dai Faruq yana da zurfin ciki kuma yana da kafiya, tun abin bai yi ƙarfi ba har ya yi yazo ya fara taɓa zuciyarshi, wata rana naje asibiti sai aka fito da kowa waje dan a duba shi amma ni kuma sai Dr ya kirani, Likita da kansa ya sanar min cewa ni ce na jefa Faruq a wannan halin, ya kamu da sona kuma gashi na masa nisa saboda ina da aure"
Jin haka ya saka Yazid miƙewa tsaye, ita kuma ta ja numfashi sannan ta cigaba da cewa "Ban bar ɗakin ba sai dana masa gargaɗi idan ma ya haukace ya dawo daidai, bayan yara biyu da nake dasu na bawa Faruq shekara uku har da watanni a duniya, ko Surayya cewa tayi ya mata yaro da aure bare ni, na faɗa masa cewar ko bani da aure ai nafi ƙarfinsa, na sanar da shi cewa muddin bai janye ba to zai kashe kansa a banza. Tun daga ranar ban sake komawa asibiti ba, ko kai nan kasha ƙwawar naje amma sai na goce, ciwon nasa ya yi tsanani shi ne aka tafi da shi Germany to ranar a airport ya bawa Saddiqa wannan ta kawo min, idan baka yarda ba ka tambayeta, wallahi Yazid ko da wasa ban taɓa tunanin cin amanarka ba, amma sai ga shi kana zargina har da ƙaurace min." Miƙewa tayi wannan karon bata yi yunƙurin goge hawayen ba ta fice da sauri.
Tana shiga ɗaki ta fashe da kuka a fili, Najma da Ihsan duk suka farka, aikuwa Najma ta hau kukan itama, ya shigo ɗakin a sanyaye ya hau kan katifar.
"Haba Sadiya ya za ki ɗagawa yara hankali a daren nan?"
Bata tanka masa ba sai dai ta daina kukan a fili sai shashsheƙa, ya janye Najma a jikinta ya ce "To yi shiru mana mene na kuka, itama Mommy ta daina, kwanta kiyi bacci abinki" Janyewa tayi ta sake komawa jikin Sadiya ta kwanta, haka Ihsan ma, shi kuma a hankali yake ɗan shafa bayan Najma har ya samu tayi bacci, dan Najma ta fi Ihsan rigima da ƙwalafacin uwa.
Yana ganin sun yi bacci ya dubeta, ya ga fuskarta har ya ɗan kumbura saboda kuka. "Sadyna ki kwanta kiyi bacci"
"Ba na ji" Ta furta da muryarta wadda da ƙyar ta fita saboda ta dashe.
"Dan Allah kiyi haƙuri na san ban kyauta ba dana kasa tsayawa na bincika amma ki bari da safe mu yi maganar."
"Abban yara wallahi bana jin bacci kawai kaje ka kwanta"
"Ba zan iya kwanciya na barki a damuwa ba, please Babyna" Ya faɗa yana komawa gabanta sannan ya miƙar da ita, ya ja ta ɗakinshi.
Suna shiga ta fashe da sabon kuka, a hankali ya rungumeta yana rarrashin abarsa da ƙyar ya shawo kanta ta samu tayi bacci, shi kuma ya ƙura mata idanu cike da tausayawa.
"Tabbas na miki bahaguwar fahimta, ki gafarce ni hubbyna" Ya daɗe a zaune kafin daga bisani bacci ya ɗauke shi.
****** ******
Sai da ta gama duba kayan sannan ta kalleshi da murmushi. "Sun yi kyau amma fa Yaya ina tsoron mijinta kar ya mana tijara"
"Kina ganin har sai ya yi haka duk da yaransa na kyautatawa?"
"Talaka fa faɗin rai ne da shi, kuma ka ga wannan atampopin da wannan lace ɗin zai ga a wane dalili zaka sayawa matarsa"
"A dalilin Nashwa, na taɓa saya mata kuma ta ɗinka na ganta dasu"
"Yaya wannan ba Nashwa bace kuma...."
"Stop it da Allah!" Ya dakatar da ita da tsawa. A tsorace take kallonsa kafin ya sauke nannauyar ajiyar zuciya.
"Lawisa kiyi abin da na saka ki"
"Allah ya huci zuciyarka Yaya"
"Amin" Ya furta tare da barin ɗakin ita kuma da ido kawai ta bi shi.
Yana fita parlour ya tarar da Mommy zaune tana waya, ya samu ɗaya daga kujerun ɗakin ya zauna sannan ya kalli Mommy, yana jin yadda take wayar ya san maganarsa ake, har sai da suka gama sannan ta kalleshi.
"Affan ya dai? Na ga baka cikin walwala"
"Mommy akwai abin da ke damuna"
"Wane abu ne?"
"Mommy wannan mai kama da Nashwa dana faɗa miki"
"E, me tayi?"
"Ba komai kawai dai har yanzu ina ji a jikina kamar Nashwa ce Allah ya dawo min da ita."
"Na yi tunanin har kun daidaita ai, yanzu muke waya da Hajiya Bilkisu ta ce min kaje ka ga 'yarta ko zaku daidaita, to kuma sai na ce mata akwai wadda kake so amma ban san ya ake ciki ba zan yi magana da kai."
"Mommy ni gaskiya babu wurin wadda zan je, kawai dai ace ta yi haƙuri"
"Ta faɗa min yarinyar za ta zo nan gobe, so ina so in san idan kun daidaita da ita wadda kake cewa tana kama da Nashwa"
"Ba mu daidaita ba, sai kin bani lokaci Mommy"
"To Affan Allah ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi"
"Amin Mommy."
****** ******
"Ki ajiye wanki nan Sadiya kin ga dai kin yi da yawa ki bari na ƙarasa sauran sai kiyi shanya"
Murmushi ta yi sannan ta ce "Abban yara kenan, tunda dai ka dage bari na je na ɗora girki"
"To ai dama wanki na namiji ne kuma kin san ko ba wanki ba ai sunnah ne miji ya taya matarsa aiki."
"Ga matar da ta shanye miji ba!" Da kakkausar murya suka ji maganar wanda maganar ita ce sallamarta.
"Yakumbo Bahijja sannu da zuwa"
"Kai dalla rufa min baki lusarin namiji kawai" Ta faɗa tana ƙara shigowa cikin tsakar gidan.
"Yakumbo ina yini"
"Idan ban yini ba za ki ganni ne? Munafukar mace"
Wani yawu mai ɗaci Sadiya ta haɗiya sannan ta sauke kai ƙasa.
"Ka zo ka saki baki kana washe wa mace baki kana mata aikin gida. Wai ba a faɗa maka abin da wannan matar tayi ba, ta tsaya da kwarto a ƙofar gidanka amma ban ga alamun ka ɗauki wani mataki ba."
"Yakumbo wallahi yadda kuke tunani ba haka bane"
"Oh baka yarda kwartuwa bace fasiƙa?" Ɗago ido Sadiya ta yi har sun kaɗa sun yi jajir ta kalleta.
"Kika ƙura min ido kamar mayya ko za ki dake ni ne?"
Da sauri ta miƙe ta shige ɗaki tana gunjin kuka.
"Ga mahauƙaciya tana magana ko, shi ne ta wuce ta barni anan tsaye."
"Yakum....."
"Ka rufa min baki Yazid wallahi ka bani mamaki, zuwa na yi yanzu a gabana ka danƙarawa matar nan saki kafin ranka ya yi mummunan ɓaci"
Kallon ƙofar ɗakin ya yi sannan ya juyo ya kalli Yakumbo Bahijja.
"Sadiya baiwar Allah ce, duk yadda kuke tunani ba haka bane."
Sallamar yaro ne ya dakatar dasu duk suka kalli ƙofar.
"Ana sallama da Sadiya" Yaron ya faɗa.
"Inji wa?" Cewar Yakumbo.
"Wani ne a mota"
"Ka gani ko? Kwarton ya ƙaraso kenan" Ta kalli yaron ta ce "Kace tana zuwa" Yakumbo Bahijja ta faɗa.
Sai da yaron ya fita sannan ta kalleshi ta ce "Sai ka kirata muje mu ƙure ƙaryarta ko"
Shiru ya yi bai ce komai ba.
"Magana nake maka ko baka ji na ne"
Jiki a sanyaye ya juya ya shiga ɗakin.
"Sadiya" Ya ambaci sunan tare da zama gefen gadon. Bata amsa masa ba sai dai hannu da ta saka tana goge hawaye wasu na sake zubowa.
"Sadiya kin yi da wani ne zai zo a gidan nan ko a family ɗinku?"
Kai ta girgiza alamar a'a.
"To waye kike tunanin ya zo gurinki?"
Bata ba shi amsa ba dan bakinta ya mata nauyi ba zata iya furta ko kalma ɗaya ba.
"Yakumbo ta ce ki fito muje, amma ina so na san waye kafin muje"
Kawai gani suka yi ta ɗaga labule.
"Malamai jiranku nake, ke ki tashi ki ɗauki hijab ɗinki."
Sam bata basu damar magana ba har Sadiya ta ɗauki hijab ta zura suka fita.
Tana fita gabanta ya yi mummunan faɗuwa ganin Affan tsaye jikin mota.
"Ka gani ko?" Yakumbo ta faɗa da ɓacin rai sannan ta fuzgi hannun Sadiya da ƙarfi ta ƙarasa gaban Affan.
"Kai ne ka zo nemanta?"
"E, amma nazo gurin yar...."
"Dakata Malam, kai baka kunyar kwartanci da rana tsaka?"
Buɗe baki ya yi yana kallonta.
"Ko bata faɗa maka ita ɗin matar aure bace, ko dan irinku masu hannu da shuni kun fi son bin matan aure saboda shi iskancin gaba kuka ba shi."
"Kin ga malama ka da ki ƙara kirana da wannan sunan domin da mutuncina da kuma kimata"
"Ai ni ban gansu ba, tunda ga shi nan kana bin matar aure"
"Sadiya kamar ƙanwa take a gurina, kece dai kike so ki mayar da abin wata kala"
"Ƙarya kake a danginsu waye kai? Saboda ka ga mun kamaka red handed shi ne zaka fake da ƙanwa" Ta juya a fasace ta kalli Yazid.
"Kai kuma me kake jira kana gani ƙaton banza da matarka sannan yana faɗa min magana son ransa amma kayi shiru ka zuba ido, ka kira a maka shege cell ya ji in fasiƙanci da matar aure abin yi ne, kuma wallahi ko baka so sai ka rabu da wannan matsiyaciyar ayau ɗin nan"
Cikin ɓacin rai Affan ya fito da waya ya kira sannan ya ce yana so azo ayi arresting ɗin Yakumbo a bisa cin zarafin da tayi masa.
"Ni zaka yi wa barazana, to ina nan zan ga uban da zai ɗaukeni anan" Gaba ɗaya ta tara musu 'yan unguwa, ita kuwa Sadiya ta ja hijab ɗinta tana ta kuka.
Yazid ba irin haƙurin da bai bawa Yakumbo kan su koma gida amma taƙi sai ma ƙara zage-zage take tana faɗin yau ta kama kwarto kuma kowa sai ya sani, yana tsaya jikin motar ya kafeta da ido, kuma gurin kowa ya kasa tunkararsa ganin yadda yake da kuma motar daya zo da ita sun san babban mutum ne.
Taku biyu ya yi ya ƙarasa gaban Sadiya, anan ran Yazid ya ɓaci sosai.
"Sadiya ki koma gida saboda ke matar aure ce kina da daraja, ki barni da matar nan"
"Kai Malam ya haka? Ina ruwanka? Ni ne mijinta ba kai ba"
"Oh kai ne amma kuma ban ga alama ba, domin ban ga ka ɗauki hakan da daraja ba matarka a waje ana wannan hayaniyar amma ka kasa suturta ta"
"Kai har ka isa ka faɗa min yadda zan yi da matata, kana da hankali kuwa?"
Cikin ɓacin rai Yakumbo ta ce "Ka gani ba, matarka amma yana maka iko da ita, wannan ai shirmen banza ne."
Affan bai ƙara cewa komai ba kawai ya koma jikin motarsa ya tsaya.
Suna nan tsaye sai ga motar 'yan sanda, suna isowa suka ƙarasa gaban Affan.
"Ga ta nan ku yi arresting ɗinta" Ya faɗa yana nuna Yakumbo, sai kuma a lokacin ido ya raina fata.
"Ki shiga mota ko na shigar dake"
"Idan baka san darajar mace ba sai ka shigar dani, Yazid kana gani ana ci min mutunci ko?"
"Yakumbo kije kawai zan biyo bayanki"
Kallon Sadiya tayi sannan ta ce "Wallahi tsanarki yanzu na fara, kuma kin gama aure a ahalinmu ni zaki saka a nuna wa arziƙi ko?"
Cikin ɓacin rai ta shiga bayan motar suka ja.
A fusace Yazid ya juyo ya kalli Sadiya ita kuma gabanta ya sake faɗuwa taji ƙirjinta ya yi wani irin duka.
"Ki wuce gida mana me kika jira" A furgice da juya ta wuce, Affan kuma da ido kawai yake bin ta yana jin da yana da iko sai ya hukunta Yazid kan tsawar da ya yiwa Sadiya.
"Kai kuma kana ganin kayi amfani da kuɗi ka tozarta mu, to ka sani ni kuma wallahi sai na rama"
"Ba zaka taɓa iyawa ba, baka da ƙarfin nan, sannan ni ban maka abin da zaka iya ramawa ba, kwarto ta kirani bayan ni ko ƙofar gidanka ban tsaya ba bare na shiga ciki, to ta ina na yi kwartancin kenan? Wallahi sai na ɗauki ƙwaƙwƙwaran mataki akan wannan ƙazafin" Yana gama faɗa ya shige mota ya ja rai a ɓace.
Da sauri Yazid ya shiga gida. Tun daga zaure yake kwaɗawa Sadiya kira har ya shiga ciki. A tsakar gidan ya tsaya yana huci, ita kuma tana zaune kan daɓe ta haɗa kai da gwiwa.
"Sadiya ki ɗago ki faɗa min alaqarki da shi da har yake zuwa gidanki kai tsaye"
Miƙewa tayi hawaye sharkaf a fuskarta ta ce "Yanzu Yazid har ka fara zargina?"
"Zargi ko gaskiya, kina ganin tijarar da ya yi sannan kai tsaye ya turo a kiraki fa, Sadiya mene tsakaninku?" Wannan karon cikin tsaya ya yi maganar.
Kuka ta ƙara saki da ƙarfi, Ihsan ta fito daga ɗaki ta ƙarasa gabanta. "Mommy wane ya dokeki?" Rungume Ihsan ta yi ta ƙara durƙushewa a wajen tana kuka.
*_Littafin nan na kuɗi ne tare da tagwayensa, zaku iya sayen ɗaya, biyu, uku ko kuma gabaɗaya huɗu, zaku iya biyan kuɗin karatu a yanzu domin ku samu damar shiga cikin group ɗin da za a riƙa yi muku posting._*
*_VIP na littafin WUTAR ƘAIƘAYI ga wanda basu son shiga group za a tura masu ta PC a farashin ₦1000 a maimakon regular da yake ₦500 ga kuma yadda tsarin biya yake:_*
Guda 1: ₦500
Guda 2: ₦900
Guda 3: ₦1400
Guda 4: ₦ 1800
_Za'a turo kuɗin ta wannan account._
*Acct no: 6370370016*
*Acct name: Halima Salahu Adamu*
*Bank name: Fidelity Bank*
*Sai a yi screenshoot a turo shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
*Idan kuma VTU ne ko katin waya za'a turo ta wannan number 07035441599.*
*Shaidar biya ta wannan wannan number 07035111671*
lLITTAFAN SUNE:
1-WUTAR ƘAIƘAYI
2-WA'ADI.
3-A CIKIN IDO..
4-TAZARAR SO
#FITATTUHUƊU2025
#WUTARƘAIƘAYI
#SaNaz_deeyah
[6/18, 1:56 PM] SaNaz_deeyah: *WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@sanazty
_Facebook@SaNaz Deeyah_
Tiktok Handle: Habibtyn Habibi👸💍🦋
Youtube: https://youtube.com/@dominkunovelstv?si=EvQRP2tRDalw8-fe
Facebook page: https://www.facebook.com/share/16d2wDeqer/
*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_Book 1_
```🆓Page 9```
Rai a ɓace ya wuce ɗaki, bai daɗe ba sai gashi ya fito haka ya saka kai ya fita ya bar ta cikin tashin hankali. Tana durƙushe a ƙasa har ta yi kuka ta gama sai hawaye kawai dake fitowa jefi-jefi, maƙotanta biyu suka doka sallama. Baki kawai ta motsa dan muryarta taƙi fitowa; su ma jikinsu a sanyaye suka shigo suka zauna.
"Sadiya dan Allah kiyi haƙuri"
Hannu ta saka ta goge hawaye sannan ta ɗan yi murmushi wanda iyakarsa leɓe.
"Sannunku da zuwa."
"Yawwa, kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki."
Sun mata kara sosai domin sun zauna har bayan magriba sannan suka tafi, Sadiya hankalinta a tashe yake sosai ta kasa sukuni ta kasa sakin jiki haka har aka yi isha'i tana zaune tana zulumin abinda zai je ya dawo.
"Ina take algungumar" Shi ne abinda ta ji lokacin ta gama yi wa yara shimfiɗa. Fatima da Maryam ne suka shigo sai wata ƙanwar Umma mai suna Aunty Adawiyya. Sadiya na fitowa tsakar gida kawai taji an rufeta da duka ta ko ina, tun tana ƙoƙarin kare kai har ta kasa jikinta gabaɗaya sun mata lilis bakinta kuwa har ya fashe haka suka barta a kwance tana numfarfashi. Najma na gabanta tana jijjigata ita kuma Ihsan tuni ta yi bacci, tun tana iya gane abu har ta daina saboda dukan da suka yi mata.
***********
"Hajiya sai dai fa ku yi haƙuri amma ba zamu iya ba da beli ba sai dai ku dawo zuwa gobe idan wanda ya shigar da ƙara ya yafe, amma ba a ba mu damar beli ba"
"Officer dan Allah ku taimaka wallahi tana da larurar hawan jini"
"Amma ta san da haka take rashin kunya?"
"Haƙuri za kuyi dan Allah"
"Gaskiya ba zai yuwu ba"
Har zai ƙara magana Umma ta ce "Rabu da su Yazid, mu je kawai"
Kallon Umma ya yi sannan ya ce "Yakumbo Bahijja bata da lafiya"
"Yazid zama anan ƙarin cin mutunci da ƙasƙanci zai ja mana, saboda talaka ba su ɗauke shi a bakin komai ba"
Kallon ɗan sanda ya yi sannan ya juya kawai ya fita rai a ɓace Umma ta mara masa baya.
"Yazid!"
Ya ji ta kira sunansa dan haka ya tsagaita saurin da yake, ita kuma ta ƙaraso gabansa ta kalle shi sannan ta ɗan kauda kai.
"Ka haƙura da wannan yarinyar indai ba da gwal aka ƙerata ba, kai ko gwal ce ita ai babu amfanin tarayya da abin da zai cutar da kai."
"Umma ba laifin Sadiya bane, saboda ni ban ga alamun ta san shi ba."
"Yazid na tabbatar da ta san shi dan ni na ga hakan da idona ba labari aka bani ba."
"Umma maganar ba ta nan ba ce, mu samu mu fitar da Yakumbo dai tukun."
****** ******
Yawo yake a tsakar ɗakin kafin ya juyo ya kalli Lawisa dake zaune kan sofa.
"Shiyasa na ce miki muje tare saboda bana so a samu matsala amma sai kika kawo min wani banzan uzurinki."
"Yaya ka yi haƙuri dan Allah wallahi ni da na san haka za ta faru da da kaina zan karɓa na kai."
"Hmmm! Ban taɓa ganin saunan miji kamar nata ba, wallahi darajar aure kaɗai ya saka ban wanka mishi mari ba, saboda idan na mare shi abin kan ta zai koma."
Ɗan zaro ido tayi sannan ta ce "To alhamdulillah tunda baka yi marin ba, amma fa wallahi da mun shiga uku, so kake ya fassaraka?"
"Na nawa kuma, ai sun yi kuma sai na shiga kotu da ita"
"Yaya Affan abi abin nan a hankali wallahi idan Mommy ta gane abin da muka aikata za a iya samun matsala"
Shiru ya yi tare da zama gefen gado ya saka hannu a fuska rai ɓace.
"Yaya!" Lawisa ta furta a sanyaye.
Ɗago ido ya yi ya kalleta.
"Ka yi haƙuri ka ba da damar a sallameta"
"Ba zan iya ba, sai na ɗauki mataki, domin da kwarto ta kirani bayan ko ina saurayi ban yi ba bare yanzu"
"To ni dai na gama shiri yanzu zan tafi, idan naje duk abin da ake ciki sai mu riƙa waya"
"Kin dage dai amma da kin bar ni naje da kaina"
"A'a duk da nan Kano ne amma za a iya samun wani wanda ƙila an masa transfer daga can yazo nan, ko kuma wani wanda ya san case ɗin ka acan Yola gara dai naje"
"Har tsawon wane lokaci kuke so na ɗauka ba tare da na sake ba?"
"Ko iya haka ma ai ka sake tunda kana zuwa ko ina."
"Ni fa yanzu babu komai a tare dani duk wani evidence da muke da shi yana gurin Nashwa kuma sun kashe ta sun karɓe komai to kina tunanin me zan iya yanzu, amma da ace ina da hujja a kansu ko ɗaya ce wallahi da sai na tona musu asiri"
"Allah ya ji ƙan Nashwa"
"Amin ya rabbi."
Tare suka jera suka fito, suna shirin fita Mommy ta sauko daga sama. "Ina zuwa kuma?"
Gabaɗaya suka jiyo suka kalleta.
"Ni fa ban gane me kuke nufi ba anya babu abinda kuke ƙullawa kullum sai na ganku tare"
Murmushi Affan ya yi sannan "Mommy ko mene za a ƙulla ai za ki sani"
"To ina kuma zaku tafi?"
"Lawisa ce za ta fita, ni ina gida babu inda zan je"
"Sabon salo ne yasa zaka rakata mota?"
Sai lokacin Lawisa ta ce "Kai Mommy"
"Kin ga Lawisa sai kin dawo" Ya furta yana juyawa ita kuma ta yi murmushi.
"Mommy an kirani emergency call daga asibiti so zan je na ji"
"Okay sai kin dawo. Kai kuma ƙaraso dama ina son magana da kai"
Suna zama ta kalleshi "Affan ka daina maganar aure ko?"
Ɗan murmushi ya yi sannan ya ce "Mommy ba haka bane, kece gabaɗaya kin yi min takunkumi"
"Affan kenan, yanzu dai ba wannan ba, ka ga dai tunda aka ɗauke Badriyya yau ku san wata huɗu kenan babu wanda ya sake kira, ko saki ma basu nema ba to shi ne na ce me zai hana mu nemesu ka sawwaƙe mata kawai"
Mommy ya ƙurawa ido dan gani yake kamar ba ita ba, bai taɓa tunanin za ta faɗi wannan maganar ba, ta cigaba da cewa "Na yi magana da ɗayar ƙawar tawa anan Kano suke zaune akwai yaranta biyu, ina so ka je ka gansu sai ka zaɓi wadda ta yi maka a ciki, sannan na yi magana da wani director abokin mahaifinku ne tun yana raye mahaifinku ya hidimta masa har ya kai wannan matsayi na Director anan wata jami'a so ya ce akwai slot da aka ba shi ya kuma saka sunanka, so at anytime za a iya nemanka"
Zama ya gyara sannan ya ce "Mommy amma mene fa'idar sakin Badriyya?"
"Saboda haka suke buƙata"
"Mommy dan Allah kiyi haƙuri mu ɗan ƙara masu lokaci, saboda ni na san Badriyya tana sona."
"So na hauka dai, duk wannan bala'in ba ita ce ta jefamu a ciki ba"
"Mommy duk da haka ina neman alfarma ki bani dama na kirasu na kuma yi magana da ita kafin yanke hukunci"
Shiru ta ɗanyi rai ɓace.
"Please Mommy"
"Na ji ba damuwa na baka dama."
"Thank you Mommy"
"It's okay. Yanzu dai yaushe zaka je gidan Hajiya Bilkisu"
"Mommy yaushe kike so na je?"
"Ko zuwa weekend jibi asabar ko kuma lahadi"
"Zan je ranar Sunday insha Allah"
"To shi kenan Allah ya kaimu"
"Amin ya rabbi."
******** *******
A hankali ta fara buɗe idanuwanta da suka mata nauyi, kallonsu ta fara yi ɗaya bayan ɗaya, Saddiqa da Surayya ne a kanta, sai Yazid.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un." Ta furta hankali sannan ta kai dubanta ga hannunta da aka sakawa drip.
"Sadiya sannu" Saddiqa ta faɗa, sannan ta kalli Surayya, ki kira Dr kice ta farka.
Ɗan lumshe ido ta yi ta ji kanta yana juyawa sosai, sai kuma ta buɗe ta fara ƙoƙarin tashi zaune, Saddiqa ce ta taimaka ta zauna sai kuma ta fashe da kuka, a daidai lokacin kuma Surayya ta shigo tare da Dr.
"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki."
"Aunty ina su Najma?"
"Suna wurin Mameey"
Kallon Dr ta yi ta ce "Dan Allah Dr ka sallame ni yau." Ta sake fashewa da kuka.
A kan ta ya tsaya sannan ya ce "Kar ki damu zamu baki sallama idan muka ga yanayin jikinki amma dole sai kin kwantar da hankalinki."
Goshinta ya sha bandeji ga kuma gefen bakinta da ciwo.
Yana gama dubata ya ce "Kiyi haƙuri zamu saka miki drip idan ya ƙare sai a sallameki" Sai daya ɗauko ruwan ya saka mata sannan ya fita.
"Yazid kayi haƙuri amma zan iya samun matsala da duk wanda ya yi wa 'yar uwata wannan abin" Surayya ta yi maganar rai a ɓace.
"Surry kar na ƙara jin kin yi magana"
"Haba Aunty Saddiqa ki duba ki ga abin da suka mata fa, wannan wane irin abu ne, tun da Aunty Sadiya ta aure shi ba ta ƙara samun kwanciyar hankali ba."
"Surayya idan kika ƙara magana wallahi sai ranki ya ɓaci"
Shiru ta yi tana ƙara ɓata rai, kawai ta juya ta fita.
Saddiqa ta kalleshi ta ce "Ka yi haƙuri Yazid ka san Auta sai a hankali"
Murmushin yaƙe kawai ya yi tare da cewa "Babu komai."
Shiru ya ɗan biyo baya ƙafin ya ce "Aunty Saddiqa ina neman alfarma"
"To ina jinka"
"Dama game da Yakumbo da aka kama to sun ƙi sakinta dan a station ma ta kwana, sai yau ya ce sai ta ba shi haƙuri a bisa ɓata suna da ta masa sannan ta bawa Sadiya haƙuri. To kuma ga Sadiya a kwance a asibiti shi ne na ce ko zaki saka baki su saki Yakumbo wallahi tana da hawan jini, ta ba shi haƙurin ma ya ce lallai sai Sadiya ta haƙura zai ba da damar a saketa"
"Subhanallahi, waye wannan?"
"Wani ne wai Sadiya na kama da tsohuwar budurwarsa."
"Kuma sai me? Kama da wane ai bata wane."
"To haka dai ya ce, ni dai fatana a saki Yakumbo Bahijja."
"A saketa dan Allah ni dama ban ji haushin abin da ta yi min ba" Sadiya ta furta a sanyaye tana kwance a gado.
Saddiqa ta kalli Yazid ta ce "Ka kira a waya zan yi magana dasu."
"Nagode" Ya faɗa sannan ya kira wayar. Lawisa ce ta ɗaga suka yi magana da shi sannan ya ba Saddiqa wayar ta sanar mata da Sadiya ba lafiya amma ita kanta ba zata so a riƙe wani a dangin mijinta ko wani makusancin shi, sannan da kanta ma ta faɗa a sake ta dan haka su yi haƙuri komai ya wuce"
Sai da Lawisa ta kira Affan da ƙyar ta lallaɓa ya yarda aka saki Yakumbo.
_Bayan Kwana Biyu_
Har zai fita daga gida Umma ta dakatar da shi, ya tsaya yana kallonta kafin ya sadda kai ƙasa.
"Yazid ko dai ka fara shan wani abu?"
"Umma babu abin da nake sha"
"Yakumbon ka fa tana asibiti amma kuma ka ƙi ɗaukar mataki akan abin da matarka ta saka wani banza ya mata."
"Umma wallahi ni a ruɗe nake a
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 15