min taɓi ne wahala na gaba a lokacin da ciki zai girma ya fara rinjayata"
"Baddy na faɗa miki bana son kiyi planning"
"Gaskiya sai na yi"
"Oh ina faɗa kina faɗa?"
"Sorry" Ta furta rai ɓace.
Har suka ƙarasa gida babu wanda ya kuma yi wa wani magana, yana sauketa ya juya yaja mota fuuu ya fita.
"Ai wallahi duk fushin da zakayi ka yi ka gama amma planning kamar na yi na gama."
_*Dare*_
Affan da Madam dai sun samu saɓani, dan gabaɗaya tun daya dawo da yamma ya ga babu fuska sai ya yi side ɗin Mommy, sai dare ya shigo kuma bai ganta a parlour ba ya san tabbas tana bedroom. Kai tsaye ya nufi can, a zaune ya ganta tana waya ya ɗan tsaya yana jira ta gama. "To duk abin da kuka ga dama ku yi, ina ruwanku? Ko ana dole? Mijina ne fa bana wani ba kuma ba dole sai na gayyaceta bikina ba, haba abu ɗaya yaƙi ci yaƙi cinyewa wata nawa ana abu ɗaya, ita abin ya dama ni ban ma san tana yi ba." Tsaki ta ja ta kashe wayar, ya san tabbas akan Aisha ake magana, dan shi kansa yana mamakin butulcin da tayiwa Aisha.
"Madam" Shi ne sunan da yake kiranta da shi a duk lokacin da suka samu saɓani ya kuma fahimci tana ta haɗe fuska. "Na shigo ban ga abinci ba" Ɗan ƙara haɗe rai ta yi kamar ba za tayi magana ba sai kuma ta ce "Ban yi girki ba, na yi tunanin a gurin Mommy za ka ci" "Amma yanzu idan naci a wurin Mommy bayan kina gida me kike tunani?"
"Babu, saboda ni bana kawo komai a raina" "Badriyya wai mene haka?"
"Komai ma Affan" Ta furta a hasale. Kai ya ɗan girgiza sannan ya wuce ya bar ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya wuce ya yi wanka ya shirya ya ɗauki key ɗin mota ya fita.
Restaurant ya nufa ya yi order na tuwon semo miyar agushi duk da baya son cin abinci mai nauyi amma da aka kawo masa menu sai ya ji kawai yana sha'awa, ya saka aka kawo masa black tea. Har ya fara ci kawai yarinyar nan ta faɗo masa a rai ya janyo waya ya kirata, sai dai har ya mata 2 missed calls bata ɗaga ba, ya ajiye wayar ya cigaba da cin abincinsa. Yana gamawa kai tsaye gida ya koma.
A parlour ya tarar da ita tsaye ta kama ƙugu, ya kalleta ya kuma kauda kai zai wuce ta ce "Affan daga ina kake?" Da mamaki ya juyo ya kalleta. "Daga ina nake?" Ya maimaita sannan ya yi murmushi "Ni ne zan miki wannan tambaya in kika fita ba tare dana sani ba amma ba ke ba, saboda ke a ƙarƙashin ikona kike" Yana gama faɗa ya wuce, ta bi shi da kallo tana faɗin "Nima ina da haƙƙi a kanka ai" Bai bi ta kan ta ba ya wuce, yana kuma shiga ɗaki ya saka masa key ya yi locking saboda ba zai iya da faɗanta ba. Akan gado ya kwanta ya fara tunani, mamaki yake yadda ta koma haka, farkon soyayyar shi da Badriyya ya san tana da kunya, haƙuri sannan mace ce da magana ma ba ta dameta ba, shiyasa har yake tunanin ita ɗin miskila ce amma kuma suna yin aure sai halayenta na gaskiya suka fara fitowa, rashin mutunci da rashin ganin darajarsa, zai wuya su rufa wata guda ba tare da sun samu matsala ba. "Why!" Ya furta a fili da juya kwanciyarsa. Kiran daya shigo wayarsa shi ne ya katse masa tunani, ya yi rejecting sannan ya bi kiran.
"Assalamu alaikum!" Ya ji sassanyar muryarta ta doka sallama. "Wa alaikumussalam!"
"Ina wuni"
"Lafiya lau ya kike?" "Alhamdulillah, ka kira bana kusa da wayar"
"Ayya ba damuwa, ya Auntyn ki fatan ta sauka lafiya?" Sai kawai ya ji ta fashe da kuka, zaune ya tashi hankali a tashe. "Lafiya mene ya faru?" Cikin kuka take faɗa masa Allah ya mata rasuwa bayan ta haihu ta samu ɗa namiji. "Kiyi haƙuri, Allah ya mata rahama"
"Shi kenan yanzu na rasa gata, bani da wanda zai tallafeni" Ta furta tana sake sakin wani kukan. "Am..am so sorry insha Allah ba za ki rasa gata ba, kiyi shiru kiyi haƙuri kin ji, kin ga kina ɗaga min hankali ga shi dare ya yi bare na zo gareki dan Allah kiyi haƙuri" Ta cigaba da shashsheƙa, "Zan kiraki gobe sai na zo na sameki" Haka ya yi ta rarrashi for no reason sai bayan daya kashe waya yake tunanin meyasa ya yi hakan? Tausayinta kawai ne a ranshi kuma dama tun fil'azal shi mutum ne mai tausayi.
****** ******
Da ido yake ƙara bin unguwar da kallo very local area, motar shi gabaɗaya ta ɓaci da kwata saboda ita kawai yake bi, layin nasu ko ina kwata ne da datti a haka har ya ƙarasa ƙofar gidan kamar yadda aka kwatanta masa. Daga motar ya fito, yara duk sun fito sun yi cirko-cirko suna kallon motar. "Barka da zuwa" Ta faɗa tana jingina a jikin motar ta gefensa. "Barka dai ƙanwata da ban san sunanta ba" Murmushi ta yi "Ko dai rowar sunan ake min?" Kai ta girgiza tare da cewa "Sunana Nashwa"
"Wow nice name, wannan suna kamar na larabawa" Murmushi ta sake yi "Nashwa kamar baki yi bacci ba ko? Na ga idanuwanki sun kumbura kuma ga shi sun yi ja" Hannu ta saka ta goge wani hawayen "A taƙaice dai na fahimci kina da arhar hawaye" Bata ba shi amsa ba, "Kin yi breakfast?" Kai ta girgiza alamar a'a. "To shi kenan in za a barki a gida kizo muje mu ci abinci"
"Ai duk inda zani bata hanani, amma kuma zaka iya ɗaukana a motarka?" Kallonta ya yi da mamaki sannan ya ce "Meyasa ba zan iya ba?" "Saboda ka ganni fa, babu wata shiga mai kyau"
"Karki ce haka dan Allah, baki da matsala muje kawai."
Ya yi mamaki sosai yadda take cin abincin babu wata kunyarsa da ta ji, kana gani ka san tana tare da yunwa. "Nashwa!" Ya ambaci sunanta a hankali, ta kalleshi "Kin yi karatu?" "Tun dana gama secondary school har yanzu ban cigaba ba" Ya yi shiru ya kasa magana. "Ina so na tambayeka" Zama ya gyara "Ok ina jinki"
"Meyasa ka taimaka min jiya, kuma a yanzu ma kazo gurina har ka bani abinci" Murmushi ya yi ya ce "Saboda kawai a labarinki akwai tausayi a ciki, kuma daga nan ma gurin Mamana zan kaiki, da ace uwar riƙonki za ta yarda da sai ta bar mana ke" Murmushi sosai ta yi sannan ta ce "Ai ba zata yarda ba, ka san duk ƙarshen shekara daga gidan marayu sai anzo ganinmu, so ka ga indai ba aure na yi ba to ba
zata barni ba, kuma ni na ce aurena ko a ina zan yi to a kano za ayi biki, zan je can gurin shugabar gidan marayu."
"Kenan kina da wayo aka kawo ki nan Yola?"
"E, shekaruna goma a lokacin, kuma ina daga cikin yara masu ƙwazo a gidan marayu, lokacin da ta ce ni take so da ƙyar shugaba ta bata ni saboda tana sona, kuma ina renon yara jarirai da aka kai gidan, saboda tun tasowata nima a gidan na tashi, shugaba ta ce min a ƙofar gidan aka ajiyeni da safe maigadi ya fito ya gani an ajiyeni da kayana masu kyau kuma da wannan fashin goshi da ɓullar hanci, tun ranar da aka bani labari duk baƙin da aka yi sai naga kamar iyayena ne suka zo ɗaukata, sai ga shi har yau babu amo babu labari, babban abinda ke bani mamaki shi ne mene na yi da mahaifiyata ta yaddani sai dai zuciyata tafi tunanin ni ɗin shegiya ce"
"Bar faɗa!" Ya furta yana ɗan runtse ido.
"Na daina ka yi haƙuri Yayana da ban san sunan shi ba" Murmushi ya yi, itama ta mayar masa "Kin rama kenan" "E mana"
"Sunana Affan" "Yaya Affan zan riƙa cewa" "Niɗan jarida ne ina aiki anan Alfahar Radio"
"Oh kai celebrity ne ko?" Tana rufe baki wasu maza biyu suka zo gurin. "Yallaɓai barka dai" Hannu ya miƙa musu suka yi musabaha sannan suka yi hoto.
Ƙura masa ido ta yi kafin ta ce "Yaya nima ina son zama 'yar jarida"
"A'a"
"Meyasa"
"Saboda ba aikin mata bane"
"Amma ai akwai mata da yawa 'yan jarida"
"E amma ni ba zan bar ƙanwata ta yi ba, saboda aiki ne mai haɗarin gaske" Sun ɗan taɓa hira kafin daga bisani suka tafi gida kamar yadda ya faɗa.
An karɓeta hannu bibbiyu domin Mommy da Lawisa da suka ji labarinta kamar su haɗiyeta, Mommy ta ba shi umarnin ya mayar da ita makaranta ya kuma cigaba da kula da rayuwarta har lokacin da Allah zai kawo mata mijin aure. Har aka yi wannan buduri aka gama Badriyya bata sani ba.
Lokacin da zai mayar da ita gida sai kuma ya ga unguwa da ban, unguwa ta masu kuɗin, kallonshi ta yi sannan ta yi murmushi "Yaya na san kana mamakin nan ko?"
"E sosai ma, nan kuma ina ne?"
"Shi ne asalin gidan da ake riƙona can gidan daka gani gidan kakar Umma ne matar da ta rasu jiya, acan na kwana dana ji kace za kazo shiyasa ban koma gidan makoki ba"
"Nashwa wai ba su kula da rayuwarki?"
Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Babu kulawa, lokacin da ta ɗaukoni na faɗa maka da ƙyar aka bata ni, sai da ta saki kuɗi sosai sannan aka bata saboda ni mace ce mai farin jini a gidan marayu, so bayan tazo dani nan na ga gata ta nuna min shi sosai da ita da maigidanta wanda nake kira da Daddy kuma nake ganin ƙaunarsa a gareta, so daga baya lokacin ina aji biyar na secondary sai Allah ya bata haihuwa tun daga lokacin sai ta fara nuna bambanci yanzu kam abin ya yi worst, Yaya wallahi in zan kwana biyu ban kwana gida ba babu wanda zai nemeni kuma in na dawo babu wanda zai tuhumeni hakanan nake rayuwa a gidan, Daddy ma baya kulani, yaran yanzu shekararsu 6 a duniya."
Shiru ya yi na wani lokaci kafin ya ce "Karki damu Nashwa kin samu wa, kuma wanda zai riƙa kula da komai na rayuwarki, ni dai addua nake Allah ya sa su yarda ki cigaba da karatu"
"Za su yarda insha Allah, kuma a kano nake so na yi karatu Yaya"
"Meyasa?"
"Kawai dai na fi son na bar gidan nan na yi boarding"
"To shi kenan ba damuwa."
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya yaje ya gaisa da mariƙiyar Nashwa kuma a iya ganin farko daya mata ya gane bata da mutunci kalar tarbar da tayi masa kamar an mata dole, kuma daya nemi yana son mayar da Nashwa makaranta ta ce masa ya yi ita ba zata hana ba amma da kanshi zai janye saboda Nashwa daƙiƙiya ce bata fahimtar komai, ya ji zafin abin amma sai ya danne.
Ta fara karatu, kuma tana mayar da hankali sosai sun shaƙu da Affan da kuma ahalinsa har ta kai ta kawo sai tayi sati biyu a gidan su Affan, shekara biyu da haɗuwarsu Mommy ta bijiro masa da auren Nashwa wanda shi kansa akwai hakan a ransa amma ganin tana karatu ya saka bai mata maganar ba. Lokacin ɗan Badriyya mai suna Fu'ad har an yaye shi, ranar kuwa daya koma da niyyar faɗa mata an saka ranar bikinsa da Nashwa wata uku sai ya ji kunyarta ta kama shi da kuma tsoron abin da ka je ya dawo saboda ya san tana da kishi matuƙa.
Yana wasa da Fu'ad ta fito daga kitchen, har za ta wuce ya kirata ta dawo. Zama ta yi tare da cewa "Affan ina jinka sauri nake naje na gyarawa Fu'ad shimfiɗa"
Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa "Amma Badriyya mene ya canja ki haka? Na ga sam baki bani kulawar daya dace"
"To ai gani na yi ka samu mai yi maka shiyasa ni kuma nake bawa ɗana kulawa dan tunda kai akwai wadda take yi ai ba sai na yi ba"
"Wace irin magana kike faɗa?"
"Na san ka gane abinda nake faɗa ko ƙarya na yi ne?"
"Look Badriyya ni ba tashin hankali nake son yi a daren nan ba, magana nake so mu yi akan haihuwa"
"Affan wai mene damuwarka dan Allah?" Ta furta cikin ɗaga murya.
"Damuwata shi ne bana so kiyi planning ina son haihuwa Badriyya" Shima cikin shouting ya yi magana.
"Wallahi planning har na sha magani na yi kuma allura, ba zan haihu ba har sai ɗana ya yi wayo ko zan ƙara haihuwa to sai Fu'ad ya shekara biyar a duniya"
"Saboda ke kike bayar da haihuwar?"
"A'a saboda ni na san ɗaukar ciki, laulayi, girma da nauyin ciki, naƙuda, uwa uba gashi ina reno har yanzu"
"Wannan ba hujja bace"
"Ni kuma ita na riƙe a matsayin hujja"
"To kada ki ga laifina idan na auro wadda za ta haifa min 'ya'ya koda ɗari nace ina so"
Murmushin gefen leɓe tayi sai kuma ta kalleshi "Affan ka fito fili kawai kace min aure zaka ƙara ba sai ka tsaya kwana-kwana ba"
"A lokacin dana aure ki bani da wannan ra'ayin amma ciwon kan da kike bani da kuma yadda kike son daƙile haihuwa bayan kin san ina so shi ne dalilina da zai saka na ƙara aure, duk da haka ban yi ba, sai da Mommy ta bani umarnin auren Nashwa kawai naga ya dace na yi aure, Nashwa marainiya ce kuma dama tana da burin hayayyafa domin ta tara zuri'ar da bata da shi, na san ko yara nawa nake so za ta haifa min. Dan haka ina so ki sani an saka min biki da Nashwa nan da wata uku, zakije umra kuma zan canja miki ɗaki shi ne goronki na faɗar kishiya ko ince abokiyar zama"
Cikin tashin hankali Badriyya ta miƙe tsaye, dan jin furucin nasa ta yi kamar sukuwar doki a ƙirjinta.
"Aure, kuma ka rasa wa zaka aura sai Nashwa da ta san komai nawa, ta rainani, Affan wallahi baka isa ba"
"Kece baki isa ba, kuma kin san Nashwa tana da tarbiyya da biyayya, idan kin so za ta miki idan kuma kin zubar da mutunci kin ga sai ƙaramar yarinya ta rainaki"
"To na rantse da Allah akan wannan ba zan raga maka ba daga kai har Mommyn....." Mari ya tsinka mata wanda ya saka ta yi shirun dole.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 13```
Da yatsa ya nuna ta tare da cewa "Ki shiga hankalinki, rashin mutuncin na ki ya tsaya iya ni kada ki yarda ki sako mahaifiyata a ciki." Kallonsa take sai kuma cikin ɓacin rai ta fuzgi Fu'ad ta yi gaba.
Tsawon sati ɗaya sam basu kula juna, har ya saba da cin abinci a waje kafin ya dawo gida, da dare kuma sai dai yaje side ɗin Mommy ya yi dinner dasu ko kuma ya saka Lawisa tayi masa abinda yake so, dan baya son cin abincin masu aiki. Yau bayan sun gama cin abinci Mommy ta dakatar da shi, "Affan lafiya dai?"
"Mommy lafiya ƙalau" "A'a Affan karka ɓoye min, ni fa mahaifiyarka ce, naga kwana biyu anan kake dinner at times har da breakfast, sannan kuma ita kanta Badriyya ina kula da ita yau kwana biyu bata zo ta gaishe dani ba, hakan ya nuna bata ɗaukeni a matsayin uwa ba."
Shiru ya ɗan biyo baya kafin ya ce, "Mommy kiyi haƙuri, kin san na fara bincike akan kisan yaron da aka yi, so ni kaina ba a nutse nake ba, ko baccin kirki bana yi, amma ban san cewa Badriyya bata shigowa ba, Mommy tun ranar dana sanar mata an saka ranar bikina da Nashwa ta fara wannan gabar dani, ni kuma aikin da nake ne ya saka ban biye mata ba."
"Matar ka ba mace bace Affan, sam baka yi sa'ar mata ba, sai dai fatan Allah yasa wannan auren da zakayi ya zama alheri ya sa matarka ta so ka ta kuma kula da kai" Shiru ya yi bai iya cewa komai ba. "Ka je kawai, da safe kafin ka wuce kazo zamu ƙarasa magana"
"To Mommy" Sallama ya yi musu sannan ya wuce.
Yana kwance a gado ta banko ƙofar har sai daya furgita dan lokacin bacci ya fara ɗaukarsa. "Lafiya kuwa?"
"Ba lafiya ba, Affan wallahi indai ina da rai ba zaka ƙara aure ba" Ƙafafuwan shi ya zuro ƙasa lokacin da take faɗin "Sai dai bayan ranka ko nawa ran." "Badriyya ko dai kin sha wani abin?"
"Babu abin da na sha amma wallahi ba zan taɓa bari na haɗa miji da wata banza ba, saboda kar ka kusanci wata macen na rabu da duk ƙawayena, duk wata mace da na san ba muharramarka bace bana yarda tazo gidana, sai kuma kawai yanzu kace zaka ƙara aure to wallahi sai dai ayi mutuwar kasko, ni da ita mu rasa gabaɗaya" Sai lokacin ta ɗago hannunta ya ga wuƙa, dan bai lura da ita a hannunta ba.
"Me kike ƙoƙarin aikatawa ne?"
"Kisa, zan kasheka in kuma kashe kaina" Ta furta tare da fashewa da kuka kuma ta nufo shi da wuƙar a hannu, cikin zafin nama ya riƙo hannun suka fara kokawa har sai da ta yankeshi a hannun hagu da ƙyar ya samu ya ƙwace wuƙar daga hannunta tare da kifa mata mari. A gurin ta zube tana kuka, shi kuma da sauri ya fita saboda yadda hannun ke zubar jini da alamu a jijiya ta yanke shi, a haka ya ƙarasa side ɗin Mommy har sun kulle ya yi ta bugawa.
A parlour Mommy da Lawisa suka yi kiciɓus, "Mommy waye haka a daren nan?"
"Ina zan sani ni har na fara bacci bugun ƙofar ne ya tayar dani." "Mommy jira anan bari na ji ko waye"
"Kar dai ki buɗe sai kin tabbatar da mai bugun ƙofar" Kai ta gyaɗa sannan ta ƙarasa jikin ƙofar. "Waye"
"Affan ne buɗe Lawisa." Jin haka ya saka ta buɗe da sauri, kasancewar barandar da haske ya saka ta ga jinin a ƙasa yana ɗiga kafin taga hannunsa daya riƙe gam "Subhanalillahi" Ta furta tana zaro ido, lokacin kuma Mommy ta ƙaraso.
"Yaya Affan lafiya? Mene haka"
"Me kika tsaya tambaya kina gani yana zubar da jini, maza ɗauko box kiyi masa dressing" Mommy ta janyoshi ciki sannan ta mayar da ƙofar ta yi mata key.
Lawisa na gama yi masa dressing ya jingina bayansa da kujera tare da lumshe ido. "Affan!" Mommy ta kira sunansa, a hankali ya buɗe ido ya kalleta. "Waye ya maka wannan? Gidan dai babu alamun 'yan fashi sun shigo"
"Mommy ku kwanta kawai da safe sai mu yi maganar, ni zan kwana anan kan kujera"
"Duk ɗakunan gidan nan ace ka kwana a kujera, ko babu extra room ai ka kwana a ɗakina bare ma akwai. Kuma ka san ba zan iya bacci ko kuma sa mun nutsuwa ba tare da ka faɗa min abinda ya faru ba."
Bai ɓoye komai ba ya faɗa musu, Mommy ta hasala sosai ta kuma ce lallai sai taje part ɗinsu a daren, da ƙyar Lawisa ta hanata saboda time ɗin ɗaya har da mintuna shidda, ta ce mata dan Allah koma mene a barwa safiya. Ranar Mommy bata samu bacci ba, sai dai shi Affan ya yi bacci saboda allura da Lawisa ta masa, Mommy kuwa tausayinsa kawai take, a ɗakinta ya kwana, ta kuma kwana tana nafila tare da yiwa Affan fatan samun mace ta gari.
_06:30am_
Kamar a mafarki ta riƙa jiyo bugu, a hankali ta buɗe ido, ganinta ta yi anan kwance dandan ƙasa, tunda Affan ya mareta ya fita tasha kuka, ta kuma raba dare tana kuka bata farka ba sai wannan bugun ƙofar ne ya tasheta, in da Allah ya taimaka ma tana cikin jinin al'ada da ta makara sallar asuba. Jiki babu ƙwari haka ta ƙarasa jikin ƙofar a buɗe ma take kawai dai an tura ne, tana buɗewa ta ji saukar mari har biyu a kumatu guda, aikuwa har sai da hawayen dole ya zubo saboda azabar marin, ji tayi an fuzgi hannunta an fita da ita sai lokacin ta ga Mommy ce, hankalinta ya tashi sosai. Mommy kuwa bata sake ta ba sai a ɗakinta inda Affan yake kwance. "Gashi nan ki kashe shi" Jin haka ya saka ta fashe da kuka mara sauti, ta saka hannu ta rufe baki lokacin da hawaye suke ambaliya a fuskarta.
"Kin san kisa ko? Za ki iya kisa saboda za a miki kishiya ko? To ki sani Affan aurensa babu fashi in ya so ga shi nan ki kashe sa, idan baki iya zama ki tafi mana ko an miki dole ne?" Kan ta a ƙasa ta kasa cewa komai sai hawaye kawai. "Tun da Affan ya aureki bai huta ba, dubi yadda kika mayar min da ɗa, duk kin bi ki zabura shi, wannan wace irin masifa ce ya ɗauko mana, kara nake miki amma ba wai dan ban san abubuwan dake faruwa ba, ana aure dan a jidaɗi amma shi Affan yana aurenki jindaɗi ya yanke masa" Mommy faɗa kawai take ta in da take shiga ba ta nan take fita ba, sai da ta gama tas sannan ta ce,"Ki tashi ki ɓace min da gani, kuma ki kira wani a cikin masu aiki a goge duk inda jini ya ɗiga." Da sauri ta tashi ta fice "Shashasha."
Tana haɗa kaya tana kuka a haka Lawisa ta sa me ta. "Wannan ba mafita bane Aunty Badriyya." Ɗagowa ta yi idanunta a jiƙe da hawaye ta ce, "Lawisa wallahi idan na zauna komai zai iya faruwa"
"E ki dai zauna ɗin, amma kin san tafiyarki za ta iya ƙara tunzura Mommy tunda har yanzu cikin fushi take" Zama ta yi gefen gadon ta saka hannu ta rufe fuskarta, Lawisa a hankali ta ƙarasa gabanta tare da dafa kafaɗarta. "Aunty wallahi Yaya har yanzu yana ƙaunarki you're his favorite, koda Mommy ta saka ya auri Nashwa kawai tausayin maraicin ta ya saka ta yi haka ba wai dan ba ta sonki ba, dan Allah karki yi abinda za ki ja Mommy ta tsaneki"
"Idan har Affan yana so na meyasa ya karɓi tayin auren Nashwa?"
"Saboda ya farantawa Mommy, ita kanta Mommy ba dan ta ƙuntata miki ta yi hakan ba." Haka dai Lawisa ta yi ya rarrashi har Badriyya ta janye maganar zuwa gida, Lawisa da kanta ta mayar mata kayan cikin wardrobe.
_*11:00am*_
Yana shigowa ta kafe shi da ido, ko amsa sallamarsa bata yi ba bare ya samu damar da zata kula shi, ya ƙarasa kujerar da take ya zauna a gefenta sai ta yi sauri ta miƙe tare da canja kujera. Murmushi ya yi sannan ya ce, "Ina so na yi magana da ke." Ba ta ba shi amsa ba, ya cigaba da cewa, "Badriyya ina sonki, wallahi da gaske ina son ki, kuma har yanzu ina son ki" Baki kawai ta taɓe tana jin ɓacin rai na ƙaruwa. "Na san kuma kema kina sona tun da har baki son kowa ya raɓeni, ki sani wallahi a abubuwan da kike min in wani ne da tuni ya ƙara aure ko kuma ya rabu dake, sai dai ni ina duba ƙaunar da kike min da ita nake
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 15