahe gaba dayan mutanen dake kasan benen sun tsayar da duk abinda sukeyi sun daga kawunansu sama suna kallonsu.Koda ganin Haka sai Yazirina tayi tsaki tace nifa babu abinda na tsana sama da a rinka kallona,kuma babu abinda nafi so sama da sirri,kai Andalu na wane kudin gaba dayan dakunan gidan nan kuma nawane kudin duk giyar da aka sha a yau da sigari zan biyaka duka yanzu amma inason ka sallami gaba dayan mutanen dake cikin gidan nan su fice ya kasance daga ni sai angona domin yaune zamuyi daren farko na AMARCINMU.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Mujahid shi kuwa Andalu tsoro ne ya kama shi jikinsa ya hau tsuma ya dubi Yazirina cikin alamun tsananin firgici yace kiyi mini rai yake wannan amarya kiyi sani cewa mutanen dake cikin gidan nan a yanzu sune mafi RASHIN IMANI a garin nan,idan naje musu da wannan bukta taki zasu iya cutar dani kuma keda angon naki ma ba zaku tsira da rayuwarku ba.Koda jin haka sai Yazirina tayi tsaki tace matsala daya ce kawai dole ne na kara asarar kudin da zan biyaka na barnar da za'ayi maka a yanzu,tana gama fadin hakan saita sauko kasa da sauri daga kan matattakalar benen a lokacin da Andalu da Mujahid sukaji cikisu ya duri ruwa don sun tabbatar da cewar tashin hankali za'ayi.Koda Yazirina ta gama saukowa kasan matattakalar saita dubi gaba daya mutanen dake cikin falon tace inason kowa ya fice daga cikin gidan nan yanzun nan domin na karbe shi haya gaba daya,wanda duk ya kara dakika dari da ashirin a cikin gidan nan saidai ya fita a karye.Koda jin wannan batu sai gaba dayan mutanen suka bushe da dariya suka rinka yiwa Yazirina kallon mahaukaciya.Al'amarin daya fusata Yazirina kenan jikinta ya kama tsuma a lokacin dataji zuciyarta ta kama tafarfasa kamar zata kone amma sai ta dake ta tsaya cak a inda take.Koda ganin haka sai wannan narkeken kato wanda yayi gasar karfi da wani dazu wato wanda ya kura mata idanun nan ya mike tsaye daga kan kujerar da yake zaune ya tunkarota.Kan Yazirina na sunkuye ko dagowa bata yi bare ta kalleshi har ya iso daf da ita.Ai kuwa sai ya yunkura cikin shammace ya kawo mata wawan naushi ta gefen fuskarta,naushi ne irin wanda duk wanda aka yiwa shi sai an karya masa kashi,cikin zafin nama ta kauce katon ya naushi iska.Kafin yayi wani yunkuri ta kama hannun nasa da hannayenta biyu ta daka akan cinyarta.Take sautin karyewar hannun nasa ya cika falon gidan ya kurma uban ihun sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji ya durkushe kasa.Koda ganin abinda ya faru sai gaba dayan sauran mazajen dake gidan suka zare MAKAMANSU na yaki suka rugo da gudu suka afkawa Yazirina da nufin su gididdibata.Wohoho!abin mamaki baya karewa a duniya lokacin da wadannan mazaje suka afkawa Yazirina ita kadai sai aka kacame da masifaffan yaki ya zamana cewa suna kai mata SARA DA SUKA tana kauce dukkan hare haren nasu ba tare data rike wani makami ba.Saita rinka gwabza musu naushi da bugu tana bazar dasu kasa kuma ko mutum yaje kasan bata kyaleshi face ta take masa kafa ko hannu ya karye nan take,komai girman kato da hannu daya take surarsa ta dokashi a kas ya kasa mikewa tsaye.Nanfa ihun mazaje ya cika gidan a lokacin data rinka hada musu JINI da MAJINA kuma tana kakkaryasu.Koda sauran karuwai sukaga irin wannan mumunar barnar da Yazirina keyi sai suka firgice suka ruga izuwa kofar gidan domin su bude su fice domin sun manta ma cewa tuni Andalu ya rufe kofar.Ai kuwa suna ganin kofar a rufe sai suka dimauce wasun su basu san sa'adda suka far fitsari ba a tsaye wasu kuwa kuka suka kamayi saboda tsoron kada Yazirina ta kakkaryasu kamar yadda ta karya mazajen gidan.Duk wannan abu dake faruwa Andalu da Mujahid ™Abubakar Haleefah Physicist™ nacan sama bene sunki yarda su sauko kasan kawai sun zuba na mukiya suna kallon ikon Allah,shidai Andalu saboda tsananin mamaki da tsoro ma tuni wandonsa ya dade da jikewa da fitsari kuma daidai da dakika daya jikinsa bai daina karkarwa ba.A hakanne ya dubi Mujahid yace me yasa tun farko baka gaya mini cewa matarka aljana bace ba mutum ba,da tun a sannan zan gudu na bar muku gidan ungo kudinku da kuka biyani dai kuyi min rai.Koda jin wannan batu sai Mujahid yaji dariya ta kwace masa sannan ya dubi Andalu yace kai matata mutum ce kamar kai ba aljana bace amma ta musamman ce.Andalu yace kai koda mutum ce ina ganin akwai aljanu a jikinta dubi fa yadda ta ragargaza komai da kowa dake cikin gidan nan,a daidai wannan lokaci ne gidan yayi tsit baka jin sautin komai face nishi da koke koken mazajen dake kwance a kas.Wadanda gaba dayansu karyayyu ne su kuwa sauran matan gaba dayansu sun cure a waje daya suna ta kyarma kamar ace kyat su tsure da gudawa,gaba daya tebura da kujerun dake falon sun kakkarye,tulunan giya sun farfashe ko ina yayi kaca kaca kuma babu mahalukin da yake tsaye a falon face Jaruma Yazirina kuma duk wannan dauki ba dadi da akayi lullubin da Yazirina tayi bai kwance ba bare aga fuskarta ko surar jikinta.Koda Yazirina taga ta sami wannan nasara sai ta dubi gaba dayan karuwan tace kowacce ta dauki saurayinta ta kaishi daki tayi jinyarsa bana son mutum daya ya fita daga cikin gidan nan har izuwa tsawon kwanakin da zanyi.Tana gama fadin hakan sai ta juya ta hau matattakalar benen ta isa Inda Andalu ke tsaye kawai sai ta fiddo kulli uku manya na dinare ta cilla masa ya cafe tace kasa a gyara komai na gidan nan kamar wani abu bai faru ba.Kasa tsaro ya kasance bashiga ba fita,duk abinda ake bukata na dangane da abinci da sauran kayan ciye ciye dana shaye shaye a kawo wanda zai ishi kowa har tsawon kwanaki bakwai da zanyi a garin nan.Daga yau nice shugaba a gidan nan babu abinda za'a zartar saida izinina,aikata sabanin hakan ranka ne fansarsa.Koda gama fadin hakan sai Yazirina ta dubi Mujahid tayi masa murmushi tace Angona mu kara cikin dakinmu nan take Yazirina da Mujahid suka shige cikin wannan daki na musamman suka banko kofa.A sannan ne matan suka fara taimakon mazajen da Yazirina ta kakkarya suna tashinsu tsaye suna shigar dasu cikin dakunan gidan kuma suka shiga gyara musu karayar jikinsu,shi kuwa Andalu tuni ya kirawo hadimansa duka yaja musu kunne akan kada su kuskura su fitar da labarin abinda ya faru yanzu a cikin wannan gidan sannan ya basu kudi suka je suka siyo abubuwan da aka lalata a gidan aka mayar dasu tamkar wani abu bai taba faruwa ba,kuma suka je kasuwa suka siyo kayan abinci da ababan sha isasu gami da tulunan giya da kararen sigari.Lokacin da Yazirina suka shiga cikin wannan daki na musamman sai suka tsinci kansu a ciki wani dan kayataccen falo wanda ke dauke da jan kilishi mai taushi wanda aka shimfida a kasa gami da jajayen kujeru da kuma jajayen labulaye.A takaice dai komai dake cikin falon launin ja gareshi akwai dakunan barci guda biyu a cikin falon sai kuma kewaye guda daya.Yazirina taje ta zauna akan doguwar kujera tana mai sauke jakar guzurinta a kusa da ita sannan ta dubi Mujahid fuskarta a murtuke tace zaka kwana a cikin dakin ni kuma nan falon zanyi barcina.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya dubeta cikin alamun tsoro yace haba ya shugabata kin sani cewa yanzu kin kara gaiyato mana abokan gaba sakamakon kakkarya mazajen gidan nan da kikayi kira tara musu gajiya.Ni gaskiya tsoro nakeji nayi nesa dake domin bazan iya kare kaina ba.Kafin Mujahid ya gama rufe bakinsa sai Yazirina ta tari numfashinsa tana mai daka masa tsawa tace kada ka raina mini hankali mana,dacan wanene yake kareka daga dukkan irin hadarin da kake shiga a lokacin da kake yawon satarka?Mujahid ya gyada kai yace ai wannan karon an turo nine na sato abinda yafi komai hadari a duniya wato Taswirar zuwa kogon Taskar Ajali kuma masu farautar wannan Taswira guda uku manyan bokaye ne da manyan sarakuna ababen tsoro.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta bushe da dariya sannan tace ni kuwa ko kadan bana shakkarsu amma ina shakkar wata mace yar uwata guda daya wadda a koyaushe zata iya baiyana a cikin wannan duniya ana kiranta da suna JARUMA SARILA.Cikin tsananin alamun mamaki Mujahid ya dubi yazirina yace yanz kina nufin kice akwai wata jaruma wadda ta fiki jarumtaka da hadari a cikin jaruman duniya?Yazirina ta gyada kai tace kwarai kuwa kuma baiyanarta a cikin duniya daidai yake da baiyanar GOBARA DAGA KOGI wacce babu abinda zai iya kasheta,inda ace itace ta shigo wannan gida yau dinnan da tuni ta kashe kowa saboda batada tausayi ko kadan,zata rinka farautata kamar yadda mai fama da kishi ke neman ruwan sha ba don komai ba sai domin ta rabani da taswirar zuwa kogon Taskar Ajali guda biyu dake hannuna.Koda jin wannan batu sai mamaki ya sake turnuke Mujahid yace au dama daya Taswirar ma ta biyu na hannunki.? Nima dai na tsaya anan saboda tsananin Al'ajabi da mamakîn Jarumtakar Jaruma YAZIRINA. Au dama daya Taswirar ma ta biyu tana hannunki? Yazirina tayi murmushi ba tare da tace komai ba sai ta zura hannunta izuwa cikin

Chapter 2 of 14