Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da kayam kamshi, sai sakon su maman Boy na jima a kasuwar sannan aka gama Had'amin komai tunda sai da na jira akayi nika. Aka had'amin komai cikin wani karamin Buhu mangyadan ne kawai na rike a hannu kada ya fashe. A bakin Titin Tsamiya na Sauka Tunda bazai shigo dani ba. Na Dauki Buhuna a saman kaina mangyada kuma yana Hannuna Lokacin Rana tayi Biyu har ta wuce. Ta layin da zai kai mutun har gidanmu na bi inda masu awara ke layi wajen su biyar suna ta siyan su har da masu Dankali da kosan manja. Da zan wuce naga matasa a wajen tunda daman wajen zamansu ne. Naji muryan wani Saurayi yana Fad'in"Ke mai awara nan barayin ina ake saida Danwake mai Dad'i da Safe haka? Na ji sanda wata yarinya tace"Nan dogon gida ana Danwake da Safe mai Dad'i Da wake in mutum na so, sannan mangyada ko manja sai wanda ka zab'a". Na wuce acikin raina ina jin dadin ko bakomai akwai jin Dad'i a yabi sanar mutum, har na isa gida bakina yaki Rufuwa ina ko sauke kayan saman kaina na fara gayama Amma. Tayi dariya kafin tace"Hasiya manya.." Ina Dariya nace"Amma baki ji dadin da naji ba" Ammh ta yi mirmishi. Sallah nace zan yi sannan na warware kayan na mikama su Maman boy sakon su har sun fara lekowa suna Fadin"Hasiya nace dai baki manta da Sako na ba ko? Tafarnuwa da ungurnu ne ni dai Sakona" Har sai da nace musu Sai na yi Sallah zan  Fito da sakon su na basu, sannan suka shafamin lafiya. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *10/09/2023* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Albishirinku ya yan'uwana An-Nisa! Ina wacce ta dade tana amfani da Sabaya amma bata ganin aikinsa duk kuwa irin shan da take masa ? To share hawayenki tamu Sabayar ingantacce ne wanda muka sake bakin aljihu muka zuzzuba kayan gyaran jiki wanda bana cutarwa ba infact shi wannan hadin 2 in 1 ne…. Hadin SABAAYA da ADUMULMULA, in kina fama da matsalar zubewar Nono to wannan had'i naki ne, in kinaso ki cicciko fatarki tayi kyau ki koma tamkar ‘yar yarinya to ki riki wannan hadi namu… Aikinsa bai tsaya iya nan ba hatta da kara lafiyar garkuwar jiki yanayi da kuma kara ni'ima…kowa na iya shansa, matan aure, Masu shayarwa in kin kusa yaye, 'yan mata, babba da yaro, maza da mata kowa na iya amfani da wannan hadi namu…. Muna maraba da mai siyan daya ko sari. Abangare guda kuma muna had'a magani ingantacce na ciwon sanyi da yaki jin magani, in aka daure ana amfani dashi ana dacewa bi'izinillahi ta'ala, kai hatta da maganin hawan jini da diabetes duk muna saidawa kuma ana dacewa in sha Allah. Atuntubemu tanan whatsApp or call 📞 07065481260.. Don Allah don annabi in kin san ba siya zakiyi ba kar kizo ki bata mana lokaci da tambayoyi please kayayyakinmu original 💯ne babu algus *07* Shi Sadiq a kan Quantity Surveying ya samu shaidar Degree d'insa na farko. Ma'ana sani kan harkan shimfid'a Titina da sauran su. Shiyasa ya ke bautar kasar sa a Dismento Nigeria limited Old Sokoto Road, Samarun Zaria. Shi kuma Tahir Politcal Sciences ya karanta wato harkan abunda ya shafi Siyasa. Ya na bautar kasar sa ne shima a wata goverment secondary na cikin Samarun zaria. Yau litini tun bakwai da Rabi ya fita ya bar Tahir a gida ya na faman nuku nukun sa, Sai da ya biya in da ya fara siyan Danwake mai d'an karen Dad'i ya mika karamar kularsa da ya ke zuwa da ita ga yaran da ba'a rabasu da wasa a kofar gida suka shiga suka amso masa. Dashi ya tafi wajen aikin nasa. ya riga ya saba tunda ya samu Danwaken nan da shi ya ke tafiya wajen yana karyawa har kuma wani Lokacin ya yi ragowa ya dawo da shi gida. Watarana kuma wani wanda suke aiki a wajen shima hidimar kasar ya ke yi suke ci tare. Karfe biyu saura ya baro kamfanin kamar yadda ya saba adaidaita ya hayo zuwa anguwar Tsamiya aka sauke sa a bakin Titi ya gangaro da kafarsa. Yasan Tahir na rigashi dawowa tunda makarantar sa ta fi kusa gida. Sannan ba tsayawa ya ke a tashi ba da ya gama Darasinsa ya ke gudowa gida Tahir dan Shiririta ne ba komai ya ke ba ma Muhimmanci ba shi dai wayarsa kamar tafi komai muhimmamci a rayuwarsa. In kaga ciwon da Tahir bai Dauki waya a hannunsa ba to kila sai dai ciwon Ajali mutun ne mai mu'amala da kafafen yad'a zumunta sosai ba irin Sadiq da waya ko hawa irin kafafen nan ba su dame shi ba, Shi dai barsa da kallon Fina Finan korea da turkish Drama suna nan cike a Laptop dinsa ko Tab dinsa. Sai kuma sanin kan Na'ura mai kwakwala wannan tun yana karami ya iya sarrafata tunda ya taso ya gansu ne shima agidan su.   Dakin a bude Tahir ya barshi Saboda Sabon Iskanci har da su Dage Labule sama a dakin na Fuskantar waje, ga shi cikin Anguwa mai cike da Mutane sai wucewa ake yi ana ganin musu asirin dakin Ba wannan ya fi bata ma Sadiq rai ba sai ganin yadda Tahir ya yi kaca kaca da Dakin Alhalin kafin fitarsa da Safe sai da ya kimtsa dakin shara ne kad'ai bai yi ba yace sai ya Dawo. Tun kafin ya shigo ya gimtse fuskarsa Sanye ya ke da Riga da wando,Rigar mai Dogon hannu ce mai ruwan Ash da layi layin blue. Wando kuma jeans ne mai ruwan kasa sai Rufaffen baki takalmin da ke kafarsa bayansa Rataye da Jakar laptop d'insa sai karamar kular da ke hannunsa. Yana shigowa ba domin sanin Darajan Sallama ba, da ba zai yi ba sai dai yasan Darajanta tunda shi Musulmi ne Murya ba Dad'i yace"Assalamu Alaikum.." Bai ko jira Tahir dake kwance kan Katifa da ya yi wani da'i da'i ya amsashi ba cikin Fusata yace"Haba Tahir. Haba Tahir meye haka? Ya fad'a yana kallon Tahir din cikin Takaici. Tahir da ke kwance daga shi sai dogon wando ko Riga ba bu ajikinsa wayarsa na Hannunsa yana Dannawa ya yi matashi da d'aya hannun na shi Cikin kosawa da irin ka katsemin aikin gabana ya Dago yana kallon Sadiq kafin yace"Miye wai? Kai dai baka raina abun korafi wlh. Zafi ne ya isheni ga shi ba wuta shiyasa na bude kofar na kuma D'age labulen mu samu iskar Duniya ya shigo mana" Daga haka ya koma ya cigaba da Dannan wayarsa yana ta faman mirmishi. Sadiq ya tsaya kawai ya na kallon Tahir bakinciki ya chuse ranshi. Kai tsaye ya sauke jakar hannunsa tare da kulan ya dago cikin Zaro ido yana nuna Dakin da kallo kafin yace"Au baka san me kayi ba ko Tahir.? Ba ka san ma me ka yi ba ko Tahir? Tahir Hankalinsa na kan wayarsa yace"Me na yi kuma? Da muryan ko ajikinsa. Sai kawai Sadiq ya yi kwallo da Takalmin Tahir da ya cire nan tsakar dakin sai da ya Daki bango ya Dawo Tahir ya Dago yana kallonsa baki Bude kafin yace"Me ya yi zafi Alarammah? A fusace Sadiq yace"Ban sani ba. na gaji da kazantar ka Tahir na gaji. Kai yaro ne? Komai sai an gayamaka zaka yi? Bakina kullum akan mgana d'aya ne ehe? Ya karishe fad'a har jijiyon kansa na tashi alamun ranshi ya baci ganin haka yasa Tahir ya ijiye wayarsa nan saman gado ya mike yana fadin"Yi hakuri to. Kasan gajiyan da nayi yau? Daman fa ina da shirin na mike na kwashe na share dakin ne ka shigo" Ya na fad'a lokaci d'aya ya duka yana kwashe kayansa da ya cire watsar da su anan. Sadiq sai faman Hararansa ya ke yi kamar idanuwansa za su fad'o kafin yace"mgana d'aya ba zaka Dauka ba Tahir. Shikenan ka cigaba" Daga haka ya karisa gaban Fridge ya Bude ya Dauko ruwa ya sha anan duka ya shanye ya fita waje ya jefar da Goran sannan ya dawo. Tahir dai dole ya kwashe duka kayansa ya kimtsa wajen saboda yaga Ran Sadiq ya baci yasan Halinsa haka ya ke ba shi da Saurin fushi ammh kuma ya tsani ya rika maimaita mgana Daya. Sai ga Tahir har da Shara, sai bayan ya gama ne ya yo alwala ya zo ya yi sallah Lokacin da ya idar Sadiq na kan katifa barayin da yake kwanciya tunda Kafitar tsakiya Dakin suka sakata kowa farko ya ke so ba Lungu ba, sai suka raba Gardama suka sanyata a Tsakiyan Dakin. Ya na sallame sallan yaga Sadiq da ke danna laptop dinsa har ya sauya kaya zuwa saukkaku  na zaman gida. Yanayin kallon kad'ai da ya gani ya sha jinin jikinsa da Sauri yace" kana wani kallo na kamar na yi sabo? Lalurin sallar azahar har sai la'asar ta gabato." Sadiq kamar ba zai yi mgana ba sai kuma ya jinjina kai kafin yace" kai dai ka sani. Kai ba yaro ba ne in daidai ka aikata ma ai ka sani Tahir ba ruwan Sadiq aciki ni dai tsakani ga Allah na fita hakkin zaman tare" Daga haka ya cigaba da kallon allon Laptop dinsa shi kuma Tahir ya mike yana Hamma kafin yace"Abokina yunwa na ke ji. Kuma miyar nan fa ta kare ita kenan jiya na yi mana shinkafa da Miya." Banza da shi Sadiq ya yi ganin haka yasa ya nufi kular da ya shigo da shi ya jawota yana fad'in"Wai miye a kulan nan ne da ko da yaushe ka ke fita da ita kuma ka dawo da ita? Sai dai me? Ya kasa mgana da ya ga Sauran abunda ke ciki Danwake da wake da Manja an chakud'a an ci an rage kad'an. Da sauri Tahir ya kauda kansa kafin ya Dago yana kallon Sadiq cikin Jin haushi yace"Haba Sadiq. Tsakani ga Allah abunda ka ke yi yanzu ka kyauta kenan? Ba tare da Sadiq ya kalleshi ba yace" me na ke yi? Tahir yace"Gidadanci mana. Eh mana Gidandanci mana ban da haka miye ribarka na zuwa da Danwake wajen aikinka Tsakani ga Allah? maganar gaskiya wannan dabi'ar taka ta katon bagidajen Kauye ne" Mirmishi Sadiq ya yi kafin yace"To miye bambamcin Tahir? Ai bagidajen kauyen ne ko baka sani ba? Ya fad'a yana saka kallon wajen Tahir wanda ya rufe kular ya dawo gaban Sadiq ya zauna saman katifa yana Fadin"Danwake a kula kamar wani yaro dan firamari Sadiq? Ina laifin in Danwaken ka ke son kaci ai akwai a Restaurant sai ka shiga ka siya kaci tunda kai dai ka san nasan abinci ko wani Restaurant in kana Ra'ayi zaka ci bai fi karfin aljihun ka ba" Yadda Tahir ya ke mganar zaka san abun ya mishi ciwo, duk da yasan Waye Sadiq ta wannan bangaran bai taba Tunanin abun na shi ya kara Lalacewa kamar haka ba. Wai Danwake a kula abun ma ba shi kunya ya ke yi wlh in ya tuna kuma wai ka shiga cikin mutane da shi kamar wani karamin yaro. Lura da Hakan da Sadiq ya yi shiyasa ya ture Laptop din gabansa ya Fuskancesa kafin yace"Rayuwa ce. Kowa da irin yadda ya ke tafiyar da tasa Rayuwar Tahir. Miye aibu aciki don na siya abunda nake so na tafi da shi wajen aiki na? Da Sauri Tahir yace"Wlh akwai aibu. Babban aibu ma kuwa. Aikin yara fa ka ke yi? Yaran ma kanana Sadiq. Haba don Allah" Tahir ya fad'a har yana wani juya Fuska irin yaji kunyan nan. Dariya Sadiq ya yi kafin yace" A wajen ka kenan  ya ke aibu ni dai a wajena a daidai na ke kallonsa kasan Hausawa na cewa Daidai wani.." " Karkatan wani.." Tahir ya karishe cikin mamaki kawai yana kallon Sadiq. Shi kuma yana yi masa mirmishi sai kawai ya rike Haba yana fad'in"Ikon Allah.. Allah mai mutane kala kala kawai sai aka ganka ka fito da kula ka bud'e ka na cin Danwake da wake da Manja." Sadiq yace"I sata na yi? ni zan ci kayana ra'ayi na ne. Ban kuma takurama Ra'ayin wasu ba." Tahir yace"Ni tsaya ma a ina ka ke siyan Danwaken nan ne? Sadiq ya ce"chan ne wani gida a kasan layin wajen masu awaran nan da Dankali" Cikin takaici Tahir yace"kai ko a ina kasan gidan? Ko da ya ke in wajen ciye ciye irin wannan ne kai tsuliyan gari ne" Sadiq yace"Ni fa ranar naje siyan awara  a wajen naji wani na tambaya ina ake saida D'anwake mai dad'i? sai wata mai awara ta kwatanta masa gidan kuma ta yabi Danwaken shiyasa nima nake zuwa ina siya. Kuma Alhandulillah akwai dadi ga tsafta" Tahir ya karkace baki kafin yace"A ina kasan ya na da Tsafta? Hala  a waje ne a ke d'anwaken? Ko kasan me yin Danwaken ne? Sadiq cikin kosawa da Tambayoyin Tahir yace"ba'a waje ba ne acikin gida ne. Ta ya za'ayi na san mai yin Danwake Tunda ba gidan na ke shiga ba" Tahir ya ce"Uhm sai kaga yadda ake D'anwaken ka raina kanka Sadiq. ba fa kowa ke tsaftace abun sana'arsa ba, barin ma irin gidajen anguwannin nan. Wani abun wlh in kagani kamar kayi Amai.." "Tahir.. Tahir don Allah.."    Sadiq ya katseshi bayan ya Daga masa hannu Dariya Tahir ya kwashe da shi kafin yace"Wai don nace Amai..Amai..!" Sadiq ya ce"Daman kazami ne kai. na sani" Tahir yace"Tabdijam! Ai dama a Shinkafi a ka haife ka zaka fi Dacewa da Katon kauyen Shinkafi ba na Birnin Zamfara ba." Sadiq ya yi dariya har sai da ta yi Sauti lokaci d'aya kuma ya kimtse fuska ya kurama gefe d'aya ido kamar mai Nazari. Kansa ya jinjina kafin yace"To ai ban yi maka karya ba Tushena kauye ne. Kuma kauyen Shinkafi. Ko ba'a Haife ni achan ba chan aka Haifi Abba. Sannan lokacin da aka haifeni Umma ta fara rashin lafiya ko arba'in d'ina ba'ayi ba Abba ya ce Innani ta tafi da ni da Umma Shinkafi ta na kula da ni, Sannan ina da wata Takwas saboda Laluran Umma Innani ta yayeni babu abunda bata ba ni na ci Saboda inganta lafiyata ba, Tahir ban sha Nonon uwa kamar yadda ka sha ba. Hannun Innani na zauna har na tsawon Shekara Shidda sannan Abba ya karbo ni na dawo zamfara Ka ga kuwa ka daina mamaki in kaga ina cin wani abu akwai sabon haka Tun ina da kuruciya da su na Saba, kuma ni Inanni ta yi min Renon uwa ka sani ko a yanzu ta mini gatan da ko Abba da ke d'anta ba ta yi ma shi ba" Tahir da ya yi Tagumi yana kallon Sadiq ya na jinsa ya Sauke ajiyar zuciya kafin yace"Shiyasa ko Hajja na je gida ta rika rawan jikin kawo min abubuwa taga na fara cewa ba na cin kaza sai ta fara fad'a tana fadin kai dai ka cika kircin tsiya shiyasa nake son abokin nan naka Saddiqu yaron nan har mamaki ya ke ba ni ga shi Dan gata gaba da baya ammh a irin Rayuwarsa kamar wanda baisan gata ba komai ci ya ke har kaji ya na fad'in Hajja zogalen nan ki ijiyemin zan ci da Daddare ammh kai sai shigen iyayin banza da Wofi tafi mara wayau shiyasa baka kiba kullum lange lange kamar iska" Gabadayan su suka kwashe da Dariya Tahir yace"Ina shan gori wajen Hajja komai sai tace Saddiqu ya fi ka Tahir kai kam sai fatan Shiriya." Sadiq yace"Allah sarki Hajja na yi kewar Dambunta da kwad'en Zogalenta yaushe zamu je Daura? Tahir yace"Kasan ko kwanaki ta yi ta fama da Zazzabi." Sadiq ya kallesa kafin yace"Subhanallah yaushe? Shine baka Fad'amin ba? Tahir yace"Kawu ya ce da Sauki shiyasa kaji ban Fad'a maka ba. Kasan Hajja da kafiya ga shi ta na ciwo ammh taki bari aje asibiti wai ita ta warke." Sadiq yace"In na ganta Innani na nake gani a tare da ita. Bambamcin kad'an ne ita Hajja ba ruwan Tsine tsine a bakinta.". Tahir ya fashe da Shegiyar Dariyansa yana Fadin"Allah Sarki Inanni gaskiya ina missing nata. Yaushe zaka gida na bika nima? Sadiq yace"mu bari weekend, Jiya Abba ke fad'amin Innani na Shinkafi chan ya barota wajen sha'anin Diyar Baba Saminu da akayi, So kuma ba na son zuwa ba ta gida. Abba yace dakyar suka lallasheta da ta ce sai tazo ta ganni ina nan ba uwa ba uba Allah yasa ina Hannu nagari" Tahir ya kara kwashewa da Dariya kafin yace"Allah ya ja da ran magajin gida da girman kujeran ka.." ya fad'a har yana daga masa babban yatsansa alamun jinjina. Sadiq ya make hannun yana Fadin"Ka bari Tahir." Shi ko sai fadi' ya ke"Takawarka Lafiya Autan Umma dan gatan Abba. shalelen Innani. Angon SULTANA" wata uwar Harara Sadiq ya sakar masa kafin yace"Tahir sunan Sultana ya fita a bakin ka? Inanni bata kyautamin ba" Ya fad'a yana yamutsa Fuska Tahir ya Dafa kafad'arsa yana Fad'in"Mutumina kaji dadin ka. Kai dan gata ne irin wannan zukekiyar Yarinyar duk ka kai kadai? Ya ke fad'a yana Dariya Lokaci daya yana kashe masa ido d'aya. Ture hannunsa Sadiq ya yi yana fadin"Tahir Allah ya shirye ka." Tahir yace"Ni dama Hajjo nima ta kamamin wata achan Daura yar Fara haka Danya Sharaf mallam" Sadiq ya girgiza kai kafin yace"Ai tasan halin yan kayanta ne. In ko ta kama maka zaka iya kunya tat Tahir." Cikin Magiya da Fuskar Tausayi Tahir yace"Wlh a'a. Kaga da mun gama Hidiman kasar nan muka kama aiki sai kawai kaji mun angwance Rana Daya da yan Shillan mu Abokina." Dukkansu Dariya suka saka har suna Tafawa kafin Sadiq yace"A'a in muka angwance Rana d'aya wa zai rakani Dakin Sultana? Tahir ya bushe da Dariya ya Daki kafadar Sadiq da karfi yana Fadin"Shige abokina ashe kana son yarinyar nan sai ka rika wani basar da ita? Sadiq na mirmishi yace"Tahir ba komai ke bukatar bayyanawa ba. Sultana Zabin Umma ce. Sannan Burin Innani ne, ni kuma kaga matan nan biyu suna da Muhimmamci a Rayuwata da ko wuta suka ce na shiga wlh zan shiga. Sun gama min komai a Rayuwata. Sultana a gaba na Umma ta Reneta  yarinya ce karama fa Tahir sai na zauna ina Biye mata? Ni ma yaron ka ke so na koma? Tahir ya ce da Sauri"ko ba ka koma yaro ba akallah dai ka Damu da ita kamar yadda ta damu da kai." Sadiq ya mike tsaye yana gyara zaman 3Quater da ke jikinsa lokaci d'aya yana Fad'in"Tahir har yanzu da Sauran Lokaci. Baka gane abunda na ke gayamaka ne? Shekarata Talatin wannan Shekaran Sultana ba ta wuce sha Shidda ba Jss3 fa take. Ba ta ko gama socondary ba, Sannan ni ma ina son Dora Masters dina bayan mun gama Servise din mu, ina da abubuwan yi a gababa ma su tarin yawan da ba na so wani abu ya Daukemin Hankali itama ba na so na zama Silan samun matsala a bangaran karatunta shiyasa kaga ina mata haka  kuma mganar kira muna gaisawa, daga gaisuwa da tambayan makaramta bata iya fa mgana da ni,wani Lokacin ma in ta kirani da wayar Umma ina Dauka sai dai ta ce bari ta kaima Umma. Ka kyale yariyanan Kuruciya ne da Wauta ke Dawainiya da ita fa" Tahir na yar Dariya yace"Kuruciya da Wauta ko dai Soyayya? Wlh Sultana ta na sonka Sadiq" Sadiq yaja tsaki kafin yace"So? Tahir kai ma shekarunka ba su yi maka amfani ba. Ina yarinya kamar sultana ta san wani So? Tahir yace"Wad'anda ma basu kaita ba susan So mallam. Ni ka manta yarinya yar Jss2 ta turomin wasikar tana so na? Sai kace me kuma? Sadiq yace"Abun ya na faruwa ne da yanayin In da mutum ya taso. Rayuwar Sultana ba daya ya ke da matan wajejjan nan ba Tahir. Kawai dai kace ta san ni zan aureta haka iyayenmu suka tsara to na yarda akwai wannan Shaukin na sanin haka Tun da karuciyarta ammh ba zencen so ba Tahir" Tahir zai yi mgana Sadiq ya kallesa yana Fadin"Tahir.." Sai ya yi shuru yana jinjina kai kafin yace"Shikenan zamu maimaita mganar nan watarana in da rai da Rabo abokina." Sadiq ya sauka Daga kan katifar yana Fadin"Ranar jumma'a zamu tafi Daura mu kwana Asabar, Ranar Lahadi mu je zamfara sai mu dawo talata da safe." Tahir ya mike ya Daka tsalle akan katifa yana fadin"Ehhyeee..Gida gida Dad'i" Sadiq ya girgiza kai bai yi mgana ba Buta ya dauka ya zuba ruwa yana Fadin"La'asar ta kusa Tahir" Tahir ya duba agogon wayarsa kafin yace"Da sauran lokaci." Sadiq ya shafa cikinsa kafin yace"Cikina ya lalace yau ina ta shiga bayi a kamfani" Tahir ya kwashe da Dariya kafin yace"Ba dole ba. Danwake da wake fa kake ci? Ga yaji. Ai cikin ka ma na baka lafiya a irin yame yamem da ka ke masa ya ci ace kashin ka ya Daina karfi ya koma zawo ma" Sadiq ya yamutsa fuska kafin yace"Da gaske fa Tahir. In na fito wannan na biyar fa kenan" Tahir ya zaro ido kafin yace"Ka sha mgani? Sadiq ya fita da Sauri yana Fadin"Duba in muna da sauran filajin in kuma babu Tahir ka fita ka siyomin. Wlh cikina sai kartawa ya ke yi" Y na fad'a ya zura a guje ya shige makewayin su na waje Allah yasa ba kowa a baranda sauran masu Dakunan ba su dawo daga cikin makaranta ba. Tahir na dariya ya saka Rigarsa Fara T.Shirt ya Dauki 500 cikin Jakarsa da ya Dawo da ita daga makaranta ya fita. Chemist din ba nisa shiyasa ya jawo kofar sai dai ya isa gaban Makewayin da Sadiq ke ciki ya Daga Murya yana Fadin"Na fita ban kulle kofar ba. Ka kula da motsi" Sadiq na ciki sai ji ya yi ya ce"Uhmmm... Tsuwww..! Zawo na fita Tahir ya Fashe da Shegiyar Dariyarsa ya tsallaka Baranda yana fadin"Eh lalle dole in nemo maka mgani. kada cikin Dare ka zame min kaya na shiga uku" ******** *Dogon gida*. Alhamis_8:30am. Habiba na ke sakawa Danwake a roba, tana tsaye a kaina ta na Fad'in"Adda kada ki sa min da yawa. Ki ijiyemin na anjuma don Allah" Kai na jinjina kafin nace"ke kam da Danwake Habi" Dariya ta yi bata yi mgana ba na gama saka mata mai da yaji na mika mata ta karb'a. Sauri ta ke yi ta makara Daki ta shige da gudu. Ni kuma ta barni ina kiciniyar kwashe wanda na saka a wuta ga mutane suna jira na cikin gida da waje. Abun ne yanzu na wannan rayuwar sai godiyar Allah. Farko an fara da cire tallafin man Fetur ne, takala ya shiga wani Hali na Babu da k'anik'ani. Sannan sai man fetur ya rika tashi ya na Hauhawa, sai kuma ababen rayuwa da yau da kullum su ka rika tashi suna Hauhawan Farashi komai yanzu ya zama dan zani. Masu kudin ma suna ji ajika ballatana mu talakawan da ba tallafi sai mun tallafama kanmu da ire iren sano'i'on cikin gida. Shiyasa komai ya yi tsada har Danwaken yanzu na 400, bai iya kosar da Mutum sai dai aci kawai a gode Allah. Godiyar da na ke yi ma Allah da Sana'ar ba ta kwace a hannun mu, duk da ciki muke wasu Hidimdimun ammh kuma da Sauki acikin lamarin ba ma abinci, mu ci danwake da Safe ko mu ci wake,Da yammah mu ci shinkafar da muke siyarwa. Amma kuma daman yar koko ce da Farau Farau. Ko ayi mata Faten Tsaki da Shuwaka, sai bangaran ci da shan mu ya samu sauki bangaran Sabulun wanka da na wanki sai kuma in Adda Fati ta yi nukasanin kawowa ammh ta Dauke mana wannan bangaran. Duk da ina gajiya ammh ba na nunawa ko a fuska aiki na ke yi kan jikina kan karfina ni ce saka Danwake, juyawa kwashewa. Zuzzuba ma Mutane tare da sallamansu Layi a ke yi min abun sai godiya kawai. Sakamakon ya kasance Safiya sai ki ga babu chanji a Hannuna in aka zo siya nakan ce aje a dawo lokacin na tara yan canji. Ina cikin Kwashe Danwake Datti yaron Maman Salihi ne ya iso gabana da kyakyawan Kular da tun kwana goma da suka gabata ake zuwa siyan Danwake da ita. Ya na zuwa tun kafin ya yi mgana na ce"Na Dari takwas ko? Waken Dari hud'u Danwaken D'ari Hud'u sannan manja za'a saka" naa Haddace lissafin koma waye mai siyan Danwaken nan yana da ka'ida da Tsari ne. Dariya Datti ya yi lokaci d'aya

Chapter 8 of 24