Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
basarwa yayi ya bashi hannu suka gaisa, sai ishaq ya kalli Abnal sukayi musabaha ishaq yana cewa "longest time bro, how have you been?" "Alhamdulillah, I've been great" Abnal ya amsa shi atakaice, cos he can already sense the tension radiating from Marwan, kallon laila ishaq yakumayi yace "okay, let me not take any more of your time, i will give you a call later" laila kasa amsa shi tayi sai kawai tayi mishi ya'ke, juyawa ishaq yayi ya shiga cikin mall din, lokacin security din ya gama sa komai a butt din motarsu, kudi Marwan ya ciro ya bawa security din sannan ya shiga cikin mota, kallon 'what the hell did you just do' Abnal yayiwa laila, sannan Shima ya shiga cikin motar, laila was the last to enter dan harga Allah duk jikinta yayi sanyi, to God who made her, the only reason why she gave ishaq the digits were just so he will leave her alone, maganar lunch din dayakeyi ma, ita tasan ko giyar wake tasha she will never follow him anywhere. Marwan baice mata kala ba, Amma inka kalleshi, one will know that this guy is upset, kasa ce mishi komai laila tayi cos ko kallon inda take Marwan baiyiba, he was just operating his MacBook. Har suka isa keffi Marwan bai bawa laila fuska ba, Abnal was the one that was directing the chauffeur har suka isa kofar gidansu, tun lokacin da motar ya shigo unguwarsu yan unguwar suka kurewa motar ido tsabagen yanda motar ta hadu gashi basu saba ganin irinshi ba, bin motar da ido sukayi dan ganin gidan da motar zai tsaya, they couldn't believe it dasu kaga gidan daya tsaya, dan a nasu tunanin babu mai irin wannan kudin dazai sosu, Marwan was more than shocked dayaga unguwar dasu laila suke, though yasan cewa they're from a humble background amma bai taba zata cewa their level of poverty ya kai wannan ba, Abnal ne ya fara fitowa daga motar, Sameera dake serving din wani customer abunci ne  tafara hango Abnal, rugowa  tayi da gudu tazo ta rungume shi, cos she wasn't expecting them today, so is Mami, zuwa lokacin Marwan da laila suma sun fito daga motar, barin Abnal sameera tayi taje ta rungume laila cos she has really missed them, gaida Marwan sameera tayi Marwan yace "where's my own hug?" ya tambayeta jokingly while smiling , sunkuyar da kai sameera tayi tana murmushi, laila ce ta tambayi sameera inda mami take, sameera ta amsa dacewa tana cikin gida, shiga  sukayi cikin gidan while Marwan shi ya tsaya a zaure yana jiran ayi mishi iso, umarni ya bawa chauffeur dinshi cewa yafara kwaso kayan dake cikin booth zuwa zauren gidan. Mami da fitowar ta kenan daga bayi ce ta hango laila da Abnal, daskarewa tayi tsaye cos she wasn't expecting them, basu gaya mata cewa zasu dawo yauba, rungumeta laila da Abnal sukayi dan ba karamin missing sukayi mata ba, daga fuskar Abnal Mami tayi tana kallon shi hawaye na fitowa daga idanuwar ta, dan bata taba zata cewa Abnal ya samu lafiya irin haka ba, share mata hawaye Abnal ya farayi yana cewa "Mami dan Allah ki daina asarar hawayenki haka nan" murmushi Mami tayi sannan tace "hawayen farin ciki ne Abnal, bansan ka samu lafiya har haka ba, godiya ga Allah" Mami tafada, laila ce tace "Mami ki dauko hijab dinki, doctor Marwan yana zaure" "wai tare kuka zo dashi?" Mami ta tambayeta "A, shi yakawo mu" laila ta amsata "shi ne kuka shanya shi acan, maza kiyi mishi iso" Mami tafada tana shiga cikin daki dan dauko hijabinta, sameera laila ta aika ya shigo da Marwan dan uptill now bata san ya zasu karkare ba, sameera na zuwa tace ance ya shigo, tare su biyu suka shigo cikin parlor din gidan, parlor din babu komai acikin sa, ko irin leather carpet dinnan babu sai cement, iya cushion chair guda biyu ne a parlourn, da one seater da three seater shikenan, ko TV babu, but if there is one thing that really impressed Marwan is how neat and tidy everywhere is, no dirty or any funny stench, Marwan na shiga , mami ita kuma ta saka hijab dinta ta fito parlor, sai Marwan ya durkusa ya gaidata, rasa inda zata sashi Mami tayi cos kallo daya mutum zaiyiwa Marwan yasan cewa babban mutum ne, godiya Mami ta fara mishi bayan ya zauna, ta inda take shiga ba tanan take fita ba, Marwan shima yasan cewa yasha godiya da adduoi daga bakin Mami, ruwa Mami ta gayawa laila ta kawo mishi amma sai Marwan yace "A'a Mami ni yunwa nakeji" ya fadi haka ne dan yana son Mami ta saki jiki dashi sosai, cos he noticed cewa kunyar shi take ji, Mami najin abun dayace, sai tadanyi jim kadan dan ita gani take basuda irin abuncin da Marwan zai iya ci, da Marwan ya lurada reaction din Mami sai ya kuma cewa "Mami karki damu duk abun da kike dashi zanci, infact ko daga abuncin da kuke siyarwa ne, i want it" da Mami taji abun dayace sai tace "kai anya zaka iyaci kuwa? Ba irin abuncin daka saba ci bane ba" murmushi Marwan yayi ya kalli sameera yace "dear dan Allah ki ibarmun shinkafa" sameera na kokarin tashi kenan laila tace "don't worry, let me do It" tafada tana tashi, kallon ta Marwan yayi yace "no, i prefer your sister to do it" yana gama fadan haka ya kuma kallon sameera yace "please do me the honor and serve me" yafada mata with a very sweet smile on his lips, sameera had no option than to go do what she's been ask of, Abnal sai murmushin mugunta yake mawa laila, maka mishi harara laila tayi. Bayan Marwan ya gama cin abunci, sameera ya kuma kira ta kwashe kwanukan sannan ya kalli mami yace "Mami dan Allah inasonyi magana dake" sannan ya kalli su Abnal yace "bruh can ya'all please excuse us?" "sure" Abnal ya amsa shi a takaice, waje wajen canteen dinsu su uku suka fito suka zauna, sai santin yanda jikinsu yayi fresh suka kara kyau sameera take tayi. da Marwan yaga cewa daga shi sai mami, sai yafara cewa "na farko Mami, Alhamdulillah cewa Abnal ya samu lafiya, duk dokokin daya kamata yabi na sanar dashi kuma nasan cewa bi iznillAh baza'a samu matsala ba, abu na biyu dana keson in rokeki, indai kinsan cewa kin dauke ni a matsayin da ko ka'ni dan Allah dan annabi wannan alfamar dazan nema banso kice a'a, indai kince a'a toh nasan cewa baki daukeni a matsayin dani na dauke kuba... "Mami ce ta katse shi ta hanyar cewa " duk wannan taimakon daka yimun banga wane irin alfarmar dazaka nema dazan ce maka a'a ba, bara ma kaji, koma menene dazaka nema, amsana shine A, indai bawai abun ya sabawa addini ba, toh amsar shi A ne, nayarda da koma menene" Mami tafada mishi, hamdala Marwan yayi sannan yace "ai baima sabawa addini ba, amma naji dadi da wannan yardar da kika yimun, dama ba wani abun bane ba face inason tura Abnal zuwa kasar waje yaje yayi masters dinsa acan, wannan change of environment din zai taimaka mishi sosai wajen kara samun sauki" aikam Mami najin abun da Marwan yafada sai tayi dan jim kadan, dan harga Allah ita bata taba kawo cewa wannan ne alfarmar da Marwan zai nema ba, yanzu kuma babu daman tace a'a, dan that will be her going back on her words, da Marwan yaga cewa Mami batace komai ba sai yaci gaba dacewa "abu na uku shine, inason laila kuma nayi mata magana ta amince, yanzu amincewarki nake so" Marwan ya karasa maganar shi, numfasawa Mami tayi kafun tafara magana kamar haka "naji duk bayaninka, nafarko dai godiya zan kuma maka abisa duk abun da kai da yan uwanka kuka yimana, duk laila ta fada mun ta waya, Allah kadai ne zai iya saka muku da mafificin alherin sa, na biyu shine maganar tura Abnal da kake sonyi zuwa kasar waje, Allah ya gani bansan cewa alfarmar da kakeson nema kenan da ban yarda ba, Amma tunda nariga nace A, toh banda zabi kuma, Amma nima ina son kayimun wani alkawari kuma banason kace a'a" Mami itama tafada "toh wane irin alkawari ne kike son inyimiki?" Marwan ya tambayeta "so nake kayimun alkawarin cewa, daga wannan taimakon na tura Abnal kasar waje da kake sonyi, bazaka kuma yi mana wani taimakon ba, indai ka yarda toh nima na yarda yaje" Mami ta fada mishi, shiru Marwan yayi na wani lokaci sannan yace "A nayarda", ya amsata a takaice, sai Mami tace "madallah, maganarka na karshe dakace kana son laila, maganar gaskiya laila ba yarinya bace ba kuma, amma a matsayina na uwa, bazanso ya'ta tayi aure zuwa gidan da bazata samu kwanciyar hankali ba, kai zaka iya cewa kana sonta koda daga gidan talaka take, iyayenka fa? Ba lallai bane su  susota ba, dan irin haka ya taba faruwa da ita, saurayin na mutuwar sonta amma iyayen shi suka hana, babu irin cin mutuncin da basuyi mana ba, toh kaga inda matsalar take" Mami tafada, bayan Marwan ya gama jin duk bayanin Mami, baice komai ba dan ya riga yasan cewa Mami zata iya fadan haka, so already shi ya tanadi abun dazaiyi, sai kawai ya ciro da wayarshi yayi dialing din wani numbar tareda sashi a handsfree, ringing wayar yafara yi, dagawa akayi da sallama, saiga shi muryar Hajiya maimuna ce, gaisawa sukayi da Marwan, Hajiya maimuna take tambayarshi ko sun iso keffi lafiya, amsata Marwan yayi da "mun isa tuntuni" sannan yayiwa uwar tashi bayanin komai na tsoron da Mami take na cewa, bazasu so laila ba because she's from a humble background, all this while Mami najin komai, sai Hajiya maimuna tace "lahh, kamarya bazamu so taba dan kudi?, toh da mai kudi da talaka ai duk jarrabtarmu Allah yayi, bawa Mami wayar inyi magana da ita" Hajiya maimuna tafada, dan ita batasan cewa wayar a hands-free Marwan yasa shiba, cireshi daga hands free Marwan yayi sannan ya mikawa Mami wayar, gaisawa sukayi, Hajiya maimuna ta kwantar mawa Mami hankali cewa karta damu, ita ta dauki laila a matsayin ya', so kar Mami ta daga hankalinta, godiya Mami tayi mata sosai, sannan Hajiya maimuna tace zata karbi number Mami daga hannun Marwan dan su ringa gaisawa, godiya Mami ta kuma yi mata sannan suka katse kiran. Mami na ajiye wayar ta kalli Marwan tace "ai da baka kira taba, duk sai naji kunya ya kama ni" murmushi Marwan yayi sannan yace "ai ba yanda zanyi miki bayani daza ki yarda, gani zakiyi kawai fada nake dan kawai ki amince, Amma yanzu data fada miki da kanta kinga zaki fi yarda" "hakane kuma, toh Allah ubangiji ya tabbatar da Alheri, tunda kace itama ta yarda, abun yazo da sauki kenan" Mami tafada, Marwan bai dade ba ya tashi tsaye tareda ajiye envelope akan table yace Mami tayi manaji dashi, ai Mami najin abun daya fada, sai tace "ai ba alkawarin da mukayi dakai ba kenan, gaskiya bazan karbi kudinnan ba" babu yarda Marwan baiyiba cewa Mami ta karba dan shi ya riga yayi niyyar bata kafun yayi mata alkawari, Amma sam Mami bata yarda ba, babu yanda Marwan ya iya, daukan envelope din yayi, rakashi zuwa waje Mami tayi inda su laila suke zaune a canteen dinsu suna hira, sai kallonsu yan unguwa sukeyi dan irin changawar da Abnal da laila sukayi, ga jibgegen motar da akayi parking a kofar gidansu, su laila na hango su, suka karaso wajen su dan yiwa Marwan sallama, bayan duk sunyi mishi sallama, ya rage laila ita kadai, laila ta budi baki zatayi magana kenan Marwan yace "you can see it's already late and i have some patients waiting for me, zamuyi magana anjima" Marwan na gama fadan haka ya shiga mota, chauffeur yaja mota suka bar wajen, without even waiting to hear what laila had to say. 16/12/2021, 9:13 am - MEEDAH'S COUTURE AND MORE: Assalam alaikum, duk wacca tasan cewa tanaso daga farko should private chat me, banson kuma turowa dan gudun takurawa sauran 17/12/2021, 3:47 pm - MEEDAH'S COUTURE AND MORE: I just published "Chapter 9" of my story "ABNAL". https://www.wattpad.com/1111816881?utm_source=android&utm_medium=whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=ummuhamdiyah&wp_originator=wssoJfBZ6Y87ce%2BM9lEqjOjRXofqU3Hv2Jf17pA29w7jKBdxIei69OLno5sRIB9qArYMae2Vuth1fNYMIm697pXQ4FwFRIDtX%2Fyhnh0cD8%2FuJ7gP%2BxwelCmjtKbpqw%2FO 🔴🔴🔴⚫⚫⚫🔵🔵🔵 Book by :Bilkis Qazeem (ummu Hameedah) ABNAL Chapter 9 THIS BOOK IS ABSOLUTELY FREE 💃 💃 💃 If at all I'm entertaining in any way or form, please do follow me on my Instagram handle 👇🏻 https://www.instagram.com/meedahs_couture_and_more  and as you do so may Almighty Allah answer all your hidden and open prayers 🙏, Ameen. And please share the book to other groups da kuke ciki, *wannan* *ne* *correct* *Instagram* *link* *dina* , *wanda* *nake* *posting* *before* *was* *wrong*, *so* *please* *show* *me* *love* *by* *following* *me* . Laila was dejected when Marwan didn't give her an avenue to explain herself, juyawa tayi taje ta samu su Mami a canteen dinsu, all of them noticed how sad laila was, sai Abnal ne yayi magana yana cewa "Mami baku gama siyarda abuncin da kuka dafa bane ba?" yayi tambayan yana kallon Mami "mungama, dama wancan mutumin daya tashi yanzu muka siyarwa da sauran, kawai tattara kayan zamuyi" Mami ta amsa mishi "in hakane, Sameera ki tattara komai, mu mushiga ciki" Abnal yafada yana kallon Sameera, da 'toh' Sameera ta amsa shi. Su Mami na shiga ciki, ta kalli laila tace "ke kuma mai yake damunki naga duk kinyi wani iri?" Mami ta tambayi laila, kasa amsata laila tayi sai Abnal ne yace "sun dan sami misunderstanding ne tsakaninta da doctor" Abnal na gama fadan haka sai laila ta harareshi tana cewa "toh radio mai jini, sannu" dariya Abnal yayi yana kuma cewa "toh karya nayi?" ya tambayi laila yana cigaba dayi mata dariya, laila bata amsa shiba, sai Mami ce tace "toh ke mai ya hadaki dashi?" "babu komai fa Mami, karki amsa Abnal" laila ta amsata, murmushi Mami tayi sannan tace "wai mai yasa ku yarannan kun fiya ja mana abun dayafi karfinmu? Yanzu muka shafa babin Abnal da rukayya, sai ke kuma kika jajibo mana likita?" (toh Mami Allah ya azurta ki da ya'ya kyawawa, what did you expect), Mami tafada tana kallon laila, murmushi kawai Abnal yayi, sai laila ce tace " Mami wa yagaya miki akwai wani abun tsakanina dashi? " laila itama ta tambayi Mami " shidin da kansa ne yafada mun" Mami ta amsata, kallon mamaki laila tayiwa Mami jin abun datace, nan Mami tayi musu bayanin komai da Marwan ya fada mata, ciki harda kiran Hajiya maimuna da kuma tafiyar Abnal zuwa kasar waje, laila, Abnal da kuma sameera data gama aikinta tazo ta samesu suna tattaunawa were surprised jin bayanin da Mami tayi musu, expecially na tafiyan Abnal, murna sameera ta dinga yi cewa finally her elder sis is getting hitched soon and her elder bro is traveling out of the country, laila and Abnal were just speechless, sun rasa abun cewa cos Marwan never mentioned anything of such to any of them, sai Mami ce tayi magana tana cewa "yanzu laila zaki gaya mun abun daya hadaki da Marwan din ko zaki cigaba da zurfin ciki?", laila had no option than to explain what happened at the mall to Mami, data gama bayaninta Mami tace "inba rashin zuciya irin nakiba laila, duk inda kika ga ishaq ya kamata ace kin kalleshi ballantana ace ki kulashi, harda bashi numbern ki, dukda irin cin mutuncin da wulakancin da iyayenshi suka yimana?" Mami ta tambayeta, shagwaba fuska laila tayi sannan tace " toh Mami ai duk abun daya faru bada sanin shiba, toh kinga ba laifin shi baneba" laila tafada, fuskantar ta Abnal yayi yace "yanzu sissy, tell us, wa kike so, Marwan ko ishaq?" ya tambayeta as a matter of fact, kallon mamaki laila tayi mishi tace "how can you even ask me that question, of course it's Marwan" laila ta amsa shi, sannan taci gaba dacewa "let's get something straight, I'm no longer in love with ishaq, I'm over him, kawai i just gave him a wrong digits just so he will let me be, cos na sanshi da kafiya, that was all it was" laila tafada musu just to clear herself, sameera ce tayi magana tace "oh you mean to say the digits you gave ishaq were fake?" "of course they were, hauka nake dazan bashi number na" laila ta kara jaddada musu, numfasawa sameera tayi sannan Abnal yace "then why are you now stressing yourself?, don't worry everything will be fine" Abnal na gama fadan haka, sameera ta kuma cewa "now that all that is settled, can we come to the interesting part and start checking what's in these boxes and shopping bags?" sameera ta tambaya tana kallon laila, murmushi laila tayi sannan tace "ai dama inda kika fi kwari kenan, you can go ahead, muma bamusan mai acikin suba" , sameera najin go ahead din laila ta sauko tafara bude kayayyakin, daga kan shopping bags din tafara, shopping bag din data fara dauka na waenda iPhones ke cikin sane, tana budewa da taga iPhones ta kwala ihu tana fitowa dasu one after the other, laila was dumbfounded, sai bin wayoyin take da kallo, Mami was the one that asked tana cewa "waennan kuma na waye?" nan Abnal yayi musu bayanin komai, sameera was super duper excited, immediately tabawa kowa nashi wayar, sai sauran shopping bags din that were occupied with kayan ciye - ciye, sai medium boxes da hajiya maimuna ta basu, nan kayan sawa iri-iri ne aciki, and all were designer made, babu na karamin kudi acikinsu, just imagine kayan lefe, ahada shi a akwati daya, the box alone itself, abun kallo ne, sai envelope da Alhaji yusuf ya basu, contain 500 thousand naira each, that's a million naira in total, then kayan da anty faty tabawa laila, sai kuma envelop da anty faty tabawa Abnal, shi kuma contain another 500 thousand naira, Abnal shi ya tashi da a million naira kenan, last but not the least, take- away na kayan da basu ciba a gidansu Marwan, shi kuma dangin su drink, fruits da gashashen naman kaza wanda yaji kayan hadi sosai ne, by the time din da sameera ta gama dudduba komai, all of them including sameera herself couldn't believe it, expecially that money da aka basu, it shocked them dan basu taba ganin kudi mai yawa irin haka ba, Sallar Maghreb da aka fara kira ne yasa suka tashi, Abnal shi kuma ya fita zuwa masallaci. Bayan Sallar Isha Mami da ya'yanta na zaune a parlor suna hira, Mami ce tayi magana tana cewa "yauwa, ya kamata mu biya malam mudi (landlord dinsu kenan) kudin hayansa gobe, dan yayi mana kokari sosai, ba kowa ne zai iya hakurin dayake mana ba" Mami ta fada tana kallonsu, laila ce tayi magana tana cewa "haka ne kam, kuma inason inje gidan anty zee (nurse din datayi musu introducing din Marwan), inje inyi mata godiya sosai, dan ta sanadinta duk waennan Alherin ya samemu" "hakan yayi daidai, kinyi tunani mai kyau, Allah kadai ne zai iya saka mata da mafificin alherinsa" Mami tafada, da 'Ameen' duk suka amsa, Mami ce ta tashi tana cewa "toh ni na shiga daga ciki, zanje in kwanta dan gobe insamu intashi da wuri dan daura girkin siyarwa" Abnal ne ya kalli Mami yana cewa "girkin siyarwa kuma Mami?, gaskiya zaki huta koda na sati dayane, tunda abun ci da sha Allah ya riga ya hore mana" Abnal yafada as a matter of fact, tsaya kallon shi Mami tayi sannan tace "hutu kuma Abnal?, kodai dan kudin da kuka samu shiyasa kake waennan maganganun?" Mami ta jera mishi waennan tambayoyin, Abnal ya budi baki zai amsa Mami kenan laila ta riga shi tana cewa "Mami, Abnal yanada gaskiya, mu huta koda na sati daya ne" laila tafada tana kallon Mami "toh naji, Amma nidai na shiga daga ciki" Mami tafada tana shiga cikin daki, sai da safe sukayi mata, tashi sameera itama tayi tabi Mami, dan itama tanada morning lecture washegari. Bayan su Mami sunje sun kwanta, laila ta matsa kusada Abnal tace "I've been calling Marwan but he's not picking my calls, da Mami ta tambayeni cewa dafatan ya isa Abuja lafiya, amsata nayi kawai da 'a ya isa', i don't even know what to do again" laila tafada looking all fed up, kallonta Abnal ya tsaya yi sannan yace "take this advice from me, let him be for today cos it's obvious he's still upset with you, zuwa gobe sai ki kirashi, by then the anger he's feeling would have subsided, atleast it's not as if he doesn't know about ishaq before, so karki damu" Abnal yafada mata in a comforting manner "actually, he doesn't know about Ishaq' s existence cos i didn't tell him" laila tafada in a skittish way, kallon mamaki Abnal yayi mata sannan yace "i thought you said you told him EVERYTHING about you, why did you now omit that part of your life? " Abnal ya tambayeta " well i don't know why i didn't tell him, i guess i thought it wasn't that important" laila ta amsa shi " well you guessed wrong, i now understand why he's this furious" Abnal ya kuma fada "agreed i messed up, just tell me what to do  now" laila tafada mishi in a pleading way, cos Abnal is her only confidant that she's free to tell every and anything, shiyasa ma bata damu da kawa ba "well i will still go by my first suggestion, let him be for today, in Allah ya kaimu gobe sai musan abunyi" Abnal yafada mata, laila had no option than ta hakura zuwa gobe, sai da safe laila tayiwa Abnal itama ta shiga daki while suka bar Abnal shi kadai a parlor dan nanne wajen kwanciyar shi, laila na shiga daki Abnal ya ciro sabuwar wayar shi da ya riga yasa sim dinshi, airtime din da ya siya a hanyarshi ta dawowa daga masallaci ya loda sannan yayi dialing din number Nadia. Lokacin da kiran Abnal ya shigo wayar Nadia, she was on her way inside their house cos ta raka Marwan zuwa parking lot (da Marwan yabar keffi, asabitinshi yayi niyyar zuwa amma aka kirashi cewa Dr khan ya riga yayi attending to patient din dayake da niyyar zuwa gani, so shiyasa kawai ya zarce gidan anty faty, anty faty was surprised data ganshi kuma, cos she wasn't expecting to see him again that same day, bayan sun gama gaisawa, Marwan yayiwa anty faty bayanin komai gameda discussion dayayi da Mami, anty faty was impressed by what Marwan wanted to do for them, expecially Abnal's traveling out, Amma inda Marwan shi ya nuna damuwarshi was alkawarin da Mami yace ya dauka cewa bazai kara taimakon suba bayan expenses na karatun Abnal, dan harga Allah he really wanna help them, shawara anty faty ta bashi cewa why not he should establish laila in such a way that she will be financially independent, inyaso laila will now be the one to uplift their family, Amma the only But din dake cikin maganar is that before he can do this he must be married to laila, at least with that laila will no longer be under Mami, na'am Marwan yayi da shawaran anty faty, suna cikin magana Nadia tazo ta samesu, bayanin komai Marwan yayi mata, Nadia was excited acigaban dasu Abnal zasu samu, while on the other hand she's a bit sad cos of tafiyan da Abnal zaiyi, gani take he's gonna forget her once he's out of the country, but she just have to be optimistic and hope for the best, wannan kenan) Nadia na ganin sunan wanda ke kiranta ta saki murmushi cos she wasn't expecting his call this early, dukda batada number Abnal but all thanks to true caller saiga sunan shi ya nuno, daga wayar tayi da sallama sannan tace "who's this please?" amsa sallamarta Abnal yayi sannan yace "it's one of your admirers ma'am" Abnal ya amsata, Nadia almost burst out with laughter but dannewa tayi sannan tace "please I'm not really in the mood for any of these idle talks, as you can see it's pretty late, so if you don't mind i will be hanging up now" Nadia tafada with a little bit of attitude, murmushi Abnal yayi sannan yace "swear it that you don't know who's on the line" Abnal yafada mata haka cos he knows that she already knows that its

Chapter 6 of 32