Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
su ba sannan bai yi mgana ba. Da sauri ya kara kiran sunansa ya na fad'in"Kana jina? Sai alokacin Sadiq ya bude idanuwansa da suka koma gauta saboda ja. Cikin Tsoro Tahir yace"Baka da Lafiya ne? Sai Sadiq ya samu kansa da Dagamai kai Lokaci d'aya ya na fadin"Ba ni da lafiya Tahir. Ba ni da lafiya." Cikin wata irin murya da ta kara Tsorata Tahir da Sauri yacr"Me ke damunka Zazzabi? Ya fad'a lokaci daya ya na Tattaba jikin Sadiq. Shi kuma sai ya kara mulmulawa saman kafita cikin nishi yace"Rufamin abun rufa sanyi nake ji." Jiki na rawa Tahir ya mike ya Dauko Bargon Sadiq ya lulluba masa ya na fadin"Maleria ce inaga. Ka dan huta zuwa anjuma sai ka tashi ka sha magani bari na fita na karbo maka a wannan chemist din" Bai jira cewar Sadiq din ba ya mike bayan ya zare ma Sadiq din takalmin kafarsa ya maida ma'ajiyar takalman sannn ya dauki kudi a jakarsa ya fita Lokaci d'aya ya na jawo ma Sadiq kofar dakin Sadiq ya dago ya na bin kofar da kallo kansa ya Dafe da hannu bibbiyu lokaci d'aya ya na fadin"Dama ace.  Dama ace. Daman tun farko na fad'i gaakiyata  da duk ban shiga wannan halin na Tsaka mai wuya ba." Ya karishe fad'a kamar ya fashe da kuka. A lokacin tunani da Hankalinsa ne ya ke jin ya rasa gabadaya. FAA'ALUL LIMA YURID LAIN YUSIBA NA ILLAMA KATABALLUHU LANA. Kuyi hakuri an samu kuskure a shafi na sha bakwai wajen Rubutawa, keyboard d'ina ke sauyamin Haruffan rubutuna. Da masu ganin Gusai suna tunanin wani gari ne, suma su kula Gusau ne ba Gusai ba. Nagode. *Janafty* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* *FATAN ALHERI DA SAKON GODIYA ZUWA GARE KU* *AISHA MUHAMMAD ALTO(SISINAH)* *MARYAM JUMARE* *NANA HALIMA(MASOYIYA)* *HAFSAH HAFNAN(SAHIBATU)* _*Nagode muku bisa yadda kuka yi ta Hidima da wannan littafin, HasiyarAssadiq tace ta gani kuma ta yaba, Innani kuma tace dukkan ku Allah ya yi muku albarka Amin*_ *20* Sai bayan Fitar Tahir yaji wani mugun zazzabi ya kara rufeshi. Nan da nan ya fara rawan Sanyi Hakoransa na had'uwa waje d'aya. Kansa kuwa kamar zai Tsage gida Biyu Tsabagegen yadda ya ke sara masa, jijiyon kansa sun mike gabadaya Rad'au a saman kansa saboda Halin da ya ke ciki. Idanuwansa biyu Tahir ya dawo da magangunan da ya siyo masa. ba domi  Tahir ya taimaka ya tada shi zaune ba ji ya yi kamar bazai iya ma tashi ya zauna da kansa ba. Tea mai kauri Tahir ya had'a masa yace bazai sha ba , shi kuma ya lallabeshi kan ya samu ya sha saboda ya samu sha mgani. Dalilin haka yasa ya sha kad'an ammh ji ya yi ba dad'i kamar ya na shan mad'aci saboda bakinsa da ya zama wani takaf kamar wanda ya yi shekaru cikin jinya. Tahir ya ballo masa magungunan Paracetamol ne sai maganin maleria d'in nan mai warin kudin cizo. Shi ba ya son magani ya fi shiri da Allura ammh Bala'in Tahir yasa sai da ya sha magungunan gabadaya sannan ya kyalesa ya koma ya kwanta Lokaci d'aya ya na kara taba goshinsa jin har lokacin da zafi. Ya dad'e barci bai daukesa ba ya na jin Tahir bi ni bini sai ya lekosa ya na masa sannu tun ya na daga masa kai in yajisa har wani wahallalen barci ya Daukesa mai cike da Tararradi da zullumi. Bai san haka ya yi barci sosai ba sai da ya farka cikin ikon Allah yaji zazzabin jikinsa ya sauka sai dai sarawan kan kad'an. lokacin da ya yunkura ya mike sai yaji ba jirin Tunda ga shi har ya iya mikewa da kansa batare da taimakon kowa ba. Tahir ya kallah da ya kwanta a kasa wayarsa na saman cikinsa kila wajen Dannan wayar ne barci ya Daukesa bai sani ba. Yasan ba shi da laulayin yawan ciwo sai ya jima bai yi ciwo ba, in ko ya yi Ciwo sai dai ko ciwon kai in ya yi Tsanani ne zazzabi shi Allah ya Tsare shi da ciwukan zamani irin su Ulcer ko Typiod. Jin ya samu karfin jiki yasa ya dibi Ruwa a buta bayan ya Dauki karamar wayarsa ya kunna Fitila. Ruwa ya zuba a karamar buta sannan ya yi addu'a ya bude kofa ya fita daidai lokacin da karfe uku na dare ta cika a wayarsa. Ba shi da tsoro daman Tahir ne ke tsoron Fitan Dare ba Sadiq ba shi da ko a gida ko karfe nawa ne zai iya fitowa Haraban gidan su in yaji wani motsi to anan ma shi ke raka Tahir in lalura ya tashe shi cikin Dare. Kai Tsaye makewayi ya haska ya shiga ya kama ruwa sannan ya fito a tsugunna a kan damdamali ya yi alwala sannan ya koma Daki har Lokacin Tahir na ta barcin bai ma san ya tashi ba. Darduma ya shimfida bayan ya cire kayan jikinsa ya saka wata farar Jallabiya ta mutanen Saudiya. Yasan akwai sallar mangariba da isha'i da ke kansa ba shi su ya fara yi kafin ya mike ya yi salla raka'a Biyu ya jima acikin Sujjuda ya na ta addu'a sannan ya Dago ya yi tahiya ya sallame nan ma d'in ya jima ya na kirga da hannunsa kafin ya daga hannunsa sama ya na addu'a na tsawon wani lokaci sannan ya shafa. Bai koma kan katifar  ba sai ya kishigid'a saman darduma ya na jin Kwakwalwarsa ta na shiga wasu Tunane Tunanen da a dazu kwata kwata ta tsaya cak. Iya hangen nasa ya gama Hango masa aikata Rokon Amma daidai ya ke da rasa goyon bayan wasu daga cikin Ahalinsa. In yace kuma ya shawarce su ya bata komai domin ba bu wanda zai rama masa baya acikin wannan Halin da ya ke ciki. A cikin zuciyarsa ya cika da Tausayinsu kuma ya na so ya taimaka musu ammh bukatar Amma ta yi tsauri ta kuma saka masa wani irin Dabaibayi ne mai wuyan fita. Ga shi ya riga ya furta tun farko shi maraya ne babu yadda za'ayi kuma daga baya ya sauya mgana. Tunanin mafita kwakwalwarsa ta Zurfafa aciki ammh sai dai har barci ya kwashe shi bai samu wata mafita mai kyau ba duk Mafitan da ya hango sai yaga bazata bulle da shi ba. Acikin barcin nan da ya koma sai ya yi mafarki ko nace kamar Allah ne ya nuna masa sakamakon zabin da ya mika garesa. Ganinsa ya yi a wani Daji ba gida gaba ba gida a baya. Shi kad'i ya na ta faman bulayi ya rasa hanyar da zata fitar da shi Kamar daga sama yaji an kwala masa kira ya na juya sai ya ganta wata Doguwar mace ammh kuma ta saka mayafinta ta yane Fuskarta ba ya iya ganin kamaninta sai dai kwayan idanuwanta. abun mamaki kuma da Tsohon ciki a jikinta. Ya na ganinta sai ya yi Saurin karisa gareta ya riko hannunta suka fara tafiya tare. Ba zato kawai sai ga Sultana ta sha gabansu ba ta tsaya ba ita ta saka karfinta ta raba Hannunsu waje daya ma'ana ta raba tsakaninsu ita ta shiga Tsakiyarsu ta jimke hannunsa ta ja shi suka cigaba da Tafiya. Waiwaye ya ke yi ya na kallonta ta na kuka ta na nuna masa bata da kowa da ita da abunda ke cikinta sai shi kada ya tafi ya barta. A cikin mafarkin yaga sanda ya kwace hannunsa acikin na Sultana ya ruga a wajenta ya riketa gam! Sultana na ganin haka sai ranta ya baci ta kara Dawowa zata rab'asu sai ba ta yi nasara ba, shi baisan ko daga ina ba ne? Yaga dai gabadaya yan'uwansa sun yi layi a gabansa da taimakon su suka raba hannayensu suka saka masa a na sultana shi kuma sai ya had'a da hannun wacce bai ga Fuskarta ba ya rike tare da na Sultana. Umma ce ta bayyana gabansa ta kwace hannun Sultana ta fara tafiya da shi sai sauran yan'uwansa suka mara mata baya. Yaga har da Abba shima bai bi bayansa ba ta karshen itace Innani ita ta jima a tsaye ta na kallonsu sannan ta juya ta bi bayan su Abba suka bace masa daga Daji nan da ba kowa daga shi sai wannan yarinyar da bai ga fuskarta ba. Gudu ya ke yi ya na ta kiran sunan Abba da Umma ammh ko me kama da su bai gani ba Sai yaji wata murya da ya na jinta yasan ya santa ta kira shi da karfi. "ASSADIQ.." Yana juyowa sai idanuwansa ya gane masa itace. Abunda ta yane fuskarta da shi ya yaye da kansa ta bayyana a gabansa ta na masa mirmishi. Har gabansa ta kariso ta dauki hannuwansa guda d'aya ta Dora saman cikinta sai yaji motsi kamar abunda ke cikinta ne ya motsa a fizge yaji kalaman ta" Ni da abunda ke cikina ba zamu taba barinka ba. Zamu zauna tare da kai sannan zamu tayaka dawo da sauran Ahalin ka." Hasken Fatar ta ya haske masa ido da yasa ya farka a firgice gabadaya jikinsa ya jike da Zufa. Cikin Fitan Hayyaci ya Furta "HASIYA." tabbas Hasiya ya gani da Tsohon ciki? Me wannan mafarkin ya ke nuna masa. Wannan mafarkin ya na nuna masa Zahirin abunda zai faru matukar ya aminta da bukatar Amma zai rasa Sultana sannan zai rasa duka Ahalinsa gabadaya. Sannan ya nuna masa amsa Bukatar Amma zai iya zama alheri garesa ammh kuma kafin cimma haka akwai tarin kalubale sannan zai iya jefa rayuwarsa cikin Tsaka mai wuya da Halin k'ak'ani k'ak'ani. Ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya ya na Share zufan Goshinsa. Wayarsa da ke gefe ya laluba ya kunna sai yaga biyar da minti goma na asuba shiyasa yaji ana kiran salla a wasu masallatan. Kansa ya koma ya dafe a fili ya sake Furta"Hasiya." Wanda kamar acikin barci Tahir yaji sunansa ya mike a razane ya na fadin"sai naji kamar kana ambatan sunanta? Ya fad'a ya na haske Sadiq din da fitila a saman gado sai kuma ya tsince shi shima a kasa kusa da shi. Cikin alamun barci a idon Tahir yace"Sunan Zabiyar yarinyar nan naji kana ambata. Na shiga uku Allah yasa ba itace ta ka maka ka ke kwance ba Lafiya ba." Cikin mamaki Sadiq yace"Ita wacece ta ka mani? Tahir ya mike ya na mutseke ido kafin yace"Ita Hasiyar da naji ka na kira ko ba sunan wannan zabiyar yarinyar kenan ba.? Karamin Tsaki Sadiq ya ja kafin ya yunkura ya mike Lokaci daya ya na Fad'in"Man ni naji sauki fa." Tahir ya dafa sa lokaci d'aya ya na Tattaba goshinsa da wuyansa lokaci d'aya ya na fad'in"Eh naji jikin ka ba Zafi sosai kila taga bazaka ciwun mata ba ne yasa ta sake ka" Sadiq ya kyalkyalce da Dariya lokaci d'aya ya na Dafe kansa saboda Saramai masa da ya yi. Tahir ya kallah kafin yace"Tahir.. Tahir.." Ya ke fad'a ya na kallonsa Tahir yace"Wlh da yanzu zan nemota duk inda ta ke ta tsallaka ka muguwa kawai." Ya na wucewa wajen kayansa ya ce ma Tahir"Ba fa mayya bace Tahir. Kowa da irin tashi kaddaran" Tahir ya karkace baki yace"Maita fa gaskiya ne." Kai Tsaye Sadiq yace"bamu san maita a addininmu ba. Mu kambun baka kad'ai muka sani maita kuma da ka ke mgana duk Aljanu ne su ke yin abun su da aikin Tsaface tsaface irin nasu" Daganan bai kara mgana ba ya Dauki Buta da Sauran ruwa ya bude kofa ya fice ya bar Tahir na mgana bai tsaya jinsa ba yasan ko kwana ya yi ya na mgana Tahir bazai aminta da mganarsa ba ya riga ya gama aminta da duk abunda aka Fad'a masa. Shi kuma cikin bayanan Amma ya Fahimci Rayuwar Hasiya ba komai cikinta sai Kaddara da ke Dawainiya da ita haka Allah ya tsara mata komai in zai Faru da mutum daman akwai Sanadi. Kuma ita sai ta kasance itace Sanadin na su kaddaran shiyasa ta ke Fuskatar kyama da Tsagwamma. ******** Na gama zura ma Amma ido ko zata min mganar abunda ta tattauna da Assadiq ammh kuma har muka yi shirin kwanciya ba ta ce min komai ba. Sai da na yi mata shirin kwanciya sannan na zauna a gefen kafafunta ina Shafa mata man zafi a kafafunta tunda tace sun rike mata. Ina cikin Shafa mata ina ta so na yi mata mgana ammh na kasa sai na yi kamar na yi mata mgana sai kuma na kasa. Dakyar na yi karfin halin kiran sunanta"Amma.." Ta amsa da cewa Umh. Kallonta na yi cikin wani yanayi kafin nace"Amma me kika fad'a ma Assadiq? a  kaina ne? Amma ta yi shuru ta na kallona kafin tace"Me yasa ki ke son sani? Kai Tsaye nace"Ina Son sani ne kawai Amma." Mirmishi ta yi kafin ta Dafa kafad'ata ta na Fad'in"Kada ki damu. In abunda na rokesa ya ji rokona ya amshi Bukata ta zaki ji komai zuwa da Safe. In kuma bai amimce da Rokona ba har Abada bazaki taba sanin me muka Tattauna ba." Cikin mamaki na kalleta kafin nace"Amma." Kai ta gyad'amin tare da mirmishi da ya Kashe min baki. A sanyaye na gama shafa mata man zafinta sannan na gyara mata kwanciya. Hannuna ta rike ta na fad'in"Khairan in sha Allahu Hasiya." Jinjina mata kai na yi batare da mganarta ta shiga jikina ba. Mamaki na ke yi wata mgana ce wannan da Amma ta kasa Fad'amin? Da farko na dauka Labarin abubuwan da suke faruwa da ni ne sai daga baya kuma na Fahimci wata mgana ne ta Dabam. Barci na a ranar rabi da rabi ne duk sanda na farka sai na hangi Amma saman Darduma ta na sallah. Na fad'a daman ba ni da kokarin sallar Dare shiyasa har akayi asuba ban iya tashi ba har sai da Amma ta tasheni sannan na iya tashi ina kallonta ina jinjina abunda zai hanata barcin na tsawon Dare duk da nasanta ta na daga cikin mata masu kokarin Ibada ammh bata kaiwa har dare ya fara ya kare bata yi barci ba Sai zargina ya tabbata da cewa tabbas akwai wani abu da ke faruwa wanda bansani ba. Jikina a sake na tashi da shi, Amma kuma ta lura ammh kuma ba ta min mgana ba sai dai na lura da wani abu tunda garin Allah ya waye Amma ke duban hanya kamar ta na jiran wani ko wata. da ta ji sallama sai ta leko har na nagaji nace mata wa ta ke nema tace min bakomai. Cikin ikon Allah mun gama karyawa kenan sai ga Hamma Isuhu ya diro ba makawa tafiya ta tabbata a ranar kenan Tunda yace tare da wani mai Motar da zai daukan mana kaya suka Taho dagachan ya Dauko Itace ne zai shiga cikin gari ya sauke sannan sai yazo ya kwashemu mu da kayanmu. Jin haka yasa Amma tace na kira su Adda na fad'a musu su zo mu yi sallama. Da wayar Maman Boy na kira su, nace Adda Fati ta kira Inna Talatu da Ramatu ta sanar da su. Daganan sai na fara wanke yan kanukan da muka bata da Safe daman kayammu suna kammale waje d'aya. Isuhu ko na ciki suna Hira da Amma na wani Lokaci kafin yace Amma bari ya shiga cikin gari ya dawo lokacin mun gama fitar da komai zai kira mai Motar in ya gama sai su dawo tare. Na kasa Fahintar yanayin fuskar Amma a lokacin. Ta na dai zaune ta na jan Cashaba ni ce na ke kazar kazar ina had'a mana sauran kayan sawan mu da kayan amfanin da na fito da su. Su Adda ba su tsaigaita nan da nan sai ga su sun taho cikin Damuwa da jimami. Adda Rukayya ma ta riga Adda Fati zuwa ita da ya'yanta duka haka itama Adda Fati har da mijinta Inna Talatu ce ta zo daga baya sai Ramatu ma ta rigata zuwa. Kowa kagani jikinsa duk ya yi sanyi na ganin tafiyar fa da gaske ne. Ni na had'a gawayi na saka mana Ruwan zafi Amma ta fara yin wanka sannan ni nayi daga baya. Na saka wani leshi na cikin kayan Abubakar ne mai Riga da zani, Amma kuma ta saka wata atamfarta da Adda Fati ta Dinka mata, ta kuma koma ta zauna ta cigaba da jan cashabanta duk hiran da su Adda ke yi bata saka musu baki ba. Tuni har yan gidanmu sun aikama Makota cewa yau zamu tashi sai shigowa su ke suna mana sallama. Ba wanda ya damu da yanayin Amma kowa ya na zaton cewa Saboda sabo me yasa jikinta duk ya yi sanyi ba ta walwala. ****** Ya gama Had'a duka Tunaninsa da Hangensa mafita d'aya ce kuma ita ya Tsaida har acikin ransa yasan Allah yaga kyakyawan Niyyarsa na Alheri da taimako kuma ya na da yakinin bazai barsa ya tabe ba. Bai yi wani yunkuri ba sai da suka dawo sallar azahar shi da Tahir saboda saboda zazzabin da ya yi yasa shi bai je wajen aiki ba Tahir ma bai Fita ba. Suna dawowa sallah daman akwai wuta ya saka ruwan wanka a Kittle sai da ya yi zafi sannan ya juyo ya yi wanka Tahir na kwance ya na ta Chart a wayarsa. Sai da ya fito yaga ba shi da Niyyar tashi sannan ya ce masa bazai yi wanka ba ne? Tahir ya dago ya na kallonsa kafin yace"Sai anjuma zan yi." Sadiq ya kallesa kafin yace"Ka tashi ka yi zaka rakani wani waje ne." Tahir yace"Ina.? Sadiq sai ya yi masa banza bai yi mgana ba Tahir ya mike ya na mika kafin yace"Ka samu kanka kenan za'a fita? Da Eh Sadiq ya amsa masa daidai Lokacin ya na bude akwatinsa. Tahir shi kuma sai ya juyo ruwan da Sadiq ya saka masa shima ya fita zuwa wanka. Ya yo wanka kenan ya shigo Dakin ya iske Sadiq ya ci gayunsa cikin wata shadda mai ruwan madara sabuwa ce ya na Tunanin ma bai taba sakata ba. Abun mamakin har da Hula dara  mai yanayin aikin jikin kayan sannan ya sanya takalmi budadde na Fatar damisa sannan ya na tashin kamshin Turare. Yana cikin karya Hulan kansa Tahir yace"Daurin aure zamu je ne? Kai Tsaye Sadiq yace"Kamar ka sani." Tahir yace"Ikon Allah Daurin aure ranar Laraba ko dai Bazawara ce.? Kai Tsaye Sadiq yace"Eh.!" Tahir ya tsaya ya na kallonsa kafin yace"Eh fa kenan bazawara ce? To kai ya aka yi ka santa? Sadiq yace"Zan sani mana." Tahir na goge jikinsa da Towel yace"Nagane kila abokin aiki ka ne ko? Sadiq ya daga masa kai Lokaci d'aya ya na Dora wani brown din Agogo na Fata mai kyau da yarari lokaci d'aya ya na ce ma Tahir"Ka yi sauri.." Tahir yace masa Toh yanzu zai shirya. Jin haka yasa Sadiq yace bari yaje ya ciro kudi ya dawo fita ya yi ya ganganra bakin Titi wajen masu POS ya ciro kudi ya Tura cikin Aljihun wandonsa. Ya jima Tsaye a wajen ya na sauke Numfashi kamar mai ciwon Asthma. Wata zuciyar tace"Anya Sadiq abunda zaka aikata daidai ne? Baka ganin cin Amanar yardan iyayenka ne? To ammh ya zai yi? Tausayi ne ya cikamasa Kirjin da ya kasa tankwafar da wannan Rokon sai dai yana da nashi lTsarin da Sharadin har ya yi wannan abun ya gama shi babu wanda zai sani daga cikin wani Ahalinsa sai Tahir shi kuma yasan in ba shi yace ya yi mgana ba Tahir bazai taba cema kowa komai ba. Da haka ya gangara ya koma ya na zuwa ya ga Tahir har ya fito shima cikin Shigan manyan kaya. Kofar su suka kule sannan suka fara Tafiya Tahir ya dauka bakin Titi suka nufa ammah sai yaga sun nufi cikin anguwa. Kai Tsaye yace"Ya na ga haka? Ba abun hawa zamu hau ba? Sadiq na cin mgani yace"A'a." Tahir ya kallesa bai samu zarafin mgana ba yaga Sadiq ya ciro wani bakin glass mai Duhuwa ya kwafa a Fuskarsa saboda batar da k'wayan idanuwansa da zasu bayyana asirin yanayin da ya ke ciki. Tahir ya saki baki kafin yace"Wannan bakin Gilashin fa? Sadiq ya yi kamar bai ji sa ba ya cigaba da Tafiya, shi dai Tahir yaga an zo wajen Taron jama'a bai gani ba sai da yaga sun tsaya a kofar wani Rubabben gida Dagargajajje. Cikin mamaki ya kara kallon Sadiq kafin yace"Ina ne nan? Kai Tsaye Sadiq yace"In da zamu zo mana." Tahir ya bude baki kafin yace"Nan ne wajen daurin auren? Sadiq ya gyad'aa masa kai lokaci d'aya ya na kwalama Salihi kira da ya gansu suna wasa a kofar gida ganin shi yasa har da Datti suka Rugo da gudu Sanin ya na ba da kudi. Suna Rige rigen gaisheshi ya amsa ba Sakewa kai tsaye yace"Ku shiga ciki ku fad'ama Maman Hasiya Abubakar na mgana a waje." Yaran suka kwashi gudu zuwa cikin gida Tahir ko mamaki ya sandarar da shi jin sunan da ya ambata kara bin gidan ya yi da kallo kafin ya Dawo da kallon kan Sadiq da baya ganin kwayar idanuwanshi saboda gilashin da ya saka. Cikin mamakinsa Tahir yace"Nan ne gidan su Hasiyan kenan? Sadiq ya gyad'a masa kai Tahir ya yi kwafa kafin yace"Tsakani ga Allah mu da zamu Daurin aure me ya kawo mu nan? Sadiq ya yi shuru kafin yace"Nan ne wajen Daurin aure" Tahir yace"Nan ne wajen Daurin auran? Ya fad'a cikin Sigan Tambaya again kuma Sadiq ya gyad'a masa kai. Mamaki dai ko takaici zan ce ya kusa kashe Tahir a tsaye. Cikin karin mamaki ya kara cewa"To waye zai yi aure? Sadiq na kallon kasa muryansa ta yi kasa kafin yace "NI.." A Firgice Tahir ya Dago ya na kallonsa Daidai Lokacin da Amma ta fito ba ko Hijabi sai zaninta da tayi lullubi da shi Domin ta na zaune ne daman tana zaman jiran Tsammani sai ga su Salihi da sako. Duk muna zaune adakin Amma Sakon yazo abunda ya bamu mamaki tashin Amma da Sauri da fitan ta batare da ta jira cewar komai ba yasa ta fita ta barmu baki sake cikin zullumi da Tunanin lafiya. Ni kuma Tunda naji sunan wanda aka ambata gabbaina suka saki a tare. Abunda bai saba gani ba ne na gani yau ya saba indai yazo sai dai yace a kirani ammh yau Amma yace a kira kai Tsaye kenan tabbas akwai wani abu a kasa wanda ban sani ba. Achan waje kuwa Amma na fita Taga Sadiq ba ta ko tsaya lura da Tahir ba ta karisa gabanshi ta na fad"in"Daman na sani. Ina da kyakyawan tabbacin zaka Dawo Abubakar" Ta fad'a Lokaci d'aya ta na mirmishi. Dagowa ya yi ya na kallonta sai dai Rauni da kukan UWA shi ne suka Dawo da shi sai kuma Tausayinsu gabadaya. Cikin wani irin yanayi yace"Nazo da abunda kika bukata Amma meye abu na gaba? Amma ta daga hannuwanta sama tace"Alhamdulillah. Alhamdulillah.! Allah na gode maka" Sai kawai ta fashe da kuka ta na neman zubewa a kasa da Sauri Sadiq ya riketa kafin ta kai kasa kada ta tara masa Mutane. Cikin kukan ta ke fad'in"Nagode Allah ya yi maka albarka. Yadda kaji kaima kaima Allah ya jikan ka, Allah ya haskaka Rayuwarka da Alheri Allah ya baka abunda kake nema Duniya da Lahira Allah ya tsareka a duk in da ka ke Allah ya sanya albarka acikin Niyyar ka ta Alheri." Amma ta ke fad'a ta na kuka ga hawaye Shabe shabe Sadiq yasa Hannu ya share mata hawaye ya na fadin"Bakomai Amma." Amma ta rike Hannuwansa ta jimke ta na fadin"Yadda ka share ma wannan UWAR hawayenta Allah ya share maka naka. Yadda ka sanyaya ma wannan Uwar zuciya kai ma Allah ya sanyaya maka taka zuciyar, Yadda ka duba lamarin wannan Uwar kai ma Ina Rokon Allah ya cigaba da Duba Lamarinka har Abada." Sadiq na ta amsawa da Ameen Tahir ko ga shi nan Tsaye ya na ji kuma ya na gani ammh ya rasa gane ina aka dosa. Amma  ta na share hawayenta ta juya ta na fadin"Ina zuwa." Cikin gida ta koma da Sauri duk muma Daki ta daga labule ta na kiran Sunan Adda Fati, ta mike ta na Fadin"Na zo ne Amma? Kai ta gyada mata da Sauri ta mike ta fita ni da Ramatu muka kalli juna bamu da amsar da tambayar da ke zuciyarmu. Suna Fita Gefe Amma taja Adda Fati tace ta yi maza ta kira mata Babammu Tanko ta na so ta yi mgana da shi. Ba musu Adda fati ta latso lambarsa ta kirasa daman wayar na Hannunta sai da ta kira kusan sau uku sannan ya Dauka daman ita ta na da lambobin su ta na kiran su ta na gaishe su ko da su sun yada mu suna da Hakki muma mu bi mu  yi zumumci da su. Bayan sun gaisa tace masa Amma ke son mgana da shi nan da nan ya bata rai duk da ya jima rabon da yaji ta nemesa yasan kila wani

Chapter 23 of 24