Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana mikamin Dubu daya lokaci d'aya da Fadi'n " ya ce ayi sauri" Kai na jinjina kawai batare da na yi mgana ba. Bansan meyasa na ji na Damu da ma ko waye mai siyan Danwake a kyakyawan kular nan ba. Ko saboda kirkin da ya ke min ne bansani ba? Tun ranar farko da ya fara siya ba chanji nace ma yaron da ya aiko ba chanji sai anjuma. Sai ya ce bakomai zai dawo gobe, washegarin da ya dawo na bashi chanjinsa bai karba ba. kuma Tun daga ranar dubu daya yake zuwa da shi cinikin 800 ya ke yi min 200 kuma chanjinsa baya taba Karb'a. Ko na aika da shi zai dawo da d'an aiken ne, kuma yaran gidan mu na son zama akofar gida da Safe haka saboda in ya aike ka ka fito sai ya baka Kudi. Ba ma su ba ni kaina ina jin dadin haka har acikin raina sannan sau biyu ina Tambayan Datti Yaro ne ko Babba ke aiko shi? Kai tsaye yace"Babba ne fa Tab" Sai da na yi Dariya ranar da ya Fad'amin haka. Jin yace ya na sauri ne yasa na ke hanzarin gama kwashewa na Fara sallaman shi, bansan fitowar Amma ba sai jin mganarta na yi a gefe na. "kawo na rika taimaka miki da zubawa" Na juyo da sauri ina fadin"Amma.." Bata samun zarafin mgana ba Habiba ta fito da shirin ta na tafiya makaranta, Ta na Fadin"Adda kudin tara zan tafi" Amma ce ta kwance hab'an zaninta ta Dauko mata naira Hamsin ta ba ta ta karb'a ta na fadin"Sai na dawo" Ni da Amma muka had'a baki muka yi mata Fatan dawowa lafiya. Robobin na mutane na tura ma Amma gabanta lokaci daya ina gayamata adadin yadda zata saka musu ni kuma na jawo kular nan mai kyau mai hawa uku yar doguwa da ita. kullum  aka zo da ita sai na Dagata na kallah tana Burgeni ban taba ganin kula mai kyan ta ba. Ashe Amma na lura da ni har na gama kallo na saka Danwaken na bi kuma Tsarinsa,Wake Dabam, Danwake Dabam sannan yaji dabam da mai. Ina gamawa na mikama Datti da ke Tsaye yana jirana kafin na yi mgana yace '"ya ce in ba chanji a bar shi kawai.." Mirmishi na yi na mika masa ya fice da gudu har ina lekensa Amma ta kalleni ta kara kallona batayi mgana ba sai da muka sallami mutanen da ke kanmu sannan ta kalleni tana Fad'in"Hala Danwaken waye? Cikin ko in kula nace"Bansani ba Amma. mee barin chanjin nan nasa ne ban taba ganinsa ba" Amma ta yi shuru kafin tace"To koma waye Allah ya yi masa albarka." na amsa da Ameen Ameem. Amma bata barni ba sai da muka gama Duka. Sannan ta barni ina Had'a kayan ita kuma ta tafi raban Fad'a Tsakanin Maman boy da Kaltume. Ire iren rigimrigimun gidanmu ba sa Damuna wlh na riga na saba. To abunda ya ke kamar Ibada ayi da Safe ayi da rana ayi da Daddare. Dambe ko tun zamanin baya an sha cin uban Dambe ballatana Dogon gida yana da karfin suna na Dabi'ar Fad'ace Fad'ace. Fad'an dai Kaltume ce  bata da gaskiya Kuma tsakani ga Allah halinta ne na Munafunci yi ma Mutane Labe in suna waya ko in sun yi baki. Shine ta yi ma Maman boy labe tayi wayarta da mijinta ta zo tana yad'ama su Maman Salihi wai mijin Maman boy neman mata ya ke yi. Taji maman boy nata fad'a a waya. Mgana ta famtsama agida har Maman boy taji shine ta Tada Rigima. Kaltume sai Rantsuwa ta ke yi ba ita ta Fad'a ba. Maman Salihi ma na Rantsuwan ita ta fad'a mata sauran na maida yadda akayi, Ina jin Amma na ta ba da hakuri Maman boy taja Daramam sai ta yi ma kaltume jina jina,abun takaici mijin kaltume fa na gidan bai riga ya fita ba ake wannan jidalin sai Dura manyan asharai suke yi ba dad'in ji, zagi Irin na ma su b'ata Tarbiyan in yaro yaji su. Shiyasa yaran su ba su da Tarbiya sai kaji munanan zagi a bakinsu ga rashin kunya. In ana irin haka Daki na ke shigewa yau ma haka nayi ina gama wanke wanke na kwashe komai na kai Daki Sauran Rushin kuma na saka mana Ruwan wanka. Ya zamu yi? Ba mu da wata mafita ammh gidan Haya ai ba gidan zama ba ne wlh. Ina fata da addu'an duk wad'anda ke gidajen Haya Allah ya Hore musu su yi na kansu. Mu kuma irin mu da muka d'and'ana rayuwar gidan kai kaddara ta kawo mu in da muke yanzu  sai nayi mana Fatan ganin karshen lamarin. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *08* Ranar Jumma'a tun safe suka shirya tafiyarsu a son samun Sadiq ma tun 6:30am na safe su bi motar Katsina. Ammh nukun nukun Tahir yasa sai dai suka wuce takwas na Safe a zariya. Kamar shima bai son Halin Tahir ba, da yace su had'a kayansu waje d'aya ya yarda da batunsa. Sai da ya gama zama ya shirya musu kayansu na tafiya a karamar akwatinsa. Da duk abunda zasu bukata na tafiyan kwana Hud'u, Ammh Tahir da iskancin sai bayan an gama shiryan kayan ya ke fito da Tsirfe tsirfe daga yace ya manta ba'a saka masa kaza ba, sai ya ce ba kaza zai je da shi ba Sadiq yaji kamar ya cire kayansa ya sauya jaka. Sai dai makaran da suka yi yasa ya yi Hakuri Tunda ya san Halin Tahir ya had'a kaya da shi. Motar katsina suka samu Direct sai sun je ne zasu Hau na cikin garin Daura. A motar KST irin mu cin mutane sha takwas din nan ne, Tahir gaban Mota ya shiga. Shi kuma Sadiq baya son matsuwa sai ya shiga kujerun baya na daga su sai Direba. Sun Dauki Hanya aka fara Hirarraki na cikin motar haya na abubuwan da ke faruwa a kasarmu. Tsadar Rayuwa da yadda komai ya sauya sai kuma aka gangaro kan yan sace sace da ake fama da shi na Mutane a hanyoyin mu na tafiye tafiye. Sadiq na jinsu bai saka baki ba. Saboda shi bai cika saka baki a irin wad'anan hirarrakin ba. Ammh Abun mamaki Tahir har yana zakewa ana Hiran yan kidanafin ya Dage yana ta zagin su yana Fad'in cewa ai yan iska ne sai sun ce a  basu kudin fansa an gama Biyansu kuma sai su kashe rai. Duk a motar Tahir ya fi kowa Zakewa muryansa tafi ta kowa amsa kuwwa acikin Motar. Har yana wani Tada jijiyan wuya Sadiq na ta so ya Juyo su had'a ido ya yi masa gargad'i ta cikin idanuwansa ammh ina Hira ta Rufe masa ido. Yasan mafita daya ce itace wayar Tahir yasan ba ta subucewa daga Hannunsa. Da Sauri ya tura masa da sako kamar haka "Tahir.. Tahir wlh ka kiyayi kanka ka na Daga murya in akwai su acikin motan nan fa? Ganin Sakon Sadiq yasa Tahir ya Dawo cikin Hayyacinsa. Sai ga bakinsa ya yi gum wani na gefensa har ya na tabosa irin acigaba da Labarinan ammh ina Sai Tahir ma ya fara barcin karya ganin Dannan wayar tasa ma bazai fisheshi ba. Kuma ya na kama bakinsa sai Hirar ta Sauya daga baya ma kowa ya cigaba da Harkan gabansa Daman Tahir ne uban yan Zakewa. A haka har suka isa katsina sha d'aya na Safe daganan suka sake samun motar Daura. Sai daya saura na rana suka iso Daura. Gidan su Tahir babban gida ne, na ginin kasa Inda yayyensa da matansa ke ciki da Sauran iyayansu da kawunansa. Tahir maraya ne ba uwa ba Uba hannun Kakarsa ya taso Hajja. Suna sauka da kayansu yaran yayyyen Tahir suka kyalla ido suka gansu suka zura cikin gida da Gudu suna murna Fad'i suke yi"Ga Baba Dahiru chan yazo. Hajjo ga Baba Dahiru." Kafin su ce me wasu yaran sun yayyayemesu har sun dauki akwatinsu zuwa cikin gida. Sai dai suka bisu a  baya suna shiga gidan Shashen Hajja na daga ciki ne sai sun wuce shashen matan gidan. Suna shiga sai tashin oyoyo Dahiru ke tashi sai dai kaji ana oyoyo Baba Dahiru mutanen Zaria. Sadiq Dariya ta kusa Shakesa yana kannewa da ganin yadda Fuskar Tahir ke yi in akace masa Baba Dahiru. Sai da suka gaggaisa da su sannan suka karisa Shashen Hajja. Allah Sarki tunda taji zuwansu ta kasa zama ta na Tsaye kofar dakinta tana Duban Hanya Tunda an shigo da kayansu dakinta. Suna shigowa ta washe bakinta cikin Tsananin Murna ta ke fad'in"Maraba da bakin Zazzau. Ah'a har da Saddiqu a she? Maraba lale da Saddiqu" Sadiq ya yi mirnishi ya karisa har gaban Hajja shi da Tahir ya rankwafa zai gaisheta ta saka Hannu ta rikosa tana Fadin"Haba Saddiqu mike mike..Ku shigo ciki maraba" Tahir ta kallah kafin tace"Dahiru maraban ku da zuwa' Tahir ya hura hanci kafin yace"Hajja wani irin Dahiru don Allah? Sunana Tahir..Sunana Tahir Hajja Ahto" Hajja ta make kansa tana Fad'in"Tafi d'an nema Dahiru muka sani mu dai ba wani Attahir ba" Me Sadiq zai yi in ba Dariya ba ya juyo yana kallon Tahir kafin yace"Dahiru shiga gaba mu je" Tahir ya balla masa Harara shi kuma yana Dariya ya bi bayan Hajja zuwa cikin Dakinta. Allah Sarki yar tsohuwar nan ta kasa zama saboda su kawo musu wannan kawo musu wannan Farinciki ya kasa barin Fuskata sai faman tambayansu take ya karatun ya'yan nan? Tahir na jin Haushin Daman sunan da ta daina kiransa da shi yace"Hajja sau nawa zan fad'a miki mun gama karatu Hidimar kasa muke yi yanzu..? Hajja ta ce'Yo ina ce duk karatun ne ko? Tahir bai kara mgana ba Sadiq ya bari da kara yi ma Hajja bayani. Ta washe baki kamar ta gane tana fadin"Yauwa na gane yanzu. Saddiqu ya wajen iyayen naka da sauran yan'uwanka? Ina kakarka? Sadiq yace"Duk suna gaishe ku Hajja." Daga nan suka bude hira tsakaninsu, Hajja da karfinta ba kamar Innani ba, Domin a shekarunta kasa da na Innani ne, ba ta wuce 70 haka shiyasa da karfi a jikinta sannan jiki ya saba da Wahala tuntuni ba kamar Inanni ba, duk dai itama ta yi zaman kauye ammh bata cikin Wahala. Ruwa kawai su ka sha sai Furar da ta Dama musu saboda jumma'a ne yasa suka yi alwala zuwa masallacin jumma'a suka yi sallah. Sai wajen uku suka dawo gidan chan suka had'e da yayyen Tahir suka gaggaisa suka kuma Dungumo zuwa Dakin Hajja a tare da aka gama cika shi da abinci kala kala na tarbansu. Sadiq ya saba zuwa gidan su Tahir tun suna makaranta ya saba da duka Ahalin Tahir kamar yadda shima ya saba da na shi Dangi. Kowa a gidan su Tahir yasan waye Sadiq kamar yadda Sunan Tahir ya yi tambari a gidan su Sadiq, tare suka had'u suka ci abinci Shi dai Sadiq Dambun Zogale ya ci Tahir kuma ya ci Taliya da Miya da Nama,Sadiq Naman kadai yaci saboda Nama na daga cikin abunda ya fi so duk Duniya. Sallar La'asar ya tada su suka tafi masallaci bayan sun fito kuma ba su dawo gidan ba, sun had'e da abokan Tahir tun na kuruciya suka zauna akofar gidan su Tahir suna ta Hira sai da aka kira sallar mangariba sannan suka tafi masallaci ba dai su suka dawo gidan ba sai bayan Sallar Isha'i. Suna shigowa suka iske kanwar Tahir mai bi masa Zulaihat tazo har da Girki ta yo musu. Tana ganinsu ta washe baki tana Fadin"Yaya Dahiru sai yanzu? Tun dazu nazo Hajja tace kun je masallaci' Tahir ya ware mata ido kafin yace"Ke.. ina wasa da ke ne? Ba na gayamiki ki daina kirana wani Dahiru ba Sunana Tahir" Hajja na saman Darduma ta na lazimi tace"Kaji tsirfan banza, da Dahiru ubanka ya yanka maka Rago. Shi muka sani kuma Shi zamu cigaba da kiran ka" Sadiq ya yi mirmishi yana Rufe baki ganin Tahir ya yi wani Fuska yana Huci Jikin Zulaihat ya yi sanyi sai ta Juya tana kallon Sadiq kafin tace"Yaya Sadiq sannun ku da zuwa" Ya amsa mata cikin sakewa yana Tambayanta ya gida da yaran. Tahir da kansa ya gaji ya saki Fuska, ballatana da ya Zulaihat tace alele ta yi ta kawo musu sai ya warware suna ta fira ballatana da yayyensa suka shigo suma aka had'e ana ta Hira ko da ba ma su kudi ba ne ammh akwai kaunar junansu da kyakyawan zumunci a Tsakaninsu. Sannan da shakuwa da kaumar junansu musamman Tahir da suke ganin shine karamin su Tunda Zulaihat ta yi aure ta gina na ta iyalan. https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Sai karfe sha daya suka watse su ma sallama suka yi ma Hajjo suka dauki kayansu zuwa Dakin Tahir na cikin Shashen Hajja daman nan suke sauka Daki ne irin na yan kauye dai. Tsaf an gyarashi Inda Sadiq ke da Tabbacin Hajja ta gyarashi ammh Tahir ai son jikinsa da kazanta bazai barshi ya tafi ya barki Dakin a gyare ba. Sakamakon sun gaji kuma ba su samu Hutu ba yasa ba su bata Lokaci ba suka bi lafiyan Katifar Tahir wata yar yaloliya da ita. Ba su farka ba sai asuba Da asuban ma Sadiq ne ya tashi Tahir kamar yadda suka saba ko achan baya. Bayan sun dawo sallar asuba suka koma barci ba su tashi ba sai goman Safe shima Hajja ce tazo dubasu tana Fadin barcin su ba na lafiya ba ne su tashi hakanan, ita ta saka musu ruwan zafi dukkansu suka yi wanka suka sauya kaya sannan suka shiga Dakinta suka karya. Sun iske kayan karyawan su kala kala daga Dakunan matan yayyen Tahir har Zulaihat ta yo musu kunin gyada da Fanke shi Sadiq ya ci Tahir kuma Tea ya sha da Buredi. Sannan suka kwanta Dakin Hajja suna ta Hira. Tahir kan gadon karfen Hajja ya yi Dare dare yana charting shi kuma Sadiq na zaune samar Darduma a tsakar daki yana taya Hajja bare gyada suna ta hira in ka shigo ka gansu sai ka yi Tunanin shine jikan nata Tahir ne bakon. Sai da abokin Tahir Jamilu yazo ya jasu suka fita zuwa gidansa ya yi aure Tahir din na Zaria. Chan suka je amarya ta yi musu abinci sai a hankali Tunda karamar yarinya ce Tahir sai shakiyanci ya ke yi ma abokinsa wai ya auri kwaila. Sadiq na kare ma Jamilu Tahir ya kallesa yace"Dole ka kare masa mana. Tunda duk tafiyar ku daya ce" Sadiq yace"Eh mun ji din". Ya na da sakin jiki sosai Tun farkonsa Daman mai son mutane ne kuma ba shi da Bakunta ballatana amincin da ke Tsakaninsa da Tahir ya wuce duk yadda Mutane ke Tunani a kansu. Ranar yini suka yi ziyarce ziyarcen gidajen yan'uwan Tahir har gidan Zulaihat sun je ta yi ta rawan jiki da su Sadiq yace Danwake zata yi masa. Shi kuma Tahir yace ta Dafa masa kwai. Sadiq ya zunguresa ya na fadin"Wai ajiyan kwan ka bata da zaka ce ta dafa maka? Tahir yace"Kai ajiyan Garin Danwaken ka bata da kace tayi maka"? Da ya ke ta na jinsu sai ta yi Dariya kafin tace"Kowa zan yi masa abunda ya ke so" haka ko akayi kowa ra'ayinsa ta yi masa Mijinta ne kuma yace duk abunda suke so ta yi musu Daga karshe Tahir nata Fad'an meyasa ta yayyaka ma Sadiq kwai a cikin danwakensa Tunda yace shi baya cin kawai Sadiq yayi masa bakam yana cin Danwakensa yana Santi. Sai Dare Hajja ta gansu sai fad'a take yi tana fadin"ina kuka shiga ne yau? Tun dazu na gama Tuwon. Yan'uwanka sai zuwa neman ku su ke yi bakwa nan" Sadiq ne ya ke fad'amata inda suke je yau tace sun kyauta sun yi ziyara. Ba su ci tuwon ba sun koshi sai dai Sadiq yace ta yi masa Dumame da Safe. Sai adaran Sadiq ke fad'ama Hajja da Safe Gusai zasu je. Ta fara fadan ba su gayamata da wuri ba nan da nan ta mike ta fara had'a abunda ta ke da shi Wanda zata bama Sadiq ya kai ma iyayensa. Tun safe suka shirya kafin Takwas sun karya ,sun kuma shirya tsab Hajja ta bama Sadiq leda cike da su kuka,kubewa garin kuni,zogale danya da wacce ta bushe kayan kamshi sai aya mai kyau ta ce a kai ma Innani. Yayyen Tahir har tasha suka rakasu suka ba su 10k. Sadiq dai bai isa ya ce komai ba tunda ko ya yi mgana ba za su saurareshi ba. Da zasu tafi Kasim wanda shine Babba ya Dafa kafad'ar Sadiq yana Fadin"Ku kula Sadiq. Allah ya tsare ku mungode Allah ya bar zumumci" Sai da Motarsu ta tashi sannan suka koma gida. Da wuri suka isa Gusai, Sadiq sai yaji wani irin iska farinciki na shiga jikinsa da gaske ne ba gida kamar gidan ku. Ba kuma gari kamar garin ku, daga nan suka samu abun hawa zuwa Tudun wadan Gusai. Lokacin da Sadiq ya Buga makeken get din gidansu Mallam Tajudeen ya Bude get din ya gansa sai ya washe baki cikin Tsananin Farimciki yace"Ma sha Allah. magajin gida barka da sauka. Mallam Attahiru maraban ku da zuwa.." Sadiq ya yi mirmishi ya na Dafa kafad'an Mallam Tajudden kafin yace"Mallam mun same ku lafiya? Daidai Lokacin da ya ke kokarin karban Jakar hannunsa sai ya hanasa ya noke yana fad'in"A'a kai fa malamina ne me yasa zan bari ka karban min kaya? Mallam Tajudden ya yi dariya kafin yace"Ammh ni a karkashin mahaifinka na ke. Biyayyata a gareka Dole ce" Sadiq bai ce komai ba ya mikamasa Akwatin ya karba da Sauri ya sake Bude musu kofar suka shiga Tahir na Binsa a baya Lokaci daya yana fad'in"Mallam Taju Tahir fa sunana ba Attahir ba." Da Sauri Sadiq yace"Ko Dahiru zai ce? Tahir ya tokare shi da takalminsa ta baya yana Fadin"Uban Dahirun" A tare suka saka Dariya shi ko Malam Tajudden da gudu ya shege shashen Innani Saboda yasan itace ta Farkon da ya kamata tasan magajin gida ya dawo. Suna tafe a haraban Gidan Sadiq na kallon Motocin da ke fake a Haraban gidan cikin Tsananin kewa ya ce"Abba na gida  kasan yau weekend ko zai fita sai yammah." Tahir ya bi motocin da kallo. Shi fa har mamaki yake in yaga Sadiq a wani wajen na wata irin rayuwa. Sai ya Tuna mahaifinsa da gidansu da Duka Danginsa sai ya rika mamaki gata iya gata ba wanda Sadiq bai mallaka ba Motar hawa ko wace iri ya ke so zai hauta ammh in ka ganshi a yana yawo da kafarsa a layi sai ka rantse bai taba ganin Mota ba. Muryan Sadiq dai ta katsesa sanda ya ke fad'in"Kaga fa Tahir akwai baki a gidan nan. Wacan kamar Motar Yaya Sa'im" Tahir dai sai dai ya kallah baya mgana suna tafe suna bangazan kafad'an juna kuma suna tafiyan wahainiya. Tahir ya juya baya ya kara kare ma girman gidan kallo da girman Shashe shashe na gidan da irin kayan alatun da ke cikin gidan sai ya koma ya bi Sadiq da kallo da ke tafiya zuwa Shashen Innani. Kawai sai ya girgiza kai ya kara d'an gudu ya cimmasa lokaci daya yana Fad'in"kamar ba daga gidan nan ka fito ba" Sadiq sai ya murmusa kafin yace"Mutane da yawa haka suke dauka" Tahir ya kallesa kafin yace"Dama ni ne kai Sadiq" Da Sauri Sadiq yace"Tahir ka zama mai godema Allah da Ni'imarsa sai ya kara maka." Tahir ya yi mirmishi kawai bai yi mgana ba. Sun kusa isa kofar Shashen Innani kenan sukaji mganarta fad'i take yi"Kai Mallam Saju ba'a san malamai makada Annabawa da karya ba. Ka Rantse Kwarankwatsa Magajin gida ne ka gani" Sadiq ya kalli Tahir shima ya kalleshi suka fashe da Dariya. Da sauri sauri suka nufi Shashenta suna shiga suka isketa Tafe da Sandarta ga gilashinta a Fuska Mallam Tajudden na gefenta. Daga bayanta kuma Siyama ce da Sultana sai yaran Sa'ima su Abadallah. Daman suna Shashen nata ne Tun Safe da Abba da Umma tare da Mama suka shiga gaisheta bayan Taba Hira sai suka tafi Shashen Abba suka barta da Sultana Daman yar gidanta ne ko Innani bata ga kowa ba bata cika Damuwa ba. Tafi damuwa da in bata ga Sulsana ba acewarta ba. Sa'ima ce tazo tafiya da yaranta da tazo gaishe da Innani suka zo tare da Siyama shikenan ta bar su nan ta koma Shashen uwarta. Ko da Mallam Tajuddeen ya shigo da akwatin Sadiq yana ma Innani albishir ga Magajin gidan ne sai Masifa take yi da faman tambayan ba Sa'imar ta zo ba? Ta kwashi ya'yanta ta tafi mana sun gaji da su. Siyama yarinya ce sa'ar Sultana sun riga sun san Halinta ba su bi ta kanta ba. Innani duk son ta da bako to in yazo gidan Sulaimanu kada ya wuce kwana uku komai mutumcinku da taga ka share kafa zata fara sakin Manganganun an zo an dora ma Sulaimanu nauyi Allah na Tuba shima Rufin asirin Allah ne ba shi da shi. Ko da kuwa jikokinsa ne tace ai suna da Gidan Ubansu su zauna chan mansa. Innani ba ta yarda da Mallam Tajuddeen ba shiyasa ta mike kamar ta kifa tana ya rantse dai da gaske Magajin gida ya gani. Ko a yanzu din ma bata lura da shi a gabanta ba, sai Faman fadi ta ke Mallam Saju ya rantse kada yazo karya ya ke mata. Sultana ta bayan Innani ta ke lekowa tana kallon Yaya Sadiq shi kuma Hankalinsa na wajen Innani yana ta mata mirmishi Siyama ta Buga Ihu ta nufesa tana Fadin"Wlh Innani da gaske Yaya Sadiq.." Ta fad'a jikinsa cikin Tsananin murna Su Abdallah ma suka nufesa suna fadin"Uncle.." Rikesu ya yi gabadayansu yana Dariya Innani sai ta rikice ta fara fadin"Ke don uwarki Siyama Ina magajin gidan" Sadiq ya saki su siyama ya karisa ya rike Sandar innani ya saka Hannu ya ciro glass din idonta ya goge mata sannan ya maida mata Lokaci daya yana Fadin"Ga ni nan fa Tun dazu a gabanki Innani ko dai har yanzu Idanuwan naki da sauran gyara bakya gani Innani" Ai jin muryan Magajin gida ya Rikita Innani ta rikesa gam cikin Lalube tana  Fadin"Allahu Akbar Abubakar Saddiqu dai a gabana."Sai ta fashe da kuka tana fadin"Yau dai ga magajin Sulaiman ya dawo. Dole na damu kwana nawa bamu yi mgana ta wayar zamanin nan ba. Sulaimanu fa kai kadai garesa magajinsa Dole na shiga Damuwa in ban jika ba" Rumgumeta ya yi yana Fadin"Innani ina nan lafiya. Ai na gaya miki Hidimar kasa na ke yi achan Zariya ko..? Innani tace"Eh haka kuma kace to yanzu daga chan Zariyan ka ke? Kai tsaye ya juya yana kallon Tahir wanda ya Dauki Afiya. Ya nuna mata Tahir kafin yace"Daga Daura muke. Tare da Tahir muke" Innani ta yi shuru ta na bin Tahir da kallo kafin ta yamutsa fusaka tace"Waye  kuma wani Sahir? Sadiq na Dariya yace"Attahiru abokina Innani" Ai sai ta washe baki tana Fadin"A'a dan kwalba uba kace Attahiru naga ya yi wani fari ne kuma shine don sheganta bai zo ya rumgumeni mun yi masa Oyoyo ba." Sadiq ya kalli Tahir ya na Dariya Shima Dariyan ya ke ya Sauke Afiya ya Nufi Innami ya Rumgumeta yana Fadin"Allah ya bar mana Ran Innaninmu" Ta make kansa tana Fadin"Kaji dadin Tsokana ta ko" Dariya ya saka idanuwansa na kallon Sultana da ke bayan innani kanta na kasa ta na wasa da gefen Hijabinta. Da karfi yace"Sultana daman kina nan? Ya makaranta" Sai alokacin Sadiq ya ganta kallo Daya ya yi mata bai yi mamakin Tana wajen bai sani ba. Yarinyar ba ta da Hayaniya ko kadan. Yana mamakin yadda ta so ta zo daya ma da Innani. Sai a lokacin ta gaishe shi ya amsa cikin Sakewa kadahan kadahan. Ta kuma gaida Tahir ya amsa yana Tsokarta da Matarmu.. Tana jin haka ta ruga da gudu tana jin kunya Sadiq ya Take kafar Tahir yana Hararansa da ido shi ko ya yi kamar bai gani ba. Innani ta tattara su sai Shashenta bayan ta ce ma Siyama"Maza je ki gayama iyayen ki ga Magajin gida nan da Attahiru a kawo musu abinci. Ta juya ta na kallonsu suna zama a kujerun falonta domin Dakin Innani ko amarya ta sameshi to sai Hamdala. Sadiq ta kalla kafin tace"Magajin gida me zaka ci ne a kawo muku? Kai ne baka fadi kuna hanya ba  da Tun Safe na hana

Chapter 9 of 24