Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
jakar guzurinta ta fiddo wannan Allon Katako sannan ta fiddo jemammiyar fatar ta ajiye akan tebur ta jonasu tare sai ga Taswirar ta hadu saura kaso daya babu.Yazirina tayi ajiyar zuciya ta dubi Mujahid yace yanzu saura kaso daya na wannan taswirar ya rage na hada da wadannan biyun sannan na gano hanyar da zanbi takai ni Taskar Ajali shin ko kasan a ina Taswira ta ukun take?Mujahid ya gyada kai yace ta yaya za'ayi na sami alhalin ta biyun ma sai yanzu nasan cewa tana wajenki,abinda na sani kawai shine mai gidana Boka Kaisu Bin Alkama ya turo ni gareki domin na sato masa wannan jemammiyar fata.Inda ya san cewa kina tare da wannan Allon Katako ma ai saiya umarceni dana hado dashi.Lokacin da Mujahid yazo nan a jawabinsa sai Yazirina ta bushe da dariya sannan ta nutsu tace ai shi wannan Allon Katako babu wani mahaluki dayasan cewa yana tare dani sai kai a yanzu sai kuma yar uwata Sarila zata zo tayi farauta ta,inason ka saurara da kyau kaji tambayoyin da zanyi maka yanzu kamar yadda na gaya maka tun a farkon haduwarmu cewa inada tambayoyi a gareka.Kasani cewa albarkacin wadannan tambayoyi ne wadanda bansan amsarsu yasa na jaka a jikina muka kasance tare har yanzu in ba don haka ba na tsani yin kusanci da 'da namiji.Koda kuwa wanda yayi sanadiyyar zuwana wannan duniyar ne,ina zaune tare dakai ne bisa larura amma duk da haka bazan yarda mu kwana a wuri daya ba kuma ko a mafarki kada ka kuskura kabar hannunka ko jikinka su rabi nawa.Idan hakan ta faru zaka gane kurenka,kada kayi kokarin lekowa wannan falo a lokacin danayi barci idan na fahimci hakan zaka sha wahala.Tambaya ta farko itace a ina fadar maigidanka Boka Kaisu take?Nayi iya kokarina akan na gano hakan na kasa,Tambaya ta biyu itace shin ka taba ganin wani farin kambu a hannun Boka Kaisu?Tambaya ta uku wacce itace ta karshe itace shin zaka iya sato mini wannan farin kambu dake hannun Boka Kaisu?Abinda nake nufi shine inason dara taci gida,ka dade kana yiwa sauran bokaye sata da manyan sarakuna da manyan attajirai,wannan karon maigidan naka nakeson ka yiwa sata.Kada ka kuskura kayi mini karya a cikin amsoshin da zaka bani domin dole ne na gano karyar taka kuma idan haka ta faru saika gwammace mutuwa da rayuwarka.Lokacin da Jaruma Yazirina tazo nan a cikin zancenta sai hankalin Mujahid ya dugunzuma ainun fiye da koyaushe ya rasa abinda ke masa dadi a duniya don haka saida ya shafe yan dakiku yana tunani har gumi ya tsatstsafo daga cikin kansa sannan ya dago kai ya dubi Yazirina yace,Fadar mai gidana Boka Kaisu tana can cikin wani daji da ake kira Darul Kinsasa a cikin yankin Birnin Kisra fiye da shekaru talatin baya fatake suka hakura da ratsawa ta cikin wannan daji,babu mai iya shigarsa face Boka Kaisu da wadanda ya lamincewa wato irinmu da muka kasance manyan hadimansa,dangane da tambayarki ta biyu,tabbas naga wani farin kambu a damtsen hannun hagu na Boka Kaisu kuma wani lokacin ma na kanga ya ciro kambun daga hannunsa ya kura masa idanu.A kan tambayarki ta uku kuwa a gaskiya bazan iya sato miki wannan kambu ba saboda nasan irin tsananin sihirin da tsaron Boka Kaisu yafi gaban ace wani barawo ya shiga har cikin fadarsa ya sami nasarar yi masa sata.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta bushe da dariyar farin ciki sannan ta dubi Mujahid tace kai samari babu wani abu wanda bazai yiyuwa ba a wannan duniya face wanda ba'a jarraba yinsa ba.Lallai zaka rakani izuwa fadar boka Kaisu tunda ba zaka iya yi masa sata ba,lallai ina bukatar wannan kambu na hannunsa domin shine abu na farko dazai iya tserar dani daga sharrin Sarila.Sa'adda Jaruma Yazirina taji wannan tambaya sai tayi ajiyar zuciya tace idan har wannan kambu na hannuna da zarar Sarila ta dira a cikin wannan duniya zai sauya kala ya koma ja,kuma ko barci nakeyi saiya tasheni sannan zai sanar dani a inda take da kuma tazarar dake tsakanina da ita,abu na biyu da zai iya kareni daga sharrin Sarila ba komai bane face wani bakon saurayi wanda ya kasance dan baiwa mai tsananin sa'a da rabi bisa duk abinda tasa a gabansa shidai wannan saurayi bashi da KARFIN DAMTSE ko na sihirin tsafi kuma ko takobi bai iya rukewa ba.Ni kuwa yanzu babban abin fargabata shine bansan a inda zanga wannan saurayi ba har na iya shaida shi kuma bansan lokacin da Sarila zata baiyana ba da kuma inda zata baiyana.Babu mamaki ma ta baiyana a inda nake ban sani ba ta shammaceni ta kashe ni ta rabani da wadannan taswirori guda biyu.Lokacin da Yazirina tazo nan a jawabinta sai Mujahid yaji tsigar jikinsa ta tashi kuma yaji ya tsargu a cikin zuciyarsa,ba komai ne yasa yaji ya tsargu ba face yasan cewa shima ai bashida karfin sihiri kona damtse sannan kuma yana da tsananin sa'a da da rabo bisa duk abinda yasa a gabansa.Anya kuwa bani bane wannan saurayi wanda Yazirina take nema?A wata zuciyar kuma sai tace da Mujahid kai dai wawa ne ta yaya zaka kasance kaine saurayin da taje nema alhalin tuni ta sanka,duniya ma ta sanka,kaine mashahurin barawon daya addabi bokaye da sarakai da kuma manyan attajirai.Mujah id na cikin yin wannan tunani ne Yazirina ta katse shi tace mekake tunani?Cikin rawar murya yace babu komai,kawai ina tunanin cewa kin jefa ni cikin TSAKA MAI WUYA ne domin tsakanin keda maigidana Boka Kaisu bansan wanda ya kamata na butulcewa ba domin na tsira da rayuwata.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta kyakyale da dariya har da fadowa kasa daga kan kujerar da take zaune.Daga can kuma ™Abubakar Haleefah Physicist™ saita nutsu ta dubeshi tace kana burgeni saboda halayenka guda biyu,na farko shine tsananin tsoronka,ba biyu kuma shine son duniyarka.Koda jin haka sai Mujahid yayi murmushi yace ai komai son duniyata ban kama farcen kafarku ba dakeda manyan sarakunan nan hudu da kuma manyan bokaye irin su Miagida na Boka Kaisu tunda kun sallama rayuwarku domin kuje inda ba'a zuwa a dawo a raye don kawai ku debo dukiyar da babu irinta a cikin fadin wannan duniya.Yazirina tayi murmushi tace aini dama na cancanta da debo wannan dukiya tunda ta mahaifina ce.Koda jin haka sai Muhajid ya zaro idanu cikin alamun matukar mamaki yace dama ke yar boka Salmara ce?Tabbas na sami labarinki a wajen Boka Kaisu amma bai taba bani labarin yar uwarki ba Sarila.Hankalinsa gaba daya a kanki yake ba'a kan Sarila ba alhalin ta fiki hadari.Koda jin wannan batu sai Yazirina tayi murmushi tace ba komai bane yasa Boka Kaisu baya tsoron Sarila saidon yana da wannan kambun sihirin a tare dashi,kafin ta cimmasa yasan a inda take kuma yasan inda zai gudu ya buya shi yasa nima nakeson na raba shi da kambun.Na yanke shawarar nayi kwana bakwai ne anan birnin Yamein saboda jikina ya bani cewar nan ne birni Na farko Inda Sarila zata fara baiyana saboda inda Mahaifiyata ta fara zama kenan a farkon yawon duniyarta kuma a nanne ta fara haduwa da mahaifina wato Boka Salmara.Lallai inason nayi FITO na FITO nida Sarila domin naga iyakar KARFIN DAMTSE nata da iya yakin nata wanda ake bani tsaro dashi.Gama fadin hakan keda wuya sai sukaji an kwankwasa musu kofar dakin.A firgice Mujahid ya mike tsaye zumbur ya ruga izuwa bayan Yazirina yana kokarin buya,Yazirina tayi dariya tace to farar kura jeka ka bude kofar ba hari aka kawo mana ba.Cikin dari dari Mujahid yaje ya bude kofar kawai sai yaga ashe daya daga cikin matan banzan ne na gidan dauke da farantin abinci,karuwar ta dubi Mujahid cikin murmushi da kallo irin na halikata da kwarkwasa ta mika masa abincin har ta juya zata tafi sai Yazirina ta bude baki tace dawo ki shigo nan.Cikin alamin tsananin tsoro jikinta na tsuma karuwar ta shigo cikin dakin ta zube kasa agaban Yazirina,faruwar hakan keda wuya sai Yazirina ta yaye mayafin data lullube fuskarta da jikinta ta dubeshi tace meye sunanki?Ba tare data dago kanta ba tace suna na Siyama.Yazirina tace inason ki bude wannan abinci kici kuma ki zauna a nan tare damu har tsawon sa'a guda.Koda jin wannan batu sai jikin Siyama ya kama karkarwa sosai tamkar an tsomata a cikin ruwan kankara,kuma sai takai hannun ta izuwa kan kwanunkan abincin amma sai ta kasa bude kwanukan.Koda ganin haka sai Yazirina tayi murmushi tace tashi kiyi tafiyarki amma ki saki jikinki kada ki kuskura ki gayawa saurayinki abinda ya faru yanzu tsakanina dake.Koda jin haka sai farin ciki ya lullube Siyama ta kama godiya ta mike tsaye da sauri ta fice daga cikin dakin tana fita sai Yazirina ta dubi Mujahid tace saurayinta ne ya bata guba ta zuba mana a cikin abincinmu kuma ba wani bane saurayin nata ba face wannan katon dana fara karyawa kuma dan leken asiri ne na shugaban dakarun sumamen da suka kawo mana hari na farko.Yana da kyau musan kowane uban gidan nasa tunda ba sarkin garin nan bane,shima sarkin nemana yake ruwa a jallo.Tunda naga ya aiko dakarunsa domin su kamani,abinda nakeso dakai shine kaje ka gayawa Andalu na janye dokar dana kafa ta shige da fice a cikin gidan,lallai idan dare ya raba a bude kofar gidan a cigaba da harka kamar yadda aka saba.Koda jin haka sai tsoro ya kama Mujahid yace haba ya shugabata in kikayi haka ai tamkar kin tona asirin inda muke ne duk masu farautarki zasu iya riskarki a koyashe.Yazirina tace sau tari zama a kusa inda ba'a zatonka yafi sirri akan ka tafi nesa,sai kayi ganganci gami da saida rai sannan ka kan tsallake hadari,ka kwantar da hankalinka babu abinda zai samemu domin nasan abinda baka sani ba.Koda jin wannan batu sai hankalin Mujahid ya dan kwanta ba tare da wata fargaba ba sai ya juya ya sauko kasan benen yaje ya isar da sakon Yazirina izuwa ga Andalu kuma a gaban mutane ya fadi sakon,Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan.Lokacin da Mujahid ya koma sama benen saiya iske Yazirina ta sauko daga kan kujerar ta kishingida a kasa ga jakar guzurinta rataye a kafadunta kuma ta lumshe idanu kamar barci takeyi.Koda ganin haka sai Mujahid ya tura kofar falon ya rufeta ruf yasa sakata da kuba sannan ya wuce kai tsaye izuwa cikin dakin data umarce shi daya shiga ya kwana a ciki.Yana shiga ya rufo kofar ya fada kan gado ya haye faruwar hakan keda wuya kuwa sai barci ya saceshi nan da nan.Can sa'adda dare ya raba sai kawai akaji wata irin iska mai karfi ta soma kadawa iskace mai ban tsoro irin wadda ba'a saba jinta ba domin tana dauke da wani irin sauti mai kama da tsatstsagewar duwatsu,daga can kuma sai sararin samaniya ta sauya launi tamakr wata damina ne alhalin ana cikin tsakiyar bazara.Kawai sai akaji an kwada wata irin tsawa mai tsananin karfi data firgita komai da kowa gami da walkiya mai ban tsoro,duk jama'ar dake yin barci saida suka farka a birnin na Yamein gaba dayansu.Tsuntsaye da dabbobin dake cikin garin da daji suka firgice suka kama guje guje da iface iface suna neman maboya,mutane kuwa saboda dimaucewa basu san sa'adda suka kama shigewa cikin karkashin gado ba da cikin rijiyoyin gidajensu ba wasu ma suna hallaka kansu a banza.Kwatsam sai akaji wani abu ya fara yowa kasa jif wanda nauyinsa ya haddasa girgizar kasa a birnin gaba daya.Karar tsawar da akayi bata sa Yazirina ta farka daga barci ba amma dirar wannan abu sai yasa ta farka a firgice,jakar guzurinta ™Abubakar Haleefah Physicist™ ta fara dafewa ta tabbatar da cewa tana tare da ita,cikin hanzari ta mike tsaye ta zare takobinta ta ruga izuwa kofar dakin da Mujahid ke kwance ta doki kofar da kafarta.Take kofar ta balle ta fadi kasa Mujahid ya mike zaune zumbur a dimauce ya dubeta yace shin kema kinji muguwar tsawar da aka tafka kuwa yanzu?Maimakon Yazirina tace dashi wani abu sai ta cakumi rigarsa tajashi izuwa falon sannan ta dubeshi tace wannan tsawa da kaji ba itace abar tsoro ba abinda ya diro kasa daga sama ya haddasa girgizar kasa shine abin tsoron.Naji a jikina cewa Sarila ce ta biyana zo muje mu gani da idanunmu ko itace din.Koda jin haka sai tsoro ya baibaye Mujahid ya dubi Yazirina yace kiyi mini rai nidai ki barni na nemi wajen buya,koda jin haka sai Yazirina ta dakawa Mujahid tsawa tace baka da hankali,idan ni da kai muka buya bamu fuskanci Sarila ba gaba dayan mutanen dake cikin gidan nan sai sun mutu.Dole ne muje mu tareta domin mu kare rayukan miliyoyin jama'ar garin nan da dukiyoyinsu,cikin mamaki Mujahid ya dubi Yazirina yace yaya ni da ban kasance Jarumi ba zaki ce na biki mu tari Sarila?Yazirina tace nasan cewa kai ba jarumi bane amma ai kana da sa'a da rabo kuma kai da bakinka ka fada mini hakan,tana gama fadin hakan sai ta kama hannun Mujahid a karo na farko taja shi suka fice daga cikin dakin gaba daya suka fara kokarin saukowa kasa daga kan matattakar benen.Ashe adaidai kofar wannan gida ne wannan abu mai nauyi ya fado kasa kuma ba komai ne ya fado daga saman ba face JARUMA SARILA.Inda ta fado din saida kasar wajen ta rufta tayi rami tamkar wani dutsen mai nauyi ya fado wajen.Sarila na sanye da jar riga da wando na miski matsatstsu wanda suka bayyana kyakkyawar surar jikinta,takalman kafarta ma dogaye ne na fata masu madauri a kuibin cinyoyinta dama da hagu wadana manyan Adduna ne guda biyu a cikin kufe.Sarila ta kasance doguwar mace mai kyawun surar jiki da kyawun fuska a bar kwatance amma kuma wannan kyawu nata kyan dan maciji ne domin inda ansan irin tsagwaron rashin imaninta da irin zaluncinta ba za'a sami namiji dazai kaunace ba.Lokacin da Sarila ta diro kasa daga sararin samaniya kafafunta suka bugi kasa wajen ya loba yayi rami kura ta turnuke wajen saita mike tsaye ta nufi cikin gidan yan bariki,dama an bar kofar a bude kawai sai ta kunna kai izuwa cikin gidan.A wannan lokaci gaba dayan mazajen gidan sun firfito sun zazzauna a falon duk da cewa akwai sabuwar karaya a jikin kowannensu suna ta shaye shayensu na giya da busa sigari,yan caca ma na sha'aninsu tamkar Yazirina batazo ta hargitsa gidan ba a yau.Dama a najin wannan tsawa da kuma karar durowar Sarila sai kowa ya firta ainun maza da mata suka yunkura da nufin su leke waje suga abinda ya fadi kasa sai ga Sarila ta shigo tana wani murmushi na mugunta.Koda ganinta sai maza suka fara yin murmushi gami dayi mata kallon raini,nan take wani katon saurayi mai son matan tsiya ya durfafi Sarila yakai hannu da nufin ya taba Kirjinta.Caraf ta rike hannun nasa ta cincika kawai sai akaga hannun gaba daya ya cisgo daga cikin kafadarsa,jini yayi feshi,katon ya kurma uban ihu kuma ya sulale kasa sumamme.Koda ganin abinda ya faru sai kowa ya girgita ainun,mazan dake wajen ma basu san sa'adda suka fara sakin fitsari ba a wando.Saida Sarila ta shigo tsakiyar falon ta karewa kowa kallo sannan ta bude baki tace ina yar uwata Yazirina take?Ku hanzarta sanar dani ko yanzun nan dukkaninku ku zama gawa.Kafin Sarila ta gama rufe bakinta sai kawai taji ance gani nan idan kinason ki karbi abinda kikazo nema a saukake ki kyale kowa ya fice daga cikin gidan nan.Yazirina ce ta fadi hakan a lokacin da take saukowa kasa daga kan matattakalar benen,Mujahid na take mata baya. Toofah!!!Nima ganin Sarila ta baiyana da yadda ta cisgewa wannan katon hannun farat daya da kuma haduwarta da Yazirina yasa na dan tsorata na tsaya ananTake saukowa kasa daga saman matattakalar benen.Mujahid na take mata baya.Nanfa Sarila ta kurawa Yazirina idanu suka fara kallon kallo kowacce na nazarin yar uwarta.Sarila na tayin murmushin mugunta a lokacin ne gaba dayan mutanen dake gidan suka fara sulalewa suna ficewa daga cikin gidan.Saidai Sarila ta gama nazarin Yazirina sannan hankalinta yakai izuwa kan Mujahid,tana hada idanu dashi sai taji zuciyarta ta buga da karfi,al'amarin dayai matukar bata mamaki kenan domin wannan ne karo na farko data taba jin hakan ya faru a tsakaninta da wani 'da namiji.Kawai sai tayi sauri ta kau da kanta ga barin kallonsa ta dubi Yazirina tace ina taswirar dake hannunki guda biyu?Ina mai shawartarki daki gaggauta miko mini su in ba haka ba kuwa zaki iya rasa rayuwarki gaba daya,idan kuma kikayi yunkurin guduwa tofa ba zaki iya bace mini ba kuma zaki janyo na baje wannan birnin gaba daya na kawar da duk wani abu dake da rai a cikinsa.Koda jin wannan batu sai Yazirina tayi murmushi tace yake yar uwata kiyi sani cewa ni a rayuwata bansan wani abu waishi TSORO ba don haka yana da kyau ki gane cewa ko kadan bana shakkar ki duk da nasan cewa kin fini karfin damtse dana sihirin tsafi.Kema kin san cewa ba zata yiyu ba na dauki wadannan taswirori da hannuna na danka miki ba face na jarraba sa'a ta ta samun taswirar dake jikinki.Don haka yanzu ga taswirori guda biyu a cikin jakar guzurina daya taswirar kuma na sani cewa mahaifina ya zanata a kan gadon bayanki tun kina da shekara shida a duniya,ni dake mu gwabza mu gani wanda zai sami nasarar hada taswirorin nan guda biyu.Koda gama fadin hakan sai Yazirina ta gyara tsayuwarta kuma ta bude hannunta mai rike da takobi kuma ta kara daure jakar guzurinta tamau a jikinta.Koda ganin haka sai Sarila tayi murmushi ta zare addunanta guda biyu kuma ta murtuke fuska,kamar hadin baki duk su biyun sai suka rugo da gudu suka kacame da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama da juriya da bajinta na gaban kwatance da matukar al'ajabi domin suna yin wannan yaki ne da wani irin gagarumin zafin nama tamkar jikinsu bana JINI DA TSOKA bane,nan da nan suka tashi hankalin falon gaba daya sai gashi Mujahid ya dimauce yana ta guje guje da boye boye don kada su lahantashi.A duk lokacin da Sarila ta kawo wa Yazirina sara da suka ta goce to fa duk abinda ta samu saita raba shi gida biyu ko kuma ta huda shi.Nan da nan ta ragargaza kujeru da teburan falon ta farfasa dukkanin tulunan giya da tambuloli.Ashe tun ma kafin a fara wannan gumurzun kofar wannan gidan ya cika ya batse da mutane mafi akasarin mutanen da suka zo wannan wuri mutanen gari ne wadanda suka firgita sakamakon jin tsawa da karar fadowar Sarila daga sararin samaniya,sunzo ne domin su ga newa idanunsu amma akwai bakin bokaye da wakilan manyan sarakai wadanda suka zo wajen a cikin badda kama kawai jira suke suga wadda zata yi nasara a wannan gumurzu da ake tsakanin YAZIRINA da SARILA suk afka mata su rabata da wadannan taswirorin guda uku.Rashin sani yafi dare duhu inda jama'ar da suka taru a wannan wuri suna leken gumurzun da akeyi sun san abinda zai biyo baya da basu kawo kansu wannan wuri ba.Koda aka shafe kusan rabin sa'a na wannan bakin artabun ba tare da dayansu ya sami nasarar koda lakutar jikin daya ba sai Jaruma Sarila ta fusata ainun ta fara amfani da karfin sihirin tsafi tayi nuni da hannunta izuwa kan Yazirna take wata irin iska mai karfi ta taso ta daga Yazirina sama ta makata a jikin garu.Take kan Yazirina ya fashe jini ya zubo ta fado kasa a galabaice,Sarila ta sake daga hannunta da nufin ta daga Yazirina sama a karo na biyu,koda ganin hakan zata faru sai Mujahid ya fito daga inda yake boye ya dako tsalle ya dira a gaban Sarila ya dubeta ya daka mata tsawa yace,kada ki kuskura ki kashe ta domin ta fiki amfani a wajen al'umma.Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama Sarila har dariya ta subuce mata ta dubi Mujahid tace kai kuwa meye takamarka har da zaka sha gabana ka daka mini tsawa haka?Shin baka ga yadda kowa ke tsorona bane ko kuwa ka gaji da rayuwar duniya ne kanaso ka tafi BARZAHU?Mujahid ya gyada kai yace yake Sarila kiyi sani cewa ni matsoraci ne lamba daya,amma a duk sa'adda naga za'ayi zalunci sai naji zuciyata ta kekashe ga barin tsoron kowane irin mahaluki walau mutum ko aljan komai girmansa da karfinsa.Ke kina so ki mallaki wannan dukiya ne domin kiyi mulkin zalunci a doron kasa ki wahalar da talakawa kuma kiyi abinda ranki yake so,ni kuwa burina shine na yi yaki da zalunci na shimfida adalci tunda har ina kan tafarkin gaskiya nayi imani cewa zan iya taimakon duk mai irin halina da zuciyata.Koda jin wannan batu sai Sarila ta fusata ainun zuciyarta ta kama tafarfsa kamar zata kone kawai sai ta daga Addarta sama da nufin ta sare kan Mujahid amma sai ta kasa,kawai sai ta cakumoshi da hannu daya tayi wurgi dashi izuwa can bayanta tamkar tayi cilli da sillan kara.Mujahid yaje ya gwaru da bango ya fadi kasa,kafin Sarila ta kaiwa Yazirina wani harin tuni Yazirina ta daka tsalle sama ta doki kirjin Sarila da dukkan karfinta da kafafunta biyu.Sarila tayi baya taga-taga kamar zata fadi kasa amma saita tsaya kyam,al'amarin dayai matukar razana Yazirina kenan domin komai girman kato idan tayi masa irin wannan duka sai yayi sama ya fado kasa ya baje amma gashi Sarila ta shanye shi,ita kuwa Sarila mamakin daya kamata shine Yazirina ce kadai ta taba yi mata dukan da yasa ta motsa har taji tana neman faduwa kasa.Cikin tsananin fishi Sarila ta dako tsalle sama ™Abubakar Haleefah Physicist™ daga inda take ta kawowa Yazirina wawan naushi a kirji,cikin bakin zafin nama Yazirina ta kaucewa naushin ta murgina a kasa can baya.Take hannun Sarila ya naushi kasan falon ai kuwa sai wajen ya burma hannunta ya lume a cikin kasa kawai sai akaga ta zaro hannun nata ko kurjewa batayi ba,ta sake rugowa izuwa kan Yazirina taci gaba dakai mata mugayen naushi da bugu da hannu da kafa,in badon Yazirina tana da bakin zafin nama ba kuma na kaucewa hare haren nata gami da karewa da takobin hannunta da tuni Sarila ta burma sassan jikinta.A wannan lokaci ne hankalin Yazirina ya DUGUNZUMA ainun domin a sannan ta tabbatar da cewa KARFIN DAMTSEN Sarila ya ninka nata sau goma,sakamakon naushin ginin falon da Sarila keyi sai gidan gaba daya ya kama rugujewa da kyar ma Mujahid ya fice daga cikin gidan sai gashi gidan gaba daya ya baje amma Sarila da Yazirina basu daina gumurzu ba.Nanfa bala'i kuma ya fara shafar yan kallo domin sauran gidajen dake wajen ma sai suka kama rushewa suna fadowa kan jama'a suna hallaka.Nanfa birnin gaba daya ya hargitse aka kama guje guje da iface iface saida ya zamana cewa kowa ya cika wandonsa da iska babu wanda ya rage a wajen face manyan bokaye da tsirarun dakaru wakilan manyan sarakunan hudu na duniya sai kuma Mujahid.Ana cikin wannan BAKIN ARTABU ne Sarila ta shammaci Yazirina ta sareta da takobi akan kirjinta daga sama.Take gurin ya dare jini yayi tsartuwa Yazirina ta kurma uban ihu sakamakon tsananin zafin dataji a lokacin data tayi tsalle sama da baya ta fado kan rusasshen gini a cikin matukat galabaita.Kawai sai Sarila ta dako tsalle sama daga inda take ta dira a gaban Yazirina ta na mai raba kafafunta akanta ta dubeta cikin murmushin mugunta a lokacin da jini ya cigaba da yoyo akan kirjin Yazirina kuma tana gani dishi dishi.Sarila ta bushe da dariyar murna bisa ganin nasarar data samu sannan ta dubeta tace yanzu zan karasa kashe ki na dauke wannan jakar guzuri taki tunda taswirorin guda biyu na ciki.Koda gama fadin hakan sai Sarila ta daga Addarta sama da nufin ta lumawa Yazirina a ciki kawai sai akaga Mujahid yayi wuf ya janye Yazirina ya goyata a bayansa ya falfala da azababben gudu izuwa cikin gari aikuwa sai suka kasa tsere shida Sarila sannan ragowar matsafa da wakilan manyan sarakuna suka rufa musu baya.Bisa mamaki sai Sarila taga Mujahid yana yin wani irin gudu na ban al'ajabi wanda yafi gaban tunaninta domin tazarar daya bata ba ta wasa bace duk da cewa ta sami horon gudu mai tsananin amma duk sai ya zamo na banza.Koda taga Mujahid na neman bacewa sai ta kara karfin gudun nata da karfin sihirin tsafi amma duk da haka sai ta kasa cimma Mujahid,al'amarin dayai matukar daure mata kai kenan kuma yayi matukar bata mamaki.Nan taje ta fara wasu wasi a cikin ranta tace anya kuwa wannan saurayi daya taimaki Yazirina ba shi bane bakon jarumin da aka bani labari cewa zai hanani samun nasara akan Yazirina?Me yasa a farkon haduwata dashi naji zuciyata ta buga da karfi?Shin na kamu da SON sa ne ko kuwa tausayinsa naji shi yasa na kasa kashe shi?Akan wane dalili zanji tausayinsa alhalin ban taba jin tausayin wani bil'adama ba?Haka Sarila taci gaba da wannan tunani tana cigaba da falfala masifaffen gudun ta na tsafi,duk inda ta gifta sai kaga kamar tauraruwa mai wutsiya ce ta wuce amma duk da haka a can nesa take hango Mujahid goye da Yazirina a bayansa wacce tuni ta dade da suma.Haka dai aka cigaba da wannan tseren gudun har tsawon sa'a daya da rabi har ya zamana cewa an fice daga cikin ainihin birnini Yamein an nausa cikin daji.Koda Mijahid ya shiga cikin wata sarkakiya mai tsawon gaske gami da hudu sai ya bacewa Sarila ta nemeshi sama da kasa ta rasa,ba shiri ta tsaya cak ta kama waige waige da dube dube a daidai wannan lokacin ne bokaye da wakilan sarakunan suka iso duhuwar da suka ga ta shiga sai kowannensu yayi turjiya ya tsaya yana haki gami da tsoron shiga cikin sarkakiya.Duk da cewa Sarila tayi nisa a cikin sarkakiyar kuma tazarar dake tsakaninta da wadannan bokaye da wakilan sarakunan su goma sha hudu takai taku dari da ashirin tana iya jiyo sautin hakinsu a cikin dodon kunnenta saboda karfin sihirinta na tsafi.Nanfa Hankalinta ya rabu biyu ta bazama neman inda su Mujahid suka buya kuma tana tunanin ta koma da baya inda wadannan bokaye suke ta hallakasu tunda suma abokan gabarta ne suna farautar abinda take nema.Har daya daga cikin bokayen da yunkura zai kunna kai izuwa cikin wannan sarkakiya sai wani daga cikin ragowar yan uwan nasa uku yace kada mu kuskura mubi su Sarila cikin wannan sarkakiya domin babu mamaki kafin mu isa inda suke tuni Sarila ta kashe Yazirina da abokin tafiyarta,kunga kenan tana ganinmu zata gama damu tunda ta san cewa abindake hannunta muke bukata,kuzo mu watse daga nan domin mu tsira da rayuwakanmu in yaso muyi bincike a cikin hallarar tsafinmu muga abinda ya faru tsakanin Sarila da Yazirina sannan musan hanyar da zamu bi mu sace taswirori uku daga hannun Sarila.Koda jin wannan shawara sai sauran bokayen da wakilan sarakunan hudu suka amince nan take kuwa sukayi amfani da karfin tsafi suka bace bat daga wajen gaba dayansu.Lokacin da Sarila ta dubi gaba da yamma,kudu da arewa a cikin wannan duhuwa bata ga su Mujahid ba kuma bata jiyo sautin numfashinsu ba sai ta fara neman sawun Mujahid amma sai taga wayam ko akamr sawun bil'dama babu a wajen da nesa dashi.Al'amarin dayai matukar kara rikirkita mata kwakwalwa kenan ta tambayi kanta tace wai shin wannan bakon saurayi wane irin shu'umi ne shi haka,tabbas na fishi karfin sihirin tsafi da karfin damtse da iya yaki amma yaya ™Abubakar Haleefah Physicist™ akayi ya tsere mini da karfin gudu kuma ya bace mini da gani sai kace aljani,Koda gama fadin hakan keda wuya sai Sarila tacigaba da falfala gudun tsiya tana neman su Mujahid har ya zamana cewa ta kusan kure karshen

Chapter 3 of 14