idan ba night duty nake ba bata yarda fa"
"It's ok Allah ya kaimu gobe"
"Amin ya rabbi."
****** ******
A bakin ƙofar ta gansu sun yi cirko-cirko, lokacin Surayya ta shigo dan har da ita ta gani. Gaban Saddiqa ta ƙarasa da ledar magunguna da ta tafi karɓowa ta kalleta "Lafiya kuwa?"
"Wai daga ɗan surutun da mukayi har jininsa ya hau, shi ne aka saka muka fito yanzu haka Likitoci biyu ne a ciki"
"Subhanallahi. To ai naga ba wata magana ya yi da yawa ba"
"Ke da kika san dama ba lafiya ne da shi ba, kuma fa abin har ya fara taɓa zuciyar shi"
"Gaskiya Faruq baya kyautawa, ya faɗa mana amma yaƙi faɗa mana ko wace ce bare mu san abin yi"
"Mun yi magana da shi jiya, yake ce min faɗar ma bata da amfani na takura masa shi ne yake cewa ai tayi aure"
"Matar aure?" Sadiya ta faɗa da mamaki.
"Yi ƙasa da murya kar Mameey ta ji, ya ce dan Allah kar na sanar mata"
"Tashin hankali" Ta furta tare da dafe goshi.
Fitowar likita ya saka suka yi shiru.
"Dr Allah ya sa dai jikin na shi da sauƙi"
"E, da sauƙi alhamdulillah, ina magungunan?"
Da sauri Sadiya ta miƙe ta ba shi sannan ta koma ta zauna.
Ya shiga ya ɗan juma a ciki sannan ya sake fitowa. "Wace ce Sadiya?"
"Ni ce" Ta furta tana miƙewa.
"To zo mana" Ya furta yana komawa ciki.
A sanyaye ta turo ƙofar yana zaune ma ya jingina bayanshi da bangon gadon.
"Wannan ce?" Dr ya tambaya yana nuna Sadiya, shi kuma Faruq ya gyaɗa kai.
"Sadiya bismilla zauna mana"
Zama ta yi sannan ta ce "Jikin na shi da sauƙi?"
"E, ku san haka"
Ɗayan Dr ya faɗa tare da jan kujera ya zauna gabanta.
"Sadiya ko?"
"E, ni ce"
Shiru ya yi sannan ya ce "Kin san kece sanadin ciwon ɗan uwanki?"
"Ni kuma? Meyasa na zama sanadi?"
"Saboda kece wadda yake so kuma ya kasa furta mata"
Cikin tsananin tashin hankali ta miƙe tsaye, ta kai dubanta ga Faruq ta ga ya sauke kai ƙasa.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[6/16, 8:51 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty_
Facebook@SaNaz Deeyah
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 7```
Murmushi ta yi sannan ta kalli Dr ta ce "Ba gaskiya ya faɗa ba, ya ɓoye ne kawai dan baya so kowa ya sani"
"Ba mu kiraki nan dan mu yi drama ba Sadiya, tabbas ya shaida mana kece sai dai kuma ya ce ba zai iya faɗa miki ba saboda kina da aure"
"Dagaske ne Faruq?" Ta furta tana kallonsa, sai dai har lokacin kanshi yana ƙasa.
"Faruq ka faɗa min cewar ƙarya ne abin da kunnuwana ke ji"
Hawaye ta ga sun zubo daga fuskarsa, itama sai lokacin ta ji hawaye masu zafi a kuncinta
"Faruq ni?" Sai kuma ta dafe kai tare da zama a kujerar da ta tashi.
Dr ya kalleta ya sake cewa "Bama so ya yi surutu da yawa, mun saka shi ya amayar da abin da ke ransa ne ko zai samu sukuni saboda ciwon yana ƙoƙarin taɓa heart ɗinsa."
Miƙewa Sadiya tayi ta koma gaban Faruq "Ɗago ka kalleni Yaro" Ta furta da muryar kuka, sai dai bai ɗago ba.
"Yaushe hakan ta faru? Yaro ka san ko bani da aure ko ace ni budurwa ce ai nafi ƙarfinka saboda ni yayarka ce, shekaru har uku na baka a duniya, kana yaro ni ce nake maka wanka da tsarki sannan na goyaka babu adadi a bayana, dan baka da kunya ni za ka kalla da yarana har biyu kace ni kake so?"
"Namiji baya taɓa fin ƙarfin mace Aunty Sady" Sai lokacin ya yi maganar a sanyaye.
"Oh haka kace, to ka sani in zaka warke daga ciwon nan ka cigaba da rayuwa ka warke in kuma son za ka cigaba to ga fili ga mai doki, ni bama zaka ƙara ganina a asibitin nan insha Allah, tunda na lura baka da hankali" Tana gama magana ta juya a fusace ta fita.
Gabaɗaya juyowa sukayi kan ta suna tambayar lafiya. Ta saka hannu ta goge hawaye sannan ta kallesu "Jikin da sauƙi"
"Amma shi ne kika fito kina kuka?"
"Maneey ya ƙi faɗa min wadda ya...." Sai kuma tayi shiru.
"Ya kuma kika yi shiru"
"Ba komai Mameey, zan tafi gida"
Kallonta Saddiqa tayi sannan ta ce "Haba gaskiya ba lafiya ba, kuma kin san ba zamu taɓa bari ki tafi gida a haka ba."
A daddafe ta kama kujera ta zauna sai kuma ta fashe da kuka, hakan ya saka dole Mameey ta nufi ɗakin hankali a tashe.
Tana shiga lokacin Doctors ɗin suna ƙoƙarin fitowa.
"Yawwa Hajiya mun samu ya yi bacci, dan Allah kar a yi hayaniya da yawa"
"Dr dan Allah ka faɗa min gaskiya mene ke faruwa mene ya sa kuka kira Sadiya kuma me aka faɗa mata wanda ya ɗaga hankalinta har haka"
"Babu komai kawai ya buƙaci ganinta ne, ita kuma tana shigowa ta fara kuka"
Bata gamsu da abin da suka faɗa ba amma ba ta so ta yi musu dasu shiyasa kawai ta ƙyale.
Ko da suka shigo Sadiya bata fi mintuna ashirin ba ta tafi gida. A gida ma kukan tasha ta godewa Allah, Yazid ya yi juyin duniya amma taƙi faɗa masa abin da ke faruwa, ta yi alqawarin barin abin a ranta har abada.
_Bayan Sati Ɗaya_
Tana zaune da yamma a tsakar gida tana gyarawa Ihsan gashi sai ga kiran Saddiqa.
"Yanzu nake maganarki a raina"
"Hmm! Baki da kirki Sadiya"
"Me kuma na yi?"
"Ai kin fi kowa sani, yanzu Sadiya na faɗa miki yau jirgin su Faruq zai tashi amma Sadiya tun lokacin nan baki sake dawowa asibiti ba, kuma ai kin zo ma kuyi sallama ko"
"Wai yau ne?"
"Ban sani ba, kar ki raina min hankali mana, ko jiya na faɗa miki kuma tun ana processing ai na faɗa miki"
"Afuwan Saddiqa ni kam sai ana mini uzuri"
"Kin kyauta ai" Ƙit ta kashe, Sadiya da sauri ta bita sai dai bata ɗaga ba, ta sake kiranta sai taga ta yanke kiran, har ta ji ba daɗi sai kuma ga Saddiqa ta biyota.
"Dan Allah kuyi min afuwa ba zan samu damar zuwa ba, Allah ya sawwaqe ya ba shi lafiya"
"Amin amma dama ai kin makara dan sai da jirginsu ya tashi sannan muka juyo yanzu haka zan mayar da su Mameey gida ne kuma kafin na wuce zan biyo ta gidan naki"
"To sai kin zo" Tana kashewa ta sauke ajiyar zuciya.
"Faruq kenan! Allah ya baka lafiya amma ka ɗauko dala ba gammo."
Ɗan maƙotansu ne ya shigo sai daya gaishe ta sannan ya ce "Sallama ake a waje"
"Kace musu baya nan"
"Ance dake ake sallama"
"Ni kuma? Su waye?"
Sai kuma ta sake kallon yaron "Kace ina zuwa" Tana gama faɗa ta miƙe.
"Ihsan ɗina ki zauna ina zuwa kinji" Yarinyar ta gyaɗa kai ita kuma ta ja hijab a igiya ta zura sannan ta fita.
Tun da Affan ya ƙyalla ido ya ga fitowarta gabansa ke faɗuwa, domin har yanayin tafiyarta sai ya ga kamar Nashwa ce.
Ita kuwa mamaki kawai take tana tunanin ko wani ne a dangin Mameey ko Abba yazo ganinta, dan ta san sune masu ƙunbar susa. Sai dai tana ƙarasawa ta ga Lawisa sai taji gabanta ya yanke ya faɗi, ta ji kamar ta juya amma kawai ta dake.
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumussalam" Ya amsa ita kuma Lawisa ta ce "Kiyi haƙuri amma Yayana ya matsa sai na kawo shi gare ki"
"Amma...."
"Ya sani na faɗa masa ke matar aure ce kuma ba Nashwa bace"
"Ina wuni" Sadiya ta furta tana kallon Affan. Yayinda shi kuma ya juya yana kallon Lawisa da mamaki, dan bata faɗa masa Sadiya na da aure ba.
"Ta ce min shekara guda da faruwar abin ko?"
Kai ya ɗaga dan ya kasa cewa komai.
"Allah sarki, ni kum ka ga shekarata 6 da aure ina da yara biyu. Ina maka jaje Allah yajiƙanta da rahama ya baka madadinta."
"Amma kamarku ta ɓaci, sai dai ita Nashwa tana da fashin goshi kuma tana da ƙullar hanci, da ace bata dasu kece mai su da sai na ce kece Nashwa, kin yi ɓula da fashin goshi ne dan kiyi ɓadda kama"
"Allah sarki, ai da sisternka ta nuna min naga muna yanayi sai dai ta fini kyau"
Murmushi ya yi wanda sai a lokacin ne ya yi.
"Amma ni har yanzu tunani nake ko dai kuna da alaqa ko kuma 'yan biyu ne"
Dariya tayi ta saka hannu ta rufe baki.
"Sai dai alaqa amma ni kam ni ɗaya ce"
"Yaya ina zuwa bari na amsa waya" Lawisa ta faɗa gami da barin wurin.
Shi kuma ya mayar da kallonsa ga Sadiya "Komai naku iri ɗaya har murmushin ku"
"Dan dai muna kama shiyasa kake ganin kamar haka"
"Kin san Allah lokacin da kika fito sai dana ji faɗuwar gaba na kuma shagala da kallonki astagfirulla ke matar aure ce amma fitowarki idanuwana Nashwa kawai suke nuna min."
"Lallai kana ji da Nashwa zan so na ji labarinta"
"Idan har mijinki ya amince zan sake dawowa har gida ko kuma ki bani numberki zan baki labarin tun daga haɗuwarmu har zuwa rasuwarta"
"Allah sarki, to bari na karɓi numberka, idan yaso in ya bani dama sai na kiraka"
"To shi kenan"
Miƙa masa waya tayi sai dai ɗaga idon da za tayi taga Umma da yaranta sun fito daga napep. Ji tayi gabanta ya faɗi saboda irin kallon da taga suna yi mata, yana bata wayar daidai lokacin Fatima da Maryam suka ƙaraso.
"Allah ya toni asirinki dai" Fatima ta faɗa tana watsa mata kallon banza.
"Da mijinki amma kina bin wasu mazan to wallahi kamar kinyi a gaban Yaya" Maryam ta faɗa, shi kuma ya kalli Maryam ɗin rai a ɓace ya ce "Ke ki iya bakinki"
"Idan taƙi fa?" Cewar Fatima.
"Duka zan mata kuma in saka a rufe min ita"
Shiru Fatima tayi, ita kuma Maryam tayi ƙwafa sannan ta ce "Za ki gane kurenki" Tana gama maganar ta juya Fatima ta rufa mata baya, dama mai napep ɗin bai tafi ba, ganin har Umma ta shiga ya saka Sadiya saurin juyawa ta ƙarasa da sauri.
"Umma ina wuni"
"Ka da ki sake kirana da Umma dan ni babu karuwa a 'ya'yana" Ji tayi hawaye ya zubo mata, ta ce "Umma wallahi yadda kike tunani ba haka bane"
"Kaga mai adaidaita mayar damu inda ka ɗauko mu"
"Umma dan Allah..." Ganin mai adaidaita ya tayar yana neman kassarata saboda ta riƙe ƙarfen machine ɗin ya saka ta saki, suka ja suka wuce, hannu ta saka tana goge hawaye a daidai lokacin Affan ya ƙaraso gabanta.
"Dan Allah ku tafi kar ku ja min matsala" Ta furta lokacin wasu hawayen suks ƙara cika kwarmin idanuwanta.
"Su waye wannan?"
"Surukata ce da ƙannen mijina" Ta faɗa a lokacin ta ji wasu sabbin hawaye.
"Yaya lafiya?" Lawisa ta faɗa tana ƙarasowa wurin, ta kalli Sadiya ta ce "Mene yake faruwa ya naga tana kuka?"
"Mother Inlaw ɗin ta ne tazo suka mana tijara"
"To akan me?"
"I don't know"
Murmushin ƙarfin hali Sadiya ta yi kafin ta ce "Kin ga Sister nagode sosai amma dan Allah ku tafi, nima yanzu na bar yarinya ita kaɗai a gida"
"Ai ba zamu barki a wannan yanayin ba"
"Idan baku barni ba, zai iya jawo min matsala dan Allah" Ta ƙarasa tana haɗe hannayenta .
"Yaya muje" Lawisa ta furta tana kallonsa, shi kuma yayiwa Sadiya ƙyar.
"Mu tafi mu barta in this situation?"
"Kar ka damu Yaya muje kawai"
Sadiya dai da sauri ta juya ta shiga gida Affan kuma ya sauke ajiyar zuciya.
Tana shiga ta zauna tare da dafe goshi, sai kuma ta sauke ajiyar zuciya tare da kafe guri ɗaya da ido.
***** *****
"Amma kina ganin hakan ba zai ja mata matsala ba?"
"To ban dai sani ba amma bana fatan haka"
"Dole zan ƙara bibiya daga baya inji, Lawisa nagode kin bani madadin Nashwa duk da ta kasance matar aure amma zan yi ƙoƙarin kyautatawa yaranta ko dan Nashwa"
"Yaya kana son Nashwa da yawa, Allah dai ya gafarta mata"
"Amin ya rabbi, me sunan yaran kuma shekara nawa?"
"E to! Ƙaramar dai bata wuce 3yrs ba babbar kuma ban taɓa ganinta ba."
"It's ok. Amma dai kamar suna fama da matsin rayuwa"
"Kuma fa a hakan gidansu ba laifi suna da hali amma ta auri talaka, a yadda aka bani labari ma ance mamanta har yau bata son auren"
"To ke ina ruwanki da jin gulma, tunda dai tana son mijinta kuma suna zaune lafiya ki barsu abin su."
Murmushi ta yi bata ƙara cewa komai ba har suka isa gida.
"Ya naga kun dawo cikin fara'a Affan kayi kyau sosai ka warware"
Ɗan sosa kai ya yi sanan ya zauna kujera.
"Mommy albishirinki"
"Goro"
"Mommy naga mai kama da Nashwa sosai Mommy kamar ta ɓaci"
"Mai kama da Nashwa fa kace?"
"Mommy dagaske bari ki ga hotonta" Lawisa ta faɗa tana buɗe wayarta. Shi kuma Affan murmushi kawai yake.
Lawisa ta miƙawa Mommy wayar, ta kalla sannan ta ce "Lallai suna fuzgen kama sai dai wannan ta ɗan fi Nashwa duhu"
"Ni kaina dana ganta nayi tunanin Nashwa ce Mommy"
"Allah sarki, ita mene sunanta kuma ɗiyar waye?"
Lawisa ta kalli Affan shi kuma ya ɗan gyara murya sannan ya ce "Sunanta Sadiya amma bamu gama sanin komai a kanta ba"
"Allah ya sa tagari ce"
Da ƙyar suka iya furta amin. Miƙewa Affan ya yi ya wuce bedroom ɗinsa, da sauri Lawisa ta bi shi.
"No matter what karki yarda Mommy ta san yarinyar nan tana da aure"
"Meyasa?"
"Saboda za ta fara nasiha kuma zata haramta min taimakon da nake son yi"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "To shikenan" Sai kuma ta juya ta bar ɗakin.
***** *****
"What!? To ke wane tsautsayi ne ya saka kika fita"
"Wallahi Aunty Saddiqa kawai ni ban ma sani ba"
"Yanzu mararsa mutuncin Allah kaɗai ya san yadda za su ƙara rura abin dan ma shi Yazid ɗin ya yarda dake"
"Wallahi na yi dana sanin fita, nifa har yanzu jikina tsuma yake."
"Ki kwantar da hankalinki insha Allah ba abinda zai faru"
"Allah yasa, hala shi ne abinda ya hanaki zuwa airport?"
Ganin ta samu mafaka ta ce "E shi ne, tun ɗazu ina zaune na kasa sukuni"
"Aikuwa Faruq yana ta maganarki kamar ma kece favorite sister'n Faruq, har jirginsu zai tashi sai ya ce min in kula dake tausayi kike ba shi"
Iska ta furzar sannan ta kalli Saddiqa ta ce "Allah ya ba shi lafiya"
"Amin, and ya bani letter ya ce dan Allah kar na karanta, da Auta za ta karɓa tun a asibiti sai ya ce a'a shi ya san idan ya bawa Auta sai ta buɗa"
Murmushi Sadiya ta yi tare da faɗin "Auta anji jiki"
"Wai ina Najma ne sai Ihsan na gani tana wasa"
"Sai 6 za ta dawo daga islamiyya" Sadiya ta faɗa tana karɓar letter da Saddiqa ta fito daga jaka.
Saddiqa ta ɗan taɓe baki ta ce "Wai Yazid ƙiri-ƙiri yaƙi yarda na riƙe Ihsan fisabilillahi ya yi adalci kenan?"
"Kin san Yazid akwai ƙwalafacin 'ya'ya kiyi masa uzuri"
"Uhmmm
"Kiyi haƙuri Aunty Saddiqa zan ƙoƙarin fahimtar da shi ko Ihsan ɗin ya baki"
"Allah ya sa, kin ga bari na tashi na tafi"
"Tun yanzu?"
"To yaushe kike so na tafi"
"Bayan isha'i in mun gama hira"
"Ai ban tambaya ba da nayi miki zaman"
Murmushi kawai tayi.
*_09:30pm_*
Har ta fara bacci dan tuni ta yi wa yara shimfiɗa itama ta yi, jin alamun shigowarsa ya saka ta buɗe ido tare da kunna hasken fitilar wayarta. A hankali ta miƙe sannan ta fita tsakar gidan, lokacin shi kuma yana ƙoƙarin shiga ɗayan ɗakin.
"Abban yara ka shigo"
"E" Ya amsa a gajarce sannan ya shige, ita kuma da sauri ta mara masa baya, yana ƙoƙarin cire kaya ta shiga.
"Yau ka yi nisan kiwo"
Bai tanka ta ba ta ƙara da cewa "Kodai na ɗora ruwan zafi kayi wankan dan naga kamar ana ɗan sanyi"
"Ban saka ki ba" Sai a lokacin ta fahimci ransa a ɓace yake.
Tana zaune har ya yi wanka ya fito, ya fara shiryawa ta tashi da nufin ta taimaka masa kamar yadda suka saba amma sai ya dakatar da ita.
"Abban yara lafiya kuwa?"
"Babu komai"
Shiru ta ɗan yi tana daga tsaye ya zira jallabiya yana ƙoƙarin kwanciya ta ce "Abinci fa?"
"Na ƙoshi"
"Amma me ka ci da har zai ƙosar da kai?"
"Sadiya dan Allah ki bar ni na huta a gajiye nake, ki tashi ki fita a ɗakin nan"
"Abban yara yau ni kake kora?"
Zaune ya miƙe sannan ya ce "I need privacy! Stay away from me please"
Ɗan zaro ido ta yi har sai da ta gigice ta rasa ina ce ƙofar fita, kafin daga bisani ta gano ta, ta tsaya jikin ƙofar ɗakin tana sake kallon shi kafin ta fice.
Ranar bata iya bacci ba, duk da ta dawo ɗakin ta tarar da shi ya yi bacci abinsa kuma baccin ma ya yi nisa, ta san halinsa sarai damuwa hana shi bacci take, wannan dalilin ne ya saka ta san lallai ƙila ya huce, sai dai tonowa da zuwan su Lawisa ya saka ta faɗa sabuwar damuwa domin tunaninta gabaɗaya ya karkata akan Umma ta kirashi ta sanar da shi. Daren ranar dai haka ta ɓata shi ta saƙa wannan ta kunce wancan. Tunda aka fara kiran asuba take ta son ta ji motsinsa amma bata ji ba, dan haka ta miƙe ta fita ta yi brush ta yi alwallah sannan ta je ɗakinsa. A zaune ta tarar da shi yana miƙa da alamu lokacin ya tashi daga bacci.
"Ka tashi kenan, nazo na tashe ka ne dama dan ban ji motsinka ba"
Da ido ya bita, ita kuma a sanyaye ta juya ta fita.
Kwana uku ya jera yana wannan sabuwar ɗabi'a ta rasa gane kan gadonsa, idan ya fita da safe baya dawowa gidan sai sun fara bacci. Yau dai ta saka a ranta za ta masa magana ta ji laifin da tayi masa, ta zauna batayi bacci ba har ya dawo duk da ko da tayi bacci idan taji shigowarsa sai ta farka.
Tana jin shigowarsa amma batayi yunƙurin tashi ba, tana ji ya fito ya ɗiba ruwa ya yi wanka ya gama shiri tsab sannan ta tashi ta nufi ɗakin nasa. Ko da ta shiga waya ta tarar yana yi duk da wayar tasa ta ga yana yi ne da ɓacin rai, tana shiga ya kashe.
Ta ajiye flask da plate a gabansa. "Abban yara sannu da zuwa" Ta furta tana ƙoƙarin buɗe flask ɗin.
"Bana buƙatar abinci."
Cak ta tsaya, sai kuma daga baya ta janye flask ɗin a sanyaye.
"Dama ina son magana da kai ne"
"Sadiya na dawo a gajiye ina buƙatar na huta"
"Dan Allah Abban yara kayi haƙuri ka faɗa min laifina, wannan hukuncin ya yi min tsauri da yawa"
"Laifin me?"
"Abban yara wallahi na tuba ka rufa min asiri da wanne zanji? Ka ƙaurace min, ka kuma ƙauracewa yaranka idan laifi na yi ya kamata ka faɗa min sai na gyara amma wannan hukunci ya yi min tsauri na kasa jurewa." Ta furta tana share hawayen da suka zuba mata.
"Sadiya" Ya furta a tausashe, kallonshi ta yi sai kuma tayi ƙasa da kai.
Hannu ya saka cikin aljihunsa ya fito da takarsar ya ce "Waye ya baki wannan?" Gabanta ya faɗi ta ƙurawa takardar ido.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[6/18, 1:56 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 8```
"Tambayarki nake?" Ya ƙara maimaitawa.
Jikinta a sanyaye laɓɓanta sun yi nauyi ta kasa ɗaga su bare har ta faɗa masa.
"Umma ta kirani tayi faɗa sosai akan ta ganki a ƙofar gidan nan da wani namiji da bata san shi a danginki ba, kuna hira sai dariya kike; ta ce min tana kallo kika ba shi wayarki ya saka miki numbersa, Sadiya lokacin da aka faɗa min na rasa wane tunani zan yi, na san ba za ki ci amanata ba kuma Umma ba zata min ƙarya ba, to waye zan yarda da shi, da wannan tunanin na dawo gida, na kwanta kenan na ji kamar takarda a ƙasan fulo ina ɗagowa naga ita ce, na kuma duba naga kalaman soyayya ne kuma har yana cewa har abada ba zai daina sonki ba kuma zai jiraki tsawon rayuwarsa, idan kuma ance ya mutu to soyayyarki ce ta yi ajalinsa, Sadiya na san kin ajiye a ɗakin nan ne dan na gani kuma na gani na ɗauka, kullum sai na karanta kuma a halin yanzu na gama haddaceta, hatta inda aka saka comma da fullstop ina iya gane gurin komai yana cikin ƙwaƙwalwata, Sadiya dama bakya sona?"
A hankali ta ɗago idanuwanta, hawaye sun mata sharkaf a fuska ta kalleshi, shima ita yake kallo.
"Ban taɓa haɗa soyayyarki da wata 'ya mace ba, na jure baƙin ciki da takaici dominki, na ji a raina iya wuya zan zauna dake, Sadiya babu abinda ba a faɗa min ba a kanki har a gabanki ana faɗa cewa ke mai farar ƙafa ce, Umma da 'yan uwana tunani suke aurenki shi ne ya ruguza ni amma duk abin da ake faɗa shanyewa nake, sai gashi kin min sakayya da wannan."
"Wallahi yadda kake tunani ba haka bane Abban yara"
"To ya ya ne?"
Hannu ta saka tana goge hawaye duk da bai bar zuba ba sannan ta ce "Ina zaune ina gyarawa Ihsan kai kawai sai aka yi sallama a waje, har ma na ce a shigo sai yaron da aka aiko ya ce maza ne shi ne na fita, sai kuma naga wannan Lawisar ce wadda tazo gidan nan har ta ce ina kama da matar wan ta, tare da shi suka zo, wallahi ba dan ina so ba na tsaya ka san wulaƙanci ba halayya ta bane, ba zan ƙaryata Umma ba amma har na gama magana dasu ban wani saki jiki ba, ita kuma number roƙota ya yi akan na ba shi tawa saboda yana so yaja yarana a jiki sai na ce masa ba zai yuwu ba saboda ni matar aure ce amma zan karɓi tashi idan ka bani izni sai na kirawo shi duk da na san ba mai wuyuwa bane tunda babu wani alaqa ta jini, zan ɗauko maka wayata ma ka duba, wallahi ka tambayi su Shamsu mai wanki sun ganmu a tsaya dani da shi da ƙanwarsa ne, sai dai a lokacin da Umma tazo ƙanwar ta tafi amsa waya." Ta saka hannu tana share hawayen da ya mata sharkaf a fuska sannan ta dube shi.
"Ita kuma takardar bata da alaqa da su, ranar da Faruq ya bar ƙasar ranar ne suka zo kuma a ranar ne Aunty Saddiqa ta kawo min takardar kuma wallahi ko ita bata san mene a ciki ba, sannan babu wanda ya san abin da ke faruwa, ada na yi niyyar na ɓoyewa na barwa zuciyata amma a yanzu zan sanar maka komai." Ta numfasa sannan ta ce "Ciwon da Faruq yake fama da shi to so ne ya jawo masa, ni da Saddiqa har da Surayya mun yi ƙoƙarin ya sanar mana ko wace ce amma yaƙi faɗa, dama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 15