Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a zancensa sai gaba dayan jama ar dake cikin fadar suka kamu da tsananin mamaki kuma hankalin jamaar gari ya dugunzuma bisa jin cewar akwai makiyansu a cikinsu basu sani ba. Take a wajan aka rinka kallon kallo tsakanin baki da yan gari koda ganin abinda ke faruwa sai sarki ya daga hannu aka yi tsita a lokacin da fadar ta cika da hayaniya sannan sarki yace yaku jama ata ku kwantar da hankalinku kuyi sani cewar na sanya gawurtaccen tsaro a cikin garin nan don haka da izinin Allah babu wani makiya ida zai iya cutar da waninmu ina so ku sani cewa ba aikin ku bane ku binciko makiyan dake cikinmu domin zaku iya zargi wasu daga cikin bakinmu wadanda basu da laifin komai idan ma kunga wani kuna zarginsa sai dai kuzo ku sanar da mu mu koma mu dauki mataki a kansa. Duk wani bako da yake son ganawa dani yanzu yaje ya sameni a can dakin gani na wajan fada duk wanda yasan akwai wani alkawari a tsakanina dashi ya tabbatar da cewar shi ma yaje can dakin gani ya jirani koda sarki yazo nan a zancensa sai hankalin Sarki Damnashi ya tashi ainun saboda ya gano cewa wannan wani mataki ne a ka dauko da za a iya tona asirinsa kawai saiya dubi shugaban dakarunsa yace dashi maza kaje can dakin gani ka wakilceni idan wannan sarki ya tambayeni kace dashi bani da lafiya ne shi yasa ban fito ba sarki damnashi ya sake duban wani hadimin nasa mai suna KAIZUR yace kai kuma kayi sauri ka koma can masaukinmu tare da sauran jama armu ka yi irin shigar da nayi ta bad da kama don ni yanzu akwai abinda zanje na gabatar a wani wurin daban koda gama fadin hakan sai sarki Damnashi ya kutsa cikin jamar dake fada ya fita daga cikin fadar ya bace bat! Bayan sarki ya fito daga fada sai ya kirawo jarumi Darusi da gimbiya suzaina yayi musu kwatancen gidan Attajiri damnashi da kuma kwatancen kamanninsa yace su yi maza suje can masaukin nasa suyi bincike a kansa sosai domin yana zarginsa nan take kuwa suzaina da darusi suka hau dawakai suka zabureshi izuwa hanyar da zata kaisu can bayan gari inda gidan Attajiri Damnashi yake ashe sarila da yazirina na labe a can gefe daya suna kallon abindake faruwa koda sukaga su darusi sun tafi sai suma sukayi bad da kama sukayi shiga irin ta 'yan kasuwar garin suka rinka bin sawun dawakan su Jarumi Darusi a kasa ba tare da su Darusi sun sani cewa Ana biye dasu ba..... ME ZAI FARU MU HADU A LITTAFI NA TARA DONJIN KARSHEN WANNAN LABARIN TASKAR AJALI Littafi na Takwas 8 Na Abdulaziz Sani M Gini Complet Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI Littafi na Tara 9 Marubucin littafin Abdulaziz Sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com Part A Al amarin mujahid kuwa lokacin da fada ta watse kowa ya kama gabansa sai yayi sauri ya koma cikin gidan sarautar bai zame ko ina ba sai masaukin su jaruma sarila da yake dakarun dake tsaron wajen sun sanshi kuma suna ganinsa tare da jarumi Darusi babu wanda ya tsayar dashi ko ya tuhumeshi akan dalilin da yasa zai shiga cikin turakarsu sarila A she jarumi darusi ne ya umarceshi da ya shiga cikin turakar tasu ya bincike kayansu gaba daya idan yaga waddannan taswirori na zuwa kogon TASKAR AJALI ya konasu. Ba komai bane yasa darusi yayi wannan tunani ba face yaji a jikinsa cewa akwai wani makiyi a boye wanda ya shigo cikin gari domin farautar wadannan taswirori kai tsaye mujahid ya kunna kai har zuwa cikin kuryar dakin barcinsu Sarila ya shiga bude akwatunan su da dukkan jakukunansu yana bincike sai da ya zazzage komai amma ko alamar taswirorin bai gani ba nan take ya shiga mayar da komai inda yake cikin hanzari yana cikin wannan haline ya juyo motsi takun sawu an durfafo kofar dakin nan take hantar cikin sa ta kada ya firgita ainun baisan sa adda ya bude daya daga cikin manyan akwatunan ba ya shige ciki ya kulle kansa kawai sai ya tuno da wata addu a wadda yaji darusi na yawan karantata da daddare don neman tsari daga sharrin mutum da Aljan kawai sai ya kama karantata a cikin zuciyarsa duk daya san cewa bai karbi addinin musulunci ba a wajan darusi. Ashe kuwa ba wani bane ya durfafo wannan daki ba face sarki DAMNASHI maimakon damnashi ya bude kofar dakin ya shigo kawai sai ya ratso ta cikin garu kamar yadda danshi ke ratsa kasa take ya baiyana a tsakiyar dakin cikin hanzari ya shiga bude jakukkunan da akwatuna yayi ta bincike yana neman wadannan taswirori guda uku har yazo kan akwatin karshe wacce mujahida ke ciki bai ga komai ba koda ya bude wannan akwatin karshe sai ya ganta wayam babu komai a cikinta hakika Allah shine sarkin iko kuma shine mai yin yadda yaso a zahirin idan Damnashi baya ganin mujahida a cikin akwatin amma kuma a badini ga mujahid nan kwance a cikin akwatin gaba daya jikinsa na karkarwa saboda tsananin razanar da yayi saboda ya tabbatar da cewa koma menene ya shigo dakin yana daga cikin makiyansu kuma indai yayi arba da shi sai ya kasheshi ba komai ne ya hana sarki Damnashi ganin mujahid ba face karfin addu ar da yake karantawa a cikin ransa in ba don wannan hijabi da Allah ya sa tsakaninsa ba da ko sautin bugabar zuciyar mujahid dake fita daga cikin akwatin ya isa ya tona masa asiri amma sai Allah ya dodar da kunnen damnashi baiji ba tabbas addu a itace babbar makami mai tarwatsa azzalumai cikin matukar karfin hali mujahid ya dago kansa domin yaga ko wanene wanda ya shigo cikin dakin ai kuwa yana dago kansa yayi arba da sarki damnashi a tsaye yana huci da kumburi tamkar bakin kumurci saboda tsananin bakin ciki ranshin ganin wadannan taswirorin. Haka dai damnashi yayi duru duru sannan ya sake ratsawa ta cikinbango ya fice daga cikin dakin a sannan ne mujahid yayi doguwar ajiyar zuciya tamkar wanda ya kubuta da kyar daga cikin bakin kura kawai sai ya dafe kirjinsa da hannayansa biyu yace '' Godiya a gareka ya ubangijin musulunci tabbas kaine kadai ubangijin da ya cancanci a bauta masa gama fadin haka keda wuya sai mujahid ya fito daga cikin akwatin da sauri ya fice daga cikin dakin Sarki na zaune a dakin gani shi kadai saiga wani hadimin attajiri damnashi ya shigo tare da dakarun sarki suna masu yi masa jagora koda ganin hadimin sai sarki ya buga tsaki ya dubeshi a fusace tun kafin ya risina ya gaishe shi yana mai daka masa tsawa yace ina mai gidan naka saboda me zai aiko ka shi yaki zuwa nan da kansa koda jin wannan tambaya sai hadimin ya zube kasa kamar zai yiwa sarki sujjada jikinsa na karkarwa yace ka gafarceni ya shugabana ya sarkin sarakuna kayi sani cewa tun daren jiya zazzabi ya kamashi don haka akwance yake bai sami karfin fitowa ba koda jin haka sai sarki yayi ajiyar zuciya yace to shi kenan ka saurara a nan ka jira zan aiko da kudin hajarku ka kaiwa shugaban naku koda gama fadin hakan sai sarki ya mike tsaye ya fice daga cikin dakin ganin yayin da hadimin yayi ta godiya + A can gidan da attajiri damnashi sauka kuwa jarumi darusi da gimbiya suzaina na isowa kofar gidan sai suka ja linzamin dawakansu suka tsaya cak sannan suka sauko daga kan dawakan nasu suka daure su a jikin dirkar gini faruwar hakan keda wuya sai suka ga an bude kofar gidan saiga wannan hadimi na damnashi wanda yace dashi yayi irin shigarsa ya fito fuskarsa cike da gashi idonsa guda like shi dai wannan hadimin yana matukar kama da sarki damnashi hatta tsawonsa da kaurin jikinsa yazo iri daya dana damnashi abin da ya banbantasu kawai shine shekaru shi wannan hadimin matashine dan shekara ashirin da biyar zuwa talatin shi kuwa sarki damnashi ya haura shekara arba in da biyar koda jarumi darusi yayi arba da wannan hadimi a karon farko sai ya zabura ya zare takobinsa domin a zatonsa sarki Damnashi ne Amma da yaga cewa hannayensa biyu ne lafiyayyu kuma ya lura da cewa ai matashine shekarunsa basu kai na sarki damnashi ba sai yayi sauri ya mayar da takobin tasa cikin kofenta ya dubi hadimin yace munzo ne muyi bincike a cikin wannan gida naku bisa wani abu da muke zargi koda jin wannan batu sai hadimin yayi murmushi yace ai babu matsala ko zamuje kuyi bincikenku amma ina mai tabbatar muku da cewa babu wani abin laifi da zaku gani domin sarkinku ma ya zo da kansa tare da dakarunsa sun bincike komai da ko ina a cikin wannan gidan . Sa adda jarumi darusi yaji wannan batu sai yayi. Murmushi aikasan shi bincike indai ba a gama shi ba ba a gajiya da yinsa nan take darusi da suzaina suka kunna kai izuwa cikin gidan wannan hadimin na biye dasu a baya da shigowarsu suka ga sama da dakaru dari a zazzaune sun kura musu idanu kawai rabon da jarumi darusi yaga manyan mutane masu tsawo kauri da kirar sadaukantaka haka kamar wadannan tun a bayan can cikin wani daji da ya shiga a yankin kasar birnin rum kimanin shekaru biyar da suka gabata kallo daya sukayi dakarun shida suzaina suka san cewa indai yaki za ayi da wadannan mutane to fa sai abin da hali yayi ko zasu sami nasarar hallaka su amma bayan sun sha bakar wahala ko kuma idan sun sami taimakon Allah ba dai jarumtarsu da karfin damtsensu ya cecesu ba Abinka da wanda ya dogara da Allah ba tare da shakkar komai ba darusi da suzaina suka shiga aikin bincike har saida suka gama duba ko ina dake cikin gidan amma basuga wani abin laifi ba har darusi da suzaina sun jyo zasu fita daga cikin gidan sai sukaji sautin faduwar wani abu daga cikin wani daki kawai sai suka juyo da nufin su koma dakin amma sai wadannan dakaru masu kirar mutanan farko suka mike tsaye suka yi masu kawanya saigashi Darusi da suzaina sun zama yan kanana tamkar 'yan tsaki a gaban muzuru. Babban hadimin mai kama da sarki damnashi ya dubi su darusi a fusace me kuma zaku koma ku duba alhalin kum gama duba ko ina darusi yace ai duban da mukayi dazu babu kowa a cikin gidan nan sabanin ku da kuke zaune a nan kuma babu dakin da bamu shiga ba mun caje shi amma yanzu munji motsin mutum a cikin wancan daki don haka dolene mu koma mu ga ko wanene kafin darusi ya gama rufe bakinsa tuni wadannan dakarun sun zare makamansu kawai sai hadimin ya dubi jarumi darusi da suzaina yace idan kuna son kuje ku duba abin dake cikin wancan daki sai kun fara kawai da wadannan jama ar tamu kafin darusi ko suzaina daya daga cikinsu ya ce wani abu tuni dakarun sun afka musu an ruguntsume da masifaffen yaki mai tsananin ban tsoro Nidai gUyson komawa gefe nayi ina kallo ashe dai kan rufin wannan gida sarila da yazirina ne a kwance suna leken duk abin dake faruwa ta cikin wata karamar kofa koda sukaga yaki ya barke tsakanin su suzaina da wadannan mugayan dakaru sai suka yunkura da nufin su diro kasa daga kan rufin gidan amma sai sukaji an dako su sun fado kasa tim ! A matukar galabaice kafin su yunkura su tashi tuni irin wadancan samudawan dakaru mikanin su arba in sun turmushe su da karfin tsiya sun rufe su da raga kuma sun watsa musu hodar barci take suka bingire kasa suka kama sharar barci lokacin da aka ruguntsume da masifaffen yaki tsakanin su jarumi da darusi da wadannan samudawan dakaru ya zamana cewa ana kaiwa juna sara da suka cikin zafin nama juriya da bajinta sai hankalin darusi da na suzaina ya dugunzuma ainun ba don komai ba sai saboda sara da sukan baya tasiri a jikin dakarun kuma duk karfin naushi da bugunsu darusi dakarun shanye shi suke tamkar shafarsu suke in ba don su darusi suna da matukar zafin nama ba fiye da dakarun kuma sun iya yaki matuka da farat daya dakarun zasu gama dasu. Su dai wadannan samudawan dakaru musamman sarki damnashi yaje yayi hayarsu daga can birnin Rum kuma ko kadan basa aiki da tsafi face tsagwaran karfi da kuma maganin tauri na saiwoyin bishiyoyi da itatuwa da suke sha sudai wadannan dakaru anbasu hayan yaki ne na musamman tsawon shekaru takwas wanda yasa har suna iya shafe sa a ashirin da hudu suna yaki ba tare da sungaji ba sai da sarki damnashiya biya dinare miliyan dubu daya sannan aka ba shi wadannan dakaru su dari da arbain farko gwajin da aka yiwa wadannan dakaru bayan sun gama karbar horon yakinsu na shekara takwas wani birni mai suna baitul hurus aka tura su a shirin sukashe gaba dayan mazajen garin suka kama matansu da yara a cikin kwanaki uku kacal tabbas karfin damtsen wadannan dakaru da juriyarsu ta yaki ta wuce gaban kwatance Ana cikin yin wannan bakin artabu ne daya da cikin samudawan dakarun ya shammaci suzaina ya gabza mata wawan naushi a ciki saboda karfin naushin sai da yayi sama ya bugu da ciki a matukar galabaice tana zubar da jini ta hanci da baki a sannane samudawan dakarun su da yawa suka daga manyan addunansu zasu gididdiba suzaina koda jarumi Darusi yaga abinda ake shirin faruwa sai ya kwala kabbara da karfin gaske kuma ya daka tsalle sama daga inda yake gumurzu tamkar an harbo shi da kibiya Guyson sunana .. Yayita filfilawa akan dakarun dake shirin sassara suzaina ya gabza musu naushi a kan fuskokinsu su duka a lokaci guda suka tarwatse kowannansu sai gashi ya furzo gudan jini gami da hakori guda daga cikin bakinsa karfin naushin kuma suka kife kasa a matukar galabaice al amarin da yayi matukar baiwa sauran samudawan dakarun mamaki kenan kuma ya fusata su ainun suka tasowa darusi gaba dayansu da suyi masa rubdugun da zasuyi filla filla da sassan jikinsa kaico idan mutum ya yanka kazar wahala dolene ya fige a banza hakika wanda duk ya dogara da Allah ba mai taba tozarta sa ashe lokacin da jarumi darusi ya kwallah wannan kabbara da karfi sai ya ci gaba da yiwa Allah kirari a cikin zuciyarsa yana mai neman tsari daga wadannan samudawan dakaru aikuwa nan take yaji wani irin gagarumin karfi yana shigarsa cikin jikinsa wanda bai taba jiba sai da yaji kamar zai iya aza gammo a kansa a dora masa duniya gaba dayanta yayi dako+ hahahah Kai madakin gini wannan anya kuwa Guyson dai yana mamakin wannan jarumta kufa+ maimakon jarumi darusi yaci gaba da yakar dakarun da makami sai ya yarda takobinsa ya rinka buge makaman dake hannunsu suna zubewa kasa kuma ko hannu suka hada dashi take suke karyewa idan kuwa ya danki hannun mutum ko kafarsa sai dai kaji kal !! Ya karyata tamkar ya karya silin kara duk sa adda suka kawo masa sara suka saidai suga suna samun iska sabida kaucewar da yakeyi cikin bakin zafin nama na gaban kwatance A hankali ne samudawan dakarun suka rinka kurma ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da suke ji suna zubewa kasa nakasassu koda wannan hadimin sarki Damnashi yaga wannan irin barnar da ake yiwa dakarunsa sai ya firgita ainun ya ruga da gudu izuwa wannan daki wanda su darusi suka jiyo motsi wadancan samudawan dakaru guda arba in kuwa wadanda suka kama su sarila suka daure ko da suka jiyo ihun yan uwansu a cikin gidan sai suka ruga gaba dayansu izuwa cikin gidan domin sukai dauki suna shiga suka iske tuni jarumi darusi ya bazar da kimanin mutum sittin daga cikin yan uwan nasu, koda ganin haka sai suka juya da baya da gudu suka nausa cikin daji ganin haka sai ragowar tsirarun dake yakar darusi suma suka tsere suka barshi a tsaye tare da nakasassun Ehm lallai Jarumi Darusi sadaukine kamar Guyson. Hh. A sannan ne darusi ya ruga izuwa inda suzaina ke kwance ya tasheta zaune kawai sai yaga ta goge jinin dake kan hancinta da bakinta da kanta sannan ta dubeshi cikin murmushi tace kada ka damu yakai masoyina babu abinda ya sameni kyaleni na dan huta saboda na bugu sosai a ciki maza ka ruga izuwa cikin dakin nan kaga ko meye a ciki batare da gardamar komai ba kuwa sai darusi ya mike zumbur ya ruga izuwa cikin dakin yana shiga sai yaga ashe akwai wata rijiya a gefe daya wacce a farkon shigarsu dakin basu ganta ba amma yanzu an kauta murfinta daga kanta koda darusi ya leka cikin rijiyar sai yaga ashe hanyace ta fita daga cikin gidan nan take ya gane cewa adazu da suka jiyo. Motsi a wannan daki wani ne ya shigo yanzu kuma wannan hadimi ne ya fice ta cikin rijiyar ya tsere take darusi ya aiyana a cikin ransa yace duk yadda akayi attajirin da ya sayarwa da sarki haja shine ya taara wadannan dakaru kuma lallai akwai abinda yazo nema ko shakka babu yana daga cikin makiya cikin hanzari. Ya dawo wajan suzaina ya taimaka mata ya tasheta tsaye suka fice daga cikin gidan tana dingishi' da fitarsu sai sukayi kicibis da sarila da yazirina kwance a kas kuma daure cikin raga suna ta fama shara barci cikin kaduwa da mamaki suzaina ta dubi darusi tace wadannan kuma menene ya kawo su nan ko kuwa satosu akayi koda jin wannan tambaya sai jarumi darusi ya gyada kai yace ba sato su akayi ba su da kansu suka kawo kansu suzaina tayi ajiyar zuciya tace ko dai suna son su munafuncemu ko kuma su hada kai da makiya darusi yace Ai baki da tabbas kawai kina zargine yanzu yaya zamuyi da su suzaina tace kawai kabarsu a nan inda ka gansu in yaso wayonsu da karfinsu ya kwacesu darusi yace A a idan muka barsu a nan makiya suka dawo suka riskesu zasu iya hallaka su ba karamin asara bace rashin sarila da yazirina saboda idan suka karbi addinin Allah zasu musuluntar da mutane da yawa wadanda bame zan iya adadin su ba saboda su masu jama ane koda gama fadin hakan sai darusi ya sa takobinsa ya yanke ragar data lullube sarila da yazirina kawai saiya kamo dokinsa ya dora sarila da yazirina a kai sannan ya dubi suzaina yace ai saiki hau kan naki dokin mu tafi nan fa gardama ta karke a tsakaninsu suzaina na cewa sai dai ya zo ya hau nata dokin ko kuma ita ma ta taka da kafarta cikin Alamun fushi ya dubeta yace kinsan cewa haramunne hada jikina da naki tunda ke ba matata bace kuma ke ba muharramata bace? Koda gama fadin hakan sai darusi yaja linzamin dokinsa yayi gaba yazirina da sarila na bisa dokin suna ta faman shara barci suzaina tayi tsaki tace a ranta ba zan iya jiran sai mun dawo daga kogon Taskar Ajali ba sanna na sami ikon kusantarka dolene na tafi a matsayin matarka nan take itama ta kada dokinta ta bi shi a baya da sauri suka tafi Guyson nake Al amarin sarki Damnashi kuwa lokacin da ya baro turakarsu sarila bayan ya caje ko ina baiga wannan taswirar da yake nemaba sai ya yi amfani da karfin sihirinsa ya dawo masaukinsa a cikin dakika goma kacal koda ya baiyana a kofar gidan yaga dawakai guda biyu a daure sai jikinsa ya bashi cewa lallai makiya ne suka zo domin haka sai ya zagaya bayan gidan ya bude wannan hanya ta sirri dake karkashin kasa ya shige gidan bai bullo ta ko ina ba sai cikin wannan dakin rijiya a dai dai lokacinne darusi ya fara samun nasara akan samudawan dakarun nan sarki Damnashi na fitowa daga cikin rijiyar sai ga wannan hadimin nasa mai kama dashi ya shigo a firgice ya na ganin sarki Damnashi sai ya dubeshi cikin dimauta da tsananin tsoro yace ya shugabana jarumi Darusi ne ya shigo gidan nan ga shi can yana ta karkarya wadannan dakarun daka hayo tabbas in ya gama dasu kanmu zai dawo ka tuna cewa sa adda kake da hannayanka ma biyu ya sami nasara akanka bare yanzu da kake da guda daya idan baka bar nan ba yanzu har a bada ba zaka dauki fansa ba akan darusi kuma ba zaka taba cika burinka ba na mallakar dukiyar dake cikin TASKAR AJALI. koda hadimin yazo nan a zancensa sai hankalin sarki Damnashi ya tashi ainun kuma ransa ya baci a lokacin da bakin ciki mara misaltuwa ya turnuke shi kawai sai ya zare takobinsa da lafiyayyan hannun nan ya yunkura zai fita can inda ake wannan gumurzun ya fafata da Jarumi Darusi amma sai hadimin nasa ya janye shi suka shige cikin rijiyarnan mai matattakala suka manta basu rube ba shine dalilin da yasa Jarumi Darusi yaga rijiyar Da karfin sihirin tsafi sarki damnashi da hadiminsa suka bace bat basu baiyana a ko ina ba sai a wani gida daban wanda suka kama dake can kudancin birnin. A cikin tsakiyar falon gidan suka baiyana sarki damnashi nata huci gami da ciza lebe saboda tsananin fushi kawai sai ya zauna akan kujera yayi tagumi shima hadimin sai yaje ya zauna akan wata kujerar dake gefe daya duk su biyun sukayi tagumi a dai dai wannan lokaci ne wata zukekiyar Kuyanga ta shigo cikin falon dauke da tambulan giya gami da kofuna guda biyu ta ajiye a gabansu kuma ta zubawa kowannansu ruwan ta mika musu maimakon sarki Damnashi ya karbi kofin yasha sai ya buge hannun kuyangar ya daka mata tsawa ya namai korarta kuyarngar ta mike da sauri jikinta na tsuma ta fice daga cikin falon faruwar hakan keda wuya sai sarki Damnashi ya dubi Hadimin yace' tun da dai yanzu asirinmu ya tonu babu sauran batun boye boye kaje can wajan alkalan gasar da sarkin garin nan ya shirya ka bayar da sunana a cikin jaruman da zasuyi wannan gasa koda jin wannan batu sai idanun hadimin suka zazzaro ya dubi sarki Damnashi cikin firgici yace ya shugabana ai idan ka bayyana kanka kama ka za ayi a kashe ka ko a tsire ka a kurkuku koda jin wannan batu sai sarki Damnashi ya bushe da dariya yace kai ba sarki bane shi yasa bakasan cewa kashe sarki ba abune mai sauki ba ka tuna cewa sarkin garin nan da jama arsa sun karbi addinin musulunci sannan kuma shi jarumi darusi bashi da burin ayita zubar da jini a doron kasa yafi son jama a sukarbi addinin nasa ya yadu ko ina idan na shiga wannan gasa darusi da sarkin garinnan zasuyi murna da hakan saboda a tunaninsu zuciyata zata karaya bisa ganin irin abubuwan Al ajabin da darusi zaiyi na jarumtaka akan hanyarmu ta zuwa kogon Taskar ajali har nayi imani na karbi Addininsa jama ar dake karkashina sunfi miliyan goma kaga ashe ina karbar addinin suma zasu karba abin da basu sani ba shine babu wata masifa da zata iya sani na bar addinina na iyaye da kakanni na da kuma al adun dana gada daga garesu zanyi amfani da wannan dama ne kawai na mallaki dukiyar dake cikin taskar ajali sannan na kashe su Darusi na zamo SARKIN DUNIYA koda gama fadin hakan sai sarki damnashi ya sake bushewa da dariya a karo na biyu yayi ta kyalkyala dariyar kamar ba zai dainaba + Ni kaina da nake muku typing dinnan wato Ni guyson na dan tsorata da dariyar tasa fa + koda ganin haka sai shima hadimin ya taya shi yin dariyar suna cikin wannan haline daya hadimin da yaje gidan sarki karbo kudi ya shigo cikin falon dauke da katuwar akwati fuskarsa cike da annuri kawai sai ya ajiye akwatin a gaban sarki Damnashi ya budeta babu komai a cikin akwatin face Lu'u lu'u koda ganin wannan dukiya sai sarki damnashi ya bushe da mahaukaciyar dariyar farin ciki sannan yace sarki ya sayi baki da kudinsa wadannan kyayyaki dukkaninsu ba kaya bane muna barin garin nan don tafiya kogon TASKAR AJALI kayan zasu rikide izuwa dakarun bakaken Aljanu suci birnin da yaki mata da kananan yara kadai za a bari a raye kaga kenan ina dawowa daga TASKAR AJALI a nan birnin zan fara yada zango nayi sha anina. Koda jin wannan gagarumin shiri sai hadiman suka rungume sarki Damnashi suna masu yi masa kirari da jinjina kwatsam sai sukaga sarki Damnashi ya murtuke fuskarsa a lokacin da hawaye ya zubo masa cikin kaduwa suka janye jikinsu daga cikin nasa suka dubeshi a firgice babban hadimin da karamin suka dubi junansu sannan babban yace ya shugabana ina dalilin wannanp Sauyin yanayi a tare dakai farat daya koda jin wannan tambaya sai sarki Damnashi yayi ajiyar numfashisannan yace ai iya gumurzun da gwagwar mayar da nayi a rayuwata ba a taba fitar mini da koda digon jini ba a filin daga bare a yi mini wani babban rauni amma saigashi jarumi darusi ya sare mini hannuna guda yanzu gashi zan zama sarkin duniya nan kaf amma bani da hannu guda hm caka buri kenan wai. Nakasa ga sarki ba karamar kankanta bace na rantse da darajar ikona sainayiwa jarumi darusi kisan wulakanci irin wanda ba a taba yiwa wani mahaluki ba a doron kasa saina wulakanta gangar jikinsa yadda labarin wulakantar sa zai baza duniya baki daya.Final Round. A can gidan sarki kuwa lokacin da sarki yaga an dade sosai su jarumi darusi basu dawo ba sai hankalinsa ya sosu nan take ya bayar da umarnin a kawo masa kayan yakinsa da dokinsa kuma ya umarta wasu dakaru wadanda zasuyi masa rakiya nan da nan kuwa aka gama shiri tsaf har sarki ya kamo dokinsa zai hau sai ga jarumi darusa janye da doki mai dauke da sarila da yazirina suna barci gimbiya suzaina na biye dashi bisa nata dokin cikin kaduwa da mamaki sarki ya taho garesu ya taryesu yana mai duban darusi yace menene ya faru ya kai uban jaruman duniya Darusi ya numfasa sannan ya risina ga sarki cikin girmamawa yace tabbas abinda kake zargi akan wannan attajiri gaskiya ne shine wanda yayi kokarin hallakani a filin gasa domin a masaukin nasu akwai wadansu samudawan dakaru daga birnin Rum kimanin su dari da doriya In ba don taimakon Allah ba da tuni sun hallakamu ni da gimbiya mun caje ko ina a gidan bamuga komai ba sai wata rijiya a cikin wani daki wacce hanyace ta karkashin kasa ta fita daga gidan bayan mun fito daga gidan sai muka tsinci sarila da yazirina kwance a daure cikin wannan hali da suke ciki yanzu amma sa adda zmu shiga gidan babu su a wurin lokacin da jarumi darusi yazo nan a zancensa sai sarki yayi doguwar ajiyar zuciya sannan yace tabbas koma menene wannan attajiri dolene ya kasance daya daga cikin manyan sarakunan duniyar nan dole ne muyi iya kokarinmu mutabbatar da cewa mun kamashi mun kaishi kurkuku mun tsare shi kafin mu tafi zuwa kogon taskar ajali saboda gama san irin mugayan abubuwan da yake kokarin shiryawa a cikin birnin nan ba to amma kuma ai in daso yake ya yakeni da tun a farkon zuwansa zai sa samudawan dakarunsa su afma mana duk yadda akayi dai yana da wata bukatar a wajanku bisa wannan daliline yasa aka kama sarila aka daure dajin wannan batu sai mamaki ya kama darusi da suzaina sannan yace'' ya shugana yanzu kuna nufin kace tare da kai zamu tafi kogon taskar ajali? Sarki ya

Chapter 13 of 14