yarda na zauna dake ba." "Affan....." Sai kuma ta yi shiru tana shashsheƙa. "Am very sorry Badriyya, na sakeki saki ɗaya, amma ki sani har abada kina raina, kuma idan iyayenki sun amince zan mayar dake ko da kin gama idda zan shiga sahun manaimanki" Wayar ta saki tana shashsheƙa, a lokacin Ammi ta fito.
"Badriyya mene haka" Kallon Ammi ta yi a take taji komai na juya mata, ta sume a gurin Ammi ta yi kanta tana kiran sunanta.
Affan yana ji, sai dai kawai ya kashe wayarsa, gabansa ya ji yana faɗuwa, ƙafafunsa ya ji sun sage dan haka ya dafa bango sai kuma ya zube a ƙasa ya fara tuno rayuwarsa da Badriyya tun lokacin daya fara ganinta.
*Waiwaye*
Mu haɗu a next page, more comments more typing...
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[6/20, 9:15 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
Please likes my facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
*_Wanda za su sa yi novels ɗinmu akwai details a ƙasan page ɗin nan ku biya ku cigaba da karatu, dan koda mutum 5 ne cigaba zamuyi, wutar ƙaiƙayi ma free pages ɗin shi na gab da ƙarewa so make your payment as soon as possible, muna maraba da ku a koda yaushe domin makarantanmu kune ƙwarin gwiwarmu🥰_*
_Book 1_
```🆓Page 11```
*Waiwaye*
Driving yake da ɗan sauri yana so ya ƙarasa office kasancewar shi sabon ma'aikaci ne baya son ya yi latti, ga kuma yanayin hadarin daya taso alamu ne na ako wane lokaci za a iya sheƙewa da ruwa. Har ya wuce su a gefen titi, kuma titin babu yawaitar ababen hawa, sai kuma ya yi reverse a hankali ya dawo ya tsaya gabansu, ya sauke glass ƙasa tare da kallonsu.
"Sannunku" Ya furta, ɗaya ta amsa ɗayar kuma ta ɗan kauda kai gefe hannunta na riƙe da wasu takardu ta rungume yayinda ta rataya school bag a bayanta. "Na ga kamar kuna neman abin hawa ga hadari?"
"Wallahi kuwa, tun ɗazu duk wanda muka tara basu tsayawa ma"
"Saboda hadarin dake garin so kowa burinsa ya samu mafaka"
"Hakane!"
"Ku shiga sai na rage muku tafiya ko zuwa bakin titi ne inda zaku samu yawaitar napep"
"To shi kenan mun gode" Ta faɗa sannan ta juya ga ƙawar.
"Muje ko"
"Ni kam ba zan shiga ba because ban san waye shi ba kar ya cucemu" Bai ji abin da ta faɗa ba amma yanayinta ya nuna kamar bata son shiga ne ga shi yana ƙara makara. "Baiwar Allah ki shiga da zuciya ɗaya, nima office nake son zuwa ga shi time na ƙara tafiya"
"Ka je babu damuwa zamu samu abin hawa."
"Ni kam gaskiya sai dai na tafi na barki, kin san dai test ne damu ga kuma hadari idan ruwa ya ɓalle mana anan ya zamuyi?"
"To ki tafi kawai ba matsala" Buɗe murfin motar ta yi ta shiga, shi kuma ya ɓalle murfin ya ƙarasa gabanta ta ƙara kauda kai. "Dan Allah ki zo mu tafi, wallahi da zuciya ɗaya zan ɗauke ku ni ba macuci bane"
"Kar ka damu, ku je kawai" Ta furta tana jin hawaye na neman zubo mata" "Ni na ji a raina ba zan iya tafiya na barki haka ba" Sai lokacin ya ga fara'arta, ta yi murmushi sai kuma siririn hawayen ya zubo a ido ɗaya, ta saka hannu ta goge. "Kar ka damu ku je kawai" "In ci darajar manzo(SAW) ki shiga na saukeku please" Ya furta yana haɗe hannayensa. "SAW" Ta faɗa sannan ta sauka ta buɗe back seat ta shiga. Yana driving amma babu wanda yake magana, ya dai zuge glasses ya kunna musu AC. Suna isa bakin titi ta ce "Ya isa nan ma" Ko ƙarasa rufe baki batayi ba aka fara ruwa. Ya ɗan juya ya kalleta kin ga da ace na saukeku da yau wannan ruwan a kanku zai sauka" "Ina zan kaiku?"
"B.U.K new site" Wadda ke gaban motar ta faɗa. "Ok" Ya furta yana taka motar. "Ku lecturers ne kenan" "Wane mu? Mu students ne, muna final year ɗinmu ɓangaren Business administration" "Wow ashe tare da masu kuɗi nake"
"Hmm! Masu neman hanyar da za a samu kuɗi dai"
"Duk ɗaya ko Hajiya" Ya faɗa yana kallon ta backseat ɗin.
"Sunana Affan Ahmad Giwa, ni ƙaramin ma'aikaci ne a gidan tv"
"Alhaji Ahmad Giwa dai da muka sani?"
"Ba wannan ba, wane ni in san babban mutum kamar shi, suna ne kawai yazo ɗaya"
"Ma sha Allah! Ni sunana Aisha Kabir ita kuma Badriyya Shehu" "No wonder take da kyau kin san masu sunanta kaɗan ne a duniya kuma kyawawa kaɗai ake sakawa sunan" "Ni kam a bakinka na fara jin wannan"
"Ya kamata dai ki bincika za ki gane kema" Duk hirar da suke Badriyya bata saka baki ba, har ya isa school ba a gama ruwa ba, ko daya ƙarasa department ɗinsu bai bari sun fita ba ya ce a bari ruwan ya ɗan tsagaita. Hira sosai ta ɓalle tsakanin Affan da Aisha anan take ba shi labarin accounting taso ta yi amma mahaifinta ya ce ba zai bar mace ta yi aikin banki ba shi ne ta haƙura take business admin. Wayar Badriyya ta fara ringing, ta kalla ta ga class rep ne ya kira. "Hello 001 ya dai?"
"Anyi cancelling test yau bamu da lectures na ga baki online na ce bari na sanar"
"Ya salam ka ga shi har mun shigo school"
"Ayya am very sorry ya kamata ace na sanar miki since"
"Ba damuwa, nagode"
"You're welcome"
"It's my pleasure" Yana kashewa ta sauke ajiyar zuciya.
"Badriyya lafiya?"
"Anyi cancelling test da duk lectures ɗinmu na yau"
"Kash! That's the reason na ce miki karmu shigo saboda hadarin dana gani"
"Haka Allah ya ƙaddara"
"Yanzu dai kawai mu koma gida ko?"
"Ok. Bari ruwan ya ɗan tsagaita sai mu sauka mu samu napep"
"Shi kuma drivern naku ku yi ya ya da shi?"
"Haba ai kuma wahalar sai ta yi yawa"
"Karku damu ai ba kune kuka tambaya ba ni ne na yi niyya"
Gabaɗaya a gidan su Badriyya suka sauka, Aisha har ta rufe ƙofar yayinda Badriyya na faɗin "Nagode" ta yi gaba. Glass ya sauke tare da cewa "Idan ba damuwa ki bani number ki mana, kin ga sai na zama driver na dindindin ko?"
Murmushi tayi tare da cewa "Ai ka fi ƙarfin driver"
"A'a fa karki saka na riƙa jin kaina na girma"
Karɓar wayar tayi ta saka masa number sannan suka yi sallama ya tafi.
Aisha na ƙarasawa inda Badriyya take ta ɗan kai mata duka ita kuma ta goce. "Wallahi gayen can son ki yake Baddy"
"Ni kuma haba sai dai ke, ki ga fa hirar da kuka sha"
"Amma a hirar waye yafi ambata, sannan kuma kina gani yadda yake ta nan-nan dake, ni na tabbatar idan ya kira numberki zai buƙata"
"Ni ban yarda ba, idan ni yake so meyasa bai karɓi numberta ba sai taki?"
"Saboda kin nuna halin ko in kula, ga kuma miskilanci shiyasa ya yi tsoron tambaya kai tsaye"
"To na ji idan ya buƙaci numberta ya kuma ce ni yake so, za ki goge numbersa daga wayarki kiyi blocking sannan kuma ko kun haɗu karki sakar masa fuska"
"Sannu sarakan kishi, kina so ɗin kenan"
"Idan har ya taya zan sayar ni fa na daɗe da saninsa hasalima ni fan ɗinsa ce, anyway ina so mu ƙulla wannan deal ɗin"
"Na amince zan ga in zaki iya"
"Deal"
"Yeah deal"
"Ok" Badriyya ta faɗa tana murmushi.
_*Bayan Wani Lokaci*_
Aisha na zaune akan gadonta ta ga saƙo ya faɗo wayarta, ɗauka ta yi ta duba, abin ya matuƙar bata mamaki dan haka da sauri ta bi kiran. "Hello"
"Kin ga saƙona kenan?"
"Na gani Suhailat amma gaskiya bana jin Badriyyar dana sani ce, ko last week na je gidansu kin san idan ana cikin hutu ba a haɗuwa sosai kuma ta ce min an ƙara 3 weeks a bikin."
"To ƙarya take miki bata so kowa ya sani ne, yau aka ɗaura aurenta, ki hau whatsapp a group ɗin class ma maganarku kawai ake, saboda kowa ya san kece ƙawarta kun ɓoye biki"
"Na rantse da Allah zan iya buɗe data yanzu mu yi video call ki ganni, ina gida fa, a kwance nake ko kayan bacci ban cire ba ina ta kallo a system"
"Ba sai mun yi ba na san ba za ki min ƙarya ba, amma meyasa ta ɓoye?"
"Ina zan sani, na yi tunanin ko za ta ɓoyewa wani ban da ni, amma ina zuwa." Tana gama faɗa ta kashe, da sauri ta faɗa toilet ita kanta ta san wankan da ta yi yau kawai dai dan kar aƙi yi ne amma bata fita ba." Material ta saka dan sune marar nauyi ta ɗauki jaka da atm ta fita, kai tsaye ɗakin Mamansu ta nufa
"Mama zan je gidansu Badriyya"
"Meya faru?"
"Idan na dawo zan baki labari"
"Ke dakata ban son shirme ta ya zan barki ki fita a haka duk kin ruɗe"
Numfashi ta sauke sannan ta ce "Mama yau ake ɗaura auren Badriyya" Kallon mamaki Mama take mata kafin ma ta yi magana Aisha ta riga ta "Mama ta ɓoye min ne, koma ince ta ɓoyewa kowa, 'yan class ɗinmu sai ganin laifina suke, shiyasa nake son zuwa na ji dalilin ta na yin haka"
"Ko za ta ɓoyewa kowa bai kamata ta ɓoye miki ba, bata kyauta ba amma dai ki bi komai a hankali karkije kuyi hayaniya dan na ga a fusace kike, idan kuma kin san hayaniya za kije kuyi to gaskiya ki haƙura idan zuciyarki ta sauko sai kije"
"Ba zan yi ba Mama amma dai ina so naje saboda na wanke kaina"
"Allah ya kiyaye, ki kula"
"Amin."
Napep na tsayawa ta hango Badriyya tare da wasu 'yan mata biyu sai Affan da abokansa ana ta hotuna, har ta biya mai napep kuɗi basu lura da ita ba, sai da ta kusa ƙarasawa kawai Badriyya ta ganta, ta ɗan furgita sai kuma ta yi murmushin ƙarfin hali.
"Aisha ki shigo mu yi hotuna"
"Ba shi ya kawo ni ba" Ta furta rai ɓace, da sauri Badriyya ta ce "Ok mu shiga gida mu yi magana" Sai lokacin Affan ya ce "Aisha yaushe a gari, kin dawo kenan" Murmushin gefen leɓe tayi sannan ta ce "Haka ta faɗa maka?"
"Baby dan Allah karka ƙara magana, kin ga Aisha muje ciki" Da sauri tayi gaba, ita kuma Aisha ta sake kallon Affan sannan ta wuce.
Gidan kamar ba na biki ba dan babu mutane sosai, a gefe suka tsaya Aisha ta kalleta cikin ɓacin rai ta ce "Badriyya duk mene wannan? Dama za ki iya ɓoye min aurenki?"
"Kiyi haƙuri Aisha gaskiya na ɓoyewa kowa ne saboda ina gudun snatchers kuma kin san ance a ɓoye nema a bayyana samu, dama na yi niyyar na faɗa miki daga baya, kuma kin san gidan nan dai gidan malamai ne ba a komai daga walima sai ɗaurin aure kawai aka yi"
"Kina tunanin ni zan iya yi miki snatching?"
"Babu wani abin yarda a wannan duniyar, kuma na ga kina ta ƙara shigewa Affan ni kuma gaskiya kishina ba zai barni na bari a raɓe shi ba koda ciki ɗaya muka fito bare ƙawa."
"Badriyya bakin ki ne yake faɗar haka?"
"Ƙwarai da gaske"
"Shi kenan ya yi kyau, Allah ya baku zaman lafiya" Daga haka ta juya da sauri ta fita, ganin fitowarta ya saka Affan ƙoƙarin tareta amma ta wuce da sauri taƙi ta saurare shi.
_Bayan Mako Guda_
Tana kwance kan doguwar kujera hannunta riƙe da waya tana game kira ya shigo mata. Kallon wayar take tana tunanin kamar ta san lambar amma ta kasa tunawa, kawai ta ɗaga tare da yin sallama, yana amsawa ta gane waye ta kuma tashi zaune. "Ina ƙofar gidanku"
"Kofar gidanmu kuma?"
"E, ki fito dan Allah idan babu damuwa"
"Shi kenan gani nan zuwa" Yana yanke kiran ta ɗanyi shiru tana tunani, mene zai kawo Affan gidansu, miƙewa tayi da sauri ta nufi ɗaki ta ɗauki gyale ta yafa sannan ta leƙa ta cewa Mama za ta waje tana da baƙo.
Jikin motarsa ta gan shi tsaye ya harɗe hannayensa, ta ƙarasa a sanyaye tare da yi masa sallama. "Ko zamu shiga mota?"
"A'a sai dai ko mu shiga daga ciki"
"Ok." Ya furta gami da rufe motar, kujerun roba ta saka musu a tsakar gidan, ya zauna ita kuma ta shiga ta kawo masa ruwa. "Sannu da ƙoƙari" Murmushi kawai ta yi. "Aisha dama.....na zo ne on behalf of Badriyya ina so na baki haƙuri a bisa abinda ya faru, tabbas bata kyauta ba kuma na nuna mata kuskurenta, so dan Allah kiyi haƙuri"
"Ni ban riƙe ta ba, na manta da komai."
"Na san ba za ki iya mantawa a ƙanƙanin lokacin nan"
"Affan abin da Badriyya ta zaɓa kenan, dama tasha faɗa min ita idan ta fara soyayya za ta ja baya da duk wata ƙawa budurwa sannan idan ta yi aure matan aure za tayi abota da su ba 'yammata ba, a lokacin da take yi min irin maganganun nan da yadda take faɗa min zafin kishinta na ɗauka wasa ne amma da ta aikata hakan sai na tabbatar, sai dai na yi mamaki tun daga yarinta na fara ƙawance da Badriyya bani da wata ƙawa kamarta hasalima a secondary school ta samu matsala ta kwanta jinya sai aka mata repeating amma ban shiga jami'a ba sai dana jira muka zana jamb tare muka cike school da course ɗaya, kuma Allah ya taimakemu gabaɗaya muka ci jamb sannan muka samu gurbin karatu a jami'a, tare muke ko yaushe sai dai dama ita miskila ce shiyasa wasu lokutan idan mun samu saɓani sai ace nice da laifi kasantuwar bata da hayaniya ni kuma am free to everyone around me" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Ba komai ta nuna min asalin kalarta a yanzu"
"Na san bata kyauta ba kuma ban goyi bayanta ba, sannan na yi mata faɗa sosai, kuma itama ta ce na baki haƙuri kuma za ta kiraki a waya ta sake baki haƙuri"
"Ta riƙe haƙurinta bana so, kuma insha Allah na rabu da ita har abada."
Duk yadda Affan ya so ya shawo kan abin amma ya kasa, sai dai babban abin da ya ba shi mamaki shi ne ko a jikin Badriyya bata damu da rabuwarta da Aisha ba.
Tun wata uku da aurensu ya fara fuskantar matsala daga gareta, kullum cikin zargi da tuhuma, babu damar yaje aiki ya dawo tun a ƙofa za ta fara shinshina rigarsa, tun abin baya ɓata masa rai har ya fara, wata ranar lahadi suna zaune suna hira ya ce da ita "Baby so nake ki ɗan rage kishin nan naki ya yi yawa" Ta haɗe fuska sosai tana kallonsa, kafin ta ce "Affan ni gani nake sam bana kishinka, wallahi da da yadda zan yi da sai na daƙile aikin nan naka, ni fa duk wani aiki da zai shigo da mata rayuwarka ba ƙaunarsa nake ba, tun ranar dana ziyarci gidan radionku naga ku san duk abokanan aikinka mata ne ranar ko runtsawa ban yi ba" Ɗan zaro ido ya yi, sannan ya yi murmushi, ki kwantar da hankalinki, kin manta a cikin dubban mata ke ɗin na gano na kuma aur"
Murmushi ta yi sannan ta ce "Hakane Babe! Amma ni gaskiya....." Sai kuma ta turo baki.
"To mene na ɓata rai, am sorry Baby kina ji?" Kai ta gyaɗa. "Ina so ki je ki bawa Aisha haƙuri."
"To mene na yi mata da har zan bata haƙuri?"
"Saboda ƙawarki ce, kuma tare na sanku, dan Allah Baby kiyi haƙuri ku daidaita"
"Ni fa ba zan daidaita ba, saboda na lura Aisha sonka take, tun farko ma so ta yi kace ita kake so bani ba, dan haka ni gaskiya ka daina min maganarta" Tana gama faɗa ta miƙe tsaye, sai kuma aka turo ƙofar parlourn aka shigo.
"Yaya ashe kana gidan"
"Eh ina nan, ya dai?" Kai ta ɗan sosa sannan ta ce "Dama...dam..."
"Kin ga ni ba sai kin faɗa min ba, bari na tashi na tafi gurin Mommy" Tana kallonsa har ya fice sannan ta zauna.
"Lawisa ya kike?"
"Lafiya lau Aunty Amarya, na zo na tayaki hira ashe ma Yaya yana nan"
"Dama fita zai yi gara ma da kika zo"
Murmushi kawai ta yi suka cigaba da hira.
*Bayan Wata Biyar*
A cikin asibitin ya yi parking sannan ya kalleta "Maman Baby mun zo" Murmushi ta yi sannan ta ce "Yauwa Babe amma dai za ka dawo ɗaukana?"
"Insha Allah, ba dan akwai wasu baƙi da zamu gana dasu ba ai da sai na jira ki gama sannan na tafi" "Amma duk da haka ya kamata ka shiga dani ko?"
"Ok babu damuwa mu je your majesty ai duk yadda kika dama haka za asha" Murmushi ta yi, ya sauka ya buɗe mata ƙofa ta fito sannan ya shigar da ita, har ƙofar ɗakin awo ya kaita sai daya tabbatar ta shiga sannan ya juya.
Yana ƙoƙarin fita ita kuma ta shigo a kiɗime bata sani ba har ta ɗan buge shi, ta ɗago tare da faɗin "Yi haƙuri dan Allah"
"No kar ki damu" Har zai wuce ta yi saurin cewa "Dan Allah ko za ka iya taimaka min?"
"Dame fa?" Ya tambaya yana kallonta.
"Na kawo wata mata ne, kuma wallahi a ruɗe nake na manta jakana a gida, ko zaka taimaka min sai na yi maka transfer daga baya?." "Tana ina" Ya furta.
"E, tana nan waje" Ta faɗa tana nuna waje da hannu, duk da sauri yake amma ganin mace da tsohon ciki ya saka ya kasa tafiya har sai daya biya kuɗin komai, tare da budurwar suka yi ta yawo suna suyo kayan da ake buƙata kafin daga bisani aka shigar da ita. Yana duba agogo ya ga ƙarfe goma da mintuna sha takwas ya riga ya yi latti, "Am...ina fatan babu abin da za a buƙata ko? Na makara ina da meeting a office ne"
"E babu, nagode Allah ya saka da alheri, in babu damuwa ko zan saka maka numberna sai ka kira wayar a kunne take idan naje sai na kira ka turo min account number" Murmushi ya yi tare da faɗin karki damu nima na bawa Mamanki gudunmawata ne ba sai an biyani ba" Yana faɗa ya ga ƙwalla ta cika maƙil a idanunta, maimakon farin ciki kawai sai ya ga ta fashe da kuka, "Lafiya?" Ya faɗa da mamaki amma kamar ƙara rura mata wuta ya yi, ta cigaba da kuka, yana ta rarrashinta saboda mutane har sun fara taruwa a wurin. Shiru ya yi ya lafe a bango yana kallon sarautar Allah, ɗaiɗaikun mutanen dake wucewa tambaya suke ko lafiya ko rasuwa akayi, sai ya ce musu a'a suke wucewa, ku san mintuna goma ta ɗauka tana kuka, shi kuma ya kasa tafiya har sai data gama kukan ta goge hawayen sai kuma ta miƙe ta kalleshi. "Ya kamata ka tafi kana ƙara makara"
"Meyasa zan tafi na barki a wannan halin"
Murmushi ta yi wanda da gani yaƙe ne "Babu damuwa fa" Shiru ya yi sai kuma a lokacin ya kalleta sosai. Matashiya ce da ba zata gaza shekaru ashirin zuwa ashirin da uku ba, ruwan tarwaɗa sai dai kuma kyakykyawar gaske ce, tana da ɓullar hanci wanda ta masa ado da dutse fari mai ƙyalli sai kuma fashin goshi da take da shi, doguwa ce sai dai ba can ba, bata da ƙiba kazalika bata da rama.
"Am.....Kawai da ka yi maganar na tuno da mahaifiyata ne duk da ban santa ba ban kuma san kamanninta ba"
"Oh so sorry, Allah ya jiƙanta da rahama ai ban sani ba da ban miki maganar da za ta sosa ranki ba"
"Amin! Amma a zahirin gaskiya ban sani ba ko ta mutu ko kuma tana raye" Furucin na ta ya ƙara dulmiya shi a tunani, ya kalleta ya kuma kasa tambaya saboda gudun kar ta kuma faɗawa damuwa ko kuma ta sake yi masa kuka. "Ka yi mamaki ko? Ni marainiya ce a gidan marayu na tashi na tsinci kaina kafin daga bisani wata mata ta fanshe ni saboda bata haihuwa sai dai ban daɗe da ita ba Allah ya azurta ta da haihuwa, daga lokacin ta fara gana min azaba wannan matar dana kawo nan itace ke jana a jiki tana kuma taimaka min da abinci, labarina yana da tsayi kar in saka ka makara"
"Zan so jin labarin naki gabaɗaya, ko zan iya samun numberki?"
"Sosai ma" Ta faɗa tare da karɓar wayarshi ta saka masa number ɗinta ya yi saving sannan ya kira "Za ki ga 81 a ƙarshe" "To shi kenan nagode" "You're welcome."
Yana fita ya ga Badriyya a gaban motar ta haɗe girar sama da ƙasa.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty_
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
Facebook: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/
_Book 1_
_🆓Page 12_
Tattaro ɗan kuzarin daya rage masa ya yi sannan ya ƙarasa gabanta, sai ƙara haɗe rai take tana kaɗa ƙafa ɗaya. "Ba dai kin gama ba?"
"Affan ina office ɗin?" "Faɗuwa ce tazo daidai da zama shiyasa na tsaya anan ɗin. Na samu wani rahoto ne shi ne na tsaya ɗauka."
"Rahoto kuma na me?" "Kin ga mu shiga mota sai na ƙarasa baki labari kin san dai ba a son ku yawaita tsayuwa yanzu ƙafarki sai ta kumbura." "Ƙaramin ciki ne fa" "Koma dai mene ni kam ba zan bari ki wahalar min da Baby ba."
"Oh babyn ma?"
"Har da big Baby" Ya furta da dariya yana ƙoƙarin buɗe mota.
Yana fara driving ta sake tambayarsa.
"Wata mata ce aka kawo kin san wai shekarunta 60 a duniya amma ta sake haihuwa wai kawai saboda mijinta ya ƙara aure." Ya samu kansa da yi mata wannan ƙaryar. "Haihuwa fa Babe, to taya ta iya ɗaukar cikin?" "To kishin ku na mata ai babu abin da ba zakuyi ba akan kishi dai"
"A'a Babe ita kam na ta ya yi yawa wace irin masifa ce wannan shekara sittin may be har jikoki ne da ita amma ta haihu"
"Yanzu ko ni idan na ce zan miki kishiya kina shekaru 60 ba zaki iya ba?" Ɓata rai tayi yayi dariya, "Anzo wurin ko?" "Babe ka san bana son maganar kishiya"
"Am sorry Babe misali ne fa"
"Ni kam ban son wannan misalin, kuma koda ya kasance dani wallahi ba zan yi gasar haihuwa ba wanda na samu ma Allah ya raya, ni fa gani nake ɗa ko 'ya ɗaya sun wadatar ni kam ko iya laulayin nan aka barni da shi ma ya isa haka Allah ya raya"
"Kin isa ma, ni da nake son 'ya'ya, ai a ƙalla sai kin haifa min ko 4 ne." "Haba Babe a wane cikin? Gaskiya ni kam ina haihuwa planning ma zanyi sai na yi shekaru biyar cif sannan zan kuma haihuwa"
"Ban amince ba" Dariya ta yi shi kuma ya ƙara haɗe rai "Badriyya idan ma wasa kike nima bana son irin wasan nan, ina son yara dan haka ban yarda kiyi planning ba."
"Gaskiya Babe rigima ne da kai, to akan me? Ka san kuwa wahalar? Kuma a wajen awo wasu ina ji suna cewa wannan so
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 15