Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafi amma na miki alƙawarin za su dawo" "Sai dai idan bayan raina" Mameey ta yi maganar da ɓacin, da sauri Yazid da Lukman suka bar parlourn, ita kuma Sadiya ta ƙarasa gaban Mameey "Mameey nice baki so? Idan har baki son su Najma saboda Yazid to nima baki sona, saboda idan da jinin Yazid a jikinsu nima akwai nawa, nina haifesu Mameey yadda kike jin son mu nima haka nake jin son yarana ak....." Bata ƙarasa ba taji saukar mari, ta riƙe kumatun sannan ta kalli Mameey "Ki dawo cikin hankalinki, da ina sonki ai kin ƙunsa min baƙin ciki kin auri wanda ba zaɓina ba, ƙasƙantattun mutane masu baƙar zuciya, to baƙin cikin da kika ƙunsa min rabinsa baki ji ba a yanzu" Doguwar ajiyar zuciya ta sauke sai kuma ta ɗiba da gudu kamar mahaukaciya ta fita, Faruq ya rufa mata baya. A gabansu Yazid ta ja tunga lokacin suna gab da get. "Yazid dan Allah ka mayar da aurenmu ko dan yarana, na san za su sha wahala idan ba su tare dani" "Kiyi haƙuri Sadiya, na miki alƙawarin yaran nan za su zauna ne kamar kina tare dasu" "Yazid wane zunubin na aikata maka da kake son rabani da rayuwata, ina son yarana dan Allah ka tausaya min" Ta furta tana kai gwiwoyinta ƙasa, Lukman wucewa kawai ya yi dan ji ya yi kamar zai zubar mata da hawaye. Faruq na ƙarasowa ya fuzgi hannunta har sai da ta miƙe tsaye, ta kalleshi rai a ɓace ta ce "Ka cika ni" "Ba zan cika ki ba, bai kai matsayin da zaki durƙusa masa ba saboda babu laifin da kika masa" Ɗayan hannu ta saka tana ƙoƙari fuzge hannunta daga riƙon da Faruq ya mata amma ta kasa. "Kiyi haƙuri Sadiya" Shi ne abinda Yazid ya furta sannan ya wuce. Hannu ta saka ta riƙe wuyanta saboda jin wani abu daya tokareta, bata san lokacin data ɗora kanta a ƙafaɗar Faruq ta fashe da kuka, shi kuma a lokacin ya ji wani abu ya tsikareshi tun daga babban yatsa har ƙwaƙwalwa, sai dai ba zai iya janyeta ba, kawai ya sauke ajiyar zuciya ne. _*Dare*_ Yana zama ya kallesu. "Ya naga fav bata fito ba?" "Waye kuma fav ɗinka?" "Ai kin san waye baya anan?" Ya mayarwa da Surayya amsa. Dan a yanzu da yake jin zai iya zama da ita a matsayin mata, ba zai iya kiranta da Aunty ba sannan ba zai iya faɗin sunanta gatse-gatse a gaban wasu, amma a gabanta yana iya faɗa. "Sau biyu ina zuwa amma taƙi fitowa kuka kawai take, ga Aunty Saddiqa ta tafi." Miƙewa ya yi Mameey ta kalleshi "Faruq ka zauna ka ci abinci kar ka biye mata, idan yunwar cikinta ta dameta za ta fito ta nema ai" "Ba zan iya ci ba idan har bata ci ba." Ya ɗebi abinci mai yawa a plate sannan ya ɗauki gorar ruwa ya wuce. Yana shiga ya ganta a kwance kan gado ko ɗankwali babu ta baza gashin kanta da yake a tsefe yake, bata ɗago ba duk da ta san an shigo, a gefen gadon ya zauna sannan ya ɗauki ɗankwalinta dake gefe. "Sady!" Jin muryar Faruq ya saka ta yi saurin ɗagowa ta kalleshi, miƙa mata ɗankwalin ya yi ta karɓa tare da ɗaure kanta sai dai gashin ya fito ta ƙasa kasancewar tana da yalwar gashi. Kallonta yake sai yake ganin kamar ta koma masa wata sabuwa fil a leda, ya ƙare mata kallo tun daga sama har ƙasa zuciyarshi na jin kamar ya janyota jikinshi ya rarrasheta. Ajiyar zuciya ta sauke ya dawo daga duniyar tunani daya faɗa, ba shi take kallo ba idanuwanta na kallon gefe. "Abinci na kawo mu ci, dan na ce idan baki ci ba nima ba zan ci ba" "Na ƙoshi" "Ni na san kina jin yunwa, dan Allah karki azabtar da kanki da yunwa." Kuka ta saki a fili ta kalleshi "Yaro me su Najma suka yiwa Mameey ta tsanesu, ko zata tsanesu saboda Yazid nima ya kamata ta sosu saboda ni, amma tun kafin na samu matsala da Yazid dama Mameey bata ƙaunar yarana" "Wallahi Mameey na ƙaunarsu, kawai dai Yazid ne take jin haushi" "Na san an rabani da yarana ne saboda a ƙuntata min" "Na miki alqawarin yaranki za su dawo gareko ko ba yanzu ba" "Idan har ba su dawo gareni a yanzu ba na san ba za su dawo ba, saboda bani da yadda zan yi" "Akwai" Kallonshi tayi da rinannun idanuwanta ta ce "Ta wace hanya?" Plate ɗin ya ajiye a side drawer sannan ya kalleta. "Idan kika aureni ni ne zan riƙe yaranki tamkar mahai...." "Ya isa Faruq" Ta furta sannan ta dafe kai. "Ka riƙa faɗin abin da zai yuwu" "Kina ganin kamar ba zai yuwu bane?" "E, saboda ni yayarka ce, kuma bazawara" "A hakan nake sonki" Murmushi takaici tayi tare da faɗin "Idan har ba so kake zuciyata ta buga ba to ka tashi ka fita ka bar min ɗaki" "Sadiya..." "Ka fita Faruq" Ta furta cikin tsawa. Miƙewa ya yi ya ce "Zan iya fita daga cikin ɗakinki amma ba zan iya fita daga rayuwarki ba, ina sonki kuma a wannan karon zan yi yaƙi ne har sai naga na mallakeki, kuma zan sanarwa da kowa cewar ke nake so ciki kuwa har da Baffa Umaru." "Idan kai mahaukaci ne ai su ba mahaukata bane." "Na haukace kam indai akan sonki ne ai na daɗe ina hauka" Yana gama faɗa ya fice. Ranar shima bai ci abinci ba haka ya kwanta ya kuma kasa bacci, yana ta tunanin ta ina zai ɓullowa lamarin, haka ɓangaren Sadiya kwana tayi tana kuka, idan ta gaji zata huta sai kuma ta ɗora daga inda ta tsaya. Tun asuba Mameey ta jiyo kakarin amai, dan haka da sauri ta nufi ɗakin nasu. Surayya ta riƙeta a toilet ita kuma sai amai take babu komai a aman face ruwa. Hannu biyu ta saka ta riƙe kanta saboda juya mata da taji yana yi. "Kin ga maza je ki kira Faruq" "Mameey gani, yanzu na dawo daga masallaci, waye ba lafiya?" Ya faɗa yana shigowa dan shima kakarin ne ya saka shi shigowa ɗakin. "Sadiya ce babu lafiya ka ɗauki key a ɗakina kan mirrow ka fito da mota mu kaita asibiti" Da sauri ya juya ya fita. ***** ***** Ba su katse mata magana ba har sai da ta gama tare da jaddada masu cewar suna son tsayar da ranar biki nan da wata uku. Ayda ta yi murmushi tare da faɗin "Kuma ni Affan bai sanar dani ba, amma Anni kece kika yanke hukunci ko kuma wa?" Kallonta Anni ta yi kafin ta ce "Ya miki yawa ne a rage?" "A'a Farhan batayi magana ba sai ni" "To ai na ga kece mara kunyar tunda maganar bikinki ake kike tsoma baki" Jin haka ya saka duk yanayin su ya canja, "Anni bikina ko dai na Farhan?" "Bikinki da Affan dan cewa ya yi kece zaɓinsa" Bata san lokacin da ta miƙe tsaye ba, Farhan kuwa ji tayi gabanta na bugu. "Anni hala kin manta ina tare da Nasir? Kuma ko da Affan yazo mun yi deciding Farhan, itama har ta aminta da shi" "Wane aminci ita da ko number juna basu, ta riƙa shan ƙamshi tana miskilanci na iskanci, to ai kuwa idan ma hange take ta daina, saboda ke ya zaɓa kuma babu abinda zai hana aurenku" Farhan da gudu ta yi ɗakinta, ita kuma Ayda ta dafe kai. "Anni dan Allah ki ƙara magana dasu wallahi ina son Nasir." "Kina son Nasir amma ƙaddara Affan ta zaɓa miki, Ayda shi fa Nasir ɗin nan bai shirya aure ba, saboda sau biyu ana cewa ya fito amma yaƙi, to mene amfanin soyayya da gaibu?" Duk yadda taso Anni ta fahimta amma ta ƙi, sai kawai ta juya ta yi bedroom, tana shiga Farhan ta ɗago ta kalleta. "Wallah ban ga wanda ya isa ya hanani auren Affan koda kuwa kece" Cike da mamaki take kallon Farhan, sai kuma ta goge hawaye tana murmushi. "Wai kina yiwa Affan wannan son amma kika kasa tsayawa ku fahimci juna?" "Ke Ayda ki shiga hankalinki, ni ba sa'arki bace" Murmushin yaƙe tayi sannan ta ce "Tun zuwansa ni ban ɗora raina a kan shi ba, saboda ina son Nasir kuma da shi nake son rayuwa." "Idan har haka ne meyasa Affan ya zaɓeki?" "Saboda shimfiɗar fuska tafi ta tabarma, zan faɗa miki gaskiya wannan jan ajin da kike yi babu abinda samari ke kallon shi face wulaƙanci, ko shi Affan tun ranar daya zo abinda kika riƙa yi naga bai ji daɗi ba kuma fuskarshi ta nuna, sai dai shi mutum ne mai zurfin ciki shiyasa ma bai taɓa faɗa min ba, kuma idan kin lura bai kuma dawowa ba. Sai dai ya faɗa min cewa zafin kishin matarsa ta farko shi ne abinda ya jawo mata baƙin jini a gurin family sannan kuma ya fara tunanin ƙara auren wannan yarinyar da aka kashe gab da bikinsu." Zama Farhan ta yi tare da faɗin "Nima da wasa nake, kin san bani da wannan kishin" "A yanzu ba zan gane ba, amma a shawarce ko kina da shi to ki rage. "Ayda wallahi na ji ina son shi, ta ina kike tunanin zan ɓullowa lamarin?" "Dole mu zauna mu nutsu sannan mu yi tunanin mafita." *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 17``` "Gaskiya jininta ya yi ƙasa sosai, dole sai an ƙara, zafin zazzaɓin ne ya jawo haka dan da baku kawo ta asibiti da wuri ba gaskiya da wata maganar ake ba wannan ba" Surayya ta kalli Mameey cikin tashin hankali. "Dr a rubuta sai aje a saya a saka mata" "Haba Mameey mene amfanin jini yazo iri ɗaya, a ɗebi nawa a saka mata, blood group ɗinmu ɗaya, dukkanmu A+ ne" "Faruq na manta ai saboda gabaɗaya a ruɗe nake, kuje a ɗiba ke kuma Surayya kije ki sayo masa malt da madara. Suna zaune jinin yana ɗiga a hankali, Surayya na riƙe da hannun da aka saka cannula, Mameey na zaune kan kujera shi kuma yana tsaye. "Jini na da Aunty Sady zai ƙara haɗuwa a yanzu, dama kuma ita ce favorite ɗina" Murmushi Surayya ta yi haka Mameey ma, dan duk basu kawo komai ba, bare gane abinda yake nufi. Shigowar Saddiqa ta saka duk suka kalli ƙofa. "Ya Allah, abin har ya kai haka?" Ta faɗa tana ƙarasawa jikin gadon. "Wallahi kuwa" "Har da ƙarin jini" Mameey ta gaida sannan ta ƙurawa Sadiya ido. "Mameey dan Allah ku dawo mata da yaranta." Ajiyar zuciya Mameey ta sauke kafin ta ce "Gani kuke kamar bana son Sadiya ko yaranta?" Shiru suka yi babu wanda ya iya cewa komai, ita kuma ta cigaba da cewa "To ba haka bane, ku sani daga ranar da muka nuna mun damu da yaran to daga ranar Yazid da iyayensa za su samu lagonmu, za su yi amfani da damar ne su riƙa ƙuntata mana kuma ba za su dawo da yaran ba, amma idan muka nuna musu bamu damu ba wallahi da kansu za su dawo dasu, kuma ko ba su dawo dasu ba a yanzu na tabbatar yaran nan in suka girma za su nemi uwarsu" "Allah ya sa haka ahi ne mafi alheri" Cewar Saddiqa. "Kin yi masa kwatancen?" "E, ya gane ma, ya ce yanzu zai zo ya dubata" Faruq ƙara haɗe rai ya yi, ya ji wani baƙin kishi ya turniƙe shi. Ya kalli Saddiqa ya ce "Ni fa bana son Affan ɗin nan ko kaɗan" "Aikuwa baya da matsala, kuma yana da kirki da jan mutane a jiki." "Ko ma dai mene bai dace da ita ba" Saddiqa za tayi magana aka turo ƙofa, Affan ne tare da Lawisa, dukkamsu da manyan ledoji biyu a hannu. Ƙarasawa ta yi ta ajiye a gefe. "Har da ɗawainiya haka?" "Babu komai Aunty Saddiqa ya mai jikin?" "Da sauƙi, ɗazu ma ta farka an yi hira da ita, bata daɗe da komawa bacci ba" "Allah ya bata lafiya" "Amin ya Allah" Itama Lawisa dubata ta yi sannan ta sanar musu Mommy ma ta ce a duba ta. Tun da Affan ya shigo Faruq ya ƙura masa ido har sai daya gane hakan amma dai ya basar. ******** Tun da aka kawo su gidan Najma take kuka, ta yi kuka har ta yi bacci amma tana tashi ta ɗora daga inda ta tsaya. Suna jin kukan na ta amma sun yi banza sun ƙyale babu wanda ya damu a cikinsu bare ya rarrasheta. Ɓangaren Yazid kuwa yana tare da Lukman ya kuma gama labarta masa duk irin abubuwan da suka faru sannan ya ƙara da cewa "Ka ga dai Umma ita ta dage in ɗauko yaran amma babu wanda ya yi maraba dasu har tsoron komawa nake kukansu har cikin raina haka nake ji" "Ba zan fasa faɗa maka cewa ka yi kuskure ba, raba yaran nan da mahaifiyarsu a yanzu kam dama akwai matsala, ita kan ta bana tunanin tana lafiya a yanzu, ina ganin me zai hana ka mayar mata da yaran kawai, idan ka yi aure sai ka kwashe su ka mayar hannun matarka." "Abu ne mai wuya mahaifiyarta ta karɓi yaran idan na mayar, a gabanka aka yi komai Lukman" "To shin su yara mene laifi nasu da suke fuskantar tsangwama ta ko wane ɓangare?" "Ni kaina abinda nake tambayar kaina kenan a kullum, amma dai na san na yi wauta, ina ji a jikina ban yiwa Sadiya adalci ba." "Hmmm! Ai ba yanzu ya kamata ka faɗi wannan ba. Yanzu dai kaje ka ga halin da suke kafin ka koma gida, sannan ka kwantar musu da hankali." Kai ya gyaɗa sannan suka yi sallama da Lukman. Tun daga zaure yake jin kukan Najma har tana kakarewa, sai dai ga mamakinsa yana sallama ya gansu su biyu rak a tsakar gidan ita Najma na kuka, Ihsan kuma tana zaune gabanta tana tsotsar hannu. Da sauri ya ƙarasa gabansu ya zauna ga uban sauro a tsakar gidan. "Waye nan?" Ya ji muryar Umma daga ɗaki. "Ni ne!" Ya furta a sanyaye. Maryam ce ta fara fitowa tana ɗan sosa kai. "Yanzu na ce bari na masu shimfiɗa" Shiru ya yi bai ce komai ba, Umma ta ce "Ai Fatima kamata ya yi ta musu shimfida kafin ta yi bacci, dan ni kam ai ba ni aka kawowa reno ba bare na yi jigilar yara." Nan ma bai ce komai ba, sai dai kawai tambaya da ya yi ko sun ci abinci. "Yaya babu yadda ban yi ba, amma suka ƙi ci" "Kawo min abincin" Kai ta ɗan sosa, "Amm....." Ta kasa magana. "Babu abinci fa, ya kike wani kame-kame ki faɗa masa gaskiya." Umma ta faɗa kai tsaye. "Umma yara ba su ci abinci ba kuma a kasa ajiye musu?" "To ya kake so a yi ne Yazid? Sun ƙi ci, har ɗure muka musu suka zubar, kuma ka san yanzu dai abinci a hannu a hannu yake, tunda ba za su ci ba ai akwai masu buƙata. Miƙewa ya yi, tare da faɗin "Ina zuwa" Da sauri ya fita. Ya ɗan juma bai dawo ba sai ga shi da ya dawo da takeaway na tuwon semovita miyar agushi da Bobo sai 'yan biscuits daya saya musu. Da kan shi ya basu abinci, ya lallaɓasu sosai suka ci, suna gamawa a jikinsa Ihsan ta yi bacci, itama Najma ta kwanta kan cinyarsa, yana ɗan musu fifita saboda sauro haka har sukayi bacci dukkansu. Yana zaune ya kwaɗawa Maryam kira, ta fito. "Kin musu shimfiɗa?" "E Yaya Yazid, na saka musu gidan sauro ma" "To muje na kwantar dasu" Sai daya kwantar dasu sannan ya kalleta ya ce "Maryam dan Allah ki kula dasu, yanzu suna tare da kewar mahaifiyarsu ne" Kai kawai ta gyaɗa, ya fiddo dubu ya bata. "Da safe sai a ƙara a break" "To Yaya sai da safe" "Allah ya kaimu" Yana kwance kan gado yana juyi ya rasa ya zai yi, Sadiya ce kawai ke faɗo masa a rai, lokacin da take kuka tana roƙonsa ya mayar da aurensu ko dan yaranta. "Anya na miki adalci Sadiya?" Ya faɗa a sanyaye, sannan ya ja numfashi da ƙarfi. "Mene ke faruwa dani? Meyasa na biyewa son zuciya na cutar da yarana da kuma Sadiya da ta sadaukar min da rayuwarta" Ya saka hannu ya damƙi fuskarsa. ****** ****** Kallonsa kawai take tana mamaki kafin ta ce "Ka ga ka tashi Affan, dan za ka roƙeni abu ba sai ka durƙusa min ba, ka da ka manta numfashi ma ina yi ne domin ku, kuma lokacin da mahaifinku zai rasu ya bani amanarku kuma ya ce kar in bari wani a cikinku ya yi kukan maraici, sannan kuma in baku tarbiyyar da har abada ba zaku ɗauko masa abin kunya ba. Na san kuma na baku tarbiyya kuma na gatanta ku, duk wani abu da kuke so na kan yi ƙoƙari na tayaku so, amma Affan a yanzu ni meyasa ba zaka so abin da nake so ba?" Lawisa ta ɗora hannunta kan cinyar Mommy tare da faɗin "Mommy kada ki manta irin son da Yaya Affan yake yiwa Nashwa, ni na san dama hakan sai ta faru" "Wannan ai ba Nashwa bace, kuma kama da wane bata wane" "Ina kallonta ne a matsayin Nashwa ta ce Allah ya dawo min da ita, Mommy dan Allah ki taimaka min ki ji tausayi na karki hanani kar ki bari na rasa Sadiya" Kan sa ta dafa tana murmushi ta ce "Na amince amma nima ina so ka auri Ayda kafin ko bayan ka auri Sadiya ka yi min alƙwari" "Shi kenan na amince Mommy" Lawisa ta sake yin murmushi. "Yaya da alama dai mata biyu zaka zauna da su a rayuwarka. "Zan yi magana da Uncle ɗinku acan Yola, in yaso sai su shirya zuwa next week su je, idan ta kama ma kawai a bayar da sadaki sai a tsayar da rana tunda bazawara ce, ba wani jan abin za a yi ba" "Duk yadda kika tsara ya yi" "Kana zuwa gurin Ayda?" "A'a tun last week ban koma ba, but muna waya" "Ka dai yi ƙoƙarin kwatanta adalci a tsakaninsu" "Insha Allahu" "Allah ya tabbatar da alheri" "Amin." Yana shiga ya faɗa kan gado tare da ɗauko waya ya kira number Sadiya, sai dai har ta gama ringing ta katse bata ɗaga ba. Ya kuma kira a karo na biyu, shima har ta kusa katsewa ta ɗaga. "Lu'ulu'u!" Ya furta lokacin da ta ɗaga, yana jiyo sautin murmushin ta. "Jiki ya ƙara sauƙi ko?" "E alhamdulillah, ai na fara cire komai a raina" "Ki cire gabaɗaya ma, Allah yana tare dake" "Hakane, fatan kana lafiya" "Lafiya lau, wani albishir zan miki amma dai sai na shigo gobe" "Kenan baka so na yi bacci yau?" "No ai albishir na ce kin ga kenan abin farin ciki ne" "Ni dai gaskiya a faɗa min" "Lu'ulu'u maganar ba ta waya bace" "To ai da sai ka ƙi faɗa in kazo kawai ayi ta" "Afuwan, zumuɗi ne ya saka na yi suɓul da baka" "To aikuwa ko hint ka bani" "Okay but kiyi min alƙawari za ki bani goron albishir" "An gama yallaɓai" "Yanzu muka gama magana da Mommy ta ce min ƙila next week za a turo gidanku tambaya kuma har da sadaki" Tana daga kwance ta miƙe zaune. "Joke aside" "Sadiya am not joking" "Alhamdulillah" "Finally dai za ki zama tawa Sadiya" Hannu ta saka ta rufe fuska kamar yana gabanta, sai kuma ta buɗe. "Allah ya tabbatar mana da alheri" "Amin" Ta furta a daidai lokacin kuma aka turo ƙofa aka shigo, ajiye wayar ta yi shi kuma da ido yake kallonta. "La...lafiya?" Ta tambaya tana kallon Faruq. Still bai magana ba har sai daya ƙarasa jikin wardrobe sannam ya jingina da ita. "Mene aibuna?" Ya furta a sanyaye, idanuwa ta lumshe sannan ta cije laɓɓanta. "Faruq dan Allah ka haƙura ka daina magana akan abinda ba zai yuwu ba" "Mene zai hana shi yuwuwa?" Kallon shi ta yi sai kuma ta miƙe a gigice. "Ka ga yadda ka koma kuwa? Faruq wai wane irin so ne wannan? Ka yi hauka ne? Ya kamata ka farka daga wannan mummunan mafarkin. "Kin san wani irin jinya na sha kafin in iya haƙura dake a wancan lokacin? Shine kike tunanin a wannan lokacin zan yi?" Murmushi ya yi tare da cewa "Ba zan iya haƙura ba a wannan karon, ba zan taɓa iya bari ki suɓuce min ba" Yana gama faɗa ya wuce da sauri. A parlour ya tarar da Mameey zaune kan kujera Surayya na mata yankan farce. "Mameey" Ya faɗa tare da zama a ƙasa gabanta. "Faruq lafiya kuwa?" "Mameey idan na roƙi alfarma za ki min?" "Idan har zan iya" "Mameey aure nake so." "Aure?" Ta maimaita da mamaki, Surayya ta saki baki tana kallonsa. "E Mameey" "To amma Faruq kana ganin Dadanka za ta amince ka yi aure at the age of 24" "E Mameey ai kece uwata, duk abin da kika ce ba za a musa ba" "Na ji, iyayen yarinyar fa?" "Idan har kun amince suma basu da matsala." "Wacece?" "Sadiya ce Mameey" "Wacce kenan?" Ta sake tambaya dan bata taɓa kowawa Sadiyarta yake nufi ba. "Mameey ta gidan nan, Maman Najma" Dafe kai Sadiya ta yi, dan ta fito kenan ta ji wannan ɗanyen aiki da Faruq ya yi, ita kuwa Surayya hannu ta saka ta rufe baki tare da zaro ido. *Saura Pages 3 mu gama free pages, ku biya in kuna so a cigaba da karatu daku.* *_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._* *_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_* Guda 1: ₦500 Guda 2: ₦900 Guda 3: ₦1400 Guda 4: ₦ 1800 _Za'a turo kuɗin ta wannan account._ *Acct no: 6370370016* *Acct name: Halima Salahu Adamu* *Bank name: Fidelity Bank* *Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* *Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.* *Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671* lLITTAFAN SUNE: 1-WUTAR ƘAIƘAYI 2-WA'ADI. 3-A CIKIN IDO.. 4-TAZARAR SO #FITATTUHUƊU2025 #WUTARƘAIƘAYI #SaNaz_deeyah [7/9, 9:43 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI* _Wattpad@SaNaz_deeyah_ _Arewabooks@sanazty _Facebook@SaNaz Deeyah_ Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe Facebook Page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/ *KARAMCI WRITERS ASSOCIATION* _[karamci tushen mu'amula ta gari]_ _Book 1_ ```🆓Page 18``` Miƙewa Surayya ta yi, Mameey ta kalleta sannan ta yi mata umarni ta zauna, jiki babu ƙwari ta zauna tana kallon Faruq yayinda shi kuma yake kallon ƙasa. Sadiya kuwa da sauri ta juya tana hawaye. "Faruq ka faɗa min gaskiya, ko dai tsokanar mu kake?" Ɗago manyan idanuwansa ya yi wanda suka rine ya kalleta, sai kuma ya ɗauke, ita kanta Mameey ta tsorata da ganin yanayinsa. "Tuntuni nake da abin a raina, da farko na ɗauka shaƙuwa ce da kuma tausayi amma daga baya na gane ba haka bane, Mameey na yi ƙoƙarin na danne kar wanda ya sani amma na kasa fin ƙarfin zuciyata, ki tambayeta ki ji wallahi ciwon daya kwantar dani a asibiti kenan, ita kuma tana jin haka shi ne ta daina zuwa inda nake, Mameey duk da na san matar aure ce amma a lokacin ji nake kawai idan ba ita ba, ba zan iya kula ko wace mace ba, sai kuma ga shi yanzu ta rabu da mijinta kuma ana so a bata wani, Mameey dan Allah ki taimaka min kar na rasata" "This is serious, what!?" Surayya ta furta cike da mamaki. "Surayya ta shi ki bar nan" "Mam..." "Ki tashi na ce bana son musu" Jiki babu ƙwari haka ta miƙe ta wuce. Mameey ta mayar da kallonta ga Faruq ta ga yana goge hawaye. "Ka kwantar da hankalinka, ai ba a riga an ɗaura ba, ka ga dai ciwonka mun

Chapter 13 of 15