son na taimaka musu."
Abba yace"Shikenan Magajin gida a taimaka musu."
Sadiq yace"Nagode Abba. Allah ya kara girma ina Innani.?
Abba yace"Sun tafi Shinkafi ita da Sultana tun jiya."
Sadiq yace"Abba Innani fa ba ta da wani karfin jiki ga Tsufa Tsakani ga Allah tafiye tafiye ai ba nata ba ne."
Abba yace"Kasan Innani da Kafiya. Ta kafe kuma kasan ko nace ta zauna bazata zauna ba. Da ma kai ka yi mata mgana to da zata ji maganarka."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Allah ya dawo da su lafiya."
Abba yace Ameen tambayan Su Umma ya yi da su Salima sun d'an taba hira da Abba sannan suka yi sallama.
Ya isa abitin Biyar Daidai,
Shi bai yi tunanin siyan komai ba, kai tsayensa ya shiga har Dakin sai dai abun da ya basa mamaki ta nan zaune ita kadai kamar yadda ya barta.
Bata ma san ya shigo ba sai da ya yi sallama sannan taji shigowarsa.
Zumbur na mike ina kallonsa shima ni ya ke kallo sai naji nauyi na dukar da kaina ina Fadin"Ina yi ni."
Cikin Natsuwarsa ya amsa da Lafiya lau ya mai jiki?
Na amsa da sauki cikin kulawa ya karisa gaban gadon Amma kafin yace"ba ta tashi ba ne?
Da sauri na ce"Ta tashi dazu, sai dai kuma ba dadewa ta koma."
Kai tsayen shima yace"Bata ci wani abu ba kenan?
Da kai na amsa masa kafin nace"Ruwa kawai tace na bata tasha sai kuma ta koma."
Jinjina kai ya yi lokaci daya ya na harde hannayensa saman kirjinsa.
Ya na kuma bin nazarin dakin da kallo daga alamun dai ba wanda yazo.
Ga sauran wainar da ya siyo mata da Safe nan ta rage. Sai ruwa wanda ya ke tunanin kila siya tayi tunda shi dai bai siyo musu har da ruwa ba.
Cikin mamaki yace"likita ya zo ne?
Kai Tsaye nace"Eh ya zo ya dubata ya tambayeka nace ka je ka dawo. Sai ya ba ni wata takarda yace na baka."
Na fad'a ina dauko masa Takardan saman dirowan da ke wajen na mika masa.
Karb'a ya yi ya duba magunguna ne shiyasa kawai ya fice bayan yace yana zuwa Phamarcy yaje ya siyo mgangunan Atm dinsa ya ba da aka cire akwai sauran kudi kafin Abba ya Turo masa daganan ya fita waje ya siyo katan din ruwa da maltina ya had'o mata da kayan marmari sannan ya Dawo daki.
Yana shigowa na taso na karbi' kayan hannun nasa ina masa sannu. Ledan mganin ya sakarmin shi kuma sauran ya karisa ya sauke da Hannunsa.
Sannan ya juyo ya na fadin"Mgangunanta ne in likitan yazo ki nuna masa."
Sai na gyad'a kai kaina a kasa ina fadin"Allah ya saka da alheri."
Ya amsa da Ameen.
Gefe ya koma ya jingina da Bango ni kuma sai na koma na zauna Shuru na wani Lokaci kafin yace"ba ki kira gidan ku ba ne?
Kaina na kasa nace"Ba ni da waya ne shiyasa."
Bai yi mamaki ba illah wayarsa da ya fito da shi ya na fadin"Ga wayata in dai kin haddace lambar."
Da Sauri nace"Eh na haddace."
Mikewa na karisa na karb'a ina fadin nagode ya amsa min da gyad'a kansa.
Gefe na koma na saka lambar Adda Fati na kirata har ta katse bata Dauka ba. Sai na kara kira sannan ta Dauka ina jin Hayaniya ta cikin wayar kai Tsaye nace"Adda ni ce Hasiya."
Dagachan bangaran tace"Hasiya. Hasiya kuna ina ne? Ga mu nan hankula tashe tun safe Maman Boy ta kirani tace Amma ba lafiya kun tafi asibiti ga shi bamu san asibitin da kuke ba kina ina ne yanzu!? Ina Amman ta ke?
Cikin Sanyin murya nace"Adda muna asibiti tun jiya. Amma kuma an bata gado."
Da Sauri Adda Fati tace"Kuna wani asibiti ne? Ga ni ga Inna Talatu ga Ramatu zamu taho."
Kallonsa na yi shi kuma hankalinsa na kan tagar dakin.
Tunani sunan da yaji ta ambata ya ke yi.
"Hasiya.?
Hasiya suna ne?
Sai kuma yaji tana fad'in bata san sunan asibitin ba.
Sai ya kalleta nima daidai na juya ina kallomsa sai ya lumshe min ido kafin ya Bude kai Tsaye yace"Ba ni wayar na fad'a mata."
Ba musu na mikamasa baayan na ce ma Adda ga shi za'ayi mata kwantance.
Karban wayan ya yi, bayan ya yi sallama sun gaisa da Adda sannan ya Fad'a mata sunan asibitin sannan suka yi sallama.
Tun bayan gama wayar sai Dakin ya Dauki shuru sai da aka kirasa a waya ya fita ya jima bai dawo ba. Sai ga shi an bude kofa ina juyowa naga Adda Fati kan gaba sai Ramatu sai Inna Talatu sai maman boy da maman Salihi da kaltume.
Ni ba ta su na ke ba mikewa na yi ina musu maraba. Ina jin Maman boy na fadin'Sannu Hasiya."
Takaici yasa ban amsa ba sun san da Sannu ne ina neman taimakon su ba su taimakamin ba.
Duka suna Tsaye gaban gadon Amma na ce ma Adda"Wa ya nuna muku dakin?
Adda Fati tace"da wayar da kika kirani, na kira sai ga shi wani Saurayi ya fito ya shigo damu har nan likita ne?
Sai na girgiza kai kafin nace"Shi ne wanda ya taimakamin aka kawo Amma asibiti. Adda tare muka kwana sai da safe ya tafi dazu nan ya dawo shi ya kashe komai da a ke bukata."
Inna Talatu tace"Allah Sarki Allah ya biyasa."
Su Adda suka amsa da Ameen su Maman boy suka fara daidaiciyar mgana wai ba su ji bugun kofata ba sai daga baya.
Ramatu ko kusa da ni ta dawo ta na fadin"Hasiya kin ci abinci!?
Na gyada kai kafin nace"Ya siyamin waina yanzu kuma ya kawo wad'anan kaya da mgangunan Amma."
Ramatu tace"Angode masa. na zo da abinci fulas ne bamu yi tunanin Daukowa ba."
Adda tace"Sai na koma na Dauko ba matsala."
Inna Talatu ta kalleni tace"ba ta farka ba ne.?
Kai tsaye nace"Ta farka ta sha ruwa ta koma sun ce jininta ne ya yi kasa."
Suka jinjina kai suna mata fatan samun lafiya.
Ba mu ji turo kofarsa ba sai jin sallamarsa muka yi.
Gabadaya mu ka juya muna kallonsa.
*Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.*
*Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.*
*SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode*
*Janafty*
*TSAKA MAI WUYA.*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Mallakar:Janafty*
*Arewabook:Jamilaumarjanafty*
https://chat.whatsapp.com/GoRzZ7ZgslV2alO5hYGAnj
*15*
Cikin takun natsuwarsa ya karisa shigowa cikin D'akin.
Yadda muka zuba masa ido ne yasa ya da'n dukar da kansa ya na fad'in"Sannun ku. Ya mai jikin?
Sai suka amsa gabadaya da sauki kafin su shiga gaishe shi ya amsa cikin sakewa Adda da Inna talatu ne suka fara masa godiya.
Kansa na kasa yace"Bakomai.."
Ni ya kallah nima daidai lokacin na Dago ina kallonsa da Sauri nace"Uhm wannan yayata ce Adda Fati. Sauran yan gidanmu ce wannan kuma kawata ce."
Na fad'a ina nuna Masa Ramatu kallonta ya yi lokaci d'aya ya na fadin"Sannun ku zuwa."
Suka amsa masa sai dakin ya dauki Shuru Adda Fati sai ta katse shurun da Fad'in"A nan garin ka ke?
Kai tsaye ya kalleta kafin yace"A'a."
Daga haka bai kara cewa komai ba.
Inna talatu tace"Angode sosai Allah ya saka maka da alheri."
Bai amsa ba kansa na kasa sai dai ya na ta faman mirmishi.
Karisawa ya yi ya duba Amma na d'an lokaci kafin yace min zai tafi.
Adda ta fara jero masa addu'o'i ita da Inna Talatu.
Baya amsawa sai dai yace bakomai kawai ammh da Inna Talatu tace"Allah ya jikan magabata. In iyayenka na raye Allah yasa su gama lafiya. In kuma ba sa raye Allah ya ba su Aljannah."
Ya na gabda zai fita ya juyo cikin mirmishi sannan ya amsa da"Ameen Ameen Nagode."
Daga haka ya fice Ramatu ta zungureni ta na fad'in"Ki raka shi mana"
Kallonta na yi sai ta gyad'a min kai daidai Lokacin da Adda ke kara fad'in"Hasiya bi shi mana. Ki kara masa godiya."
Maman boy da gulma tace"Wlh kuma daga gani asibitin akwai cacan kudi. Tunda ba ta gwamnati ba ne"
Jin haka yasa na bisa da Sauri har ya kai Haraban asibitin ya na tafiya. Sai na kasa kiran sunansa illah sauri sauri da na rika yi har na cimmasa.
Tsayawa ya yi ya na kallona kafin yace" Me yasa ki ka fito?
Kaina na kasa nace"Na zo ne na kara maka godiya."
Mirmishi ya yi kafin yace"Godiyar nan ta isa hakanan HASIYA.."
Kallonsa na yi cikin mamakin kiran sunana da ya yi sai ya ware min ido ya na fad'in"Ko ba sunan ki kenan ba?
Kai na gyad'a masa cikin kunya alamun hakane cikin yar mamaki ya kalleni ya na fad'in"Hasiya sunane? Sunan ba Asiya ba ne?
Kai na girgiza masa kafin nace"Hasiya ne sunan."
Shima cikin girgizamin kai yace"To ko dai sunan Fulani ne?
Kallonsa na yi kai tsaye kamar yadda ya ke kallona. Ya ga mahaifiyarmu da zanen Fulani a gefen bakinta, Da kuma gefe da gefen fuskarta.
Sannan yaga Adda Fati da nace yayata ce itama sai yaga yanayinta kamar na Fulani ko buzaye so ya ke ya tabbatar.
Na rasa me zan ce masa ne yasa nace"Amma ce bafullatana. Baba kuma bazazzagi ne, Sunan Hasiya kuma kanwar Baba ce da ta rasu, sai ya maida min sunanta."
Kai tsaye yace"Kenan ki na jin Fullanci.?
Kai Tsaye nace"ba na ji fa sai abunda ba'a rasa ba."
Mirmishi ya yi kafin yace"Na sha kina ji ne nace ki koyamin. ni ban iya kowani yare ba."
Baki na bude kafin nace"Wlh ni ma ban iya ba."
Yadda na yi saurin rantsewa yasa ya yi mirmishi kafin yace"Ban ce ki rantse ba. Yanzu ammh gida zaki koma ki yi wanka ki huta ko?
Ni ban yi wannan Tunanin ba sai da ya fad'a sai na kara bin kaina da kallo yarkace yarkace kamar yar gudun Hijira.
Sai naji kunya na dukar da kaina ina wasa da gefen zanin Amma da na yi Lullubi da shi.
Shi ko bai damu ba kai tsaye yace"Gaskiya ya kamata ki je gida ki Huta."
Da toh na amsa shi har mun yi sallama akan gobe zai dawo ya kara Duba Amma da jiki. Na juya zan koma cikin asibitin sai ya kawai naji muryansa cikin kaushi ya kira sunana.
"Hasiya.."
Da sauri na juyo ina fad'in"Na'am.."
Ya na daga in da ya ke yace"Ki kwantar da Hankali zata warke kin ji ko?
Sai na gyada masa kai. Mirmishi ya yi ya juya ya fara tafiya sai ga shi na Tsaya har sai da ya bace ma ganina.
Mirmishi na yi acikin raina nace"Daman ma su suna Abubakar suna da kirki da jin kai."
Cikin asibitin na koma na iske duk sun fito waje Adda Fati ne ke tare da Amma aciki sai na karisa kusa da Ramatu na zauna muka kara gaisawa.
Nura na tambaya tace min da Safen nan ya wuce na gyada kai ina masa Fatan isa lafiya.
Noor ta ke ba ma Nono sai da ta gama na karbeta ina yi mata wasa. kallona ta yi kafin tace"Ya jikin ki ke ma?
Kai tsaye nace"Ni ai na warware."
Da sauri tace"Sai kumburin Fusakarki bai sabe ba."
A hankali nace"Zai washe shima."
Ramatu tace"Ki ci abinci ga shi nan na Fito miki da shi."
Na amsa mata da toh.
Tazo da filet da cokali sai na Dibi abincin naci Faten wake ne da kifi kadan ma naci saboda cikina ba ya min dad'i.
Ramatu tace"Yakamata ki je gida ki yi wanka ki sauya kayan jikin ki."
Kai Tsaye nace"Shima haka ya ce."
Ramatu tace"Shi wa?
Cikin sigar mamaki. Mirmishi na yi kafin nace
"ABUBAKAR SADIQ.."
daga kasan raina na fad'i sunan saboda Muhimmanci da sunan ke da shi a Rayuwata.
Ramatu tace"Au Abubakar Sadiq sunansa? Ma sha Allah wai a ina kuka had'u?
Kallonta na yi kafin na fara bata labarin hadu'warmu na karishe da fad'in"Saboda Rudewa haka na zo asibitin nan ba takalmi. Bawan Allah nan takalminsa ya bani na saka sai da ya fita ya siyomin wannan sannan ya karb'i na shi. Ramatu gaskiya ya na da kirki tare da abokinshi suka kwana a asibitin nan da Amma fa."
Ramatu tace"Gaskiya ya na da kirki. Allah ya ba shi lada."
Na amsa da Ameen. Mun cigaba da Hiran kirkin Sadiq. Kafin Adda ta fito tace Amma ta farka gabdaya muka Dumguma cikin dakin.
Amma ta bude ido tas ta na kallon kowa ta na gane kowa duk wanda ya gaisheta sai ta amsa sannan ta ambaci sunansa.
Ina zuwa kusa da ita na riko hannunta ina Fad'in"Amma kin bani Tsoro na zata tafiya za ki yi ki barni."
Amma ta yi mirmishi cikin muryan ciwo tace"ke ce ki ka ba ni Tsoro, Ba na so ki yi nesa da ni Hasiya."
Kai na gyad'a mata ina fad'in"In sha Allahu ba in da zan je Amma. Ina nan tare da ke sai mutuwa."
Amma na dariyan jin dadi murya a sanyaye tace"Sai aure dai ko Hasiya.?
Sai naji kunya na dukar da kai Inna Talati ke fad'in"In sha Allahu sai aure zai Rabaku."
Gabadaya Murna ta cikani ganin Amma ta samu lafiya.
Cikin muryan ciwo Amma tace"Wa ya kawo ni asibiti?
Muka kalli juna ni da Ramatu kafin ma nayi magana Adda tace"Wani bawan Allah ne Amma. Yanzu ya fita ba da jimawa ba."
Amma ta jinjina kai kafin tace"Allah ya biyasa da Aljannah."
Muka amsa da Ameen Ameen.
Adda Fati na fad'ama zan je gida na Dawo tace ya kamata kan naje na gyara jikina.
Nan na bar Adda Fati da Ramatu tare muka fita da Inna Talatu da su Maman Salihi Inna talatu ta samu abun hawan zuwa sabon gari. Mu kuma muka samu na anguwan mu.
Suna ta min daidaiciyar mgana ko kallonsu ban yi su kan su susan ba su kyauta ba kowa ya yi nagari ai ya sani.
Ina komawa gida na iske dakin sakayashi kawai akayi, Gawayi na fara Hurawa na saka ruwan zafi sannan na gyara dakin na Share.
Matan gidanmu sai fad'a min su ke yi an yi ta zuwa neman Danwake babu. Ya ke kawai na yi musu ana ta rai wa ke ta wani Danwake.
Sai da na yi wanka na cire kayan jikina na saka wata atamfa Riga da Sikat na siya kamu na Dama na sha, sannan na Dorama Amma ajug zan kai mata asibiti na kuma Daukan mata zannuwa da Hijabi nima na Dauki kaya kala d'aya da Hijabi sai abunda zan gyara jikina Tunda ba na Sallah.
Sai yammah na Rufe Dakin Amma da makulli na koma asibiti. Adda kad'ai na iske Ramatu ta tafi, itama ina Dawowa ba Dadewa ta tafi akan sai gobe zata dawo. Ni na kwana da Amma wacce ta ji sauki sosai likita ya zo ya dubata sannan Nurse suna zuwa bata mgani da saka mata ruwa.
Washegari na yi ma Amma wanka Tunda ga bayi sannan akwai Ruwa. Da ya ke na Tsaftace makewayin yasa nima na shiga na yi wanka na gyara jikina.
Har rana ba wanda ya zo. na zo da kudi a hannuna na fita waje na siyo ruwan zafi da kayan tea na zo muka had'a tea ni da Amma muka sha ni kuma sai na had'a da waina.
Nazo da magunguna nima na balla na sha Amma ta na yawan yin barci Saboda inaga allurai da magunguna da suke bata tunda sun ce Hutu ta ke Bukata.
Wani abun mamaki da na ji karan Bude kofa sai na juyo da Sauri na zata ko Shine sai naga bashi ba ne.
Har Adda Fati ta zo da rana, zuwa la'asar sai ga Adda Rukayya da Habiba sai bani Hakuri ta ke yi da abunda ya Faru ta na gayamana ta yi ma Babansu Amna Hauka da yasa Dole sai da yaje ya ja ma yan'uwansa kunne.
Ban ce komai ba sai da ta Dafani ta na Fad'in"Ki yi hakuri don Allah Hasiya."
Sai na girgiza kai kafin nace"Bakomai Adda."
Amma na barci sai daga baya ta tashi. Maltina na bata tasha na rakata bayi tunda sun cire mata karin ruwa alwala ta Dauro.
Tazo ta yi sallolinta daga zaune daman da Safe haka ta yi ammh Alhamdulillah jiki da sauki.
Adda Fati ne tace"Amma ko na kira Adda na fad'a mata?
Amma tace''A'a kada ki tada mata Hankali kyaleta kawai."
Daman nasan haka Amma zata ce, ko ciwo ta ke yi bata son a kira mata Adda kada wai a tada mata Hankali.
Adda Fati da Adda Rukayya tare suka tafi sai aka bar min Habiba tare da ni.
Ba matsalan abinci Adda Fati ta zo min da Fanten doya da allayahu.
Har na cire rai da zuwansa sai ga shi da Daddare bayan isha'i sun zo da abokinsa mara sakewa da Mutane sai akaci sa'a Amma na farke ba ta koma barcinta na fama.
Sanda suka shigo ina bayi sai Habiba kadai suka iske kallon rashin sani Sadiq ya yi mata. Ita ma haka ta yi masa sai dai ya ga kamarta da Amma da Adda Fati su suna da jan fata ba irin Fari na garesu ba.
Habiba ta gaishesu suka amsa suna tambaya ya mai jiki?
Habiba tace ta samu sauki gata nan ma ba ta koma barcin ba.
Tahir dai na daga baya Sadiq ne ya karisa gaban gadon Amma.
Sanye ya ke da kananun kaya Riga da wando. Rigar mai kalan Ruwan kasa da layi layi ta na da Dogon Hannu. Wandon kuma mai ruwan kasa ne kafarsa cikin Rufaffen takalmi.
Amma tunda ta gansa jikinta ya bata Bawan nan ne Allah da ya kawota asibiti.
Daman tun dazu ta ke ma Hasiya mgana sai tace mata bai zo ba.
Yana gaisheta ta amsa cikin Sakewa lokaci d'aya tace"Abubakar ne?
Cikin mamaki ya ce"Eh ni ne Mama."
Amma ta muskuta ta na son mikewa da Sauri ya kamata ya na kara mata Filo ta baya.
Amma ta kallesa haka kurum taji Saurayin ya shiga ranta.
Cikin Mirmishi da muryan ciwo tace"Nagode Allah ya yi maka albarka."
Ya amsa da Ameen sai lokacin Tahir ya kariso ya na mata sannu ta amsa masa shima cikin sakewa.
Sadiq yace"Abokina ne."
Amma ta jinjina kai kafin tace"Allah Sarki nagode sosai Hasiya ta ba ni labarin irin taimakon da kayi mana. Allah ya ba ka lada. Allah ya biya ka da gidan Aljannah"
Da Ameen Ameen ya ke ta amsawa.
Tahir ko na gefe ya na bin ko'ina da kallo fuskar nan dihim.
Ya rasa dalilin Sadiq na matsa masa sai ya rakosa asibitin nan. Ka taimaki mutane to ba sai ka rabu da su ba ina laifi? Ammh lamarin Sadiq sai Allah kawai da ya Hallicesa game da maida lalura da Damuwan Mutane na shi.
Amma ta kalli Habiba ta na fad'in"Habi Hasiyan ba ta fito ba ne?
Habiba tace"Ba ta fito ba Amma."
Sai Amma ta kallesu ta na Fad'in"Hasiyan ta shiga makewayi ne."
Sadiq ne ya gyad'a mata kai, Suna Tsaye dai daga gefe ledan da Sadiq ya shigo da ita a hannun ya mikama Habiba ta karb'a ta na fadin"Angode."
Sai ta duba abunda ke ciki Taga Tsire ne mai yawa da Sauri tace"Amma nama ne."
Ta fad'a cikin jin dadi. Daman Habi da son Nama kamar wata kura. Amma ta yi mirmishi kafin tace"Allah ya ba da Lada. Allah ya yi shi albarka"
Dukkansu ba su amsa ba Tahir sai danna wayarsa ya ke yi shi kuma Sadiq ya harde hannayensa saman Kirjinsa.
Kai tsaye na fito daga makewayin. Tabbas na ji mganganu ammh ban Dauka shi ba ne. Na zata nurses ne ko Likita sai da na fito dagani sai Doguwar rigar jikina da Dankwali.
Kuma ta facing dinsa na fito daidai ya Dago nima na Dago mu ka had'a ido.
Wlh sai na ji kunya. na dukar da kaina kafafunawa na rawa na fara takowa cikin Dakin.
Amma ta tareni da Fadi'n "Sun zo tun dazu Hasiya."
Tahir a ransa ya maimaita Sunan Hasiya a ranshi.
Tabe baki ya yi yace daman ai daga ganinsu kauyawa ne.
Kuma ta dace da sunan nata Hasiya.
Ban samu natsuwa ba sai da na Rarumi Hijabina na zura sannan na gaishesu Abubakar ne kad'ai ya amsa cikin Sakewa Tahir daga lafiya shikenan bai kara ba.
Habiba ta nuna min Naman da suka zo da shi,godiya na yi masa bai amsa ni ba illah cewa da ya yi"Kuka ya kare ko? Tunda naga jikin Maama ya yi Sauki ko?
Ban ce komai ba sai dai na Rufe Fuskata da Tafin hannayena.
Amma ce ta amsashi da cewa"Hasiya ai sarkin kuka ce. Ita dai in dai ta ganni ina ciwo bata kara sukuni sai ta ganni na warke tukunnah."
Sadiq yace"Allah sarki. To ta kwantar da Hankalinta kin samu lafiya."
Amma tace"Ah Alhamdulillah. Jikina ne kawai ba karfi."
Sadiq yace"Shima a hankali zaki ji ki warware."
Amma tace"In sha Allahu."
Shuru na wani lokaci ba wanda ya yi mgana Tahir na kuncin ya gaji da Tsayuwa Sadiq kuma na Tunanin Jikin Hasiya da yanayinta ya boye Shekarunta. In dai ya canka daidai Yarinyar nan kanwarta ce kenan ta girmi Sultana sai dai kila sa'ar Salima.
Amma ce ta katse masa da Tunani da Fad'in"A nan garin ku ke ne?
Sadiq yace"A'a Mama karatu mu ke yi anan d'in."
Amma tace"Allah Sarki Allah ya taimaka."
Sadiq ya amsa mata.
AMMA bata gaji ba ta kara kallonsu ta na Fad'in"To a wani gari ku ke ne?
Tahir ya kallesa shima ya kallesa ganin Haka yasa Amma tace"ku yi hakuri ina son sani ne saboda taimakon da ka yi mana."
Sadiq ya jinjina kai kafin yace"Ni d'an kauyen Shinkafi ne da ke zamfara. Abokina kuma mutumin Daura ne."
Tahir ya kura masa ido ya na mamakin meyasa Sadiq ke son boye kansa.
Bai gama mamaki ba yaji Amma na tambayan akwai iyaye ko babu?
Bude ido ya yi da hanci ya na kallon Sadiq sanda yaji ya na fad'in"Ba bu Mama a kauyen mu na taso hannun Dangin mahaifina"
Amma cikin Tausayawa tace"Allah sarki.Allah ya jikansu da Rahma kada ka damu ni ka Dauke ni a matsayin uwa kaji ko?
Sadiq ya jinjina kai ya na fadin"Nagode Mama."
Tahir mamaki bai barsa ya yi mgana ba.
Yana jin Amma na ta yi ma Sadiq tambayoyi yana amsa mata da cewa sun gama karatu suna Hidimar kasa ne a zariya d'in. Suna cikin mganar ne Likita ya shigo ya duba Amma ya na fad'ama Sadiq bayan sun gaisa cewa Amma zata kai sati anan suna Bukatar ta kara Hutawa ya ce bakomai.
Bai jima ba ya fita bayan ya yi ma Amma yan Tambayoyi. Bayan fitan likita ba su jima ba suka yi mana Sallama suka fita Amma na ta saka albarka da addu'o'i.
Har waje na rakasu Tahir haraban Asibitin ys fita ya na jiran Sadiq da Tarin mamakin da ke ransa.
Nima dai godiyar na sake masa bai amsa ba kai tsaye yace"Kannen ki nawa ne?
Cikin mamaki nace"Ni?
Sai ya gyad'amin kai cikin natsuwa nace"kanwata d'aya ce Habiba wacce kuka gani. Mu hud'u Amma ta Haifa Adda Rukayya baka ganta ba sai Adda Fati wacce ka gani jiya sai ni sai Habiba."
Kai ya jinjina kafin yace"Ashe ba yarinya bace. Da kallon yar ficika na ke yi miki."
Maganarsa sai ta sakani Dariya kafata ya bi da kallo. Nima sai na bi in da ya ke kallo sanye na ke flat shoe baki na Habiba ne ma ya yi min yawa Tunda Habiba ta fi ni cikar tsokar kafa.
Kai tsaye yace"Wannan takalmin ba naki ba ne ko??
Ina yar dariya nace"eh na Habiba ne. Ammh ya aka yi ka gane ba nawa ba ne?
Yana mirmishi yace"Saboda kafarki ba ta boye takalmin ki."
Dariya na yi har hakora suka bayyana waje. Shima sai naga ya yi dariyan sai na shagala da kallonsa ganin yadda ya yi kyau kamar wata Daran goma sha Hud'u.
Cewa ya yi na koma ciki bari ya tafi muka yi sallama sai da na juya yaga wucewa sannan shima ya tafi.
Ko da yaje Tahir ya cika saura kadan ya fashe ya na cewa"mu je.'
Tahir ya balla masa Harara ya na Fad'in"Wai son zabiyar yarinyar nan ka ke yi ne Sadiq?
Cikin mamaki Sadiq yace"Sunanta Hasiya ba Zabiya ba."
Tahir ya yi dariya kafin yace"Wai Hasiya. Juz imanging fa, Sadiq ka fara son wannan yarinyar ne?
Sadiq ya yi gaba ya na fadin"Wani irin so kuma? Tahir ka rika saka Tunani in zaka yi mgana pls"
Tahir ya bi bayanshi ya na fadi'n"To na rasa gane maka. Yadda ka rasa sukuni Saboda Mutanen nan da yadda ka ke washe ma yarinyar nan baki Sadiq Sannan har da karyan su Umma da Abba sun rasu fa! Duk saboda menene ka ke aikata haka?
Kamar bazai yi mgana ba sai dai ya juya ya na kallon Tahir suka Tsaya a bakin asibiti suna kallon juna kafin yace"Tahir kasan taimako dabi'ata ce ba su ne na farko ba. kuma baza su zama na karshe ba. Baka ga su na bukatar neman taimako ba ne?sannan da ka ke mganar so? Son wa? Wannan yarinyar ne zan so? Bata cikin Tsarin matan da ni ke so Tahir."
Tahir yace"Na ji ba sonta ka ke yi ba. Taimako ne. To kashe su Umma da kayi da ran su ba da karyan asalin da ka yi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 24