Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
barci Sadiq ya yi ta sha ya na Hutawa duk da wayoyin yan'uwansa sun cika masa waya da kira suna rokon sa don Allah yazo gidajen su. Kowacce Burinta yaje gidanta kuma bai cika zuwa ba sai dai su suzo su same shi a gida. Gwara ma gidan Surayya tunda itace Big Sis kuma ta su tafi zuwa daya da Sadiq daga ita sai Sa'ima sai kuma Shahida da ke aure a katsina ita in suka shiga katsina za su je Daura sun sha biyawa shi da Tahir. Sajida sakonsa ne domin Umma tace kwata kwata shekaru biyu ne a Tsakanin su. Bayan fad'a tsakanin Sako da Sako jininsu kuma bai had'u ba. Saboda Sajida na da Surutu da son jin gulma sannan ta na diban mgana sai ayi mgana da ita ta sirri sai aji ta a bakin wata a cikin su, Mace ce mai kishi da son komai ya zama ita kad'ai ta mallaka shi kuma Sadiq baya son halinta na Surutu shiyasa ba su cika Shiri ba, zai iya kirga saunawa ya taba zuwa gidanta duk da ta na kusa ba ta da nisa da gidan tsakaninsu bai wuce Naira Dari ba. Yafi yarda da Surayya fiye da kowa a dakin su da gidan su. Saboda ta na da kirki da kamewa sannan cikin Nasiha da Lallashi zata yi maka mgana har ka Fahimta. Ya na zuwa gidanta sosai barin ma in yazo garin Hutu ya jima. Shiyasa wannan karon ma ita kad'ai yace mawa zai zo mata kafin ya tafi. Ranar da ya cika sati biyu a garin Gusai ya shirya ya je gidanta. Umma kad'ai ta san ga inda zai je Abba ya fita da wuri Mama kuma bai shiga shashenta kafin ya wuce ba, innani kuma ta na chan bata dawo ba daga ita har su Sultanan. Umma ce ma da ta kira Mallam zakari tace a ba ma Innani su yi mgana. Bayan an bata sun gaisa ta tambayeta yaushe za su dawo? Innani tace uban wa ta ijiye a gidan Sulaimanun da za'a dameta sai ta dawo? Ita ba d'a ba ita kuma ba jika ba kada a dameta sai taga dama zata Dawo tunda Umma taji haka ta kama bakinta Sanin Halin Innani yanzu sai cibi ya zama kari in ma batace ta na so ta yi mata gorin gari tunda taga gidansu ne. Da ta fad'ama Sadiq karamin Tsaki yaja a fili ya Furta"ku kyaleta Umma ranar da ta gaji kuna zaune zaku ganta. Yaran nan dai su dawo saboda ana komawa Hutu zasu fara zuwa makaranta." Umma tace"Wa ya isa ya ce su Sultana su dawo Innani ta tsine masa." Sadiq kai tsaye yace"Ni na isa. Kuma zan kira mallam d'in da kaina nace a bata wayar na fad'a mata." Umma na Dariya tace"Sai dai kai d'in." Haka ya ke maida ma Surayya yadda suka yi da Umma da ta tambayesa Innani ta dawo? Shine ya ke gayamata yadda suka yi da Umma. Surayya ta yi dariya kafin tace"Innani Rigima. Ai in kaine bazata yi fad'a ba tunda Shalele ne." Bai yi mgana ba sannan bai ko yi mirmishi ba. Suna zaune ne a falon Surayya ta cika gabansa da kayan makulashe yaranta duka basa nan suna gidan kakaninsu na bangaran uba sun je Hutu. Daga ita sai yar aikinta a gidan sai zuwan Sadiq maigidanta sunansa D'aya da Sadiq wato Dr. sadiq. Dacta ne a bangaran ilimi. Ba iya a gidan su Sadiq ke da gata ba har a wajen mazajensu tunda har Sun haddace sunansa komai Sadiq ko magajin gida. Ballatana shi Sadiq da ya ke yawan zuwa gidan Surayya akwai Sabo sosai a Tsakaninsa da Dr.Sadiq Da wuri yaje sun dade suna Hirar rayuwa suna Tattauna wasu abubuwan da suka Shafe su na yan'uwa masu kaunar juna. Sai ta gangaro masa mganar auransa da Sultana. Kai tsaye ya kalleta ya na fadin"Big Sis aure na ba yanzu ba sai na gama bautar kasa, na kuma taba fad'a miki zan koma Masters dina. Kuma burina shine sai na Fara aiki kafin na yi aure.'" Surayya ta kallesa cikin mamaki kafin yace"Nan da shekaru nawa kenan? Sadiq ya gyara zama ya na fad'in"Ni bazan kayyade ba. Allah shi ke da komai Tsarin ne kawai na Dan adam. Surayya ta katseshi da Sauri lokaci d'aya da fadin"Mu kuma har muna cewa nan da Shekaru uku lokacin Sultana ta gama makaranta." Mirmishi ya yi kafin yace"To ki yi fatan na samu aiki kafin Lokacin." Surayya na dariya tace"Aikin me? Kai ai dan gata ne dukiyar da Abba ya tara maka kila Har ya'yan Jikokin ka ma sai su iya ci" Ido ya zaro ya na kallonta kafin yace"Kudin Abba ba kud'ina ba ne big sis. Kudin Abba amfanina da su shine na yi karatu na tsaya ga kafafuna." Tasan ya na da Tattausaran Ra'ayi ammh bata taba zaton Ra'ayinsa ta wannan bangaran ya yi tsanani ba. Kai tsaye tace"Wannan ba matsala bace ko baka samu aiki ba sai ka cigaba da Tafiyar da Business din Abba na shigowa da Cumputers" Sadiq yace"A'a ni kasuwanci baya burgeni. Ku barni na tsaya da kafafuna a bisa ra'ayina." Surayya ta lamgwabar da kai kafin tace" mu dai kada garin tsayuwa da kafafunka wata ta zo ta yi ma kanwarmu kafa fa Autan Umma." Dariya ya yi har sai da Hakoransa Farare suka bayyana. Cikin Tattausan lafazi yace"Baku yarda da kan ku ba kenan? Surayya ta bushe da Dariya kafin tace"Wa ya fad'a maka? mun yarda da kanmu shiyasa muka ce a bari sai kanwarmu ta kara girma mun koya mata komai ta yadda zamu kama Autan Umma a hannu ba wacce kuma ta isa ta nuna mana yatsa." Shi dai dariya kawai ya yi bai yi mgana ba ita kuma ta cigaba da fad'in"Ni fa tsoro ma na ke yi kada wata yar zariya taga dogo autan Umma Shalelen Innani ta lafe maka mu muna nan hamgame da baki." Sai a wannan karon yace"To miye? In naga ta yi min sai na aureta." Surayya ta bude baki kafin tace"Ka aureta kuma? Kai Sadiq fita daga idon mu." Ya na yar dariya yace"To ai naga ni ba Mijin Sultana ita kadai ba ne. Ni sadiq mijin Mace ne har guda Hud'u." Surayya tace"Uhm ai fa." Ta fad'a ta na mele baki. Mirmishi ya yi kafin yace"Yes kin ga ko bayan kanwar ku akwai wajen mata uku so gwara ku bi a sannu." Surayya tace"Mu zamu cike gurbin wajen mata ukun in sha Allahu." Sadiq yace"Zaku iya? Surayya tace"Sosai ma." Sadiq na dariya yace"Shiyasa ki ka hana Dr kara aure ko? Ke kadai ki na wahalar da shi ko? Fari ta yi da ido kafin tace"ni ban hana shi kara aure ba. Gurbin sauran matan ne na cike masa kaga kenan baya bukatar kara auran" Nan fa suka fara musu ya na cewa ta sakar ma Dr. Kanbun da ta daureshi ya kara aure ita kuma ta na rantsuwan cewa ita bata hanashi kara aure ba ya yo auran ya gani ko a jikinta ita dai Tunda tasan kanta kishiya in dai ba ta karkashin kasa zata bi bazata taba kada ita ba. Da ta ga ya dage ne kawai sai ta karkace baki ta na kallon shi kafin tace"Tsaya Tsaya. Wai ko ka samu wata ne a zariya ka ke min sharan Fage? Wannan karon sosai ya yi dariya kafin yace"In na samu wata a zariya ai ba na bukatar wani sharan Fage Big Sis. Ina ce ni ne mai auran kuma naga shi auran Sunna ne da Ra'ayi ba na Tunanin in ina Ra'ayi wani zai iya Dakatar da ni." Surayya ta kura mishi kafin tace"Ka tabbatar ba wata ko Sadiq? Kai Tsaye yace"Wlh ba wata Bigs Sis  in da ita da tuni kun sani." Sai alokacin ta sauke ajiyar zuciya kafin tace"Yaushe zaka baro zariyan nan ne? Kai tsaye yace"Nan da wata shidda. Ko kilama na yi masters dina achan." Surayya ta zaro ido kafin yace"A'a wlh bamu yarda ba. Tunda bakasan waje ga BUK ta garin kano" Kai Tsaye Sadiq yace"Ni kuma Duk wata makaranta bayan ABU ne a wajena Big sis." Cikin mamaki tace"Na rasa me ka ijiye a garin nan ne Sadiq baka san barin shi ko sultanan ma chan zamu kai ma maka ita? Sadiq ya yi shuru kafin yace"A'a." Tabe baki ta yi kafin tace"Allah yasa da gaske ka ke yi." Dariya Sadiq ya yi kafin yace"Da gaske na ke yi ma in nagama abunda ya kaini dawowa zan yi nan ne asalina Big sis. Sultana kuma in da na samu aiki nan zan ijiyeta." Jin abunda yace ne yasa Surraya taji dadi suka cigaba da Hira. Yana gidan har bayan La'asar ya na ma shirin tafiya sai ga Dr ya shigo. Sai ya tsaya suka gaisa har ya rika jansa da Hira da yasa ya bata lokaci sai gabda mangariba ya fita. Da d'aya motar Abba yaje ya shigo anguwan kenan aka kira sallar mangariba sai da ya tsaya ya yi sannan ya karaso gida. Akwai sakon Umma Dambun kaza ita da Mama sai na Abba kuma yamball ne. Shi kuma na shi pepe chicken ne abunda ya fiso tace in zai koma ya gayamata ta yi masa kayan Fulawa ya tafi da shi. To a daran Tahir ya kirasa yace gobe zai dawo Zariya. Ganin shi bai shirya ba yasa yace ya fara yin gaba shi sai jibi sai ya dawo da haka suka rabu. Sai da Safe da yaje shashen Umma ya gaisheta ya sanar da ita gobe zai koma Ita ta kira yan'uwansa ta sanar da su tafiyarsa. Zuwa Dare sai ga sakonnin su dukkansu har Sajida ita Dambun nama ta yi masa mai yawa sauran kuma kayan Fulawa ne soyayyan Nama tunda susan ya na so. Umma kuma ta yi masa miya mai yawa daman ita ta saba yi masa mama ta saka Salima ta yi masa Cookies da yawa na tafiya tunda yace in ya tafi zai jima bai dawo ba. Innani dai bata dawo ba har ya tafi Abba 100k ya saka masa ta acct dinsa bayan Direba ya kaisa har zariya. Da kaya niki niki tunda harta kayan abinci da su Ruwa da Drinks da su ya ke tahowa daga gida tun baya Dauka Umma ke matsawa ya ke tafiya da shi. Wasu kayan maggi mangyada Duk Umma ke sakamai sai ya je ne ma in Tahir na duba kayan sai yace abu kaza ne da kaza ne shi tunda ba Dubawa ya ke yi ba. Ya dawo zariya daidai ya yi kwana sha shidda baya nan ya iske Tahir da yadawo ba abunda ya yi sai ma Datti da ya karama Dakin dole ya Tube ya gyara Dakin sai Dare ya gama wanka kawai ya yi ya kwanta. Koda ya tashi Tahir ya dafa musu Farar shinkafa sai suka ci da miyar nan da Nama. Sai da suka je sallar Isha'i suka dawo sannan suka zauna saman Hira. Tahir na ba shi labarin yadda yaji dadin zuwa gida hutu da sakon gaisuwarsa Sadiq daga Hajjo da Sauran yan'uwansa. Tahir ne ya tambayi Innani shi kuma ya fad'a masa ta na Gummi gidan su Umma har ya dawo bata dawo ba. Ranar raba dare suka yi suna Hira kafin su kwanta da gari ya waye kuma  da wuri suka tashi suka yi shirin fita wajen aiki. Sadiq ya zo da sabbin T.Shirt da Jeans daga gida harda Sabbin Yadika dikkaku da Shaddodi kayan da ya tafi da su bai dawo da su ba Shinkafi ya tsinta yaje da su ya bama su Goggo Husai yace ta bama ya'yansu tunda kayan su chan sai a hankali. Sabbin da ya zo da su rabi ya raba rabin kuma ya ba ma Tahir daman ya na masa haka ya karb'a ya na ta godiya. Tare suka fita saboda sun makara yasa suka hau mashina kowa ya nufi inda za shi. Sadiq ya riga Tahir dawowa yau shiyasa har sai da ya yi wanka sannan Tahir ya shigo. Shi ya Dafa musu macaroni da wake suka ci da Miya suka kora da lemu da Safe Tea suka sha da Cakes har kuma Diba Suka yi da za su fita. Sadiq ya fara d'iba Tahir ma ya gani shima yace tunda zama da madaukin kanwa shi ke kawo farin kai bari shima ya D'iba. Sai da sukaje masallaci suka yi sallar la'asar suka dawo sannan Sadiq ya sauya kananun kaya jikinsa zuwa wani yadi mara nauyi. Tunda Tahir yaga haka ya sha jinin Jikinsa kai tsaye ya kallesa ya na fad'in"Ina zaka je? Kai tsaye yace"Gidan su Hasiya" Tahir ya yi shuru batare da ya yi mgana ba jin haka yasa Sadiq ya juyo daidai ya na fesa Turare ya ke fad'in"Ko zaka rakani ne muje tare? Sai da Tahir ya ja karamin Tsaki kafin yace"Allah ya tsareni." Sadiq ya yi dariya bai ce komai ba ya gama fesa Turarensa ya zura Hula sannan ya zo wajen ma'adanan takalmansa ya Dauki wani baki Budade ya saka lokaci d'aya ya juyo ya na kallon Tahir Kafin yace"Sai na dawo." Har ya fice Tahir bai ce masa komai ba ammh ko dannan wayar da ya ke yi alokacin ya dakatar. Har ga Allah ya dauka Tafiyar su gida yasa Sadiq ya manta da wannan zabiyar yarinyar ashe ashe bai manta da ita ba. Har Sadiq ya fice ya na chan ya na saka Tunanin yadda zai raba Sadiq da wannan yarinyar da ya ke tabbacin mayyace daga labaranta marasa Dad'i. ******* Har acikin raina na cire rai tare da Tsammani zan kara had'uwa da Assadiq. Shiyasa har acikin raina ban kawo ma tunani zan kara ganinsa ba. Na riga na sakama rai na zan bar wannan muhallin zuwa wani waje na dabam. Duk da har lokacin Isuhun bai zo ba bamu kwance shirin mu ba Tunda Adda Ta tabbatar mana da cewa zai zo kuma zai taho damu. Musan yanayin Rayuwa ballatana kuma da ga shi an masa haihuwa akwai tarin Hidima a gabansa. Adda ta sake kiranmu tace mu zama cikin shiri ko gobe ko jibi Isuhu zai zo mu tafi satin chan da ya fita abunda yasa bai samu zuwa ba matarsa suka mayar asibiti daga baya jini ya balle mata ammh taji sauki har ta koma gida Adda na kula da ita. Tunda Habiba ta koma wajen Adda Fati ni kuma na zama shuru shuru tunda ba Danwake na ke yi ba. Sai ya kasance ba na fita tsakar gida sai in ko zan yi girki ko kuma zan Dafa mana Ruwan zafi gabadaya komai na Rayuwar ne ya daina min dadi. tuni Maman boy ta fara sana'ar Danwake ni na fara kwaba mata ranar farko ga shi har ta kware. Kuma mutane na siya duk da wasu in akace musu na daina Hakura suke yi saboda sun fi son nawa. Ammh duk da haka ta na samun Ciniki daidai gwargwardo. Yau tun safe da Fad'uwar gaba na tashi ko mgana akayi sai naji gabana ya ba da wani Ras! Har sai na fad'a ma Amma tace na karanta Falaqi da nasi da Ayatul kursuyi kafa uku uku da Amanar Rasuli. Shawaranta na bi na karanta sai abun ya yi sauki ammh Suku suku na tashi har ina zaton ko Ulcer dina ce ta tashi jin baya na da kugu duk ya rike, Kuma da Safen na sha mgani ammh jikina kamar an yi min duka ko Amma ta fi ni karfi da Kuzari. Ita na kai ma ruwa ta yi wanka ni ce ban yi ba saboda naji ba na ra'ayi. Da Safe kunu na dama muka sha da rana kuma na siyo mana Alala. Shiyasa na yini kwance kamar ruwa Amma dai har ta gaji ta kalleni bayan na idar da sallar la'asar taga na kara bin leda na kwanta tace"Hasiya lafiyar ki kuwa? Ina daga kwance nace"Amma ni yau bansan me ya sameni ba. Faduwar gaba da mutuwar jiki." Amma ta yi shuru kafin tace"To Allah ya sauwake." Nace mata Ameen a Hankali. Lumshe idanuwana nayi kamar baeci na son fizgata Amma na daga gefe ta na jan cashaba Naji muryan Salihi ya fad'o dakin mu ya na fad'in"Adda Hasiya ga mai siyan Danwaken nan da safe, a waje ya ce ki zo." Sai naji kamar a mafarki naji mganar da Sauri na Bude idanuwana. Sai dai ban tashi ba sai da naji Amma na fad'in"Ke Hasiya Abubakar ne inaga" Sannan na yi zaraf na mike jikina ba inda baya rawa. Da Hijabin da nayi sallah takalman Amma silafas na wajen na zura na fice da gudu. Ban zarce ko'ina ba sai kofar gida Fata na da Muradina na ci karo da abunda Zuciyata ta gama yanke kauna da sake gani. Shi ne ko yana Tsaye daga gefe rike da Hannun Datti da ya ke ta zuba masa uban surutu. Ganin fitowata da yadda naja na tsaya ina kallonsa ko Kiftawa ba na yi yasa ya zaro walet dinsa ya Dauko 200 ya bama Datti ya karb'a ya na ta washe baki da tsalle ya shige cikin gida. Da kansa ya kariso gabana hannuwansa duka zube cikin Aljihun wandon da ke jikinsa. Kallonsa na ke yi ko kiftawa ba na yi kamar wacce ta warke makanta. Shi kuma ganin haka yasa ya ciro hannunsa guda d'aya ya murza a saman Fuskata lokaci d'aya ya na fadin"Kin yi mamakin ganina ne? Da sauri na Dawo hayyacina sai kuma naji dariya ta kwacemin. Shima Mirmishin ya yi kafin yace"Baki zata zan dawo kwanakin nan ba ko? Daman nace miki bazan wuce sati biyu ba in ma na wuce bazan kai uku ba" Cikin shagwaban da bansan sadda ta kwace min ba nace"Ban zata zan sake ganinka ba ASSADIQ." na fad'a idanuwana na kawo Ruwa kai Tsaye yace"Da sai ku tashi ku koma wani garin Batare da kun jirani ba HASIYA.? Kallonsa na yi ina mamakin ina yaji labarin tashin mu sai ma Tuna Datti nasan bani da haufi shi ya fad'a masa. Rufe fuskata na yi da Tafukan hannayena ina yar dariya wani Farincikin da bansan daga ina ya ke Tunkudo'wa daga kasan raina ba. Cikin sanyin murya nace"Shiyasa muka kasa tafiya ko'ina har sai da ka dawo ka ganmu." Kai ya jinjina kafin yace"Ina Amma? kanwata Habiba ta na lafiya? Fuskata na bude ina fadin"Bismillah mu shiga." Ina gaba ya na baya har zuwa Dakin Amma bayan ya gaisa da matan gidanmu. Gulmammu kafim ma ya fara gaishe su su suke fara gaishe shi suna washe bakin munafunci da Gulma. Amma ma bakinta yaki rufuwa ganinsa a gabanta a duke ya na gaisheta ta amsa ta na fad'in"Abubakar idanuwanka kenan?har na fidda rai da zamu sake Had'uwa ga shi Hasiya ba ta da lambar wayarka." Kansa na kasa yace"Haka yaron chan ke fad'amin zaku tashi Amma" Amma tace"Wlh kuwa ba domin an samu Tsaiko ba da tuni muna chan da yanzu baka same mu ba." Cikin mamaki yace"Me nan gidan ya tada ku ne Amma.? Amma ta girgiza kai kafin tace"A'a wlh. Mu zamu tashi da kanmu" Shuru ya yi jin Amma bata warware mgana ba. Ni ina daga gefe ina Sauraransu sai ya waiwayo ya na fadin"Habiba na makaranta ne? Amma ce ta amsa shi da cewa"Habi ta koma wajen Fati da zama gabadaya." Cikin mamaki yace"Me yasa Amma? Sai da ta kalleni na wani Lokaci ni kuma sai na daga mata kai sannan ta jiya ta na fuskantansa tace"Saboda zamu koma mahaifata da zama gabadaya." Sadiq ya dago ya na kallon Amma kafin yace"Ina kenan? Amma tace"Gadan mallam Mamman chan hanyar kaduna zuwa Abuja." Ni ya kallah kafin ya kalli Amma lokaci d'aya ya na fadin"Har da Hasiya? Sai Amma ta kasa mgana Idanuwanta suka ci ko da kwallah. Ni ce na ba shi da amsa da cewa"Eh harda ni. Gidan Adda zamu koma yayar Amma ce can take  da zama ita da iyalanta." Gabadaya Dakin sai ya Dauki Shuru shi bai yi mgana ba nima ban kara mgana ba. Kaina na kasa ina wasa da gefen Hijabin jikina kawai sai ji nayi Amma ta fashe da kuka da sauri na Dago ina kallonta a tare da ni da shi muka isa gabanta cikin rawan jiki da na murya muke tambayamta me ya faru? Amma ta kalleni hawaye Jage jage haka shima ta juya ta na kallonsa ko Kiftawa ba ta yi na tsorata na kalleshi shima ya kalleni a tare muka Dora hanmu a kaf'adan Amma muka girgizata kuma bakin mu a tare ya Furta sunanta. "AMMA.." Kuma a tare hannumuwan mu suka had'u waje d'aya sai da muka ji wani Zir kamar wutar lantar yajamu da kuma Sauri muka saki hannun juna. Amma ta kallemu kafin ta murmusa da haban zaninta take sharewa. Ni kuma na durkusa gabanta ina fadin"Amma baki da lafiya ne? Sai ta girgizamin kai shi kuma sai yace"Taba jikinta ko da zafi sai mu tafi asibiti." Ba gaddama na taba goshinta naji sanyi sai na juya ina masa motsi da ido alamun lafiyanta kalau. Kallona na maida kanta kafin nace"Amma me ya same ki? Cikin mirmishin karfin Hali tace "Bakomai Hasiya. Ina so ki bamu waje zan yi mgana da ABUBAKAR." Dagani har shi juna muka kallah cikin mamaki kafin na kalli Amma zan yi mgana kenan tace"Gaddama ba Halin ki ba ne Hasiya kada ki fara Daga yau." Jikina ne ya yi sanyi ina jin haka sai na mike shi na kallah shi kuma kansa na kasa daga gaban Amma inda ya Durkusa. Har zan fice Amma ta kira sunana na waigo kafin tace"Matso ma da Abubakar Darduman nan ya zauna dakyau." Ba musu ma matsar masa da shi gabansa yaja ya zauna ya tankwashe kafa ya na Fuskantar Amma. Ni kuma sai na fita waje na koma bakin kofar Maman Salihi na zauna. Wake take tsinta sai na saka hannu in tayata domin kada na zauna shuru Tunani ya yi min yawa. Kallona ta yi kafin tace"Bakon ya tafi ne? Bakinta washe cikin basarwa nace"Suna mgana da Amma." Sai ta shuru nima daganan ban kara mgana ba duk ko da suna sako ni cikin Hiransu sai kiji suna ko ba haka akayi ba Hasiya? Iyakata mgana da kai ko na yi gum suna ganina zaune ne ammh gabadaya Tunanina da Hankaluna suna dakin Amma ina Hasaso wani irin mgana ne Amma zata gayama Assadiq ya sa sai da tace na basu waje? Wata zuciya tace ya wuce Labarin ki" Daman nasan ai Tsatsuniyar gizo bata wuce ta kogi. Har aka kira sallar mangariba Assadiq bai fito ba. Ganin duk sun watse sun shige dakanunsu yasa na ari butar maman Boy na yi alwala na yi sallar mangariba adakinta. Ina cikin azkar naji na kasa natsuwa a Daddafe na gama na mike na fita. Ganin ba takalminsa kofar dakin Amma yasa nasan ya tafi. Da sauri na fad'a dakin Amma sai na yi Turus ganinta ta na sallar mangariba. gefenta na koma na zauna gabana naji ya na Di' di' Bakina kuma ya kasa Furta komai. ******* Tunda ya baro gidansu Hasiya ya fara ganin Duhu Duhu. Kansa ko da ya ke sara masa daman tun yana gaban Amma ya fara sara masa. Ko da ya iso dakinsu jikinsa ne ya saki kwata kwata kwakwalwarsa ta daina amfani ballatana ta kaisa ga wani Tunani na Dabam. Yaraf ya fad'a kan katifa ko takalminsa bai cire ba. Tahir na Dakin Ammah ko kallo bai ishesa ba ballatana ya fahimci halin da ya shigo, ya na jinsa ya fita ya je ya yi alwala yazo ya sauya kaya ya fita zuwa masallaci ammh shi duk yadda ya so ya yunkura ya mike domin ya fita ya Dauro alwala ya tafi masallaci ya kasa. Gabbansa yaji kamar an sauke masa su ko'ina na jikinsa ya saki kamar ba shi da lakka ajikinsa. Kansa na sara masa ammh kuma kwakwalwarsa ta tsaya cak din da ya kasa Dora wani sabon Tunanin tun bayan fitowarsa daga gidan su Hasiya. Halin da ya ke ciki shi ake kira TSAKA MAI WUYA halin da ya kasa sarrafa Tunaninsa ma gabadaya. Tahir sai da tara ta wuce ya shigo Dakin yana jin tashin muryansa a waje yana hira da yan makaranta da suke zaune tare. Har kuma alokacin bai iya ko motsi da kafarsa ba. Yana jin Tahir har takasa ya yi ammh bai iya tashi ba. Shi kuma Tahir haushin Sadiq yake ji shiyasa ya yi kamar bai gansa ba. Da farko ya zata gajiya ce ta kwantar da shi sai da yaga bai je sallar mangariba sannan aka yi isha'i ma bai je ba sai yasan ba lafiya. Lafiyar Sadiq kalau baya fashin sallah Ko da ba shi da lafiya ne sai dai ciwon da ya kasa tashi shine zai hanasa zuwa masallaci. Sannan ya shigo yagansa yarda ya barshi da gangan ya takashi Saboda ya yi mgana ya Fahimci Halin da yake ciki ya ji shuru daganan yasan ba lafiya Kusa da Sadiq ya matsa ya na Taba kafarsa lokaci daya ya na kiran sunansa "Sadiq Sadiq. Kai Sadiq" Har Tahir ya fara tsorata ganin bai yi motsi ba sai kuma yaga ya juyo idanuwansa suna rufe bai bude

Chapter 22 of 24