Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
a fuskarta. "Kafin na fito parlour ki tabbatar kin ɗebi yaranki kin bar min gida, in ba haka ba wallahi ranki sai ya ɓaci." Juyawa kawai ta yi kafin ta fita ta ji Mameey na faɗin, "Idan kina son zuwa gidan nan to ki kashe aurenki dan bana ƙaunar wancan matsiyacin." Fita kawai ta yi, a corridor ta tsaya ta goge hawaye sannan ta ƙarasa parlourn, ta tarar sun haye kan Faruq suna ta wasa. "Wato duk kun haye Uncle kuna neman karya shi" Ta faɗa cikin ƙarfin hali tana dariyar yaƙe. Kallonta ya yi, ya ga yanayinta ya canja, kuma da mamakinsa sai ya ga ta sauke Ihsan daga kan shi tana ƙoƙarin sauke Najma. "Ya za ki sauke su muna wasanmu?" "Zamu tafi ne" "Tafiya?" Kai ta gyaɗa. "Amma ke kika ce min zaku yini a nan" "A'a dama na faɗa ne kawai" Sai kuma ta yi saurin goge hawayen daya zubo mata. "Aunty Sady lafiya kuwa?" "Ba komai Yaro abu ne ya faɗa min a ido" Kallon side ɗin Mameey ya yi sannan ya kalleta "Idan ina ƙarami kun min wayo yanzu ni ɗin fa ba Yaro bane, kawai suna ne daya zama linzami" "Kawai zamu tafi ne" Ta furta tana riƙe yaranta, shima miƙewa ya yi "Dan Allah Aunty Sady ki zauna." "Ka barta ta tafi, ba ta zaɓi aure sama da uwar da ta kawota duniya ba." Dukkansu kallon Mameey sukayi data fito daga side ɗinta, ta ƙaraso parlour sannan ta ajiye ƙatuwar ledar dake hannunta "Gasu nan ka kaiwa Saddiqa, kace mata lace ɗin ɗaya aka samu shiyasa na ɗaukar mata atampopi guda uku." "Mameey dan Allah kiyi haƙuri, shekaru nawa da auren nan amma har yanzu..." "Yaro kai ɗa nagari ne, kana jin maganata karka yarda ka fusata ni" "Mameey dan Allah karki min baki, ina da dalilina na zama da Yazid kamar yadda kema kike da naki dalilin, Mameey mijina yana ƙaunata yana kuma ƙoƙarin kyautata min, dan me zan rabu da shi? Talauci? Mameey a duniya babu wanda yake ma wani arziƙi, sannan ko waye zan aura Allah zai iya masa jarabawa irin wadda yawa Yazid idan yaso" Mameey a fusace tayo kanta, Faruq ya yi saurin shiga tsakaninsu. "Haba Mameey dan Allah kiyi haƙuri" "Kana jin abinda take faɗa fa?" "Dan Allah kiyi haƙuri Mameey" "Sadiya idan na ƙara ganinki a gidan nan wallahi sai ranki ya ɓaci" Da sauri Sadiya ta fita, shi kuma ya kalli Mameey sannan ya bi bayansu. A farfajiyar gidan ya tsayar dasu. "Dan Allah Aunty Sady kiyi haƙuri, in dai Mameey ce kin ri ga kin saba da halinta." Bata ce komai ba ya ce "Bari na ɗauko kayan sai muje gidan Aunty Saddiqa tare" "A'a Yaro, ba zan iya zuwa yanzu ba, gida zamu wuce" "Meyasa? Haba Aunty Sady a gidan nan na san kin fi kowa haƙuri" "Yaro ba zan iya zuwa ba, kuma kada ka faɗawa Saddiqa abinda ya faru." "It's okay bari na ɗauko kayan sai na miƙa ku gida kafin na wuce" "Gaskiya a'a, ni ba zan ƙara jawa kaina wani faɗan ba, so kake ta sake zagina in na shiga motarta" "Mahaifiya ce, ba yadda muka iya" "E, amma gaskiya ba zan shiga ba" Tana gama maganar ta juya, shi kuma ya zaro dubu ɗaya a aljihu ya bawa Najma "Ga shi ko, ku sayi sweet." Kallon Faruq ta yi lokacin Najma na faɗin angode. Wuce wa kawai ta yi, yana nan tsaye har suka bar gidan sannan ya koma ciki, bai tarar da Mameey a parlour ba, dan haka zama kawai ya yi, dan baya so ya fita ya ga Sadiya na tafiya zuwa titi shi kuma ya wuce a mota. ****** ****** ******* Shiru ta yi na wani lokaci kafin ta ce "To ɗaki na zuba, bayi kuma ya rufta ga damuna yanzu a tsakiyarta muke, kana ganin yadda gari yake a yanzu ma hadari ne gashi nan, ya zakuyi?" "Umma tun farkon damuna haka muke ta fama wallahi, indai ana ruwa to a tsaye muke har a gama, idan da dare ne kuwa sai dai mu tsaya a soro, wallahi ni na fi tausayin yaran da kuma Sadiya da take da tsohon ciki" "Amma baka tausayin kanka ko? Yarinyar nan na tsaneta, saboda kana aurenta komai naka ya lalace" "Umma dan Allah ki daina faɗar haka, ni na yi imani cewar duk abinda ya faru dani yana cikin ƙaddarata ne" "Har da auren mai baƙinjini? Wadda tayi sanadin rugujewar lamuranka" "Umma..." "Yazid zan iya baka umarni ka ɗauka?" "Umma ai ba zan taɓa iya tsallake umarninki ba" "To ka saki Sadiya" Zaro idanuwansa ya yi yana kallonta, dan bai taɓa tunanin zata faɗi haka ba. _Littafin WUTAR ƘAIƘAYI ba free book bane, amma ina muku albishir da cewa book1 gabaɗaya zai kasance free, sannan akwai yuwuwar zaɓar mutum biyu da suka fi kowa yin sharhi akai su karanta kyauta._ _Sannan littafin tafe yake da tagwayensa. *TAZARAR SO, WA'ATI* da kuma *A CIKIN IDO* za ku samu littattafan a farashi kamar haka. Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* _Domin neman ƙarin bayani sai a tuntuɓemu a WhatsApp ta wannan number 07035111671._ ```Sai kunzo!``` #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazdeeyah_ _Facebook@SaNaz Talkshow_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 2``` "Wannan zazzare idanuwan da kake ya tabbatar min da ba zaka iya ba." "Umma dan Allah kiyi haƙuri, amma Sadiya bata min laifin da zan saketa ba, tana kyautata min, sannan kuma uwar 'ya'yana ce" "Gayyar 'ya'ya matan, sam babu magaji, wannan cikin ma bana fidda ɗayan biyu ko dai ya zube ko kuma shima a haifi mace." Umma! Haba Umma, ciki wata takwas ai ba za ai fatan haka ba" "Bayan waccan yarinyar Lihisan take ko wa, sau biyu tana ɓari fa, ga kuma talauci sai ƙara binku yake" "Umma idan ba Sadiya ba, na san babu macen da zata iya zama dani a haka, da wata ce da tuni ta gudu, amma Sadiya ta zauna dani, kuma a hakan tana kyautata min daidai gwargwado" "To tunda haka ne ai sai ka tashi ka tafi ku ƙarata ko." Jiki babu ƙwari ya miƙe. "Allah ya huci zuciyarki Umma" Baki kawai ta taɓe tana binsa da ido. ******** ******** Kitchen ɗin ya leƙa "Oh wai kina nan nake ta kwaɗa sallama" "Faruq kaine a gidan nawa?" "Ni ne fa" Kallon 'yan aikin ta yi sannan ta ce "Ku ƙarasa ina zuwa, amma ku kula karku bari ya sayu da yawa" Tana gama faɗa ta fita. Kayan ta karɓa tana fito dasu "Kenan dai zuwan ba nawa bane, gaskiya Faruq baka da zumunci" "Haka dai ake ta faɗa" "Allah ya shiryeka, ai ba dan Sadiya ta faɗa min zata zo ba da daga nan gidanta zaka wuce dan wannan kayan nata ne." "Wai dama ita kika sayawa?" "Eh amma ban faɗawa kowa ba, har Mameey" "Ai gara da baki faɗa ba, dan yanzu ta gama ciwa Aunty Sady mutunci" "Ai dama Sadiya bata da farin jini tunda ta auri Yazid" "To wai mene laifin Uncle Yazid ɗin?" "Kawai ba shi ne zaɓin Mameey ba, ita burinta Sadiya ta auri wani ɗan siyasa ita kuma Sadiya ta dage sai Yazid" "To tana son mijinta, ni wallahi ban ga aibunsa ba, ga fara'a da wuya ka ga fushinsa" "Itama tana shanyewa fa, duk abubuwan da Mameey ke mata" "Amma duk da haka yau da kuka ta bar gida" "Gaskiya Mameey bata kyautawa wallahi" "Hmm! Ai ni rasa bakin magana na yi, kuma na ce mata ta zo mu taho nan tare ta dage gida zata wuce" "Kenan dai ba zata zo ba?" "Gaskiya ko za ta zo ba yau ba, dan yanzu haka rai ɓace ta bar gidan" "Auta na nan kuwa?" "A'a gaskiya bata nan, tana school bata koma ba" "Okay yanzu dai haƙuri za kayi idan mun gama hira ka tafi gidan Sadiya tunda a mota ne sai ka kai mata, kuma ga awarar da nayi mata sai dai ka haɗa duk ka kai mata" "Aunty Saddiqa ni fa ba wai na zama ɗan aike bane" "To idan bamu aike ka ba waye zamu aika?" "Ya na iya!" Ya furta yana gyara zama. ******* ******* ******* Suna zaune a tsakar gidan bisa tabarma, Sadiyar na ɗan matsar hawaye jefi-jefi, sallama ta ji daga waje dan haka da sauri ta miƙe tare da zura hijab, ta fita dan ta duba. "Sannunku" "Yawwa sannu dai, maigidan yana nan kuwa?" "Baya nan" "Dama 'yan nepa ne mun zo karɓar kuɗin wuta." Sai lokacin ta kai dubanta ga kurangar da suka jingine jikin tumbar wuta. "Dan Allah ku yi haƙuri idan ya dawo zan sanar masa sai ya kai kuɗin har ofishin ku." "Idan ya kai kuɗin sai a dawo a mayar masa amma yanzu gaskiya yankewa zamuyi dan tun jiya muka sanar da shi cewa indai bai kawo kuɗi ba zamu zo mu yanke, kuɗaɗen da ake binku suna da yawa" "Mun sani amma wallahi iya haske kaɗai muke gani ko fanka bamu da ita" "To Hajiya wannan kuma ai ba laifun mu bane, kune kuka ga zaku iya, ka ga Bala, maza hau ka yanke, idan sun biya sai a gyara." Tun da motar ta shawo kwana Sadiya ta kafeta da ido, gabanta ba ƙaramin faɗuwa ya yi ba, dan in dai Mameey ce ta tabbatar sai an samu matsala. Faruq ne ya fito daga motar, ya ƙarasa gabanta "Aunty Sady ba dai wutar ku za a yanke ba" "Sun ce sai sun yanke" "Ai ba munce bane, ke kanki kin san mun ɗaga muku ƙafa" Ajiyar zuciya kawai ta sauke bata sake magana ba. "Har nawa ne kuɗin?" Faruq ya tambayi ogan nasu. "21,000. Duk wata dubu uku kaɗai muke karɓa a gidan nan na su, amma wannan shi ne wata na bakwai basu bayar da kuɗi ba, tunda suka dawo gidan nan sau ɗaya suka bayar." "Zan bayar, ya sauka kar a yanke musu wuta" "A'a Yaro kar ma ka fara, ina ka ga wannan kuɗin" "Amma dai Aunty kin san idan bani dasu ai ba zan ce a sauka ba" "Ka bari su yanke, idan Yazid yazo sai ya biya a gyara" "Hmmm! Oga bari na maka transfer." Sadiya komawa cikin gidan ta yi dan ta lura Faruq ma ba zai ji maganarta ba. Tana nan zaune ya shigo da ledar a hannunsa, Ihsan da Najma da gudu suka je suka rungume shi. "Uncle ka dawo" "E babies" Ya fara ƙarewa gidan kallo yana sake shiga tsananin mamaki. "Aunty Sadiya anan kuke rayuwa?" "Faruq karka ce komai dan Allah" "Kiyi haƙuri amma dole na faɗa, duk yadda nake ganin munin wancan gidan naku sai naga ya fi wannan daraja." "Ka zauna Yaro" Kan tabarmar ya ƙarasa ya zauna. "Can daya rushe ina ne?" "Banɗakinmu ne, shiyasa ma na tafi gida dan nayi wanka acan tunda na samu dai na yiwa yara, amma kuma ka ga abinda Mameey ta yi" "Aunty Sady kuma a haka kuke haƙuri da rayuwa, naga kin fito da kaya da alamun ma ɗakin zuba yake" Murmushin yaƙe ta yi kawai. "Zan yi wa Aunty Saddiqa magana sai mu haɗa a gyara banɗakin da rufin ma, ni ba zan iya ni kaɗai ba, musamman ma banɗaki at anytime za a iya buƙata." "A'a ni ban ce ku yi hakan ba, ba alhakinku bane gyara muhalli na, kuma shi kansa Yazid ɗin ya fita samo mai aiki ne." Murmushin yaƙe Faruq ya yi sannan ya ce "Ga wannan ashe ma naki ne aka saka ni wahala biyu, wannan awarar ma takice ta ce tunda baki je ba, sai na kawo miki" Sadiya ta buɗe ledar da mamaki take ɗaga leshi da atampopin "Wai Saddiqa bata gajiya ne?" "Ta ya zata gaji, ai ba'a gajiya da kyautatawa ɗan uwa" "Hakane, amma gaskiya sun yi kyau sosai, nagode Allah ya saka da alheri kace zan zo har gida na kuma yin godiya." "Insha Allah" Ya faɗa yana miƙewa. "Ya kake ƙoƙarin tashi?" "E, zan tafi" "Tun yanzu?" "Akwai abinda nake son yi" "Kai dai baka son ka zauna saboda ka ga gidan nawa duk sai a hankali" "Aunty Sady kenan!" "Anyway, ka gaida min Auta, ita ce bamu haɗu ba" "Za taji insha Allahu" **** **** **** Yana shiga Mameey da Auta suka ɗago suna kallonsa. "Lafiya kuwa? Na ga ka shigo kamar wanda aka jefo" Zama ya yi a ɗaya daga cikin kujerun, ya ɗan dafe kansa kaɗan sannan ya ɗago. "Mameey dan Allah ki ɗan ragawa Aunty Sady, wallahi tana buƙatar mu, tana da damuwa" "Yaro kana ganin irin abinda take yi, ni wallahi bana tausayin Sadiya domin ita ta jefa kan ta a halin da take ciki" "Ƙaddararta ce a haka Mameey" "Yaro! Batun fa Aunty Sadiya da laifin ta, ko dangin mijinta ma kallon mai farar ƙafa suke mata amma ta nacewa Yazid" "Baki da kunya Auta, yanzu kin taɓa kiran sunan mijin Saddiqa babu kara?" "Ni fa dama tun can bai min ba, kuma a yanzu ma wallahi gani nake shi ne ya saka ta a baƙar rayuwar nan" "To dama waye, tun lokacin daya fara son ta, nake ƙoƙarin rabasu amma Sadiya taƙi ganewa, gani take kamar zan rabata da rayuwarta, tun lokacin daya sanar min shi malamin makaranta ne kuma albashinsa naira dubu talatin ne na san tabbas irin wannan ranar zata zo" "Mameey yanzu duk ba wannan ba, tunda aure dai ta riga tayi, kuma dole sai ta aure shi saboda Ihsan da Najma, amma dan Allah a duba lamarin ta" "Yaro me kake so a duba? Ta karɓi gadonta ta bashi yayi noma suka salwanta, 'yar uwarta ta bata kuɗi dan ta ja jari nan ma ta ba shi ya lalata su a banza, yanzu har gadonta ta sayar fa kuma still babu kuɗin, so me kuma zamu yi da ya wuce mu zuba masu ido" "A'a Mameey hannun ka baya taɓa ruɓewa ka yanke ka zubar" "Faruq kenan, wallahi idan ya isheka da azabar ciwo tuni zaka yanke shi" "Dan Allah Mameey ki taimaka, wallahi yanzu haka daga gidan nake, banɗakinsu ya rufta, sannan duka ɗakunansu zuba suke, ta ce min jiya ma sai a zaure suka kwana" "Anty Sadyn?" Cewar Auta "E ita fa" "Mameey..." "Surayya dan Allah ka da ki saka na yi abinda ban yi niyya ba" Tana gama faɗa ta miƙe ta bar parlorn. Surayya kallon Faruq ta yi ta ce "Yaro wai da gaske kake?" "Kin san ba zan yi ƙarya ba, kaɗan ya hana na yi wa Aunty Sady kuka" "Nawa ne zai isa a yi aikin gabaɗaya" "Zai ci kuɗi da yawa kin san rufi yana da tsada" "Banɗaki daya rufta shima fa zai ci kuɗi" "Wallahi kuwa" "Zan bayar da 20k sai a yiwa Aunty Saddiqa magana ma" "Amma a ina kika samu?" "Ka san Mameey tana bani 10k duk ƙarshen month, na transport da abinci, so dama ina da 15k a ajiye idan ta bani na this month gobe zuwa jibi sai na haɗa na bayar" "Amma kina ganin ke ba za ki takura ba?" "Yaro muddin muka bar Aunty Sady a haka mu za a zaga, muna gari ɗaya amma tana fama da rayuwa, ni da za a bani gado na da zan raba biyu ne na bata rabi" Murmushi ya yi, tare da faɗin "Lallai Auta kin fara hankali." Harara ta watsa masa tare da faɗin "Kai ma kayi hankali bare ni" Murmushi ya yi, dan baya da energyn yin faɗa a wannan lokaci. ****** ****** ****** Kyakkyawar mace, doguwa fara sol ta fito daga toilet, dogayen hannayenta suna kan doguwar fuskarta tana goge ruwan dake kan girarta, ta ƙarasa jikin drawer ta buɗe tare da ɗauko hijab, tana ƙoƙarin zurawa ta ji anyi knocking ƙofar, da sauri ta kai dubanta ga ƙofar sannan ta saka hannu a hankali tana laluben glass ɗinta, tana ɗauka ta saka sannan ta ƙarasa jikin ƙofar ta buɗe. "Ya dai?" "Mommy ta ce na sanar miki Yaya Affan ya farka" "What?" "Ehen! Ya farka kuma sunanki ya fara kira" "Muje na gan shi" Ta faɗa tana yin gaba, har ma ta wuce Lawisa da tazo kiranta, a parlour suka ci karo da Mommy. "Badriyya dama idanunki biyu amma kika zauna a ɗaki, bayan kin san Dr ya ce ki daina zama ke kaɗai" "Ance min Affan ya farka?" "E, amma ba za ki samu ganin shi a yanzu ba?" "Amma Mo...." "Ki bi umarnina kawai Badriyya" Ɗan lumshe idanunta ta yi, sannan ta buɗe ta diresu akan Mommy wadda taga ɓacin rai kwance saman fuskarta. "Har yanzu Affan bai dawo dai-dai, kuma daya farka sunan Nashwa ya kira, kuma ya buƙaci ya ganta, dan haka kafin ki ga Affan da buƙatar Dr ya fara ganinsa." "Nashwa!" Badriyya ta maimaita sannan ta samu kujera a daddafe ta zauna jin kanta yana sara mata, sai kuma tayi zubur ta miƙe tsaye tare da nufar gaban ƙatuwar plasma dake ajiye kan tv stand ta rage volume sannan ta tayar da sallah. Tana idarwa ta ɗaga hannayenta hawaye masu zafi suka kwanta saman fuskarta ta fara addu'o'in neman mafita a rayuwarsu, sannan ta shafa ta lalubi glass ɗinta ta mayar da shi fuska sannan ta miƙe tsaye, bata ga Mommy a parlour ba sai Lawisa da ta zabga uban tagumi a bisa rug dake shimfiɗe tsakiyar parlourn. "Aunty Badriyya" Lawisa ta furta tana kallonta, ita kuma bata ce komi ba, sai ido da ta bi Lawisa da shi. "Tabbas ya farka kuma da kunnena na ji ya ambaci sunanki ba Nashwa ba" "Lawisa baki ji daidai ba, amma ni na san idan sunana Affan ya kira, babu abinda zai hana Mommy ƙin bari na ganinsa" "To ko dai kunne na ne bai faɗa min daidai ba" Murmushin yaƙe Badriyya tayi lokacin kuma taji wasu siraran hawaye sun ƙara zubo mata. Zama tayi ɗaya daga cikin kujerun sannan ta ce "Tsayin watanni shidda kenan, ban fita ko ina sannan kuma ina gida ɗaya da Affan amma an hana na ganshi, Lawisa ya Affan ya koma?" "Aunty Badriyya Affan ya rame sosai, ya yi duhu, sannan kuma ya tara suma da yawa" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badriyya ta furta tana dafe fuska da hannu. "Yanzu duk gayu irin na Affan haka ya koma" "Ƙwarai Aunty, sai dai kuma...." Shigowar Mommy ne ya saka Lawisa ƙin ƙarasa maganar da take ƙoƙarin yi. "Badriyya!" "Na'am Mommy" Ta furta tana tasowa. "Zauna ma ba sai kin tashi ba" Mommy ta furta daga inda take tsaye kafin ta ƙaraso ta zauna kan kujera. "Tsawon watanni shidda kenan sai yau Allah ya tashi Affan, kuma Nashwa ya ce yana son gani bake ba, duk da kece a tare da shi a lokacin da wannan iftila'in ya same ku, amma meyasa ya nemi Nashwa?" Kallonta Badriyya ke yi sai dai ta rasa amsar da zata bata. "Badriyya anya babu haɗin bakin ki wurin kai Affan ƙasa?" Da sauri ta ɗago ta kalli Mommy hawaye tuni sun wanke mata fuska. "Mommy ko da zan kai kowa ƙasa ban da Affan" "Ta ya zan gaskata haka? Meyasa ya ambaci Nashwa bake ba?" "Ban sani ba" Ta furta tana sakin kukanta a fili. Sai lokacin Lawisa ta ce "Amma Mommy da bakina na ji ya ambaci sunan Aunty Ba...." "Dilla rufa min baki, ki bini a hankali Lawisa. Kin ci sa'a sosai dana barki kike ganin Affan" Tana gama faɗa ta tashi ta wuce ta barsu anan parlour. "Sai yaushe zan bar gidan nan? Sai yaushe zan ga ko da hasken rana ne Lawisa? Meyasa ba a kashe ni ba? Gabaɗaya an garƙame rayuwata a wannan sashe an kuma rufe ko ina, ko haske bana gani sai na lantarki" Dafe goshi ta yi tana sakin wani sabon kukan. Lawisa da sauri ta taso ta ƙaraso gabanta ta ce "Aunty Badriyya kiyi haƙuri, insha Allahu komai ya zo ƙarshe tunda Yaya Affan ya tashi" Riƙota Badriyya tayi tare da faɗin "Lawisa kin tabbatar Affan ne ba musaya aka yi ba?" "Aunty babu wanda ya yi musaya, kin san Affan tun fil'azal ɗan lelen Mommy ne, kuma ko bayan rasuwar Daddy Mommy tafi tausayawa Affan. Aunty na san Mommy ba za ta taɓa cutar da Affan ba, sai dai...." "Sai dai me?" "Babu komai" "Ki faɗa min gaskiya Lawisa, na san in har Affan ya rasu to tabbas ba za a barni a raye ba" "Rayuwarki ba a hannun kowa take ba" "Idan har haka ne a barni naje ga iyayena da kuma dangina meyasa aka ajiye ni anan?" Ajiyar zuciya Lawisa ta sauke sannan ta ce "Maganar gaskiya fitarki anan abu ne da zai matuƙar wahala muddin ba Affan bane ya tashi" "Meyasa?" "Saboda daga ke har Affan a idon duniya matattu ne tun ranar da kuka samu haɗari..." Ko maganar bata ƙarasa ba Badriyya ta sume a gurin. ***** ***** ***** Kallon shi take tun daya fara shan ruwan bai ajiye ba sai daya shanye tas, ta kalli kofin sannan ta ce "Gaskiya kasha rana Abban Najwa" "Sosai ma, kin ga dai jiya an kwana ana ruwa amma kin ga yanda rana ta ƙwalla har zuwa yanzu da yamma tayi." "Bara na kawo abinci, idan ka ci sai ka huta, sannan mu mayar da kayan ɗaki" Bata jira me zai faɗa ba kawai ta miƙe ta ɗauko masa abincin, ta dire masa a gabansa. "Yau dai Saddiqa ta aiko mana da awara mai yawa" "Yanzu nake shirin cewa ina kika samo awara" "Ita ta aiko Faruq ya kawo." "Yawwa Sadiya, kin ga dai bana nan kika fito da kayan nan kika yi aiki, dan haka yanzu haƙuri za kiyi ni na mayar ba tare da kin yi aiki ba, ki daina dan Allah kinji" "Yazid abu ne daya zama dole sai anyi" "To kin yi naki yanzu ki bari nayi nawa" "Wani aikin kayi fa, kuma sai na bari ka sake kama wani" "Ni na ce zan iya ai" Murmushi tayi sannan ta ce "Yanzu ya ake ciki game da gyaran banɗaki?" Shiru ya yi kafin ya ce "Sadiya ni kaina abin nan yana damuna wallahi, gaskiya sana'ar buga-buga ba ta mai iyali bace, kin ga dai yanda rayuwar ta zama a yanzu, sai muyi dakon ma ko mu sauke kaya amma sai a bamu dubu biyu, dubu uku" "To ko dai a faɗawa mai gidan? Sai nake ganin ai shi ne da alhakin gyarawa ba kai ba" "Wallahi ba zai yi ba, baki san zaluncin su ba, akan gyaran nan zai iya cewa mu bar masa gida, kuma in muka bari gyarawa zai yi ya saka wasu" Miƙewa tayi, ya yi tunanin ko ranta ne ya ɓaci, sai ya ga ta ɗauko wata leda ta dawo ta zauna. "Saddiqa ce ta aiko min da kaya wai na yi fitar suna, to ni ina naga kuɗin da zan ɗinka kayan ma, shi ne na ce bari na kawo maka kawai a sayar a saka rufi ko a ɗaki ɗaya ne, sai kuma a gyara banɗaki in za su isa, dan kayan gaskiya masu tsada ne sosai." "Sadiya ba zai yuwu ba, ki ɗinka kayanki ta gani ta ji daɗi" "Gaskiya ni nafi buƙatar gyaran nan fiye da ɗinka wannan kaya." "Duk da haka ki bari a samu wata mafitar dai, yanzu dai za a shigo a kwashe ƙasar kafin mu ga abinda Allah zai yi." Ba dan taso ba haka ta haƙura ta riƙe kayan. _Washe Gari_ Tana cikin shirya Najma ya fito, suka sakarwa juna murmushi. "Daddyn Najma ina kwana" "Lafiya lau Momyn Najma" "Har ta karya?" "E, da yake akwai sauran bread sai na ɗumama awara na haɗa mata ruwan lipton tasha" "Sugar a ina kika samu?" "Na bayar ta sayo ne, ai ka san jiya Faruq ya basu kuɗi so dasu nayi amfani" "To bari nazo na kaita ko" "To!" Ta faɗa tana goya mata school bag sannan ta ce Najma ban da wasa" Ta miƙa mata lunchbox ɗinta. Yana ƙoƙarin fita Umma ta doka sallama, abin ya basu mamaki sosai ganinta da sassafe ko ƙarfe takwas bata yi ba. "Umma lafiya kuwa?" Yazid ya tambaya yana kallonta da mamaki. "Oh sai babu lafiya za ka ganni a gidanka?" Murmushi ya yi, kafin ya sake magana Sadiya ta duƙa har ƙasa ta gaisheta, sai dai bata ko kalleta ba bare ta amsa gaisuwarta. Sai ma cewa Yazid ta yi "Ga kuɗi a samu a gyara banɗaki ayau, domin shi ba kamar ɗaki bane da zaku yi ta faman raɓe-raɓe in ana ruwan sama" Kallon kuɗin yake kafin ya ce "Umma a ina kika samo kuɗi masu yawa haka?" "Ka dai riƙe sai nayi maka bayani" Karɓar kuɗin ya yi yana kuma kallonta har a lokacin. "Tinkiyar ka dake ƙauye ita naje na sayar dan a samu a gyara inda ya ɓaci" Zaro idanuwa ya yi, ya kalleta sannan ya kalli Sadiya da har lokacin tana nan a ƙasa. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku

Chapter 2 of 15