Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ake yi Faruq bai san Sadiya na asibiti ba sai dare, kuma wurin 10:30 daya dawo Mameey ke sanar masa, a hakan ya dage sai yaje asibiti. A can ya kwana Mameey tausayinsa kawai take tana ganin son Sadiya kamar wata babbar ƙaddararsa ce tunda tare suka taso kuma bai taɓa faɗa ba sai a yanzu da har tayi aure ta hayayyafa. ********** "Gaskiya ban yi tunanin Sadiya bata so ba, a ƙa'ida babu yadda za ai mu aura mata wanda bata so, tana da 'yancin zaɓar mijin aure" Cewar Baffa, Faruq ya ji gabansa ya faɗi hanjin cikinsa sun kaɗa. Sadiya murmushi ta yi cikin jindaɗi ta ce "Baffa ina da wanda muka yi magana, idan ka bani dama zan ce su turo" "Malama sai ki bari ki gama warwarewa dududu jiya kika dawo daga asibiti" Ɗan zuɓurar baki tayi a lokacin da Mameey ke furucin. "Ki barta lafiya ai ta samu, Sadiya ki masa magana su turo zuwa jibi" "To Baffa" Ta furta tare da miƙewa, Faruq da ido kawai ya bita, Saddiqa kuwa sam bata ji daɗi ba amma ba zata iya cewa komai ba. Baffa ya gyara zama ya kalli Faruq "Ka yi haƙuri ka nemi wata, Sadiya ta fi ƙarfinka, ga Surayya ko kuma ka zaɓa a cikin 'ya'yan dangi" "Baffa ni ita nake so, kuma idan har kuka ce ba zaku bani ba zan kashe kaina ne" "Kisa? To shi kenan Allah yajiƙanka, ai mu bamu sangartaka ba, kuma ba zamu ɗauki rashin hankali ba" Cikin ɓacin rai Faruq ɗin ya tashi ya fita. ************ Kallon shi Umma take yana dire maganar ta ɗauke shi da mari, hannu ya saka ya kama kuncin, Maryam da Fatima kuwa dukkansu da mamaki suke kallon Umma. "Ashe kai mahaukaci ne ban sani ba? To ka gaggauta zuwa ka karɓo motar da ka mayar da duk wani abu idan ba haka ba wallahi sai na tsine maka" "Umma!" "Rufa min baki, ita matar da zaka aura kana tunanin ba zata riƙe yaranka ba? Ko kuma ni riƙon da nake musu bai maka ba?" Miƙewa ya yi tare da cewa "Umma duk riƙon da za ayi wa yaro ba kamar uwar data haife shi ba, Allah ya sani ina son Sadiya kuma ina ji a raina har abada ba zan samu madadinta ba" "Ni kuma na maka alqawarin duk ranar daka dawo da Sadiya to daga wannan rana sai dai ka canja wata uwar bani ba" Kallon Ihsan ya yi tana gefe ta yi shiru, duk yaran sun fita hayyacinsu, ga babu wata kula, kayanta sun yi datti sosai. "Maryam ki shirya su anjima zan kai su gurin Mamansu" "Babu inda za ka kaisu, idan ganinsu take son yi tazo nan ta gansu" Bai ƙara cewa komai ba ya saka kai ya fita. A ƙofar gidan ya zauna, ya rasa abinda ke masa daɗi, ya kuma rasa ta ina zai fara yiwa Sadiya bayani har ta fahimcesa, ga Lawisa ta addabeshi da kira, haka shago ma mutane sun dame shi duk da ya mayarwa duk wanda ya saka order kuɗinsa. Kai ya sunkuyar ƙasa, tare da riƙewa sosai. "Meyasa na aikata hakan a gareki?" Ya furta kamar zai yi kuka. Ya daɗe a zaune a gurin kafin ya janyo waya ya saka number Sadiya, sai dai har ta yi ringing ta katse bata ɗaga ba, ya sake kira a karo na biyu. Tana fitowa daga toilet ta ji wayar na ringing, da sauri ta ɗauka, tana ganin number gabanta ya faɗi, duk da ta goge amma lambar a kanta take, a sanyaye ta ɗaga tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum!" Yana jin muryarta ya sauke ajiyar zuciya. "Sadiya fatan kina lafiya" "Hmmm! Yazid lafiya kuwa?" Wani iri ya ji dan ya daɗe bai ji Sadiya ta kirashi da sunansa ba. "Lafiya lau, yaranki ne ke kewarki" "Uhm! Allah sarki, ina fatan suna lafiya?" Ta faɗa lokacin da ta ji wasu hawaye masu zafi sun zubo mata . "Lafiya lau sai dai ko yaushe sai sun tambayeki" "Meyasa ba zaka kawo min su na gansu ba?" Ta furta murya a karye. "Sadiya kuka kike?" Hannu ta saka ta rufe baki, "Dan Allah Sadiya ki daina" "Ina fatan yarana suna nan lafiya?" Ta sake maimaitawa. "Lafiya lau, amma yaushe za ki zo ki gansu? Ina so na kawo su amma Umma ta hana, kuma suna son ganinki" "Zan zo insha Allah, ka gaishe min dasu" Tana gama faɗa ta kashe tare da fashewa da kuka. *SAURA 1 PAGE MU GAMA FREE PAGES* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```Last🆓 Page 20``` "Sadiya kina ji na kuwa?" Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "E" "Sadiya idan babu damuwa ina son ganinki, akwai wata magana mai muhimmanci da nake so mu yi" "Gani na ba abu bane mai yuwuwa Yazid kawai ka yi haƙuri" Har za ta kashe ta ji ya ce "Ina so na faɗa miki dalilin daya saka na sake ki" Jin haka ya sa ta kalli wayar sannan ta ce "Idan har ka san ba wannan bane dalilin ganin kada ka saka na ɓata lokacina" "Wallahi shi ne Sadiya" "Shi kenan, zan yi tunanin inda zamu haɗu da yamma" "To babu damuwa Allah ya kaimu" "Amin." Tana ajiye wayar aka turo ƙofar. "Sarakan kuka, ke dai ba zaki bari ba" Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Na tuno su Najma ne" "Allah sarki, ni kaina kullum cikin tunanin su nake, last week ma naje na gano su, ban faɗa miki ba dan bana so na ɗaga miki hankali" "Surayya ya suke dan Allah?" "Alhamdulillah! Amma dai gaskiya suna cike da kewarki har yanzu basu manta ba" "Da raina amma an rabani da yarana" "Ki cire su a ranki dan Allah Aunty Sadiya" "Hakan ba mai yuwuwa bane, ba zan iya ba" "Za ki iya indai kika saka hakan a rai" Shiru babu wanda ya ƙara magana. "Aunty Sadiya yanzu nan da kwana huɗu kin zama mallakin Affan" "Kamar a mafarki ko?" "Sosai ma, ai na ɗauka Mameey za ta dage sai kin auri mai kuɗi, ko dan ashe Affan ɗinma masu kuɗi ne" Murmushi Sadiya ta yi. "Amma Faruq tausayi yake bani" "Tausayi kuma?" "E, baki ga ko zaman gidan baya yi" "Daga zarar na yi aure zai manta komai tunda zai koma karatu ma, Surry idan na auri Faruq ban masa adalci ba, a gaskiya so bai ma Faruq adalci ba daya saka masa ni a ransa" "To hakane, amma gaskiya yana bani tausayi wallahi ramar tsaye kawai yake" Murmushi Sadiya ta yi sannan ta ce "Ni kuma yarana kawai nake tausayi, ina so naje na gansu, amma bana son zuwa har sai bayan na yi aure" "Tabbas su Najma abin tausayi ne, amma still ba kamar Faruq ba" "Surayya kina son Faruq" "A baya ai ban fi ki son shi ba" "Har yanzu he's my number 1, amma ya kamata na taka masa burki dan ya san cewa ina gaba da shi." Shiru na ɗan wani lokaci ta yi kafin ta ce "Wallahi har yanzu mamaki nake sosai idan na tuna wai Faruq ya iya buɗe baki ya faɗawa Mameey yana sonki" "Ni kuma raina ne yake ɓaci, saboda Faruq nawa yake, nan fa nake fighting ma shi ke, ashe shi hangensa da ban ne" "Aikuwa dai da ban ne, shi Yayata ya gani" Murmushi ta yi sannan ta ce "Ina tunanin tausayina kawai yake, da kuma irin gwagwarmayar da nake fama da ita, amma kin san wani abu kuwa?" "Sai kin faɗa" "Idan har da gaske Faruq sona yake to lallai yana da matsala a ƙwaƙwalwa" Dariya Surayya tayi "Kai Aunty" "Allah dagaske nake?" "Yanzu ban ma sani ba, ko zai je wajen walima" "Bana jin zai je gaskiya, Faruq fa bacci kaɗai yake shigo da shi gidan nan" "Allah ya yaye masa" "Amin dai" "Anjima za ki rakani wani wuri" "Ina kenan?" "Ke dai zamu je" "To partyn fa?" "Ni fa babu wani party da zan yi yau, jibi in aka yi walima ta wadatar" "To Allah ya baku zaman lafiya Mrs Affan" Murmushi ta yi sannan ta cigaba da abinda take yi. ********** A ƙofar gidan napep ya sauke shi, jiki a sanyaye ya fita ya sallami mai napep yana ƙarewa gidan kallo. A haka dai ya ƙarasa bakin get ya ƙwanƙwasa. Maigadi ya fito ta ƙaramar ƙofa. "Sannu" "Yawwa, ko Affan yana ciki?" "E, bai daɗe da shigowa ba" "To in babu damuwa ka yi mini iso." "To ka ɗan shigo daga ciki, sai a kirawo shi" Bai musa ba ya shiga, ya kuma tsaya har maigadi yaje ya dawo. "Ya ce yana zuwa" "To nagode" "Haba karka damu" Yana nan tsaye Affan ya fito kuma tun daga nesa yake masa kallon mamaki har zuwa lokacin daya ƙaraso ya miƙa masa hannu duk da bai tunanin zai ba shi ba amma sai ya ba shi suka yi musabaha. "Mu ƙarasa ciki" "A'a nan ma ya isa" "Okay bara na ɗauko kujeru" maigadi ya saka ya kawo musu kujeru suka zauna. "Ina jinka, mene ke tafe da kai?" Shiru Faruq ya yi kafin ya ce "Alfarma na zo nema wajenka" "Alfarma?" "E" "To ina jinka?" Iska ya furzar sannan ya kalli Affan "Ina so ka yi min alfarma na auri Sadiya" Kallon mamaki yake bin sa da shi kafin ya ce "Ka san kuwa abinda kake faɗa?" "Na sani, dan Allah ka taimaka min, bana so Sadiya ta yi aure inda za ta wahala, ni kuma koda zan yi yawo da yagaggun kaya, ba zan bar Sadiya ta shiga wani yanayi ba" Hannu Affan ya saka ya dafa kafaɗar Faruq "Sadiya ba zata taɓa wulaƙanta ba, domin ina mata son da ko kai baka yi mata" "A'a, ka sani Sadiya jinina ce, kai kuma kana son ta ne kawai saboda kamar da take da tsohuwar budurwarka" "Wannan ba gaskiya bane" "Wallahi idan ban auri Sadiya ba ba zan taɓa samun sukuni ba, wallahi har mutuwa zan iya yi" "Nima haka nake ji a raina" Cije laɓɓa Faruq ya yi, sannan ya miƙe a fusace. ******** Tana zaune ta sake kallon Surayya da take shiri sannan ta kalli wayarta. "Surayya time yana ƙurewa dan Allah kiyi sauri, kin san idan 5 tayi ba lallai Mameey ta bari mu fita ba" "Yi haƙuri Aunty Sady, bari na ɗaura ɗankwalin" Ta faɗa tana ƙarasawa gaban madubi. Mameey da Umma Habiba da wasu baƙi biyu suna falo suna hira, tsakar gidan ma akwai tsirarrun mutane da suka fara zuwa saboda bikin. Faruq kai tsaye ya faɗo falon, Mameey ta kalleshi, dan gabaɗaya ya burkice. "Mameey Aunty Sadeey tana nan kuwa?" "E suna ciki amma suna shiryawa za su fita su karɓo ɗinki." Bai ce komai ba taga ya wuce kitchen, bai daɗe ba kuma ya fito ya yi ɗakin Sadiya da Surayya. Yana tura ƙofar suka juyo gabaɗaya, dan a tunaninsu Saddiqa ce saboda itace ta ce musu tana hanya. "Oh Faruq ka shigo kenan" Cewar Surayya. Ita kuma Sadiya tunda ta kalleshi sau ɗaya ta ɗauke kai. "Kin ce ba zaki aureni ba saboda na miki yaro? Kin kuma ce ni ba sa'an aurenki bane" Jin haka ya saka Sadiya ta kalleshi, sai data ɗan tsorata dan idanunsa sun zama jajir amma sai ta dake. "Kai Faruq ka shiga hankalinka, ni ba sa'arka bace, kodan ka ga babu wanda yake taka maka burki?" Murmushin yaƙe ya yi sannan ya ce "Mace bata taɓa fin ƙarfin namiji Aunty Sady, ki sani nana Khadija ta girmi manzon Allah amma kuma itace uwar 'ya'yanshi, sannan mu kuma muna koyi da shi dan haka ba zaki taɓa fin ƙarfina ba. Surayya ɗan lumshe ido ta yi sannan ta ce "Faruq ya kamata ka bar maganar nan tun da an riga an warware komai kum...." "Dalla malama rufa mini baki" Ya daka mata tsawa, kallon shi ta tsaya yi da mamaki. "Duk ba kune ke zuga ta ba, musamman ma ke sai na yi maganinki" "Ni kake yiwa tsawa?" "Na yi miki, ko haifa ta kikayi?" Za ta sake magana Sadiya ta yi saurin dakatar da ita. "Ki ƙyale shi kawai" Murmushin gefen leɓe ya yi sannan ya ce "Za ta ƙyaleni kam, kamar yadda na shirya ƙyaleku gabaɗaya" Yana gama faɗa ya ciro wuƙa, Surayya ta tsorata amma Sadiya ko a jikinta. "Zan kashe kaina ne, da naga aurenki da wani na, gara na bar duniya" "Ba zan hanaka ba, saboda ka san hukuncin wanda ya kashe kansa" "Faruq kada ka aikata haka dan Allah" Cewar Surayya. "Ki rabu da shi, tunda baya da hankali ya kashe kan nasa, ai da tuni sai ya kashe bama sai yazo gabana ba" "Hakan da kike ya ƙara tabbatar da baki sona, amma ki sani ni ina sonki har cikin raina, gara kawai na mutu dan ki samu kiyi rayuwa mai kyau" Yana gama faɗa da mamakinsu suka ga ya ɗaga wuƙar da ƙarfi ya sokawa cikinsa, Surayya ta ƙwalla mahaukacin ƙara yayinda Sadiya ta ƙame a tsaye idanuwanta gabaɗaya a waje. Cikin tashin hankali Mameey da Umma Habiba ke rige-rigen shigowa ɗakin, a lokacin kuma ya faɗi ƙasa Surayya taje gabansa shi kuma ya saka hannu yana ƙoƙarin zaro wuƙar Mameey ta riƙe hannun tare da fashewa da kuka, "Mene haka? Ya nake ganin wuƙa a cikin Faruq" Surayya kuka kawai take, lokacin idanunsa suna kanta amma da gani baya cikin hayyacinsa saboda jini kawai ke fita a cikinsa kafin daga bisani ya fara aman jinin. "Shi kenan mun shiga uku, Furuq duk wannan na mene?" Mameey ta furta tana kuka, Surayya ma kuka, Sadiya kuwa har lokacin ko motsayawa batayi ba daga inda take tsaye. Maƙocinsu da wasu samari biyu da sauri suka shigo aka fita da shi, duk cikin tashin hankali suke, sai da aka fita babar Rayyana ta kula da Sadiya a tsaye ƙiƙam ta zama shocked, ta ƙarasa gabanta . "Sadiya ki kwantar....." Ko gama faɗa batayi ba Sadiyar ta sume mata anan. _*Asibiti*_ Suna tsaye ƙofar emergency Surayya kuka kawai take, yayinda Saddiqa take zaune ta dafe kai, sun fi awa biyu a gurin kafin likita ya fito. "Dr ya jikin nasa?" Mameey ta tambaya cikin tsananin tashin hankali. "Ku kwantar da hankalinku, anyi nasarar fitar da wuƙar har an masa ɗinki, amma yanayinsa ya saka dole zamu tura shi ICU." "Shi kenan Faruq, innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Mameey ta furta tana fashewa da kuka. A hankali ta buɗe idanunta, sai kuma ta fara ganin abinda ya faru kamar mafarki ne ta yi. "Sannu" Jin haka ya saka ta yi saurin duban gurin, sai dai ganin maƙociyarsu ya saka ta miƙe zaune cikin tsananin tashin hankali ta ce "Kenan ba mafarki nake ba?" "Sad...." "Ina Mameey take, ina Faruq dan Allah kada ki ce min ya mutu" "Ki kwantar da hankalinki, Faruq sun tafi asibiti, kema tun ɗazu wayarki take ringing na ɗaga na faɗa baki da lafiya to mutumin ma har yazo" Ba ta ko kulata ba kawai ta miƙe da sauri taja mayafi ta fita. A ƙofar get ta ci karo da Affan. "Sadiya kin far...." "Affan na shiga uku, Faruq ya taɓawa kansa wuƙa wai saboda ni" Sai kuma ta fashe da kuka tare da jingina kanta jikin motarsa. Sai da tayi kuka sosai sannan ta ɗago jajayen idanunta ta kalleshi. "Sadiya kar mutane su gane halin da kike ciki dan Allah ki shiga mota." Bata musa ba, ta buɗe ta shiga tare da kwantawa jikin kujera, shima shiga ya yi, ya kunna motar tare da kunna AC. "Meyasa Faruq ya yi haka?" "Ni kaina har yanzu da kike faɗa mini ban gaskata ba." "Wai saboda zan aureka shi ne ya ce gara ya mutu ya bar mini duniya." "Yanzu yana ina?" "Asibiti, ban ma san a wane asibiti suke ba, dan Allah ka kira Surayya ta faɗa maka sai ka kaini." "Ok, amma ina so ki kwantar da hankalinki please." Surayya ya kira ta faɗa masa asibitin da suke ya ɗauki Sadiya suka tafi. A tsorace ta ƙarasa inda ta hango su Mameey zaune, sai dai tana zuwa Mameey ta miƙe tsaye tare da faɗin "Mene ya kawo ki nan?" "Mameey....." "Sadiya ko nan ma zuwa kika yi ki ƙarasa shi?" Kuka ta saki. "Ki tafi daga mu har Faruq babu mai buƙatar daganinki, dan Allah ki bar wajen nan." Babu wanda bai bawa Mameey haƙuri ba har Affan amma haka ta rufe ido gani take kamar ma Sadiya ce ta soka masa wuƙar. A mota kuka kawai take Affan dai ya zuge glasses ya kunna AC, shima shiru ya yi yana nazari, sai da tayi kuka mai yawan gaske sannan ta share hawayenta. "Affan...!" Ta ambaci sunanshi da dasasshiyar murya. "Sadiya karki ce komai a yanzu, kiyi haƙuri ki kuma kwantar da hankalinki insha Allah komai zai daidaita. Ajiyar zuciya ta sauke tare da riƙe ƙirjinta da taji ya mata nauyi sosai. "Ka mayar dani gida" Bai musa mata ba, yaja motar suka koma, sai dai bai ma ƙarasa ba Saddiqa ta kira shi ta ce masa kar ya bar gurin Sadiya har sai tazo dan gudun kar ta aikata wani abun. A ƙofar gidan ya parker mota ya kunna karatun al-qur'ani sannan ya kwantar da bayansa jikin kujera gami da lumshe ido. "Sadiya ki riƙa istigfari" Kai kawai ta gyaɗa masa, a haka har Saddiqa ta zo sannan tayi masa godiya taja Sadiya suka shiga ciki. "Aunty dan Allah kina ganin Faruq zai tashi? Bana so Faruq ya mutu Allah ya saka shi a wuta." "Muna saka rai insha Allah zai tashi, amma for now yana ICU" "Mameey ma ta kasa fahimtata, Aunty ba zan iya zaman aure da Faruq ba ganinsa nake a matsayin ƙani na, ban san ta ina zan fara yi masa biyayya a matsayin miji ba" "Sadiya ki kwantar da hankalinki, dukkanmu mun fahimceki, ita kanta Mameey ruɗewa ce ta saka tayi haka" Sosai Saddiqa ta rarrasheta, ranar ma tare suka kwana, su Mameey dai basu dawo daga asibiti ba duk da Faruq ɗin a ICU yake. _Ranar Juma'a_ *04:00pm* Tana kwance akan gado, idanuwanta suna kallon POP ɗin ɗakin, jin an turo ƙofa ne ya saka ta kai dubanta ga ƙofar ganin Saddiqa ya saka ta miƙe zaune a hankali. "Aunty ya jikin Faruq ɗin?" "Da sauƙi" "An fito da shi daga ICU ɗin?" "A'a amma dai yana ta samun sauƙi" "Aunty dan Allah ki bawa Mameey haƙuri ta bani damar naje na dubashi." "Za kije amma kafin nan dai taso muje Baffa na kira" "Baffa?" "E, ke amarya ce Sadiya" "Amaryar wa? Kenan ba a ɗaga bikin ba? Kuma ina ta kiran Affan tun safe wayarshi bata shiga" "Ki dai zo muje" Hannunta Saddiqa taja a lokacin kuma hawaye ya sake zubo mata. A parlour ta ga Baffa da ƙanensa sai wasu mutane biyu da bata sansu ba, zama tayi a ƙasa Saddiqa ta zauna kusa da ita. "Sadiya!" "Na'am" Ta amsa a sanyaye. "Karɓi wannan" Ɗagowa tayi ta kalli Baffa taga ya miƙo mata bandir biyu na kuɗi. "Wannan sadakin ki ne, dubu ɗari biyu, yanda aka saka bikinki ba'a ɗaga ranar ba, mun ɗaura aure kuma a yanzu girma ya ƙara hawa kanki, a yanzu ke matar aurece, matar...............! *Wa kuke tunanin Sadiya ta aura?* *Affan ko Faruq? Ko kuma wani ne da ban?* *Amsoshinku suna cikin Book2, ku biya ₦500 kacal domin cigaba da karanta littafin *WUTAR ƘAIƘAYI* *VIP ɗin littafin ₦1000 ne, sannan idan ya zama Complete a ₦1000 za a sayar da documents* _Mu kasance daku a fagen cigaba ga wanda suka biya kuɗaɗensu ta asusun dake ƙasa👇_ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 15 of 15