samu ka warke karka ƙara ɗago mana shi, tashi ka zauna nan mu yi magana"
A sanyaye ya miƙe ya zauna gefenta.
"Faruq"
Bai amsa ba, bai kuma ɗago ya kalleta ba.
"Ba zan hanaka Sadiya ba, amma bana so na tauye maka haƙƙi, na farko Sadiyar nan ta baka shekaru har 3, she's 26 you're 24 Faruq you're still young, sannan Sadiya a yanzu bazawara ce har da yara biyu dan ma ɗayar ta rasu da uku za a ce, kai kuma saurayi ne ɗanye yanzu ma ka fara tasowa, ka ji biyu ko, abu na uku koda ni na amince da aurenku da Sadiya bana tunanin dangin mamanka za su yarda hatta dangin babanka wasu gani za su yi na zalunceka, yau da ace Surayya kace wallahi zan baka ita koda ba ta so, amma ka zauna ka zurfafa tunani."
"Mameey ni ban damu da duk abinda za a faɗa ba, saboda a yanzu idan har mutum zai biye faɗar mutane to ba zai taɓa yin abinda ya dace da shi ba. Mameey dan Allah ki taimaka min, dan Allah Mameey."
Hannu ta saka ta shafa kansa "Ya isa, ka je zan yi tunani akai"
****** ******
Tana ƙarasawa gabansa ta juyar da kai tare da haɗe fuska.
"Na yi laifi ko? Afuwan"
"Ni kam ban karɓi wannan ba"
"To ko dai na kama kunnuwana" Ya faɗa yana riƙe kunnen.
"Ni na isa na ce haka, please a'a"
Saukewa ya yi yana murmushi, "So ya kike, ya Anni and sister"
"Duk lafiya lau, mu ƙarasa ciki mana" Har sun juya suka ji horn, amma ba su yi tunanin gidan za a shigo ba har sai da maigadi ya wangale gate.
"Nasir ne!" Ta furta tana tsayawa.
"Waye Nasir?" Ya tambaya, ita kuma ta ɗan saka hannu tana sosa kai cike da kunya.
"Oh I understand, so ko dai na tafi?"
"No ka jira ku gaisa sai mu shiga ciki, Farhan ma tana son ganinka"
"Okay"
Suna tsaye ya ƙaraso, fuskar nan ta ci mur, shima Nasir ba laifi black beauty ne.
"Ke waye wannan?"
Murmushi ta yi duk da a tsorace take da yanayinsa. "Shi ne Affan da nake faɗa maka cousin bro...."
"Saurayinki dai" Ya furta da tsawa, kallonshi Affan ya yi cike da mamaki.
"Dama an daɗe ana faɗa min kina cin amanata ban yarda ba, ga shi yanzu na gani da ido na"
"Nasir wace irin magana kake haka"
"Asirinki ne ya tonu munafuka babu wani daɗin baki da za ki min"
"Karka sake ce mata munafuka"
"Idan na sake me zaka iya?"
"Zan saka a fitar da kai daga gidan nan"
"To bari na dake ta naga abinda zaka iya"
Affan bai gaskata ba sai daya ga ya kai hannu ya wanketa da mari.
Ɗan runtse ido ya yi lokacin ya ji Nasir na faɗin "Ai bata da wani daya fini, saboda na riga na mata abinda ba zata iya rabuwa dani ba, dama ka haƙura dan babu abinda ban sani a jikinta ba, so ko ka aureta guntuna ce."
Yana buɗe ido ya tsinkawa Nasir mari har biyu, sannan ya fuzgosa ya fara bugu, maigadi ya kwaɗa salati ita kuma tana kuka take roƙar Affan ya sake shi, da ƙyar ma'aikatan gidan suka raba lokacin har ya haɗa masa fuska da jini ya kuma ya ga rigarsa.
"Kin ga Farhan je kiyi driving Nasir zuwa asibiti"
"No need zan iya"
Ya kalli Affan "Baka ci banza ba" Yana gama faɗa ya wuce ya shiga mota ya tayar cikin ɓacin rai.
Affan sai lokacin ya gaishe da Anni. "Mu shiga ciki Affan"
"A'a zan wuce ne" Ya furta da dakakkiyar murya. Sannan ya miƙe ya wuce kawai, Ayda kuka kawai take saboda duka biyu ga mari ga tsinka jaka.
Kai tsaye gida ya nufa dan kan shi ya ji yana masa zafi tare da barazanar tarwatsewa, sai dai har ya ɗauki hanyar gida kawai ya juya akala ya nufi gidan su Sadiya. Tun a farkon layinsu ya kirata a waya ya ce ta fito.
Ta fara son Affan shiyasa ba zata iya masa musu ba, amma da sai ta ce masa "Ba zata zo ba, dan tunda Faruq ya je ya baje ta gaban Mameey ta kasa fita, da rana tana ji aka zo kiranta cin abinci amma baccin ƙarya ta yi, sai kawo mata Surayya ta yi ta dire, gashi har yamma ta kasa fita bare ta haɗa ido da wani,.
Saɗaf-Saɗaf haka ta fito kamar ɓarauniya, ta ji daɗi ganin babu kowa a parlour sai dai tana gaf da fita ta ji Mameey ta ce "Ina zuwa?" Sai da ta furgita, sai kuma ta runtse ido, bata juyo ba ta ce "Dama Affan ne yazo"
"Shi ne kike sanɗa kamar mara gaskiya"
"A'a"
"To kije idan kin dawo ina son magana dake" A sanyaye ta wuce.
Ƙofar motar ta buɗe ta shiga sannan ta kalleshi, ya kwantar da kujera sannan kuma bayanshi yana jikin kujerar. "Sadiya" Ya kira sunan da wata iriyar murya.
Kallonshi ta yi sai kuma ta ce "Lafiya kuwa?"
"Ina cikin damuwa" Sai kuma ya riƙo hannunta tare da buɗe idanunsa da suka yi jajir "I need you." Ya furta yana murza hannun, da ƙarfi ta fuzgi hannun cikin ɓacin rai ta buɗe motar sai ta ji taƙi buɗuwa, a rufe take ya yi locking ɗinta.
"Affan mene haka? Ka buɗe min mota na fita"
"Sadiya please..." Ya furta muryarsa na rawa.
"Ba zan iya aikata abinda kake so ba kawai ka bar ni na tafi"
Idanunsa ya buɗe ya dubeta "Wane abu nake so ki aikata?" Shiru ta yi saboda ta kama kanta.
"Sadiya! Talk please"
Kan ta ta ƙara saukewa ƙasa, shi kuma ya ce "Sadiya akwai wata wadda Mommyna take so na aura, yanzu haka daga gidansu nake, Sadiya a gabana wani banza yazo yana faɗin irin abubuwan da suke aikatawa tare, ban taɓa zina ba, ba zan iya auren mazinaciya ba, Sadiya ina sonki kuma bana so na rasaki, dan Allah ina so ki min alƙawarin kare kima da martabar iyayenki, kodan yaranmu"
Hannu ta saka ta rufe baki lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo mata, haƙiƙa ta yi masa mummunar fahimta, ashe shi ba wannan yake nufi ba.
"Ba zan taɓa aikata saɓo ba duk runtsi duk wuya, ko ba dan yarana da iyayena ba dan lahira zan kare mutuncina" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sauke.
"Tunda na fito daga gidan su Ayda sai yanzu na ji na samu relief"
Kawai ji ta yi kishi ya turniƙeta. "Mu biyu za ka aura?" Ta jefe shi da tambayar.
"Ke kaɗai ce Sadiya, naje ne kawai dan na bi umarnin Mommy kuma yanzu na samu hujjar da zan faɗa"
"Dan Allah karka faɗawa Mommy, kar ma ka kuma ɗaga maganar da kowa, ka rufa mata asiri kaima sai Allah ya rufa maka"
"Ke ta da ban ce Sadiya"
Murmushi kawai tayi tana goge hawayen daya zuba.
****** ******
"Faruq anya baka fara shan wani abu ba?"
Murmushi ya yi tare da faɗin "Idan ina sha ai zai nuna ni, Aunty Saddiqa kece last hope ɗina"
Zama ta yi kan hannun kujera "Yanzu idan da Yazid bai saketa ba ya zakayi kenan?"
"Ba zan taɓa dawowa Nigeria ba, kuma soyayyar ta ce za ta kasheni da sonta za a binneni"
"Idan kana wannan maganar sai na ga kamar a film"
"Hmmm! To shin mene laifina dan na ce ina sonta? Ni fa namiji ne"
Dariya Saddiqa ta yi ta ce "Sadiya fa ta girmeka, har wanka ta yi maka, sannan kuma tana da yara, abu ne mai wuya ta yarda da kai"
"Ni bana neman yardarta a yanzu, amma na san a gaba idan na kasance miji a gareta ai dole ta yarda dani"
"Innalillahi Yaro wai dagaske kaine?"
"Ni ne mana, Aunty Saddiqa dan Allah let's be serious"
"Okay! To yanzu kai karatu kake fa, kana nufin Sadiya ta jira har ka gama school?"
"Ni fa ko gobe a ɗaura, zan iya riƙe matata, ba dole sai da aikin gwamnati ba, zan fara ɗan business"
Dariya ta sake yi tare da faɗin "Kamar almara"
"Ba almara bace, yanzu dan Allah mene abin yi?"
"Ina ga ka shirya kawai ka je gurin Baffa"
"Kina ganin Baffa zai duba lamarin?"
"To zai iya cewa kayi yaro a aure, kai kanka ba a gama riƙon ka ba bare ka riƙe wani."
"Wallahi idan na auri Aunty Sadiya riƙon da zan yi mata ko Yazid bai yi shi ba, zan iya hana kaina idan har ita za ta ci ta ƙoshi."
Ganin dagaske yake, ya saka Saddiqa ɗaukar ƙudirin taimaka masa, sai dai ta umarce shi da kar ya bari kowa ya san tana da hannu akan hakan.
_*A Week Later*_
Shiru Mameey ta yi kuma kanta a ƙasa yake lokacin da Baffa ke mata bayani, bata katse shi ba har sai daya gama sannan ta ce "Baffa shi fa Faruq a yanzu haka karatu yake, kuma nan da wata biyu zai koma can Germany, idan har ya yi aure to waye zai riƙe matar?"
"Ya ce zai iya, wanda ya ce zai haɗiyi gatari sai a sakar masa ƙota"
"To da mene zai riƙeta, baya aikin komai, sannan uwa-uba Sadiyar nan ta girme shi fa"
"Khadija!"
"Na'am Baffa"
"Ki sani dan Sadiya ta girmi Faruq hakan ba zai haramta aure a tsakaninsu ba, ka da ki manta manzon Allah (SAW) ya auri Nana Khadija (R.A) yana saurayi ita kuma bazawara, kin ga idan Faruq ya yi haka kamar ya yi koyi ne da manzo (SAW)"
Sai dai ta numfasa sannan ta sake cewa "Dangin mahaifiyarsa za su ga kamar ni ce na saka ya auri Sadiya, sannan mutanen gari ma gani za su yi kamar na tauye musu"
"Dangin Dada Rabi zan yi magana dasu, su kuma mutanen gari ai ba dole sai an burge su ba. Na yanke shawara kuma har na yi magana da Habu da Isma'il mun saka ɗaurin auren ranar juma'ar nan mai zuwa, hidimar biki kuma za a iya saka rana a yi daga baya. Ba akwai gidan sa na gado anan ba?"
"Akwai amma ba a gyare yake ba"
"To sai a haƙura da tarewar yanzu sai a samu a mata passport"
Shiru Mameey ta yi bata sake cewa komai ba har ya gama tsare-tsarensa ya tafi.
*Bayan Sati Ɗaya*
A wajen adana motoci ya ajiye tashi, sannan ya fito jiki a sanyaye ya ƙarasa inda take. Tana ganin shi ta ƙara haɗe rai har ya samu guri ya zauna.
"Yazid! Ka san maganganun da kake faɗa kuwa?"
"Na sani saboda a cikin hayyacina na yi, kuma bana shaye-shaye"
"Kana ganin mai yuwuwa ne?"
Murmushin takaici ya yi tare da ɗora hannayensa akan table ɗin wurin.
"Ni a wajena kamar ya yuwu ne, babu wata barazana da za ta dakatar dani daga abin da na yi niyya. Sai dana rabu da Sadiya na gane kuɗi ba sa taɓa sayen farin ciki, na ɗauka kuɗi sune maganin matsalata amma dana same su sai matsalolin suka ƙaru. Bani da nutsuwa, haka yarana, a lokacin da nake talauci ma na fi samun kwanciyar hankali da nutsuwa, ban sani ba ko dan kuɗin na same su ne da hanyar cin amana"
Kallon shi kawai take tunda ya fara magana har zuwa lokacin daya kai aya.
"Yazid amma idan kana tuya kamar kana mantawa da albasa, kai kana tunanin abu mai sauƙi ne Sadiya ta yarda da kai?"
"Ni da Sadiya akwai yarda da kyakyawar fahimta."
Kai ta girgiza tana murmushi tare da faɗin "A baya kenan, amma ina mai baka shawarar kada ka tunkari Sadiya da wannan maganar, wallahi ina mai tabbatar maka mutuwar kasko za ayi"
"Ban fahimce ki ba?"
"Kai ka rasa Yaya Affan ya rasa, har gara Yaya Affan shi bai ma san komai ba dalilin haka zai iya sakawa ta aure shi"
"Haka kike gani?"
"Haka ne ma."
Miƙewa ya yi tare da ajiye mata mukullai a gabanta. "Wannan mukullan gidan da kika bani ne da kuma mota, dana shagon dana buɗe a kasuwa, takardunsu suna cikin motar ga ta can" Ya furta yana nuna mata motar da hannu. Juyawa ya yi tana kiran sunansa amma sam yaƙi ya saurareta.
*Saura shafuka biyu mu gama free pages, ku garzayo ku saya domin cigaba da karatu*
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 19```
Suna zaune a dining area suna cin abinci, sai dai ya lura da Lawisa kawai juya spoon ɗin take a cikin abincin amma sam taƙi ci, baya so ya yi mata magana dan kar Mommy ta fahimta, sai dai haƙonsa bai cimma ruwa ba dan Mommy ce ta ce "Ya naga kina cakula abincin kin ƙi ci?"
"Babu komai Mommy, kawai bana jin cin abincin"
"To me kika ci? Ko kuma daga asibitin kin wuce restaurant ne?"
"A'a Mommy akwai wata patient da aka kawo mana unconscious itane ta tsaya min a rai" Tana gama faɗa ta tashi ta wuce ɗakinta.
Mommy ta kalli Affan ta ce "Ko ka san mene ke damunta?"
"Tun ɗazu na lura da yanayinta amma sai na yi tunanin ko gajiya ce"
"Kana asibiti ai dama babu abinda ba zaka gani ba."
A zaune ya tarar da ita ta yi tagumi, ya ƙarasa bakin gadon tare da janye hannunta da ta ɗago kai ta kalleshi. "Na san abin da kika faɗawa Mommy ba gaskiya bane, ki faɗa min mene ke faruwa?"
"Yaya gaskiya na faɗa, kai ma ka san idan akwai wani abu kaine wanda zan fara sanarwa."
"Kin tabbata?"
Kai ta gyaɗa alamar eh.
Zama ya yi gefen gadon sannan ya ce "Mene ke damun ita patient ɗin wanda har ya hanaki sukuni?"
"Am...am..." Sai kuma ta saka hannu a wuyanta tana shafawa sannan ta ce "Dama ɗane ya mutu a cikinta"
Murmushi ya yi sannan ya ce "To ai ko ƙaramin yaro kika faɗawa haka ba zai yarda ba bare ni mai hankali."
"Yaya am sorry!" Ta furta tana goge hawaye.
"Sorry for what?"
"Na san na tafka babban kuskure dan Allah ka yafe min"
"Explain to me, ina jin ki what's goin on?"
Idanuwa ta ƙura masa sannan ta ce "Yaya dama....dam...." Sai kuma ta sake yin shiru. "Idan har baki faɗa min ba, kenan bani da wannan matsayin da kike faɗa"
Ji ta yi hawaye masu zafi sun zubo mata, ta danne zuciyarta sosai ta faɗa masa duk irin tuggun da ta haɗa har ya kai ga rabuwar auren Yazid da Sadiya. Miƙewa ya yi cike da mamaki yana kallonta, fuskarsa ta bayyana tashin hankali ƙarara. "Lawisa why?"
"Yaya na ga ka damu ne shiyasa" Ta furta a lokacin wasu hawayen suka sake zubo mata.
"Kina nufin da sanin Yazid lokacin da muka je har babarshi da ƙannensa suka zo, sannan zuwan da na yi na biyu wanda har na kai ƙanwar mahaifiyarsa station duk ya san da zuwanmu?"
"Wallahi Yaya ya sani, tun kafin mu taho zan ce yanzu zamu zo shi kuma idan ya kintata lokaci sai kawai su zo, kuma duk mun yi haka ne dan a kawar da zarginta daga saki, ko sakin daya mata za ta ga ba laifinsa bane tunda dama danginsa ba su ƙaunarta."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Lawisa duk ranar da Sadiya ta gano gaskiya ba za ta taɓa yarda babu hannuna ba, sannan kuma za ta tsaneni ne ba zan kuma yin wani abu da zai burgeta ba"
"Ko za ta gane ma, insha Allah sai bayan bikinku"
Ɗagowa ya yi a fusace ya kalleta, ita kuma da sauri ta sauke kai ƙasa.
"Baki kyauta min, sannan kin cutar da Sadiya idan har bata yafe miki ba to tabbas sai Allah ya saka mata"
"Na san na yi kuskure amma ni a lokacin bani da wani buri daya wuce na ga ka mallaketa saboda tsananin kamannin da suke da Nashwa."
"Kama da wane ai bata wane, duk da Sadiya ma tana da hali mai kyau amma dai ban ji daɗin wannan lamari ba." Yana gama faɗa ya miƙe tare da mata sai da safe sannan ya wuce.
Kwance yake ruf-da-ciki akan lafiyayyen gadonsa, ya rasa wane kalar tunani zai yi, mafita yake son samowa amma duk hanyoyin sun toshe. Idan ya ce zai faɗawa Sadiya gaskiya to ya tona asirin Yazid wanda za ta iya kallon abin a matsayin ya faɗa ne dan ya kare kansa kafin ta sani ta ɗauki mataki. Idan kuma ta sani da kanta za ta riƙa masa kallin maci amana kuma azzalumi. Wayarsa ya janyo ya tura mata text sannan ya lumshe ido yana jin faɗuwar gaba.
Jin wayarsa na ƙara ya saka gabanshi faɗuwa, dan a tunaninsa Sadiya ce, sai da ta kusa katsewa ya buɗe ido, ganin Ayda ce ya saka bai ɗaga ba, daya ga ta dame shi da kira kawai ya kashe wayar gaɓaɗaya.
***** *****
Tana shafa addu'a ta ji ƙarar shigowar text, hannu ta saka ta ɗauki wayar sannan ta buɗe.
_Sadiya! You should know that I love you, and my love is true. I did not come to you with the intention of deceiving you, and I was not part of any plan to deceive you, Allah is my witness to that. There is something that happened which I find difficult to explain to you, because you might think I was involved in a plan against you, but know that I truly love you, now and forever._
_Affan_
"Mene yake faruwa?" Ta furta a lokacin kuma ta yi dialing numbersa, sau uku tana bai ɗaga ba, sai dai hakan bai saka ta haƙura ba, ta kira ya kai sau biyar bai ɗaga ba dan haka itama saƙon ta tura masa.
_Affan, what is going on? I hope this text isn't about a breakup. Affan, you have to know that your love now means everything to me, losing you would feel like losing a part of my life. You started loving me because I resemble Nashwa, but as for me, it was your beautiful character that made me fall in love with you._
Tana turawa ta sauke ajiyar zuciya tare da fatan Allah yasa lafiya.
_Washe Gari_
Tun da ta farka take jin faɗuwar gaba, haka ta daure ta shiga wanka ta fito da niyyar ta shirya kawai ta tafi gidan Saddiqa dan gabaɗaya gidan nasu baya mata daɗi. Sai dai hayaniyar da ta jiyo ne ya saka ta yi sauri ta zura riga a gaggauce ta fita.
Mameey, Dada(mahaifiyar Faruq), sai ƙanwar Faruq da suke uwa ɗaya sai Surayya da Faruq ɗin ne a parlour, Dada na ta faɗa.
"Yanzu wannan za a aurawa ɗana?" Shi ne abinda ta faɗa lokacin da Sadiya ta fito. "To na rantse da Allah ki gaggauta bayar da umarnin a janye saboda a gidan Baffa na fara dira kuma ya ce aure babu fashi muddin ba daga nan aka janye ba.
Mameey ta girgiza kai kawai sannan ta ce "Daga nan ɗinma mun so hanawa amma Baffa ya ce tunda Faruq ya ji ya gani babu yadda muka iya, idan har Faruq bai janye ba babu yadda zamuyi"
"To idan ba asiri ba me Faruq zai yi da macen da take da har yara biyu, bazawarar da ta girme shi ma."
Cikin ɓacin rai Mameey ta mayar mata da martani "Na ɗauka Sadiya 'ya ce a gareki, na yi tunanin za ki kare Sadiya a ko ina, na yi tunanin sai inda ƙarfinki ya ƙare idan aka yiwa Sadiya gori amma sai ga shi da kanki kike faɗar maganganu"
"Dole ne na faɗa, da farko an ƙwace yaro an baki, yanzu kuma kuna son cutar da shi ta hanyar aura masa tsohuwa, saboda ku ci gadon shi"
"Dada dan Allah ya isa haka, ni babu wanda ya tursasa ni akan na auri Sadiya, ita nake so kuma ita naga zan iya rayuwa da ita" Sai lokacin Faruq ya yi magana cikin ɓacin rai.
Sadiya zama ta yi a ƙasa kawai ta fashe da kuka, dan bata da wani abu da za tayi daya wuce kukan.
"Faruq kar na sake jin ka kuma yin wannan furucin, ko mene ta faɗa mahaifiyarka ce, kuma tana da iko da kai"
"Ai bai sani ba, wataƙila yanzu ke yake tsammanin kece mahaifiyar" Ta kalleshi "Ka sani da ka auri wannan bazawarar gara na tsine maka na san duniya ka bi, akan zama da wannan"
A fusace Sadiya ta taso, "To me zan yi da shi? Mene yake da shi, har yanzu bai ma san ciwon kanshi ba shiyasa yake faɗar wannan maganganun, nima ba auren shi zan yi ba, saboda ni bazawara ce ina da ikon zaɓar mijin aure da kaina"
"Sadiya..."
"Mameey ki bar ni na faɗa mata, duk Faruq shi ne ya ja min wannan wulaƙancin"
"Kenan alfahari kike da kasancewa bazawara? Kuma ni kike kallo kina faɗawa maganganu?"
"Ni....."
"Idan kika sake magana ranki zai mummunan ɓaci Sadiya" Mameey ta furta a fusace.
Dada ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Faruq "Yanzu a haka kake son ɗauko yarinyar da take tsayawa gabana tana faɗar magana. Faruq kai kaɗai ne ɗana namiji, burikan dana ci a kanka suna da yawa, amma ka rasa wa zaka ɗauko sai wannan?"
Sadiya da sauri ta ƙarasa gaban Faruq "Wai Yaro duk kana ganin abinda ke faruwa? Ko dai ka fara shan wani abu? Yaro idan har baka so zumuncin mu ya ɓaci to ka janye maganar nan, Dada mahaifiyarmu ce, amma maganganunta sun fara tunzura ni, ka sani muddin aka tilastani na aureka a daren zan kashe ka." Tana gama faɗa ta juya da sauri ta koma ɗakinta, kan gado ta faɗa ta fashe da kuka a fili. Sai da ta yi mai yawa har muryarta ta dashe sannan ta miƙe zaune kanta ta ji yana wani irin sarawa. "Yazid me nayi maka? Wannan shi ne tukwuicin irin soyayyar dana nuna maka? Na rabu da komai ciki har da farin cikina duk dan na faranta maka amma kayi min sakayya da saki" Pillow ta damƙo ta kuwa ƙwalla wani gigitacce ƙara tare da kuka a lokaci ɗaya.
Shigowar Saddiqa kenan tana rarrashin Mameey akan abinda ya faru suka ji ihun Sadiya da sauri suka yi ɗakinta.
Mameey ta riƙota sosai lokacin tana ta ƙara ƙwalla ƙara kamar wadda bata hayyacinta.
"Sadiya...!" Mameey ta furta tana jijjigata a lokacin taga idanunta a juye suke bata cikin hayyacinta. "Saddiqa muje ku kaita asibiti kamar bata cikin hayyacinta, Surayya ɗauko hijabi ki saka mata. Da sauri ta ɗauko Mameey ta ɗauketa ta kai motar Saddiqa.
Suna zaune sun ƙura mata ido tana bacci lokacin an saka mata drip. Wayarta ta fara ringing, ta kalla "Affan ne ke kiranta" Cewar Surayya.
"To ki ɗaga sai ki sanar masa bata da lafiya tana asibiti"
Tana sanar masa ya kuwa ce ga shi nan zuwa.
"Wai Dada wulaƙanci sosai ta yi?" Saddiqa ta tambaya tana kallo Surayya.
"Wallahi mantawa da alaqa ta yi ta karta rashin mutunci, nima ganin Faruq a tsaye ne kaɗai ya saka ban mata rashin kunya ba.
"Shima Faruq kafiya ya haƙura mana, wallahi Sadiya bama sa'ar auren shi ba ce"
"Uhmm! Ni kaina haka na ce a lokacin da Aunty Sady na ƙoƙarin haɗamu na ce ai ni na fi ƙarfin Faruq, ashe shi ita yake kallo bama ni ba"
"So dai bai masu halacci ba, yanzu ga shi ana neman lalata zumunci"
"Wallahi kuwa."
Ko mintuna talatin ba ayi ba sai ga Affan tare da Mommy da kuma Lawisa. Surayya ta bawa Mommy kujera ta zauna cike da mamakin kamanninta da Nashwa.
"Ya jikin nata?" Affan ya tambaya.
"Da sauƙi, ai bamu daɗe da zuwa ba, kuma ana saka mata drip ta samu bacci"
"Amma me doctor ya ce?"
"Kawai damuwa ce, ka san Aunty Sady akwai zurfin ciki, idan kuma abin ya yi yawa sai ya zamar mata damuwa"
"Allah ya ƙara sauƙi"
"Amin ya rabbi"
Sun ɗan juma a asibitin kafin su tafi, da yamma kuwa Mameey tazo, sai dai duk budirin da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 15