An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*WUTAR ƘAIƘAYI*
_Wattpad@SaNaz_deeyah_
_Arewabooks@Sanazdeeyah_
#FITATTUHUƊU2025
_*KARAMCI WRITERS ASSOCIATION*_
_[karamci tushen mu'amula ta gari]_
_BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM_
_Dukkan godiya da yabo su tabbata ga Allah maɗaukakin sarki mai kowa mai komai, tsira da amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta annabi Muhammad(SAW)._
_Wannan littafin mallakata ne, ban yarda wani ko wata ya yi amfani da shi ta wata siga ba, yin haka saɓawa doka ne kuma ba zan lamunta ba, a kiyaye!_
🆓Page 1
*_SHIMFIƊA_*
Tun daga ƙofar get na fara jiyo guɗa da shewa ta mata, na kai dubana ga ƙofar da mata ke ta tururuwar shigowa cikin gidanmu wasu daga cikin su suna ɗauke da akwatunan lefe. Ina kallo ana nuno inda nake da Yazid na tabbatar gulmata suke, ina kallo suka wuce da akwatuna set biyu ma'ana guda sha biyu cur. Murmushin yaƙe kawai na yi sannan na kai duba na ga Yazid dake zaune gabana, kan sa na gani a ƙasa, tuni ya lula wata duniyar tunani. "Yazid!" Na kira sunan sa a hankali, ya ɗago yana kallo na, "Tunanin me kake?"
"Wannan lefen Saddiqa ne?"
Murmushi na sake faɗaɗawa tare da cewa "E nata ne, ni sam ba a sanar dani cewa yau za a kawo lefen ba, na dai san ance mini cikin satin nan ne."
"Kiyi haƙuri Sadiya, sai na ga sam ban yi ƙoƙari ba."
"Ni kuma na ga ƙoƙarin ka Yazid, ka daina damuwa da abinda wani ya kawo, ka yi alfahari da naka, akwati biyar da ka kawo min duk wanda bai gode maka ba, ba zai zage ka ba, sannan ni ina alfahari da hakan. Yazid yatsun hannu ma ba ɗaya bane, samunka dana wani ba zai taɓa zama ɗaya ba."
"Nagode 'yar aljanna" Ya faɗa yana murmushi.
"Haka nake son ganin fuskar ka a ko da yaushe."
Hirar su suka cigaba da kuma tsara yadda abubuwan bikinsu zai kasance. Kafin daga bisani ya yi mata sallama ya hau machine ɗin sa ya bar gidan.
Tana shiga tana ana ɗaga kayan lefe ana ta yabawa, ta gaida su tana ƙoƙarin wucewa Umma Habiba ta kirata, dawowa tayi tare da tsayawa gabanta, "Baki ga lefen Saddiqa ba"
"Na gani Umma, so nake ku gama gani sai inzo in kalla, amma yanzu ga manya ai bana zauna ba."
"Yazid ɗin ya tafi ne?"
Kallon mamaki ta yi mata sannan ta ce "E, ya tafi!"
"To shi kenan, za ki iya tafiya."
Tana zama akan gado ta ji hawaye masu zafi sun sauka a kuncinta. _In dai Yazid za ki aura wallahi ba zan kai wannan kayan ɗakin gidan matsiyaci ba, gara na ajiye wa Auta._ Hannu ta saka ta goge hawayen da suke sunturi saman fuskarta, kafin ta miƙe ta cire gyalenta ta ninke ta saka a drawer. Tana juyowa Umma Habiba ta faɗo ɗakin.
"Ko aiki kike?"
"A'a Umma, babu abinda nake yi."
"Yawwa to zauna magana za mu yi."
Tana zama Umma Habiba ta riƙo hannayenta tare da faɗin, "Sadiya! Kar ki yarda ki ɓata ƙuruciyarki, a yanzu ba a auren soyayya auren mafita ake yi"
"Auren mafita kuma Umma?"
"E, ina nufin ko wace mace tana kallon inda za taje ta huta ne, har yaran talakawa bare ke da kike da gata."
Shiru Sadiya ta yi, dan ta fara fahimtar inda maganar ta dosa.
"Sadiya ki farka daga nannauyan baccin da kike yi, ki amince da zaɓin mahaifiyarki"
"Umma gaskiya ni bana son Alhaji Sani, kuma hankali na bai kwanta da shi ba, sannan bana son shiga ramin da ba nice na haƙa ba"
"Dalla shashasha, matar sa ɗaya ce, sai kuma yara biyu, ke kina tunanin idan Yazid ɗin ne ya samu dama ba zai ƙara aure ba, akwai wanda ya fi talaka rashin mutunci a lokacin da Allah ya ara masa lokaci"
"Umma ni dai Yazid nake so, kuma shi ne zaɓina, ko Abba kafin ya rasu ya sanarwa da Mameey cewa ta aura mana wanda muke so matuƙar baya da aibu."
"To aibun Yazid talauci, ba lallai ya iya riƙe ki ba."
Murmushi ta sake yi tare sa janye hannayenta.
"Ni dai Yazid ne zaɓina, kuma baya zaman banza yana da abin yi" Tana faɗa ta sauke kai ƙasa, Mameey ta shigo ɗakin hakan ya saka ta sake sauke kai ƙasa.
"Habiba! Ta ga lefen da aka kawo wa Yayarta?"
"E ta gani, amma hakan bai saka ta saduda ba"
Kallon Sadiya tayi, sai kuma ta juya ta fice. Umma Habiba ta kalli Sadiya ta ce "Ki dai zauna kiyi tunani"
Ita dai Sadiya bata ce komai ba har Umma ta fita.
Ranar a ɗaki ta yini har zuwa bayan magriba lokacin Saddiqa da Surayya suka dawo gidan. "Ya naga kin yi lamo kamar mara lafiya"
Tashi ta yi ta zauna lokacin kuma Surayya ta fara ƙoƙarin cire kaya ita kuma Saddiqa ta zauna gefenta. "Mene ya faru?"
"Akan lefen ki da aka kawo ne"
"Bai masu ba?"
Kai Sadiya ta girgiza sannan ta ce "Kawo lefen ki da aka yi ne ya jawo aka cigaba da rura wutar tsanar Yazid a gidan nan"
"Wai mene aibun Yazid?"
"Babu kawai dan dai ba shi ne zaɓin Mameey ba"
"Ki kwantar da hankalinki Sadiya, tunda dai kina son shi shima yana sonki insha Allah komai zai wuce da zarar an gama hidimar biki"
"Ni ma fa har ga Allah bana goyon bayan ta auri Yazid" Cewar Surayya
Kallon Surayya ta yi kafin ta yi magana Saddiqa ta ce "Sannu mara kunya, waye ya saka bakin ki a maganar mu?"
"Allah ya baku haƙuri" Ta faɗa tana shiga toilet, ajiyar Zuciya Sadiya ta sauke tare da dafe fuska.
Mameey kuwa sai da ta bambanta auren Sadiya da Saddiqa, domin sai da ta ƙara sati ɗaya a bikin Saddiqa saboda kawai Yazid ya ce baya da kuɗin da zai yi kamu da dinner sai dai walima, ƙarshe ma sai kiranshi tayi ta ce ba ta son walimar za a ɗaura aure a yi yinin biki a kai amarya. Hakan kuwa aka yi dan da ƙyar ma ta yarda ta bayar da kayan ɗakin aka kai Sadiya dasu, dan cewa tayi ba zata bari akai kayan ɗaki masu tsada gidan da bai dace ba, kuma ahalin da ba su san darajar kaya masu tsada ba. A haka dai 'yan uwa suka saka baki, haka Saddiqa ma tayi kuka ta kuma ce muddin ba a kaiwa Sadiya kayan ta ba, to itama bata so.
Sati ɗaya da kai Sadiya aka fara bikin Saddiqa wanda biki ne kamar shi ne auren fari a gida, party ma kala biyar ne, tun daga ranar talata har zuwa asabar, taso zuwa amma Yazid ya hana ya ce ta bari ranar yinin biki sai ta je, abinda ya guda kuwa sai da hakan ta faru domin ranar yinin da taje kallon wulaƙanci suka yi mata suna ganin sun raina leshin dake jikinta, duk da a cikin leshin shi ne mai tsada a cikin kayan lefenta. A gidan Saddiqa ce kawai ke goyon bayan auren Sadiya da Yazid.
**************
Ruwan da ta ji yana zuba a jikinta ya saka ta yi firgigit ta buɗe ido tare da miƙewa zaune, saboda yadda sanyin ruwan ya ratsata. Najma da Ihsan suka farka, tuni Ihsan ta fara kuka dan ita ce ƙarama, sanyin ruwa ya farkar da ita daga baccin da ba su daɗe da farawa ba. Cikin hanzari suka sauka daga katifar, Sadiya ta ɗauke katifar ta jingine a gefen da ruwa baya zuba, sannan ta ɗauki bargonsu ta zura a leda ta ƙulle ta fita da sauri, a lokacin ta ga Yazid ya hasko fitila ya fito daga na shi ɗakin, wanda ta tabbatar shima ruwan ne ya farkar da shi dan gidan babu inda baya zuba, shiyasa duk albarkar ruwan sama amma su gudun shi suke.
Ledar ta kai zaure dan nan ne mafakar su idan ana ruwan dare, ta ƙarasa can gefen da babu feshin ruwan kasancewar zauren yana da ɗan girma, dan murhunanta ma da take girki anan suke tun lokacin da damuna ta shigo. Yazid ya ƙaraso zauren da Ihsan a kafaɗarsa hannunsa na riƙe da Najma. "Kin ga bari na ɗauko kayan namu kar su jiƙe sai a canja masu saboda kar danshi ya masu illa." Kai kawai ta gyaɗa tana janyo yaran, ya dawo da sauri da bakkon kayansu, ta sumu ta shimfiɗa tabarma tana ganin yaran suna ta rawar ɗari, ta saka zannuwa akai sannan ta kwantar dasu ta ruɓanya bargo ta yafa masu har kansu, sai lokacin ta fara jin hawaye kwance saman kuncinta, ta dafa tsohon cikinta da ta ji yana motsawa. "Sadiya ki tashi ki canja kaya" Kallon shi ta yi sai kuma ta fashe da kuka a fili, da sauri ya ƙarasa gabanta ya jata jikinsa duk da a jiƙe take "Kiyi haƙuri na san bana sauke haƙƙin da Allah ya ɗora min naku."
"Ka daina faɗar haka abban Najma" Ta furta tana ɗagowa. "Na san kana iya ƙoƙarinka, kuma Allah yana sane damu."
Tana gama faɗa ta miƙe ta buɗe bakko ta ɗauki kaya ta canja sannan ta kalleshi. "Ka samu ka kwanta, ka ga da wuri kake fita aiki."
"Ba zan iya kwanciya na yi bacci ba, ko da na kwanta ma na san ba zan iya komawa bacci ba." Ji tayi wasu hawayen sun ƙara cika kwarmin idanunta, ta koma kusa da shi ta zauna, ya janyota ya ɗora kanta bisa cinyarsa tare da faɗin ki samu kiyi bacci. Idanuwanta kawai ta rufe amma sam bata samu tayi bacci ba, sai ma rawar ɗari da ta fara kasancewar tana da pneumonia, da sauri ya cire rigar sanyin dake jikinsa ya yafa mata, ta haɗe ƙafafunta sosai, ranar ba ƙaramin ruwa aka tafka ba, sai gab da asuba ya tsagaita.
Da fitila yake haskawa ya ga tsakar gidan nasu ya cika maƙil da ruwa, banɗaki kuwa ya rufta, dama na ƙasa ne. "Ya Allah mun gode maka" Ya furta sannan ya ɗauki buta ya yi alwallah, yana idarwa ya ga Sadiya ta shigo.
"Abban Najma banɗakin mu ya rufta"
"Wallahi nima yanzu na gani"
Ajiyar zuciya kawai ta sauke babu wanda ya ƙara magana a cikinsu.
Koda ta yi sallah miƙewa ta yi ta shiga ɗakin, ta fara ta ɗakin kwanansu, nan ta fara yiwa aiki, tana ta tsane ruwa bayan ta gama fito da kayan ɗakin, har gari ya fara haske sannan ta gama ta koma ɗayan ɗakin da kujerunta ke ciki nan ma ta hau aiki sai dai har ta gama Yazid bai dawo ba lokacin kuma yara sun tashi daga bacci. " 'Yan matana an tashi?" Ta faɗa lokacin da Ihsan ta rungumeta itama Najma ta ƙaraso gabanta "Mommy sanyi muke ji"
"Akwai sanyi fa, amma karku damu yanzu da Daddy yazo mun yi breakfast sai muje gidan Mameey kuna son zuwa?" Kai suka gyaɗa suna dariya, inda ya ɗan bushe a taɓen gidan nan ta shimfiɗa masu tabarma, sannan taje zaure ta ɗebe shimfiɗar ta dawo da ita ciki, ta ajiye sannan ta sake komawa ta hura wuta a murhu ta ɗora ruwan zafi yaran ta ce su dawo zauren su sha ɗumin wuta.
"Najma karku yi wasan wuta kin ji ko?"
"To Mommy"
"Yawwa Najmata bari na ƙarasa aiki kafin Daddy ya dawo ya kawo abin kari ko?"
"Mommy yau ba zan je school ba?"
"E yau mun makara sai dai gobe"
Bata ce komai ba, ita kuma Sadiya ta shiga ciki.
Ƙarfe takwas da kusan rabi taji yaran suna "Oyoyo Daddy" Ta kai dubanta ga zauren sannan ta ajiye tsintsiyar hannunta ta ƙarasa.
"Sannu da zuwa Abban Najma" Ta faɗa tana karɓar ledar hannunsa.
"Kamar na sani na sayo bread da lipton da sugar, sai a haɗa saboda yaran, akwai pasta da ɗan kayan miya sai ayi da rana ko?"
Masha Allah, kace yau mun dace"
"Ai yau ina fita naga ana sauke kaya, shi ne nima na shiga cikinsu, to bayan mun gama sai aka bamu dubu biyu kawai na yi cefane da ita"
"Allah sarki Yazid, Allah ya maka buɗi na alkhairi"
"Amin mar'atussaliha"
Murmushi tayi sannan ta ce "Na ga kayi ƙura, bari na sauke ruwan idan na ɗebi na tea sauran sai kayi wanka"
"Kin manta banɗaki ya rufta? Yanzu fa dole sai an gyara" Ya furta yana shigewa ciki da damuwa. Kallon shi tayi itama jikinta gabaɗaya ya yi sanyi. Har za ta bishi sai kuma ta kalli yaran ta ga duk suna tare da yunwa, tunda jiya ba wani ƙoshin kirki suka yi ba. Da sauri ta koma ciki bata ga Yazid ba, ta tabbatar ya shiga ɗaki ne, ta ɗauki flask da cups ta koma zauren, rufe gidan ta yi ta saka sakata sannan ta haɗawa yaran shayi ta gutsura masu bread ɗin, akan tabarmar ta saka suka zauna ta surka masu sannan ta miƙe ta shiga gidan. Ɗakinta ta shiga ta ganshi zaune ya haɗa kai da gwiwa "Habibi!"
Ɗago kai ya yi yana kallonta, ta ƙarasa gabansa tare da miƙa masa hannu, hannun ya riƙe sannan a hankali ya miƙe tsaye, rungumarshi kawai ya ji tayi dan bai yi expecting hakan ba "Haba Babyna idan kana damuwa ni ina kake so na kai tawa rayuwar, ka san fa kaine farin cikina" Ɗago ta ya yi yana kallonta, ta ɗan sakar masa murmushi "Jiya kuka kika yi sosai, yau kuma kina murmushi, Sadiya na san ni ɗin ba miji nagari bane a garek...." Da sauri ta saka hannu ta rufe masa baki. "Dan Allah ka daina faɗar haka, kar ka saka ƙwarin gwiwata ya sace, Yazid kai miji nagari ne, wanda ko wace mace ke fatan samu."
"Sadiya! Ki duba daga gidan dana ɗauko ki, amma kalli gidan da muke rayuwa a yanzu, ba kece macen daya dace na aura ba, saboda cimar da nake baki a gidanku a guba suke kallonta"
"Yazid meyasa kake faɗar haka? Lokacin da muka yi aure babu abinda na nema na rasa a gidanka, a yanzu ma da karayar arziƙi ta same ka ba zan zama mai butulci a gareka ba."
"Ko lokacin dana aure ki ai ni mai ƙaramin ƙarfi ne, abinda kike so kin samu ne a lokacin muna daga ni sai ke, amma tunda aka haifi Najma buƙatu suka ƙaru sai abubuwa suka taɓarɓare a ciki kuwa har da rasa aiki na"
"Kar ka yi yaƙi da ƙaddara, ka bi komai a sannu Allah zai warware mana, kuma yara da kake magana rahama ne a gare mu, wasu da kuɗinsu neman haihuwa suke amma ba su samu ba, mu kuma ka ga ko a haka alhamdulillah mun samu albarkar aure, ga Najma ga Ihsan kuma ga unborn a cikina."
"Hannu ya saka ya shafa cikin nata, sannan ya ce "Kullum na kalli cikin nan sai na godewa Allah da ya bani ke a matsayin mata, yanzu fa tun cikin nan yana ƙarami kika bani shawara na sayi wannan ƙaramar tunkiyar na kai gurin Iya Mama, gashi yanzu da Iya Mama ta haɗata cikin dabbobinta har ta haifi 'yan biyu."
"Ai dama shiyasa na ce ka saya tunda har aka ce tana da ciki sai ka ga an dace."
"Wallahi kuwa gashi dai an dace ɗin, Iya Mama ta ce suma har sun fara tasawa."
"Ma sha Allah"
"Yanzu fa kuɗin rago ya kai dubu ɗari, kuma shima na dubu ɗarin ba wani bane"
"Wai dagaske?"
"Wallahi fa, ai ba ƙaramar dabara bace da muka sayi tunkiya kuma ta haifi mace da namiji, yanzu idan Allah ya sauke ki lafiya sai kawai na sayar da ita a sayi ragon suna, su kuma sauran sai a barsu har zuwa su girma mu gani"
"Hakane, to Allah ya inganta"
"Amin"
"Muje mu karya, ina so muje gida da yara sai mu samu mu yi wanka acan tunda banɗakin mu ya rufta, kuma ka ga kayan nan dole sai ɗakin ya bushe kafin na mayar"
"Nima zanje gidan Umma sai na yi wanka, dama ina so na miki magana, kin san dai tsohon ciki ne dake amma shi ne kika yi aikin nan, meyasa baki bari nazo na kama miki ba"
"To ba gashi har na gama ba"
"A'a Sadiya dan Allah ki riƙa hutawa"
"Hutu ai ba na mace mai yara bane"
"Ni dai na faɗa miki"
"To ka fito dai mu karya, kuma ka daina zama a danshi in ba so kake sanyi ya kama min kai ba"
Murmushi kawai ya yi, sannan ya ce "Kin san tsabar damuwa ban ma san nan na shigo ba"
"Ka rage damuwar nan dan Allah"
"Insha Allahu. Ki je ki karya ku kaɗai na sayawa"
"Ai ya mana yawa, dan Allah karka ƙi karyawa"
"To shi kenan muje"
"Yawwa Babyna"
Murmushi kawai ya yi, yana lumshe ido.
Suna shiga zauren ta kalli yaran ta ce "Najma bari na gama haɗawa Daddy breakfast sai na yi muku wanka ko?"
Kai Najma ta gyaɗa, ita kuma ta janyo cups ta haɗa masu, suna sha suna ɗan taɓa hira har suka gama. Yana ƙoƙarin fita ta ɗan dakatar da shi ya tsaya yana kallonta "Dama na ce kodai kujeruna za a sayar a gyara mana rufi?"
"A'a Sadiya wannan karon ba zan ɗauki shawarar ki ba, haka kika sayar da gado abu bai yi ba, sannan gadonki ma...." "Ya isa dan Allah Yazid, bana son ka riƙa faɗar haka, ni da kai duk ɗaya ne meyasa kake wannan maganar, duk wani abu dana mallaka ai naka ne"
"Na yarda amma kujerunki ba za a sayar ba, yanzu haka fitar da zan yi insha Allah akwai aikin da zanyi na samu kuɗi, na san Basiru zai min gyaran nan koda bashi ne insha Allah."
"Bana so ka yi ta wahalar da kanka"
"Abinda ya zama dole ne Sadiya" Ya saka hannu a aljihu ya fito da naira ɗari biyar ya miƙa mata, "Wannan fa?"
"Ku yi kuɗin napep zuwa gida."
"Kai fa? Kana da wasu a hannunka?"
"Kar ki damu, ke dai ki karɓa kawai"
"To mungode Allah ya ƙara maka buɗi Abban Najma"
"Amin Maman Najma"
Murmushi ta yi tana rufe fuska.
***** *****
Tun da Napep ya sauke su take jin gabanta yana faɗuwa ‘lahaula wala ƙuwata illa billah’ Shi ne abinda take nanatawa a ranta, mai napep ya bata canjin ɗari biyu ta juya ta shiga gidan. "Ya na ji gidan shiru" Ta faɗa lokacin da ta kutsa kai cikin parlourn.
"Wa nake gani kamar Aunty Sady?" Jin haka ya saka ta kai dubanta gare shi. "Kai! Yaro yaushe ka diro garin?"
"Ban daɗe ba Aunty ina ta son zuwa gidanki sai ga ki kinzo"
"Faɗi gaskiya dai, borin kunya kawai kake dan ka ganni anan"
Najma gaishe sa ta yi, ya janyota ita da Ihsan ɗin "Ga su duk sun yi wayo"
"Aikam dai kana ubansu amma basu sanka ba, rabonka da gidana an fi shekaru biyu ka gyara hali Faruq"
Kai ya sosa yana dariya.
Umar Faruq ɗa ne ga ƙanen mahaifinsu, kuma mahaifiyarsa 'yar asalin maiduguri ce babanshi ya aurota zuwa kano, sai dai tun Faruq na da shekaru 4 a duniya Allah ya yiwa mahaifinsa rasuwa, bayan mahaifiyarsa ta gama takaba ta koma can maiduguri da shi sai dai yana ɗan shekara 6 a duniya ta dawo da shi Kano wurin mahaifin su Sadiya anan ya girma yanzu haka shekarunsa 22 a duniya, Saddiqa ta ba shi shekaru 7 a haihuwa, Sadiya ta ba shi 4 yayinda suke sa'anni da Auta.
"Ina Mameey da Auta ne na ji gidan shiru?"
"Mameey tana ɗaki ta je ɗauko min saƙo zan kai wa Aunty Saddiqa, ita kuma Surayya tana school bata dawo ba"
"Nima ka san ina son zuwa gidan Saddiqa"
"To kizo muje tare"
"Gaskiya ba zamu tafi tare ba dan sai na gama hutawa a gida sannan zan je" Ta ƙarasa maganar tana miƙewa "Bari na je gurin Mameey"
"To sai kin dawo."
Tana tura ƙofar Mameey ta ɗago ta kalleta, "Wa nake gani a gidan nan kamar Sadiya."
"Mameey ni ce, ina kwana"
"Lafiya lau, mene ya kawo ki da safiya haka?"
"Yanzu 11 ta wuce fa"
"Ba time na tambaya ba, abinda ya kawo ki na tambaya."
Ji ta yi jikinta ya yi sanyi.
"Na zo ne kawai na yini anan."
"To ki koma gidan ki" Furucin ya daketa, ta kalli Mameey dan ta tabbatar da maganar da take faɗa. "Ki koma gidanki na ce kafin ranki ya ɓaci"
"Mameey naz..." "Ki rufa min baki Sadiya, ba zan taɓa lamuntar zuwanki gidan nan ba muddin ba da takardar saki na ganki ba" Zaro idanuwa ta yi tana kallon mahaifiyarta.
"Dube ki da Allah, shekaru ashirin da biyar ne ko shidda kike dasu amma 'ya'ya biyu har da cikin na uku, kin zama kamar tsohuwa, wani ya kalle ki zai yi tunanin kin haura arba'in a duniya"
Ɗan lumshe ido ta yi tana jin raɗaɗin furucin, lokacin kuma ta tsinkayi muryar Mameey tana faɗin "Sai a rantse kin girmi Saddiqa, ga ta nan har yanzu kamar budurwa, amma ke kin liƙewa talaka kuma kince kina ta haihuwa saboda rashin sanin ciwon kai"
Kallon Mameey ta yi lokacin wasu siraran hawaye suka fito daga fuskarta zuwa kuncinta.
"Kiyi haƙuri Mameey"
"Haƙuri ɗaya zan yi kije ki karɓo takardar saki a gurin wancan matsayacin, ni kuma zan riƙe ki domin ni dolenki ce, amma muddin kina tare da Yazid to wallahi mun ta samun matsala dake, haba Sadiya so hauka ne? Kin sayar da gado kin bashi ya lalata kuɗin, sannan kika matsa min kan lallai sai na baki gadonki, na baki nan ma kika ba shi kuɗin suka nutse"
"Amma Mameey kowa ya san duk manoman da sukayi noman shinkafa a shekarar da ta wuce babu wanda bai yi asararta ba, ruwa ne ya shanyeta, Mameey na faɗa miki ya fi a ƙirga."
"Dalla rufa min baki, me kika ce min lokacin da za ki karɓa? Kin ce min sana'a za kiyi ashe ƙarya kike mijinki ne ya zugo ki kika karɓa kika danƙa masa"
"Wallahi Mameey ba shi ya ce na karɓa ba, ra'ayi na ne kawai"
"Wallahi idan na sake faɗa kika faɗa sai na tsinka miki mari."
Kan ta kawai ta sauke ƙasa hawaye na ta sintiri
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 15