Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ce Sanadinsa halin da muke ciki duka Laifin na kaina, Sabo da ni Dangin mahaifin mu suka Gujemu kowama ya gujemu Abubakar ya aureni ya sakeni Salisu ma haka. Duk kuma ace haka kurum abubuwa ke faruwa dani kamar ni kad'ai ce Y'a a wannan Duniyan? Tabbas akwai kamshin gaskiya. na fara Tunanin tunda na zama Annoba ga al'umma to banga amfanin Rayuwata ba ko na Mutu, ko kuma na yi nesa da Rayuwar da ni ke ciki. Ina ji Adda Rukayya ta kira Adda Fati sun yi mgana sannan an ba ma Amma ta na ta bata Hakuri. Adda Fati ta dafani ta na Fad'in"Rukayya na gaishe ki. Tace a yi miki sannu gobe kila ta shigo ita da Habiba." Ban so na yi mgana ba Saboda ba na jin yin mgana da kowa ammh a wannan gabar ina bukatar wani karin bayani, idanuwana jajir na dago ina kallon Adda Fati fuskata duk ta kumbura saboda kuka da duka cikin Dashewar murya nace"Adda Fati ban gane wani abu ba? Me yasa Adda Rukayya ta damu saboda dangin Mijinta sun Tozartani." Adda Fati tace"Kada ki manta Rukayya jininki ne Hasiya. Duk in da aka kai aka kawo ba ta da kamarki kamar yadda ke ma baki da kamarta." Na yi mirmishi ina jin yadda bakina ya Bushe da makogwaro na. Ban ce komai ba na maida kaina cikin gwiwoyina na suke. Inna Talatu ne tace"Ita Halin Rukayya Wauta ne da rashiin wayau. Ammh ba ka budema miji sirrin yan'uwanka ka rika bata su a idon sa saboda gudun watarana ga shi yanzu sun yi abu kuma ya zo ya na Damunta." Sai alokacin Amma ta saka baki jikin Raunin zuciya da na jiki tace"Kuma shi wannan dan'uwa da ka ke Tunanin wani ya fisa. To duk duniya shi ne naka akwai kuma bangaren da Dole naka ne zai iya kare maka shi. Baren bazai iya ba. Ina Fatan wannan abun ya yi sanadin dawo da Rukayya cikin Hayyacinta." Adda Fati ta amsa da Ameen kafin tace"Kuma fa Amma ita zata iya yima Hasiya. ammh in wani ya ci zarafinta sai abun ya fi yi mata zafi kamar yadda ya faru. Wani kuma Tozarcin da suka yi har da zugan Kanwar Abubakar din nan tare da maganganun dangin mu muma." Adda Fati ta sauke ajiyar rai kafin ta cigaba da fad'in"Tunda da bakinsu suke fad'in ga abunda suke fad'i a kan Hasiya. Har suna fad'in suma Dalilin haka suka gujemu, Kuma da gaske ne sun gujemu ba mai neman mu ko sha'aninsu wani Lokacin bama sani suna yin shi. Yanzu Baaba ta lagos sai ta zo garin nan sau biyar dakyar zata zo gidan sau d'aya to wai har gwara ita akan su Baba Tanko shi Baba Jibril karshe da shi da iyalansa ma ba su san inda muke Rayuwa ba. Sai Baba Saminu shi kuma daman tsegumi ke kawosa ya zo ya fad'i mganganu ya kara gaba gabadyansu ba mai Mu'amala mai kyau damu." Amma ta jinjina kai kwarmin idanuwanta sun cika da ruwa cikin wani yanayi tace"Uhm. Ni kaina sun ba ni mamaki kuma lokacin da Alhaji ke Raye wlh ya yi musu komai ya samu na yan'uwan shi ne da iyalansa, ammh yanzu in da zai dawo Duniya yaga Halin da suka barmu a ciki na Tabbata zai yi bakinciki mai yawa." Inna Talatu tace"Ai Allah ne ya kawo mu zamanin Zumuncin zamani. Daga kai sai kauri, in kana da shi ayi da kai in baka da shi kuma kai da banza duk Daya." Amma na sharan hawaye da Gefen zaninta Lokaci daya ta na fad'in"Akwai Allah. Watarana sai Labari komai zai zo ya wuce Rayuwa zata fita daga cikin Tsaka mai wuya, komai kuma zai yi daidai in sha Allahu." Duk ina jinsu ammh ban tankan su ba na riga na samar ma kaina mafita da ni ke ganin shine daidai da Rayuwata da rayuwar kowa sai dai na zabi na yi shuru da bakina ba na son ma wani ya Lallasheni ballatana ya bani baki. Adda Fati ita tayi aikace aikace ta yi abinci ni kam ko a bakina sun yi sun yi nace na ce na koshi ina nan kwance ina kukan zucci da na Sarari jiya an yi min Tozarcin da bazan taba mantawa da shi ba Tsirara a kayi min ana dukana da Zargin maita da kananun Shekaruna na ashirin da Biyar Shekaruna na Duniya, na Dand'ani Dacin Sakin aure har sau biyu bayan Tarin Tozarcin da ke bibiye da Rayuwata. Adda Fati da Inna Talatu sai da Yammah suka tafi, Adda ta yi ta ba ni Hakuri kan ta tafi,  inna Talatu kuma roko na ta ke yi kan naci abinci toh kawai na ce musu ba domin na amince da duka mganganunsu ba. Zama a iren gidajen haya irin Gidan mu mtsala ne duk abunda ya faru in dai sun sani sai mutanen gari sun gama ji ballatana ni da Labarina ya yi Tambari a gari. Magana har ta yad'u a gari makotana nata shigowa yi ma Amma jaje da ganin Halin da na ke ciki, abun sai ya kara tabani batare da Tunanin komai ba su Adda na tafiya na mike ina ganin jiri ammh ban damu ba na fara Had'a kayana cikin akwatina babba tun ta auran Abubakar ne, Tunda ya barmin komai da akwatin da duka kayan gidan Gabadaya. Amma na kallo na ta kasa mgana sai da taga shirin nawa ya fi karfin hankali sannan tace"Hasiya lafiya.? Me yasa kike had'a kaya.? Kai Tsaye nace"Amma wajen Adda zan koma bazan iya juran zama na anan ba." Da Sauri Amma tace"Hasiya ba na kashe wannan mganar ba? Ba inda zaki koma nan zaki zauna tare da ni." Kai Tsaye nace"ni kuma ba zan zauna ba Amma ko ki barni na koma wajen Adda ko kuma na shiga Duniya." "Hasiya..!" Tsawa Amma ta dakamin da yasa na Fashe da kuka ina Fad'in"To miye amfanin Rayuwata tun bazan sama ma kaina sukuni da mutanen da ke Zagaye da Duniyata ba? Amma ki Fad'amin meye amfaninna? Ai gwara na Mutu ko kuma na yi nesa da ku gabadaya hankalin ku ya kwanta nima nawa ya kwanta.." Na karishe fad'a cikin gunjin kuka Juyowa na yi ina kallon Amma Lokaci D'aya ina nuna saitin zuciyata na cigaba da fad'in"Anan daidai wajen na ke jin kuna Amma. Jiya fa Tsirara a ka yi min ana kira na da sunan Maita. Amma ki fad'amin akwai Tozarcin da yafi wannan ne? Ki fad'amin ta yadda zan iya yaki da Tsaka mai wuyar da ni ke ciki? In ban yi tunanin kashe kaina ba, ban yi kuma yi tunanin shiga Duniya ba. To Amma ki bar ni na koma wajen Adda zan fi samun kwanciyar Hankali." Kuka na ke yi har sai da na Durkushe Amma ta kasa tasowa itama jiri ta ke gani in ta mike cikin karfin Hali tace"Hasiya na ce miki ba zaki koma ko'ina ba ko? Tare zamu zauna Mutuwa ce ko aure kad'ai zasu Rabamu." Cikin Ihu nace"Ni kuma in na cigaba da zama anan mutuwa zan yi Amma don girman Allah ki bar ni na tafi." Amma na kuka ina kuka kafin tace"Sai dai ko mu tafi Gabadaya ammh bazan barki cikin wannan rayuwar ta tsaka mai wuya ke kad'ai ba." Jin haka yasa na kasa mgana na koma na dora kaina kan akwatin da na cika da kaya ina ta kuka Halin da nike ciki yasa ko Danwake ban tuna da shi ba. ina ji da Safe ana ta zuwa Nema su maman Boy suna fad'in babu mai Danwaken ba ta da lafiya. Bayan mangriba sai ga Ramatu da Nura sun zo Dubani ita tazo min da Su maltina da Madara sai kayan Marmari da magungunan jiya da Aka Rubuta suka siyomin. Zuwan Ramatu yasa Amma tace duk yau ban ci wani abu ba Ramatu ta fara lallashina da Fad'in"Haba Hasiya kin san kina da lalura me yasa zaki zauna da yunwa.? Hannunta na Dauka zuwa Saitin zuciyata ina fad'in"Daidai nan ne ke min ciwo Ramatu. Wlh na zabi mutuwata da wannan Rayuwar." Da Sauri ta Rufemin baki ta na Fad'in"Ki daina fad'in haka Hasiya. Allah na sane da ke kuma shi ya zaba miki wannan Rayuwar. Fad'in haka kuma Daidai ya ke da nuna masa baki yarda da kaddaransa ba." Kuka ya kwace min na kwanta akan Cinyarta na fashe da kuka ina Fadin"Kaddaran ne tamin nauyin Dauka Ramatu ya zan yi? Ki fad'amin ya zan yi? Wlh ina so na mutu mutuwa zan yi." Na ke fad'a ina wani irin Gunjin kuka Ramatu ma sai kukan Nura ne ya ke ta lallashin mu ya karishe da kallon Ramatu ya na fad'in"Ke kuma miye haka? In kina kuka wazai lallashe ta.? Jin haka yasa ta daina kuka,ni kuma kukan da Amma ke yi yasa na tsaigata nawa Ramatu ta had'amin maltina da Madara na sha ta kuma saka sai da na sha Kayan marmari,sannan ta bani magunguna na sha. Amma ta kalli Ramatu ta na fadin"Ramatu ki kara lallasamin kawarki. Ta kafe Wajen Adda ta ke son komawa" Ramatu ta kalleni ina Runtse ido kafin tace"Hasiya Amma ba ta son tafiyarki.  Kuma in kika duba duk in da kike je ba zaki samu sukuni ba in dai ba kina tare da Amma ba ne. Don Allah ki yi hakuri watarana sai Labari." Kai kawai na gyada mata bawai don na aminta da mganarta ba. Ai nasan Hanya Amma sai dai ta tashi taga na tafi bazan zauna ina Kara Rusa mata Rayuwa ba. Ga ciwo ga kuma jikin girma. Haka Ramatu da Nura suka tafi akan gobe zasu dawo. Bayan sun tafi Amma ta zauna ta na ta min nasiha ina sharan kwallah itama ta na sharan kwallah acikin raina ina Tunanin ita Rayuwa meyasa ba ta cika ne sai da Kalubale.? Sai dai ni nawa kalubalen mai girma ne, mai tafiya cikin Tsaka mai wuya. Na firgita ne Lokacin da Amma ta mike zata fita ta Dauro alwala jiri ya kwasheta saura kad'an ta fad'i sai da ta Dafa Bango ta na salati. Duk da nima ba jin dadin na ke yi ba. Sai dai Amma ce komai nawa gwara ni na Raunana da ita ta Raunana Haka na mike na rikota ina Fad'in"Amma. Me ya faru..? Cikin Damke Hannuwana tace"Bansani ba, tun safe na ke ta fama da jiri ga ciwon kai" Jikinta na taba na ji zafi sai gabana ya fad'i cikin wani yanayi nace"Amma Akwai zazzabi a jikin ki fa." Tsoro daya kada ciwonta ya tashi zaunar da ita nayi, baho na samo da Ruwa a buta na yi mata alwala nace ta yi sallar a zaune Tunda ta na ganin jiri. Mangariba da Isha'i ta had'a Lokaci daya Bayan ta idar na sakamata abinci taci na bata panadol ta sha ina Fadin"Amma ki kwanta ki Huta." Kallona ta yi lokacin da na kwantar da ita ina lulluba mata zani a wajen kafafunta. Hannuna ta rike guda d'aya lokaci d'aya ta na kallona cikin wani yanayi. Cikin sanyin murya nace"Amma menene..? Cikin wani sauti tace"Don girman Allah kada ki je ko'ina Hasiya. Ina tsoron na kwanta barci ki aiwatar da Kudurin ki." Sai Amma ta bani Tausayi da Sauri na jinjina mata kai Lokaci daya ina jimke hannunta kafin nace"in sha Allahu bazan je ko'ina ba Amma. Ina tare da ke." Da Sauri tace"Kin Tabbata.? Jinjina mata kai na yi ina Fadin"Na Tabbata Amma." Sai taji dadi ta saki hannuna ta koma ta kwanta tana sauke ajiyan rai. Ni kuma matsuwa sai ta kamani na Zuba ruwa a buta, na fita zuwa makewayi sanda na dawo har Amma ta samu barci sai nima na samu gefenta na kwantar da kaina Saman katifar jikina na kasan leda ina Tunanin makomar Rayuwata. ******* *9:30pm* Jiya bai ci Danwake ba yau ma ga shi bai ci ba, Jiya saboda wankin da ya yi ne yasa bai je ya siya ba. Yau kuma barci suka yi tayi dagashi har Tahir sai Sha daya na Safe suka tashi kuma yana da Tabbacin ko yaje Danwaken ya kare sai ya Hakura. Gyada ya fita ya siya da rogo chan Babban Titi. Tahir kuma Taliya da wake ya Dafa mai kifi duk ya karnace musu Daki. Shi kuma baya  Shiri da kifi kwata kwata in har abinci da kifi ba ya ci Tun yana yaro haka ya ke. Ko yaya ya ci abinci da kifi to ranar yini zai yi amai ba sukuni. Kuma ko karnin kifi yaji yanzu sai zuciyarsa ya tashi. Kuma Tahir yasan da haka ammh Saboda ya saka shi mgana yasa ya kirkiri dafa Taliya da kifi. Gabadaya Dakin sai da ya Dauki karnin Tsabar wulakanci irin na Tahir akwai nama acikin Miyan da Umma ta yi masa ya zo da shi da ya yi masa mganar ya yi amfani da shi cewa ya yi shi fa yau ji ya ke yi in bai ci taliya da kifi kamar dan cikinsa zai Zube. Sanin Halin Tahir na wulakanci yasa ya fita batun shi. Yinin Ranar a rashin sukuni ya yi shi da Daddare zuciyarsa ta rika ta shi cikin Masifa ya kalli Tahir da ya gama cin taliyarsa ga farantin nan a gabansa da abun maltinan da ya gama sha, shi kuma yana ta faman Danna wayarsa cikin Nishadi. Kai Tsaye yace'Tahir kasan me wannan abun da ka yi ya jawo min? Dakin nan gabadaya sai karnin kifi ya ke yi kuma kasan yadda na ke da Kifi ko? Kai Tsaye Tahir yace"Sorry Abokina  wlh yau da ban ci taliya da kifi ba, da kaga Hanjina ta waje." Ran Sadiq ya baci yace"Na kasa cin komai yau a dakin nan  Tahir karni na shiga min ciki cikina." Tahir ya Dago ya na kallonsa kafin yace"Is That Serious..? Saboda Takaici Sadiq bai kara mgana ba jin garin akwai sanyi sanyi yasa ya mike ya nemo Jaket din sa ya saka saman Rigar da ke jikinsa. Ya shuru takalminsa ya fice ya na jin Tahir na fad'in"Ina zaka kuma..? Ko Tankashi bai yi ba  ya Fice karamar wayarsa ke jikinsa da ita ya yi amfani ya haska tunda ba wuta anguwan ta yi Duhu. Ba domin siyan wani abu ya fito ba iskar gari ya ke so ya shaka Tunda Tahir ya sauya iskar Dakin gabadaya. Tafe ya ke kawai ya na kallon zirga zirgan Mutane kamar rana sai kuma yaji ya samu natsuwa har bakin Titi yaje sannan kuma ya sake kwana ya Juyo yana cikin tafiya ne ya hangi dandalin Samari a wani Rumfa sai da karisa yaga mai Shayi ne matasa da magidanta an taru ana ta shan Shayi ana Hiran Siyasa da yadda kasa ta ke ciki na Hauhawan man Fetur kowa na fad'in Ra'ayinsa. Sai kawai yaji abun ya Burgesa Sallama ya yi musu suka amsa kafin ya ba su hannu dukkansu suka yi musabaha. Shima ya samu gefen wani matashi ya zauna. Mai Shayin da bai taba ganinsa a wajen ba ya kariso ya na Fadin"Yallabai me za'a yi maka? Shayi ka ke so ko kwai za'a soya maka ko kuma wainar kwai? Sadiq ya dago ya na kallonsa matashi ne ba Wani babba ba shi fa a Tunaninsa Masu yin shayi sai magidanta sai daga baya ya Fahimci matasa suma sun mike da neman na kansu. Saboda yadda Kasar tamu ta koma aikin Gwammati sai wane da wane. Aljihunsa ya laluba ya ciro wallet dinsa duka duka 2k ne a ciki sai ya Dago ya na kallon mai shayin kafin yace"Tea zaka had'amin." Sale mai Shayi ya ce"An gama yallabai sikari da yawa ? Madara ko melo? Sadiq yace"Madara. Sugar din ba da yawa ba." Ya juya kawai ya wuce wajen tukunyar Shayinsa. Su kuma sauran suna ta labarinsu, acikin Hiran na su ne yaji wasu duk sun yi karatu ammh ba bu aikin yi sai Buga Buga mai shayi na Had'a masa Tea ya Daga Murya yana Fad'in"Yallabai a had'o da Buredi.? Sadiq bai san ma da shi ake mgana ba sai da na kusa da shi ya tabashi sannan ya amsa masa da kadan ba da yawa ba. Cikin Lokaci ya hado masa Tea dinsa mai kauri ya kawo masa. Ruwan ya yi zafi da ya sa yaji dadinsa ya gasa masa ciki. shi kanshi da ya kalli kansa a Teburin mai shayi sai da ya Murmusa Sadiq mai abun mamaki suna da kayan Tea a gida ammh sai yaji kamar yafi samun jin dadi da sukuni shan shayi a cikin Mutane daman haka ake ji? Abun mamaki ya sha da yawa kadan ya Rage saboda ya na sha ne ya na jin Hiran matasan da ke wajen. Anan kuma ya ke jin ashe Sale mai Shayi Degree garesa a BUK  ya yi karatu bai samu aiki ba ya fara sana'ar Shayi ya na Rufa ma kansa asiri da iyayensa. Tambayan kudinsa ya yi aka gayamasa  600 sai ya ba shi Dubu Daya yace ya rike chanjin Sale na ta Godiya baisan ya Dauki Lokaci ba sai da ya Duba agogon wayarsa ya ga sha daya saura na Dare Dole ta sakashi ya mike ya yi ma matasan sallama ya wuce. Tunda ya zo garin zariya bai taba wuce tara a waje ba. Ba shi da Dabi'ar yawo hatta Tahir da ke da Rawan kai baya yawo Tunda ba su san kowa a garin ba. *** Bansan Lokacin da Barci ya kwasheni ba chan cikin barci naji Nishi da wani irin kakari. Na mike a firgice jin Sautin daga wajen da Amma ke kwance ya ke fitowa da sauri na mike ina Fad'in"Amma. Amma.." Na ke fad'a ina Yin kanta da Sauri na Dagota ammh ina Amma bata hayyacinta numfashinta na fita da Sauri Sauri jikinta ya Dauki Zafi sai makyarkyata ta ke yi kamar wacce aka Jona ma Shooking. Bude Murya na yi ina Kiran sunanta Ammh ina Amma ba ta jina kamar ta yi nesa da Duniyarmu gabadaya. Jikinta ya saki Gabadaya ga Zufa na uban keto mata ta ko'ina. Zufan da nagani da kuma nauyin da ta sakarmin yasa na Tsorata tunda na sha jin ance in mutum ya mutu ya na yin nauyi sannan ya na jikewa da Zufa ya yin Daukan rai sai na gigice. Na fara girgiza Amma ina kiran sunanta cikin kuka da wani irin Tsoro ta ina zan iya daukan rasa Amma a wannan Lokacin? Fadi' na ke yi"Amma don Allah kada ki mutu ki bar ni. Ka da ki tafi ki barni cikin wannan rayuwar ni kad'ai bazan iya ba. Wlh bazan iya ba." Na ke fad'a ina kuka ammh sai naga kamar Amma ba ta Numfashi ji nayi zuciyata ta tsinke da Gudu na Saketa na fice ina haki nima kamar Shed'ata zata Dauke. Dakin Maman Boy na tafi ina Bugawa Cikin kuka nake fad'in"Ku taimaka min Amma Amma kada ta mutu" Duka Dakunan gidanan ba in da ban buga ba. Na tabbata in wasu ba su ji ba, wasu sun ji kuma lokacin dare bai Raba ba duk da ban kalli Lokaci ba ammh ba wanda ya fito ballatana ya taimakamin. Ganin haka yasa na kwashi gudu na koma Daki na kara tarairayo Amma jikina na kara kunnena saitin zuciyarta ta ji dif kamar bata Numfashi, sai naji kamar wani abu ya Sare daga baya na. Tashi na yi ina Haki kafata ba takalmi zanin Amma na Raruma na yafa na fice daga Dakin da gidam ma gabadaya domin neman agajin nutane. Kamar an yi ruwa an dauke ban ga kowa a waje ba shiyasa na Dauki Hanya ina tafiya gudu gudu tunanina na tafi Chemist din gaban gidanmu na nemo Taimako ba na ko ganin gabana jefa kafafuwana kawai na ke yi ina ji kamar zuciyata zata fashe. Sai ji nayi na bangaji mutum da karfin da yasa ya yi baya nima na yi baya ina rawan jiki. Sadiq da yaji ya sha bangaza kamar wasa ya ja baya cikin mamaki gabansa bai Fad'i ba sai dai ya yi kokarin kiran sunan Allah. Ni ko yamayin da na ke ciki yasa ban ko Tsaya ba sa Hakuri ba na kama Hanya zan wuce da fitilar wayarsa yasa ya haske Fuskata daga sama har kasa ya ke bi na da kallo ganin kafafuwata ba Takalmi da kuma yanayin da ta ke ciki yasa da Sauri ya ce"Ke ke Baiwar Allah." Jin ya kirani yasa na juyo ina kallonsa da idanuwana da suka Kumbura. Cikin Wata irin murya naji yace"Lafiya kike tafiya ba takalmi? Har zan wuce sai na Tuna Amma kawai sai na dawo gabansa na Duka ina Fad'in"Amma Amma ce. Don girman Allah bawan Allah ka taimakamin Amma ce ga ta chan. Kamar ta mutu bata Numfashi." Na fad'a cikin gunjin kukan da yasa na Duka na Dafa kafafunsa ina Cigaba da Fadi'in"Bawan Allah ka taimakamin don Darajan Allah. Don Daraja da kaunar da ka ke yi ma iyayenka ka taimakeni kamar yadda Allah ya taimake ka. Ka taimaki mahaifiyata kada ta mutu." Sadiq ya ja baya da Sauri cikin in ina ya ce"Kinga yi shuru yanzu ina mahaifiyar ta ki ta ke? Ina jin haka na mike jikina na rawa nace"Ta na. Ta na gida." Sai kawai yace"Mu je na gani." Jin haka yasa na yi gaba da Sauri ina Tafiya ina Hardewa shi kuma ya bi bayana har acikin zuciyansa Lokacin da nake tafiyan nan ya Tsorata. Wata zuciyar tace"To in Aljana ce fa Sadiq? Tuna haka yasa ya rage tafiya har sai da na yi masa nisa sannan na juyo ina kallonsa ba na wani ganin Fuskarsa akwai Duhu daga nesa yace"Ina ne gidan? Da hannu na nuna masa gidanmu ina Fad'in"Ga ga gidan chan." Jim Sadiq ya yi kafin ya kad'a kai yace "Muje.." A ransa yace Allah kaga Niyyata na Tausayi da taimako kada ka bari wannan yarinyar ta Cutar da ni in ta na da Niyyar haka. Yadda da Allah da kuma addu'a yasa ya bi Bayan Hasiya har cikin gida saboda dare da kuma yanayin da Sadiq ya ke ciki yasa bai iya gane gidan da ya ke zuwa Siyan Danwake ba ne. Bai ji hankalinsa ya natsu ba sai da Hasiya ta yi masa Jagora har cikin Dakin Yaga Amma kwance kamar ta Mutu. Cikin kuka na Nuna masa Amma ina Fadin"Ka duba ta. Ta mutu ko? Da Sauri ya isa gabanta ya rike hannunta na wani Lokaci kafin ya Dago ya na kallona cikin kuka nace"Ta mutu ko? Da Sauri yace"A'a ta na numfashi sai dai muna bukatar kai ta asibiti da gaggawa." Kawai sai na sulalle ina wani irin kuka bai Saurareni ba ya fice daga Dakin da sauri ni kuma sai na Dora Hannuna a saman kaina ina Fadin"Wayyo Allah na shiga ni Hasiya na lalace" Na Dauka ya tafi ne shiyasa kawai na koma na zauna ina Rafzan kuka babu wanda zai taimake ni a wannan Halin da muka samu kan mu aciki. Sai dai me sai ga shi Mutumin nan ya Dawo da Sauri ya na fadin"kama min ita ga adaidata chan na samo mu kaita aaibiti." Ina jin haka na mike jikina na rawa na tayasa ya daga Umma sai ya Fahimci nima sai a Hankali Tunda jiri ya kwasheni na kusa Fad'i sai da ya Rikemin hannu da hannunsa Guda daya cikin Tausayawa ya ce"Ki na lafiya.? Kai na gyad'a masa ina sharan Hawaye ganin bazan iya ba yasa ya ba  ni wayarsa ya na fadin"Rike min ki gani" da Sauri na karb'a sai ga ni nayi ya ciccibi Amma da dukan Karfinsa yana fadin"Ki biyo ni a baya ki rika haskamin hanya." Da Sauri ko na bi bayanshi wai sai da muka fita ne sai ga matan gidanmu suna Bude kofa suna Fitowa ganin an Dauko Amma kamar ba rai yasa su Maman Salihi ke fad'in"Wayyo jikin Amma ce ya tashi? Ko kallonsu ban tsaya yi ba daman shi Tuni ya yi gaba. Da muka fita mai adaidaitan ya taimaka muka sakata a adaidaitan shi gaba ya shiga ni kuma na shiga baya na rike Amma. Mun fara Tafiya mai adaidaitan yace"Wani asibiti zamu je yallabai? Juyowa ya yi ya na fadin"Wani asibiti ku ke zuwa.? Cikin kuka nace"Kowanne muna zuwa." Tsayawa ya yi kawai ya na kallona ina kuka ba haske acikin adaidaitan shiyasa baya ganin Fuskarta. Cikin natsuwa ya maida Hankalinsa wajen mai adaidatan Lokaci daya yana Fadin"Asibitin da ya fi kusa ka kaimu chan." Kukan ne baya so ya na da Raunin zuciya bangaran Tausayi. Wani asibitin kudi da ke samaru ya kaimu muna zuwa ya fita ya kira Nurses suka zo da abun Daukan marasa lafiya suka Dauki Amma suka yi ciki da ita. Mu kuma muna waje muna jira yadda bai zauna ba nima ina Tsaye ina Tsiyayan hawaye. Kaina na rufe shi da zanin da Lallube jikina baya ganin Fuskata Tunda muka kawo Amma

Chapter 15 of 24