Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
fara taruwa a filin gasar jarumtaka domin su morewa idanunsu kallon yadda wannan karshen na kambun jarumta zai kasance tsakanin gimbiya suzaina da jarumi darusi kafin cikar sa a daya fili ya cika makil fiye da ko yaushe lokacin babu masakar tsinke tunda aka fara wannan gasa bisa tarihi ba a taba samun cikowa irin ta wannan rana ba domin har a kan katangu da benayen gidajen jama ar gari mutanen baja baja wani zai samu iya raba ba komai ne ya janyo hakan ba face za a sake fafata gumurzu a tsakanin gimbiya suzaina da jarumi darusi wato gawurtaccen sadauki daya kawo addinin musulunci a kasar bisa wannan daliline jama a sukayi ta tururuwa daga cikin birane da kauyuka suna shigowa cikin babban birnin Al amin Ahmed Guyson ke magana A wannan rana dai gimbiya suzaina da mahaifinta da wuri suka zo fada ba tare da bata wani lokaci ba aka buga gangan fara gasa nan take su jarumi darusi suka shigo cikin tsakiyar filin gasar suka tsaya suka fuskanci yan kallo koda suzaina ta hada ido da sarila wacce ke zaune a cikin yan kallo tare da yazirina da kuma mujahid sai suzaina taga sarila ta dago mata hannu tanayi mata jinjina da murmushi Al amarin da yayi matukar daurewa suzaina kai kenan ta kamu da tsananin mamaki amma koda ta tuno da irin furucin da sarila ta yi gareta bisa daukar fansar abinda tayi mata bisa tsautsayi cewar saita tozartata a gaban jama a sai nan take taji ta tsani sarila ainun don haka sai ta murtuke fuskarta ga sarila ta daka mata harara kuma ta kauda kai ga barin kallonta a dai dai wannan lokacine su sarila suka ga wani bakin attajiri ya shigo cikin filin gasar wadansu bakin dakaru na musamman na take masa baya fuskar attajirin cike da gemu da kasumba kuma idonsa guda a nane yake da wani kyalle baki alamar cewa idonsa guda ne yake da gani gaba daya jikinsa a lullube yake da wata doguwar alkyabba mai daraja ko hannayensa da kafafunsa ba a gani abin ka da mai hannu da shuni nan da nan dakarun suka rinka buda masa hanya yana wucewa har saida ya kusa zuwa inda karagar sarki take sannan dakarun sarki suka tsayar dashi aka tuhumeshi domin a san ko waye shi dakuma abinda ya kawoshi dajin haka sai attajirin yace shi bafatake ne daga can wani birni da ake kira Damar kusa da kasar misra kuma yana fatauci kayan kyale kyale donhaka yazone domin tallata hajarsa ga sarki nan take akaje aka sanar da sarki wannan jawabi lokacin da sarki yaji wannan abinda take tafe da wannan bakon attajiri sai sarki yace aje a gaya masa cewa ba a nan ake kawo tallan haja ba sai a can fada nan filin gasa ne yanzu ya zauna yayi kallon gasar jarumta in yaso daga baya sarki zai aiko azo dashi fada su gani bayan sarki yayi wannan jawabi sai ya dubi hadimin dayayiwa bayanin yace ka gayawa sarkin yaki ya zuba ido akan wannan bakon attajirin saoda zata iya yiwuwa cewa dan leken asirine akan bakinmu ko mu kanmu hadimin ya gyada kai yace angama ya shugabana shi kuwa jarumi darusi yana tsaye a cikin filin gasar suna masu fuskantar juna shida gimbiya suzaina sai ya hango shigowar bakon attajiri koda darusi ya hada idanu da attajirin sai yaji zuciyarsa ta dan buga da karfi nan take yaji bai aminta dashi ba duk da cewar fuskarsa cike take da gashikuma idonsa guda a like yake sannan akwai tazara mai dan yawa a tsakaninsu da darusi yaga kaamar ya taba ganin fuskar wannan attajirin amma saiya kasa tuno a inda ya taba haduwa dashi Guyson ko shagala boy. Nan take dai alkalin gasa ya daga hannunsa sama kuma ya sauke faruwar hakan keda wuya aka buga gangar fara gasa aikuwa sai jama a suka kaure da shewa gami da tafi da jinjina kowa na wasa gwaninsa duk da cewa jarumi darusi bai kasance dan gari ba amma sai ga . Gashi masu goyon bayansa na neman yin kunnen doki dana gimbiya suzaina Al amin Ahmed Guyson Lokaci guda darusi da suzaina suka zare makamansu ita suzaina addunanta ne guda biyu shikuma darusi takobice garkuwa kawai sai suka rugo da gudu izuwa kan junansu suka ruguntsume da masifaffen yaki ya zamana cewa suna kaiwa junansu sara da suka cikin zafin nama juriya da jarumtaka mai matukar ban al ajabi nan fa filin gasar ya dada rudewa da shewar jama a sai da suzaina da darusi suka shafe sa a daya da rabi suna mugun bakin artabu banda karar haduwar makamansu da fitar nunfashin bakinsu da kuma karar dake tashi a cikin filin babu wani sauti dake tashi saboda gaba daya yan kallon sun tattara hankalinsu a kan jaruman biyu ko motsin kirki babu mai yi A na cikin wannan gumurzu ne yazirina ta dubi sarila tace hakika suzaina ta cika jarumar gaske tunda koni dake ba zamu iya shafe wannan lokaci mai tsawo ba haka muna fafatawa da jarumi darusi face ya gama damu sa adda sarila taji wannan batu sai tayi murmushi sannan tace gaskiya ne suzaina jarumace ta kwatance sai dai duk wannan jarumtakar tata ta banza ce domin nan da cikar wani dan lokaci zata zama gawa a nan cikin filin gasa kuma a yau din nan zan fara samun yardar jarumi darusi ki sani cewa a gobe sai dai a tafi da gawar suzaina izuwa kogon Taskar Ajali koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke yazirina ta dubi sarila cikin kaduwa da dumbin mamaki tace me nene zai kashe suzaina kuma yaya mujahid zai baki amincinsa? Da jin wannan tambaya sai sarila ta bushe da dariya tace ki zuba mini idanu kawai zakiga amsar wadannan tambayoyi naki daga nan inda kike zaune a dai dai wannan lokaci ne suzaina da jarumi darusi suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki saboda gajiya domin karfi yazo daya a iya yaki ai kuwa sai fadar ta sake kaurewa da shewa a nayi musu jinjina kamar hadin baki sai duk su biyun suka yarda makamansu suka gyara tsayuwarsu sannan suka rugo da gudu suka ruguntsume da sabon masifaffen fada suna masu kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa nan fa jama a suka ga wani abin Al ajabi nata faruwa da zarar darusi ya sami nasarar naushin suzaina sai akaga nan take itama ta rama da irin naushin da yayi mata duk irin gwanintar da dayansu yayi sai aga shima dayan yayi irin ta sak nan fa yan kallo suka rinka cewa wannan fada shiri ne dama jaruman biyu sun tsara yadda zasuyi gumurzun to amma abinda ya rusawa yan kallo wannan tunani shine dukan gaske jaruman suke yiwa juna domin har sun hadawa junansu jini da majina tsananin juriya da bakin naci ne yasa daya daga cikin su ya kasa kai abokin gwaminsa kasa nan fa gumurzun yaki ci yaki cinyewa ya zamana cewa an sake shafe wata sa a daya da kusan rabi amma abinda karshen gumurzun ke nuni shine ragas shi kansa jarumi darusi yayi matukar mamakin yadda akayi wannan karon karfinsa yazo dai dai da na suzaina duk da wata dabara da yayi kuma yayi amfani da dukkan karfin damtsensa amma a banza su kansu yan kallo saida suka kosa suga karshen wannan masifaffen gumurzu sai da takai cewa suzaina da darusi sun fara layi tamkar wadanda suka sha giya suka bugu saboda tsananin gajiya da galabaita bisa ka idar wannan gasa da zarar sa a uku ta cika ba a sami gwarzon ba za a tsayar da wasan a sauya masa tsari koda sarki da mahaifiyar suzaina sukaga an shiga wannan hali sai hankalinsu ya dugunzuma ainun saboda tsoro kada suzaina da darusi su rasa lafiyarsu kwatsam ba zato ba tsammani sai darusi yaga wani uban gudan jini bakin kirin ya furzo waje daga cikin bakin suzaina nan take suzaina ta durkushe kasa bisa guiwowinta cikin matukar galabaita cikin firgici da tsananin mamaki da midauta darusi ya tallafo suzaina a kirjinsa ya kurma uban ihu yana mai kwalawa likitoci kira kafin ayi wani yunkuri sai akaga wata doguwar kibiya ta taho da gudu zata soke jarumi darusi amma sai sarila ta dako tsalle sama daga cikin yan kallo ta sha gaban darusi take kibiyar ta soki sarila a gefen kirjinta ta hudo ta gadon bayanta sarila ta fado kasa tim !! Ta baje a kasa sumammiya nan fa Al amin Guyson ya rude sbd tun farkon ganinsa da ita ya kamu da sonta ehm. Darusi ya sake dimaucewa ya rasa inda zai tsayar da hankalinsa a tsakanin masoyiyarsa suzaina da kuma sarila wacce ta ceci rayuwarsa yanzu take tabbas in ba don ta tari wannan kibiyar ba da goshinsa kibiyar zata shige shikuwa sarki da dakarunsa tuni sun zare takubba sun daga garkuwoyi suna yiwa filin gasar kawanya a lokacin da filin gasar ya motsi jama a suka kama guje guje da iface iface cikin firgici nan da nan aka dauke suzaina da sarila gudu a ka shige dasu izuwa cikin gidan sarautar likitoci suka dukufa a kansu sarki, darusi da sauran dakarun birnin kuwa sai suka shiga bincike don gano makiyin da suka harbo wannan kibiya kuma aka tsananta tsaro a cikin birnin ya zamana cewa an kulle gaba dayan kofofin gari ba shige ba fice aka kafa dokar kai kawo lokacin da su sarki suka shafe kusan rabin sa'a suna ta kai kawo a cikin birnin suna bincike baki da mutanan gari amma basu gano wani mai laifi ba. Sai hankalin sarki ya dugunzuma ainun ya dubi darusi cikin alamun tsananin damuwa yace yakai jarumin jarumai ka yi sani cewa hankalina bai taba tashi ba irin yanzu ga gimbiya can a kwance rai a hannun Allah kuma ga sarila can ma a kwance magashiyan wacce ta ceto rayuwarka da farko nayi zaton cewar wannan lugudan duka da kayiwa suzaina ne ya sata yin wannan aman bakin jini amma daga bisani likitoci sunyi bincike sun gano cewar guba aka bata ta sha kuma gubar tana da tsananin karfin da take kashe mutum a cikin dakiku kadan nayi mamakin data kawo har i yanzu wanene ya bata guba tasha kuma waye yake kokarin kashe ka wannan shine abinda ya kamata mu yi kokarin ganowa bi sa wannan daliline yanzu ni da kaina tare da dakaru zamu rinka shiga gida gida muna bincike duk inda mukaga irin gubar da aka baiwa gimbiya tasha ko kuma irin kibiyar da aka harbo maka mun san a nan ne makiyan suke kai yanzu ka koma can gidan sarauta kaga halinda gimbiya take ciki kuma ka hada karfi da yaranka da dakarun gidan sarautar ku kafara tsananta tsaro sosai kada a bar kowa ya shiga cikin dakin gimbiya da sarila hatta abokiyar tafiyarku yazirina ban yarda da ita ba kada a barta ta shiga in da suke ko wama yanzu abin zargi ne koda jin haka sai darusi ya dubi sarki cikin alamun damuwa yace ya shugabana idan hakane a nima abin zargi ne ya kamata a bincikeni sarki ya gyada kai yace idan har za a bincikeka to dole ne nima a bincikeni ina mai tabbatar maka da cewa jama ar garin nan ma sun yarda dakai fiye da ni saboda kaine ka kawo musu addinin gaskiya....Sarki ya gyada kai yace idan har za a bincikeka to dole nima a bincikeni ina mai tabbatar maka da cewar jama ar garinnan sun yarda dakai fiye da ni saboda kaine kazo da addinin gaskiya. Addinin da shine ya saita rayuwarsu ya fitar dasu daga cikin tsananin duhu ya sanya su a cikin haske mabaiyani' koda gama fadin haka sai sarki ya dubi sarkin yakinsa yace maza muje mu fara aikin binciken nan nan take sarki da sarkin yaki tare da dakaru kimanin su dari uku suka nausa izuwa cikin garin shi kuwa jarumi darusi tare da dakarunsa sai suka ruga izuwa gidan sarautar A cikin wani babban daki aka kwantar da suzaina da sarila likitoci suka dukufa kansu saida likitocin suka shafe sama da sa a hudu suna kokarin kashe dafin gubar dake cikin suzaina amma abu ya gagara itama sarila an zare kibiyar da ta soke ta a kirji amma kuma an kasa gano irin dafin dake jikin kibiyar bare a bata maganin da ya dace da gubar don haka sai aka rinka baiwa kowacce magunguna iri iri domin a ceto rayuwarsu da kyar a ka dace akan sarila ta farfado ta dawo cikin hayyacinta amma saboda raunin da kibiyar tayi mata babba ne ko mikewa zaune kasawa tayi All amarin suzaina kuwa numfashinta a sarke yake kuma kadan kadan yake fita koda ganin haka sai guiwoyin likitocin sukayi sanyi kuma zuciyoyinsu ya karaya suka saddakar da cewa lallai suzaina ba zata tsira da rayuwarta ba lokacin da mahaifiyar suzaina ta ga likitocin sun kasa ceto rayuwar yanta sai ta koma gefe daya ta kama jan casbaha tana zubar da hawaye kawai A cikin zuciyar ta cewa take ya Allah ya ubangijin musulunci ka sani cewa wannan yarinya ita kadai gareni idan har ba wa adin nata ya cika ba toka tashi kafadunta Sarila na daga kwance saita dubi suzaina wacce take kan gangarar mutuwasaita juyo da kanta da kyar ta kurawa mahaifiyar ta idanu tana mai muna mata alamun cewa tana son ta fada mata wata magana koda ganin haka sai mahaifiyar suzaina ta murtuke fuskarta takau da kanta ga barin kallonta Ba komai ne yasa mahaifiyar suzaina tayi haka ba face suzaina ta bata labarin duk abinda ya faru tsakaninsu har da furucin da tayi na cewar sai ta yiwa suzaina tsirara a bainar jama a duk da cewa taga lokacin da sarila ta sallama rayuwarta don ceto ta jarumi darusi sai da taji ta tsaneta A na cikin wannan haline jarumi darusi ya shigo cikin dakin a guje kuma a dimauce ko da ya dubi inda sarila ke kwance yaga har ta farfado kuma ta kura masa idanu tana murmushi sai yayi murna ya yunkura zaije gareta sai kuma ya hangp inda suzaina take numfashinta a sama sai ya juya ya ruga gareta amma sai sarila tayi caraf ta ruko hannunsa ta dubeshi lokacin da hawaye ya zubo mata tace kayi hakuri yakai jarumin jarumai domin likitoci sun kasa gano irin gubar dake jikin masoyiyarka ina ba don ma tana da taurin raiba da tuni ta sheka barzahu na sani cewa kayi mamaki bisa ganin na sallama rayuwata domin ceto taka to ka sani cewa nadama ce tazo mini na gane kuraina kuma ina rokonka daka yafe miki ka karbe ni a matsayin masoyiyarka domin a halin yanzu na kamu da tsananin sonka da kaunarka Topa Guyson dai bai yarda da wannan sonba kufa? Idan har ka karbi soyayyata lallai zan karbi addininka kuma na tayaka jaddada shi a ko ina cikin duniya koda sarila tazo nan a zancenta sai jarumi darusi yayi wuf ya fisge hannunsa daga cikin nata. Ya ruga izuwa kan suzaina da zuwa yaga idanunta a wurkile kuma numfashinta na kara sarkewa sai hankalinsa ya dugunzuma kawai sai ya kore dukkan likitocin dake kanta suka koma gefe daya sannan ya debo ruwa a kofi ya karanta wadansu addu'o'i na musamman ya durawa suzaina a baki duk wannan abu da jarumi darusi keyi sari na kallonsa tana yin murmushin mugunta saboda ta tabbatar da cewa dole ne suzaina ta mutu bata isa ta tsallake sharrin gubar dake jikin ta ba a she tun a daren jiya bayan suzaina ta baro turakar sarki ta koma tata kafin ta kwanta saida wata kuyangarta ta kawo mata ruwan inibi tasha a cikin wannan ruwan inibi ne ka sawa suzaina wani mugun dafi mai kisa farat daya albarkacin addu ar da suzaina tay ne karfin tasha ruwan inibin yasa dafin ya tsaya a iya cikinta bai zagaya cikin jinin taba Ba wani bane ya zuba wannan guba a cikin ruwan inibi ba face SARILA da kanta kuma tayi amfani da Karfin sihirinta na tsafi wajan samo gubar da kuma shiga har cikin turakar suzaina a sirrance ba tare da kowa ya ganta ba. Ita kuyangar data kawo wa suzaina ruwan inibin bata san cewa an zuba guba a cikinsa ba lokacin da mahaifiyar suzaina taga jarumi darusi na yin wannan kokari na ceto rayuwar gimbiya sai ta kamu da farin ciki ta taso da sauri daga inda take zaune tazo kanta ta kura mata idanu tana mai ci gaba da addu'a kwatsam ba zato ba tsammani sai akaji tari ya sarke suzaina daga nan kuma sai ta mike zaune da kanta ta kama kwarara amai wani irin amai ne na tsurar jini wanda ya kasance bakin kirin kuma mai kaurin gaske babu kyan gani sai da suzaina ta cika wani akushi da wannan aman jinin Sannan idanunta suka dawo dai dai daga wurkulewar da sukayi kuma ta dawo cikin haiyacinta koda ganin haka sai farin ciki ya kama darusi da mahaifiyarta basu san sa adda suka rungume ta ba a tare ita kuwa sarila bakin cikine ya dameta taji zuciyarta na tafarfata kamar zata kone saboda hakanta bai cinmma ruwa ba sotayi lallai ayau ta kashe suzaina domin ya kasance za a tafi kogon taskar ajali babu ita kuma taci gaba da yaudarar jarumi darusi a matsayin ta kamu da sonshi har su isa can taskar ajali ta shammaceshi ta kasheshi Al amarin sarki kuwa lokacin da suka fara shiga cikin gida tare da sarkin yakinsa da dakarunsa suna bincike sai da suka kusan karade birnin har izuwa tsakiyar dare ba tare da sun kama wani mai laifi ba wanda ake zargi da kaiwa jarumi darusi hari ko kuma wanda ya sawa suzaina guba Lokacin dasu sarki suka iso kofar wani gida ne dake can bayan gari sarki yaji ya gaji likis har ya juya da nufin ya daina binciken a koma gida sai ya fara ya juya ya dubi kofar gidan sannan ya dubi sarkin yaki yace wai shin wanene mai wannan gidan ne? Sarkin yaki yace Ai gidan sarkin kasuwa ne wanda yake baiwa fatake haya koda jin haka sai sarki yace a buga musu kofa su bude mu shiga Nan take kuwa aka cika umarnin bugun farko aka bude kofar saiga wannan bakon Attajiri mai ido daya ya zube har kas ya kwashe gaisuwa cikin girmamawa sarki ya kama kafadunsa ya tashe shi tsaye sannan ya dubeshi yace yakai wannan babban attajiri kayi hakuri bisa tashinka da mukayi daga barci muna kan aikin mune na bincike domin gano wadanda suka kaiwa jarumi darusi hari dasu a filin gasa da kuma wadanda suka cutar da yata gimbiya suzaina da guba koda jin wannan batu sai attajirin ya ce wannan dakyau ya shugabana a sa dakaru su caje ko ina a cikin gidan nan kuma su duba dukkan kaya na ina murna da haka ba tare da bata wani lokaci ba aka shige cikin gidan aka kama bincike babu inda ba aduba ba a cikin gidan hattama cikin rijiyar saida aka yi nutso izuwa can karkashinta aka tabbatar da cewa babu komai a cikinta akwatunan da hajojin attajirin ke cike kuwa kimanin guda dari uku da ashirin saida aka fito da gaba dayan kayan cikinsu akayi musu filla filla ama ba aga komai ba face kayankyale kyale masu daraja irin na sarakai nan take sarki yayi sha awar kayan har yayi cinikinsu yace gobe da safe attajiri yazo fada ya karfi kudinsa har sarki ya yiwa attajiri sallama ya juya zasu tafi sai attajirin yayi gyarar murya yace ya shugabana ina da shawara a kan yadda za a gano masu laifi ka sani cewa sau tari makashinka na jikinka saboda haka ina mai shawartarka dakasa a caje dakin koda da kowa a cikin duk mutanen dake daf dakai komai gaskiya da amanarsu kuwa ta wannan hanyace kadai za a iya gano wadanda sukayi wannan sa adda attajiri yazo nan a zancensa sai sarki ya numfasa yace tabbas kazo mini da shawara mai kyau kuma lallai zanyi aiki da ita. Al amin Ahmed guysonke magana. Lokacin da sarki ya dawo fada ya tske cewa suzaina da sarila sun tsira da rayukansu har kowacce ta koma turakarta sai farin ciki ya kamashi ainun musamman da yaji cewar darusi ne ya baiwa suzaina ruwa wanda ya tofa addu a a cikinsa tasha ta warke da yake dare ya raba sosai sai sarki ya tafi izuwa turakarsa inda ya iske matarsa mahaifiyar suzaina a zaune cikin farin ciki tana jiransa da shigowarsa saita mike ta taryeshi ta cire masa rawaninsa da alkyabbarsa da kuma takalminsa sannan ta jashi izuwa kan gado suka kwanta tana mai dora kanta akan kirjinsa tace yakai Abul suzaina hakika yaunaga ikon ubangijin musulunci kuma naga wani abu dayayi matukar daure mini kai koda jin wannan batu sai sarki ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace ni kaina nayi Al'ajabi matuka to amma wai shin wani abune ya daura miki kai? Mahaifiyar suzaina ta ce nayi matukar mamaki bisa ganin yadda ta sallama rayuwarta domin kare ta jarumi darusi da cewar alhalin yanzu ta kamu da tsananin sonsa har ma tana cewa itace zata maye gurbin suzaina idan ta mutu koda jin wannan batu sai hankalin sarki ya tashi ainun ya mike zaune zumbur ya yunkura zai sauka daga kan gadon domin ya sanya kayansa ya fice amma sai mahaifiyar suzaina tayi wuf ta riko hannunsa tace lafiya? Me zakaje kayi yanzu? Sarki ya dubi matarsa a cikin alamun firgici yace jikina da zuciyata sun bani cewa wannan yarinyar sarila itace take da hannu a harin da aka kawowa jarumi darusi da kuma gubar da aka baiwa gimbiya ki tsaya kiyi nazari a kwakwalwarki ki tuna cewa babu wanda ya tsani gimbiya sama da sarila tun daga ranar da ta kayar da ita a gasar jarumtaka ki tuno da duk irin furucin da tayiwa suzaina akan rabata da darusi da son tozarta ta a bainar jama a ki tuna da yadda take burin zuwa kogon TASKAR AJALI bakya tunanin cewa ta sallama rayuwarta ne don ceto tasa saboda nan gaba zai iya taimakonta wajan isa kogon Taskar Ajali? Lokacin da sarki yazo nan a zancensa sai matar tasa tayi shiri tana tunani sannan tace to amma tayaya sarila zata iya zubawa gimbiya guba a cikin abincinta ko abin shanta alhalin bata isa taje turakarta ba? Guyson nake. Sarki ya gyada kai yace ni ma nayi tunani a kan hakan amma dai ai maso abinka ya fika dabara a gobe ne likitoci zasu kammala bincike a kan duk abincin da abin shan da gimbiya tayi amfani dasu a ranar mahaifiyar suzaina ta sake ajiyar numfashi tace to yaya batun wannan kibiyar da aka harbo domin a kashe jarumi darusi? Al amin Guyson nake shinka gano wanda ya harbota ne sarki ya girgiza kai yace bamu gano ba amma dai har yanzu muna aiki a kan hakan mahaifiyar suzaina tace ka tsananta wannan bincikea cikin bakin da suka shigo garin nan domin dan gari bashi da kwarin guiwar harbar darusi sai dai kuma ance da dan gari akanci gari koda jin wannan batu sai sarki ya koma ya kwanta yana mai cewa na yar da da shawararki zamu ci gaba da bincike domin inaji a raina cewar mai laifin nan a cikin garin nan yayi basaja wannan shine abinda ya faru a gidan sarauta Al 'amarin wannan attajiri wanda ya siyarwa da sarki hajojinsa kuwa bisa cewar gobe da safe zaizo fada ya karbi kudinsa sai bayan sarki da dakarunsa sun dan jima da tafiya sanan ya tara gaba dayan yaransa ya bushe da dariyar farin ciki yace tabbas shirina yana tafiya dai dai kamar yadda na tsara koda gama fadin hakan saiya umarci daga daga cikin yaran nasa ya dauke alkyabbar dake jikinsa sai ga shi ashe hannu daya gareshi nan take kuma yasa lafiyayyen hannun nasa ya daye gemu da sajen dake kan fuskarsa kuma ya bude rufaffen idonsa A she idon nasa lafiyayye ne ba wani bane ba wannan attajiri face SARKI DAMNASH wanda ya fafata kazamin yaki da JARUMI DARUSI har darusi ya sare masa hannu guda bayan sarki Damnash ya gama baiyana fuskarsa da jikinsa sai ya sake bushewa da dariyar mugunta lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dubi dukkanin yaran nasa yace kun sani cewa na batar da kamannin nane nazo nan birnin domin na dauki fansa a kan jarumi darusi sannan kuma na kashe sarila da yazirina na dauke taswirorin dake hannunsu na isa can kogon TASKAR AJALI na kwaso dukiyar dake ciki wacce da zarar na mallaketa duniya kaf data dawo karkashin ikona dani daku duk mun huta da wahalar duniya har abada don haka dolene muci gaba da jajircewa iya ranmu wajan ganin mun cinma burinmu tabbas in ba don sarila ta ceci rayuwar Darusi ba a lokacin da na harba masa wannan kibiya mai mugun dafi ba da tuni ya sheka barzahu yanzu itace zata mutu kuma bamu san a inda ta boye taswirarta ba Abin tambaya anan shine menene dalilin da yasa sarila ta ceci rayuwar darusi? Tabbas ruwa baya tsami banza kodai ta kamu da tsananin sonsa da gaske ko kuma tana sonta yaudare shi don amfani dashi wajan isa kogon Taskar Ajali. Sa adda sarki Damnashi yazo nan a jawabinsa sai shugaban dakarunsa ya risina a gareshi yace ya shugabana yanzu dai dole ne mu dakatar da komai har sai mun gano halin da sarila ke ciki walau tana raye ko ta mutu sarki Damnashi ya numfasa yace sarila zata iya yiwa kanta maganin dafin wannan kibiya domin tasan shi amma wai shin ta yaya aka baiwa gimbiya suzaina dafi tasha domin wannan gudan jini daya furzo daga bakinta akwai guba a cikinsa yanzu dai akwai yiyuwar mutuwar gimbiya idan kuwa ta mutu na tabbatar da cewa komai zai koma hannun yazrina da sarila da darusi abu ne mai sauki a wajena domin nafi tsoron sarila da su saboda dukkaninsu tafisu kaidi da makirci da kuma sanin tuggun duniya sai da aka shafe kwanaki uku cif a cikin wannan birni ana bincike da neman masu laifi bisa dokar hana kowa shige da fice amma ba agano komai ba aranar kwana na ukunne da farkon safiya aka janye dokar kowa ya fita don aiwatar da harkokinsa a ranar ma sai da kasuwa taci. Attajiri Damnashi kuwa sai a ranar kwana na ukunne ya sami damar isa fada don karbar kudin kayan hajojinsa yana isa ya iske jama a sunyi dandazo a fadar ana jiran sarki ya fito domin aikalan gasa su yanke hukunci bisa wanda ya cancanci a ba shi kambu kai nima dai Guyson na cancanci ku bani Kambu a wannan zauran+ koda attajiri damnashi tare da yaransa suka shigo cikin fadar sai suka hango jarumi darusi tare da gimbiya suzaina zaune a can saman gini kusa da karagar sarki cikin hanzari damnashi ya buya a cikin yaransa ya sake batar da kamanninsa yayi shiga irin ta yaran nasa saboda ya tabbatar da cewar idan har ya kusanci darusi suka hada idanu sai ya shaida shi. A wannan lokaci sarila da yazirina na zaune a gefe daya kusa dasu darusi shikuwa mujahid yana tsaye a hannun hagun jarumi darusi yana ta kalle kalle da waige waige yana lura da duk mutanan dake cikin fadar da kuma wadanda ke shigowa jarumi darusine ya bashi wannan aiki domin kada makiya su shammacesu su sake kawo musu wani harin duk da cewa an kara tsananta tsaro a fadar an ninka yawan dakaru sau uku a dai dai wannan lokacine sarki ya shige cikin fadar ai kuwa sai kowa ya mike tsaye don girmamawa shi har sai da sarki ya iso inda karagar sa take ya zauna sannan kowa ya koma kan mazauninsa A sannan ne jama suka fara yin kus kus kowa na fadin albarkacin bakinsa bisa abinda ake zaton zai wakana kawai sai aka ga sarki ya mike tsaye ya fuskanci jama ayayi gyaran murya yace. Yaku jama ar wannan biri namu mai albarka kamar yadda kukaga ni da idanunku abubuwan da suka faru a gasar jarumta na ban tsoro da ban mamaki abubuwane wadanda basu taba faruwa ba kuma hakan ya na nuni da cewar akwai makiyanmu a cikinmu amma bamu san su ba kowa ya sani cewa jarumi darusi da gimbiya suzaina sunyi ragas a wannan gasa babu wanda ya sami nasarar karbar kambun jarumta daga cikinsu bisa dokar wannan gasa idan har ta kai da anyi kunnan doki to dolene a sauya salon gasar kuma a sake yin wata gasar sabuwa A yanzu na yanke shawarar cewa za a sake yin wannan gasa kuma yanayinta shine za ayi shiri a tafi izuwa kogon TASKAR AJALI duk jarumin da ya iya yakar mugayan abubuwan dake kan hanyar zuwa can din da kuma abubuwan dake cikin kogon ya hallaka su sannan ya iya dauko dukiyar dake cikin kogon shine ya lashe wannan gasa ta birnina kuma shi za a baiwa kambun jarumta na duniya gaba daya Ehm An ya bada Guyson za ayi wannan gasar ba kuwa. Amma dai bari muji cigaban labarin.. Za ayi wannan tafiya ne nan da cikar kwana bakwai don haka duk wanda yake da sha awar shiga wannan gasa to ya kai sunansa zuwa alkalan gasa ayau din nan kafin gari ya waye lokacin da sarki yazo nan

Chapter 12 of 14