Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gajine maza ka turomin abokin gwami na gaba daga cikin wadancen jaruman uku dajin haka sai alkalin gasa ya juya ya dubi inda jarumi darusi yazirina da sarila ke tsaye ya dubi yazirina yace kece mai wasa na gaba dajin haka sai yazirina ta dako tsalle daga inda take tsaye tamkar an cillota daga cikin baka ta dira a tsakiyar filin gasar ya zamana cewa ta zarar dake tsakaninsu da gimbiya suzaina bata wuce taku biyar ba kawai sai ta zare takobinta ta jujjuyata tana mai sarrafa ta cikin tsananin gwaninta take gaba dayan jama ar dake filin suka kaure da shewa gami da tafi saboda ba a taba ganin jarumin da ya iya sarrafa makami ba haka ita kuwa gimbiya suzaina saita dubi yazirina cikin murmushi gami da kallon raini kawai saita mayar da addunanta cikin kufensu dake rataye a bayanta ta gyara tsayuwarta kuma tayafito ta da hannu koda yazirina taga suzaina tayi mata irin wannan raini da wulakanci wato ma tafi karfin ta yaketa da makami sai ranta ya baci ainun ta yunkura cikin zafin nama da dukkan karfinta kuma cikin tsananin fishi ta rugo izuwa kan suzaina koda ya rage saura taku biyu kacal su hadu sai duk su biyun suka daka tsalle sama take yazirina ta kawowa suzaina sara a wuya da nufin ta cisge mata kai cikin bakin zafin nama suzaina ta sunkuya a saman takobin yazirina ta sari iska kafin yazirina ta waigo ta kawowa suzaina wani harin tuni suzaina ta gabza wa yazrina budu da kafarta akan kunnenta na dama. Take akaga yazrina ta fado kasa sumammiya ko kyakkyawan motsi batayi ba kuma ta kife kasa rub da ciki jini na yoyo a hancinta da bakinta a dimauce likitoci suka rugo izuwa cikin filin gasar suka dauke yazrina a lokacin da gaba dayan mutanen dake filin suka kame saboda tsananin mamakin yadda suzaina ta yiwa sarila kwaf daya haka ita kuwa jarumar jarumai sarila zuciyarta ce ta kama tafarfasa kamar zata kone saboda bakin cikin ganin abinda suzaina tayiwa yazirina don haka kafin ma alkalin gasar ya sake shigowa cikin filin gasar ya kira jarumi na gaba tuni sarila ta dako tsalle a sama daga inda take tsaye cikin shammace ta jerawa suzaina duka akan kirjinta sau biyu kuma ta naushi fuskarta sau daya saboda karfin naushin saida suzaina tayi taga taga saura kiris ta fadi kasa amma sai akaga ta tsaya cak a wannan lokacinne ta shafo lebenta taga dan jini sakamakon yar tsagewar da yayi koda suzaina taga jini a kan lebenta sai ta dako sufa daga inda take tsaye ta fyalli kafafun sarila, sarila tayi sama tayi juyi tamkar an murza tayi katantanwa kafin ta faddo kasa tuni suzaina ta daki kirjinta da karfin gaske saboda karfin dukan saida tayi sama ta fice daga cikin filin gasar gaba daya bayanta yaje ya gwaru da katangar gini amma sai akaga ta diro kasa bisa kafafunta amma sai da ta furzar da gudan jini daga bakinta kuma ta sosa kirjinta saboda tsananin zugi da radadin da taji Take itama ta dako sufa daga inda take tana mai zare takobinta kafin ta diro kan suzaina tuni itama ta zare addarta guda ta tareta sun ruguntsume da azababben yaki. Take ita ma sarila ta dako sufa daga inda take ta na mai zare takobinta kafin ta diro kan suzaina tuni itama ta zare addarta guda ta tareta sun ruguntsume da azababben yaki Wohoho, idan gwani da gwani suka hade kuma jarumta ka da sadaukantaka tayi karo da takwararta dole ne gumurzu ya zama ta shin hankali ga dan kallo ma ana fara wannan gumurzune hankalin yan kallo ya dugunzuma domin take jama a suka fara guduwa suna barin inda suke zaune a kewayen filin gasar saboda barazanar dirar makaman jaruman biyu a kan kujerunsu suna ragargajewa saboda tsalle tsallensu suna dira a ko ina tamkar kwari ko tsintsaye duk abinda suka sara ko suka soka a filin gasar take yake rabewa biyu ko kuma ya huje hatta sarki da jarumi darusi saida hankalinsu ya dugunzuma bisa ganin wannan mugun artabu da akeyi tsakanin gimbiya suzaina da sarila kafin cikar yan dakiku duk yan kallo dake gaba gaba a filin gasar sun tarwatse sun koma can baya babu shiri mutane suka rinka kama katanga suna hayewa don su tsira kuma saboda nacin son ganin yadda karshen gumurzun zai kasance saida jaruman biyu suka shafe kusan sa a guda suna ta fafatawa ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba alamar cewa iya yakinsu yazo daya gami da zafin namansu bisa dole kowannansu ya ja da baya sukayi cirko cirko suna haki saboda tsananin gajiya a lokacin da fadar tayi tsit tamkar mutuwa ta gifta kuma a lokacinne kurar da jaruman biyu suka tayar ta fara lafawa sai a dai dai wannan lokacine jaruma yazirina ta dawo hayyacinta bayan likitoci sun jima a kanta suna kokarin ceto rayuwarta a firgice ta mike zaune zumbur ta bangaje likitocin dake zagaye da ita ta rugo da gudu izuwa cikin yan kallo koda ta iso taga sarila da suzaina a tsaye suna kallon kallo kawai kuma kowannansu a kwai busashshen jini akan fuskarsa saita cika da tsananin mamaki domin a zatonta yadda suzaina tayi mata dukan farat daya haka itama sarila za ayi mata yazirina ta dubi jarumi darusi tace tabbas sarila ta cika jaruma amma yaya kake ganin yadda karshen wannan gumurzu zai kasance? Kafin darusi ya budi baki ya bawa yazirina amsa sai kawai yaga suzaina da sarila sun zubar da makaman hannunsu sun dunkule hannayensu koda ganin haka sai darusi ya gyada kai ya dubi yazirina yace ai yar uwarki ta tafka babban kuskure data yarda makamanta domin yanzu ne zata gane banbancinta da suzaina kafin darusi ya gama rufe bakinsa tuni sara da suzaina sun rugo izuwa kan juna sun ruguntsume da azababben yaki suka wanzu suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa ai kuwa a na fara wannan gumurzu a karo na biyu sai sarila ta raina kanta saboda suzaina ta fita zafin nama da karfin damtse kafin sarila ta naushi suzaina sau daya tuni suzaina ta jera mata naushi uku kuma karfin naushin nata ya ninka na sarila sau uku duk sa adda sarila ta kare naushin suzaina da hannayenta saitaji hannayanta nayin mugun zugi da radadi tamkar zasu kakkarye nan da nan suzaina ta kuntata sarila ya zamana cewa bata iya maida martani sai kokarin kare hari koda aka sake dan jimawa kadan sai kare harinma ya gagara nan fa sarila ta fara shiga cikin mugun hali domin tuni suzaina ta fara jera mata luguden naushi sai gani akayi tana furzar da jini daga cikin bakinta tana yin tangadi da layi tamkar wacce tasha giya ta budu A na cikin hakane suzaina ta shammaci sarila ta yi mata wani wawan dundu a gadon bayan take sarila ta sunkuya kasa tayi ruku'u a lokacin da taji wani irin mugun jiri ya kamata kuma idanunta suka kama lumshewa tana gani dishi dishi har suzaina ta yunkura zata gabzawa sarila naushi a fuskarta da kafarta sai ta hada idanu da jarumi darusi take yayi mata inkiyar kada ta bugeta kawai sai suzaina ta fasa dukan nata tasa danyatsanta guda ta ture ta take sarila ta tuntsire da baya ta baje a kasa ta kasa koda mikewa tsaye koda ganin abinda ya faru sai jama a suka rude da shewa ana tafi akaci gaba da yiwa gimbiya suzaina jinjina hatta sarki sai ya mike tsaye tare da matarsa suka rinka yiwa suzaina tafi gami da jinjina. ( Al amin Guyson ma saida ya tafa mata ) a dai dai wannan lokaci ne alkalan gasa ya shigo cikin filin gasar da sauri ya dubi suzaina yace shin zaki iya wasanki na karshe ne yanzu ko kuwa sai gobe ko anjima? Kafin suzaina ta bude baki tabada amsa sai jarumi darusi yayi wuce yace sai gobe da safe zan fafata da ita yana gama fadin hakan sai jama a suka kaure da shewa a dai dai wannan lokacine sarila ta mike zaune dakyar sa adda hawayen takaici ya subuto daga cikin idanunta ita kuma yazirina saita ruga da gudu izuwa gareta ta taimaka mata ta tasheta tsaye ta janyeta suka fice daga cikin filin gasar tare. Lokacin da magariba tayi sai darusi da mujahid na zaune a cikin turakarsu bayan darusi ya idar da sallar magariba yana zaune yana lazimi sai ga wani hadimin sarki ya shigo cikin turakar da sallama ya risina ga jarumi darusi yace ya shugabana sarki yace na shaidamaka cewa yana gaiyatarka izuwa Dare bayan sallar isha koda jin wannan batu sai darusi yayi murmushi ya dagawa hadimin hannu yana mai yi masa nuni da cewar ya amsa wannan gayyata kuma yana nan tafe nan take hadimin yayi musu sallama ya juya ya fita daga turakar fitarsa keda wuya darusi ya hattama lazimin nasa sannan yayi addu a ya shafa ya juyo ya fuskanci mujahid kawai sai yaga mujahid ya daga kansa sama yana kallon rufin dakin alamun cewa ya fada cikin kogin tunani mai zurfi koda ganin haka sai darusi ya dafa kafadarsa take mujahid yayi firgigit kamar wanda ya farka daga barci ya dubi darusi cikin alamun razana yace '' Eye me a kace? Darusi yayi dariya yace saboda me kake damun kanka a kan abinda bai damu da kai ba ina mai shawartarka daka koyi yadda ake danne zuciya a lokacin da ta kamu da son abu kamar yadda nake danne son gimbiya suzaina a cikin raina duk da cewa nasan tana tsananin kaunata, koda jin wannan tambaya sai mamaki ya turnuke mujahida yace kai kuwa yaya akayi kasan cewa tunanin sarila nake yi? Koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi yayi murmushi yace ai tatsuniyar gizo bata .wuce ta koki duk abinda mutum yake so yana tare dashi kada ka manta cewa tun a farkon haduwarmu daku na gane cewa kana matukar son saril abinda zan yi maka albishir dashi shine mahakurci mawadacine kaci gaba da jira akwai lokacinda sarula zata baka soyayyarta amma ba yanzu ba koda jin wannan batu sai mujahid ya kamu da tsananin farin ciki bai san sa adda ya rungume darusi ba yana mai cewa yaya akayi kasan cewa sarila zata soni a nan gaba? Darusi yace bana duba ba na tsafi amma ina amfani da tunani ne da kuma hangen nesa a yanzu haka son da kake yiwa sarila yasa ka kasa karbar addinina saboda kana tunanin cewa idan ka karbe shi bazata taba yarda dakai ba har ta baka soyayyarta toka sani nayi maka uzuri kuma nayi maka alkawari akwai lokacin da zaizo komai ya daidaita mujahid ya dubi darusi cikin alamun rashin fahimta yace me kake nufi da cewar akwai lokacin da komai zai dai daita darusi ya sake yin murmushi yace wai shin me kake ci ne na baka na zuba ka sani cewa gaggawa aikin shaidanne zaka ga komai da idanunka kawai kabi a sannu har jarumi darusi ya yunkura zai mike sai mujahid ya ruko hannunsa yace dashi ina kuma zaka tafi ka barni alhalin ni ma ina da wata magana mai mahimmanci wacce zan gaya maka? Darusi yace ina son zanje masallaci ne na zauna naci gaba da addu oina saboda ina da wadansu manyan bukatu a gabana wacce magana ce mai mahimmanci wacce tun tuni baka sanar daniba? Mujahid yayi ajiyar zuciya yace ka taka a hankali na fahimci cewa yazirina ta kamu da sonka kuma ita ma tana son ta karbi addininka koda jin wannan batu darusi yayi murmushi yace sai yanzu haka tuntuni na san da hakam amma saboda nasan cewa ba abune da zai yiyuba shi yasa tuntuni ban daukeshi da mahimmanci ba darusi na gama fadin hakan sai ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin shikuwa mujahid saiya bishi da kallo kawai yana mamakin irin kwakwalwarsa da kuma basirar da Allah ya bashi. ++ ++ A can ban garen masaukin su sarila kuwa bayan sunci abinci sun sha magunguna bisa tsamin jikinsu saboda dakuwar dasukayi a filin gasa sai suka kishingida akan shimfidunsu cikin tsananin gajiya tamkar zasuyi barci amma sai dukkaninsu idanunsu suka bushe kowacce tayi shiru tana tunanin a cikin ranta tsawon yan dakiku dayansu baice kala ba daga can sai sarila taja dogon numfashi ta ajiye ta dubi yazirina cikin alamun tsananin takaici tace a duniya ba a taba tozarta jarumtakata ba da wulakantani kamar yadda suzaina tayi mini ki sani cewa a halin yanzu ina jin tsananin kiyayyarta a cikin zuciyata fiye da yadda na tsani mtuwata kuma na rantse da girman mahaifinmu saina cusa mata bakin ciki da zata tafi dashi har kabarinta koda jin wannan batu sai yazirina ta dubi sarila cikin alamun tsananin mamaki tace ke kuwa ta yaya zaki sami nasarar cusawa suzaina bakin ciki alhalin ta fiki komai ta fiki kyau ta fiki jarumtaka gami da dukkan gata na duniya sa adda yazirina tazo nan a zancenta sai sarila ta bushe da dariyar mugunta lokaci guda kuma ta hade fuskarta tace. Al amin Guyson ke magana idan mutum ya zame maka alakakai kana tsayawa ne kayi tunani ka gano lagonsa suzaina bata da wani lago face son da take yi wa jarumi darusi daga yau zan fara kafa bacin soyayyarsa a kan darusi kuma dole yadda zanyi na ribaceshi na rabashi da ita sai nayi wannan shine babban makamin da zan iya tarwatsa rayuwar suzaina da shi ina mai tabbatar miki da cewa sai na mallaki jarumi darusi komai rintsi da tsanani koda kuwa sama da kasa zata hade zan jure duk irin wulakancin da zaiyi mini kamar yadda na wulakanta shi a baya har sai zuciyarsa ta karaya ya kamu da tsananin kaunata ki sani cewa ba wai sai da kyau da kudi ko jarumtaka ba mace zata iya siye zuciyar da namiji ba akwai hanyoyi na kissa gami da nuna masa tsananin so da kuma sihiri wanda bana tsafi ba akwai sirrika da dama na al ada wadanda na gada tun iyaye da kakanni lokacin da sarila tazo nan a jawabinta sai hankalin yazirina ya dugunzuma ainun idanunta suka Zazzaro cikin alamun tsananin damuwa ta dubi sarila tace amma dai ni a ganina bai kamata kiyi haka ba kuma ko kin aikata hakan ba zaki yi nasara ba dajin haka sai sarila ta dakawa yazirina tsawa ta firgita ainun har hantar cikinta ta kada sannan sarila ta dubeta a fusace tace kada ki daukeni wata shasahsha ki dauka cewa bansan abinda ke cikin rankiba toki sani tun a farkon haduwarmu da jarumi darusi na gane cewa kin kamu da sonsa ki kwantar da hankalinki ni soyayya ta a gareshi bata gaskiya bace kawai zanyi amfani da shine izuwa tsawon dan lokaci sannan na bar miki shi idan kika kuskura kika tona mini asiri bisa abinda nake shirin kullawa mutuwace hukuncinki koda gama fadin hakan sai jaruma sarila ta juyawa yazirina baya ta rufe idanunta ta kama barci abinta ita kuwa yazirina hankalinta ne ya dugunzuma ainun ta rasa abinda ke mata dadi a duniya bayan an gabatar da sallar isha i a masallaci jama a sun fito daga cikin masallacin sai sarki ya kama hannun jarumi darusi ya ruke ya jashi suka tafi izuwa can turakarsa domin suci abindin dare tare kamar yadda ya tsara lokacin da suka fara tafiya a cikin harabar gidan sarautar sai sarki yace wai shin menene dalilin da yasa kaki yarda kuyi wasan karshe na wannan gasar jarumtaka ayau dinnan ? Koda jin wannan tambaya sai darusi ya maidawa sarki martanin murmushi yace ya shugabana kowa a garin nan ya san irin jarumtaka ta kuma ansan cewa nafi suzaina iya yaki da karfin damtse dukda cewa sa adda muka fafata a waccen gasar da kyar na sami nasara akanta ka tuna cewata gaji likis a lokacin da tayi wannan gumurzu har sau uku a filin gasa idan muka fafata na bata dama tayi nasara dole mutane su gane cewa alfarma nayi mata amma idan a gobe ne muka fafata dukkaninmu zamuji jiki kuma yan kallo zasu gamsu da dukkan sakamakon karshe na gasar koda darusi yazo nan a jawabinsa sai sarki yayi dariya yace tabbas Allah ya hore maka basira da hangen nesa irinka basu da yawa a duniya amma abinda nake so dakai shine a gobe idan kuka fafata kada ka bata dama ta sami nasara a kanka kai nake so ka karbi kambun gasar daga hannunta koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke darusi yace ya shugabana me yasa kake son na karbi wannan kambun jarumta daga hannun yarka sarki yayi ajiyar zuciya yace yakai wannan jarumin jarumai ina so ka sani cewa duk abubuwan da suke faruwa a yanzu a cikin birnin nan nawa manyan sarakunan dake wannan nahiya da manyan bokaye suna gani ko kuma ince suna samun labari idan aka ga ka karbi wannan kambun jarumtaka zukatan makiya zasu karaya su fara tunanin cewa lallai addininka abin gasgatawa ne musamman a nan gaba idan akaga kun shiga cikin Kogon Taskar Ajali ka fito a raye cikin koshin lafiya Al amin guyson ke magana koda sarki yazo nan a zancensa sai darusi ya cika da mamaki ya jinjinawa sarki yace tabbas duk wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi gashi dai yanzu saboda ka rigani zuwa duniya ka hango mini abinda ko kadan ban yi tunaninsa ba a cikin kwakwalwata koda jin wannan batu sai sarki ya rungumo darusi a jikinsa ya bushe da dariya yace wannan gaskiya ne to amma akwai wani abu guda danake so na gaya maka lallai kayi tsantsan da duk masoyanka da makiyanka domin a ko yaushe komai na iya sauyawa sa adda jarumi darusi yaji wannan batu sai hankalinsa ya dugunzuma yai sauri ya janye jikinsa daga jikin na sarki ya dubeshi a firgice yace ya shugabana me kake nufi da na kula da masoyana da makiyana komai na iya sauyawa? Sarki yayi murmushi sannan yace ka zamo mai hakurin jin amsar wannan tambaya a yanzu ka nutsu ka yi amfani da basirarka da kwakwalwarka domin ka gano komai saboda yin hakan shine sanin karatun a cikin wannan duniya wacce ta kasance babbar makaranta koda gama fadin haka sai sarki yayi shiru bai kara cewa uffan ba yaci gaba da jan hannun darusi har izuwa cikin falon turakarsa da shigarsu cikin turakar sai sukayi kicibis da gimbiya suzaina a zaune bisa kan teburin cin abincin ta caba ado na musamman ga mahaifiyarta zaune a kusa da ita fuskar suzaina na cike da annuri gami da murmushi ta mike tsaye ta tarbi sarki tana maiyi masa maraba da zuwa kuma ta ruko hannun damansa suka taho tare izuwa kan teburin abincin da isowarsu sai mahaifiyar suzaina ta mike ta karbi sarki daga hannunsu tace ku bani abina domin nan fada tace bata kowa ba dajin haka sai suka bushe da dariya gaba daya jarumi darusi sai yar guntuwar dariya ya sake ya hada idanu da suzaina sai ya hada rai da yake suzaina ta san laifin da tayi masa ko kadan bata damu da fishin da yake yi ba kawai sai yaci gaba da sha aninta batare da bata wani lokaci ba mahaifiyar suzaina ta zubawa sarki da suzaina abincin a kan faranti din dake gabansu kafin a zubawa darusi sai suzaina tayi wuf ta zuba masa nan dai kowa yayi bismilla a ka fara cin abincin inda jarumi darusi ya kasa daga kansa ko sau daya ya dubi sarki da matarsa saboda tsananin kunya kuma da kyar ma ya iya yin loma biyu koda sarki ya fahimci halin da jarumi darusi ke ciki sai ya dubi matar tasa yace abincin nan ya fita daga raina kayan Marmari kawai nake bukata ki je ki kaimini cikin turakata a yanzu yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya nufi cikin turakarsa cikin hanzari itama mahaifiyar suzaina ta mike tsaye ta nufi wani dakin da ban koda ganin haka sai shima jarumi darusi ya ajiye cokalin da yake cin abinci ya mike tsaye da nufin ya fice daga cikin falon amma sai suzaina tayi wuf ta mike da sauri tasha gabansa kamar zata rungume shi domin ta kusance shi ainun har suna iya jin numfashin juna .... . ME ZAI FARU MU HADU A CIKIN LITTAFI NA TAKWAS (8) DONJIN CIGABAN WANNAN KASAITACCEN LABARI TASKAR AJALI Littafi na Takwas 8 Na Abdulaziz Sani M Gini Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com CIKIN RAZANA DARUSI yaja da baya amma sai ta matse shi a jikin bango ta dubeshi tace' wallahi idan ka sake yunkurin guduwa zan rungumeka na kankame jikinnka koda jin wannan batu sai ya tsaya yace don Allah kiyi hakuri karkiyi min haka wai shin ke bakya jin kunya ne sarki ko ummanki ta leko ta ganmu a haka? Suzaina ta kyalkyale da dariya tace menene don an ganmu a rungume da juna waye bai san cewa ni dakai masoya bane na kwarai iyayen na sun yar da da imaninka da kuma tsoron Allan ka sun san cewa bazakayi wani mugun abu ba a gareni wanda ya sabawa shari'a darusi ya murtuke fuska yace amma dai ni kin sani cewa haramun ne mu hada jiki ni dake tunda ke ba muharramata bace suzaina ta sake yin dariya tace to mun hada jikinne yanzu harda zaka fara yi min wa azi idan kana son na matsa daga kusa dakai saika furta da bakinka kace ka yafe mini laifin da nayi dazu a filin gasa koda jin wannan batu sai darusi ya sake hada rai yace ai ba a wajena zaki nemi gafara ba face a wajan Allah saboda shine ya hana mana nuna tsiraici saboda me kike sanya sutura data baiyana dukkan surar jikinki? Koda jin wannan tambaya sai suzaina ta sunkuyar da kanta cikin alamun takaici tace tabbas na san na aikata zunubi kuma tun a sannan nake ta yin istigfari amma nayi hakane domin na karya zuciyar sarila da yar uwarta domin su gane cewa nafi su komai kuma nayi musu nisan da ba zasu iya kamoni ba tunda Allah ya yi mini baiwar da basu da irinta Wannan shine bukatar ka kamar yadda na sami labari daga bakin abokin tafiyarka mujahid asirrance tun kafin ayi wannan gasa burina shine kowa ce irin bukata taka ta biya lokacin da gimbiya suzaina tazo nan a jawabinta sai murmushi ya subucewa jarumi darusi yace to shi kenan na gode amma daga yau kada ki sake aikata duk abinda kika san cewa Allah ya hana duk da dai nasan akwai dokokin Allah da yawa wadanda baki sani ba amma dai aikin san wadansu kafin jarumi darusi ya gama fadin abin dake bakinsa tuni gimbiya suzaina ta sumbaci kumatunsa ta juya cikin sauri ta ruga izuwa cikin gida tana mai cewa yau zanyi barci mafi dadi a dukkan kwanakin rayuwata na duniya caraf sai taji darusi ya kira sunanta take ta tsaya cak amma sai taki yarda ta juyo ta fuskanceshi saboda a zaton ta wani laifi ta aikata yanzu kawai saiji tayi darusi yace gobe da safe idan Allah ya kaimu mun hadu a filin gasa kada ki ragwanta mini ko kadan domin nima ba zan ragwanta miki ba ko kadan duk damar da kika samu kada kiyi wasa da ita domin so nake muyi gasa ta tsakanin da Allah domin na karbi wannan kambu daga hannunki ki nemi taimakon Allah nima shi zan nema duk mai sa a da rabo sai ya samu koda jarumi darusi yazo nan a zancensa sai gimbiya suzaina ta kamu da tsananin mamaki cikin kaduwa ta juya da sauri domin ta tambayeshi dalilin wannan jajircewa da yake son duk su biyun suyi sai kawai taga ya yi wuf ya fice daga cikin falon yabi ta wata kofar wacce zata kaishi can hanyar da zata kaishi inda masaukinsa yake Al amin Ahmed guyson nake cewa. Nan take jikin gimbiya suzaina yayi sanyi taji kamar ta buya a wani wurin inda ba za a ganta ba saboda kada ta halacci wannan gasa ta gobe amma data tuna cewa rashin zuwanta gasar zai lalata tarihin gasar ma gaba daya sai hankalinta ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe haka dai suzaina ta kama tafiya a cikin gidan sarautar ba tare da sanin inda ta dosa ba saboda damuwa gami da tunanin zuci Al amarin da ya janyo ta nufi bangaren masaukin su jaruma sarila kenan ba tare da ta ankara ba sai dai wannan lokaci sarila na zaune a kofar dakinsu daga ita sai wani mayafi daurin kirji kuma ta juya baya ne tana tsefe gashin kanta tana tasheshi da mataji kawai sai suzaina ta bugi kujerar da sarila take zaune a kai bata sani ba mayafin dake jikin sarila ya cire ya fadi can gefe daya tayi tsirara kuma gashi a lokacin kuyangin gidan sarautar na zaune a wajan cikin tsananin dimauta suzaina ta mike zumbur ta ruga inda mayafin sarila ya fadi ta dauko shi ta sake rugowa da gudu zuwa gareta da nufin ta rufe mata jikinta kawai sai sarila ta fisge mayafin ta yi jifa dashi sannan ta dubi suzaina a fusace cikin tsananin kiyayya tace meye nufinki ki suturce jikina alhalin kinyi min tsirara a gaban bayi domin ki tozartani koda jin wannan batu sai suzaina ta ce ko kadan banyi niyar tozartaki ba tsautsayine yasa nazo na doki wannan kujera saboda bana cikin hayyacina sakamakon halin da na shiga na tsananin tunani koda jin wannan batu sai sarila ta bushe da dariya har izuwa wani lokaci bata rufe bakinta ba kuma babu alamar tanajin kunyar tsiraicin data yi kawai sai sarila ta murtuke fuskarta ta sake duban suzaina a cikin alamun kiyayya mara misaltuwa a karo na biyu tace na rantse da girman shekaruna sainayi ramuwar gaiya a kanki lallai sainayi miki tunbur a gaban dimbin mazajen garin nan domin na kunkatar da mutuncinki da darajarki koda jin haka sai suzaina tayi hailala tace da izinin Ubangijin musulunci ba zaki samu wannan dama ba koda kuwa a cikin daji ne Ba wai a cikin gari ba gaban al umma sarila ta yi murmushi na mugunta tace kada ki.manta cewa akwai doguwar tafiya a gabanmu tunda tare dake zamu tafi izuwa kogon TASKAR AJALI zan ga yadda zaki iya tsallake dukkan sharrina A dai dai wannan lokacine yazirina ta fito daga cikin turakarta su itama tana taje gashin kanta batare da tasan abinda ke faruwaba koda ta hango sarila a tsaye tumbur a gaban suzaina suna ta sa insa sai ta ruga da gudu ta lullube jikinta ta shiga rarrashinta tana bata baki haka dai ta janyeta da kyar suka shige cikin turakarsu wannan abu daya faru a tsakanin suzaina da sarila sai daya jefa suzaina cikin tsananin damuwa da tashin hankali har saida tayi kuka kuma har dare ya yi nisa batayi barciba koda taga haka sai ta mike tsaye taje tayi alwala sannan ta zotayi nafila raka a biyu ta shiga rokon Allah tana mai cewa ya ubangijin komai da kowa ka shiga tsakanin na gari da mugu ka sani cewa bada gaiya nayiwa sarila wannan abu ba a bisa tsautsayine amma gashi tana son ta dauki mugun mataki a kaina ya Allah ya ubanginin sammai da kassai ka kare ni daga dukkan sharrinta Aikuwa gimbiya suzaina na cikin yin wannan Addu a ne tafara yin gyangyadi daga zaune daga can kuma saita bingire ta kama barci batare da tasaniba suzaina bata farka daga barcin da takeyi ba har saida akayi kiran sallar assalatu saida gari ya waye sosai sannan jama a suka

Chapter 11 of 14