Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wannan lamarin, itama Sadiya har gida aka je aka mata duka, kuma 'yan uwanta na zargin Fatima da Maryam ne, ga ta a asibiti" "Ok so kake ka faɗa min cewa ba zaka iya rabuwa da karuwar yarinyar nan ba" Ɗan lumshe ido ya yi, dan har cikin ransa sai daya ji wani iri da aka kira Sadiya da wannan suna. "Umm...." "Dakata Yazid wallahi a wannan gaɓar zan iya yin fito na fito da kai idan baka rabu da wannan yarinyar ba." "Umma zan rabu da ita amma dan Allah ki bari sai ta samu sauƙi" "Shi kenan Allah ya kaimu." Da ƙyar ya iya cewa "Amin." Yana fita kai tsaye gidan wan mahaifinsa ya nufa, wanda shi ne waliyyinsa a lokacin bikinsa da Sadiya. Ko daya je a ƙofar gida ya same shi da almajiransa. Bayan sun gaisa ya ce masa ya shiga ya gaisa da 'yan gida. Tunda ya kalli yanayinsa ya san akwai matsala dan haka yana shiga ya miƙe ya bi bayansa. Suna zaune a zaure Yazid ya zayyana masa duk irin abubuwan da suke faruwa. "Assha! Garin ya duk haka ta faru amma ba ka zo ka sanar dani ba Yazid?" "Baffa na ɗauka zan iya kashe wutar amma abin ya ci tura" "Subhanalillahi, yanzu ya jikin nata?" "Da sauƙi tunda jiya ma har tana iya cin abinci da kanta" "To Allah ya bata lafiya yasa kaffara ne, kuma insha Allah da yamma zan je na samu mahaifiyar taka, daga nan kuma zan yi ƙoƙari naje asibiti na dubata" Kai Yazid ya gyaɗa. "Dan Allah irin haka ta faru a riƙa sanar mini da wuri" "To Baffa insha Allah" Baffa da yamma kuwa ya samu Umma kamar dai yadda ya alƙawaranta kuma ya zaunar dasu tare da Yazid da ƙannen nasa. Dukkansu babu wanda ke fara'a dan sun tabbatar zuwansa ba zai zama alheri ba. "Kenan ƙarana ka kai gurinsa?" Umma ta yi maganar rai a ɓace tana kallon Yazid. "Ai ya isa ya kawo ƙarar saboda ni mai faɗa ne aji a gidan nan tun da ni wan mijinki ne" "Hmmm!" Ta sauke numfashi tana ƙara haɗe rai. Kallon Fatima da Maryam ya yi ya ce "A cikinku wace ce taje ta daki matarsa." "Baffa ƙarya take saboda mu bamu zuwa gidan sa ba dan babu abin da zamu tsinta a gidan" Maryam tayi magana rai ɓace. Hannu ya watsa mata sannan ya ce "Kin ci gidanku, gidan ɗan uwanki kike cewa babu abinda za ki tsinta" Baki ta turo bata sake cewa komai ba. "Wannan ba daidai bane, duk irin abubuwan da kuke ina sane ƙyalewa kawai na yi amma lokaci ya yi da zan ɗauki mataki akan hakan" "Baffa abubuwan sun fara yawa ita...." "Idan kika sake magana sai ranki yayi mummunan ɓaci. Ku bar yaro ya samu nutsuwa da iyalinsa." Sai lokacin Umma ta sake cewa "Ba zai yuwu mu bar yarinya tana abin da take so, dan haka dole ne ya rabu da ita ko kuma ya ƙara aure." "Idan ya ƙara auren kina ganin wadda za a kawo muku alheri zata haifar ko kuwa idan ya saki matarsa kina ganin shi ne sauƙi ko kuma jindaɗinku, mene ribarki akan haka?" "Ni kaɗai na san irin abubuwan da nake fuskanta, dan haka ni dai na ba shi zaɓi." Duk yadda Baffa yaso ya nusar da su amma suka kasa fahimta haka ya haƙura ya tafi ya ƙyalesu da mummunan ƙudurinsu. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [6/19, 8:47 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty_ _Facebook@SaNaz Deeyah_ _Tiktok@Habibtyn Habibi👸💍🦋_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 10``` Cikin nutsuwa ya fito daga mota yana ƙarewa farfajiyar gidan kallo, ko ina ya ƙayatu da flowers, ga kuma wani guri gefe guda anyi rumfar shaƙatawa. "Barka da zuwa" Ya ji siririyar murya ta sauka a dodon kunnensa, da sauri ya juya ya kai dubansa gareta. Murmushi ta yi masa sannan ta ce "Sannu da zuwa" "Yawwa" Ya furta a taƙaice. "Bismilla ka shigo" Da ido ya bita sannan ya motsa, tana gaba yana biye da ita har suka ƙarasa katafaren falon da ya gaji da haɗuwa. Kujera ta nuna masa tare da faɗin "Bari a kira Anni ɗin" "Ok" Ya furta a taƙaice tare da zama, ita kuma ta bi wata slicing door ta wuce. Ta ɗan juma a ciki sai kuma ta fito hannunta ɗauke da ƙaton tray da drinks akai sai wasu bowls ɗauke da dambun nawa ɗayan kuma cin-cin ne. Kan center table ta ajiye sannan ta ja table ɗin gabansa. "Bismilla ka taɓa kafin a kawo abinci" "Thank you" "Never mind" Ta furta tana zama a kujerar dake gefe. "Kai ne Affan Ahmad Giwa?" Murmushi ya yi yana gyaɗa kansa alamar eh. "Tun jiya Anni take faɗa mana zuwanka, barka da zuwa." "Barka dai" "Amma your face looks familiar kamar na sanka somewhere" Fitowar Haj. Bilkisu ne ya dakatar da ita, ta miƙe tsaye, ganin haka ya saka Affan miƙewa shima. Kamar bata son taka ƙasa haka take tafiya har zuwa lokacin da ta samu kujera ta zauna, Affan ya kai gwiwoyinsa ƙasa tare da gaisheta. "Affan bismillah koma kan kujera ka zauna." Zama ya yi amma ya kasa ɗago kai, gabaɗaya ji ya yi tana masa kwarjini. "Ina Farhan ne?" "Tana ɗakinta" "Kirawo ta, kice ta fito ina son ganinta" Tana knocking ta murɗa handle bata jira an mata iso ba, Farhan na kwance a gado tana kallo a system Ayda ta rungumeta "He's cute kuma handsome ne, wallahi kun dace da juna sosai." Ayda ta faɗa cike da murna. "To don't break my legs kin ga ɗagani tukun." Murmushi ta yi sannan ta ɗagata ita kuma ta gyara zama. "Har ya ƙaraso kenan." "Yeah yana parlour, kin gan shi kuwa? Wallah top class ne." "Ki daina zaƙewa da yawa saboda kin san halin yaran masu kuɗi yanzu sai ya ce kece kika masa." "Haba dai, ni ai ina da Nasir ba zan ma Nasir butulci ba amma maganar gaskiya Affan ya haɗu kuma na san ke zai zaɓa ma, kin san yaran masu kuɗi akwai son farar fata" Ta ƙarasa faɗa tana dariya, sai kuma ta saka hannu ta dafa kafaɗarta tare da cewa "Be calm, ai tun kafin yazo na ce inya miki kawai ki amsa" "Ya yi min 100/100" Murmushi Ayda ta yi tare da cewa tun ma kafin ki gan shi?" "E mana, ai na san ki kin san high and low class tun da kika ce ya yi to yes na yarda, kin ga muje dai kar Anni ta fara faɗa." Miƙewa suka yi cikin fara'a suka fita, sai dai suna fita Farhan ta haɗe rai, "Anni barka da gida" Ta faɗa tare da zama. Farhan ita ce babba tana da shekaru 23 fara ce sol dan farin ta har ɗaukar ido yake, tana da kyau daidai misali, dan tana da sexy eyes ɗin da sune suke ƙara mata kyau, ta yi karatun ta har matakinn master a ƙasar china inda yanzu take aiki da wani company na sufuri. Yayinda Ayda ta kasance ruwan tarwaɗa, sai dai kuma fannin kyau Ayda ta fi Farhan kyau, saboda ita yanayinta ya yi kama da shuwa arab ga kuma ɗan duhun fata da take da shi, shi ne ya ƙara fito da kyawun na ta, tana da manyan idanu, dogon hanci da ƙaramin baki, itama a U.S ta yi karatunta har matakin degree, sai dai yanzu tana masters anan B.U.K tana da iyeyi sai dai bata da wulaƙanta mutum dan ko baƙi a gidan itace mai tarba. "Baki gaishe da Affan ba ko baki gan shi ba ne" Ɗan ɗago kai ta yi ta kalleshi a ranta ta furta _Wow_ a fili kuma a yatsine ta ce "Ina wuni" Kamar kar ya amsa haka ya ji, amma ya daure ya ce "Lafiya lau." Haj. Bilkisu ta yi murmushi tare da cewa "Affan wannan sune ƙannen naka, wannan ita ce Farida muna kiranda da Farhan ita kuma wannan ita ce Aisha muna kiranta da Ayda. Farhan ta gama karatu a yanzu haka aiki take, ita kuma Ayda tana kan karatun dan shekara ta ƙarshe take a masters, project take ta fama da shi a yanzu." Murmushi ya yi sannan ya kallesu "Allah ya taimaka." "Amin" Ayda ta amsa. Haj. Bilkisu ta ce "Shi kuma Affan dama na yi muku bayani akan sa ko? Kun san waye shi da komai na faɗa muku jiya" "E Anni mun sani." Cewar Ayda ita kuwa Farhan sai ƙara shan ƙamshi take. "Bari na barku da shi sai ku samu tattaunawa kuna 'yan uwa amma babu zumunci ko, Affan ai kamata ya yi ku taho da Lawisa" Murmushi ya sake yi sannan ya ce "Ta je aiki amma next time insha Allah" "To babu damuwa." Suna ta hira da Ayda yayinda Farhan tana ji amma ta yi pretending tana danna waya ita a dole sai ta ja ajinta. Anan ya bawa Ayda labarin Nashwa da dalilin ajiye aikinsa sai dai yanzu ya samu lecturing a northwest university. "I wish a B.U.K ne, ka ga na san zamu riƙa haɗuwa" "Yeah da a B.U.K so shi bai samu ba" "Eyyah! Ban ji daɗi ba." Sai lokacin Farhat ta ɗago suka haɗa ido da Ayda ta ɗan ƙyafta mata ido. "Farhan muna ta hira kin yi shiru" "Yeah am busy doing something, kuma it's very important so kin ga ba zan tsaya hira ba" Murmushi Affan ya yi dan ya san ɗagawa ne take wanda in jan aji ne da ɗaga kai bata kai shi ba, amma tun lokacin daya auri Badriyya ya watsar da makaman yaƙi, bala'i da baƙin kishinta sai da suka canja masa rayuwa. Da zai tafi kuwa tun a parlourn ya karɓi number Ayda, Farhan na jira ya ce mata ta bashi ta ta saboda ta ji ya ce zai karɓi number dan a ƙara sabawa da juna amma sai kawai gani ta yi ya miƙe, abin ya sosa mata rai. "Bari na kira Anni sai ku yi sallama" Cewar Ayda, da ta tafi sai kuma Farhan ta fara kallonsa a sace, yana gani ya basar, Haj. Bilkisu ta fito ta yi masa godiya sannan ya wuce Ayda ta masa rakiya har jikin mota. "Ke ban gane ba, wai naga yana ta wani nan-nan dake kuma ya karɓi numberki" Farhan ta yi maganar lokacin da Ayda ta dawo daga rakiyarsa. "To ai kece kika tsaya kina wani jan aji, shiyasa na ƙyaleki haba ai bai kamata ba, haka za ayi soyayya har ta kai ku ga aure?" "Ni fa ba jan aji na yi ba, gani na yi bai min magana ba shiyasa nima na basar" "Ni magana ya yi min, ai shi ne baƙonmu mu zamu fara masa magana sannan ya saki jiki damu" "To na ji na yi kuskure mene abin yi?" "Idan ya kirani zan haɗaku ku yi magana, kin ga daga nan sai na tura masa numberki shi kenan" "To babu damuwa." ******* ******* Sai da suka gama fita da kayan kaf sannan suka dawo, Sadiya ta sauka daga gadon, Saddiqa ta kama hannunta suka fita. Mota ƙirar Peugeot 206 ta gani baƙa Yazid na tsaye jikin motar. Suna ƙarasawa ya buɗe mata baya ta shiga ita da Saddiqa shi kuma tare da Surayya suna gaban mota. Ganin Yazid yana jan motar abin ya ƙara bata mamaki sai dai bata bar mamaki ba sai da ta gansu a wata unguwa da ban ƙofar wani gate ash, suna fitowa ta tsaya. "Sadiya muje mana" "Aunty ina ne nan?" "Gidanki ne." Kallon Yazid tayi sannan ta kalli Saddiqa. "Ban gane ba?" "Mu shiga ciki duk daga baya za ki ji komai. Shiga suka yi, madaidaicin tsakar gida ya sha tarazo sai flowers ƙananu daga gefe, sai ƙofar parlour, safe content mai ɗakuna biyu da dinning area sai kitchen da store, ko wane ɗaki akwai toilet a ciki sai kuma wani extra toilet a tsakar gidan. Kai tsaye ɗaya daga cikin ɗakunan suka shiga ta kwanta kan gado tare da lumshe ido. "Surayya ki shiga kitchen a dafa mata ruwan tea da ko indomie ce" Miƙewa Surayya tayi ta fita. Sadiya ta miƙe zaune tare da kallon Saddiqa "Aunty dan Allah ki faɗa min ina ne nan, na san dai gidanki yafi wannan girma bare na ce sabon gida kika koma." "Sadiya gidan ki ne wannan" "Gidana!" Ta furta da mamaki tana ƙara kallon ɗakin. "E, ki godewa Allah Sadiya, Allah ya muku arziƙi kuma zaku fantama, ko wannan motar da kika gani tashi ce, ai ku kam noma ta muka rana." "Wai har an sayar da attarhun?" "Hmmm! Ai Sadiya tarhu ya yi albarka, kina asibiti ya kirani ya faɗa min ya sayar da attarhunsa ya saya muku gida, ni da shi ne muka zaɓo furniture muka kuma kwaso kayanki saboda ya ce daga asibiti so yake ya yi surprising ɗinki da gidan nan" Murmushi ta yi tare da faɗin "Allah sarki Yazid, Allah ya ƙara masa buɗi na alkhairi" "Amin Sadiya." Sai da yamma lis sannan suka tafi lokacin kuma Yazid ya ɗauko yaran daga wurin Mameey. Suna zaune da yaran a parlour an kunna musu cartoon ita kuma tana kwance kan three seater sai ga shi ya dawo gidan. A hannun kujerar da take kwance ya tsaya tare da faɗin "Ya jikin naki?" Ɗan murmushi tayi sannan ta ce "Da sauƙi" Sai kuma ta miƙe zaune "Abban yara wannan gida har haka na yi mamaki sosai" "Ko dai bai miki ba?" "Ya yi min amma yanzu har abin ya kaimu ga wannan gida?" "Sadiya wannan ai ba wani babban gida bane rabin ploti ne kawai dai tsarin ginin ne ya yi kyau, a gine na saya na kuma sayi mota" "Alhamdulillah" Ta furta tana goge hawaye. "To mene na kuka? Kin ga ki kwantar da hankalinki, yanzu dai ki faɗa min me kike so a saya miki da dukiyar nan da muka samu" "Abban yara kenan, ai ni kam ba sai ka sayi komai ba, fatana kawai ka gina rayuwarmu kuma Allah ya baka ikon amfani da dukiyar ta hanyar halak" "Amin Mommyn yara kuma ina mai ƙara miki godiya domin arziƙin nan namu ne baki ɗaya, kin taimaka da harshenki wajen ƙarfafa min gwiwa da kuma ƙarfinki wurin bayar da gudunmawa wanda zan iya cewa wannan noman ku san rabin kuɗinki ne aka yi amfani da su." "Kai daina faɗar haka Abban yara, kuɗina ai naka ne" "Haka ne, Allah ya miki albarka" "Amin ya rabbi." Washe gari tare suka je suka kai Najma wata private school aka mata register, Sadiya mamaki kawai take ganin 100k ne school fees, Najma da take government school amma sai gata a private school mai kyau. A hanya suna dawowa Sadiya ta kallesa ta ce "Abban yara amma kana ganin zaka iya affording school fees ɗin nan, sai nake ga kamar ya yi yawa" "Bai yi ba, zan iya insha Allahu, kuma ai ba haka zan zauna ba zan fara kasuwanci ne baki san har na bayar ayi min cigiyar shago a kwari ba, ke kuma na kama miki shago anan zooroad" "Kwari da zooroad kuma? Ban gane ba" "Na bayar da order zan fara sayar da shaddoji da yadika, huluna na maza da dai sauransu, ke kuma shagon zan zuba miki shoes and bags ba dai ke zaki zauna ba zamu samu wanda za su zauna sai dai kuɗin dai asusunki zai riƙa zuwa, domin ke za ki riƙa controlling komai." Ɗan zaro ido ta yi sannan ta ce "Abban yara ni kam gaskiya a'a ban yarda da wannan ba, ka dai riƙe shago ka haɗa mana kuɗaɗe ka ƙara bunƙasamu, ni abu ɗaya nake buri a yanzu" "Me kenan?" "Karatu nake so na koma" "Karatu?" Ya maimaita. "E, dan Allah ka barni" Ta furta da shagwaɓa. "To shi kenan zan yi tunani akai." Ɗan turo baki ta yi. Ranar bai fita ko ina ba tun bayan fitar da sukayi sai ɗauko Najma da ya yi daga school tun bayan nan bai ƙara fita ba, dan sallah ma a gida ya yi azhar da la'asar, sai da magrib ya fito da shiri, tana kitchen tana kwashe tuwo da ta gama tuwon semovita miyar agushi, "Ashe kina nan" "E, kamar fita za kayi ko?" "Fita zan yi, maybe sai bayan isha'i zan dawo" "Abinci fa?" "E, idan na dawo zan ci, ki duba mirrow drawer na ajiye miki saƙo" "To shi kenan, a dawo lafiya" "Allah yasa" "Amin ya rabbi." Sai da ta shirya kayan a dinning area ta zubawa yaran abinci sannan ta shiga ta yi wanka, ta saka kayan bacci silk riga da wando, ta fesa turare sannan ta janyo drawer, tana ganin takarda gabanta ya faɗi, jiki a sanyaye ta ware, sentence na farko da ta karanta ya ɗaga mata hankali tana shirin miƙewa ta zame ta faɗi. Sai da ta ɗan saki ƙara sannan ta cije laɓɓanta, ta sake kallon takardar da take kallonta a matsayin baƙar takarda sannan ta sake fara karanto rubutun da aka yi da manya baƙi kamar haka. _NI YAZID USMAN NA SAKI MATATA SADIYA BELLO SAKI ƊAYA(1) IDAN TA SAMU MIJI TA YI AURE._ Ji tayi ko ina yana juya mata, sai kuma ta miƙe tsaye ta haɗe takardar. "Saki? To laifin me na yi dana cancanci saki?" Wani ƙarfi ta ji yazo mata, da sauri sannan ta janyo akwatin da ta gani ajiye wanda Saddiqa ta ce mata da shi suka kwaso kayanta. Kayan ta haɗa tare dana Najma da Ihsan sannan ta fita parlour, a lokacin Ihsan har ta yi bacci saboda tara na dare ta wuce, Najma ce dai tana zaune tana kallo da yake har solar ya saka musu. Zane ta ɗauko duk girman Ihsan shekara uku amma haka ta goyeta da zane ta ce Najma ta taso su tafi. Da ta rufe gidan kuwa key ɗin ta wulla ta saman get dan ta san yana da extra, sannan ta wuce tana jan akwati Najma na biye da ita har titi, basu daɗe a tsaye ba suka samu Napep kai tsaye ta ce a kaita Sultan Road, kwatance ta yi masa har ƙofar gidan Saddiqa basu yi ciniki ba shiyasa ya cajeta har ₦4000 haka ta ɗauka ta ba shi sannan ta doshi get ɗin gidan, tana knocking maigadi ya ce "Waye" "Sadiya ce" Ta furta a taƙaice, ya buɗe mata ƙaramar ƙofar tare da yi mata barka da zuwa, shi ya karɓi trolley ɗin ita kuma ta kama hannun Najma suka shiga cikin gidan. "Sadiya kuma?" Saddiqa ta faɗa lokacin da maigadi ya shigo da akwatin, sai dai kafin ya bayar da amsa kukan Sadiyar ne ya mata sallama, da sauri ta miƙe ta fita, a daidai lobby ta zauna tana kukan ga kuma Ihsan ta farka. "Sadiya lafiya?" Bata ba ta amsa ba sai kuka da ta cigaba da rerawa. Saddiqa ta kunce mata goyon sannan ta ɗauki Ihsan ta ja hannun Najma suka shiga ciki ta kwantar da Ihsan kan kujera ta kuma dawo taja hannun Sadiya. Tsawon awa guda ta yi tana kuka da babu tsayawa kafin daga bisani ta fara shashsheƙa. "Sadiya mene ke faruwa?" Miƙewa ta yi ta buɗe saman trolley ta janyo takardar ta miƙa mata, karɓa ta yi ta ware ta fara karantawa. "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ta furta har sau uku sannan ta dafe goshi, ta daɗe bata sauke hannu ba, sai daga baya ta janye tare da kallon Sadiya har lokacin ta kan goge hawaye. "Sadiya mene ya faru har Yazid ya aikata ɗanyen aiki haka?" "Ban sani ba, lafiya lau muke da shi, kuma yau babu inda ya fita sai magrib da zai fita ya ce ya ajiye min saƙo ashe wannan baƙar wasiƙar ce" Sai kuma ta sake fashewa da kuka, da sauri Saddiqa ta sauka tana share mata "Ki daina zubar da hawayenki, bari na kira Yazid ɗin naji" Da sauri ta ɗauki wayarta ta yi dialing number ɗinsa, sai dai cikin rashin sa'a a kashe ta sameta. "Tabbas ya san za a kirasa shiyasa ya kashe waya." "Tun akan wannan case ɗin ne, dama Umman shi ai bata ƙaunata, kuma har 'yan uwansa sun ci alwashin rabamu, na san shi ne dalilin, na san Yazid ya sake ni ne ba a son ransa ba" "Sadiya ni ban ɗauki wannan a matsayin hujja ba, kin sadaukar da komai ciki har da farin cikinki dan kawai ki daɗaɗa masa amma shi ya kasa ɗauke damuwar 'yan uwan shi saboda ya faranta miki, sai lokacin da wahalarku ta yanke sannan zai ce ki tafi gida, ke da shan wahala wata banza da morar daɗin." Hannu Sadiya ta saka ta sake goge hawaye ta ce "Nima na yi wannan tunanin lokacin ina tahowa nan, amma a raina ina jin cewa ba laifinsa bane, cikin ƙannensa da mahaifiyarsa dole a samu wanda ya raba auren" "Ƙannensa ɗin banza, kima bar maganar nan, Sadiya ki share hawayenki kawai, amma dole ne Yazid ya faɗa min dalilinsa na sakin ki, kuma dole ya mayar dake dan ko Mameey ba zamu bari ta san kun rabu ba, ko bai ɗaga wayata ba zan bi shi gida ne, muje mu kwantar da yaran kema kiyi bacci." Ranar Sadiya da Saddiqa duk babu wanda ya runtsa, dan dai ba ɗaki ɗaya suka kwana ba, ita tana tare da mijinta, kuma bata faɗa masa gaskiyar abin da yake faruwa ba, kawai dai ta ce masa Yazid da Sadiya sun samu matsala shi ne Sadiya ta taho gidanta, kuma ita take son ta gyara komai basu so Mameey ta sani. "Kin yi daidai haka ake so babba ya kasance, amma mene ya haɗa Sadiya da Yazid har haka, gaskiya a bincika dan na san Sadiya macece mai kawaici" "Wallahi kuwa kai da ka san halin naku na maza, duk amincin da mace za ta muku sai kun kai ta maƙura" Murmushi ya yi tare da faɗin "Kullum burinki shi ne ki ɓata mu" "Gaskiya nake faɗa, saboda kai ma babu yadda ban yi muje asibiti ba amma kaƙi" "Inje asibiti su yi min me? Saddiqa na sha faɗa miki ki kwantar da hankalinki indai haihuwa ce akwai wanda suka fimu daɗewa kuma daga baya sun samu haihuwa muma mu haƙura mu gani, aurenmu fa ko shekara goma bai yi ba" "Amma a waɗan da suka fimu daɗewa ka samu labarin wanda suka zauna basu nema ba kawai suna jira, Allah ma fa cewa ya yi tashi in taimakeka." "To addu'a bata wadatar ba? Kin ga Saddiqa na kwaso gajiya dan Allah kar ki ɓata min rai, ni dai asibiti ba zanje ba ai yi ta min wasu gwaje-gwaje mararsa ma'ana" "Ai shi ke nan" Ta faɗa tana saka hannu a haɓa. ****** ****** Jiki a sanyaye ta karɓi wayar daga hannun Ammi tare da karawa a kunne. "Badriyya!" Jin muryar Affan ta dira a dodon kunnenta ya saka tayi saurin miƙewa ta bar ɗakin, hannu ta saka a baki tana son hana hawayenta zuba amma ta kasa. "Kina ji na kuwa?" "Affan dama za ka nemeni?" Ta yi maganar da muryar kuka kuma lokacin hawayen har sun zubo. "Dole na nemeki Badriyya saboda har yanzu akwai igiyar aurena a kanki" "Affan dan Allah ka yi haƙuri dani, duk wasu abubuwa dana aikata kishinka ne da tsananin soyayyarka suka ja min, amma dana ji labarin rasuwar Nashwa hankalina ya tashi kuma na ji a raina ban kyauta ba, musamman haɗuwarmu ta ƙarshe da ta kasance faɗa har da zage-zage, har yau ina dana sani." "Haka Allah ya shirya, karki damu, dama na kira ne dan na sanar miki saƙon da iyayenki suke so na baki" "Wane saƙo, Affan dan Allah kar kace zaka rabu dani" "Badriyya iyayenki sun matsa akan sai na sakeki, sun ce ko ban sake ki ba su da kansu za su kai ƙara kotu a raba aurenmu" Hannu ta saka ta rufe baki tana shashsheƙar kuka. "Kiyi haƙuri Badriyya na san iyayenki ba za su ƙara

Chapter 8 of 15