akan ta zai iya saɓawa kowa"
"Na ga alama kam!" Ta furta tana cire gyale kafin ta ce "Gaskiya test ɗin yau tayi masifar wahala, ni Allah yasa ma na ci"
"Amin, ya kike yiwa kanki mugun baki, ni yanzu ai kece hope ɗina, tunda wancan sakaran na haifawa mace."
"Umma insha Allahu ba zan baki kunya ba"
"Allah ya sa."
***** *****
Kallon banza ta sake watsa masa kafin ta ce "Amma ai da buƙatar kanka ce da har gida za kazo, ni kam baka kyauta min ba, yanzu idan da Sadiya ta farka ban zo ba ai babu yadda za ai na wanke laifi na"
"Aunty Saddiqa dan Allah a huce haka, wallahi ki tambayi Auta, daga ni har ita mun miki kira yafi a ƙirga, kuma bani da nutsuwar zuwa na faɗa miki" Ya ƙarasa yana ɗan murmushi wanda har sai da lips ɗinsa ya loɓa.
"Za kayi dariya mana, tunda ka san abinda ka aikata."
Surayya zama tayi gefen gadon da Sadiya take tare da faɗin "Kema Aunty Saddiqa da laifin ki, sai ayi ta kiranki ki ƙi ɗaga waya"
"Amma dai kin san ina sane ba zan ƙi ɗagawa ba, ina can kitchen mun fito da komai na ce yau general cleaning zan yi, saboda azumi yana ta ƙaratowa, gara na gama kintsa komai"
"Kin ga kenan bamu da laifi, kin bar waya a sama kin sakko parlorn ƙasa kuma cikin kitchen"
Za ta sake magana suka ga Sadiya ta motsa, da sauri Faruq ya miƙe ya ƙarasa jikin gadon nata.
A hankali ta fara motsa baki suna kallo, sai data gama salati sannan a hankali ta fara buɗe idanuwanta, sai da ta kallesu ɗaya bayan ɗaya sannan ta kai hannunta saman cikinta taji wayam, da sauri ta miƙe zaune, har sai da ta ɗanji zafi Saddiqa ta riƙeta, "Auta maza kirawo Doctor"
Surayya da sauri ta fita kiran Doctor.
"Saddiqa na haihu kenan? Me na haifa? Yana ina?"
Rasa amsar da za su bata sukayi, ta kalli Faruq shima ita yake kallo.
"Kin ga ki kwantar da hankalinki tukun, kin ga dai C.S ne aka yi miki, akwai ɗinki a cikin ki kar ki fama"
"Ina Babyn?" Ta sake tambaya a kuma daidai lokacin Dr ya shigo. Jikin gadon ya tsaya ya gama duba ta, sannan ya ƙara da cewa "Mun rasa babyn, amma ke kuma mun yi nasarar ceto rayuwarki, ki godewa Allah kuma kiyi tawakkali da shi, insha Allahu za ki samu wasu rabon a gaba" Har ya gama magana bata ce komai ba, sai daya fita sannan ta fashe da kuka.
"Kiyi haƙuri Aunty Sady..." Auta ta faɗa a lokacin kuma Saddiqa ta yi saurin yi mata alama ta yi shiru.
Sai da Sadiya ta yi kuka sosai sannan ta share hawaye ta kallesu.
"Mene na haifa kuma ina Yazid da yara?"
"Ba mu ga yaran ba, wataƙila suna gidan kakarsu, amma shi Yazid bai daɗe da fita ba kika tashi."
"Saddiqa mene na haifa?"
"Mace ce"
Ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa "Allah ya sa mai ceto ce"
"Amin ya rabbi"
Satin ta ɗaya aka sallameta sai dai gida aka wuce da ita saboda ɗinkinta sai ya ƙarasa warkewa a cewar Mameey. Tana kwance a kan kujera yaran suka shigo, Ihsan tana ƙoƙarin hawa jikinta Surayya ta janyeta "Sarakan san jiki ni ai naso an miki ƙanwa ko kin bari Yayata ta huta"
Murmushi Sadiya ta yi sannan ta kalli Surayya sai kuma ta ɗan tashi zaune.
"Autah"
"Na'am"
"Wai ko dai kun daidaita da Faruq ne?"
"Wane Faruq"
"Har guda nawa ne damu?"
"Aunty wai wannan ɗan yaron? Taɓ! Allah ya kiyaye"
"Kin dai san mace ba ta fin ƙarfin namiji ko?"
"Ai wallahi ni kam ba dai Faruq ba haba ki daina faɗa ma kar ya raina ni"
Murmushi ta sake yi tare da faɗin "Na ɗauka 'yar gida za a yi"
"Aunty Sady kenan."
Fitowar Mameey ce ta dakatar da su. Ta samu kujera ta zauna sannan ta kalli Surayya.
"Auta kama yaran ku tafi ina son yin magana da Sadiya."
Ji tayi gabanta ya yanke ya faɗi, a kuma lokacin Autah ta kama hannun yaran suka wuce.
"Sadiya!"
Shiru tayi kanta a ƙasa, zuciyarta na harbawa da sauri.
"Kin san babu abinda mijinki ya kawo sannan danginsa babu wanda ya zo?"
Kallonta tayi sannan ta ce "Mameey naman da aka kawo daga gidan Aunty Saddiqa shi ne ya kai mata ya ce ta sarrafa sai ta kawo mi..." "Dalla rufa min baki. Ni za ku rainawa hankali?"
Kai Sadiya ta girgiza lokacin kuma hawaye masu zafi suka subo mata.
"To na san cewa ba Yazid bane ya kai, kuma C.S aka yi miki kina buƙatar ki ci nama sosai ko da shi ne ya kai wannan yana nufin sau ɗaya za ki ci naman ƙan-baki? To ni duk ba wannan ba, a rasa wanda zai zo ya duba ki bare ya miki jaje, wai dole ne aure a wannan ahalin matsiyatan, to ki kirawo min shi yanzun nan"
"Mameey dan Allah kiyi haƙuri"
"Za ki kirawo min shi ko kuma ni in tashi in tafi gidansu"
"A'a Mameey" Sadiya ta faɗa da sauri sannan ta ɗauki wayarta ta kirashi.
"Ki duba wayar da kike amfani da ita, ko an baki ma sai kin ba shi ya sayar kamar wadda aka yi wa asiri, so ai ba hauka bane"
Ita dai bata ce komai ba ta miƙewa Mameey waya lokacin da Yazid ya ɗaga.
Jin muryar Mameey ya saka ya gaisheta "Ba gaisuwarka nake buƙata ba ka riƙe kayanka. A daidai lokacin Faruq ya yi sallama ya ji Mameey na faɗar haka. Kallon Sadiya ya yi sannan ya kalli Mameey.
"Sadiya nake so ka saka, dan ko yanzu ka saketa ba zata rasa miji ba, amma ni har yau ban ga wata ribar aurenka ba, bayan rama da lalacewa da tayi, sannan ta haihu amma a rasa wanda zai zo ya mata jaje a gidanku, to Yazid na baka nan da anjima ka turowa Sadiya takardarta, bata jira me zai faɗa ba ta kashe.
"Mameey dan Allah kar ki rabani da Yazid, wallahi ba zan iya rayuwa ba sai da shi."
"Sadiya!" Mameey ta furta da mamaki tana kallonta.
"Ni kike kallo kina cewa kar na rabaki da ɗa namiji?"
Shiru tayi hawaye na tsiyaya daga idanunta. Faruq ya samu guri ya zauna "Mameey tunda tana son mijinta please let it be!"
"Faruq idan ina magana da Sadiya akan miji kana saka baki wallahi sai ranka ya yi mummunan ɓaci"
"Am sorry Mameey"
Kallon Sadiya ta sake yi sannan ta ce "Sai ki zaɓa ko Yazid ko mahaifiyar ki, tunda ke baki san annabi ya faku ba."
"Mameey...." Sai kuma ta tsaya lokacin da taji komai yana juya mata. A take a gurin ta suma.
**********
Tana kwance akan gado ta ji anyi knocking ta san ko bata bayar da umarni ba dole a shigo domin mutum biyu ne kaɗai take iya gani, daga Mommy sai Lawisa.
Shigowar Lawisa ta saka Badriyya saurin tashi zaune.
"Meyasa yau baki fito ba"
"Bana jindaɗi ne"
Miƙewa Lawisa tayi ta ƙarasa gaban kwanukan abincin, babu abinda ta taɓa, kallonta ta yi sannan ta ce "Tun safe babu abinda kika ci, ko dai akwai wani abu?"
"Lawisa so nake na fita daga gidan nan"
Kallonta sosai take kafin ta ce "Zamanki a gidan nan yafi fitarki alheri"
"Meyasa?"
"Saboda dake da Affan gabaɗaya wanted ne"
"Shin wai me muka aikata ne? Affan bai yi kisan kai ba, haka ni kuma ban san mene ake ba ina cikin gida fa lokacin da ya yi aikin, shi da Nashwa suka yi amma bani ba"
"Dalilin daya saka suka kashe Nashwa kenan"
"What?" Ta furta tana miƙewa tsaye.
"Abinda ya kamata ace kin sani ne tuntuni, Nashwa ta rasu, kuma a dalilin ƙoƙarin bankaɗo abinda bai shafeta ba, har gara Affan ma aikinsa ne duk da shima bai zama wajibi a garesa sai ya kutsa inda yafi ƙarfinsa, amma ki sani tun daga ranar suke neman Affan, shi ne dalilin daya saka suka buga motarku a tunaninsu kun mutu mune kaɗai muka san kuna raye"
"Amma......" Sai kuma ta yi shiru.
"Ki faɗi duk abinda ke ranki."
"A lokacin da abin ya faru Nashwa bata garin, ta tafi Kano tunda ita tun satin bikin ma ta tafi, mu kuma a hanyar zuwa dinner ne accident ɗin ya faru"
"To kina tunanin idonsu baya kanta bayan ta bi Affan sun ganowa kansu abinda yafi ƙarfinsu."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Badriyya ta furta tana dafe kai.
"Abinda ya kamata ace kin daɗe da sani ne na sanar dake a yanzu. Kun yi hatsari a kuma wannan hatsarin yaronku ya rasu, ku kuma aka ɗauke ku ranga-ranga zuwa asibiti, bayan an tabbatar da kuna raye shugabansa ne ya bayar da shawarar a bayyana rasuwarku ga duniya hakan kaɗai zai saka masu nemanku su haƙura, domin yadda kukayi hatsari ana gani an san shiryayye ne, muna tsaka da wannan tashin hankalin aka kiramu aka sanar mana da an harbi Nashwa, ita a take aka ce ta rasu dan ba a kaita asibiti da rai ba."
Shiru Lawisa tayi kafin ta cigaba da cewa "Yadda kika riƙa ɗagawa Affan hankali akan auren, da yadda kika riƙa faɗar maganganu da ace babu ke hatsarin nan da ya afku da kuma ace bamu san da case ɗin nan ba, to babu yadda zai ai mu kasa ɗaura laifin mutuwar a kanki"
Kuka sosai Badriyya take, "Aunty Badriyya na san duk abinda kika yi a wancan lokacin kinyi ne saboda son da kike yiwa Affan, to a yanzu Affan naki ne ke kaɗai, Nashwa bata raye"
"Affan ba zai taɓa zama nata ba" Da sauri suka kalli ƙofa. Mommy ta shigo ɗakin sannan ta tsaya tana kallonsu.
"Affan ba zai taɓa kasancewa tare da ita ba, domin ni ban yarda babu hannunta a kisan ba, tunda dai ga shi har yanzu Affan bai damu ya ganta ba"
"Mommy wallahi ba zan taɓa iya kisa ba, ko in saka hannu a kisa"
"Bincike ne kaɗai zai tabbatar da haka, kuma daga zarar Affan ya miƙe zai iya tona miki asiri, wannan dalilin ne ya saka kika zama matatta har a gurin iyayenki"
Kai ta riƙe tana jin wani irin zugi, ita bata taɓa sanin son da takewa Affan zai zama matsala har haka ba.
"Mommy gaskiya bata da hannu, idan da hannunta, ba zata yarda su tafi mota ɗaya da Affan ba"
"Lawisa a yanzu ba zai shaideta ba, zamu jira har lokacin da Affan zai samu lafiya"
"Ajiyar zuciya kawai ta sauke. Yayinda Badriyya ta cigaba da rera kuka.
****** ******
Shiru Lawisa ta yi na ɗan lokaci kafin ta ce "Amma kina ganin babu matsala idan mun koma Kano Mommy?"
"E, in sha Allahu babu komai, tunda kin ga duk abinda ya faru da shi a Yola ne, babu haɗi gwamnatin Kano da Yola"
"Amma kuma ai Nashwa 'yar Kano ce, kuma har can suka bi ta suka kashe"
"Ita sun bita Kano saboda dama bibiyarta suke, Lawisa idan muka bar Affan a haka zai iya haukacewa gabaɗaya saboda a yanzu haka in kika kalli Affan kin san ba daidai yake ba"
"Hakane Umma"
"Ana so ya fara ɗan fita, kuma kin ga nan Abuja masu kuɗi anan suke lafewa, duk inda zai kai Affan zai iya haɗuwa da wasu daga cikinsu"
"Amma Mommy meyasa sai Kano?"
"Saboda ina da 'yan uwa sosai acan yanzu haka na bayar da cigiyar gida, daga zarar an samu to zamu koma can, sai kuma mu sama masa personal consultant da zai riƙa duba shi"
"Badriyya fa?"
"Na kira iyayenta, na sanar masu tana raye, yanzu haka suna hanyar zuwa nan Abuja"
"Mommy ba matsala?"
"Insha Allah babu"
"To Allah yasa"
"Amin ya Allah. Ki kirawo min Badriyya ta sameni a bedroom ɗina"
"Okay." Ta furta tana da miƙewa ta bar parlourn.
Tana shiga ta ga badriyya ta fito daga toilet tana laluba hanya tana tafiya, murmushi Lawisa ta yi sannan ta ƙarasa jikin side drawer ta ɗauki glass ɗinta ta ƙarasa gami da saka mata a fuska.
"Aunty Badriyya ki riƙa shiga toilet da glass ɗinki idan ba haka ba wata rana za ki iya rasa inda yake kuma babu wani a kusa da zai kawo miki"
Murmushi ta yi tare da zama sannan ta kalli Lawisa "So nake na koyi yawo babu shi saboda hakan zai min amfani wata rana"
"Wane ya faɗa miki ba zaki samu lafiya ba?"
"Bar wannan maganar Lawisa ai ni na san ganina ya tafi"
"A'a Aunty tunda har kike gani da glass ina mai tabbatar miki nan gaba kaɗan za ki riƙa gani ba tare da shi ba, tunda ba da shi aka haife ki ba."
"Ai ɗan adam ba a gama masa halitta har sai ya koma ga mahaliccinsa"
"Hakane amma insha Allah za ki cigaba da gani"
"Allah ya sa"
"Amin Aunty. Wani albishir nazo miki da shi."
"Na me?"
"Abbu da Ammi ɗinki suna hanya"
Ƙirji ta dafe tare da faɗin "Dan Allah dagaske kike?"
"Sosai, yanzu ma Mommy ce ta ce na kiraki" Cikin farin ciki Badriyya ta juya, Lawisa ta yi saurin cewa "Ɗan ji mana" Tsayawa tayi tana kallonta.
"A bedroom ɗinta za ki same ta"
Kai ta gyaɗa sannan ta wuce, ita kuma Lawisa ta yi murmushi.
Da sallama ta shiga ɗakin, Mommy ta kafe ta da idanuwanta.
"Mommy barka da gida"
"Yawwa Badriyya ki samu waje ki zauna" "To Mommy" Ta faɗa sannan ta zauna a gabanta amma akan carpet ta zauna.
"Badriyya"
"Na'am"
"Iyayenki za su ƙaraso yau, kuma sai sun iso ne za su gane cewa kina raye, sai dai zuwansu ba zai sa su ɗauke ki ba, dole ne ki zauna tare damu har zuwa lokacin da Affan zai tashi"
Ba ta iya cewa komai ba, har sai da Mommy ta ba ta umarnin tafiya sannan ta miƙe a sanyaye ta bar ɗakin.
****** ******
Tana buɗe idanuwanta akan Faruq ta fara sauke su, kafin ta kai dubanta ga Mameey sai kuma ta lumshe ido.
"Tun da ta farka alhamdillah". Mameey ta furta tare da wucewa, Faruq a gefen gadon ya zauna yana kallonta cike da tausayawa.
"Aunty Sady" Ya furta a hankali, ido ta buɗe ta kalleshi.
"Please ki kwantar da hankalinki, Uncle Yazid naki ne har abada"
Idanuwanta ta ɗan lumshe sannan ta buɗe tana kallon Farouq.
"Dan Allah ki daina damuwa, domin idan kina damuwa mu ma ba zamu taɓa samun kwanciyar hankali ba.
Ƙoƙarin tashi take, dan haka ya taimaka mata ta zauna tare da jingina bayanta da fuskar gado.
Kallon Farouq ta yi sannan ta ce "Farouq mene laifin Yazid? Saboda Allah bai mi shi arziqi ba? Idan kowa ke zaɓawa kansa rayuwa na tabbatar Yazid ba zai zaɓi talauci ba"
"Aunty Sady dan Allah ki kwantar da hankalinki, kin dai san halin Mameey ya kamata ace kiyi haƙuri da irin abubuwan da take miki"
Haka Faruq ya yi ta kwantar mata da hankali duk da shi ƙane ne a gare ta amma shawarwari da kuma nasihohinsa sun kwantar mata da zuciya sosai, a lokacin ta ƙara tabbatar da lallai Faruq ya yi hankali.
Da yamma tana kwance a gado Surayya ta shigo ɗakin. "Kowa yana parlour amma kina nan abin ki" Ta faɗa tana zama kan gadon, ita kuma ta tashi zaune. "Hmmm kin san tunanin me nake yi?"
"A'a sai kin faɗa"
"Surayya wallahi gani nake kin dace da Faruq"
"Kai Aunty!" Ta dafe kai sannan ta ce "Kodai zamu bari Najma ta girma sai a bawa Faruq"
"Ai ba za ki yiwa Faruq fatan ya jira Najma ba"
"To ni kuma ta ya ya kike tunanin zan jira shi?"
"Oh za kiyi aure ne yanzu?"
"Sai na gama school amma ni kam Faruq ya min yaro"
Dariya Sadiya ta yi tare da faɗin lallai ma yarinyar nan to yaushe kika fara soyayya da har Faruq zai miki yaro?"
"Aunty ni dai ki rufa min asiri ki daina maganar nan ka da ma ya ji ya raina ni"
"Sannu babba to an daina, amma ni ina hango miki dacewa ne"
"Kin san Allah dan ba ki ganin Faruq kullum shiyasa kike masa kallon salihi"
"To ai shi kenan, Allah ya zaɓa mafi alheri"
"Amin."
A*Dare*
Tana zaune a ƙasan rug ɗin dake ɗakin tana bawa Ihsan abinci ta jiwo hayaniya daga parlour, gabanta ya faɗi ta miƙe tare da cewa Ihsan "Baby cigaba da cin abinci ina zuwa" Da sauri ta fita jikinta a sanyaye.
Ganin Yazid abin ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. "Yawwa dama yanzu nake shirin kiranki sai ga ki kin kawo kanki" A ƙasa ta zauna tare da sauke kai ƙasa lokaci guda ta ji bugun zuciyarta na ƙaruwa.
"Na fara tunanin wannan mutumin asiri ya yi miki Sadiya"
Kai ta ɗaga ta kalli Mameey hawaye na zuba a idanuwanta.
"Zan baki zaɓi biyu ne ki zaɓi ɗaya, ko dai ki zauna anan wannan gaulan mijin naki ya baki takardarki ko kuma ki bi mijinki ni kuma bana buƙatar ganinki a gidana har abada"
"Mameey..."
"Babu abinda zan ji Sadiya zaɓi ya rage naki" Tana gama faɗa ta wuce abinta ta bar Yazid da Sadiya a parlour cikin furgici.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah🦋✍️
[6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
Faceboo@SaNaz Deeyah
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 5```
Sun fi mintuna biyu zaune babu wanda ya tankawa wani, sai dai Sadiya hawaye kawai ke zuba a fuskarta.
"Sadiya"
Ta ji ya kira sunanta a sanyaye, ta ɗago ta kalleshi idanuwanta har sun fara canja launi.
"Dan Allah ka da ki rabu dani wallahi ba zan iya rayuwa babu ke a ciki"
Ba ta ba shi amsa ba haka zalika ba ta bar kuka ba.
"Na yi miki alƙawarin ba zan taɓa bari ki wulaƙanta ba, kuma na san Mameey tana fushi ne amma za ta sauko saboda tana sonku"
"Ina tsoro Yazid"
"Kar ki zaɓi rabuwarmu saboda ba zan iya rabuwa da ke ba, dan Allah ki tausaya min" Ya furta yana haɗe hannayensa.
Haka ya yi ta roƙonta har ta ji cewa za ta iya bin sa, duk da tana cikin fargabar furucin Mameey, amma rayuwa da mijinta da kuma yaranta ya fi mata komai.
Tana cikin haɗa kayansu Mameey ta shigo.
"Sadiya haɗa kaya kike za ki bi miji?"
Ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta ta kalli Mameey.
"Kiyi haƙuri Mameey bana so na raba kan yarana dan Allah Mameey ki fahimc...."
"Dakata, tunda dai haka kika zaɓa ya miki kyau, Allah ya barku tare ke da shi." Tana gama faɗa ta juya.
**********
Ko da ta shiga gidan ta yi mamaki sosai da ta gan shi a tsaftace, kuma an gyara bayin sannan an sake musu rufi.
Sai bayan sun huta ne take tambayarsa inda ya samu kuɗin da ya yi wannan aikin, anan yake sanar da ita sauran kuɗin aikin da aka mata ne ya haɗa ya yi gyaran gida.
Shiru ta yi idanuwanta cike da ruwan hawaye dan ƙiris suke jira su zuba.
"Sadiya kiyi haƙuri, ki ɗauki dangana Allah ya sa mai ceto ce, ke kuma Allah ya baki lafiya me ɗorewa"
"Ban taɓa yin wahalar labor kamar na wannan cikin ba, ashe bama zamu rayu tare ba"
Ta saka yatsa tana goge hawaye.
"Haba Babyna, dan Allah ki bar kuka, insha Allah zamu samu wasu" Jin haka ya saka ta lumshe ido cikin jindaɗi, duk da suna da yara kuma suna cikin matsi na rayuwa amma hakan baya hanasu shan soyayya.
Ranar cikin farin ciki da annashuwa suka kwana, duk da ɗinkin ta bai gama warkewa ba amma dai sai daya daɗaɗa mata ya kuma mantar da ita damuwar da ta taho da ita daga gida.
*08:00am*
Tana gaban murhu tana dafa ruwan shayi sai ga shi ya fito ya ƙarasa inda take. "Maman Najma ni zan tafi kasuwa."
"Haba Abban Najma ya za ka fita baka karya ba"
Murmushi ya yi sannan ya ce "Kar ki damu nima zan samu abu a waje na ci, amma kin ga na yi rana yanzu"
Miƙewa ta yi tana kallonsa.
"Dama akwai abinda nake son baka, amma tunda yanzu ka yi rana sai mu bari sai gobe idan Allah ya kaimu."
"Allah ya kaimu"
"Amin Abban Yara Allah ya tsare hanya"
"Amin Babyn Baby"
****** ******
"Saddiqa a haka kike tunanun zan cigaba da haƙuri da Sadiya bayan ba ta jin magana ta kuma ba ta san kima da darajata ba" Mameey ta yi maganar cikin ɓacin rai.
"Mameey dan Allah kiyi wa Sadiya uzuri, ni na san tana yin haka ne saboda yaranta ba ta so ta fito kuma ace za a ƙwace mata yara"
"Haba Saddiqa ai ban san meyasa da ke da Faruq sam baku ganin laifin Sadiya sai kuce wai na yi mata uzuri, wane uzuri ne ban mata ba, dole sai ta tura kan ta inda ba a yi da ita."
Faruq zama ya gyara sannan ya ce, "Mameey dan Allah kiyi haƙuri"
"Ni fa ina ganin mijin nan nata asiri ya mata, haba wannan wane irin so ne?" Cewar Surayya.
"Babu asirin da ya yi mata, kema idan kika yi aure kika haihu za ki gane irin yanda ɗa yake a zuciyar mahaifiya" Saddiqa ta faɗa tana kallon Surayya.
"Amma dai kin san ko yaran Sadiya sun kai dubu zan iya riƙewa ko?"
"Mameey za ki iya amma kina da tabbacin 'yan uwansa za su yarda su bar mata yaran? Musamman ma mahaifiyar shi da ba ƙaunarta take ba"
"To sai ta bar musu dama ai ba dasu taje gidan ba."
"Mameey kema fa kina jin zafin yadda Sadiya ke shan wahala a gidan Yazid duk da cewar Yazid yana ƙaunar Sadiya, to ya kike tunanin Sadiya za taji idan aka ƙwace yaranta aka damƙa a hannun da babu kulawa?"
"Shi kenan tunda kun zaɓi Sadiya sama dani, taje ga miji nan ai dama itama miji ta zaɓa sama da mahaifiya" Tana gama faɗa ta tashi rai ɓace ta bar parlourn.
Faruq ya sauke ajiyar zuciya tare da faɗin "Aunty Sady dai ƙaddararta ce a haka, kuma naga da ita da Uncle Yazid gabaɗaya suna son junansu ya kamata both family ɗin su bar su su yi rayuwarsu mu bisu da addua"
"Ai ƙiyayyar Yazid a gurin Mameey fa ta daɗe Faruq"
"Na sani Aunty Saddiqa amma tunda har da yara ya kamata Mameey ta haƙura."
Sai lokaci Surayya ta ƙara soma baki a maganar ta ce, "Ni fa bana son Yazid ɗin nan, dama tun farko ba su dace da Aunty Sadiya ba, ni wlh ban san me ta gani ba"
"Ki rufa mana baki mara kunya kawai"
"Daga faɗar gaskiya"
"Ke har wata gaskiya ne da ke"
"Kai kuma Faruq ka kiyayeni wallahi"
"Oh ni dai kike so kice na kiyaye ki"
"Kin san dai ba zan taɓa faɗa miki haka ba Aunty Saddiqa."
Tana gama maganar itama ta miƙe ta wuce. Saddiqa ta girgiza kai tare da cewa "Allah ya kyauta."
****** *******
Kuka sosai suke yi ita da Ammi sai da suka yi mai isarsu sannan suka tsagaita.
"Amma gaskiya baku kyauta mana ba da kuka kasa faɗa mana gaskiya"
"Yanzu ai ga shi kun sani, kuma a baya da mun faɗa muku gaskiya ai ba zaku iya protecting ɗin ta ba."
"Haba Malama, ita ɗin fa 'yar mu ce jininmu" Ammi ta furta rai a matuƙar ɓace.
Abbu ya yi saurin cewa "Mariya kiyi shiru ba abin faɗa bane, tunda dai tana raye mu godewa Allah, da fa har mun fitar da rai da ita."
"Wannan ai mugunta ce, kalli yadda Badriyya ta koma, wata takwas kana ɗaki, kawai dai so sukayi su kwantar da ita kamar yadda shima Affan yake a kwance"
"Wace irin magana kike faɗa haka Mariya?"
"Komai ma, taya za ki ɗauko mutum ki ajiye wata takwas a ɗaki kuma ba wani ciwo yake ba, to wallahi sai na ɗauki matakin shari'a dake."
Murmushi Mommy ta yi sannan ta ce, "Wannan shi ne babban kuskuren da za ki tafka a rayuwarki,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 15