Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TASKAR AJALI 1 Littafi na daya 1 Na Abdulaziz Sani M gini Ebook creat by Shuraih Usman Ebook publish by www.hausaebooks.cf Ebook din nan yazo maku ne daga shafin www.hausaebooks.cf Kuna ziyarci shafinmu don samun sababbin littatafai Ga duk wanda ke bukatar ebooks nashi ya samu shiga cikin wepsite namu sai ya turo mana da littafin ta Email namu hausaebooks@gmail.com [2BUDUWARCE 'yar kimanin shekaru goma sha tara,ma'abociyar kyawu irin wanda a ganin farko zata ruda dukkan 'da namiji dayayi arba da ita musamman a cikin irin wannan shiga da tayi ta ratso tsakiyar kasuwa.Riga da wando ne na fatar damisa matsatstsu ta sanya wadanda suka baiyana dukkan kyakyawar siffar jikinta,kuma a bayanta ta ratayi wata zabgegiyar takobi.Kallo daya zaka yiwa wannan budurwa ka tabbar da cewa jaruma ce domin tana da kira irin ta sadaukai.Ta daure dogon gashin kanya mai kyalkyali ya zuba a bayan kafadarta har bisa mazaunanta.Tsananin kyawunta da kwarjinita ne yasa gaba dayan jama'ar dake cikin kasuwar suka tsayar da harkokinsu suka zuba mata na mujiya kai wasu ma yan kasuwar basu san sa'adda suka rinka tsallake hajarsu ba suka rinka binta a baya domin ta tafi da imaninsu.Bawai maza ba hatta mata masu siye da masu siyarwa watsar da komai sukayi suka rinka bin wannan bakuwar budurwa a baya don kawai su san ko ita wacece da kuma abinda ya kawo ta cikin wannan kasuwa.Dama a guje wannan budurwar ta fado cikin kasuwar sannan ta tsaya cak ta dubi gabas da yamma kudu da arewa ga dukkan alamu dai wani ko wata ta biyo a fusace tane neman inda ta shiga amma bata gani ba,don haka sai ta sake nausawa cikin kasuwar da sauri ta rinka leke cikin rumfuna da lunguna lunguna na cikin kasuwar.Dukka da cewar taga jama'a sun biyo bayanta da yawa ko kada bata damu ba,itadai kokarinta shine taga wanda take nema ruwa a jallo amma ko alamunsa bata gani ba.Al'amarin daya dugunzuma hankalinta kenan.Koda taga ta karade kasuwar gaba dayanta har tsawon kusan sa'a daya da rabi ba labari kuma jama'a sunyi cincirindi a bayanta sai ranta ya baci ainun bata san sa'adda ta yunkura ba ta kurma uban ihu mai tsananin firgitarwa tane mai zare takobinta.Kafin kace wani abu tuni an tattake kayayyakin jama'a tamkar yaki akeyi kuma kowa ya watse kasuwar tayi tsit tamkar mutuwa ce ta gifta.Tsananin shirun daya wanzu ne yasa jarumar ta jiyo sautin numfashin mutum a cikin wani dogon durum na karfe wanda ke cike da ruwa.Saidai wannan ruwan durum ruwane na kazanta wanda ake wanke kwanukan abinci dashi a kusa da rumfar da ake siyar da abinci.Koda jarumar ta jiyo numfashin mutum a cikin wannan darum sai ta daka tsalle sama ta dira akan durum din tana mai raba kafafunta a kansa duk da cewar bakin durum din siriri ne matuka amma ko girgidin faduwa batayi ba.Kawai sai ta sunkuya ta tsoma hannunta cikin ruwan take taji ta kama gashin mutum ai kuwa sai ta fincikoshi sama ya na kwala ihu sakamakon tsananin zafi da zugin da yaji.Take ta kwalashi a kas yana jike sharkaf ya sake kurma ihu a lokacin yaji kamar kashin bayansa ya karye ba wani bane face matashin saurayi dan kyakyawa wanda shekarunsa bazasu haura ashirin da uku ba.Koda wannan saurayi yaga wannan jaruma ta dirfafoshi rike da takobi tsirara sai ya zube kasa a gabanta ya kama tuba yana cewa tayi masa rai.A lokacin da jikinsa ya kama kyarma a daidai wannan lokaci ne mutanen kasuwar suka fara dawowa,nan da nan suka taru wajen sukayi musu kawanya suna kallon abinda ke faruwa cikin al'ajabi.Budurwar ma'abociyar kwarjini ta iso daf da saurayin ta dora kaifin takobinta akan wuyansa take gumi ya karyowa saurayin sa'adda yaji kamar ya saki fitsari a wandonsa sannan ta dubeshi tace,ina abinda ka sata a cikin jakar guzurina?Jikin saurayin na kyarma ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya fiddo wata guntuwar jemammiyar fata wacce ke nannade yamika mata.Cikin hanzari budurwar ta amshe ta bude jakar guzurinta tasa a cikin sannan ta cire kaifin takobinta daga kan wuyan saurayin koda ganin haka sai saurayin yayi doguwar ajiyar zuciya kuma fuskarsa ta fadada da murmushin murna bisa ganin cewa jarumar ta kyaleshi bata kashe shi ba kawai sai ya mike tsaye zumbur ya juya da baya ya falfala da gudu izuwa wani bangaren daban na kasuwar yana cikin gudu ne yaga wannan budurwa jaruma tsulum a gabansa cikin tsananin kaduwa yayi tirjiya a gabanta ya dubeta cikin alamun tsananin tsoro yace,tundai na baki abinda na satar miki kiyi mini rai don girman iyayenki kada ki kashe ni.Koda jin haka sai jarumar tayi masa murmushi lokaci guda kuma ta murtuke fuskarta tace,ba kasheka zanyi ba amma dole ne ka amsa wadansu tambayoyi daga gareni tunda kana biye dani tun daga birnin Misra har izuwa nan birnin Yamein,kasashe uku muka ketare ta cikin teku duk jirgin da nashiga kaima saika shiga ashe akwai abinda kakeso a wajena?Ina da kudade masu yawa a cikin jakar guzurina amma ko dinare daya baka dauka ba sai ka dauki abinda yafi dinaren daraja kuma yafu duk wata dukiyar a wannan duniya.Dole ne nasan dalili kuma nasan wanda ya turoka watakila sanin hakan ya kaini ga samun nasarar gano inda nake nema.Koda wasa kada kayi tunanin guduwa daga hannuna ko kuma kayi mini karya bisa abubuwan da zan tambayeka domin yin hakan daidai yake da siyar da ranka.Kasani zan iya shaftare makogwaron bil'adama da kaifin takobina kamar yadda kullum ake yanka kaza ko naman miya a kasuwa,ni da kai duk nasan cewa muna jin yunwa don haka ka biyo ni muje mu nemi abinci muci domin mu sami nutsuwa.Koda gama fadin hakan sai jarumar ta juya ta nufi cikin kasuwa cikin razana da dari dari saurayin ya bita a baya kamar ace kyat ya saki gudawa a wando,su kuwa jama'ar kasuwar wannan karon sai aka rasa wanda zai sake bin bayan wannan budurwa saboda an razana da ita ainun bisa ihun da tayi a wancan karon wanda ya zamo sanadiyar tarwatsa kasuwar gaba daya.Kai tsaye jarumar ta nufi rumfar wata mata mai siyar da abinci jama'a suka rinka ratsewa suna bata hanya har suka shiga cikin rumfar ita da saurayin suna shiga sai gaba dayan jama'ar dake zaune bisa kujeru suna cin abinci suka tarwatse suka gudu suka bar abincinsu alhalin basu gama ci ba,wasu ma anan suka bar takalmansu da yan kayayyakinsu.Ita kuwa matar mai rumfar sai ta durkusa kasa bisa guwiwowinta a gabanta.Matar tace kiyi mini zan baki gaba dayan cinikin yau.Koda jin haka sai jarumar tayi sauri ta kama kafadun matar ta tashe tsaye ta dubeta cikin alamun tausayawa tace,ni ba yar fashi bace abinci mukazo mu siya muci kuma sauran kwastomomin kima da suka gufu basu biyaki kudade ba sakamakon firgita dani zan biyaki kudin abincinsu,ki kwantar da hankalinki ni ba mai cutarwa bace.Koda gama fadin hakan sai Jarumar taje ta zauna a kan wata kujera dake karkashin wani tebur mai kujeru biyu kacal,shima saurayin sai ya zauna tare da ita amma har a sannnan akwai alamomin tsoro a tare dashi.Mai abincin ta dubi Jarumar tace,ya shugabata wane irin abinci zan kawo miki? Jarumar tayi murmushi tace suna na Yazirina bin Salmara karki kara bani girma domin nida sarauta ko wata daukaka,shinkafa da kaza zaki kawo mini amma shi abokin tafiyar tawa bansan abinda yake so yaci ba.Cikin nutsuwa mai abincin ta dubi saurayin tace kai kuma fa?Saurayin yayi murmushi cikin yake yace suna nan Mujahid Ibini As Sudusi nima ki kawo mini irin abincin da abokiyar tafiyata ta bukata.Koda jin haka sai Jaruma Yazirina ta yiwa Mujahid wani irin murmushi na mugunta tace wato kaga banza ta fadi ko zaka kwashi bati shine kai ma kace a kawo maka kaza to kasani bayan cin kaza akwai cin kwakwa a gaba.Cikin razana Mujahid ya zaro idanu yace me kike nufi da cin kwakwa?Yazirina tace karka damu lokaci zai baka amsa.Nan da aka kawo musu shinkafa da kaza dafaffiya kowa farantinsa daban kuma aka kawo musu ruwan inibi a cikin tambula da kofuna guda biyu suka kama kintsa cikinsu.Muhajid ya bude cikinsa yayi ta zuri har saida ya koshi yayi gyatsa amma duk da haka bai rage ko fiffiken kazar ba duk da cewar kazar katuwa ce sosai,sai mutum yana da matukar cin abinci yake iya cinye rabin wannan kaza.Ita kuwa Yazirina kaso daya cikin kaso hudu na kasar ta cinye shinkafar ma cokali uku tayi kawai,itama kanta tayi mamakin yadda Mujahid ya cinye gaba dayan abincinsa.Nan take Yazarina ta bude jakar guzurinta ta fiddo da kudi ta biya abincin da suka ci ita da Mujahid sannan ta biya na kwastomomin da suka gudu kamar yadda tayi alkawari,kawai sai ta dubi Mujahid tace zo mu tafi.Maimakon Mujahid ya bita da sauri sai ya tsaya yanason ya tambayi mai aminci yace ta bashi wani abun daga cikin kudin da Yazirina ta bata,kawai sai yaji Yazirina ta kamo wuyan rigarsa ta baya ta fincikoshi.Ba shiri ya bita a baya da sauri suka fice daga cikin rumfar,Koda ganin haka sai mai abinci ta daka tsalle sama ta kama rawa saboda murna bisa ganin cewa kudaden da Yazirina ta bata yau yakai adadin cinikinta na mako guda.Al'amarin daya baiwa Mujahid mamaki kenan ya dubeta a dan tsorace yace wai shin ina kike son zaki kai ni ne?Ni fa ban san ko ina ba a garin nan kuma bansan kowa ba.Koda jin haka sai Yazirina ta juyo a fusace ta cakumi wuyan rigarsa da hannu daya ta dagashi sama sai gashi kafafunsa na wutsil wutsil a sama tamkar sillan kara ta daga,sannan ta daga kanta sama ta dubeshi tace,Kai tsohon barawo kada ka rainan hankali,gaba daya kasashen dake nahiyar nan kasan cikinsu da wajensu kamar yadda kasan yunwar cikinka saboda kwarewarka a iya sata.Kana zaton bansan ka bane?Kaine ka sace hular sarautar Sarki Atman Bin Ka'ab na birnin Kisra.Kaine ka sace dukiyar attajiri Katadata bin Al Aswad na birnin Sham kuma kai ne ka sace lemar sarauniya Iklaira bin Aslam ta birnin Hindu kuma Boka Kaisu Bin Alkama ya baiwa dukkan wadannan abubuwan uku,ya biyaka ladanka yau kusan shekara biyar kenan kana aiki a karkashinsa yana baka sa'a akan sana'arka ta sata.A halin yanzu duk fadin duniya babu wani barawo daya kaika shahara,dauka da tarin dukiya.Tana gama fadin hakanne sai ta dire shi kasa.Lokacin da Jaruma Yazirina tazonan a jawabinta sai gumi ya tsatstsafowa Mujahid saboda tsananin mamaki da firgitar da yayi saboda yanzu ne ya tsorata sosai da Al'amarin Yazirina ya gane cewa tabbas ta cika shu'umar bokanya domin in bata kasance haka ba babu yadda za'ayi tasan duk wannan sirrmallaketa.Bisa wannan dalili ne boka Salmara yasa aljanu suka kwashe gaba dayan dukiyarsa suka kaita can wani kogon dutse wanda ake yiwa lakabi da TASKAR AJALI,Masana tarihin wannan kogon dutse sun tabbatar da cewa fiye da shekaru dubu uku baya babu wanda yasan hanyar da za'abi a je inda wannan kogo yake kuma kogo ne wanda babu komai a cikinsa face tarin dukiya ta zinare,lu'u lu'u,jauhari,murjani da sauran duwatsu masu daraja,wadanda aljanu ke satowa daga sassan bangaroro na duniya suna kaiwa can su boye tun daga farkon wanzuwar duniya kawo iyanzu.Su kansu aljanun da suke kai wannan dukiya izuwa kogon Taskar Ajali a makance suke shiga dajin kuma su fito a makance domin duk wanda ya shigeshi idanunsa a bude toya daina gani kenan har abada.Tsananin mugunta ce tasa aljanun suka rinka kai duniyar izuwa taskar ajali saboda kawai basa son waninsu ya mallaki dukiyar kwatankwacin irin tasu ko ta iyayen gidansu,inda za'a ce su koma izuwa taskar ajali idanunsu a bude ba zasu iya gane hanyar ba dama da karfin sihirin tsafi kadai ake zuwa wajen.Boka Salmara ya gano cewa shi ko wani jininsa zai iya zuwa taskar ajali idanunsa a bude kuma harma ya sami nasarar zana taswirar zuwa can din amma dayaga cutar ajali ta kamashi sai ya yanke shawarar yakai tasa dukiyar izuwa can yadda babu mai iya mallakarta har abada,sannan kuma sai ya raba taswirar izuwa kaso uku kaso na farko na taswirar sai ya barshi a jikin jemammiyar fatar dabba,kaso na biyu sai ya zanashi a gadon bayan wata yarinya yar shekara tara a duniya wacce ta kasance hadimarsa ce,ita dai wannan yarinyra ana kiranta da Suna Sarila.Asalin Sarila tsintarta Boka Salmara yayi tun tana jaririya a wani daji inda aka tare wadansu fatake aka kashesu aka kwashe dukiyarsu.Boka Salmara yazo giftawa ne ya hango Sarila tana ta tsala kuka irin na jarirai har ya gifta ta sai tausayi ya fado masa a rai ya dawo ya dauketa.Daga wannan rana yaci gaba da renonta amma sai ya baiwa wata farkarsa tana shayar da ita,ita kuwa wannan farka tasa ana kiranta da suna Basma.Saida Basma ta shafe shekara uku tana renon Sarila ya zamana cewa ta shaku da ita tamkar itace ta haifeta amma dare daya boka Salmara yazo ya rabata da ita.A wannan rana Basma tayi kuka kamar ranta zai fita kuma babu irin rokon da bata yiwa boka Salmara ba akan ya bar mata Salira amma yaki kawai sai ya tafi da Salira izuwa gidansa yaci gaba da renonta kuma ta zama kamar tafinta a tsakaninsa da aljanun da sukeyi masa hidima ya zamana cewa tana taimaka masa matuka a harkokinsa na tsafi amma har tsawon shekara shida bata taba fita ba daga cikin gidansa tun daga ranar daya kawota.Sau daya a cikin wata guda Boka Salmara ya amincewa Basma tazo gidansa taga Sarila kuma bai taba yarda ta kusanceta ba saidai suga juna a daga nesa.A watan karshe da Basma ta kawo Ziyare ne izuwa Gidan Boka Salmara bayan taga Sarila zuciyarta tayi fari sai ta juya da nufin ta fice daga cikin gidan kawai saitaji boka Salmara ya kira sunanta.Cikin mamaki ta tsaya kuma ta juya ta fuskanceshi saboda rabon daya kira sunanta ma tsawon shekara shida kenan tun daga ranar daya rabata da Sarila bare wani abu ya shiga tsakaninsu.Kawai sai taji Boka Salmara ya kama hannunta ya jata izuwa can dakinsa na tsafi.Ashe kamuwa yayi da tsananin bukatarta don haka a wannan lokaci hankalinsa ya dan gushe bai san sa'adda ya kaita cikin dakin tsafinsa ba ya kawar da bukatar tasa.Faruwar hakan keda wuya sai yaji rabin jikinsa ya shanye ashe ya karya tasirin tsafin nasa ne bai sani ba.Koda ya gane hakan sai ya kurma uban ihu kuma ya fashe da kukan bakin ciki a yayin da nadama tazo masa.Al'amarin daya razana Basma da Sarila kenan.Sarila ta fashe da kuka tana mai tambayarsa tace yakai Abbana ina dalilin wannan kuka naka?Waishin ma menene dalilin da yasa ka nisantani da wannan mahaifiyar tawa? Koda jin wannan tambaya sai boka Salmara ya dubi Sarila cikin alamun tsananin tausayi tace yake 'yata ki gafarceni bisa abinda zan gaya miki yanzu domin wani babban sirri ne wanda ban taba gaya miki ba,kafin haka inason ki sani cewa daga yau duk sirrikan tsafina sun mutu bazan iya yin komai ba da karfin sihirin tsafi face abu guda,wannan abu kuwa shine zan iya kwashe duk dukiyata dana mallaka na kaita can kogon Taskar Ajali.Wannan dukiya tawa zan kaita canne saboda babu wanda zai iya amfanarta face ni kadai ko kuma jinina ke ba jinina bace,tsintarki nayi a daji an kashe iyayenki da dukkan jama'arsu kece kadai kika tsira da rayuwarki kuma a wannan lokaci kina jaririya.Koda jin wannan batu sai idanun Sarila suka zazzaro ta cika da tsananin mamaki gami da dimbin bakin ciki kuma taji ta tsanin komai da kowa kawai sai ta fashe da kuka.Boka Salmara yace waccan da kike kallo a matsayin mahaifiyarki kuwa ba ita ce ta haifeki ba amma ta shayar dake kuma ta reneki har tsawon shekaru uku daga nan na karbeki daga hannunta naci gaba da renonki kawo izuwa yanzu da kika cika shekara tara a duniya.Yake Sarila ki sani cewa rayuwata ta zo karshe nan da cikar kwanaki kadan zan mutu na barki amma ki sani cewa ba zaki taba wulakanta ba a duniya domin zaki sami daukaka da arziki mai yawa amma zaki nisanta da kowa da dukkan mutane kuma zaki yi rayiwa ne a wurin da dan adam bai isa yaje ba koma hatsabibancinsa kuma aljanu ne zasu rinka yimiki hidima sai kuma tsurarun bayi na bil'adama da zaki iskesu acan wadanda dama can nine na tanadesu domin ki.Koda Boka Salmara yazo nan a jawabinsa sai Salira ta rungumeshi ta sake fashewa da matsanancin kuka da kyar ya rarrasheta tayi shiru sannan ya janyeta daga cikin jikinsa ya dubi Basma yaceYa dubi Basma yace ke kuma daga yau dinnan kin sami gaba dayan sirrikan tsafina kuma babu wanda zai iya gadarsu daga gareki face ki sami juna biyu dani wanda sai tsananin sa'a da rabo sannan hakan zata iya kasancewa.Ke kanki baki isa ki iya zuwa kogon taskar ajali ba ki dauko wadannan dukiya tawa amma inda zaki sami juna biyu sakamakon sadauwar da mukayi to duk abinda kika haifa walau mace ko namiji zai iya zuwa Taskar Ajali ya dauko wannan dukiya tawa amma fa sai ya gwammace baije ba saboda tsananin wahalar da zai sha a cikin tafiyarsa izuwa Taskar Ajaki don saiya gwammace MUTUWA akan RAYUWA.Ke ma zaki sami daukaka,mulki da dukiya kuma har ki bar duniya ba zakiyi aure ba kuma babu wani da namiji daya isa ya sake tarawa dake.Da wannan furuci nakeyi muku bankwana na karshe don haka na sallameku saiku kama gabanku amma ku sani cewa zamanku a tare ba zai haifar muku da komai ba face masifu,tashin hankali da annoba iri iri don haka dolene ku rabu ko wannan ku yabi hanyarsa daban,amma idan kuna shakka ne akan hakan to ku jarraba zama a waje guda zaku sha mamaki.Koda gama fadin hakan sai Boka Salmara yayi tari sau uku saiga gudan jini ya furzo daga cikin bakinsa.Take idanunsa suka juye sukayi jawur ya kife kasa yana numfashi sama sama al'amarin da yasa Sarila da Basma suka kamu da tsananin tausayinsa kenan kuma suka fashe da kuka.Cikin matukar karfin hali boka Salmara ya mike tsaye ya nufi inda kofar dakinsa na tsafi yake har ya sanya kafarsa guda izuwa cikin dakin saiya tsaya cak ya juyo ya yafito Basma da hannu ta taho gareshi,kawai sai ya zura hannunsa cikin aljihun rigarsa ya fiddo da taswirar zuwa kogon taskar Ajali dake jikin jemammiyar fata ya mika mata ta karba yace wannan taswira ce izuwa kogon taskar ajali amma kaso daya cikin ukunta ki duba gadon bayan Sarila kaso na biyu na zane akai,kaso na uku kuwa yana can inda zaki zauna ki karasa sauran rayuwarki ta duniya rubuve akan wani allo na katako.Dole sai an hada wadannan taswira guda uku sannan za'a iya samun cikakken zance na hanyar da za'abi aje kogon taskar ajali.Kinga kenan idan kin sami damar samun juna biyu na kin haifeshi to zaki iya baki taswirar guda biyu,ta cikon ukun kuwa dolene ya tafi neman Sarila.Ki sani cewa Sarila na fita daga nan yanzu Aljanu ne zasu dauketa su kaita can tsakiyar birnin Jannatul Duniya.Wannan tsibiri shine wurin da yafi ko ina tsaro da ni'ima a cikin kaf din wannan duniya,kuma yana tsakanin karshen birnin sin da Mastur Kusa da dan karshen bangon duniya.Ba'a tsufa a wannan tsuburi ba'a rashin lafiya koda kuwa mutum ko aljan zai shekara dubu a wajen,amma ana mutuwa.Koda Boka Salmara yazo nan a jawabinsa sai ya yiwa Basma kallon karshe.A lokacin da hawaye ya zubo masa sannan ya juya da nufin ya shige cikin dakinsa na tsafi amma sai Basma ta dakatar dashi tace,yakai Salmara yanzu ta yaya zan kai kaina inda zan karasa sauran tawa rayuwar kuma inane wannan wuri?Koda jin wannan tambaya sai Boka Salmara ya numfasa yace kamar yadda aljanu zasu kai Sarila Tsuburin Jannatul Duniya kema akwai wanda zai yi miki jagora izuwa masauki wanda shine Darul Azmin,shi kuwa wannan wuri a karshen bangon duniya yake daf da birnin Hindu,zamanki acan shine kadai kubutar dukkanin matsafan duniya,in ba haka ba kuwa sai ki zame musu annoba mai shayar dasu mugunyar mutuwa domin sai an wayi gari babu sauran boka guda daya a raye a doron kasa face ke.Idan kuma kinason ki zama sanadin mutuwar miliyoyin wadannan rayuka to ki cigaba da zama a cikin mutane kada ki tafi izuwa wannan masauki naki.Koda gama fadin hakan sai Boka Salmara ya shige izuwa cikin dakin halwar tsafin nasa bai yarda ya sake waigowa ba ya dubi Basma da Sarila.Ai kuwa yana shigewa sai kofar dakin ta kullo kanta,wannan shine ganin karshe wanda Basma da Sarila suka yiwa Boka Salmara.Ba tare da bata lokaci ba kuwa Basma da Sarila suka fice daga cikin gidan Boka Salmara suna fita sai gidan ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a wajen.Faruwar hakan keda wuya kafin Basma ta dubi Sarila tace wani sai sukaji wata iska mai karfi a samansu.Kafin su daga kawunansu suma suga abinda yayi musu inuwa tuni an suri Sarila anyi sama da ita,ita da abinda ya dauketan kafin dakika guda sun kule a cikin gajimare.Ita kuwa Basma sai ta hango wani mutum akan wani farin doki sanye da bakaken tufafi ya durfafo inda take a sukwane,abinda ya razana ta dangane da mutumin shine ya lullube kansa da bakin mayafi amma kuma bashi da fuska,ma'ana babu fata,tsoka ko kashi akan fuskarsa bare a sami hanci,baki ko ido kawai sai wani irin haske mai dallare idanu tamkar an ajiye madubi a rana.Babu shiri Basma ta sunkui da kanta kas ta daina kallon fuskar mutumin da isowar wannan mutumin daf da Basma sai ya sureta da hannu daya ya azata a bayansa bisa wannan farin doki ya zabureshi cikin azababben gudu na gaba misali.Tunda Basma tazo duniya bata taba ganin doki mai gudun wannan doki ba domin ko walkiya bata fishi saurin baiyana da bacewa ba,ai kuwa ko rabin sa'a basuyi ba da fara wannan tafiya ba sai barci mai nauyi ya dauke Basma.Lokacin da Basma ta farka daga barci sai ta tsinci kanta a cikin wani kasaitaccen daki wanda komai dake cikinsa anyi shine da gilashin lu'u lu'i mai launi fari hatta luntsumemen gadon da take kao kuwa.Tana bude idanunta taji kanta yayi mata nauyi tamkar an dora mata katon dutse haka kuma taji ciwon kai ya kamata,tsaitsaye a gefe daya a bayanta gadon da take kwance a gabansa kuyangi ne na bil'adama su arba'in da daya,koda kuyangin suka ga Basma ta farka daga barci sai biyu daga cikinsu sukayi sauri suka matso gareta.Daya na ruke da tambulan cike da sabuwar madarar shanu mai gardi da dumi dayar kuma na rike da dogon kofi na gilashi take suka zuba mata madarar a cikin kofin suka cika shi taf sannan suka bata ta kama sha.Bata san sa'adda ta shanye shi tas saboda dadin dandanon tana gama shanye nonon taji ta daina ciwon kan take ta dawo cikin haiyacinta tare da lura da cewa ashe an canja mata ma suturar jikinta an sanya mata wata.Farar doguwar riga cikin dimauta da firgici Basma ta dubi kuyangar data bata madarar da tasha tace yaushe ne nazo nan kuma ina abokin tafiya wanda ya kawo ni nan akan farin dokinsa?Koda jin wannan tambaya sai kuyangar tayi murmushi tace ya shugabata ai abokin tafiyarki manzo ne kawai ba kowa ba,ya gama aikinsa ya tafi izuwa can kasarsu ta birnin matsafa a wata nahiya dake cikin kasashen aljanu.Ki sani cewa yau kwanaki arba'in da daya kina barci tun akan hanyarku daga can birninku zuwa nan dajin Iblas dake daf da birnin Hindu,ki kwantar da hankalinki ya shugaba kiyi sani cewa indai kina nan baki da wata fargaba ko bakin ciki ko kewa kuma duk abinda kikeso indai akwai shi anan cikin duniya zaki sameshi face abu guda wato abokin rayuwa.Kowacce 'ya mace tana bukatar namiji abokin rayuwarta amma ke ba zaki taba samun saba har ki kammala rayuwar kwanakinki na duniya.Koda kuyangar tazo nan a jawabinta sai hankalin Basma ya dugunzuma ainun ta rasa abin dake mata dadi a duniya.Daga wannan rana Basma ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa irin wadda bata taba tsintar kanta a ciki ba domin rayuwa ce wadda babu matsalar ci da sha ga makwanci wanda ma yafi na wadansu sarakan,kuma babu abinda takeyi da kanta komai saidai kuyangi suyi mata,abinda ya daurewa Basma kai shine ganin yadda sauran kuyangin suke rayuwa a wannan tsibiri a cikin daji haka ba tare da wata rayuwa ba domin a ganinta babu rayuwar da tafi dadi face ta zama a cikin gari tare da al'umma koda kuwa dadin da mutum zaiji a irin wadannan gidaje na bokaye babu kamarsa a duniya.Koda Basma tazo nan a jawabinta sai idanunta suka ciko da kwallah hawaye ya zubo mata,nan ta kamu da tsananin bakin ciki gami da takaici taji tayi nadamar kaddarar data hadata da Boka Salmara a tafarkin barikanci.A kwana a tashi,a ranar da Basma ta sami kwanaki sittin daidai a wannan kayataccen gida na daji,sai ta wayi gari a cikin tashin zuciya har da kumallo.Nan da nan ta fita daga cikin haiyacinta har ta fadi kasa a lokacin da taji jiri ya kwasheta kuma kanta ya kamu da ciwo cikin hanzari kuma a guje kuyangin suka rugo da gudu suka dauketa suka kaita can cikin turakarta suka kwantar da ita a kan gado.Shugabar kuyangin wata tsohuwa tasa aka rinka gasa gashin Basma sannan ta kama tsintsiyar hannunta ta rike tana nazari irin na likitoci.A daidai wannan lokaci ne Basma ta farfado daga dogon suman da tayi,koda ta bude idanunta saitayi arba da wannan tsohuwa zaune a gabanta ta kura mata idanu tana yi mata murmushi.Kawai sai tsohuwar ta bude baki tace yake Basma muna ta yaki murna saboda kin sami juna biyu tare da shugabanmu Boka Salmara kafin ajalinsa ya cika.Tabbas abinda zaki haifa zai zamo babban jarumi abin kwatance kuma shine kadai zai iya zuwa TASKAR AJALI ya dauko dukiyar da mahaifinsa ya tara wato Boka Salmara..... ,TASKAR AJALI!!! Littafi Na Daya (1) Part D Ya tara wato Boka Salmara.Yake Basma kiyi sani cewa duk mahalukin daya mallaki wannan dukiya ta Boka Salmara zai iya amfani da ita wajen mulkar wannan duniya gaba dayanta,domin gaba dayan attajirai da sarakai sai sun zamo almajirai masu yin bara a gabansa.Akwai matsaloli guda biyu a gaba ga Jarumi ko Jarumar da zaki haifa.Matsala ta farko itace dole ne a baiwa dan naki ko yar taki horon yaki mai tsananin gaske yadda zai iya tsare taswirar da zaki danka masa guda biyu saboda matsafa da masu mulki zasuyi kokarin rabata da su.Matsala ta biyu kuma waccan yarinya Sarila wacce zannen taswirar na uku ke bisa gadon bayanta zata baro can Jannatul Duniya a lokacin da yarki ko danki ya shiga duniya nemanta.Zai kasance suna farautar juna a wannan lokaci,ita Sarila zata kasance azzaluma ainun kuma karfin damtsenta dana sihirinta sai ya ninka na danki ko yarki saboda albarkacin rayuwar datayi a tsibirin Daulatul Duniya.Burinta shine taga danki ko yarki ta kashe ta ta dauke Taswirar biyun dake hannunta,ita ma yar taki ko dan naki burinsa ya kashe Sarila ya kwafe taswirar dake zane a bayanta domin ya sami damar zuwa Taskar Ajali.Wannan 'da naki ko ya taki ba zai sami nasara ba akan Sarila face da taimakon wani bakon saurayi wanda ba'a san daga nahiyar dazai fito ba,shidai wannan saurayi ya kasance kyakkyawa abin kwatance kuma bashi da karfin damtse ko kadan kuma bashi da karfin sihirin tsafi sannan bai iya yaki ba,asali ma bai taba rike takobi ba saidai ya kasance yana da wata irin baiwa ta musamman sannan yana da tsananin sa'a da rabo bisa duk abinda yasa a gabansa duk da cewa shi mutum ne mai matukar tsoro,wannan saurayi shine kadai zai iya takawa Sarila birki a cikin zaluncinta kuma shine kadai zai iya kare abinda zaki haifa daga sharrin Sarila.Koda tsohuwar tazo nan a jawabinta sai bakin ciki ya sake turnuke Basma hawaye ya zubo mata tace yanzu kenan Sarila da abinda zan haifa zasu zamo ABOKAN GABA har dayansu ya zamo sanadin ajalin daya alhalin su

Chapter 1 of 14