Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
banda wacce tayi mana a cikin gari,yanzu mene ne abin yi?Lokacin da Sarki Ubaiyu yazo nan a jawabinsa sai Boka Matawus yaja dogon numfashi sannan yace hakika duk abinda ka fada gaskiya ne babu kuskure a cikinsa to amma tunda dai yanzu Sarila ta aminta da duk abinda na fada mata zamuyi amfani da dutse daya mu jefi tsuntsu biyu.Abinda nake nufi shine zamu iya cutar da Sarila mu bata wani abun dazata sha wanda zai zamo sanadin ajakinta ko ya jirkitar da hankalinta yadda zamu iya kwafe wannan taswira dake zane a gadon bayanta,shike nan ta rasa dukkan karfin jikinta dana sihirin tsafinta,kuma ba zasu sake dawowa gareta ba face ta kone wannan taswirar wacce aka kwafa Koda kuwa takai guda miliyan daya ma'ana ya zamana cewa babu guda daya irinta.Sa'adda Sarki Ubaiyu yaji wannan batu sai ya girgiza kai yace tabbas muna da babbar dama amma kuma hadarin dake cikinta tamkar mutum ya sayi ajalinsa ne da kudinsa.Idan har asirinmu ya tonu Sarila ta gane cewa mun zuba mata wani abu a cikin abin sha ko ci domin cutar da ita saita kashe kowa dake cikin gidan sarautar nan hatta iyalaina kuwa kuma ba'ama san iya inda barnar tata zata tsaya ba,watakila ma ya zamo sanadin da zata rushe gaba daya gidajen dake cikin birnin ta kone su kuma ta kashe duk wani abu mai rai dake cikinsa,ina mai baka shawara da idan akwai wata hanyar mafi saukin hadari da zamu cutar da Sarila to mu ajiye wannan tunda dai ance tsalle daya shi ke sawa a fada rijiya.Koda jin wannan batu sai Boka Matawus ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace tabbas kaima kayi tunani mai kyau saboda haka zan duba wannan al'amari da idanun basira nan da rabuwar dare domin na yanke hukunci,amma a halin yanzu ba zamu dauki wani mataki ba akan Sarila.Koda gama fadin hakan sai Sarki ™Abubakar Haleefah Physicist™ yasa aka kirawo hadimansa suka dauke shi suka tafi dashi izuwa cikin turakarsa domin ya cigaba da jinyar raunin dake jikinsa.Shima Boka Matawus saiya ja sarkin yaki suka tafi izuwa wani bangaren daban na gidan sarautar inda aka saba saukarsa idan zaiyi yan kwanaki a cikin fada yayin da wani gagarumin abu ya taso. *Al'amarin Sarila kuwa lokacin da wadannan kuyangi suka kamata suka tafi da ita izuwa masaukinta sai taga har aka shigar da ita cikin kewayen aka cire mata dukkan makamanta na yaki daga jikinta kuma aka cire dukkan tufafin jikinta jikin kuyangin bai daina tsuma ba saboda tsoronta da suke ji.Koda fahimtar hakan sai Sarila ta dubi shugabar wadannan kuyangin tace ku kwantar da hankalin ku na rantse da girman iyayena ba zan cutar da dayanku ba saboda yanzu ina cikin nishadi da farin ciki bisa sanin cewa na sami wanda zai taimake ni na gaggauta cika burina na kashe yar uwata Yazirina.Nan da kuka shigo dani ya tuno mini da irin rayuwar Ni'ima dana tsinci kaina a ciki a can tsibirin Jannatul Duniya.Maza ku shigar dani cikin bahon wankan nan kona huce gajiyar jikina.Koda Sarila tazo nan a zancenta sai kuyangin suka sami nutsuwa gami da kwanciyar hankali don haka nan da nan suka shigar da Sarila cikin wani katon bahon wanka na zinare wanda ke cike da ruwan dumi na wanka ga furanni a cikinsa gami da kanshin turaren miski dake tashi.Nan take suka fara yiwa Sarila wanka a hankali ita kuwa ta lumshe idanunta saboda jin dadin dukin ruwan da kuma wankan da akeyi mata.Bayan an gama yi mata wankan ne aka fito da ita daga cikin bahon tsirara aka shiga goge danshin dake jikinta.Wohoho! !!Hakika babu wani 'da namiji da zaiyi arba da Sarila a cikin wannan yanayi batare daya dimauce ba ya fita daga haiyacinsa ba,saboda irin tsananin kyawun surar da Allah ya bata,abin yafi gaban kwatance sai abinda idanu suka gani kawai,saidai ku wannan kyawu nata na banza ne domin kyan dan maciji ne tunda bata da imani kuma bata da tausayi ko kadan.Sarila bata san wani abu waishi sabo ba domi ta mayar da ran dan adam tamkar na kiyashi.Bayan an gama goge danshin jikin Sarila sai aka jata izuwa wajen kewayen aka shigar da ita cikin wani kasaitaccen dakin barci aka tsayar da ita a gaban wani katon madubi aka shiga shafe jikinta da mai sannan aka sanya mata wata farar doguwar riga irinta sarakai.Gashin kanta kuwa bayan an tsefe shi an busar da danshin dake jikinsa sai aka shafe shi ya rinka kyalli sannan aka tattare shi aka daure shi ya zubo gadon bayanta har izuwa kan mazaunanta masu tudu.Koda Sarila ta dubi kanta a cikin madubin taga irin kyawun da Allah ya bata da yadda tayi matukar kyau sakamakon wannan ado da akayi mata saita kama murmushi nan take taji babu abinda takeso sama data gaggauta cika burinta na mallakar wannan dukiya ta Boka Salmara domin ta zamo SARAUNIYAR DUNIYA!!!A sannan ne zata nemi namijin daya dace da ita ta aura domin ya zamo abokin rayuwarta,to waishin wanene wannan 'da namiji wanda zai dace da zabinta?Koda Sarila tayiwa kanta wannan tambaya a cikin zuciyarta lokacin data kurawa fuskarta idanu a cikin wannan madubi sai kawai hoton fuskar Mujahid ya fado a kan Madubin ta kura masa idanu tana mai cewa a cikin ranta tabbas wannan shine saurayin daya dace dani domin yana da kyau da sura irin wacce zuciyata keso.Koda gama aiyana hakan sai zuciyar Sarila ta buga da karfi tace a ranta lallai yanzu ne ta gane cewa ashe kamuwa tayi da son Mujahid shi yasa ta kasa kashe shi alhalin kuma gashi tana ganin cewa yana taimakon abokiyar gabarta.Lallai kuwa idan ta daka ta wannan SOYAYYA zata fuskanci babbar matsala wajen samun biyan bukatarta,ya zama dole tasan hanyar da zatabi ta gaggauta kashe Yazirina ta rabata da wadannan taswirori guda biyu tun kafin soyayyarta da Mujahid ta kara zurfi akai munzalin da zata cutar da kanta,yanzu dai zata zuba ido taga iyakar taimakon da wannan boka zaiyi mata idan ta fuskanci akwai karya da yaudara a cikin lamarinsa kawai zata kashe shi ne ta kashe sarkin nasa kuma ta cigaba da farautar Yazirina a cikin birnin koda kuwa yin hakan zai janyo sanadin mutuwar gaba dayan mutanen kasar gami da konewar komai dake bisa doron kasar birnin.Sarila na cikin yin wannan tunanin zuci ne kuyangin suka janyeta daga gaban madubin suka fitar da ita falo Inda Sarila taga wani dogon tebur mai tsawo kamu dari,a karkashinsa dama da hagu akwai kujeru guda hamsin hamsin bisa teburin an zuba farantai cike da abinci iri iri sama da kala dari.Ruwan inibi,ruwan tatattun sauran yayan itatuwa kuwa a cikin tambuka sun kai kamar kala ashirin.Koda Sarila taga an shirya wannan daula duk saboda ita sai tasha jinin jikinta tayi zargin cewa lallai akwai wani abu da ake shirin kulla mata na cutarwa.Koda aka zaunar da Sarila akan wannan tebur aka bude mata kwanukan abincin domin ta zabi wanda take sha'awar ci a zuba mata sai tayi murmushi ta dubi shugabar kuyangin tace inason kisa yaranki su debi loma dai dai daga cikin dukkanin wannan abincin su ci yanzu take a gaban idanuna har sai bayan cikar sa'a guda in banga wani abu ya samesu ba sanna zan iya yarda da wannan abinci naci.Koda jin wannan umarnin sai shugabar kuyangin tayi murmusgi tace ya shugabata ai duk wannan mai sauki ne,nan take kuwa shugabar kuyangin ta umarci kuyangin dasu aikata yadda Sarila keso sukabi umarnin cikin gaggawa,saida sa'a gudan ta cika Sarila taga babu abinda ya sami kuyancin walau na cuta kona jirkitar hankali sannan taci wannan abincin ta cika cikinta ta koshi.Koda ta kammala cin abincinta sai ta tafi izuwa dakin barci tana shiga ta turo kofar dakin ta kulleta sannan ™Abubakar Haleefah Physicist™ ta fada kan gado ta kama shara barci abinta tamkar a cikin turakarta take dake can tsibirin Jannatul Duniya. *A can gidan Matsafiya Muznaira kuwa lokacin da dare ya raba,Yazirina na kwance a cikin dakin barci shi kuwa Mujahid a falon dakin ya kwanta bisa kilishi yana ta faman rusar barci abinsa.Ashe dai ita Yazirina idanunta biyu ko rintsawa batayi ba don haka saita mike zaune daga kan gadon ta karanta wadansu dalasimai na tsafi sannan ta fito falon ta tashi Mujahid daga barci.A firgice Mujahid ya mike zaune firgigit ya dubeta cikin tsananin kaduwa yace lafiya me ke faruwa ne? Yazirina ta dubeshi cikin bata rai tace tashi zakayi muje mu sace wannan Kambun Sihiri dake hannun Muznaira yanzu mu sulale mu bar gidannan ko ta halin kaka. Toohfahh!!!Su Yazirina zasu sace Kambun Sihiri Bari dai in tsaya nan in buya kar su ballo mini ruwa dan nasan za'a gwabza gumurzu.Mu bar gidan nan ko ta halin kaka.Koda jin wannan batu sai hankalin Mujahid ya dugunzuma cikin alamun matukar firgita yace haba ya shugabata ta yaya kike zaton cewa zamu iya zuwa har cikin turakar Muznaira mu sace wannan kambun sihiri alhalin duk abinda muke takama dashi ta fimu.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta dakawa Mujahid harara ta dubeshi cikin karamar murya tamkar rada tace amma dai ka bani mamaki da haushi tace,yanzu kai baka ji kunya ba kake fada mini haka?Shin ka manta ne cewa kaine shugaban dukkan barayin wannan nahiya,kai fa saboda shahararka da gawurtarka bakawa karamin attajiri sata sai masu mulki da hamshakan attajiran da suka tumbatsa.Gaba daya manyan sarakunan nan guda hudu babu wanda bakaje har cikin masarautarsa ba kayi masa sata,akan wane dalili yanzu zaka yi shakkar karamar bokanya wacce bata kai su ba a komai?Maza ka tashi mu nemi inda turakarta take yanzun nan ku kuma nasa takobina na sare hannayenka da kafafunka tunda baka da sauran amfani a wajena.Koda jin wannan batu sai Mujahid ya mike zumbur da sauri yace ya na iya da ciwon ido dole sai hakuri muje kawai amma dai kece zakiyi mini jagora.Yazirna tace babu matsala.Koda gama fadin hakan saita juya ta nufi kofar fita cikin hanzari Mujahid ya bita har yana tuntube,kai tsaye Yazirina ta fito daga cikin dakin da suke ta nufi cikin gidan kai tsaye ba tare da tayi wani dube dube ba tamkar a cikin nata gidan take,shi kuwa Mujahid saiya cigaba da binta a baya a tsorace yana waigen bayansa tamkar ace kyat ya fita da gudu.Ta cikin fadar Muznaira Yazirina da Mujahid suka ratso bayan sun wuce kofofi goma sha daya kuma ko ina a tsaye masu gadi ne,duk inda sukazo da an tambaye su inda zasuje sai yazirina tace yar uwata Muznaira nake son gani.Ko musu ba'ayi musu ake bude musu kofar su shige,da suka iso kofa ta sha biyu ne sukayi kicibus da wani narkeken aljani mai matukar kwarjini da sura irin ta manyan sadaukai,Aljani n ya dubi Yazirina fuskarsa a murtuke yace ai maigirma Muznaira bata gaya mini cewa zaku kawo mata ziyara ba a matsayina na sarkin gida,don haka babu wani dalili da zaisa na barku ku wuce.Koda jin wnnan batu sai Yazirina tace ai kuwa babu wani mahaluki wanda ya isa ya hanani ganin yar uwata tunda dai ubanmu daya,idan kaga ban wuce cikin wannan kofa ba na isa turakarta to saidai idan bana numfashi a doron kasa.Koda jin wannan batu sai Aljanin yayi dan guntun murmushi irin na manyan jarumai masu takama da kansa sannan yace ai kuwa idan kika ga kema kin wuce ta cikin wannan kofa saidai idan na zama gawa domin ina kan aiki na ne na tabbatar da tsaro,idan kina ganin cewa zaki iya kawar dani ki shige to sai mu RABA GARDAMA.Koda gama fadin hakan sai Aljanin ya zare wata sharbebiyar takobi dake rataye a bayansa sannan ya bude ya dubi sauran yaran nasa yayi musu inkiyar su gusa su basu wuri.Nan take kuwa dakarun suka ja da baya ba tare da shakkar komai ba kuwa sai Yazirina ta zare tata takobin itama ta bude tana mai gyara tsayuwarta.Koda ganin haka sai tsoro ya kama Mujahid yasha gaban Yazirina yace saboda me zakiyi tunanin yakar dakarun gidan nan alhalin so muke mu gama komai cikin sirri da sa'a.Maimakon Yazirina tace dashi wani abu sai tasa hannunta ta bangaje shi yaje ya buga kai da bango ya fadi kasa sumamme ko kallonsa batayi ba,saita fuskanci wannan Aljani wato shugaban dakarun gidan tace lallai kuwa yau saidai uwarka ta haifi wani domin babu abinda zai hanani wucewa ta cikin wannan kofa.Koda jin wannan batu sai Aljanin ya tuntsire da dariya yace suna nan Lafwas Bin Zabbar yau shekarata dari da ashirin kenan ina aikin tsaro a gidajen manyan bokaye na duniya.Nayi aiki a gidajen Bokaye saba'in da uku kuma a tarihin wannan aiki nawa ba a taba zuwa an shiga inda nake tsaro ba walau da KARFIN DAMTSE kona Sihiri,tabbas yau kin taba tsuliyar dodo don haka zaki gane kuskurenki.Koda gama fadin hakan sai Lafwas ya dako tsalle a sama yana mai daga takobinsa sama ya kawowa Yazirina mugun sara a wuya da nufin ya cisge mata kai.Cikin bakin nama Yazirina ta goce takobin tasa ta sari dirkar gini take dirkar ta rabe gida biyu ta fadi kasa amma duk da haka rufin ginin saman bai fado ba kasa sakamakon cewa dirkokin suna da yawa.Nanfa Yazirina ta taso da dukkan karfinta suka kacame da masifaffen yaki na ban al'ajabi da ban tsoro wanda ya jefa sauran dakarun cikin tsananin mamaki saboda a iya zamansu a cikin wannan gida basu taba ganin wani mahaluki mai tsaurin ido daya taba tarar Aljani Lafwas da yaki ba sai Yazirina kuma gashi ta kasance bil'adama kuna 'ya mace ba komai ne yasa wadannan dakarun aljanun sukayi mamakin Yazirina ba face sanin cewa a cikin jaruman Aljanu na duniya a yanzu babu mai karfin Damtsen Lafwas gami da iya yakinsa.Koda aikin tsaro babu mai iya daukarsa face wanda yake da dimbin dukiya mai tsananin yawangaske,sabo da a duk karshen wata ana biyansa albashin dabai gaza dinare miliyan uku ba.Wani lokacin kuma koda Boka bashi da kudin da zai iya biyansa yana dubwa ya gani ko wannan boka yana da wani babban aiki a gabansa wanda idan ya kammaka shi zai iya samun babbar daukaka ko kuma wata gagarumar dukiya sai suyi hakkinsa na iya watannin dayayi yana aiki a biya shi,tabbas Aljani Lafwas ya kasance mai rike alkawari da amana don haka komai tsanani baya yarda a sami sabani.Saida Yazirina da Aljani Lafwas suka sha tsanainin zafin nama,juriya da bajinta ta gaban kwatance amma dayansu bai sami nasarar koda lakutar jikin daya ba saboda iya yakin nasu yazo iri daya tamkar malamin daya koya musu yaki daya ne.Abinda ™Abubakar Haleefah Physicist™ ya daurewa Aljani Lafwas kai shine hatta zafin namansa yazo daya alhalin shi yana matsayin Aljan ita kuma bil'adama.Bisa dole duk su biyun suka ja da baya sukayi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru.Duk tsawon wannan lokaci da ake fafatawa Bokanya Muznaira dake can cikin turakarta tana ta fama shara barci bata ma san abinda akeyi ba duk da cewa sakamakon artabun da Lafwas da Yazirina keyi wasu garuka na gidan sun rurrushe kuma kayan alatu dayawa sun ragargaje.Shima Mujahid tunda yayi wannan dogon suma bai fardado ba.Bayan anyi kallo tsakanin Aljani Lafwas da Yazirina sai Lafwas ya mayar da takobinsa cikin kufe ya dubi Yazirina a fusace a lokacin da har wani tiriri na takaici ne ke fitowa daga cikin bakinsa tace tunda iya yakinmu yazo daya ai sai mu jarraba karfin damtse mu gani kafin ta kaimu gayin amfani da karfin sihirin tsafi,idai nasani cewa ruwa ba sa'an kwando bane.Koda gama fadin hakan sai Sadauki Lafwas ya dunkule tafin hannayensa biyu take kwanjin jikinsa ya kumburo,jijiyoy insa suka kumbura yana mai gyara tsayuwarsa kuma yana kada fuka fukansa guda biyu.In badon fukafukan Aljani Lafwas ba da kuma kahon dake kansa guda biyu gami da manyan kunnuwansa guda biyu da kuma faratan hannayensa dana kafafunsa da dauka za'ayi mutum ne shi ba aljan ba saboda komai nasa irin na bil'dama ne kuma ya kansace kyakkyawa a cikin jinsin Aljanu.Ita kanta Yazirina da taga irin murdewar Aljani Lafwas gami da tarin kwanjinsa saida ta dan tsorata ta tabbatar da cewa ya cika zarto kuma jarumin maza domin alamar karfi tana ga mai kiba amma a rayuwarta tada da kuma irin gwagwarmayar data sha gami da fafatawa da miliyoyin aljanu sai taji ko kadan bata shakkar komai don haka sai itama ta dunkule hannayenta biyu suka rugo da gudu izuwa kan juna suka kacame da sabon masifaffen fadan hannu ya zamana cewa suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa.Ana fara wannan gumurzu ne mamaki ya kama Aljani Lafwas bisa ganin irin tsananin karfin damtsen Yazirina da kuma juriyarta domin duk irin uban naushin da yake gabza mata a sassan jikinta tana iya shanyesu kuma ta maida masa martani ya zamana cewa suna hadawa kansu jini da majina.Fara wannan gumurzu keda wuya labari yasha bambam domin a lokacin ne hankalin sauran dakarun dake wajen ya DUGUNZUMA ainun suka firgice suka kama boye boye saboda masifar ta fara shafarsu.Saboda duk sa'adda Aljani Lafwas ko Yazirina suka kawo naushi dayansu ya goce duk Aljanin da aka samu saidai kaga ya baje kasa sumamme.Adaidai wannan lokaci ne Mujahid ya farfado daga dogon suman da yayi,koda yaga ana yin wannan masifaffen yaki yaga saman rufin gidanma ya fara runguzowa kasa yana danne Aljanun suna tsira da kyar sai shima ya ruga izuwa karkashin wata rusasshiyar dirkar gini ya buya.Karar rugujewar gidan ce tasa matsafiya Muznaira ta farka daga bacci a dimauce,koda ta jiyo sautin rushewar wani bangare na gidan nata sai ta sauko daga kan gadonta ta debi makamanta tayi girgiza ta bace bat,bata baiyana a ko ina ba sai a can inda ake gumurzun.Koda taga cewa tsakanin Aljani Lafwas da Yazirina akeyin wannan gumurzu kuma alokacin duk su biyun sun dako tsalle sama tamkar daga cikin baka aka cillosu da nufin su yiwa kawunansu gware sai itama Muznaira ta daka tsalle sama da nufin ta shiga tsakiyarsu ta raba fadan.Koda Yazirina ta kyallara ido taga wannan Kambun Sihiri a hannun Muznaira sai ta shammaceta ta sunkui da kanta kasa,ai kuwa sai kan Aljani Lafwas ya gwaru dana matsafiya Muznaira,take Muznaira ta dimauce kuma ta fita haiyacinta sakamakon tsananin zafi da zogin da yaji don hakar saida taga taurarin wuya a idanunta.Damar da Yazirina ta samu kenan ta cisge wannan kambun sihiri daga jikin hannun Muznaira ta diro kasa daidai inda Mujahid uake tasa hannayenta biyu ta sure shi sukayi sama tamkar ta kasance tsuntsuwa mai fukafukai,kawai sai ta naushi nurin sama gidan ya burma suka fice ta cikinsa suka luluka a cikin gajimare suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba.Muznaira da Aljani Lafwas suka diro kasa suna sosa fuskokinsu wadanda ke yoyon jini ta cikin hanci da baki,koda suka watstsake suka dawo cikin hayyacinsu Muznaira ta dubi sama da kasa,gabas da yamma kudu da arewa bataga Yazirina da Mujahid ba sai ta kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa ta dubi Aljani Lafwas tana mai daka masa tsawa tana mai cewa sun sace mini kambuna maza ka bisu ka kwato shi kuma lallai ka kawo mini Yazirina a raye tare da wadannan taswirori guda biyu dake hannunta.Idan har ka sami wannan nasara nayi maka alkawari idan na debo dukiyar mahaifina dake can kogon Taskar Ajali kaine zaka zama wazirina a yayin dana zamo SARAUNIYAR DUNIYA.Koda jin wannan batu sai Aljani Lafwas ya daki kasa da tafin hannunsa yayi sama a cikin tsananin gudu tamkar tafiyar tauraruwa mai wutsiya ya luluka a cikin gajimare. *Acan gidan sarautar Sarki Ubaiyu kuwa kashe gari da sassafe Sarila nata fama shara bacci akan gado tamkar tana cikin tsiribirin Jannatul Duniya sai taji ana tashinta daga bacci tana bude idanunta tayi arba da shugabar wadannan kuyangi tsaye a kanta kawai sai ta dubeta tace ya shugabata ga ruwan wanka can yana jiranki kuma an shirya miki abinci Buda baki,mai girma Boka Matawus yace in gaya miki akwai labari mai dadi don haka yana jiranki a fada.Koda jin wannan batu sai Sarila ta sauko da sauri daga kan gado ta ruga izuwa kewaye kafin kuyangin da zasuyi mata wanka su shigo tuni ta kwabe kayanta ta fada cikin bahon ta fara yiwa kanta wanka don haka da kuyangin suka shigo karasa mata sukayi.Ana gama yi mata wankan ta dauki makamanta na yaki ta ™Abubakar Haleefah Physicist™ daurasu a jikinta bayan ta mayar da asalin kayan da tazo dasu gidan,ba ta yarda an sanya mata wadansu tufafin ba kuma bata tsaya anyi mata wani ado ba amma abinka da kyakkyawa sai gashi kamar ma tayi kwalliyar,ko tsayawa yin buda bakin batayi ba ta durfafi fada.Tana isa fadar kuwa ta iske Boka Matawus a zaune tare da sarkin yaki da kuma dakaru dubu daya a tsaitsaye.Koda Boka Matawus ya hango Sarila ta nufo su sai ya mike tsaye ya tarbeta yana mai risina mata kuma ya gaisheta cikin girmamawa sannan ya dubeta cikin nutsuwa yace,ya shugabata ina mai sanar dake cewa a halin yanzu nasan inda Yazirina take don haka ina so na kai ki wajen domin ki cika burinki na karbar wadannan taswirori guda biyu dake hannunta amma bisa sharadi guda sharadin kuwa shine inason ki daukar mini alkawarin cewa nan birnin Yamein shine zai zama babban birninki na mulkin duniya kuma ni da sarkina zamu zamo manyan fadawanki.Ina mai tabbatar miki da cewa da zarar mun isa inda Yazirina take ni zanyi miki maganin wannan yaro dan baiwa wato Mujahid saboda shi kadai ne zai iya tarwatsa miki dukkan shirinki ya tserar da Yazirina daga hannunki.Koda jin wannan batu sai Sarila tayi shiru tana tunani da nazarin al'amarin har izuwa tsawon yan dakiku daga can sai ta dago kai ta dubi Boka Matawus tace na yarda da wannan sharadi naka kuma na rantse da darajar iyayena zan zamo mai cika alkawari a gareka amma kasan cewa idan muka isa inda Yazirina take ka kasa yi mini maganin Mujahid saina kasheka na kashe Sarki Ubaiyu sannan na baje birnin Yamein yadda har abada ko a tarihi ba za'a sake tunowa da ita ba.Koda jin wannan batu sai hantar cikin Boka Matawus ta kada yaji kamar yace ya janye wannan yarjejeniyar amma daya tuna cewa yana zuwa da wani abu akasin hakan rai zai iya baci sai ya amsa cewa shima ya amince da nata sharadin.Nan take suka dunguma suka fice daga cikin fadar suka iso babban fili na gidan sarautar inda suka iske Sarki Ubaiyu tare da dukkanin fadawansa da sauran mutanen gari a tsaitsaye sunyi jugum jugum Cikin yanayi na jimami da fargaba da tsananin damuwa.Da isowarsu sai Boka Matawus ya iso gaban sarki Ubaiyu ya risina ya gaisheshi a wannan lokaci hannun sarki Ubaiyu a sakale yake kuma a daure da yanki sakamakon raunin da Sarila tayi masa.Nan take Boka Matawus ya kwashe labarin duk abinda ya faru tsakaninsu ya zaiyane masa.Koda sarki Ubaiyu da jama'arsa sukaji sharadin da Sarila ta shimfida sai hankalonsa ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe.Ba tare da bata lokaci ba aka kawo dawakai Boka Matawus,jaruma Sarila da dakaru dubu suka hau suka fice daga cikin gidan sarautar.Fitars u keda wuya sai sarki Ubaiyu ya dubi gaba dayan jama'ar tasa cikin alamun karayar zuciya yace to kunji dai sharadin da Sarila ta gindaya don haka mecece shawarku da kuka yanke?Koda jin wannan tambaya sai gaba dayan yan majalisar suka kama kace nace wasu sukace kawai ayi hijira gaba daya abar birnin ya zamana fanko,wadansu kuwa sai sukace a bari aga dawowar Boka Matawus tunda ana da yakinin cewa duk bala'i ma da zai biyo baya shi zai iya guduwa ya tsira daga sharrin Sarila,haka dai akayi ta kace nace aka rasa hukuncin daya dace a yanke. *Al'amarin Yazirina da Mujahid kuwa lokacin da suka luluka a cikin gajimare suka bace bat basu sake baiyana a ko ina ba sai a tsakiyar wani daji mai ni'ima wanda ke dauke da korama,bishiyoy i da yayan itatuwa iri iri.Koda Mujahid ya bude idanunsa yaga ni'imomin dake cikin wannan daji sai ya ruga izuwa cikin wata korama yana mai cire rigarsa ya fada ciki ya kama wanka.Ita kuwa Yazirina sai ta dauko wannan kambun sihiri na Muznaira daga cikin aljihunta ta kura masa idanu.Take taga hoton Sarila bisa doki tare dasu boka Matawus a sukwane sun durfafo wannan daji da suke ciki kuma dawakan nasu wani irin gudu suke yi mai tsananin karfi na sihiri wanda suna iya shafe tafiyar sa'a guda cikin dakika goma.Koda ganin wannan Al'amari sai hankalin Yazirina ya dugunzuma ainun ta mike tsaye zumbur da nufin ta ruga izuwa inda Mujahid yake domin ta sanar dashi abinda ke shirin afkuwa.Kwatsam sai taga Aljani Lafwas ya diro daga sama tsulum ya dira a gabanta.Saboda nauyinsa saida kasar dajin gaba daya tayi girgiza har wajen daya dira ya loba kamat zai rufta ciki.Babu shiri Yazirina taja da baya kadan ta zare takobinta kuma Lafwas saiya zare takobinsa ya nuna yazirina da ita yace...: Ya nuna Yazirina da ita yace,kina zaton cewa akwai inda zaki iya zuwa ne ki tsare mini a cikin wannan duniya,ina mai shawartarki daki dauko wadannan taswirori guda biyu dake wajenki ki bani na kaiwa uwargida Muznaira wato yar uwarki idan har kinason ki tsira da rayuwarki,in ba haka ba kuwa zan kasheki a banza.Duk wannan bayani da Aljani Lafwas ke fadi Muhajid dake cikin korama ya tsaya cak yana sauraro don haka lokacin da yaji batun Aljani Lafwas na karshe sai ya tari numfashinsa yace,Kai Lafwas kayi babban kuskure har da kake tunanin cewa zaka iya raba Yazirina da wadannan Taswirori guda biyu don kaima ina mai baka shawara da ka cire hannunka daga cikin wannan al'amari domin yafi karfinka.Har Aljani Lafwas ya bude baki zai maidawa Mujahid martani sai Yazirina ta sake tarar numfashinsa tace a yanzu haka ga Sarila anan ta taho nan kuma nan da cikar rabin sa'a zata iso tare da Boka Matawus na birnin Yamein da dakarunsa guda dubu daya.Shin yanzu zamu cigaba da yaki ne nidakai kafin su iso ko kuwa zamu jira ne su iso mu hada karfi da karfe mu yaki Sarila mu kasheta domin mu kwafe taswira ta uku sannan ka kashe ni ka hada taswirori guda ukun ka kaiwa uwargidan naka? Koda jin wannan tambaya sai Aljani Matawus ya kama duru duru ya rasa abinda zaiyi wanda zai fishshe shi haka dai suka yi cirko cirko su duka.Koda Mujahid yaga aljani Lafwas ya kasa yanke hukunci sai ya dubi Yazirina yace kizo kawai mu gudu mubar wajen nan domin idan muka bari Sarila tazo nan ta riske mu tamu ta kare domin wannan karon ba zamu iya tsira daga sharrinta ba saboda nasan cewa Boka Matawus zai iya yin maganina kuma kin sani cewa nine kadai wanda zai iya tserar dake.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta dubi Mujahid cikin alamun tsananin mamaki tace Ashe dai kai ne bakon jarumin da aka tabbatar mini da cewa zaka iya kubutar dani daga sharrin Sarila,shin kai ne dan baiwa mai sa'a da rabo bisa duk abinda yasa a gabansa?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid yace tabbas nine amma dai ki dauki shawarata indai kinason ki tsira da rauwarki.Yaziri na tace ni ban damu da rayuwata ba muddin gudun banza zanyi wanda babu kubuta kuma babu tabbacin tsira.Kai meye yasa bazaka gudu ba tunda kana son ka tsira da rayuwarka? Koda jin wannan batu sai Mujahid ya risina yace abinda yasa banzan gudu na barki ba shine tun a ranar farko dana fara haduwa dake duk da cewa ina matukar tsoranki naji kuma na kuma da tsananin SONKI irin son da nake jin kamar zan iya salwantar da rayuwata domin taki.Saboda haka ni yanzu na zabi na mutu tare dake anan wurin idan kuma zamu tsira to mu tsira tare.Koda jin wannan batu sai Yazirina ta kamu da tsananin mamaki kuma nan take taji ta kamu da tsananin SON Mujahid bata san sa'adda taji kwallar farin ciki ta cika mata idanu ba,saboda Mujahid ne saurayi na farko a duniya wanda ya taba furta mata KALMAR SO gaba da gaba.Kafin Yazirina ta budi baki tace da Mujahid wani abu sai kawai Mujahid yaga wata igiyar tsafi mai kaurin gaske ta kanannade shi daga kasan kafafuwansa har izuwa kan kirjinsa ta daureshi tamau yadda ko motsin kirki ba zai iya ba,kawai sai jiyo sukuwar dawakai sukayi a bayansu suna waigawa sukayi Arba da Sarila,Boka Matawus da dakaru dubu a sukwane sun durfafo kansu kuma tazarar dake tsakaninsu bata wuce taku ashirin ba.Koda ganin hakan sai Aljani Lafwas ya dubi Jaruma Yazirina yace a yanzu mun zama abokai kuma yan uwan juna don haka inason mu hada karfi da karfe ni dake mu yaki Sarila kada ki damu da Boka Matawus da sauran dakarunsa inada maganinsu.Masoy inki dai Mujahid bansan yadda zanyi na iya kwance igiyar data daureshi ba saidai bayan wannan yaki idan mun tsira da rayuwarmu sai mu nemi mafita.Aljani Lafwas na gama fadin hakan sai shida Yazirina suka daka tsalle sama suka kaiwa Sarila mugun hari a lokacin da take bisa dokinta,koda ta hango su a sama sun taho kanta sai ita ma ta daka tsalle sama daga kan dokinta cikin matukar zafin nama ta doki kirazansu suka fado kasa a galabaice suna sosa kirazansu sakamakon mugun zafin da sukaji amma sai suka mike tsaye zumbur a tare suka rike takubbansu da hannayensu biyu suna masu gyara tsayuwarsu.Adai dai wannan lokaci ne ta dubi Aljani Lafwas da Yazirina tayi musu wani dan guntun murmushi sannan tace yanzu ku a tunaninku kuna ganin cewa zaku iya dani ne?To ai shike nan masu iya magana sun ce ba'a kwacewa yaro goruba don haka sai ya gwaguya yaci iya cikinsa duk da cewa bashi da hakori kuma indai babu kasa anan ake gardamar kokawa.Tabbas yanzun nan zan gama daku na cika burina.Kafin Aljani Lafwas ko Yazirina daya daga cikinsu yace wani abu tuni Sarila ta zare takobinta ta daka tsalle sama ta dira a tsakiyarsu sun ruguntsume da azababben yaki,nanfa ita kadai ta zame musu alakakai ta kuntatasu ya zamana cewa da kyar ma suke iya kare hare harenta amma basa iya mai da martani.Hakika mai karfi sai Allah ya isa kuma duk wanda ya riga kwana dole ne ya riga ka tashi,ana fara wannan gumurzu Yazirina da Aljani Lafwas suka raina kanus suka tabbatar da cewa Sarila tafisu karfin damtse gami da iya yaki nesa ba kusa ba domin bambancin a bayyane yake.Shi kuwa Matawus sai ya tafi izuwa inda Mujahid ke tsaye a daure cikin igiyar tsafi ya dube shi ya bushe da dariya sannan yace rana da yawa ta barawo rana daya tak ta mai kaya,yau shekara biyar kenan maigidanka Boka Kausi yana turoka har gidana kana yi mini sata na kasa kamaka amma yau gashi ka fada tarkona a saukake. WAYE ZAI SAMI NASARAR A WANNAN BAKIN GUMURZUN DA AKEYI TSAKANIN SARILA DA SU YAZIRINA? INA LABARIN MANYAN SARAKUNAN DUNIYA KUMA WANE MATAKI SUKA DAUKA AKAN YAZIRINA DA SARILA? YAYA SOYAYYAR YAZIRINA DA MUJAHID ZATA KASANCE? SHIN MUJAHID ZAI TSIRA DAGA SHARRIN BOKA MATAWUS? YAUSHE ZA'A TAFI KOGON TASKAR AJAKI KUMA WAYE ZAI IYA DEBO WANNAN DUKIYA TA MARIGAYI BOKA SALMARA? INA LABARIN BASMA MAHAIFIYAR YAZIRINA? Mu hadu A "Taskar Ajali" Littafi na Hudu don jin cigaban wannan labari.TASKAR AJALI Littafi na Uku Na Abdulaziz sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI Littafi na Uku Na Abdulaziz sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya

Chapter 5 of 14