Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Kwad'ayi ne da Innani komai na Duniya ba bu abunda bata ci. Tace da wuya ta kasheta gwara dad'i ya kasheta. https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V Cikin Dariyanta tace"ina lafiyar ita uwar taki? In ji dai lafiyanta lau? Ina shi Baban naku? Tun asuba da ya leko muka gaisa ban kara ganinsa ba." Muryanta a sanyaye tace"Umma tana lafiya. ABBA kuma yana bangaransa shi da Mama" Nan da nan Annurin fuskar Inanni ya Dauke ta wani Dauke kai kafin tace"Uhm ko da naji." Daganan tayi Dif tana faman girgiza sadan dake gefenta. Sultana sai satan kallonta ta ke yi tana danne mirmishinta. Sai jin mangari ta yi a kai lokaci d'aya Innani tace"Munahika yi dariyar taki mana a sarari yarinya sai bakar gulma kamar haihuwar Ssuwaiba. Da sauri ta kalleta cikin mamaki Lokaci daya tana dafe kanta in da Inanni ta mangareta. Innani ta yayyako mata cikin masifa tace"Miye kuma kike kallona? Ko na fad'a a bakin yan baka ne ko ke ma kin koyi halin ya'yan Suwaiba ne  ban sani ba?Allah to ya sauwake kin cuci Salamatu da Sulaimanu domin ba haka suka tarbiyantar dake ba" Ko gajiya da mgana Innani ba tayi, haka Sultana ke fad'i a cikin ranta. Mirmishi ta yi kafin tace"Innani.." Innani ta kalleta batare da tayi mgana ba, ganin Sultana taki mgana sai kuma wasa da gefen hijabinta take yi yasa Innani ta yi tsaki kafin tace"Nace miye ne kika tasani kina faman kiran sunana? Shuru Sultana taki mgana kanta na kasa sai wasa da gefen hijabinta ta ke yi, Innani tayi sakate kafin ta juya cikin jin haushi goronta da ke cikin wani karamin kwano ta jaho,ta fara yayyankashi a saman tafin hannunta. Chan kasa kasa taji Sultana ta kara kiran sunanta"Innani.." "Kina kara kiran sunana zan kwad'a miki mari, bar ganin ina raga miki,sai naci mutumcin ki. Yarinya kin zo kin tasani kina faman kiran sunana, kuma ki yi mgana kin ki yi to uban waye shashasha irin ki? Mtswwww.." Bayan taja tsaki ta cigaba da bambare gorinta tana watsawa cikin bakinta. Sultana sai kallonta ta ke yi ta kasa mgana sai daga baya ta kara kiran sunanta ta juyo a zafafe da niyyar kara sauke masifarta. Sultana ta lamgwabe kai lokaci d'aya  tana mika mata siririn hannunta cikin Shagwaba tace'"Innani san min goron" Innani tayi kwafa kafin ta dauko goro karami cikin kwanon gabanta ta dangwara ma Sultana a hannu Lokaci daya tana fadin"Na shige su da kwazzaban ki Sulsana. Wannan yarinya Magajin gida zai yi fama" Fad'ar sunan yasa dukkansu suka kalli juna Sultana ta kauda kanta. Innani kuma kamar an tunasar da ita ta gyara zama tana fad'in"Ke sulsana kun yi mgana da Magajin gida ko kwanaki nan? Ni wajen kwana uku kenan bana samun sa a waya kuma bai kirani ba, Allah yasa lafiya ina ta zuci zuccin in yi ma Sulaimanun tad'insa sai sha'anin duniya ya mantar da ni." Da kai sultana ta yi mata mgana da girgiza mata kai alamun itama ba su yi mgana ba. Nan da nan Innani ta kara Harzuka cikin daga murya tace"Ke uwarki. Baki zaki bude ki yi min mgana ba ne Sultana tace" A'a Innani" Nan da nan Hankalin Innani ya tashi ta fara salati tana Direwa kafin tace"Wayyo jikana. Yana chan wata uwa duniya ba uwa ba uba. Ba kuma dangi ko wani hali yake ciki? Ke sulsana dubamin wayata cikin daki ki zo ki kara kiramin shi Allah yasa jikana yana lafiya. Magajin Sulaimanu bayan shi ba shi da wani magaji anan duniya" Ta ke fad'a tana kokarin fashewa da kuka. A sanyaye Sultana ta mike tana wannan tafiyar nata Innani ta kalleta cike da takaici tana fad'in"Zaki yi sauri ko sai na turaki da wannan Sandar ta hannuna? Ta fad'a tana kokarin dauko sandan nata da gudu Sultana ta shige cikin Uwar Dakin Innani, ta fara neman wayar na ta. Ta duba ko'ina bata gani ba, ga shi daga Falo Innani sai faman kiran ta take yi sai da ta gaji ta fito ammh Daga gefe ta tsaya tana fad'in"Ni fa ban ga wayar taki ba Innani" Yadda Innani ta kalleta da tana kusa sai ta sha duka da sanda, shiyasa ta tsaya daga baya baya. Tsaki tsaki tsut.! Kafin tace"Ko ke ma idon naki na da Rauni ne na saka Sulaimanu ya kai ki in da ya kai ni aka ba ni wannan gilashin? Ammh ace waya na barta saman katifar da na kwanta ki zo kina ce min wai baki gani ba? Ta fad'a tana nuna ta da Sanda,kamar zata daketa. Sultana ta tura baki tana kallon gefen kwanon Innani ga wayar nan kirar kamfanin Tecno karama, ammh tana ta kumfar bakin a saman katifa ta barta. An ci sa'a ne da tana cikin Lalinta ne zata rika bala'i tana tsine tsinen an sace mata waya. Yanzu ma ido ta mutsike tana fad'in"Baki gani ba fa da gaske Sulsana? Allah dai ya tsine ma barawo da uwar barawo wlh" Sultana ta zaro ido kafin ta karisa gaban Innani ta duka ta Dauki wayar ta mika mata tana fad'in"Ga fa wayar taki nan a gaban ki Innani" Innani ta bi hannun Sultana da kallo kafin ta karbi wayar ta jujjuya tana Fadin"Ikon Allah! Ni fa saman katifata na barota. Ni fa daman na dad'e da sanin abun nasara ba shi da tabbas, sai ka ijiye abu ka nemeshi ka rasa sai chan ka ganshi a wani waje mtseww" Ta karishe da tsaki daman Tsina da Tsaki a bakin Innani Allah ya fissheta kada ta zo mutuwa su kama bakinta. Sultana ta kara damgwara ma wayar tana Fad'in"Maza kiramin magajin gida. Allah yasa yana hannu nagari." Sultana ta dukufa kiran Magajin Gida kamar yadda Innani ta saka akayi mata Saving a lambarsa. Itama cikin mazari ta latsa lambar nasa sai dai kuma kuzarinta ya ragu da wayar ta ke kara duui! Sai kuma ta yanke, tayi haka har sau uku duk tafiyar d'aya ce tana ji Innani na fad'in"Kin samu magajin gidan ko? Ta kasa bata amsa Dagowa ta yi ta kafe Inanni da ido. So ta ke yi ta ce mata ya yi blooking dinta ne,ammh tasan Innani ko za'a shekara bazata gane komai ba. Shiyasa ta mikama Innani wayarta ta ki mgana, da kallon mamaki ta bita baki bude kafin tace"Ke na ce kin samu magajin gidan a waya? Sultana ganin Innani ta ki karban wayanta sai ta dungure mata a saman cinyarta ta mike tana fad'in"Innani wayarsa ba ta shiga." Inna ta rafka salati tana fadin"Na shiga uku na lalace ni Dije. Ke kinga Sulsana maza jeki ki gayama Babanku yazo ina nemansa" Sultana tace"Innani Abba kuma? Barci fa ya ke kinsan yau weekend ne" Innani ta rarumi sandarta tana fadin"Ko barcin mutuwa ya ke nace ki taso min shi kaji min ja'irar yarinya tabbattaciya. Ba gwara ya tashi da wannan barcin da tashin hankalin da ke Tunkaromu ba, Magajin gidan ne gabadaya ba'a san inda ya ke ba yanzu kai co na Dije, daman wlh ban so tafiyar yaron nan ba, ya lallameni da Kalamansa na bayan ya had'a da su jawomin manyan ayoyin Allah Sai na amince ammh har cikin raina Hankalina bai kwanta ba" Ta karishe fad'a tana face majina,Sultana ta yi tsaye tana kallonta ganin yadda Lokaci daya ta rikice, To daman ai shi kad'ai ne ke rikitar da Innani sannan kuma cikin Mintina ya ke dawo da ita saiti, wanda ko Abba da ta haifa sai ya Dauki awa Biyar Innani ba ta ji mganarsa ba. Bata sani ba Inanni ta daga Sandarta sama tana fad'in"Zaki wuce ki taso min shi ko sai na Rafke ki? Sakarya mara wayau in kina da Tunani da Hankali ai kema abun kukan ne ya same ki, in da kara zama zaki yi mu taru mu tashi gidan da koke koken mu" Sultana dai da gudu ta fice daga Shashen Inanni tana haki kamar ta yi wani gudun tsere. Babban gida ne mai shashena biyar,bi da bi, biyun na jikin juna suna da girma,Karamin ne ke chan gefe shashen Innani kenan, wanda ya fi girma gabadaya shine na jikin wani karamin Shashe shima. Sai da ta tsaya a wajen ta kallah kamar zata ganshi ya fito. Sanin ba Fitowar zai yi ba yasa ta juya ta tunkari shashe guda biyun da suka fi girma. Na farkon ta bude kofa ta shiga, Sad'af Sad'af kamar barauniya. Ta kawo Tsakiyar Falon taji an ce"Sultana." Cak ta tsaya ko ba ta juyo ba. Ta san Muryan wacece Umma ce! Cikin sanyin jikinta na Hallita ta juyo kanta na kasa tana had'e kafafunta alamun ba ta da gaskiya. Doguwar mace ce,mai dan kaurin jiki baka zaune kan kujera remot a hannunta. Sanye ta ke da Atamfa super aura mai kalan Duhuwa ta ci Daurinta kamar wata matashiya. Alhalin zata ba ma Shekarun Hamsin baya. Sama da kasa ta kalleta kafin tace"Daga ina kike da sassafe daga tashin ki a barci na duba ki ban ganki ba? A sanyaye tace'"Shashen Innani na je" Hajiya Umma ta gyad'a kai kafin tace"Ta na lafiya ko? Da kai ta amsa mata bata damu ba sanin Halinta. Mirmishi ta yi mata kafin tace"Sai ki wuce ki je ki yi wanka ki zo ki mu karya" Kamar tana jira ta amsa da Toh ta wuce da Sauri Umma ta bita da kallon mamaki a ranta tana Tunanin Saurin me Sultana ke yi haka? Tunaninta ya tsinke ni Lokacin da taji mganar Innani da karfi tana kwalamata Kira. "Salamatu.. salamatu.." Kina ina ne salamatu,? Zumbur ta mike lokaci d'aya tana watsar da Remot din hannunta. Zata iya banzarta da kiran kowa ammh ba zata iya kyale kiran Innani ba. Uwar mijin da ta yi mata rikon uwar da ta rasa tun a zamanin baya. Uwar da ta Fifita son da take yi mata sama da d'anta data haifa. Ita ko mai zata saka ma Innani? Ba bu ban da ta rika yi mata Biyayya da yi mata duk abunda take so har ma da wanda ba ta ce tana so ba. Da sauri ta fita daga Falon a kofar shigowa suka ci karo da Inanni ta fito tana dogara sandarta. Kai wannan tsohuwa da Jaraba ta ke, ta tsufa har ta duke sai ma da taimakon sanda ta ke iya tafiya, Kanta gabad'aya ba baki sai Furfura. Fuska duk ta tamuke sai dai Fatar taushi da hutu tare da jin Dadi ammh mganar gaskiya Inanni zata bama Chasa'una baya. Umma ta tsorata da taga Inanni na kuka yarkace yarkace. Da Sauri ta riko hannunta tana fad'in"Ga ni nan Inanni lafiya? Ko yunwa kike ji ne? Domin a tunanin Umma, Hajiya mama bata kai ma Innnani abun karyawanta ba. Tunda yau lahadi megidan na nan kuma ba da wuri suke karyawa ba. Tasan Innani da abinci kamar mai tsotsan ciki. Shashenta baya rabo da abinci har cikin Dare sai ta tashi in ba abinci ta fashe da kuka. Innani jin Muryan Umma sai taji sanyi ammh jin Abunda tace ne yasa ta kwace hannunta tana fadin"Matsa ba ni waje. Hala bani da aiki ne sai cin abinci kamar wata tsutsa!? Ana ta rai mai Daraja wa ke ta abinci? Umma ta sauke muryanta kasa tana Fadin"Yi hakuri Innani mu je ciki sai ki fad'amin me ke faruwa? Ta fad'a tana kokarin kamo Sandan hannun Inanni, ganin haka yasa Innani ta turje tana fad'in"Ina naga ta shiga ciki Salamatu? Ina nan tsaye har sai Sulaimanu ya fito" Umma ta kalleta cikin mamaki kafin tace"Wani abu ne ya faru Innani? Sai kawai Innani ta kalli Umma ta faahe da kuka da karfi tana Fad'in"Ina zan iya fada miki. Ai sai hankalin ki ya tashi bari dai shi Sulaimanun yazo shi Tunda namiji ne ya na da Dakiya zai iya saurarana" Kafin Umma tace wani abu Mallam Tajuddeen maigadi ya zo in da suke da Sauri yana fad'in"Subhanallah Hajiya lafiya kuwa? Ya fad'a yana kallon Inanni cikin damuwa ganin tana kuka, duk da kukan Innani in dai kana gidan Alhaji Sulaiman Abubakar Shinkafi to ya zame maka jiki. Innani ko kallonta ka yi in bai yi mata ta ga daman ta fashe da kuka. Innani na jin muryan Mallam Tajudden ta watsake ta daina kuka Umma ko ce masa tayi"Bakomai Mallam. Koma bakin aikin ka kawai" Har ya juya Inanni tace"Ya koma ina Salamatu? Ai gwara ya tsaya in Sulaimanu ya fito aji in dole sai an had'a da ayoyin Allah. Mallam Saju tsaya tsaya Sulaimanu ya fito" Umma ta rike haba cikin mamaki kafin tace"Innani Abban Su siyama fa bai fito ba! Ko kin kirashi ne? Innani tace"Na aika yarinyar taki Sulsana ta taso min shi. Ina ya ga ta barci Magajin gida gabad'aya ba'asan inda ya ke ba" Umma ta bude baki, kafin ta rufe Mallam Tajudden ya kalleta ta kalleshi kafin ta juya tana kallon Inanni da ke fad'in"Wai ina Sulaimanun ne? Kaji min watsewa ni Dije ni uwarsa ma na taso kan kafafuna shi uwar me ya ke yi da bai fito ba har yanzu? Kada fa na zama uwar banza ne yasa ban je har shashen na shi na taddo shi ba, na tsaya a bangaran salamatu" Sai da Umma ta Murmusa kafin tace"Innani wata Sultanan? Sultanan da ke cikin daki tun dazu? Da wani kallon Innani ta bita da shi kafin ta yi kwafa tace"Lalle ja'irar yarinyar nan da ni take mgana. Tunda taki zuwa ke uwarta je ki taso min Sulaiman." Umma ta yi kokarin riko Innani tana Fadin"Mu shiga ciki Innani. Magajin gida kuma lafiyansa kalau. Kin manta yana Zariya yaje makaranta? Innani ta yi shuru alamun Nazari kafin tace"Tsakaninki ga Allah Salamatu kwananki nawa baki yi mgana da Magajin Gida ba? Umma tace"Na yi mgana da shi jiya ma Innani" Innani ta kalleta kafin tace"Sai kin Rantse zan yarda da ke Salamatu." Umma ta yi mirmishi Tana kallon Mallam Tajuddeen. Wanda ya juya shima yana mirmishin Diraman Innani da mutum ba ya gajiya da Dariya. Umma sai da ta rantse sannan Innani ta amince da ita ta shiga Shashenta. Ta zauna kan kujera ta na share hawaye da Haban dankwalin kanta. Umma ta zauna gefenta ta ja Haban zaninta mai kyau da Tsada tana Share ma Innani hawaye cikin Sigan lallashi ta ke fad'in"Ki yi hakuri Innani. Magajin gida yana nan lafiya zai zo ya ganki kwananan in sha Allahu" Innani ta yi mirmishi kafin tace"Shikenan tunda kin tabbatar da yana lafiya. Ni daman rashin samun sa ta wayar zamanin nan ne ya Dagamin Hankali. Ammh tunda ke uwarsa kin tabbatar da yana lafiya ba ni da tacewa" Umma ta yi mirmishi kafin tace"Yana lafiya Innani in sha Allahu. Zan kuma sa ya kiraki in sha Allahu. Innani ta gyada kai batace komai ba. Umma ta mike tana fad'in"Innani me zaki ci in kawo miki? Innani ta yamutsa fuska kafin tace"Na riga na ci goro salamatu zauna abun ki. Nagode sosai Allah ya shirya miki zuru'a, yadda kike kula da lamarina kema Allah ya shiga lamarin ki" Umma ta mike ta na ta amsawa da Ameem Ameen. Duk da yadda Inanni ta ke da Tsine Tsine akwai saka albarka da kyawawan addu'o'' a bakinta. Umma kitchen taje ta hado abun karyawan su,Ta leka da kanta ta kira Sultana wacce har ta yi wanka ta saka Doguwar riga baka. Kai tsaye tace"Kina Fiki fiki da ido. Sai ki fito mu karya" Dakyar ta fito tana Tafiya sannu Sannu taki dagowa su had'a ido da Inanni, ita ko sai faman Hararanta ta ke yi tana kyafci. Umma na kallon su tana Dariya. Bata yi mgana ba sai da Innani ta tabe baki tace"Bar wani rabe rabe. Kiyuwa ko? Kin koyi bakar Dabi'a wajen yaran chan na Suwaiba kamar ni na aike ki ki k'i zuwa ko? Sultana ta zauna ta rab'e bayan Umma tana fadin"ki yi hakuri Innani" Innani ta washe baki kafin tace"Me kika yi min yar nan? Ke dai bari Uwar ki tace magajin gida na lafiya. Ni daman lafiyarsa ya dameni in ta ni ce ai Sulaimanu ya kwana ya na barcin asara Mutumin banza kawai zai ce duk koken koken da nayi bai ji ba ne Salamatu? Umma na Had'a tea tace"Bai ji Ba Innani. In da yaji kinsan zai fito shi da baya son ganin ki cikin damuwa." Innani ta tabe baki bata kara mgana ba, sai dai Umma na janta da mgana Jefi jefi. Suna gama karyawan Sultana ta kwashe komai zuwa kitchen. Daganan tana fitowa ta koma Daki ta dauki aikin makarantarsu tana Dubawa. Umma da Innani na Falo sun tsinke da Hira. daga dakin tana jin muryan Innani a sama tana mgana da Anty Surayya sai faman bude murya ta ke yi. Sultana ta Dafe kanta a fili ta Furta"Innani Hayaniya da kanta" ***** Alhaji Sulaaiman Abubakar Shinkafi Bakin Dattijo Dogo baki. Ya yi sallama Shashen Hajiya Umma, Bayansa kuma Hajiya Mama ce Farar mace alkyabban mata. Ta ci kwalliya sai faman tashin kamshi take yi. Suna tafe, wasu yara guda biyu mace da Namiji suna bin su a baya. Da sallama suka shigo falon. Shashen Innani suka fara isa bata nan. Su san ba inda zasu sameta sai Shashen Hajiya Umma. Shiyasa suka garzayo da sauri. Umma ce ta mike tana musu sannu da zuwa cikin natsuwa tace"Abban su siyama barka da Safiya.! Ina kwana Maman yara? Afiya Gud mrning" Umma ta fad'a ta na rike yar mace ajikinta. Namijin ya karisa gabanta tana fad'in"Umma" Kansa ta shafa tana fad'in"Abadallah bawan Allah" Wacce aka kira da Maman yara ta saki fuska sosai ganin Umma cikin Dariya tace"Hajiya Umma mun tashi lafiya? Ya kwanan Sultana? Umma tace"Sai hamdala ya kwanan su Abdallah? Mama tace"Ga su nan rigiman mu. Su Salima sun fara tsuwwaa sun gaji da su a maida su gidan su" Umma na dariya tace" Nan ma ai gidan su ne. Ban da abun su salima." Matan kadai ke hiran su Alhaji Sulaiman ya gurfana gaban Inanni yana gaisheta. Sai da ta dafa kanshi Sannan ta amsa lokaci d'aya tana fadin"Allah ya yi maka albarka Sulaimanu. Allah ya albarkaci samun ka,da arzikin ka. Ya raya maka zuru'a ya shirya maka su. Allah ya tsole idon makiya a kan ka yarona." Cikin jin dad'i ya ke ta amsawa'"Ameen Ameem Innani." Sannan ya koma gefenta ya zauna yana gyara zaman shaddan jikinsa. Inanni kasa kasa take kallon Mama ganin haka yasa itama ta bi bayan mijinta ta zube tana gaisheta ta amsa a Kirne kafin tace"Yaran ki hala basu gidan nan ne Suwaiba? Mama ta dago tana fad'in"Suna nan Mana Innani. Da Safe ma ai Siyama ce ta kawo miki abun karyawan ki" Innani ta tabe baki kafin tace"Au ita ce? Ai ba ta jira na ganta ba afalo ta Damkwafar min da shi ta kara gaba." Mama kanta na kasa tace"ki yi hakuri Innani zan yi musu mgana za su gyara." Innani ta kauda kai ta maida wajen Danta da ke wasa da jikokinsa,Takaici ya isheta shi kuma ganin haka yasa da Sauri ya tura su gabanta yana fadin"Ku je ku gaishe da Inanni" Gabanta suka tsaya suna kallonta. Ta dafa kan Afiya tana fadin"Yaran nan yaushe zasu koma gidan Uban su ne? Falon shuru ya yi daga Umma har Mama an rasa mai mgana sai Abba ne ya yi gyaran murya kafin yace"Sa'imar ba su dawo ba ne. Da sun dawo zata zo ta Dauke su ko Sauwaiba? Mama tace"Eh Innani da zarar sun dawo zata zo ta Dauke su' Innani ta kallesu tsab har ta na wani gyara zaman gilashinta kafin ta tabe baki tace"ai shikenan. Sulaimanu nace baka ji kuka na ba ne yau? Da Sauri yace"Subhanallah me ya faru Innani? Innani tace"To magajin gida ne ban ji sa ba kwana biyu. sai hankalina ya tashi na zata ko ya fad'a hannun banza ne, Sai da salamatu ta lallashe ni da cewa sun yi mgana sannan na yarda itama sai da ta rantse na yarda kasan karya ba ta da wuya a wajen Babba." Abba ya nmurmusa kafin yace"Ya na nan lafiya Inanni. Jiya da Daddare ma mun yi mgana" Innani tace"Shikenan tunda yana lafiya. Sati mai zuwa na fasa zuwa sha'anin nan na yar gidan Sammani Wajen jika na zani na gansa ko Hankalina ya kwanta" Abba ya kalli Matansa suka kallesa sigina ya yi ma Umma shiyasa ta gyara zama tana fad'in"A'a Inanni ai basai kin je ba. Da kanshi zai zo ya ganki" Innani ta yi shuru ta na kallonta ta cikin gilashinta kafin tace"In ma bai zo ba ke kika sani Salamatu. Alhakin rashin zuwa Duba magajin gida na kanki" Umma na mirmishi tace"shikenan innani. Sai kuma ta juya tana mgana da Abba kan bikin diyar kaninsa Sammani da za'ayi a Shinkafi Sati na sama Innani tace ita zata wakilceshi ba sai yaje ba. Abba na fad'in"Innani tare zamu. Ina so na samu Daurin aure" Kai tsaye tace"To da an gama Daurin auran ka dawo gida kaji ma na Fad'a maka" Mirmishi ya yi kafin yace"Naji Innani." Umma na jin su duk da Hankalinta na wajen su Afiya, sannan suna taba Hira da Mama. Sai dai ita tasan Dalilin Innani saboda kada yan'uwa su gansu su kawo bukatotunsu ba ta son D'anta na fitar da kudi. Abunda Inanni bata sani ba ko mako da son kudi Alhaji Sulaiman Shinkafi ya fita. Mutum d'aya ne shi kadai jalli Tal ke iya saka shi fitar da kudi ko da bai yi niyya ba. Kuma shi ke iya yanke Hukuncin da Ko Innani bata isa ta ce A'a ba ballatana shi. Innani mikewa ta yi tace zata koma Shashenta ta kwanta Harkarkarinta na ciwo. Abba Da Umma har Mama suka mike suna rawan jikin kamata. Abba ya rike mata Hannu Umma ta kama Sandarta. Ita kuma Mama tabi bayansu bayan tace ma su Afiya su zauna su dawo. Ko da batayi niyya ba dole ta raka su in ba Haka ba yanzu Innani zata hau ta kanta ta zauna. Suna fita Haraban gidan Haushin kare Huhuhuu!!! Innani ta razani ta kamkame Abba tana Fad'in"Innalillahi ni Dije? Yanzu daman Sulaimanu baka fita da wad'anan bakaken Halitun da ke Firgitani mutane da makota ba? Har ni uwarka suna hanani barci. Nan fa na gayama mala'ikun Allah basa ta kan mu tunda ka ke ijiye karnuka a cikin gidan ka" Cikin ladabi yace"Inanni ai sabo gadi ne, kinsan irin Sana'ata" Kai tsaye tace"Ka ci uwaka kai da sana'ar taka. Allah dai ya tsine ma wad'anan karnukan gabadaya" Umma na Danne Dariyanta tace"Innani Kin manta Magajin gida yace miki a bar su yana so" Nan da nan Innani tace"An yi haka kin ga ko na sha'afa salamatu. Sulaiman to kaji Magajin gida yace yana so. Kuma tunda magajin gida yace yana so an gama mgana maza ka barsu, sannan a rika basu abinci kada ya dawo kuma yaga an yi masa ba Daidai ba." Kai tsaye yace"In sha Allahu Innani." Yana mirmishi. Mama na baya sai bata rai take yi, har shashenta suka rakata nan din ma sai da suka gurfana gabanta har sai da tace su je su barta zata kwanta huta. Dalilin da yasa suka yi mata sallama kenan suka fita. Yau lahadi ce daman a  ka'idan Alhaji Sulaiman akan had'u a falon Shashen sa shi da matansa su yi su tattaunawa yaji matsalolinsu. Yau ma shashen nasa suka wuce bayan Mama ta koma Falon Hajiya Umma ta damkama Sultana su Afiya ta fice ta barta tana Tura baki. Sam bata son Hayaniya gashi kuma Mama ta had'ata da wad'anan yaran. Alhalin su Salima na chan  kwance suna hutawarsu. Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA*  zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu fama da  Ciwan sanyi  duk nacin sanyin ki hajiya kikai amfanin da maganin Mmn khairat saikin warke duk ko iya da d'ewarshi ajikinki..Domin k'arin bayani👉 WhatsApp no 07044450136, 08167453086 *Janafty* *Sep 09/2023* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:Jamilaumar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabook:Jamilaumarjanafty* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 Slm ina maiso taga tayi kiba jikinta yayi kyau tazama yar lukuta 😘ina maiso taga nono yacika yayi kyau ina maiso taga duwawu yafito kinzama cikakiyar mace ❤️ina maza da basacin abinci ina maza masuso suyi kiba ina yara da basuda kiba ina mai farin cikin sanar daku *ZUMAR K'IBA*, zumace wadda take saka k'iba cikin kwana 7 da yardar Allah *ZUMAR K'IBA* zumace mai inganchi wadda aka had'ata da magun-gunan gargajiya Masu kyau da da tasiri ajikin d'an Adam,hajiya indai kina fama da rama d'an gwada shan zumar mu kisha mamaki indai kika sha zuma sai kin chanza..,Ina masu

Chapter 6 of 24