Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka sai ya ga jini bai daina tsatstsafowa ba kuma har a sannan Sarila bata farfadowa ba.Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Jarumi Darusi kenan ya kasa zaune ko tsaye ya rinka kai kawo yana tunanin abinda ya kamata yayi.Koda ganin haka sai Mujahid ya dubi Darusi a fusace yace saboda me mu ba zaka zo ka taimake mu ba alhalin kana ganin cewa duk mu biyun mun sami karaya a jikinmu kuma jikinmu ya bugu sosai ba zamu iya yiwa kanmu komai ba.Koda dai ka kamu da son Sarila ne shi yasa ka dimauce haka?Koda jin wannan batu sai jarumi Darusi ya fusata ainun ya dakawa Mujahid tsawa yana mai cewa baka da hankali ne ko kuwa baka ganin halin da take ciki ne?Duk ku biyun kuna cikin haiyacinku ita kuwa bamu san ma halin da take ciki ba,shin ka manta ne cewa nayi alkawarin zan ceci rayuwarku a duk sa'adda kuka kasa ceton kanku.Koda gama fadin haka sai jarumi Darusi ya koma kan Sarila ya tofa mata wata addua'a akan raunin,faruwar hakan keda wuya sai jini ya daina tsatstsafowa daga cikin raunin amma kuma da Darusi ya dubi yadda take sai hankalinsa ya dugunzuma ainun saboda ya fahimci cewar jini mai yawa ya zuba a jikinta.Mafi akasarin mutanen da suka rasa jini mai yawa haka a jikinsu mutuwa sukeyi kuma koda sun rayu sai an basu kyakyawar kulawa kuma sai sunyi jinya ta dan lokaci sannan zasu sami cikakkiyar lafiya gami da kwarin jiki.Jim!Kadan da tofawa Sarila wannan addu'a saita farfado daga dogon suman da tayi tana mai jan dogon numfashi gami da bude idanu a hankali da farko cikin dishi dishi taga jarumi Darusi tsugune a gabanta kuma fuskarsa a rufe idanunsa kadai ne a waje,sannu a hankai idanun nata suka washe amma sai taji kanta da sauran gangar jikin nata sunyi mata nauyi ainu ko motsin kirki ba zata iyayi ba.Da kyar ta juya da kan nata ta dubi inda Yazirina da Mujahid suke,kawai sai taga kafar Yazirina a karye har ta dan fara kumbura shi kuma Mujahid hannunsa ne a karye kuma dukkaninsu akwai alamun tsananin jigata a tare dasu.Sarila ta dago hannunta da kyar ta shafi raunin nata koda ta jishi a dinke har an shafa masa magani sai ta dubi Darusi tayi masa dan guntun murmushi a karon farko tunda suka hadu tace ina godiya a gareka bisa ceto rayuwata da kayi.Koda jin haka sai Darusi yace ki gafarceni lalura tasa na taba jikinki domin yi miki maganin.Sarila ta sake yin murmushi tace nayi farinciki daya kasance addininka bai hanaka taimako ba a irin wannan domin da tuni yanzu na dade da zama gawa.Darusi yayi murmushi yace ai addinina yana da adalci kuma baya son zalunci,na sani cewa ba zaki iyayin komai ba yanzu da kanki don haka in Allah ya yarda zan cigaba da taimakonki har izuwa lokacin da zaki sami lafiya.Yanzu zanje na taimaki sauran yan uwan naki. HALEEFAH A ABUBAKAR Yanzu zanje na taimaki sauran yan uwan naki.Koda gama fadin haka sai Jarumi Darusi ya mike tsaye ya tafi inda Yazirina ke kwance ya shiga gyara mata karayar dake kwaurin kafarta.Nan da nan cikin kankanin lokaci ya daure kafar da karare ya shafa mata wani magani na musamman sannan ita ma ya tofa mata addu'a daga nan sai kuma ya mike tsaye ya koma kan Mujahid yayi masa duk irin taimakon da yayiwa Sarila da Yazirina.Bayan ya gama yi masa komai tsaf sai ya dubeshi yace dazu kace naki na taimake ku na taimaki Sarila har kana cewa ko na kamu da sonta ne ko?To yanzu kuma me zaka ce tunda gashi nayi muku duk irin taimakon da nayi mata kuma ka gane cewa na fara taimakonta ne saboda halin data shiga yafi naku hadari.Koda Darusi yazo nan a zancensa sai kunya ta kama Mujahid ya dan sunkui da kansa kas yana sosa keya yace ka gafarceni yakai JARUMIN JARUMAI hakika zargina kawai yasa na fadi haka.Dajin haka sai Darusi ya mike tsaye daga gaban Mujahid ya juya masa baya sannan yace a addinina zargi haramunne koda ya zamana gaskiya don haka sai ka kiyaye.Darusi ya dubi Sarila,Yazirina sannan ya juya ya sake duban Mujahid yace duk ku ukun ba zaku iya cigaba da tafiya ba a cikin halon da kuke ciki yanzu.A kallah sai kunyi jinya ta kwanaki ashirin kunga kenan kwanakin tafiyarmu sun karu.Koda jin wannan batu sai hankalinsu Sarila,Yazirina da Muhajid ya dugunzuma ainun,Sarila ta dubi Darusi ta budi baki cikin matakuar karfin hali tace yakai wannan GWARZON JARUMI yanzu babu yadda za'ayi mu cigaba da tafiyar nan a haka in yaso mu cigaba da jinyar jikinmu akan hanya.Ka sani cewa zamanmu a waje daya yana da matukar hadari saboda duk sa'adda ka gusa daga kusa damu masu farautarmu zasu iya baiyana su kashe mu domin su rabamu da taswirar zuwa kogon Taskar Ajali.Koda Sarila tazo nan a jawabinta sai Jarumi Darusi yayi murmushi yace da izinin Allah babu abinda zai sameku a tsawon zaman da zamuyi,inaso ku tuna cewa a halin yanzu fa doki daya ne jal daya rage mana tunda Aljana Marwisa ta kashe naku dawakan.Ta yaya zamu cigaba da tafiyar da doki daya kuma a cikin yanayin da kuke musamman ma Sarila wacce ko zama akan dokin ba zata iya ba,ko zata iya fara zama sai nan da cikar kwana bakwai kuma ko ta fara zama ba zata juri dadewar zaman ba a kan doki.Koda jin wannan batu sai duk su ukun suka jinjina kai alamar cewa sun gamsu da abinda ya fada amma sai Sarila ta kuma budar baki tace na amince muyi kwanaki bakwai muna jinya a nan.A ranar kwana na bakwai ni da Yazirina sai mu hau dokinka,Mujahid a matsayinsa na wanda ya karye a hannu zai iya taka kafarsa yayi tafiya kaima haka,idan kun gaji da tafiyar kafa zamu iya tsayawa ku huta sannan mu cigaba da tafiya hankalinmu zaifi kwanciya idan ka amince da wannan tsari dana zo maka dashi.Koda jin wannan batu sai Jarumi Darusi ya kawo gwauron numfashi ya ajiye sannan yace hakika wannan shawara da kika zo da ita zata yiwu to amma kuma akwai yan matsalolin da zamu iya fuskanta wadanda zasu zamo tamkar munyi gudun gara ne mun tarar da zago.Caraf sai Yazirina ta tari numfashinsa tace babu matsala zamu iya jurar duk irin matsalar da muke fuskanta.Dajin haka sai Darusi ya gyada kai yace shikenan tunda kun aminta da hakan,yanzu abu na farko da zamuyi shine mu dauke gawar wannan Aljana mu kaita can nesa mu kone ta yadda warinta ba zai dame mu ba koya dami sauran halittun dake cikin dajin nan.Bayan nan kuma sai mu shiga cikin wannan kogon dutse na wannan Aljana mu caje shi mu tabbatar da cewar babu wani mugun abu a cikinsa domin mu zauna acikinsa.Koda jin wannan batu sai Sarila tace to yanzu in banda abinka ta yaya mu da muke a nakasce zamu iya tayaka wannan aiki?Darusi yayi murmushi yace ai dama ba cewa nayi sai kunsa hannu ba a cikin wannan aiki,kawai dai ina sanar daku ne yadda ya kamata ayi.Gama fadin hakan keda wuya sai Darusi yaje ya dauko wata doguwar igiya a cikin jakar guzurinsa wacce matafiya ke amfani da ita wajen hawa duwatsu da tsaunika masu tsawo ya hada gawarwakin dawakan a waje guda gami da gawar Aljana Marwisa ya daure su tamau kawai sai ya kama igiyar da hannu daya yaja gawarwakin duka a kas ya nufi wani bangaren daban na dajin.Yana cikin tafiya ne ya tsaya cak kawai sai ya dawo da baya ya baro mushen gawarwakin acan gaba yazo gaban su Sarila ya tofa wata addu'a sannan ya dube su yace kada dayanku ya kuskura ya ketare nan inda kuke.Koda gama fadin hakan saiya juya yaje ya cigaba dajan mushen su kuwa su Mujahid sai suka bishi da kallo kawai cikin tsananin mamaki har saida ya kauce,ba komai ne ya basu mamaki ba face ganin irin tsananin KARFIN DAMTSEn sa sun sami cewa inda zasu taru duk su ukun ma ba zasu iya jan gawarwakin ba uku a kasa saidai da karfin sihirin tsafi amma gashi Darusi ya hada har dama gawar Aljana Marwisa wacce nauyinta ita kadai ya ninka na doki guda sau uku.Nanfa sukayi ta Al'ajabi suna tattaunawa akan al'amarin inda Yazirina ta dubi Mujahid tace kai waishin anya kuwa Darusi mutum be kamar mu dinnan?Koda jin wannan tambaya sai Mujahid ya bushe da dariya yace tabbas Darusi mutum ne kamar mu yana ci yana sha kuma yanayi duk irin bukatar da mukeyi,idan yaji ciwo jini na fita a jikinsa,idan ciwo ya kama shi sai yayi jinya,to menene bambancinmu dashi?Bambanci shine yana da baiwa ta matukar karfin damtse,Addininsa ba irin namu bane,yana da matukar hakuri gami da jurewa wahala komai tsananinta domin cika burinsa,ban taba haduwa da mutumin daya burgeni ba kamarsa.Koda Mujahid yazo nan a zancensa sai Sarila da Yazirina suka kamu da tsananin mamakinsa. 5 hours ago Abubakar Haleefah Physicist Yazirina ta dubeshi tace idan har Darusi yana burgeka hakan na nufin cewa zaka iya yin imani da addininsa haka ne?Mujahid yayi murmushi yace wannan tambaya ba akaina ni kadai take ba,tana kanmu duk mu ukun nan nina tabbatar da cewa kuma Darusi yana burgeku.Koda kuwa kun tsane shi a cikin zukatanku amma na sani cewa da sannu za kuji kuna sonsa kafin mu kare wannan tafiya.Akwai abu guda dazai faru yasa dukkaninmu muyi amanna dashi.Koda jin wannan batu sai Sarila da Yazirina suka dubi Mujahid,cikin mamaki Sarila ta budi baki da kyar tace menene wannan abu dazai faru wanda zai sa na kaunaci wannan shashashan jarumi?Ka sani cewa na tsaneshi kamar yadda na tsani mutuwa ta duk da cewa ya cece rayuwata ni kawai inayin wannan tafiya ne tare dashi bisa larura saboda yana da matukar amfani a garemu.Sa'adda Mujahid yaji wannan batu na Sarila sai ya gyada kai yace ba zan gaya miki abinda zakiyi ki kaunaci Jarumi Darusi ba,anan gaba kuma ina mai shawartarki daki boye kiyayyarki a gareshi kuma kiyi kokari ki saisaita zuciyarki a kan kinsa saboda tsananta KIYAYYA ko SOYAYYA abu ne mai hadari a rayuwa saboda makiyi kan iya zama masoyi kuma masoui kan iya zama makiyi.Koda Gama fadin hakan sai Mujahid ya mike tsaye yaje inda dokin Darusi yake ya dauko battar ruwa ya bude ya kurba sau biyu sannan ya juya ya dubi Yazirina cikin murmushi yace kina da bukatar ruwan ne?Yazirina tayi murmushi tace ina bukata mana.Mujahid ya nufi inda Yazirina ke zauna domin ya bata ruwa tasha amma sai Sarila ta kira sunansa tace ni laifin me nayi maka da bzakayi mini tayin ruwan ba?Ka sani cewa ko don doguwar tafiyar da muka sha kafin muzo nan da kuma bakin gumurzun da muka sha da Aljana Marwisa dole ne kowannenmu yaji kishirwa,idan kuma son da kake yiwa Yazirina yafi wanda kakeyi yi min ne saika fara bata ruwan tasha na gani.Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Mujahid ya kasa gane abinda take nufi,shidai ya sani cewa tsakanin ita da Yazirina babu wacce ya furtawa KALMAR SO a fili amma kuma ya fuskanci cewar kowaccensu tana sonsa amma a badini cikin zuciyarsa hankalinsa yafi karkata izuwa kan YAZIRINA saboda yana matukartsoron Sarila bisa ganin irin tsantsar rashin imaninta da yadda ta mauar da rayukan bil'adama tamkar na kiyashi.Mujahid ya tsaya yana duru duru ya rasa wacce zai kaiwa battar ruwan yayin da yake ruke da battar da lafiyayyen hannunsa,daya hannun nasa kuwa Sa'adda Darusi ya gyara masa karayar ya rataye shi bisa wuyansa da wani farin kyalle mai kwari.Mujahid na cikin wannan hali ne suka jiyo sukuwar dawakai da yawa an durfafo bakin wannan kogon dutse daga can nesa.Nan take duk su ukun suka dimauce hankalinsu ya DUGUNZUMA ainu Mujahid ya rasa abinda ya kamata yayi har ya yunkura zai ruga izuwa gaba ya barsu Yazirina a wajen sai Yazirina ta daka masa tsawa ta dubeshi da idanunta da suka ciko da kwallah tace Kai!Mujahid ashe dama zaka iya guduwa ka barni yayin da kaga masifa?Ni a tunani na kana sona kamar yadda na kamu da tsananin sonka na zaci cewa zaka iya sallama rayuwarka domin ceto tawa tamkar yadda zan iya sallama tawa don taka.To ka sani cewa tsayuwarka anan ne kadai zaisa ka tsira da rayuwarka amma idan kayi taku daya gaba mutuwa zakayi tunda Jarumi Darusi ya gargademu akan hakan,idan ka manta ne yanzu na tuna maka kaga kenan na ceci rayuwarka.Yanzu nike binka bashi a rayuwa ba zan sake yarda da kai ba har abada face ka biyani wannan bashi da nake ninka wato ka ceci rayuwata.Koda jin wannan batu sai Sarila taji wani irin mugun KISHI ya turnuketa har ta bude baki zata ce wani abu saiga rundunar mayaka ta iso daf da bakin kogon dutsen.A kalla mayakan sun kai su Dubu Dari Hudu kuma dukkaninsu a cikin gagarumar shigar yaki suke dauke da muggan MAKAMAN YAKI a gabansu mutum hudu ne mafiya kwarjini.KALLO DAYA zakayi musu ka gane cewa SARAKAI ne saboda yanayin shigarsu da kuma kayan yakin nasu irin na sarakai.Uku daga cikin sarakan fitattu ne a nahiyar,daya kuwa bakon sarki ne daga wata nahiyar daban kuma duk ya fiso girman kwarjini gami da kira irin ta manyan SADAUKAI.Da kira irin ta Manyan Sadaukai.Da isowar wannan runduna sai suka ja linzamin dawakansu sukayi cirko cirko suka kurawa su Yazirina idanu yayin da kurar dawakan su ta fara lafawa,bayan kurar ta lafa sai bakon sarkin ya dubi Sarila da Yazirina ya bushe da mahaukaciyar dariyar mugunta sannan ya murtuke fuskarsa tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace yanzu gashi a karon banza mun sami tsuntsu daga sama gasasshe,kun gama yakar junanku kunyi hadin kan dole domin kuje ku malli dukiyar dake can taskar Ajali amma ga iya inda gudunku ya kare ba tare da mun sha wahalar komai ba zamu kashe ku mu dauke taswirorin dake tare daku tunda abin dogaron naku Jarumi Darusi baya nan bare ya baku kariya.Ku sani cewa nine Sarki Damshan na birnin Damashkar a halin nine shugaban sarakuna uku na nahiyarku dake tare dani domin sunyi muba'aya a gareni,ina mai tabbatar muku da cewa duk duniya babu wani matsafi daya kaini karfin sihirin tsafi,nasan komai akan dukiyar taskar ajali kuma duk abinda ya faru tsakaninku da wannan bakon jarumi na gani a cikin madubin tsafina,yanzu kuna da zabi biyu ko dai kuyi mubaya'a a gareni ku bani wadannan taswirori guda uku cikin ruwan sanyi ko kuma na kashe ku na kwace taswirorin da karfin tsiya.Koda Sarki Damshan yazo nan a zancensa sai kawai yaji Sarila ta bushe da dariya cikin tsananin karfin hali duk da cewa a kwance take tana jin matsanancin zafi da zugi a jikinta.Dafa can sai ta karkato da kanta da kyar ta dubi sarki Damshan ya budi baki tace yakai wannan sarki kayi sani cewa kamar yadda wannan duniya take da fadi haka ma abin cikinta yake da yawan gaske.Komai sammakonka wani a tafe ya kwana,komai nisan gari akwai wani a gabansa,idan ka gane abinda nake nufi kome kake takama dashi sai an sami wanda ya fika bisa ganin yadda aka raine ni a cikin tsumin tsafi kuma aka bani gagarumin horon yaki dazai iya fafatawa dani ba ya kaini kas,amma dana hadu da wannan bakon jarumi sai na raina kaina alhalin da ina ganin kamar zan iya aza gammo a kaina nayi dakon duniyar gaba daya.Kamar yadda ka bamu zafi guda biyu nima yanzu na baka zabi biyun kodai ku gudu kaida mukarrabanka domin ku ceci rayuwarku kafin jarumi Darusi ya dawo nan ko kuma ku jarraba karbar wadannan taswiroro guda uku daga hannunmu wanda hakan bazai taba yiyuwa ba.Koda jin wannan batu sai Sarki Damnashi ya fusata ainun take zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone kawai sai ya dubi dakarun dake bayansa yace kuyi musu ruwan kibiyoyi.Nan take dakarun suka zazzaro kibiyoyi suka dana akan baka kowa ya tabe bakan nasa ya saki harbi.Wohoho!Ha kika abin al'ajabi baya karewa a cikin wannan dubiya,koda dubunnan dakarun suka harbo kibiyoyin su sai kibiyoyin suka tsaya cak a gaban su Yazirina a sama su basu cake su ba kuma basu fadi kasa ba.Koda ganin haka sai Sarki Damnash ya fara amfani da karfin sihirinsa da hannayensa ya rinka motsa kibiyoyin domin suje su cake su Sarila amma sai kibiyoyin suka jiyo da baya da gudu tamkar sannan aka harbo su daga cikin bakan suka je suka cake gaba dayan dakarun da suka harbo su da farko.Nan take gaba dayan dakarun suka fado kasa matattu daga kan dawakansu.Sai sarakunan uku suka firgita ainun suka dimauce nan take suka kada linzamin dawakansu suka juya da baya da gudu suka runtuma izuwa cikin daji suna yiwa dawakansu kaimi domin su tsira da rayuwarsu suka bar sarki Damnash shi kadai a tsaye zuciyarsa a kekashe ko alamar tsoro babu akan fuskarsa duk da ganin abinda ya faru,fuskarsa ce kawai ta cigaba da yatsinewa zuciyarsa na cigaba da tafarfasa kamar zata kone.Adaidai wannan lokaci ne suka hango Jarumi Darusi ya durfafo su a guje yana ruke da takobinsa tsirara,ba komai ne yasa Darusi ya zare takobinsa ba ya rugo da gudu face hango dubban daruruwan dawakai daga can nesa amma koda ya matsa kusa sai yaga ashe gaba daya mahayan dawakan sun zube kasa matattu saura mutum daya jal a tsaye a wajen sai ya daina gudu kuma ya mayar da takobinsa cikin kufenta.Koda ganin haka sai Sarki Damnash ya saulo daga kan dokinsa ya rike kugu yana mai fuskantar jarumi Darusi yana jiran isowarsa.Da isowar Jarumi Darusi ya zamana cewa tazarar dake tsakaninsu da sarki Damnash bata wuce taku biyar ba sai ya tsaya cak suka kurawa junansu idanu.Kawai sai sarki Damnash ya bushe da dariya bayan yayiwa Darusi kallon raini da wulakanci,lokac i guda kuma saiya murtuke fuskarsa yace yakai wannan wawan jarumi kayi sani cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane.A halin yanzu duk fadin duniya babu wani jarumi daya fini KARFIN DAMTSE,iya yaki da kuma karfin sihirin tsafi,idan ka isa kazo mu fafata da zallan karfin damtsenmu da iya yakinmu.Na rantse da girman iyayena bazanyi amfani da karfin sihirin tsafi na ba kai ma ka rantse da girman iyayenka cewa ba zaka yi amfani da karfin sihirinka ba yanzun nan cikin dakiku kadan zan kashe ka.Na rushe burinka na son yada addininka a wannan nahiya gaba daya sannan na kashe wadancan matan na dauke taswirorin dake hannunsu guda uku naje na mallaki taskar ajaki na zamo SARKITa gaban kwatance.Tunda Darusi yake karo da mazaje bai taba haduwa da zarton jarumi mai zafin nama,karfin sara da nauyi ba tamkar sarki Damnash domin suna fara yin wannan gumurzu ne ya gane cewa lallai yaufa ya gamu da gamonsa,amma saboda karfin imaninsa da dogaro da Allah ko kadan zuciyarsa bata karaya ba.Sarila,Yazirina da Mujahid kuwa ko da sukaga irin salon yakin sarki Damnash kuma sukaga yadda yake neman kuntatawa jarumi Darusi sai hankalinsu ya dugunzuma ainun suka fara tunanin cewa lallai wannan takadirin sarki zai iya samun nasara akan jarumi Darusi kuma da zarar ya gama dashi suma tasu ta kare.Nanfa zuciyoyinsu suka karaya suka kamu da tsananin bakin ciki gami da karayar zuciya suka fara tunanin cewa dukkan burinsu na duniya ya rushe.Babban abinda ya daga musu hankali shine koda aka sami kusan rabin sa'a anayin wannan bakin gumurzun sai ya zamana cewa da kyar jarumi Darusi ke iya kare hare haren sarki Damnash kuma ko kadan baya iya mayar masa da martani saboda ya fara gajiya,shi kuwa sarki Damnash kamar ma a sannan ya fara gumurzun.Anan cikin haka ne sarki Damnash ya shammaci Jarumi Darusi ya daka tsalle sama ya kawo masa wani wawan sara a kafada.Darusi yayi amfani da hannayensa biyu ruke da takobi ya kare saran amma saboda karfin saran da nauyinsa saida kaifin takobin ya dira akan kafadar tasa ya yanke shi.Take jini yayi tsartuwa,Darusi bai san sa'adda ya kwala kabbara ba sakamakon tsananin zafin zogin da yaji amma sai shima ya yunkura cikin shammace ya daka tsalle sama ta gabzawa Damnash duka da kafarsa a fuska.Saboda karfin dukan saida Damnash yayi katantanwa a tsaye sau biyu amma saiya tsaya cak ba tare daya fadi ba saboda tsananin jarumtaka.Koda Damnashi yaji danshi a kan lebensa ya shafa yafa ashe jini ya fito sakamakon bugun da Darusi yayi masa sai ya kamu da tsananin takaici ya kurma uban ihu a karo na biyu sannan ya dubi Jarumi Darusi yace kaine Jarumi na farko daya taba samun nasarar fitar da jini a jikina,tabbas daga yau ba zaka sake samin irin wannan damar ba kuma yanzu take zan maishe dakai tarihin da ko a labari ba za'a sake tunowa dakai ba.Darusi yace ni kuma yanzun nan da izinin ubangijina zan bar maka shaidar da saidai a binneka da ita a kabarinka kamar yadda za'a binne tarihin daukakarka da jarumtakarka.Kafin Darusi ya gama fadin abin dake bakinsa tuni Sarki Damnash ya fara ja da baya.Koda ganin haka sai shima Jarumi Darusi ya fara ja da bayan yana kirga takun da Damnash keyi har saida kowannensu ya kurawa abokin gwamin idanu suna tunani da nazari akan abinda zasuyi su sami nasarar hallaka juna.Duk wannan abu dake faruwa Mujahid,Sarila da Yazirina sun zuba idanu suna kallo cikin tsananin tsoro da fargaba.Kamar hadin baki sai Jarumi Darusi da sarki Damnash suka daga takubbansu sama a lokaci guda kuma suka rugo da gudu izuwa kan juna.Koda ya rage saura taku uku kacal su hadu sai kowannensu ya daka tsalle sama ya kaiwa dan uwansa mugun hari.A tare suka diro kasa suna masu juyawa juna baya amma sai su Muhajid sukaga Darusi da Sarki Damnash sun kame cak kamar gumaka kowannensu akwai jini a jikin takobinsa amma kuma a sasssan jikinsu ba'a ga digon jini ba.Tsawon yan dakiku kimanin goma suna tsaye a kame kawai kuma sai akaga hannun sarki Damnash na hagu ya tsinke ya fadi kasa jini ya kama zuba daga cikin dungulmin hannu amma saboda tsananin juriya da jarumtaka sai sarki Damnash ya sunkuya ya dauki yankakken hannun nasa ya kura masa idanu yana mai tsananin mamaki da takaicin yadda akayi jarumi Darusi ya sami nasarar sare masa hannu.Shi kuwa Jarumi Darusi sai gani akayi ya dafe gefan cikinsa bangaren dama jini na zuba kuma ya durkushe kasa bisa guiwoyinsa amma saiya yunkura cikin jarumta ya mike tsaye yaje inda dokinsa yake yana layi kamar zai sake faduwa,a haka ya bude jakar guzurinsa ya dauko zare da allura ya kama dinke raunin dake gefen cikin nasa da kansa.Har ya kammala dinke raunin Sarki Damnash na tsaye ruke da yankakken hannunsa yana kallon hannun yana dukan kansa tamkar mahaukaci sabon kamuwa.Kuma yana cizon lebensa saboda tsananin takaici da bakin ciki.Daga can kuma saiya takarkare ya kwarara uban ihu,ihun nasa ya cika dajin gaba daya da amsa kuwwa ya firgita duk wani abu mai rai dake cikinsa. Mu Hadu A ''Taskar Ajali' Littafi Na Shida(6) domin jin cigaban wannan kasaitaccen kayataccen labari. TASKAR AJALI 5 Littafi na biyar 5 Na Abdulaziz Sani m gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com TASKAR AJALI Littafi na Shida 6 Littafin Abdulaziz Sani m gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyartar shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com Sannu a hankali kuma sai ihun nasa ya rikide ya koma kuka,idanunsa na zubar da hawaye shabe shabe,adaidai wannan lokaci ne Jarumi Darusi ya karanta wata addu'a ya tofa akan raunin da sarki Damnash yayi masa sannan ya mike tsaye daga durkusan da yayi bisa guiwoyinsa ya goge jini Damnashi dake jikin takobinsa a kasa cikin yashi sannan ya mayar da takobin cikin kufenta ya daga kai ya dubi sarki Damnash yace,tabbas ka cika Gwarzon Mayaki kuma gawurtaccen jarumi da bazan taba mantawa da biwarka ta jarumta ba,amma ka tafi da yankakken hannunka izuwa birninka idan tsafinka zai iya dinke maka hannun ya koma daidai kamar yadda yake da to sai yayi idan kuma bazai iya ba to lallai da dungulmin hannu guda za'a binneka cikin kabarinka kamar yadda nayi alkawari,kaga kenan na dakusar da dukkan daukakar ka da kuma shahararka ta jarumtaka a yanzu cikin kankanin lokaci bisa taimakon ubangijina.Koda gama fadin hakan sai Jarumi Darusi ya karasa inda Sarila ke kwance a kas ya sunkuya ya dauketa ya goyata a bayansa sannan ya dubi Yazirina da Mujahid yace ku tashi mu shiga cikin kogon dutsen nan mu kwanta domin dukkaninmu muna bukatar muyi jinya amma wancan sarkin mai yankakken hannu a yanzu ya fimu bukatar agajin gaggawa indai yana son ya rayu dole ne ya gaggauta tsayar da jinin dake zuba a dungulminsa.Koda gama fadin hakan sai Darusi ya juya ya kunna kai izuwa cikin kogon dutsen goye da Sarila ba tare da tsoron komai ba duk da cewa kuwa basu caje kogon dutsen ba sun tabbatar da lafiyarsa.Cikin hanzari Yazirina da Mujahid suka yunkura cikin matukar karfin hali suka mike tsaye suka ruke kafadun junansu suka taka Yazirina na dingisa kafa suka bi Darusi a baya izuwa cikin kogon dutsen suka kule.Sai bayan kulewar tasu ne sarki Damnash yaji ya fara jin jiri kuma ya kama yin layi daga tsaye saboda jininsa dake zuba nan take ya sake kurma ihu wanda yafi na farko kara da tsoratarwa sannan yayi sauri ya yagi kasan rigarsa ya daure dungulmin hannun nasa ya nannadeshi don tsaida jini,kawai sai ya ruga izuwa kan dokinsa yai tsalle daya ya haye kan dokin ya zunguri cikin dokin da kafafunsa,dokin ya zabureshi da gudu da baya,lafiyayyen hannunsa na ruke da yankakken kuma ya cigaba da kwarar ihu tamkar wanda ake sara a sannan.Kamar yadda Jarumi Darusi ya fada haka al'amarin ya kasance wato saida suka shafe kwanaki bakwai a cikin wannan kogon dutse suna jinyar jikinsu amma a cikin kwanaki biyu rak raunin Jarumi Darusi ya warke sumul tamkar ma bai taba yi saidai tabo wajen kawai.A tsawon kwanakin bakwai Darusi ne ke ta fama yin hidima ga Sarila domin shi ke bata abinci da baki har ta koshi sannan ya goge mata maikon bakin,idan zata kawar da wata bukata sai ya bata wuri ta kawar da bukatar idan ta gama zata kwala masa kira ya dawo ya dauketa ya sake goyata ya mayar da ita cikin kogon dutsen.Abinda baya yi mata kawai shine sauyin tufafin jikinta wannan Yazirina ce keyi mata duk da cewa ita ma tana da karaya a kafarta.Mujahid da Yazirina sunyi matukar mamaki bisa ganin yadda Jarumi Darusi ya rinka dawainiya da Sarila tamkar yar uwarsa ta jini,alhalin ita ko kadan bata sonsa a cikin zuciyarta.Duk tsawon wannan lokaci babu wanda yaga fuskar Jarumi Darusi a cikinsu bare yaga irin kamanninsa ko

Chapter 8 of 14