tuntuɓi wannan lambar 07035111671_*
*_Har yanzu na yi VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah🦋✍️
[6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanasdeeyah_
_Facebook@SaNaz Talkshow_
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 3```
"Umma dan Allah idan ma wasa kike ki daina, wallahi zuciyata bugawa take"
"Ni sa'ar wasanka ce da zan maka wasa? Ai ko tsokana tun ranar dana baka umarni ka rabu da wannan annobar mai farar ƙafa ka kafe ka ƙeƙashe kace ka ji ka gani na fita sabgarka, yanzu ma dan ka kawo min kukan ka shiyasa na ga ya dace na yi abinda zan iya"
"Umma....!" Sai kuma ya dafe kai, sannan ya sake juya kuɗin "Umma wannan tinkiyar fa na ajiyeta ne saboda haihuwa idan Sadiya tayi in musaya da rago a yanka, amma...." "Dalla dakata Yazid" Ta katse shi cikin ɓacin rai.
"Haihuwar da ba a san ranarta ba shi ne zaka kasa gyara banɗaki, idan ta haihu yanzu a nan tsakar gida za ta riƙa wankan jego? To gasu nan dai na fita haƙƙinka, in ka ga dama kar ka gyara banɗakin ruwanka ne wannan." Tana gama magana ta juya ta fice, sai lokacin Sadiya ta sauke ajiyar zuciya gami da miƙewa ta shiga ɗaki.
Gefen katifa ta zauna sai kuma ta fashe da kuka mara sauti, yana shigowa ta fara ƙoƙarin goge hawayen duk da a lokacin wani bai bar zuba ba. Kusa da ita ya zauna tare da faɗin "Dan Allah kiyi haƙuri da abinda Umma ta miki" Ba ta ce komai ba, sai ma kanta data sauke ƙasa.
"Wannan kuɗin ba za taɓa ba, zanje na sayo rago komin ƙanƙantarsa, ko kuma na je ƙauye sai na haɗa yaran data haifa a sayar sai a sayi rago."
"A'a Yazid! Umma ta fimu gaskiya, ka yi amfani da kuɗin a gyara bayin da kum...." Bata ƙarasa ba ta ji cikinta ya karta, ta ɗan cije leɓe "Ya dai?" Ya tambaya yana kallonta.
"Cikina!" Ta furta sai ƙuma ta sauka ƙasa lokacin da taji bayanta ya riƙe. Hannun Yazid ta riƙo ta kalleshi cikin tashin hankali "Cikina da bayana Yazid" Sai kuma ta fashe da kuka. Ganin dai ta ruɗe ta ce nan ta ce can ya saka da sauri ya tashi ya tafi neman mota zuwa asibiti.
****** ****** ******
A hankali ta ajiye ledar sannan ta juya zata fita taji ya kira sunanta. Juyowa tayi ta kalleshi, sai kuma ta ƙarasa gaban gadon.
"Dama za a iya haɗa baki dake aci amanata?"
Kai ta girgiza lokacin da hawaye masu zafi suka fito daga idanuwanta.
"Ina Nashwa take?"
Kallonshi take, kafin tayi magana aka turo ƙofa, juyawa tayi tana kallon Mommy da ta shigo. "Lawisa! Me kika faɗa masa?"
"Babu komai Mommy"
"To fita, tun da kin kawo abinda na saka ki"
"Mommy...!" Ya furta a sanyaye lokacin kuma Lawisa ta juya zata fita.
"Dan Allah ki bani dama na yi magana da Badriyya"
"Affan har yanzu baka da lafiya, ka bari ka warware sai kayi magana da duk wanda kake so"
"Kun hanani ganin kowa Mommy ko dai Nashwa ta haƙura dani? Ta tsaneni bata son ganina ko?"
"Nashwa ba zata tsane ka ba"
"Idan har Nashwa na ƙaunata ita ya kamata na fara gani a lokacin dana buɗe idanuwana, Mommy ki bani damar magana da Badriyya please"
"Badriyya bata tare damu, daga ni sai kai sai Lawisa a gidan nan"
"Mommy na san tana gidan nan Lawisa ta faɗa min please Mom" Ya furta yana haɗe hannaye ita kuma ta dafe goshi.
"Affan ya tambayeni?" Badriyya ta faɗa lokacin tana zura glasses ɗinta bayan ta gama goge hawayen daya wanke fuskarta.
"Aunty Badriyya kiyi haƙuri amma har yanzu Nashwa yake son gani duk da na sanar masa muna tare dake a cikin gidan nan"
Riƙo hannun Lawisa ta yi cikin kuka ta ce "Meyasa ban mutu ba? Meyasa na rayu? Nashwa ce ya kamata ta rayu amma bani ba"
"Saboda Affan bai nemeki ba shiyasa kike wannan fatan? Aunty Badriyya ko da Affan baya son ki bai kamata kiyi wa kanki fatan mutuwa ba"
"To mene ya rage Lawisa?" Ta furta tana miƙewa tsaye "Na rasa komai Lawisa, rayuwa nake kamar gawa a gidan nan, an hanani fita, an hanani waya, hatta iyayen da suka kawo ni duniya a tunaninsu ina ƙarƙashin ƙasa, mene yafi wannan ciwo, me ake nufi dani ne?"
"Na san rayuwarki ba zata taɓa ƙarewa a haka ba, Mommy tana so komai ya lafa sai mu tattara mu bar garin nan."
"To ni mene nawa a ciki? Meyasa ke ake bari ki fita kije office ni kuma aka kulleni anan, karatu da kuma yarona babu Lawisa" Ta faɗa tana ƙara fashewa da kuka.
"Karatunki yana nan insha Allah, bambanci kuma ke matar Affan ce, zasu iya bibiyarki"
"Idan har basu bibiyi ƙanwar Affan ba, ba zasu bibiyi matarsa ba"
"Aunty Badriyya, nima iya asibiti ne kaɗai nake zuwa, kuma kullum bana cire nose mask da glass ɗin idona, daga asibiti sai gida, amma akwai wani ƙoƙari da zan miki"
"Wane iri kenan?"
"Zan miki hanyar ganin Affan ba tare da Mommy ta sani ba, sai dai akwai abu ɗaya da nake so na roƙeki"
"Ina jinki"
"Karki ɗaga hankalinki idan kin ga yadda ya koma, idan kika ɗaga hankalinki to Mommy zata iya ganewa"
"Insha Allah ba zan ɗaga hankalina ba Lawisa, amma kina ganin Affan zai so ganina?"
"E me zai hana, kefa matarsa ce" Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ce "Allah yasa ya yi farin ciki da hakan"
"Amin ya rabbi" Hannu ta saka tana goge mata hawaye fuskarta ɗauke da murmushi.
****** ****** ******
Yana tsaye a ƙofar labour room shi kaɗai yake ta zagaye, ya kira wayar Siddiqa yafi a ƙirga amma a kashe, Auta da Mameey kuwa gabaɗaya sun jefashi a blacklist.
"Kaine mijin Sadiya?" Jin an yi maganar ya saka shi saurin kallon matar.
"Ni ne"
"Ok. Ka biyoni office na maka ƙarin bayani" Tana wucewa ya kalli labour room ɗin sannan ya bi bayanta da sauri.
Takarta ta miƙa masa lokacin tana zare glass ɗin fuskarta "Gaskiya dole sai dai a yi mata c.s saboda ɗan a gicciye yake ba zata iya haihuwa da kanta ba."
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" Ya furta da jimami sannan ya ce "Allah yasa ayi aikin lafiya"
"Amin. Zaka biya kuɗin aiki dubu ɗari da hamsin, sai kuma jini da muke buƙata leda biyu, idan ka biya zamu bayar da takarda kayi signing"
"Oh...oh..ok" Ya faɗa sannan ya miƙe, maimakon ya fita sai ya fara yin hanyar toilet"
"Waccan ce ƙofar fita" Ta furta tana kallonsa.
Yana fita kai tsaye gida ya koma ya ɗauko kuɗin da Umma ta kawo da wanda ya ɗan samu ya haɗa ya ƙirga gabaɗaya dubu casa'in da ɗaya da ɗari biyar ne. Tunani ya fara yi, ta ina zai nemo cikon, ganin babu sarki sai Allah ya saka ya ɗauki napep zuwa gidansu. Da Fatima ya fara cin karo a tsakar gida tana tsintar wake "Ina Umma" Shi ne abinda ya furta bayan sallama.
"Yaya ina wuni"
"Ina Umma na ce?"
"Gani, lafiya kake mata masifa, kaje waccan mai farar ƙafar ta haɗo maka zafi shi ne zaka huce kan ƙanwarka"
"Umma akwai matsala"
"Allah ya rabamu da ita, mene ya faru?"
"Sadiya ce babu lafiya, tana can haihuwa tazo kuma ance dole sai an mata c.s Umma wallahi bani da wasu kuɗi face wanda kika kawo ɗazu, kuma ba za su isa ba"
"To me kake nufi kenan?"
"Umma dan Allah ko ranta min ne kiyi"
"Rance? Ni in ranta maka kuɗi ka kai ayi wa waccan yarinyar da bata ganin mutuncina aiki"
"Bata gani kam, ga son nuna ita ta Allah...."
"Ki rufa min baki Fatima ko na mangareki"
Maryam da ta fito tana hamma kallon shi tayi sannan ta ce "Yaya ina wuni" Bai amsa ba, Umma ta ce "Ai ba zai amsa miki ba tunda an taɓa 'yarso gayyar 'ya'ya mata, na tabbatar yanzun ma mace za a fiddo. Mtsww"
"Umma ki sani wannan ba zaɓin Sadiya bane yin Allah ne"
"To na ce zaɓinta ne? Ai uwarsu ma haka ta diresu babu namiji a cikinsu shiyasa gidan babu tarbiyya babu ƙwaɓa, ka ga Yazid ka tashi ka bar min gida kafin ka gama ɓata min rai."
"Maryam" Ya faɗa yana kallonta.
"Dan Allah ko zan samu rancen dubu hamsin a wurinki"
"Wooo! Yaya ni da ita waye ya ajiye wani"
"Amma naga business kike kuma baki rasa kuɗi"
"Oh ni Rahane, kenan har ka fara zargin 'yan uwanka suna da shi suka hana ka" Miƙewa ya yi, suna kallon shi har ya bar gidan.
"Dan Allah dubesa yana tafiya sumi-sumi duk ya bi ya lalace ya mayar da kanshi talakan ƙarfi da yaji"
"Ni wallahi haushi ma take bani na tsaneta shiyasa ma ko gidan bana zuwa" Cewar Fatima, Maryam ta ɗora da faɗin "In kinje ma da takaici za ki dawo, ko kuma ki dawo da baƙar yunwa.
_*5 hours later*_
Kallon nurse ya yi ya ce "Please ko zan iya shiga na ganta?"
"E ai tana ward zaka iya shiga" Har ya wuce ta ce "Amma bawan Allah ɗan ji mana"
Juyowa ya yi sannan ya dawo gabanta.
"Ka tausayawa baiwar Allahn nan kar ta rasa rayuwarta ko kuma mahaifarta ta samu matsala dan Allah"
"Wallahi tunda na fita ban zauna ba, fafutukar haɗa kuɗi kawai nake"
"Kuma har yanzu basu haɗa ba?"
"90k ne kawai a hannuna."
"To ina ganin ka je kayiwa Doctor magana, zai iya yi mata aikin in yaso daga baya sai ka biya sauran kuɗin kafin a sallameta"
"To shikenan, bari na dubata tukun."
Halin daya same ta kuwa sai daya ji kamar ya zubda mata hawaye. "Abban Najma ka samo kuɗin?" Ta faɗa da ƙyar, hawaye na fita a idanunta.
"Su nake fafutukar nema insha Allah za a samu"
"Dan Allah ka nemo, ni kaɗai na san irin azabar ciwon da nake ji, ko kuma ka je ka sanarwa da Mameey"
"Haƙƙina ne ba haƙƙinsu ba, bana so ya zama takura"
"Ka taimaka min kar in mutu dan Allah" Ta faɗa tana sakin kuka, shi kuma cikin tashin hankali ya miƙe tsaye"
"Bari na je na ga yadda za ai"
Har ya wuce ta riƙo hannunsa, ya kalleta "Koda na mutu dan Allah ka kular min da yarana, kar ka bari su yi kukan maraici"
"Ki daina wannan maganar, insha Allahu zamu rayu tare mu kuma gina rayuwar 'ya'yanmu tare." Yana gama faɗa ya wuce da sauri.
Ajiyar zuciya Doctor ya sauke kafin ya ce "A baya muna yin haka, amma sai wasu patients suke samu su sulale daga zarar an masu alfarma, wannan dalilin ne ya saka muka daina"
"Wallahi ba zan taɓa guduwa ba, zan iya baku adireshi na"
"Ka yi haƙuri yallaɓai, matsalar ba daga mu bane daga sama ne aka aiko cewar mu daina wannan alfarmar"
Shiru ya yi kafin ya miƙe ya fita kawai. Kai tsaye makarantar su Najma ya wuce lokacin ma daya je har ɗalibai sun gama tafiya sai kaɗan da aka makara wurin ɗaukarsu. Ya ɗauketa suka koma gida baya da wani kuzarin yi masu wanka kawai ya ɗauki kayansu a leda ya saka sannan ya shiga maƙota ya karɓo Ihsan, har zai tafi Fiddausi ta biyo shi "Lafiya kuwa har yanzu Sadiyar bata sauka ba?"
"Wallahi har yanzu dai tana can tana fama, yanzu haka ma sun ce aiki za su yi mata"
"Aiki kuma?"
"Wallahi kuwa"
"Oh! Shi fa ciki haka yake da wuyar sha'ani ko wanne da kalar nasa naƙudar, ga Najma da Ihsan lafiya ta haifesu amma wannan sai anyi aiki."
"To ya za ayi"
"Tana labour? Dan na gama abinci yanzu nake ƙoƙarin zuwa, dan ma ka dage sai kun tafi ai da har kai ka tsaya ka ci tunda bata nan, Ihsan ce kaɗai ta ci ga kuma Najma ma na san tana jin yunwa."
"Ai ina sauri ne zan kaisu gida"
"Nan ma ai gida ne da ka barsu na yi mata wanka, ka ga sai na tafi dasu asibiti amma babu daɗi mene amfanin maƙotaka ace ka tafi ka kai su har can unguwar dan Allah ka bar su anan"
"To shi kenan nagode, amma dan Allah in za ki tafi ki barsu a gida kar ki tafi dasu kin san yara kar su je can su yi ta ƙiriniya ga kuma mararsa lafiya"
"To shi kenan ba damuwa"
Godiya ya yi mata sannan ya bar su Najma anan, dama suna wasa da yaran gidan shiyasa ma daya ce su zauna ya je ya dawo ba su wani damu ba.
****** ******* ******
A hankali suke tafiya gabanta bayan faɗuwa babu abinda yake, a haka har suka ƙarasa ɗakin da Affan ke jinya. Lawisa ta kalli Badriyya murya ƙasa ta ce "Dan Allah karki daɗe, kuma duk yanayin da za ki ganshi ka da ki tsorata." Kai Badriyya ta gyaɗa sannan ta murɗa handle ɗin ɗakin ta shiga. Yana kwance a gado amma tsabar ramarsa bata gane da mutum a gadon ba, tana tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo kawai taga ya ɗan motsa, da mamaki take kallon gadon kafin kai tsaye ta ƙarasa gabansa.
"What!? Affan kaine a haka?" Ta furta da ƙarfi lokaci guda kuma ta runtse ido tare da rufe bakinta da hannu. Tuni hawaye sun fara mata sintiri a fuska duk da idanunta a rufe suke.
"Tunda kin gansa hankalinki ya kwanta ai" Ta ji muryar Mommy kamar daga sama, da sauri ta buɗe idanuwanta ta kalli Mommy sannan ta ƙara kallon Affan, ya koma kamar ƙwaringwal idanuwansa sun zama ƙwala-ƙwala yayinda fatarsa gabaɗaya ta wani bushe, kanshi am masa aski ral. "Ban yarda wannan Affan bane Mommy ina Affan kuma me kuke nufi dani?"
"Ai dama na san ba za ki yarda ba shiyasa tun farko ban bari kin ganshi ba, fita." Ta ƙarasa magana cikin tsawa.
"Mommy wannan zalunci ne, ya kamata akai Affan asibiti yana buƙatar kulawa ta musamman"
Kusa da ita Mommy ta ƙarasa sannan ta ce "Me kike faɗa Badriyya?"
"Mommy idan ɗan da kika haifa ne a haka wallahi na tabbatar sai kin nemo mafita, ba za ki bar shi a haka ya kom...." Mari taji lafiyayye a kuncinta, wanda har yayi sanadiyyar faɗuwar glass ɗinsa, cikin ɓacin rai Mommy ta saka ƙafa ta take glass ɗin.
"Daga yanzu a haka za ki cigaba da zama a cikin gidan nan naga da wane idon za ki kalleni kina faɗar maganganu har haka, ke kin isa ki faɗa min yadda zan so Affan, kin san yadda nake ƙaunar Affan a raina, da yaushe kika san Affan ɗin? A ƙarƙashin kulawa ta ya rayu har ya zama mutum kika same shi har kike faɗa min wannan maganar banza"
Hawaye kawai take, dusu-dusu take ganin Mommy dan ganinta kawai take amma bata iya gane ita take kallo ko kuma ta juya mata baya.
"Badriyya!" Ta ji muryar Affan ta doki dodon kunnenta. Da sauri ta juya tana kallonsa sai dai a yanzu bata iya gane komai saboda babu gilashi, tana iya gane akwai mutum a gadon amma bata iya gane komai nasa.
"Ki je gurin mijinki, tunda baƙin naci ya kawo ki" Hannu ta saka tana tafiya tana lalube har ta ƙarasa jikin side drawer ta zauna "Kuma ki faɗa masa wani abu da zai ɗaga hankalinsa ki ga yadda zan saɓa kamanninki"
"Affan..!" Ta furta lokacin da wasu siraran hawaye suka zubo mata.
"Affan kana jina? Kuma kana iya gane komai?"
"Ina Nashwa take?" Shi ne abinda ya faɗa, ta sake jin hawaye a fuskarta.
"Affan ka kwantar da hankalinka, Nashwa tana nan kuma na san za ta zo gareka"
"Yaushe?"
"Soon insha Allah"
"Badriyya mene ya same ki naga kamar bakya gani?" Bata iya ba shi amsa ba sai hawaye daya mamaye mata fuska.
"Kukan da kike yi ya tabbatar min ba dake aka haɗa baki wajen ajiye ni anan ba, ina fatan daga wajen Nashwa ma ya kasance haka"
"Nashwa ba za ta taɓa cutar da kai ba Affan"
"To amma meyasa ta gujeni?"
"Ba tafiya ta yi ba, ina mai tabbatar maka da zata dawo gareka, aiki ne ya ɗan riƙeta a Abuja"
"To nan ina ne?"
"Nan muna Ibadan ka kwantar da hankalinka"
"Nashwa nake son gani ko ta halin ƙaƙa"
"Kin ga Badriyya tashi ki fita ya isa kuma, dan ance ba a so ya fiya surutu"
Tana ƙoƙarin miƙewa tana dafa bango, Mommy ta ƙaraso tare da fuzgar hannunta hakan ba ƙaramin tsorata ta yayi ba. Sai data jata har parlour sannan ta hankaɗata ta faɗi ƙasa.
"Wannan ya zama shi ne farko shi ne kuma na ƙarshe da za kije gurin Affan musamman ba tare da sanina ba.
Lawisa da tun shigowarsu ta miƙe sai lokacin tayi saurin sauke ƙwayar idanunta ƙasa.
"Ke kuma kin kyauta" Tana gama maganar ta juya ta barsu anan. Ranar kwana Badriyya tayi tana kuka, Allah yaso ba gilashi ɗaya ne da ita ba.
***** ***** ******
An ɗebi kusan awowi shidda Yazid na ta fafutukar neman cikon kuɗin aiki, amma bai samu ba, gashi nurse ɗin sai kira take, ya rasa ina zai tsoma gudan ransa. Kai tsaye gidan su Sadiya ya nufa dan nan ne last hope ɗinsa.
Yana tsaye a farfajiyar gidan sai ga maigadi daya tafi yi masa iso ya fito tare da Faruq. "Oh ashe ma ɗan gida ne, Uncle Yazid ai da ka ƙaraso ciki" Ya faɗa yana miƙa masa hannu suka yi musabaha.
"Ai bama wani abu bane dama Sadiya ce naƙuda ta kama, to tun safe ma tana asibiti" Sai kuma ya yi shiru wanda hakan ne ya tabbatarwa da Farouq akwai matsala.
"Aunty Sadiya'n ta haihu ne?"
"A'a dole C.S za ayi saboda yaron a gicciye yake to sai dai kuɗin dake hannuna basu da yawa tun safe nake ta fafutukar neman ciko, dana ga yamma naVyi sai na ce gara dai na sanar daku"
"Subhanallahi! Bari na sanarwa Mameey in yaso sai mu wuce tare"
"To babu damuwa" Ya faɗa yana gyara tsayuwa.
"Hmmm! Ba ga irinta nan ba, kuɗin da za a yiwa matarka aiki baka da shi, wallahi ban taɓa ganin faƙirin mutum irin mijin Sadiya ba, ni ban ga abinda ta gani a jikinsa ta nace masa ba."
"Mameey a fara ceton ran Yaya Sadiya first, in ya so duk maganar da za ayi ta biyo baya" Surayya tayi magana tana yana gyalenta.
"Shi kenan ku je, duk abinda ake ciki ku riƙa kirana kuna sanar min, Faruq ka kira Saddiqa kuwa?"
"Na kira har 3 times bata ɗaga ba, na san idan ta gani za ta kira"
"Ok. Allah ya raba lafiya"
"Amin Mameey"
Suna zuwa suka tarar babu kowa a wajen Sadiya face wannan maƙociyar ta su, lokacin Sadiya ta galabaita ko magana aka yi mata sai dai ta bi mutum da ido, kuma shima kallon da gani bata san waye akanta ba. Yazid da Faruq sune suka biya kuɗaɗen da aka buƙata sannan aka basu receipt suka kaiwa likita, cikin mintuna talatin aka gama shiryata zuwa theater room.
Suna nan zaune, amma Yazid ya kasa zama yana tsaye yana addu'ar Allah ya sauketa lafiya, Faruq da wayarsa ta fara ringing ya kalla. "Mameey" Ya furta lokacin daya kara a kunne.
"Ya ake ciki ne Faruq?"
"An dai shigar da ita theater sai fatan a yi aiki lafiya"
"Dan Allah ana ciro Baby ku kira ku sanar min, sannan kuma ku tabbatar Sadiya ta tashi please"
Murmushi ya yi kafin ya ce "Mameey ki tayata da addua, insha Allah da ƙafafuwanta za ta fito"
"Allah yasa"
"Amin ya rabbi." Tana kashewa ya kalli Yazid ya ce "Uncle ka zauna tun ɗazu kake a tsaye"
"Kar ka damu Faruq zan zauna" Ya furta a sanyaye sannan ya mayar da kallon sa theater room.
_Bayan wasu awoyi_
Mameey ta kira ya fi a ƙirga ana faɗa mata Sadiya har lokacin ba a san komai game da ita ba, domin wanda aka shigar da ita tare an fito da matar kuma ma tagwaye ta haifa, amma Sadiya shiru, suna dai ta addu'a tare da fatan samun nasara.
Likita daya fito da sauri suka miƙe, Yazid kuwa dama a tsayen yake.
"Kune kuka kawo Sadiya Mustapha?" Ya tambaya tun kafin su yi tasu tambayar.
"E mune"
Shiru ya ɗan yi kafin ya ƙara kallonsu, Faruq kasa haƙuri ya yi ya ce "Doctor dan Allah ka faɗa mana shin ya 'yar uwarmu take, wannan kallon da kake mana wallahi ba ƙaramin furgita muke ba"
"Am sorry to say...."
"Doctor dan zatin Allah kar ka ce Aunty Sady ta mutu" Surayya ta faɗa tare da fashewa da kuka, ta kuma kai gwiwoyinta ƙasa, dan ta ji gabaɗaya sun kasa ɗaukarta.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting. Sannan ina maraba da duk wanda suke so a tallata musu hajarsu, a cikin littafin, ko kuma a facebook da tiktok ku tuntuɓi wannan lambar 07035111671_*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah🦋✍️
[6/16, 8:47 AM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
Arewabooks@sanazdeeyah
Facebook@SaNaz Talkshow
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 4```
"Karku ɗaga hankalinku, 'yar uwarku ba rasuwa tayi ba tana nan da ran ta, sai dai ɗiyar da aka cire mata ta rasu sannan itama mun saka mata oxygen dan haka a yanzu ba zamu baku ita ba sai zuwa dare"
"To Doctor babu matsala, a bamu yarinyar sai muje mu yi mata sutura" Cewar Faruq, dan Yazid ya kasa magana.
"Za a fito da ita yanzu tare da uwa"
Doctor na wucewa Faruq ya kalli Surayya ya ce "Auta ki tashi tunda dai tana nan da ranta ai da sauƙi ma."
Miƙewa ta yi tana goge guntun hawayenta. Yazid ma ajiyar zuciya ya sauke, duk da an rasa jaririyar amma dai da sauƙi. Shi ya karɓi jaririyar tare da uwa ya tafi da ita, su kuma suka zauna jiran a fito da ita duk da ance masu za a ɗauki lokaci kafin a fito da ita.
***** ***** *****
Kallon gawar ta yi sannan ta ce "Astagfirullah, kar dai ace min mara mutunci amma ai can gidan ya kamata a kai gawar ko?"
"Umma da nan da can ɗin duk ɗaya ne, kuma ni tunanin in kai can bai zo min ba, har ma na kira liman na sanar masa, tunda dai jaririya ce"
"Shi kenan, Allah ubangiji ya sa mai ceto ce"
"Amin ya rabbi."
Fatima da take tsaye sai lokacin ta ce "Da alama dai Sadiya uwar mata ce, da wannan ta rayu mata uku reras fa"
"To ke ɗin ba mace bace, bana son rashin kunya Fatima"
"Allah ya baka haƙuri Yaya" Ta faɗa tana wucewa. Har sai da aka gama sutura sannan ya samu ya sake dawowa gurin Umma.
"Wallahi duk ka fita hayyacin ka Yazid."
Murmushi ya yi sannan ya ce "Umma dan Allah ku shirya ku dubo Sadiya" Shiru ta yi kamar tana karantarsa sannan ta ce "Kai dai komai Sadiya, to idan bamu dubo ta ba za a doke mu ne?"
"Umma ba maganar duka ba ne, maganar dacewa ce"
"To tunda bana yin abinda ya dace ba zanje ba, 'yan uwanta su zo su rufeni da duka" Shiru ya yi, ya ɗan lumshe ido sannan ya buɗe, ya kuma miƙe tsaye "Umma ni zan wuce" Bata kula shi ba har sai daya fita ta ce, "Mace ta bi ta shanye ka"
Maryam a zaure ta ci karo da shi, ta gaida shi ya amsa sannan ya fita ita kuma ta shiga gidan.
"Umma! Umma!!"
Kallonta ta yi sannan ta ce, "To makauniya gani anan, ke baki da aiki sai kwaɗawa mutum kira kamar kin bani bashi"
"Yi haƙuri Umma, naga Yaya ya fita da ɓacin rai, hala kuɗi ne suka sake yanke masa"
"A'a, ke dai kawai ki saka ɗan uwan nan naki a addu'a Allah ya haɗa shi da mayya, matarsa ce ta haihu ɗan babu rai"
"Umma 'ya dai" Cewar Fatima"
"Au wai macen aka kuma?"
"E, amma dai babu rai"
"Lallai wannan mata ta zame mana alaƙaƙai"
"Hmm! Ai wannan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 15