tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 15```
"Aunty Sady lafiya kuwa" Surayya ta faɗa tana ɗaukar wayarta, Allah ya taimaka bata fashe ba. "Mene ya faɗa miki wanda har ya ɗaga miki hankali haka?"
"Surayya idan Faruq ya kira ko ya ce ki haɗa mu ka da ki kuma kawo min"
"Wai lafiya kuwa?" "
"Kin dai ji abinda na faɗa ai, ki fita ina so na kwanta" Kallonta Surayya ta yi sannan ta wuce.
****** ******
"Yaya Affan" Ta ambaci sunansa sannan taja kujerar dining tana facing ɗinsa. "Yaya nazo maka da wani albishir"
"Na me?"
"An saki Sadiya kuma har ta gama idda"
"What?"
"Wallahi dagaske ɗazu wannan ƙawar tawa take faɗa min"
"Anya mijin yarinyar nan yana da hankali kuwa?" "Ya naga kamar baka ji daɗi ba, na ɗauka za kayi farin ciki"
"Haba Lawisa, yanzu sai a saki mutum na yi farin ciki, to mene ribata?" "Gani na yi yanzu kana da damar zuwa gurin ta" "Ni dai duk da haka ban ji daɗi ba, kuma ina fatan Allah yasa bani ne sila ba, saboda naga soyayyar mijinta ƙarara a idanuwanta"
"To ai kuma ka san aure rai ne da shi"
"Hakane, Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi" "Amin ya Allah"
"Zan samu na je kuma zan nemi aurenta insha Allah"
"Allah ya sa a dace, amma dai da wuri za ka je ko?"
"Ai ban san gidan ba, kuma gaskiya ko na je ba kai tsaye zan fito ba."
"Kar fa ka tsaya jan aji ayi mana sakiyar da babu ruwa"
"Hakan ma ba zai faru ba bi'iznillah amma kin san dole sai na ga kamun ludayinta"
"Hakane, to Allah ya sa a dace"
"Amin."
_Bayan Sati Ɗaya_
Yana saka kaya a mota wayarsa ta fara ringing, ganin Ayda ce ya saka ya ɗaga tare da rufe motar sannan ya shiga driver seat lokacin ya furta "Hello"
"Hi! Ya kake, hope you're in good condition"
"Yeah, fatan kema haka"
"Alhamdulillah, har yanzu dai mun ji ka shiru babu ziyara"
"Wallahi ina taso na zo so lectures sun ɗan riƙeni."
"Farhan ma tana taso ka zo ku yi hira, na ce tunda yau saturday let me call you na ji ko you are free"
"Ayya, kin san yanzu haka bana gida but insha Allah ƙila na shigo gobe"
"Haba why not ka zo yau?"
"Ya yi late coz kin ga na ce miki na fita, ba zan gama abin da nake har na samu shigowa."
"Allah ya kaimu goben"
"Amin ya rabbi."
Kai tsaye gidan su Sadiya ya nufa sai dai gaban shi na ta faɗuwa, adireshi ya bi har ya ƙarasa unguwar sai dai ya yi matuƙar mamaki da aka nuna masa gidan, _kenan da gatanta take auren wahala, lallai tana son mijinta._ Ya fito daga mota yana neman yaron da zai tura ya yi masa sallama.
Mameey da Surayya ne zaune a parlour lokacin da yaron ya shigo "Wai ana kiran Sadiya"
"Sadiya kuma?" Yaron ya gyaɗa kai. "Waye?"
"Wani ne a mota" Jin haka ya saka Surayya taɓe baki "Yanzu haka Yazid ne dan na san shi ƙaɗai ne zai zo gurinta tunda ba fita take ba bare asan ta fito."
"To mene ya kawo shi, ko zuwa ya yi ya ƙara ɗaga mata hankali?"
"Wa ma ya san masa" "Jeki ki ji da wacce yazo."
Da ɓacin rai Surayya ta fita sai dai ganin baƙon mutum ya saka ta yi turus. "Sannu da zuwa, ina wuni" Ta furta tana ƙara kallonsa a ranta tana yaba kyawunsa.
"Lafiya lau, Sadiya ko tana nan?"
"E tana nan, bismilla" Ta furta tare da juyawa. A farfajiyar gidan ta ɗauko kujeru biyu ta ajiye sannan ta ce "Bari na kirawo ta"
"Okay thanks" Har ta juya sai kuma ta juyo "Wa za a ce mata?" Murmushi ya yi wanda suke ƙara masa kyawu ya ce "Baƙo ne" Juyawa ta yi ta shiga. "Mene ya kawo shi" Shi ne abinda Mameey ta faɗa. "Ba fa Yazid bane wani ne da ban"
"Wani wa?"
"Wallahi ban sani ba, na dai ce ya shigo wataƙila ita ta san da zuwansa" "Je ki kirawo ta" Da sauri ta wuce ɗakin Sadiya.
A kwance ta tarar da ita ta ƙurawa guri ɗaya ido.
"Ki fito kin yi baƙo" Jin haka ya saka ta miƙe tare da faɗin "Baƙo kuma?"
"E, yana farfajiya"
"Waye?"
"Wallahi ban sani ba" "Baki sani ba kuma kika ba shi damar shigowa?" "Bai min kama da macuci ba, ki fito dai Mameey ma na kiranki" Tana gama faɗa ta fita.
"Mameey ga ta nan zuwa, bari na kai masa ruwa"
Yana danna waya ta ƙarasa tare da ajiye ruwa a gabansa. "Su Najma ba sa nan ne?"
Ɗagowa ta yi ta kalleshi kafin ta ce "E, suna gidan Yayarmu."
"Okay. Amma ban sanki ba, but naga kuna yanayi da Sadiya, mene sunanki?"
"Sunana Surayya, kaima ban gane ka ba"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Za ki sanni soon"
"Okay, ga ruwa bismilla, bari naje"
"To nagode Surayya."
"Ni ban yi da kowa yazo ba gaskiya" Ta faɗa tana ƙara tsuke fuska, lokacin da Surayya ta shiga.
"Ai ba zuba ido zamuyi muna kallonki ba, kuma ba dole sai kin cewa mutum ya zo sannan zai zo ba"
Zama Surayya ta yi tare da faɗin "Har Najma ya tambaya, amma kuma he's matured"
"Tashi kije karki bar mutum tsaye shi kaɗai"
Jiki babu ƙwari haka ta miƙe ta fita.
Turus ta yi a lokacin da ta gan shi, ta ji gabanta ya yi mummunar faɗuwa.
"Ki ƙaraso mana." Ya furta yana kallonta, bata musa ba ta ƙarasa tare da jan ɗayar kujerar ta zauna.
"Na san kin yi mamakin ganina a gidanku ko?"
"Sosai kuwa, dan ban yi tunanin ka sani ba"
"Kin san bahaushe ya ce mai son ɗan tsuntsu shi yake bin sa da jifa"
Shiru ba tayi magana ba.
"Sadiya ban san kin fito daga gidan mijinki ba, sai yanzu ake faɗa min har kin gama idda."
Ji tayi wasu hawaye masu zafi sun zubo mata babu shiri, ta saka hannu da sauri ta goge "Kiyi haƙuri ban san maganar za ta ɓata miki rai ba da ban yi ba"
"Me kake buƙata?"
"Dama nake so ki bani, Sadiya ina so na aureki" Murmushi ta yi wanda kana gani ka san na yaƙe ne.
"Dan...."
"Ka ga malam ɗan dakata" Ta furta tare da miƙewa tsaye.
"Bana fidda ɗayan biyu shigowar ka rayuwata ya saka aka tilastawa mijina ya sakeni, bana sonka kuma har abada ba zaka taɓa mallakata ba" Tana gama faɗa ta juya, yana kiranta amma bata tsaya ba.
Tana shiga suka kalleta, sai dai yadda ta wuce da sauri kuma tana hawaye ya saka suka gane lalle akwai matsala.
"Surayya je ki duba ki ga lafiya" Da sauri ta fita, sai dai a tsaye ta gan shi kamar jiran fitowarta yake.
"Am...dama Mameey ce ta ce na zo na ji ko lafiya, saboda mun ga Aunty Sady ta shiga da kuka."
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Surayya ban sani ba, amma....am...ko dan babu komai"
Murmushi tayi tare da cewa "Karka damu, ka faɗa min koma mene"
"Surayya!"
"Na'am"
"Maganar gaskiya na kamu da son yayarki, sai dai ita ba tani take ba, gani take kamar nine na zama silar fitarta daga gidan miji"
Da mamaki ta ce "Dama kun san juna ne?"
"E, amma ba can ba, na san ta gab da za ta samu matsala da maigidanta"
"Amma ai hakan ba zai zama hujja ba"
"A taki mahangar kenan amma ita yanzu haka take gani."
"Kayi haƙuri, insha Allahu zan yi magana da ita, kuma idan har da gaske kake zamu shawo kan ta, zan yi magana da Mameey"
"To shi kenan, zan iya samun number ɗinki dana Sadiya?"
"E, bara na baka" Karɓar wayarshi ta yi ta saka masa numbers ɗinsu.
"Akwai kayan dana tahowa da su Najma, ko zamu je mota sai ki karɓa"
"To ba damuwa"
Ƙatuwar baƙar leda ne bata ma san mene a ciki ba, ta karɓa tayi godiya.
Bayan ta gama faɗar duk abubuwan da suka faru Mameey ta girgiza kai, "Har yanzu akwai ƙuruciya a tattare dake Sadiya, yanzu shi daya ƙwatar miki 'yanci shi kike kallo a matsayin maƙiyi"
"Mameey da ace bai shigo rayuwata ba, da duk haka bata faru dani ba" Ta faɗa tana share hawaye.
"Shi kenan, kina budurwa ma ban miki dole ba, bare yanzu da kike da damar zaɓen mijin aure" Miƙewa tayi ta bar ɗakin Surayya ta dafa Sadiya ta ce "Ki jarraba ki gani, wataƙila shi alheri ne a gareki, karkiyi gaggawa karɓarsa kuma karkiyi gaggawar korarsa, ki tsaya kiyi tunani sosai Aunty Sadiya"
"To shi kenan, nagode sosai Surry"
"Karki damu Aunty Sady, ga kayan daya kawo wa su Najma"
"Ok, mun gode"
Suna buɗewa suka ga kayan wasa na yara sai kuma chocolates da nau'ikan biscuits, dasu ice cream"
"Lallai wannan da gaske yazo"
"Hmmm! Kin ɗauka kashe kuɗi ne so?"
"A'a amma ai suna daga cikin sunnonin soyayya"
Murmushi kawai Sadiya ta yi dan a cikin damuwa take.
****** ******
Da sallama ya shiga bedroom ɗin Mommy.
"Affan ka dawo kenan"
"E Mommy" Ya furta tare da zama sannan ya gaisheta.
"Dama magana nake son yi da kai akan yaran ƙawata dana ce kaje ka gani, kuma na ji baka ce komai ba"
"Mommy ai bamu gama fahimtar juna ba."
"Duk da haka ina son dai na san a cikinsu wacce ce tayi maka"
Shiru ya yi, dan har ransa baya jin son ko wacce a cikinsu, shi a yanzu Sadiya ce kaɗai a gabansa.
"Mommy akwai wata dana haɗu da itane, so gaskiya hankalina yafi karkata a kanta"
"A cikin Kano? Yaushe muka zo bare har ka fara son wata, ko shekara bamu yi ba"
Shiru ya yi tare da sauke kai ƙasa.
"Affan!"
"Na'am"
"Ka faɗa min Farhan ko Ayda wace ce ta yi maka?"
Shiru ya yi baice komai ba.
"Kai nake sauraro"
"Mommy na fi sabawa da Ayda"
"To na baka sati biyu kaje ku fahimci juna da ita"
Shiru ya sake yi har sai da ta ce "Je ka na sallameka" Miƙewa ya yi jiki babu ƙwari ya bar ɗakin.
Yana shiga ɗakinsa ya faɗa kan gado, idanuwansa na kallon sama, ya rasa me zai yi. Tabbas yana son Sadiya amma baya so ya yi wa Mommy musu, wayarsa ya janyo ya kira Lawisa, tana ɗagawa bai jira ta ce komai ba ya ce "Lawisa kina ina ne?"
"Ka san yau evening nake, ina asibiti"
"Ina son ganinki ne, kaina ya ɗauki zafi"
"To ko zaka zo?"
"A'a, ban daɗe da dawowa gida ba, kuma a gajiye nake"
"Okay to ko kawai mu yi magana a waya"
"No kar ki damu, idan kin dawo gida sai mu yi magana."
****** *****
"Gaskiya Yaya kayan nan sun yi kyau sosai, kuma sun dace da Aunty Salma"
Murmushi Umma ta yi sannan ta ce "Ai yanzu ne zai san ya yi aure, ba waccan sakaran mai farar ƙafa, yanzu ga shi ƙofofin arziƙi suna ta buɗe masa"
Fatima ta yi murmushi, sai kuma ta juyar da kai ganin yana aika mata harara.
"Shi fa Yaya Yazid har yanzu baya so a faɗi laifin Sadiya" Maryam ta faɗa tana taɓe baki.
"Ke ki kiyaye ni, kar na sake jin kin furta wata kalma akan Sadiya"
"An taɓo uwarka ba, ai dole ka nuna ɓacin rai. Ni Sadiyar nan ban san wane malami ke mata aiki ba data shanye ka" Shiru ta yi sannan ta kuma cewa "Kuma a cikin satin nan kaje ka karɓo yaranka ni zan riƙe kafin Allah yasa ayi auren su koma hannunka, dama ai yaran ne za su saka ka riƙa tunaninta ko ka samu damar zuwa gurinta to ka karɓo su" Ɗan lumshe ido ya yi, yana jin zafi a ransa.
"Ko baka ji abinda na faɗa ba?"
"Na ji." Ya furta sannan ya miƙe.
"Zan wuce"
"Allah ya taimaka"
"Amin." Ya furta a sanyaye.
Yana fita ya tarar da Lukman tsaye yana jiransa. "Ya naga ka fito rai ɓace?"
Da jikin get ɗin gidan ya jingina sannan ya ce "Lukman ji nake kamar na cuci Sadiya"
Murmushi Lukman ya yi tare da cewa "Oh kama ne ma? Ai ka cuceta, ni kaina kawai dole ta saka nake tare da kai"
"Na san ba zaka taɓa fahimta ta ba, amma rabuwata da Sadiya shi ne maslaha"
"A naka tunanin da hange mara tushe, shi kenan dai Allah yasa wadda za ka aura ta zame maka mace ta gari"
"Amin, amma bana jin zan samu madadin Sadiya a wannan duniyar"
"Kuma dai."
_*Bayan Sati Ɗaya*_
Tana zaune taji shigowar motoci, haka nan taji gabanta ya tsananta faɗuwa. Shigowa da trolley da Surayya ta yi ya saka ta miƙe tsaye, kafin ma ta yi magana Faruq da Saddiqa sun shigo, yana ɗauke da Ihsan a kafaɗarsa.
"Ke dai Allah ya shiryeki" Saddiqa ta faɗa tana harararta, Najma kuma da gudu ta rungumeta, a lokacin Mameey ta fito.
"Baƙin Nigeria sannu da sauka" Murmushi ya yi yana sauke Ihsan, sannan ya ƙarasa gaban Mameey ya durƙusa har ƙasa ya gaisheta.
"Ka tuno damu kenan"
"Mameey a kullum kuna raina tun ranar dana samu kaina"
"Kuma shi ne ka yi zamanka"
"Karatuna naso in ƙarasa kuma kewarku ta hanani zama na ce bari nazo na ganku sai na koma"
Sai da duk aka zauna sannan Sadiya ta ce "Yaro sannu da zuwa" Bai tanka mata ba, ya yi kamar ma bai san tana yi ba, sai da Surayya ta ce "Yaro ana magana fa"
"Kin ga ki kiyayeni, karmu fara tun yanzu, sunana Faruq kuma ni bana cin miƙe, bata rakani ba sannan da zan dawo bata je taroni ba"
"Gaskiya dai bata kyauta ba, nima yanzu na gama mata faɗa akan haka" Cewar Mameey, ita Sadiya bata ce komai ba dan tayi imani Faruq ya gama raina ta.
Miƙewa ya yi tare da cewa "Mameey an gyara ɗakina?"
"Tun jiya na saka aka gyara ma tas"
"Bara naje na ɗan watsa ruwa na huta"
"Ya kamata dai, abinci fa?"
"Na ci a jirgi sai dai ko bayan magrib"
"To shi kenan, amma fa karkayi bacci ka san ba a son baccin yamma"
"Okay."
Har ya fara tafiya ya ji Surayya na faɗin "Yau Affan zai zo gara da Allah yasa kina nan Aunty Saddiqa yana ta so ku gaisa"
"Wai saurayin Sadiya?"
Kai Surayya ta gyaɗa saboda haka Faruq bai ji tayi magana ba, lokaci guda ya ji zuciyarsa na ɗaci.
"Sadiya wai yana da wani aibu ne?"
"A'a Aunty amma ni bana so 'yan uwan Yazid da shi kansa ya ga kamar na kashe aurena ne saboda Affan."
"To ya gani mana, mutumin daya sakeki babu wani dalili mene na yi masa kara?"
Ɗan lumshe ido kawai tayi, wayarta data fara ringing ta kalla.
"Ko shi ne?"
"E, to tashi ki fita"
"Haba kai tsaye haka babu wani jan aji"
"Ma za ja ajin ya tsinke" Allah ya sa lokacin Mameey ta bar gurin.
Miƙewa tayi tare da kara wayar tayi ɗakinta.
"Lu'ulu'u" Shi ne sunan daya ke kiranta da shi duk da ta ce bata so amma yaƙi ya daina faɗa.
"Sady kina jina kuwa?"
"E, ina ji"
"Oh shi ne kika ƙyaleni, ba dai zan yi zuciya ba"
"Uhmm" Ta furta kawai.
"Ina ƙofar gida"
"To ka shigo mana"
"Ban isa na shigo ba har sai kin min iso"
"To na yi maka ka shigo"
"Nagode lu'ulu'u"
Bata ɓata lokaci ba ta shirya ta fita sai baza ƙamshi take. "Aunty da alama an faller ba" Juyowa tayi ta kalli Surayya lokacin za ta wuce tayi maganar.
"Sorry" Ta furta tana rufe bakinta da hannu.
"Ni dai ina jira yazo ya gaisheni"
"Aunty ni fa har yanzu ba wani sakewa nayi da shi ba"
"Za ki sake ai" Ta furta tana murmushi.
Suna zaune akan kujeru suna taɓa hira sai dai har lokacin bata sake da shi ba, ko magana ya yi wani lokacin bata cewa komai.
"Sady dama ina so naje na gaishe da Aunty Saddiqa so kuma tunda tana nan sai kawai na gaisheta anan"
Kallon shi kawai tayi, ta tabbatar ya girmi Saddiqa amma saboda yana da respect baya iya kiran sunanta kai tsaye.
"To babu damuwa" Ta furta a sanyaye.
Cikin gida kuwa Faruq yana shiryawa ya fito. Saddiqa ta kalleshi ta ce "Na ɗauka zaka ɗan kwanta ka huta"
"Ki bar hutun nan Aunty Saddiqa, gara in zo mu sha hira da ku"
"Aikam gara ka zauna ka bamu labarin abroad, kaga mu ko ƙafar jirgi bamu taɓa takawa ba, har gara Aunty Saddiqa da Mameey sunje hajji sun je Umra amma ni da Aunty Sady ne bayin Allah"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Kuma zakuje insha Allah, ina Aunty Sady?"
"Tana waje tayi baƙo"
"Baƙo kuma?"
"E, wanda zata aura, ka gan shi kuwa wallahi handsome ya fi Yazid komai" Cewar Surayya.
"Bari naje na gan shi"
"Kai dilla zauna zai shigo gaida Mameey ai"
"Ba jira fa" Ya faɗa tare da wucewa.
Saddiqa ta yi murmushi tare da cewa "Ke da kika san halinsa"
Tun da ya tunkarosu Sadiya ta ƙura masa ido, dan ta ga ya haɗe ransa sosai. Yana ƙarasawa ya kalleta "Mameey ta ce ki sallamesa kizo"
"Lafiya kuwa?"
"Nima ban sani ba"
Ji tayi gabanta ya faɗi. Affan kuma ya miƙawa Faruq hannu sai dai ga mamakinsu kawai suka ga ya juya, a daidai lokacin kuma aka turo ƙofa, shigowar Yazid ya saka Sadiya miƙewa tsaye shi kuma Faruq ya juyo.
*SAURA 5 PAGES MU GAMA FREE PAGES*
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
*Saura Pages 4 free pages sun ƙare, har na gama da group 1 grouo 2 yana jiran wanda basu biya ba, ku hanzarta a karanta tare daku*
_Book 1_
```🆓Page 16```
Kallon Affan ta yi ta ga ya haɗe rai, ta mayar da kallonta ga Yazid daya ke tunkarosu tare da Lukman abokinsa, sai dai tun kafin su ƙarasa Faruq ya tare su, Sadiya ta lumshe ido ta yi dan ta san zuwan Faruq ba zai haifar da ɗa mai ido ba.
"Malam lafiya kuwa? Na yi tunanin babu abinda ya yi saura, mene ya kawo ka gidanmu?"
Murmushi Yazid ya yi tare da faɗin "Akwai kuwa, idan ka manta zan tuna maka, akwai Najma da Ihsan kuma sune suka kawo ni gidan nan"
"Su ma a yanzu baka da cikakken iko dasu, dan haka ka fice ka bar mana gida"
"Kodai har yanzu baka warke daga ciwon son ba? To ka sani Sadiya ta maka zarra kuma tafi ƙarfinka, koda a mafarki kuwa" Jin haka ya saka Faruq cikin ɓacin rai ya ɗaga zai wanke Yazid da mari. "Faruq...." Sadiya tayi saurin furtawa, hakan ya saka shi tsayawa cikin ɓacin rai ya juya ya kalleta. Da sassarfa ta ƙaraso inda suke. "Baka da hankali ne? Abban su Najma ne fa"
"Koma waye?" Ya furta cikin tsawa.
Jin hayaniya ya saka Saddiqa da Surayya fitowa daga cikin gidan.
"Yazid kuma a gidan nan" Saddiqa ta faɗa tana ƙarasawa.
"Lafiya kuwa? Mene ke faruwa?" Ta furta lokacin data ƙarasa gabansu.
"Kana kallo wannan zai aureta, saboda tafi ƙarfinka har abada." Ya nuna Affan da hannu.
Hannu Sadiya ta saka ta dafe kai, ganin Yazid na neman tona sirrin da babu wanda ya sani.
"Wai mene ke faruwa ne? Yazid dan Allah kar ka biyewa Faruq ku yi ta sa'in sa"
Kallonsa Faruq ya yi sannan ya ce "To bari ka ji muna nan da kai zaka ji labarin aurena da Sadiya kai ni da kaina sai na kawo maka katin ɗaurin aure"
Surayya baki ta saki, yayinda Saddiqa ta ɗauki maganar Faruq a matsayin shirme. "Faruq idan na isa to kar na kuma jin kayi magana"
"Aunty Saddiqa ki ƙyaleni da shi yana kallona a matsayin wanda ba zai iya ba"
"To ina iyawar bayan har kayi jinya ka tashi bata so ka ba, idan da zata so ka ai da tun kana jinya ta tausaya maka, ko ka ɗauka ban san komai ba, Sadiya ba matar yara bace"
Sai lokacin Sadiya ta fashe da kuka, kawai ta durƙushe a ƙasa. "Faruq ka koma cikin gida ko na kira Mameey"
"Babu inda zan koma sai dai idan tare da ita dan ba zan barta da wannan azzalumin ba"
"Sadiya tashi ki koma ciki" Saddiqa ta faɗa tana kama hannunta.
"To mene ya kawo shi, ya koma inda ya fito"
"Ina ruwanka kai dai ka tafi kawai" Ta faɗa rai ɓace.
Tana miƙewa ta janye hannunta daga na Faruq ta ƙarasa gurin Affan da sauri.
"Affan dan Allah ina so ka turo magabatanka tare da sadaki a satin nan"
"Am....Sadiya am very sorry ni ban san mene zan faɗa ba am speechless because shi wannan ɗan uwanki ne, wannan kuma tsohon mijinki kuma akwai yara tsakani"
"Karka damu, ka tafi kawai zamuyi waya" Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "But dan Allah kar ki ɗaga hankalinki" Kai ta gyaɗa tana murmushin yaƙe.
Suna zaune a falo kowa ya yi shiru, har lokacin Sadiya ta kan goge hawaye, shi kuwa Faruq ransa a ɓace yake sosai ganin Mameey ta bawa Yazid damar shigowa.
"Dama nazo ne na karɓi yarana ne dan ina so riƙonsu ya dawo hannuna" Cikin tashin hankali Sadiya ta ɗago kai tare da faɗin "Wallahi baka isa ba, ba zan taɓa yarda in bayar da ƙananan yarana ba"
"Kar na ƙara jin kinyi magana" Mameey ta faɗa rai ɓace "Dama ko bai zo ba na yi niyyar mayar masa, dan bana so ya riƙa mana sintiri gida, na fi so a yi rabuwa ta har abada" Da sauri ya ɗago ya kalli Mameey sai kuma ya sake sauke kai ƙasa. Faruq kuwa daɗi ya ji sai dai bai so Mameey tayi furucin zata mayar da su Najma ba.
"Mameey gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a ba shi yaran ba, saboda mata ne kuma baya da aure." Saddiqa ta furta rai ɓace.
"Amma ai ina da iyaye, kuma ina da ƙanne mata"
"To hakan me zai amfanar? Yazid wallahi ba zan iya baka yarana ba, sai dai duk abinda zakayi ka yi, saboda ban san wane hali za su shiga ba idan bana tare dasu"
"Idan kuma mutuwa kika yi fa? Ba dole a wani wurin za su rayu ba, ni kuma wallahi sai kin ba shi yaransa, sai mu ga idan rantsuwarki tafi tawa."
"Mameey a gaskiya nima ban bayar da goyon bayan a bawa wannan azzalumin yaran ba" Faruq ya furta yana haɗe rai.
"Azzalumin ai ubansu ne idan ya ga dama ya kashe su ai jininsa ne"
Da sauri ta miƙe cikin tashin hankali tayi bedroom ɗinta, Yazid da ido kawai ya bita yana jin zafi a ransa.
"Surayya tashi ki haɗa sauran kayan yaran dama yanzu suka dawo ai, ya ɗauka ya tafi."
"Mameey dan Allah kar ki raba Aunty Sady da yaranta"
"Kiyi abin da na ce ko kuma ranki ya ɓaci"
Da sauri itama ta miƙe ta bar parlourn.
*Bayan Wasu Mintuna*
Jin kukan Najma ya saka ta miƙe daga kan gadon, idanuwanta jajir ga kanta da yake sara mata haka ta fita falo taga Yazid ya ɗauki Najma sai zullo take, Ihsan ce bata ma yi kuka ba, za ta ƙarasa gurinsu Saddiqa ta riƙo hannunta, ta kalleta cikin tashin hankali sai ta ga ta girgiza mata kai saboda lokacin Mameey na tsaye.
"Ba su ƙaunata wallahi na san ba za su riƙe min yarana ba, dan Allah kar ku rabani dasu" Kuka sosai take kuma a fili, Faruq ya ƙaraso gurin tare da kallonta "Ki bari su
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 15