Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nasan amsar shurunta. Adda Rukayya ce fa ita ce jini na uwa d'aya uba D'aya ammh in ba'a fad'a maka ba sai kace bamu Had'a komai da ita ba. Cikin karyewar murya nace"Ba sai kin ce min komai ba Ramatu na Fahimta. Allah ya sa mu dace" Sai ta kasa amsamin, kallona take yi a sanyaye ni ko sai na kauda kaina. Adda Rukayya ce fa ta kalleni ido cikin ido tace'"Gaskiya Hasiya ki daina zuwa gida na. In wani abu kuke da Bukata ki kirani kawai. Baban su Amna ma baya so yace tsoro yake ji. Baya son zuwan ki gidan shi" Tunda ranar da ta fad'amin wannan mganar na san in da na sauke Matsayin Adda Rukayya a wajena. Ko Amma ta na fad'a ta kuma sha Fad'amin cewa"Hasiya ku yi hakuri da Rukayya. Kaf cikin ya'yana tana da Bambamci ba D'aya take da ke ba, sannan ba D'aya take da Fati ba. Ku yi mata addu'an da Fatan Allah ya Daidaita rayuwarta. Rokona shine kada ku yanke zumumci da ita ko bayan kasa ta rufe idona" Nasan ta zo ne ma da Safen gudun Fad'an Amma, ba sabo da ni ba. Gabadaya Hidiman auran nan Ramatu ne da mahaifiyarta sai Adda Fati kan lamarin ni ko sau d'aya ban ma sakata aciki ba. Ni fa ko ciwon Amma ya tashi bana jiranta tun kiran ta da na tab'a mata kan  kan jikin Amman ya tashi ta fara min Fad'a da cewa komai ya ke faruwa ni ce Sila tun haihuwata Rayuwan mutane da Dama ba su wuta ba ciki har da su da Amma ni ce silar Cutar Amma da bata da mgani. Tun daga ranar na kiyaye mata, sai Amma ta sha ciwonta bata sani ba. Sai in taji daga baya ta fara kumfar bakin ba'a Dauketa bakin komai ba tunda Ba'a fada'a mata ba. Har tutiya ta tab'a yi a asibiti Lokacin da aka kwantar da Amma. Ban kirata ba Adda Fati na kira ta zo muka taho asibitin sai bayan an ba ma Amma gado ta kirata ta Fad'amata. Shine da tazo ta rika fad'an meyasa ban kirata na fad'a mata ba? Kuma a lokacin kai tsayen ta kalli Adda Fati tace"Naga kamar sun fi daukan ki wata Tsiya. Allah na tuba me kike da shi Ballatana shi Habibun? Ni dai da kuka raina ni nake da shi,kuma nake rufa muku asiri ni da Mijina" To me wad'anan kalaman ne kuma don in bata zo ba meyasa zan damu? Ina ta kokarin nuna yanayina ba komai ganin haka yasa sai Dakin ya Dauki shuru daga ni har ita ba mai wani mgana kowa na saka wasu abubuwan acikin ransa. Sallar mangariba ya Tada Ramatu ta fita tayo alwala tazo ta gabatar da sallaar tana cikin sallar ne kafin ta Idar, wayarta dake gefena ta Dauki neman Dauki. Ina dubawa naga Salisu ne sai da gabana ya Fad'i. A kasalance na dauki wayar ganin ya sake kira bayan kiran D'azu ya katse. Na latsa koren alamun Dauka na kara kunne ina jin muryansa cikin Shauki da murna yana Fad'in"Ramatu ga mu nan zuwa. Kada ku ji mu shuru mun bari mu yi sallar mangariba ne" Numfashina ne ya kwace min batare da na shirya ba, kuma da hakan ya fallasa ma da ni ce na Dauki wayar. Cikin Shauki da Soyayya yace min"Hasiya..! Hasiya. Numfashin ki Kad'ai ya isa ya shaida min da ke kika Dauki wayar nan" Sai na kara sakin Numfashin cikin Rashin Mafita tsoro nake ji kada wannan Shaukin da Muryan Salisun ta Rikid'e ta koma shaukin bakinciki da takaici. shiyasa na kasa mgana Dakyar na iya bude baki nace"Sai kun kariso. Allah ya tsare" Daga haka na yanke wayar ina jin kamar ana Saremin gwiwoyina. Daidai Lokacin da Ramatu ta Idar da sallar ko kafin ma ta nemi ba'asi tace"Salisu ne ko? Sun taso ne? Dakai na amsa mata sai ta mike Dakyar ta fice tana fadin bari tayi ma su Adda Fati mgana. Ni dai in da ta bar ni nan nake zaune wani Lokacin ina jin yayan mutane alamun ina cikin duniyarmu. Wani Lokacin kuma sai na tafi dogon zangon Tunanin da zan ji kamar komai ya tsayamin Dif! Bana jin yayar wannan duniyar tamu. Da mganar mu da Salisu an fi minti talatin kafin naji Hayaniyar cikin gidanmu tafi ta kowani Lokaci karfi. Tabbas ba Lafiya in dai hayaniyar gidanmu ta rika amsa kuwwa acikin Dakuna. Gabana ya yanke ya Fad'i ras!. Kaina ya saramin a lokaci d'aya, mikewa nayi da sauri jikina da gabbaina sai da suka amsa saboda karfin da na saka wajen tashi. Habiba ta fad'o dakin da sauri sai muka kusa cin karo da juna cikin Fitan hayyaci Tace"Salisu..Salisu ya yi hatsari.! Kamar saukan Aradu haka naji kalamanta,Shuu! Naji kunnuwana sun yi kafin naji Habiba na jijjigani, kafafuwana sun yi sanyi kalau din da suka kasa Daukata,sai ji nayi na tafi luu numfashi na tare da ji na da ganina suka Dauke gabad'aya. Ammh zuciyata harbawa ta ke yi da tunanin Ni HASIYA tabbas ina cikin TSAKA MAI WUYA..! Ba suma nayi ba,ina cikin Hayyacina sai dai ji nayi kamar na samu cutar shanyewan duka jikina, Tunda ina jikin Habiba ne, ammh gabbaina ba inda yake iya motsi wani irin mutuwar jiki ce ta kamani kamar wacce likitoci suka yi ma alluran kashe jiki. Naji mutane nata shigowa Dakin, a na ta maganganu a saman kaina ina jin Muryan Adda Fati tana Salati tare da Fadin"Mun shiga uku. Allah yasa ba abunda ya faru akan Abubakar ba ne zai maimaita kansa a kan Salisu ba" Shine ma! Naji na amsata a raina ai ba bu wani bambamci balle da naji Muryan Ramatu cikin Damuwa tana Fadin"Yanzu abokinsa Musabahu ya kirani cikin damuwa yana fad'amin. Ashe suna kokarin tahowa nan Daukan mu sai ga waya Shagon Salisu ya kama da wuta ga kayan mutane aciki. Shine a rud'e ya hau mashin din kaninsa ya tafi,to ya ce min bai ko karisa ba Mota ta tureshi ya Fad'a ma wani mai adaidaita suka yi fadin anrigizo tare" Sai salati ke tashi a dakin da Hayaniya. Muryan Inna talatu naji tana fad'in"Wani hali Salisun ke ciki? Ramatu tace"Yace suna Emergency har yanzu likitoci na kanshi ammh shi Direban adaidaitan ance nan ta ke  ya rasu" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un. Su Adda fati ke ta faman maimaitawa. Gidan Gabadaya ya Hargitse har da makota masu shigowa jin gulma da ganin yadda za'a kaya. Muna nan ana ta maida zence ni dai tun bayan da Habiba ta jinginar da ni jikin garun Dakin Maman boy ban kara motsi ba, kuma ba Hawaye acikin Idanuwana. Ramatu ta zauna a gabana tana fad'in"Don Allah Hasiya kada ki damu Musbahun ya tabbatar min komai zai zo da sauki" Kallonta kawai nake yi ina jin kamar karo na farko da Naji  kalaman Ramatu ba su burgeni ba. Tunda karya take Fad'amin babu abunda zai yi daidai karya take min. Na sani! Itama ai ta sani komai zai kwabemin ne kamar yadda ya kwabemin Lokacin aurena da Abubakar. Yana sona ina son shi ammh Kaddara da Tsaka mai wuyar da Rayuwata take ciki ta yanke aurena tsakanina da shi Har Abada. Daga kofar D'akin Maman Boy ma muna jin kururuwa da Muryanta, tare da mganan wasu suna fad'in"Ku rike ta mana" Ammh ina kururuwa take yi,kamar tsohuwar mahaukaciya, kamar an samin magad'isun mganin a jikina sai gani na mike kan kafafuwana, ko mutuwa nayi na dawo nasan muryan Sahura Matar Salisu, ba sau daya ba ba sau biyu ba tasha zuwa ta min kashedi kan mijinta. Ramatu na kokarin rikeni na Fizge jikina na fice,ina ratsa matan gidanmu da suka yi Dafifi kofar Dakin Amma. ba wuta ammh akwai hasken Farin wata ya haske tsukakken tsakar gidan namu Tarwai ana ganin komai. A gabanta na tsaya ana rike da ita, ihu take tana kuka tare da kuruwan ina nake sai ta kashe ni. Ba zato ba tsammani taji muryana a saman kanta ina Fad'in"Gani..Gani Sahura" Na fad'a cikin wani yanayi a muryata,gabadaya sai kallo ya Dawo kaina har da Ramatu da ta biyo bayana. Adda Fati a rude' ta riko ni tana Fadin"Ke Hasiya lafiyan ki kuwa? Amma na da cikin Daki tunda Labarin ya shigo gidan taji zazzabi mai zafi ya Rufeta ammh kiran sunana da Fati tayi sai ya tafi da kaso mafi girma na cikin sauran kuzarinta sai ga shi ta kife saman katifar da ta ke zaune tana makyarkyatan Sanyi. Adda Fati na kokarin janyeni Sahura ta kyalla ido ta ganni tayi kukan kura kwace rikon ta da kannenta mata suka yi mata,ta nufeni gadangadan tana zuwa ta shakemin wuya, shakar da har ina kakari da gaske take yi Halakani zatayi kuma Daman ta Dauki alwashi. Idanuwanta Jajir kanta ba ko Dankwali gashin kanta ya mike tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu Cikin kuka ta jijjigani tana Fad'in"Daman sai da na ce kada ya aureki. Ga mata nan kala kala Dole sai ke? Ina zaman zamana da mijina zaki kashemin shi. Na rantse da Ubangijina in Mijina ya mutu sai nayi ajalin ki Hasiya ni zan kashe ki da Hannuna" Cikin ido na kalleta kafin nace"Nima zan so haka. Zan so ki kashe ni kamar yadda kika ce" Na fad'a cikin muryata mai cike da yakinin nima mutuwar ce ta Dace da ni. Kara makureni tayi tana ikirarin sai ta kasheni. Naji hannaye da yawa suna kokarin bambare hannayenta daga saman wuyana da kuma masu janyeni daga gareta. Ammh ni na kasa wani yunkuri na kwatan kaina. Na riga na gama sadaukarwa Rayuwa ta bata da amfani in dai zan rika zame ma duk wani mai sona Tashin Hankali da Bakinciki. gwara na Mutu kowa ma ya Huta. *Littafin TSAKA MAI WUYA paid book ne, iya Book 1 ne free Pay N500 For BOOK 2,3. Regular group or VIP GROUP N1000. Via 0552179550 Jamila Umar gt bank.* *Shedar biya ta wad'anan lambobin 09069067488 or 08032773332.* *SPECIAL GROUPS Follow@Jamilaumarjanafty On AREWABOOKS mutanen mu na Niger za su Tuntubi Kausar Aglan nissa +22796562223 Nagode* *Janafty* *Friday 11/08/2023* *1:30pm* *Post on 01/01/2024* *TSAKA MAI WUYA.* *Wattpad:JamilaUmar315* *Mallakar:Janafty* *Arewabooks:JamilaUmarjanafty* *GAISUWA BAN GIRMA ZUWA GA IYAYEN D'AKINA.* *HAJIYA HADIZA MAHE MUHAMMAD* *HALIMA DALHA SHEHU(MAMA)* *ANTY ZAINAB ABDULWAHAB* *HAJIYA AISHA AHMAD IYA* *HAJIYA LUBABATU MUSA* *ANTY FIRDAUSI KABIR* *ANTY FADILA KABIR* *ALHERIN ALLAH YA LULLUB'E RAYUWARKU GABADAYA AMIN* https://chat.whatsapp.com/CPRnRPcAD5K8vEY91Ziz8V +201123302418 *02* Dakyar mutanen da ke zagaye damu suka samu nasaran raba hannayen Sahura da wuyana. Ammh kafin su samu nasaran raba hannayen nata da Wuyana na jigata, domin shaka ne ta yi min da niyar da ke zuciyarta da kuma kalaman bakinta na sai ta kashe ni. Ko bayan an samu ta sakeni karin kokarinta kuma ta kara rike wuyana. Da gaske take yi sai ta kasheni ni ko gabbaina sun yi sanyi da ba na iya ma wani motsi Adda Fati ne da Ramatu ke faman ja na. Ammh na kasa kokarin Tallafa musu wajen kare kaina. Kafin kace me? Gidanmu ya cika Damkam da mutanen anguwa har da Maza magidanta da Samari, ana ta faman maida zencen abunda ke faruwa. Ko ba'a maida ba irin zage zagen da Mugun alkaba'in da Sahura ke jifana da shi kada'i ya isa mutane su gane abunda ke faruwa. Sahura ta haukace ko na ce ta fita daga Hayyacinta ihu take yi tare da kwakwazo tana Fad'in duk mganar da tazo daga bakinta a kaina mara kyau da mugun Fata. An yi an yi a fitar da ita daga gidanmu ammh abun ya ci tura kannenta bazasu iya ba. Sai da suka kira wasu daga chan gidan ba jimawa sai ga su ciki har da yan'uwan Salisun. Wata mata kamar yayar mahaifiyar Sahuran ce sai da ta tsinke Sahura da kyakyawan maruka har guda Biyu. sannan ta dawo cikin hayyacinta ta koma ta zube a kasa tana sakin wani Gunjin kuka mai fitowa daga karkashin zuciya. Buda'r bakin Matan cikin Fad'a tace" ashe baki da Hankali ban sani ba Sahura? Mijin ki na asibitin rai ko mutuwa ammh ke kina nan kina Hauka da Shirme? In yau Salisu ya mutu babu wacce tayi asara sai ke, kin zama bazawara sannan ya'yanki sun zama marayu" Kalamanta suka sanyayyar ma da kowa jiki ciki har da ni da nake tsaye cikin Halin Tsaka mai wuya. Jikin Sahura sai ya yi sanyi ta koma ta na kuka Kasa kasa, Umarni taba ma sauran aka kamo Sahura daga zaune ta mike tana Sharbe kuka cikin Kaushin murya tace"Mu je gida Sahura. addu'a mijin ki ke bukata ba wannan hayaniyar ba, kina mganar zaki kasheta in kika Fad'a gaban yan Amin fa? Kika kashetan fa? Ke ma kina da Labarin kashe ki za'ayi? Sai sahura ta kasa mgana sai Kuka, Wata kanwa ga Salisu ta na matsayin Diyar kanwar mahaifiyarsa ne Zaliha ta kyabe baki tana Fadin"To ba gwara ta kashe mugun iri ba. Ban da Abun Namiji me Salisu ya gani ajikin wannan abar da ya kasa sukuni sai ya aureta? Ta fad'a tana nuna ni sama da kasa kafin ta cigaba da fadin"Ba yadda yan'uwa ba su yi da Salisu kan ya hakura da yarinyar nan ba ammh yak'i Yarinyar da akace ko iyayanta kan Dole suke zaune da ita tun haihuwarta bala'i ke fad'a ma Ahalinta tayi auranta na Farko ta Tsiyace mijin da Ahalinsa gabadaya, ammh kasan da wannan abun kace kai ma sai ka aura ? Haba haba ai wlh ba haka nan ba ne wannan al'amarin da wata a kasa" Karaf wata tace"Kila farar fatan ta ke Rud'an su. Ko lange langen jikin nata? Ammh ni ban ga abun sha'awa a tare da wannan abar ba sai jaraban tsiya da Bala'i" Sai kuma da suka Fad'an na kara bin kaina da kallo duk mganganun da suka Fad'a gaskiya suka fad'a. Ba ni da kyau na azo a gani sai farin fata ,ammh ko dirin nan na mata ba ni da shi siririya ce ni sosai kamar a hureni na Fad'i. Sun yi ta Fad'an mganganu marasa Dad'i su Adda fati da matan gidanmu ke basu hakuri. Shudewar awa d'aya sannan balataliyarsu ta bar gidanmu sai gidan ya yi tsit sai dai tashin yan kananun mganganu. Ni dai juyawa nayi kafana na taku daya bayan d'aya cikin sanyi da wani irin yanke kauna zuwa Dakin Amma. Duk girman tashin hankalin da zan shiga Amma ce mace ta farko da kan Fad'omin araina a irin wannan yanayin. Ina shiga Dakin Duhu ne ya fara mamaye ganina, ana cikin wannan halin waye zai tuna da kunna yar karamar Fitilar mai chaji din da Adda Fati ce ma ta siya mana ita. Sakamakon Dakin namu falle daya ne karami yasa ina shiga ko da Duhun dakin nasan mazaunin katifar Amma chan na nufa kai tsaye gabana na Fad'uwa. Sai dai naji gwiyoyina sun yi sanyi ne sanda na isa gefen katifar na ji tashin nishin Amma da kuma rawan sanyi mai had'uwa da sautin karan Bugawar Hakora. Cikin Daburcewa na Fara lalubanta da Hannayena Lokaci daya ina fadin"Amma..! Amma..! Jin muryata yasa ta Dago daga kifewar da tayi a tsakanin Wuyanta zuwa cikinta, Da sauri itama ta fara mikomin hannunta guda Daya ta na so ta tab'ani cikin ikon Allah naji Hannunta cikin nawa,sai na kara Firgita jin Dumin hannunta Rau har ya Gauraye da Sanyin na wa Hannun Bakina da Jiki na rawa da Tuni na manta da Halin da nake ciki na Fara fad'in"Amma jikin ne ya tashi? Ta shi muje asibiti jikin ki ya Dauki Zafi" Na ke fad'a cikin Fitan Hayyaci, na mike kenan da karfin gwiwata Amma ta yunkura ta mike zaune Lokaci D'aya tana riko hannuna, sai da na dagata na juyo ina kallonta ta cikin Duhun Dakin muryanta a shake tace"Dawo ki zauna Hasiya" Musu ba Halina bane balle Musu da Amma sai na dawo gefenta na zauna ammh ban saki hannunta ba Zafin jikinta na shiga jikina ta Dalilin hannayenta da ke cikin nawa na Jimke. Sai da ta ja gauron numfashi sannan ta kira sunana cikin karyayan Sauti na amsa mata da Sauri cikin Fargaban jin yadda take sauke numfashi, ina tsoron tashin hankali ammh na fi tsoron Tashin hankalin tashin Ciwon Amma da bai da mgani. Tayi ta wahala ko mun je asibiti sai dai su bata allurai da Ruwa shikenan ya lafa mu dawo gida ammh ni kad'ai nasan a irin yanayin da Amma take kwana ta na tashi in ciwon ta ya tashi. Shiyasa nake a firgice ko tari mai karfi naji tayi sai Hankali ya tashi matuka. Cikin Tattausan lafazi ta fara fadi'n"Kiyi hakuri da Kaddaran ki Hasiya. Watarana zaki ji dad'i in sha Allahu" Kallonta na ke yi ina laluban Fuskarta ta cikin Duhun Dakin, tunani ya tafi nesa da mganar ta ina tunanin yaushe ne Ranar jin Dad'in? Sai naji mganar Amma daga sama tana Fad'in"Kada ki sake ki saka Tunanin da mutane suke yi a kan ki. Kada ki kuskura ki yarda da su karya suke yi. Abunda suke Alakanta ki da shi Jahilci ne ba Farar Kafa a addini mu Kambun baka kada'i Annabin Rahma ya sanar damu, ko maita babu shi a addininmu saboda haka kada ki damu da duk abunda ke faruwa, Allah ne ya Saukar ma Abubakar duka kaddarorinsa. Sannan shi ya kara Dauro ma Salisu na shi Jarabawan, Ba ke ba ce Hasiya ke baki isa ki zama silar kaddara ko Jarabawan bayin Allah ba. Ba ke ba ce baki da wannan Hurumin komai da ke faruwa da sanin Allah kuma ikon shi ne" Ta karishe Fad'a tana faman jan Numfashi Lokaci daya Jikinta na kara makarkyata. Na rude hankalina ya kara tashi sai kawai na fashe da kuka ina Fadin"Amma jikin ki na rawa ga shi Zazzabi ya rufeki ki bari mu je asibiti" ko da ba na ganinta nasan mirmishin nan nata na karfin Hali tayi min kafin ta saki hannayena ta koma ta kwanta tana fadin"Bafa wani abu Hasiya.. dubamin dai panadol na sha Zazzabin zai sauka" Kafin ta gama mgana ma na bazama Bangon yammah na Dakin saboda Tsabar yadda nasan kowacce kusurwa na Dakin yasa ko cikin Duhu nasan inda muhallin komai ya ke. Wata jaka ce tawa a rataye nan nake saka Tarkacen magungunan Amma in ciwon ta ya tashi kafin mu tafi asibiti. A cikin Duhun na Dauko mganin, ammh ganin ba na gani yasa na lalubo fitilar na kunna haske ya gauraye Dakin. Da ita na samu na Haska na Debo ma Amma ruwa cikin wani karamin kofi na kuma ballo mata panadol guda Biyu, na tada ita na kuma bata tasha sannan ta koma ta kwanta tana Fad'in"Nagode Hasiya. Allah ya miki albarka Allah ya warware miki kaddarorin da suka Zagaye rayuwarki" a cikin zuciyata na amsa da Amin ganin ta koma ta kwanta ta na sauke Numfashi yasa na mike a kasalance na karisa wajen ma'ajiyar kayan sawanmu na dauko mata zani cikin zannuwan ta na rufa mata daga kafafunta zuwa kugunta. Sannan ni kuma na koma gefenta na jingina da Bango ina faman kokuwa da Numfashi na. Ammh kuka ko Hawaye gabadaya sun kafe a idanuwana. Kirjina na ke wani irin suya,ga harkarina duk ya rike nasan kuma Ulcer ce ammh ba ni da kuzarin mikewa domin na taimaki kaina Ahalin da nake ciki ba na bukatar komai ma duniya komai ya ficemin a raina. Ina jin tashin Hayaniyar su a tsakar gida, ana ta uban maida zence da Hayaniya kafin Daya bayan daya su fara shigowa dakin Amma, ina jAdda Fati da Ramatu na tambaya ta ko jikin Amma ne ya tashi? Da kai kawai na iya amsa musu na kasa mgana sai bin mutane da kallo, abun mamaki duk sun ki tafiya har da yan gidan su Babanmu. Su da basa kaunar su Rabemu Daurin auran ma Alhaji Tanko da ya kasance Shakikan Mahaifin mu guda daya daya ragemana, da Adda fati taje har gida ta Fad'a masa mganar Salisu lokacin da yace zai turo. Ammh Bude bakin sa sai cewa ya yi"Ai kawai Fati ku samu Limamin anguwan ku ya amshi mganar har Daurin auran ma. Wahala ce sai an zo har nan d'in" Ba nisa fa, ina Samaru ina Dirimi chan gidansa yake ammh a bayyane ya ke kowa baya son Rabarmu saboda ni Hasiya. Ko su Gambo da suka k'i tafiya saboda jin kwakwaf ne da samun abunda za'a koma ana ba da Labarinsa. Duk maida zencen da Ramatu da Adda Fati suke a kunnena ammh na kasa wani motsi, sai da naji Ramatu na waya bayan ta gama. Na kura mata ido ina neman karin bayani sai dai kafin na kai ga muskutawa ta fara fad'in"Musbahu ne" Gabana sai da ya fad'i na Runtse idanuwana ina jin kaina na wani Gif Gif jira kawai naji Ramatu tace Salisu ya rasu. Ammh sai ajiyar zuciya ta kwacemin sanda naji Ramatu na Fad'in"Ya ce likito su ce karaya ce guda biyu ya samu, kafa da cinyarsa ta Dama sai kuma yan Rauninka. Ammh ya tabbatarmin da Sauki" Bansan ajiyar zuciya ta kwacemin ba sai da naji ta fito sarari sannan da kuma kallon da kowa ya bi ni da shi. Sai na samu kaina da Sadda kai na kasa ina jin yar salama da Natsuwa kad'an suna shigata. Bazan iya sanin iya tsawon Lokacin da na Dauka ban yi barci ba. Abu d'aya na sani shine sai da gabadaya kowa ya yi barci ya barni Har Amma ta samu barci, ta kuma kara farkawa Zazzabin ya sauka tace na bata ruwa ta sha na Dauko mata. Bayan ta sha ta koma ta kwanta tana ce min"Hasiya ki kwanta ki yi barci kin ji ko" Da kai na amsa mata,ba domin ina jin barcin ba, Hatta Ramatu da Innarta nan suka kwana Dakin bazai Daukemu ba ita da Adda Fati Dakin Maman Boy suka kwana Tunda ita Mijinta Direba ne baya nan. Nasan ba ni da kokarin Ibada bar ni da Khamsil Salawati da nake yi a kullum, ammh bangaran Dagema Sallar Dare da Sauran Ibadu ina da wannan Raunin Shiyasa har barci ya Daukeni gabanin asuba ban iya tashi na Raya wannan daren ko don rokon Sauki daga wajen Allah a kan Halin Tsaka mai wuyar da ta ke ciki. Tare da Fatan samun waraka ga Salisu ni ba ma Aurena na ke ji ba. Lafiyar Salisu ta fi damuna fiye da aurena da ni da shi. ***** Washegari ma abubuwan da suka faru duka ba masu dad'i ba ne. Daga iren mutanen da suka rika shigowa da sunan Jaje ana maida zence tare da nuna ni, da kuma watsewar da taron biki da Salisu ya yi ba wani armashi. Ramatu ta koma gida Daman a Tukur-Tukur take aure Inna Talatu kuma Sabongari take da zama da Gida d'aya muka zauna da su kafin Yayan Ramatu ya yi gidan kanshi su koma chan Gabad'aya. Su Gambo kuwa sai yammah suka koma, bayan sun gama ganin duk abunda ya faru,suka yi ma Amma sallama suka kara gaba. To gwara su sun zo din ko da na ganin ido ne, A gidan su Babanmu su shida ne yan Daki daya Hudu sun rasu ciki har da Babanmu Alhaji Tanko shi ne babba sai Mahaifimmu, sai karamarsu Halima ita tana Birnin Ikko tana auran wani Babba ne a aikin Costume. Suna da tarin ya'ya da Jikoki kaf garin Zaria da kewayanta ba wanda bai san gidan Alhaji Mammadi kona ba. Ammh an wayi gari ba bu mai son Huld'a da mu saboda rashi da babu, Tare da Tsoron kada su rab'emu na shafa musu tsiyata kamar yadda suka sha fad'i a kaina. A kwana uku da Faruwar abun da na Fita sai da na raina kaina. Da kuka na dawo gida haka ake nuna ni dandalin matasa har da Dattawa. Chemist naje siyan mganin Ulcer saboda ta tasan min a kwanakin nan. ganin kuma Jikin Amma ya yi sauki yasa na Dauki Dubu Daya cikin Jarin Danwake da nake yi ne naje siyan mgani. Har achan Chemist din a gaban idona wani ya nuna ni yana fadin"Wannan ce mai Farar kafa da ake mgana? A aureta a auri bala'i ance mijinta na Farko mai kudi ne ammh yanzu ko keke bai da shi, yadda ma naji Biyar ma na bashi sha'awa yanzu" Wani na gefenshi ya karb'e da fadin"To shi wanda aka daura musu aure cikin Satin nan fa? shagonsa ya kone ko tsinke ba'a fita da shi ba. Ga karaya har biyu ga rauninka naji ma ana labarin Kano za'a kaisa ayi masa Dauri wajen miliyan Biyu ake nema kaga shima karshenta Sanadin Jinya ya rasa komai na shi" Ina kallon cikin idanuwan matashin ya kalleni ya tsintar da yawu yana Fadin"Tab.. irin su ai bala'i ne ga al'umma. Allah ya yi mana Tsari da Dangin tsiya" Mganin da ban karba ba kenan na Dawo gida da kuka. Ina zuwa kuma na kara cin karo da wani abun

Chapter 2 of 24