Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gyada kai cikin murmushi yace tabbas dani za ayi wannan tafiya saboda wannan tafiya itace babbar jahadi na yada addinin Allah a wannan nahiya tamu Idan har muka yi nasara a kan tsafi to ko wacce kasa sai sun karbi musulunci kaga kenan ko dani za ayi wannan tafiyar jahadi koda sarki yazo nan a jawabinsa sai jarumi darusi yayi murmushi yace hakika kayi gaskiya ya shugabana kuma kayi tunani irin wanda ban taba zatoba gama fadin haka keda wuya sai sarki ya dubi sarkin yakinsa yace ka tura da dakaru dubu dari suje su kewaye masaukin wannan attajiri sannan kuma abaza wadansu dakarun yan leken asirinmu a binciko inda yake boye a kamashi sarkin yaki yace an gama ya shugabana har sarkin yaki ya juya zai tafi domin zartar da wannan umarnin sai aka hango mujahid ya taho garesu a guje mujahid ya karaso gaban sarki yana haki sannan ya risina yace ya shugabana ba wani bane wannan bakon attajirin face SARKI DAMNASHI. Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama kowa mujahid yaci gaba da bayanin duk abinda ya faru a cikin turakarsu sarila sannan kuma ya kara da cewa a yanzu haka sarki Damnashi yasa sunansa a cikin jaruman gasar da zasu tafi zuwa kogon taskar ajali dajin wannan batu sai aka sake cika da mamaki shi kuwa sarki sai yayi murmushi yace ba komaine ya kawo sarki damnashi birni na ba face abubuwan nan biyu abu na farko shine domin ya dauki fansa akan jarumi Darusi abu na biya shine yanzu yana kan bakansa na son mallakar dukiyar da mahaifin yazirina ya bari a cikin TASKAR AJALI hm lallai Sarki damnashi ya cika mai son duniya A halin yanzu bashi da wani amfani mu kama sarki Damnashi mu tsare a kurkuku kawai mu tafi tare da shi zuwa kogon taskar ajali koda jin wannan batu sai gimbiya suzaina ta dubi sarki cikin alamun tsoro tace haba ya abbana saboda me zamu sake jiki da wannan shaidanin sarki harmuyi wannan tafiya tare dashi alhalin kasan cewa zai iya shammatarmu ya cutar da kowa? Kada ki damu yake yata idan har kinyi imani da cewa mune akan gaskiya sukuma suna kan bata to Insha Allahu ba zasu taba samun galaba a kanmu ba dajin haka sai jikin suzaina yayi sanyi tayi shirutana mai sunkui da kanta kas amma sai ta sake dago kai ta dubeshi tace wane sakamao aka samu a cikin binciken na gano wanda ya samini guba acikin abincina? Koda jin wannan tambaya sai sarki yayi yar doguwar dariya sannan yace mun gano cewa acikin ruwan inibin da kika sha aka sanya gubar kuma babu hannun hadiminki a cikin wannan al amari mun san kowanene ya yi wannan yunkurin na hallakaki amma bashi da wani amfani kisan kowanene a yanzu sai dai nan gaba don ha ka kimanta da wannan batu, Yanzu na sallami kowa a je a fara shirye shiryen tafiyarmu izuwa kogon Taskar Ajali koda gama fadin haka sai sarki ya juya ya shige cikin gidan sarautar shima jarumi Darusi sai ya kama hannun mujahid suka juya zasu nufi nasu dakin amma sai suzaina ta sha gabansa tace ya za ayi da wadannan masu yin barcin a kan doki? Darusi ya gyada kai cikin murmushi yace '' Ai hodar barki aka shaka musu don haka kin fini sanin abinda yakamata ayi musu koda gama fadin hakan sai jarumi darusi ya sake jan mujahid sukayi tafiyarsu tafiyarsu keda wuya sai ga wadansu kuyangi sunzo giftawa kawai sai suzaina ta dubi kuyangin tace dasu su dauke sarila da yazirina daga kan dokin su kaisu can turakarsu nan take kuwa kuyangin suka cika umarni bayan an kai sara da yazirina turakar gimbiya suzaina an shimfidesu a kan gadonta sai da aka dora musu wani magani a cikin bakinsu kuma suka ci gaba da barci har izuwa tsawon sa a uku da rabi sannan suka farka a firgice suka mike zaune zumbur domin a zatonsu zasu tsinci kansune a daure a gaban makiya amma sai suka tsinci kansu a cikin kasaitaccen daki bisa luntsumemen gado shidai wannan daki yasha ado da kayan kawa iri iri masu matukar ban sha awa nan dai sarila da yazirina suka sauko daga kan gadon suka kama kalle kalle sama da kasan dakin da jikin bango kwatsam sai suka jiyo takun sawu an nufo cikin dakin a tare sarila da yazirina suka yunkura domin su zare takubbansu amma sai suka kasa sakamakon ganin cewa ashe gimbiya suzaina ce ta durfafo su fuskarta cike da annuri kawai sata wuce ta tsakiyar su ta karasa kan gadonta ta zauna gefe kuma ta dora kafarta guda kan dayar ta dubi sarila tace in ba don na ceci rayuwarku ba da tuni yanzu kun dade da zama gawa yake sarila shin har yanzu kina na a kan bakanki nason tozarta mutuncina a gaban jama a domin ramuwar ga tunkudekin da nayi bisa tsautsayi? Sa adda sarila taji wannan tambaya saita bushe da dariya lokaci guda kuma ta turbune fuskarta tace kina zaton cewa saboda kin ceci rayuwata shikenan kin katse gabar dake tsakaninmu? To bara kiji idan kina son na kawar da batun fansana saidai kiyi abu biyu abu na farko dolene ki hakura da batun zuwa kogon Taskar Ajali abu na biyu kuma dolene ki fansar da soyayyarki a gareni ma ana ki hakura da jarumi Darusi ki bar minshi saboda ahalin yanzu na kamu da tsananin sonshi fiye da komai a cikin wannan duniya kafin sarila ta gama fufe bakinta tuni gimbiya suzaina ta kyalkyale da dariya sannan itama ta hade fuska tace ki daina tunanin cewa zaki iya yaudarata ki cutar dani waya gaya miki cewa ana iya fansar da so na gaskiya dukiya ko mulki ko mai basa iya fansar da soyayya ta gaskiya abinda zaisa na iya bar miki darusi ba komai bane face mutuwa ina ji a jikina cewar kedai har abada ba zaki taba son darusi bisa gaskiya ba saboda kasancewarsa musulmi nasan yadda kika tsani musulunci da musulmai kuma nasan yadda kike da matukar son duniya akan abin duniya babu abinda ba zakiyi ba hatta yazirina ta dake tare dake so kike ki yaudareta ki rabata da dukiyar mahaifinta dake cikin taskar ajali kuma ki hallakata tsoronki da takeji ne ya hanata karbar addinin na sani cewa kina matukar son mujahid kamar yadda shima yake sonki kuma tuni zuciyarsa tayi imani da addinin gaskiya don haka babu sauran kwadayin abin duniya a ransa zai aureki ne bisa soyayyar gaskiya donku zauna kyi rayuwa ta farin ciki da kwanciyar hankali shin kina son ki mallaki masoyin nakine ko kuwa kina son kici gaba da bin yar uwarki mai mugun nufi a kanki a cikin zuciyarta? Hm Al amin Ahmed Guyson sunana. Lokacin da gimbiya suzaina tazo nan a wannan zance nata sai hawaye ya zubowa yazirina ta juya da baya daga inda sarila ke tsaye ta dawo dai dai gun suzaina ta tsaya sannan ta nuna sarila da dan yatsanta tace tabbas ke shaidaniyace kuma azzaluma ki tuna irin miliyoyin rayukan da kika kashe a wannan duniya ke kanki baki san iyakarsu ba dai dai da rana daya baki taba jin tausayi ko nadamar abinda kike aikatawa ba kullum burinki shine dukiya da mulki daga yau na yanke duk wata hulda a tsakaninmu dake na dawo bangaren gimbiya suzaina kuma da yanzu ba zan sake kwana a daki tare dakeba domin babu sauran yan uwanta tsakaninmu ni dake kowa tasa ta fishsheshi koda yazirina tazo nan a zancenta sai sarila ta kama yake gami da murmushin mugunta kawai saita nuna yazirina da dan yatsa tace sai kinyi nadamar nisantata caraf sai suzaina ta tari numfashinta tace yazirina ba zatayi nadamar dawowa bangaren gaskiya ba kece zakiyi babbar nadama a lokacin da babu damar mu karbi tubanki kifice mini daga cikin turakata domin idanuwa na sun gaji da ganin fuskar azzaluma kuma kunnuwana sun gaji da jin maganganunki sarila ta bushe da dariya tace shi kenan ni daku zanga wanda a karshe zai zubar da hawaye tana gama fadin haka saita juya da sauri ta fice daga cikin turakar ita kuwa yazirina saita fada kan kirjin suzaina ta fashe da kuka a lokacin da suka rungume juna daga wannan rana taci gaba da kwana a dakin gimbiya suzaina bayan ta karbi Addinin musulunci shi ma mujahid take ya musulunta a cikin yan ragowar kwanakin da suka rage na yin tafiya izuwa kogon taskar ajali yazirina da mujahid suka tsinci kansu a cikin sabuwar rayuwa ta dinbin farin ciki saura kwana biyu a tafi kogon taskar ajaline yazirina da mujahid suka bukaci a daura musu aure. Koda jin wannan batu sai ita ma suzaina tace sai dai a hada da auranta da jarumi darusi ai kuwa sai sarki yace sam ba zaiyi wuba sai sarki yace samba zaiyiwuba domin mujahid ba zai sami sukunin gabatar da babban aikin dake gabansa ba idan nauyin aure ya hau kansa. Nan fa suzaina ta firgice kuma ta dimauce ta rinka kuka da bakin ciki dare da rana har sai da darusi ya rarrashe ta dukansa ya tabbatar mata da cewa ana dawowa daga kogon Taskar Ajali za a daura nasu auran haka dai a kayi bikin auren yazirina da mujahid cikin murna aka gama da ranar tafiya kogon taskar ajali tazo sai jama a suka yi cincirindo a fada sarki da darusi mujahid da Sarki Damnashi yazirina da sarila da gimbiya suzaina na zaune bisa ingarman dawakai kowannansu yayi gagarumar shigar yaki dakarun birnin kuwa su dubu dari uku ne sukayi hawa saboda kwadayin samun shahada cikin wannan gagarumar tafiya Ba tare da bata wani lokaci ba sarki ya wuce gaba mukarrabansa na take masa baya suka fice daga cikin birnin gaba daya sarki Damnashi da sarila a can karshen baya sun jeru kawai sai Damnashi ya dubi sarila yace duk kece kika wahalar damu saboda mugun burinki na son kanki ke kadai in da kin hada kai dani da yanzu mu biyar kacal zamuje wannan wuri mu mallaki wannan dukiya kafin sarila ta bude baki tace da shi wani abu sai kawai aka hango kura ta turnuke sararin samaniya acan gaba koda ganin hakan sai sarki ya bayar da umarnin a tsaya nan take aka yi cirko cirko sannu a hankali kurar ta rinka lafawa kuma aka rinka jiyo sautin takun dawakai barkatai marasa adadi jim kadan kuma sai aka fara hango runduunoni na kasashe da yawa dake nahiyar kowacce kasa sarkin su da kansa yake yi musu jagora in da ace mutun na nan a wannan lokaci yaga miliyoyin mahayan da suka durfafo zato zaiyi gaba dayan mutanan duniya ne ke tafe saboda yawansu su jarumi Darusi basu yi motsin komai ba har wadannan rundunoni na miliyoyin suka iso daf dasu A sannan ne sarki da ya dubi mahaifin suzaina yace yakai wannan sarki na Arnan daji wadanda suka karbi addinin musulunci a yanzu kayi sani cewa ina yin magana neh da yawun gaba dayan sarakunan dake wannan nahiya tamu mun sami labarin cewa jarumi Darusi zai iya kaimu kkogon Taskar Ajali ba tare da taswirori ukun da mai kogon ya kirkira da dukkaninmu mun sani cewa duk sarkin da ya mallaki wannan dukiya ta kogon TASKAR AJALI shine zai mallaki duniya gaba dayanta bisa wannan daliline muka dungumo gaba dayanmu muka taho domin a raba gardama mai rabo a cikinmu nan duka sai ya samu koda jin wannan batu sai sarki ya yi murmushi gami da gyaran murya sannan yace kuyi sani cewa ni yanzu banyi imani da duk abinda kuka fada ba saboda haka idan mukaje can za a baiwa kowa damar sa ya shiga cikin kogon ya dauko Dukiyar dake ciki da karfin damtsensa karfin sihirinsa da dabararsa amma bisa sharadi guda sharadin kuwa shine idan kowa ya kasa jarumi darusi zai shiga ya dakko dukiyar da taimakon ubangijin musulunci idan har haka ta faru to dolene kowane sarki ya karbi addinin musulunci idan kuma baku yarda da wannan sharadi ba to yanzu take zamuyi yaki Mu kashe junanmu in yaso kasar ta tafi can kogon ta dauko dukiyar sa adda gimbiya suzaina taji wannan bayani sai hankalin kowa ya dugunzuma aka yi tsit tamkar mutuwa ta gifta nanfa gaba dayan mutanan kimanin su dari da sittin suka sauko daga kan dawakansu suka zauna suna tattaunawa sai da aka shafesama da sa a uku ana mahawara da shawarwari sannan aka yanke shawarar a tafi gaba daya aje can din kowa ya jarraba sa arsa kaico hakika tsautsayi baya wuce ranarsa kuma idan masifa ta tunkaro to fa babu abinda zai tsaidata face Allah tun da aka durfafi hanyar zuwa kogon Taskar Ajali aka rinka haduwa da masifu iri iri nan fa mutane da dawakansu suka rinka hallaka tamkar wata annobace ta sauko daga sama kafin a isa can kogon na taskar ajali ya zamana cewa saura baifi runduna arba in ba su kansu su jarumi darusi da suke ta neman tsari da taimakon Alla saida suka sha bakar wahala amma ko mutum daya bai mutu ba daga cikinsu sai dai akwai wadanda suka raunana da yawa abinda ya daurewa kowa kai shine SARKI DAMNASHI da sarila ko kurjewar jiki basuyi ba amma kafin a isa bakin kogon taskar Ajali gaba dayan jama ar sarki Damnashi sun mutu saura shi kadai shi kansa yayi mamakin yadda ya iya haye dukkanin masifun A kofar kogonne aka sake baiwa kowace runduna damar jarraba sa arsu nan fa duk rundunar da ta shiga cikin kogon sai aji shiru tamkar maye yaci shirwa domin ko duriyarsu ba za a jiba anan ma dai saida runduna ashirin da shida ta salwanta ya saura runduna goma sha hudu kacal wadannan rundunan suka karaya sukace sun yarda darusi ya shiga indai ya fito a raye zasu karbi musulunci koda jin haka sai sarila da sarki Damnashi sukayi caraf sukace su basu yarda ba sai dai suyi yaki da darusi idan ya kashe su ya shiga idan kuma su suka kashe shi su shiga nan take aka basu wannan dama suka afkawa darusi su biyu aka ruguntsume da Azababben yaki tabbas idan kaji makaho yace ayi wasan jifa toya taka hoge A shie a cikin wannan tafiya sarila ta shammaci darusi tasa an zuba masa wani sinadari mai la anta idanu a cikin abincinsa yaci bai sani ba ai kuwa ana fara wannan gumurzu ne darusi yaji idanunsa sun daina gani gaba daya tamkar daman can shi makaho ne koda jin hakan sai ya shiga rokon Allah ya na mai cewa ya Allah indai saboda kai zanyi wannan aiki to ka zamo jina da ganina wohoho nan fa jama a suka sha mamaki da abin al ajabi da basu taba gani ba domin Darusi na makaho ya rinka yin gagarumar jarumtaka yayi ta yakar sarila da Sarki Damnashi har ya sami nasarar sare daya hannun na sarki Damnashi ya durkushe kasa yana kwarara uban ihu ita kuma sarila wani wawan naushi yayi mata a kirji tayi sama ta soke gadon bayanta a jikin wata bishiya nan take ta zama gawa ko shurawa batayi ba hm sarila an zama gawa sarauniyar makircin duniya sai muga ta mallakar wannan dukiyar ai + A wannan lokaci ne darusi ya shiga cikin kogon TASKAR AJALI a makancan ya dade a ciki sannan ya fito a raye cikin koshin lafiya take gaba daya jama ar dake wajan suka karbi Addinin musulunci Lokacin da aka dawo birnin su gimbiya suzaina sai aka iske bakaken Aljanun da sarki Damnashi a mace gaba dayansu mutanan gari kuwa babu abinda ya samesu cikin tsananin farin ciki aaka daura auran JARUMIN DUNIYA SADAUKI UBAN SADAUKAN DUNIYA WATO JARUMI DARUSI DANA GIMBIYA SARAUNIYAR KYAU WATO SUZAINA. Aka shiga shagali daga wannan rana aka sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a nahiyar gaba daya kuma addinin musulunci yaci gaba da yaduwa har izuwa sauran nahiyoyi....................................... ALHAMDULILLAH !!! Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya nufemu da kammala wannan littafi na TASKAR AJALI tun daga na 1 zuwa na 9 Ni guyson nake cewa Ku kasance da shafin http://hausaebooks.cf Don samun wasu kayatattun littatafan Yaki TASKAR AJALI Littafi na Tara 9 Marubucin littafin Abdulaziz Sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 14 of 14