Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
miki uzuri. Badriyya, Nashwa ba ta da matsala ni na tabbatar zuwanta gidan nan ba....." "Hold on da Allah, ka ga Affan idan maganar waccan yarinyar za ka yi zan tashi ne in tafi karka sake yi min maganarta saboda na tsaneta kuma kome zaka faɗa ba zan taɓa ƙaunarta ba koda na second ɗaya ne." "Amma ki sani wannan abubuwan da kike yi jahilci ne." "Ka faɗa kanka tsaye Affan, ka ce ni jahila ce ba sai ka tsaya kana kwaskwarima ba." "Hmmm! Ban san haka kike ba, gabaɗaya gani nake kamar canjo min ke aka yi" "Ai fiye da haka ma zaka gani muddin baka janye maganar auren nan ba to wallahi kisa ne ƙarshen ta sai dai a shigo da gawarta gidan nan." Tana gama faɗa ya yi daidai da shigowar Mommy da Lawisa wanda a kunnensu suka ji furucinta na ƙarshe. "Gawa kuwa wataƙila taki za a fitar a nan gidan, ki sani zan ajiye surukuntaka in kashe ki a duk ranar dana shigo na iske kin kashe min ɗa, ba zan bari hukuma ta ɗauki mataki ba saboda na san za a barki ne ki cigaba da shaƙar iskar duniya saboda yanzu ba a kashe wanda ya kashe, to ni kuma a lokacin za a bugani a jarida da sunan na kashe matar ɗana." "Mommy..." "Ka rufa min baki Affan, ba zan zuba ido ana wannan shashancin a gabana ba, shiyasa tun jiya na ce ka sawwaƙe mata amma shegen baƙin na ci ya hanaka, to wallahi ba zan lamunta ba." Tana gama faɗa ta wuce, Lawisa da ido kawai take bin Badriyya da kallo, kenan duk irin nasihar da ta yi mata bata ratsata ba. ****** ****** Kallon ciwon ta yi wanda har ya warke. "Yaya ko dai zamu haƙura da juna?" Murmushi ya yi sannan ya ce "Saboda wannan ɗan ciwon?" "A'a ba dan shi ba, ka san nima Aunty Badriyya tana kirana tana kuma min gargaɗi a kanka" "Oh wai bata daina ba?" "E, amma ban faɗa ba dan ka mata faɗa dan Allah" "Ina ɗaga mata ƙafa ne kawai saboda wannan aikin da nake." Kallon takardun tayi sannan ta ɗauka. "Habu Labbo Bala" Ta furta a fili tare da zaro ido. "Wannan ba ɗan takarar senator bane?" "Shi ne" "To me ya yi?" Gyara zama ya yi sannan ya ce "Wata biyu da suka wuce akwai wani yaro ɗan tiktok da ya fito ya yi magana akan 'yan siyasa har ya ce zai tona asirin 'yan siyasa guda biyar ya kuma lissafo sunayensu, kwana biyu da yin abin aka nemi yaron aka rasa kuma har yau babu labarinsa, jami'an tsaro sun yi burus da lamarin kasancewar ɗan talaka ne ya yi ɓatan dabo, to mu kuma 'yan jarida mun ƙi mu haƙura shi ne muka shiga rigar 'yan sanda" "To amma meyasa sai Labbo Bala kaɗai?" "Ba fa abinda ya kamata ki sani bane, ki bari idan komai ya bayyana za ki ji, amma maganar gaskiya dukkansu mun yi bincike akai sai dai zarginmu yafi karkata a kan sa, yanzu ma da na saukeki a gida zan je in cigaba da aikin bincike ne." "Yaya yamma ta yi fa, ya kamata kaje gida ka huta" "Hutu ba nawa bane a yanzu Nashwa, yawwa ina son inji nawa zan baki na event ɗin?" Ya faɗa dan ya kawar da waccan maganar. "E to! Hall already an kama kuma ka bayar da kuɗin komai, sai na lalle da gyaran gashi" "Okay zan tura miki ta account" "Zuwa next week zan wuce kano, yaushe zaku shigo?" "E to ina tunanin ranar dinner" "Yanzu har sai na kai wannan lokacin ban gan ka ba?" "Kwantar da hankalinki, keda zan ɗauko ki na kawoki gidana ki riƙa gani na kullum" Hannu ta saka ta rufe fuska, ya yi murmushi tare da faɗin "Nashwa akwai kunya" Ɗan lumshe ido ta yi tare da janye hannun. "Yaya duk ranar dana haihu ace wannan ɗana ne, kuma wanda muka haifa ni da kai, to gaskiya ban san irin farin cikin da zan yi ba. Ji zan yi duk duniya na fi kowa sa'a da ina ganin kamar ranar ba zata zo ba" "Kamar yau ne Nashwa, insha Allah za ki ga yaranki" "Allah yasa" "Amin." A gida ya sauketa, sai dai yana wuce wa Allah ya kawo mata empty napep ta tara ta ce yabi bayan Affan amma karya bari ya sani. Ganin sun nufi bayan gari abin ya bata mamaki, ta fito da wayarta tana ɗaukar guraren da suke wucewa, sai da suka shiga wata doguwar hanyar da babu titi sannan taga ya parker mota, ta yi saurin fita ta ɗauki 10k ta miƙawa ɗan napep ta ce ya juya da sauri dan ta san Affan zai iya cewa a juya da ita, yana juyawa Affan ya juyo a tsorace, ganin Nashwa abin ya matuƙar ba shi mamaki" Da sauri ya ƙarasa gabanta "Meyasa kika biyoni?" "Saboda ba zan iya barinka a halin nan ba" "Wane hali? Zuwanki nan akwai risk, shiga mota muje" "Muje ina? Kawai mu ƙarasa zan iya tayaka aikin." "Su waye nan" Jin magana da ƙarfi ya saka suka ɗaga ido, han go bodyguards ɗin Labbo Bala suka yi, sun saito bindiga. "Na shiga uku" Nashwa ta faɗa tare da fashewa da kuka. "Ki shiga mota" Ya furta lokacin da bodyguards ɗin suka yo kansu su huɗu. "Bindiga ce Affan kawai mu miƙa kai." Ganin za ta ɓata masa lokaci ya saka ya fuzgeta yana buɗa motar aka harba bindiga. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 14``` Cikin azama ya jefata mota shima ya shiga, kafin kace me tuni sun fito da mota sun biyo bayansu, da ƙyar Allah ya saka suka kauce musu dalilin traffic daya tsayar dasu kuma suna wucewa su kuma aka ƙara tsayar dasu. Kai tsaye gida ya wuce hankalinsa a matuƙar tashe, tunda ya shiga layinsu yake horn duk ya furgita 'yan unguwar a haka ya ƙarasa gaban gidan nasu maigadi ya buɗe masa gate shi kuma ya shiga da mota, yana fakawa Badriyya ta fito daga side ɗinta "Kam bala'i" Ta faɗa tare da ƙarasawa inda suke. "Ke uban me ya kawo ki gidana?" "Kamarya? Dama yau ta fara zuwa gidan nan? Ko kin ga ta shiga side ɗinki?" Affan ya yi maganar rai ɓace. "Hmm! Ai tsiyar auren tsintacciyar mage kenan, tun kafin aje gidan mijin har an san juna a titi, banza karuwa koma na ce shegiya" Mari Affan ya wanka mata, ita kuma ta riƙe gurin "Akan wannan matsiyaciyar yarinyar wadda bama asan asalinta ba ka mareni?" Sai lokacin Nashwa ta fashe da kuka tare da wucewa side ɗin Mommy. "Idan har baki iya bakinki ba wallahi zan mugun saɓa miki" Ya furta cikin ɓacin rai sannan ya wuce rai a ɓace. Sosai Mommy ta yiwa Nashwa faɗa saboda abinda ta yi ba ƙarami haɗari bane, shi kansa Affan ɗin ba dan tana so yake wannan aikin ba. Haka Affan ya yi ta fushi da ita ko wayarta baya ɗagawa sai dai su yi communicating da Lawisa. Ya rasa ma abinda ke masa daɗi, ga biki, ga rusa masa shiri da Nashwa ta yi ga masifar Badriyya da taƙi ta ƙare. Har Nashwa ta tafi Kano ba su magana da Affan, ranar dinner kuwa har ya ce ba zai je ba Mommy ta tilasta masa ta ce tunda har ya yi niyya ba zai fasa ba, kuma itama Nashwa ai za taji babu daɗi idan bai je, haka ya shirya tsaf Lawisa ita kam tuni ta yi gaba. Yana saka trolley a but sai ga Badriyya ta fito da na ta trolley" "Ke kuma ina zuwa?" "Kano mana, ka san dai ba zaka tafi ka barni har tsawon kwana uku ba. Lokacin da nake tafiya in bar ki baki ga haka ba sai yanzu?" "Affan ni ban ce zan je wajen bikinku ba, ina son zuwa kano na daɗe da wannan burin saboda ina son na yi yawo, akwai ƙanwar Ammi a gidanta zan sauka dani da Fu'ad idan kun gama bikinku sai ka ɗaukeni mu dawo" "Hmmm! Idan ma wata fitina kike ji wallahi kan ki zai ƙare" Bata tanka masa ba ta saka kaya a but ya koma ya yi sallama da Mommy ta yi masa fatan alheri sannan suka tafi. Tun a hanya ya lura kamar akwai motar da take bin su amma dai ya share, sai da har suka fita daga Kano sun ɗauki hanya babu tsammani suka kara musu, ya kasa controlling saboda waccan motar babba ce, haka ya yi ta tura shi har sai da suka wurgashi ƙaton rami. Da ƙyar aka fiddosu daga mota sai dai Fu'ad dama ba a fito da shi da rai ba. Affan da Badriyya kuwa sun shiga Coma dan ƙarshe ICU aka mayar da su, sai dai tun da aka fitar dasu aka ƙona motar dalili kenan daya saka aka ɓoye aka sanarwa da mutane cewa sun ƙone ƙurmus. Shugaban gidan radio ya bawa Mommy shawarar ayi haka dan ana ganin accident ɗin an san set-up ne. Badriyya bata ɗauki lokaci mai tsayi ba ta farfaɗo sai dai ta samu karaya biyu a ƙafa sai kuma gani da ta daina yi da ƙyar aka samu aka mata wankin ido shi ne ta fara gani da glasses amma idan babu wannan glasses ɗin ba ta iya gane mutum sai dai kawai ta ga shadow. Nashwa kuma tun ranar aka aiko musu da ta rasu, sun yi baƙin ciki kuma basu samu damar ganinta ba, an ce masu a Kano za ayi jana'iza ba sai an yi doguwar tafiya da gawa ba, Lawisa a lokacin tuni ta taho jin accident ɗin su Affan tana hanya kuma ta riski rasuwar Nashwa itama ta shiga tashin hankali sosai. Tattarawa suka yi suka koma ƙasar germany anan aka cigaba da jinyar Affan bayan ya warke suka sayi gida a Abuja sai dai ta hana Badriyya fita ko nan da can, daga bedroom sai parlour, shi kuma Affan har lokacin kwance yake ba lafiya yana ta ƙara ramewa yana bushewa, wannan dalilin ya saka Badriyya take ganin kamar Mommy so take ta kashe shi, ita kuma Mommy ta tsani Badriyya dan gani take kamar itace ƙashin bayan matsalarsu. _Cigaban Labari_ Jin ana knocking ya saka shi kai duba ga ƙofar "Come in" Ya furta a sanyaye. Lawisa ce ta turo ƙofar ta shigo. "Yaya lafiya kuwa?" Ta faɗa tana ƙarasawa gabansa. Ɗan lumshe ido ya yi ya ja dogon numfashi ya sauke sannan ya buɗe idon a hankali ya kalleta "Lawisa yau na rabu da Badriyya " "What!?" Ta furta a tsorace. "Yes na sawwaƙe mata, amma sai nake ji kamar na rabu da wani bangare na rayuwata ne, tabbas Badriyya tana sona kuma so ne ya saka take nuna zafin kishi a kaina, akwai matan da ba su iya controlling kishinsu dole sai an lallaɓasu haka ya kamata na yi tun farko, sannan Badriyya bata da laifi a accident ɗina da kuma kisan Nashwa hasalima bata ji ba bata gani ba ta rasa ɗanta da kuma ganinta, gani nake kamar na zalunceta" Iska mai zafi ya furzar, Lawisa ta ce "Yaya wallahi kai ma baka da laifi, ina ƙaunar Aunty Badriyya amma gaskiya kishinta ya wuce na hankali, tun Mommy na mata kawaici har ta daina, ina ganin tsanar Aunty Badriyya sosai a idanuwan Mommy, duk da haka Mommy bata saka ka rabu da ita ba, ta ce tunda bata son ka zauna da kowa to gata gaka babu inda za taje, a lokacin kamanninka ma tsoro suke bamu Yaya, gani muke kamar ba kai ba. Daga baya sai Mommy ta yi tunanin gara kawai a faɗawa iyayen Aunty Badriyya gaskiya, to shi ne fa tun da aka faɗa musu suke ta tijarar sai an sakar musu 'ya" "Ni sam ban ga laifinsu ba" "Ai dama kai haka kake" Ɗan murmushi ya yi wanda kana gani ka san ba daga zuci bane. "Shi kenan na rasa Nashwa yanzu kuma na rasa Badriyya" "Amma ai kana da Sadiya" Ta faɗa tana kauda kai gefe. "Wace Sadiya kenan? Macen da take da aure" "Yaya ni fa ina ganin saboda mu suka tashi daga wannan unguwar" "Hmm! Sadiya ai bata yi sa'ar miji ba, dan kwatakwata bai san darajar mace ba" "Ƙilan a banza ya sameta shiyasa yake wulaƙanta ta" "A banza kamarya?" "Ko auren haɗi ko kuma wani abu makamancin haka" "Ki daina faɗa wallahi har raina abin ya sosa" "Tofah." Sai kuma ta yi murmushi. ***** ***** Knocking ta ƙarayi a karo na uku sannan ta ɗan dakata tana tunanin ko dai ba a gida ya kwana ba, har ta juya ta ji yana faɗin waye. "Saddiqa ce." Ta furta tana kallon gate ɗin. Ƙofar ya buɗe sannan ya mata iso ta shiga sai dai a farfajiya ta tsaya shi kuma da alamu bai ma daɗe da tashi a bacci ba ko kuma bugun get ne ya tayar da shi. "Yazid nazo ne akan batun saki, ka san an ce zuwa da kai yafi saƙo, na kira wayarka tun jiya bata shiga maganar gaskiya ko bacci ban iya ba, shiyasa na ce gara na yi sauko na sameka kafin ka fita." Shiru ya yi ya kuma sauke kai ƙasa. "Yazid ina jinka, dan Sadiya a gidana ta kwana, ko Mameey bamu sanarwa ba na ce zan yi fixing matsalar ba sai ta sani ba." "Saddiqa ki bawa Sadiya haƙuri amma a yanzu ba zan iya dawo da ita ba, umarni ne daga manya ba laifina bane." Saddiqa ta kasa cewa komai, ta sandare a gurin idanunta cak akan Yazid. "Zan shiga ciki saboda ina son fita kasuwa da wuri, nagode ki gaida gida. Anan tsaye ya barta ta kusa mintuna goma kafin taja ƙafafuwanta da suka yi sanyi ta bar gidan. Da ƙyar ta iya driving kanta zuwa gida. A parlour ta tarar da Sadiya zaune kan kujera tana goge hawaye, Najma da Ihsan sun ɗora kansu a cinyarta, ji tayi kamar ta fashe da kuka. Ta ƙarasa gurin sannan ta ja yaran, muje in haɗaku da Dije ta muku wanka ko" "Maama! meyasa Mommy take kuka?" Najma da tafi hankali ita tayi tambayar. "Mommy bata da lafiya muje ayi wanka ayi break ko?" Haka taja yaran ta shigar dasu ta saka mai aikinta tayi musu wanka ita kuma ta koma gurin Sadiya. Jin an dafata ya saka ta ɗago rinannun idanuwanta ta sauke kan Saddiqa "Sadiya kiyi haƙuri babu wanda yafi ƙarfin ƙaddara" Jin haka ya tabbatar mata da ba a dace ba, a take ta saki kuka a fili, ita kaɗai ta san irin ɗaci da raɗaɗin da take ji. "Ban taɓa tunanin ko a mafarki Yazid zai iya rabuwa dani ba, na ɗauka cewa ko an sakawa Yazid wuƙa a wuya aka ce ya sakeni zai ƙi, sai ga shi salin alin ya sakeni, ya ruguza duk wata yarda dana yi masa" Ta ƙarasa tana sake rushewa da kuka. "Ni kaina na yi mamaki amma ba yanzu ne lokacin tattauna maganar nan ba, kiyi haƙuri, kin ga Habibi bai tashi ba bana so ya gane abinda ke faruwa dan ban faɗa masa komai ba, please tashi mu koma ɗaki, haka ta kama hannunta kamar ƙaramar yarinya suka nufi ɗakin, kan gado ta kwanta ta cigaba da kuka. _01:30pm_ Tana durƙushe kan abin sallah tana hawaye ga zazzaɓi da taji yana ƙoƙarin rufeta, idanuwa kuwa ƙarfin hali kawai take tana buɗesu saboda kanta da taji yana barazanar tarwatsewa, ko magana bata son ji saboda jin ta take har cikin ƙwaƙwalwa. Saddiqa da ta shigo da tray akan table ta ajiye sannan ta ƙaraso gabanta "Ki tashi kici abinci Sadiya, kar damuwar wanda bai damu dake ba ya saka ta miki illa" Ɗagowa tayi a hankali fuskarta jiƙe da hawaye ta kalli Saddiqa "Kina nufin Yazid bai damu dani ba?" "A'a ba haka nake nufi ba" "Aunty dan Allah ki tashi mu tafi gida, ina so naga Mameey ji nake kamar zan mutu Aunty" Rungumeta Saddiqa ta yi sai lokacin ta ji zafi zum jikinta. "Baki da lafiya ai, zazzaɓi ne a jikinki" Bata gama faɗa ba kawai taga idanuwan Sadiya na juyewa, ta ɗan fara jijjigata kawai taga baƙar ƙwayar tayi sama "Na shiga uku wayyo Allahna" Ta furta tare da miƙewa da gudu tayi ɗakin Ahmad. "Lafiya ya faɗa yana kallonta" "Habibi Sadiya ta mutu na shiga uku." "Wane irin magana kike faɗa haka" Ya furta tare da miƙewa da sauri suka yi ɗakin da Sadiya take. Yana taɓa kumatunta ya ɗauke hannu yadda yaji mugun zafin da jikinta ya yi. "Maza samo ruwa da towel" Da sauri tayi toilet ta ɗebo ruwan ta dawo ta miƙa masa, kallonta ya yi sannan ya ce "Ki nutsu ki shafa mata ko ina a jiki, tsugunnawa tayi gaban Sadiya shi kuma ya koma gefen gado ya zauna, ta cire mata hijabin sannan ta shafa mata sai da tayi second round sannan Sadiya ta sauke ajiyar zuciya ta dawo daidai sai kuma ta saki kuka. "Kin ga ku sameni a waje bari na fito da mota a kaita asibiti. ****** ****** "Saki?" Mameey ta faɗa tana kallon Saddiqa, ita kuwa tana durƙushe a ƙasan carpet ta kasa cewa komai tunda ta bawa Mameey takarda. "Saddiqa wai Yazid ɗin ne ya bawa Sadiya takardar nan?" "Mameey ni kaina ban gaskata ba, tun jiya abin ya faru amma na kasa sanar miki na ce in akwai yadda za ayi a gyara, da kaina naje gidan na sameshi amma ya gaskata min sakin ya kuma bani haƙuri" "Haƙurin banza haƙurin wofi me zamuyi da haƙurinsa wulaƙantacce irinsa, kin ga abinda nake gudu ai, kin ga tsiyar auren talaka, wancan gida da ɗan ƙaramin shago da wannan akurkin motar sune suka saka ya fara jin kansa wani shege ko, bayan da kuɗinta ya yi arziƙin, to bari komai ya lafa wallahi duk abinda ya san na ta ne ita ta ba shi sai ya dawo mana dasu har gadonta daya cinye" Mameey faɗa sosai tayi ta inda take hawa ba ta nan take sauka ba. Kwanan Sadiya biyu a asibiti aka sallamota, sai dai Mameey kullum cikin faɗa take bata tsayawa ta rarrasheta bata kula da damuwar da take ciki, yaran kuma ta rantse sai an mayar dasu gurin ubansu, dama bata wani shaƙu dasu ba, ba ta sakar musu fuska, haka ya ƙara jefa Sadiya cikin tashin hankali da kuma tunanin halin da zata shiga idan har aka rabata da yaranta. *Bayan Wani Lokaci* Sadiya tuni ta shiga sati na biyu da gama idda, sai dai bata fita ko ina, dama Najma ce take sintirin kaiwa school to ganin tana da damuwa sosai ya saka Saddiqa ɗauke su gabaɗaya, ga kuma Mommy da take nuna ba ta son yaran. Surayya data fito daga bedroom da waya a hannu ta ƙarasa parlour ta tarar Sadiya tana kwance kan three seater tana barci. "Faruq ka ga ma bacci take" Ta faɗa tana ɗan haska masa sannan ta ɗauke. "Ƙara haska min ita please" "Kai ban haskawa idan kana son ganinmu ka dawo mana, ka je kayi zamanka a ƙasar da ba taka ba" "Wallahi kin raina ni da yawa Surry amma zan yi maganinki" Dariya tayi tana zama kan kujera "Amma dai Yazid baya da mutunci wallahi" "Babu Uncle ɗin?" "Dama ai kara ce yanzu kuwa babu tunda bai san ta ba, kuma kun min laifi da kuka kasa sanar mini" "To ai ba abu bane mai daɗi bare a faɗa, ba ga shi yanzu ka ji ba" "Haba Surayya sai da har ta gama idda, nima fa ɗan uwanku ne damuwar nan har dani ya kamata ayi sharing" "Aunty Sady dai har yanzu taƙi barin damuwa" "Dole ta damu mutumin nan azzalumi ne, ai insha Allahu cikin satin nan zan dawo, dan Allah idan ta tashi ki kirani mu gaisa zan bar data kunne" "Ba ka da matsala" "Yawwa thank you" "You're welcome." **** Tana shafa addu'a Surayya ta ƙaraso tare da zama gefen gado. "Yau dai kin samu nutsuwa Aunty Sady dan na ga har bacci kika yi" "Ina so in fitar da komai ne a raina, a baya gani nake kamar ban rasa Yazid ba amma tun da na gama idda bai mayar dani ba na san shi kenan kuma" "Na ji daɗi da kika fara manta komai, Allah yasa haka shi ne mafi alkhairi" "Amin Surry" "Yawwa ɗazu kina bacci mun yi waya da Farouq shi ne ya ce dan Allah idan kin tashi na kira shi ku gaisa" "Ina fatan baki faɗa masa mun rabu da Yazid ba?" "Ya sani fa, amma Mameey ta sanar bani ba. Na kirashi?" "E, kira shi" Ta furta a sanyaye. Yana ɗagawa ya ce "Mara kunya yane?" "Kai fa dan ka fara tara saje kake ganin ka kai ko? Ko da ake ce maka age mate ɗina ai na baka watanni" "Baki da kunya wallahi, shiyasa tuntuni naso Mameey ta yi mini jumping amma babu komai ai yanzun ma na san an bigger than you" "Girman jiki ba, ka je ƙasar wasu kayi kane kane" "Ke kuma abin ya tsone miki ido ko?" "A'a a wane dalili" Sadiya dai tana jinsu suna ta shirmensu kafin daga bisani ta ce "Ni ka ga, ga Aunty Sady ɗin, shi ne dalilin kiran" "Oh wai dama tana nan kina min rashin kunya bata tsawatar miki ba" "Kai ka sani kuma" Ta faɗa tana miƙawa Sadiya waya. "Ga shi bari naje ɗakin Mameey kafin ku gama." Tana bata ta fita. Bai ce komai ba ya tsaya kawai yana kallonta har sai da ta ce "Yaro jira kake na gaidaka?" Ɗan lumshe ido ya yi, har cikin ransa yake jin muryarta tana masa daɗi. "Na yi tunanin zamu gaishe da juna ne" "Hmm ok to ina yini Faruq." Ta furta da gatse. "Lafiya lau ya yara?" "Kai!" Ta furta da mamaki, sannan ta sake yin dariya. "Aunty Sady ashe har kin gama idda ban sani ba, gaskiya ba a kyauta min ba" "To ai baka da lafiya, taya za a faɗa maka abinda ba na farin ciki ba" "Hakane Aunty amma kuma duk da haka ya kamata ace na sani, saboda yanzu inda wani ya min sakiyar da ba ruwa fa" Da sauri ta kalli ƙofa. Ya yi murmushi "Kina tsoron kar wani ya ji ne? To ai babu amfanin ɓoyewa tunda a yanzu zan iya shigowa cikin manemanki" "Faruq wai kana da hankali kuwa?" "Indai akan soyayyarki ne bani da shi SADIYA! INA SONKI kuma na shirya yin ko wane irin yaƙi dan ganin na mallakeki" "SADIYA!" Ta maimaita. "Ni ne a samanki saboda nan gaba kaɗan zaki cigaba da gaisheni kamar yadda kika yi yanzu, kuma abu ma in za ki bani sai kin rissina, zan zauna dake tare da yaranmu Najma da Ihsan dama wanda zamu haifa a gab....." "Ya isa haka" Ta furta tare da buga wayar akan tiles, a daidai lokacin Surayya ta shigo ɗakin. *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a

Chapter 11 of 15