Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ya subuto ma ta. A sannan ne ta gane cewa lallai ta kamu da son Shaddadu ne, kuma a sannan ne ta tuna cewa ai bai gaya mata sunansa ba. Nan take Yaldisa ta ruga da gudu izuwa kofar gida. Tana fita ta dubi gabas da yamma, kudu da arewa amma ba tá ga alamar Shaddadu ba, ya 6ace ɓat! Tamkar daukewar ruwan sama, kawai sai ta yi ajiyar zuciya ta juyo ta koma cikin gidants zuciyarta na cike da damuwa da takaici. (KE YALDISA. AI WUTSIYAR RAKUMI TA YI NESA DA KASA) **** Lokacin da Shaddadu ya fito daga cikin gidan karuwa Yaldisa a cikin siffar wannan tsohuwa yana dogara sanda sai yai tsafi wani dan koko ya bayyana a hannunsa. Nan take ya kunna kai izuwa cikin gari yana bara tamkar tsohuwa ce mai neman abin da za ta ci. Sai da ya shafe sa'a 202 TASKARNOVELS.COM.NG guda yana yawon bara bai hadu da wanda ya ba shi koda ruwan sha ba bare abinci ko durhami guda. Al'amarın da ya ba shi mamaki ke nan, duk da cewar shi rayuwarsa a can Birnin Kufa bai taba yin bara ba asali ma a gidan Sarauta ya taso cikin gata amma ai ya san cewa mutanen gari suna taimakon Almajirai. Abin da bai sani ba shi ne, game da al'adar mutanen wannan gari ba a yin bara a ko ina sai dai Almajiri ya je ya sami wuri a bakin hanya ya zauna ya yi bararsa in yaso masu wucewa mai niya ya ba shi. Shaddadu na cikin yawon barar tasa ne ya hango Almajirai a gefen hanya kimanin su goma maza da mata a zaune sun yi layi mutane masu wucewa suna ta ba su sadaka. Cikin murna Shaddadu ya karasa inda Almajiran suke a cikin siffarsa ta tsohuwa tukuf gami da dogara sanda da kyar. Yana isa gare su sai ya tsaya ya fara kokarin zama kusa da wani tsoho wanda ya fi shi tsufa nesa ba kusa ba. Amma bisa mamaki sai ya ga tsohon ya mike da sauri cikin kuzarinsa tamkar ba tsohon ba ya taimaka masa ya zaunar da shi kuma ya mika masa sandarsa ya rike. A sannan ne suka dubi juna cikin murmushi sai tsohon ya dubi tsohuwar ya 203 TASKARNOVELS.COM.NG ce, "Ya ke wannan almajira in ce ko ke bakuwa ce a garin nan? Na ga kina bara akan hanya alhalin ba haka dabi'ar g garin nan take ba?" Koda jin wannan tambaya sai Shaddadu ya ji bai amince da wannan tsoho ba don haka sai ya ɓoye masa gaskiyar al'amari ya ce, "A'a ni ba bakuwa ba ce a wannan gari amma dai daga kauye na zo nan. Wannan ne dai karon farko da na fara yin bara anan. Koda jin haka sai tsohon ya sake yin murmushi ya ce, "To ai a nan ba a yin bara a ko ina sai a gefen hanya don haka sai ki kula saboda gaba". Da jin haka sai tsohuwar ta maidawa tsohon martanin murmushi kuma ta yi masa godiya. A daidai wannan lokaci ne suka hango Sarauniya Zubaina ta tunkaro su bisa doki tare da Dakarunta su ma bisa dawakai kimanin su dari biyu. Da isowar Sarauniya Zubaina gaban Almajiran sai ta sauko daga kan dokinta ta shiga rabawa Almajiran sadakar dirhami guda-guda. Duk wanda ta zo kansa sai ta kura masa idanu ta yi wani surkullenta na tsafi domin ta gano akwai bakon saurayin nan a cikinsu wanda ya karya dokarta ya shigo gari ba izini ya ɓalla kofar garin kuma ya yi wa Dakaru duka. Haka dai Sarauniya Zubaina ta ci gaba da 204 TASKARNOVELS.COM.NG bai wa almajiran sadaka har ta zo kan wannan tsoho wanda ya taimaki tsohuwa. Da zuwanta kan tsohon sai ta tsaya cak! Ta dade tana kallonsa kuma tana surkullenta a kansa har sai da gumi ya tsattsafo mata amma ba ta gano komai ba. A sannan ne ta yi ajiyar numfashi ta dubi tsohon ta ce, "Ya kai wannan almajiri shin ba ka ga wani bakon saurayi ba a cikin garin nan wanda ya shigo mini gari ba izini kuma ya balla mini kofa?" Dattijon ya gyada kai ya ce, "Ban gan shi ba amma dai na ji ana zanċensa a cikin nan kuma da zarar na gan shi zan gaggauta zuwa fada na sanar". Koda jin haka sai Sarauniya ta yi murmushi sannan ta matsa gaba wajen tsohuwar ta ba ta sadaka tana mai kura mata idanu gami da yin Wannan surkulle. Ai kuwa sai da ta ɓata lokaci fiye da sa'adda ta tsaya a gaban wannan tsoho har ya zamana cewa ta jike sharkaf da gumi. Sarauniya Zubaina ta sa hannu ta share guminta tana mai ajiyar zuciya sannan ta dubi tsohuwar ta ce. "Ya ke wannan almajirila yaushe ki ka zo garin nan? Tabbas ban taba ganinki a cikin wannan birnin ba. Koda jin wannan tambaya sai tsohon almajirin ya tari numfashin tsohuwar almajirar 205 TASKARNOVELS.COM.NG ya ce, "Ai wannan Almajirar bakuwa ce daga kauyen LAIRUF, ba ta ma saba yin bara a nan ba. Dazun nan muka hango ta tana yin bara a cikin gari sai da ta zo nan muka yi mata bayanin al'adar garin nan". Sa'adda Sarauniya Zubaina ta ji wannan batu sai ta sake yin ajiyar zuciya sannan ta mike ta dubi Almajiran da ke zaune a wajen gaba dayansu ta ce "Duk sa'adda dayanku ya ga wani bakon Jarumi saurayi ya hanzarta zuwa fada ya sanar da ni, zan ba shi lada na adadin dukiyar da har ya mutu ba zai iya cinyewa ba". Koda jin wannan batu sai gabadayan Almajiran suka kama shewa suna yi wa kansu fatan su dace da samun wannan lada. Nan dai Sarauniya Zubaina ta je ta kama dokinta ta hau ta wuce gaba Dakarunta na take mata baya. A lokacin ne wata rundunar daban ta Dakarun Sarauniya Zubaina suka shigo cikin garin suka barbazu a ko ina lungu-lungu, sakosako suna neman bakon Jarumi. Koda wannan tsohon Almajirin ya hango abin da ke faruwa sai ya dubi tsohuwar Almajirar ya ce, "Kai al'amarin nan da ban mamaki yake. To wai shin shi wannan bakon Jarumi wane irin hatsabibi ne haka? Tun jiya ake nemansa a garin nan amma 206 TASKARNOVELS.COM.NG an rasa inda yake. Anya kuwa shi ma bai kasance hatsabibin matsafi ba?" Koda jin haka sai tsohuwar ta ce, "Ai kai ma ka san ruwa ba ya tsami banza. Duk yadda aka yi wannan bakon Jarumi shi ma ya taka babban matsayi a tsafi da jarumtaka, in ba don haka ba da tuni Sarauniyar garin nan ta kamo shi tunda na ji an ce ita ma shahararriyar matsafiya ce kuma Jaruma". Tsohon Almajirin ya gyada kai sannan ya ce. "Tabbas zancenki dutse ne. Yanzu dai ga shi mun sami babbar dama bisa tayin da Sarauniya ta yi mana. Ya ke wannan Almajira tunda dai na ga kina da kokarin yawo a garin nan sai ki zuba ido da kyau da zarar kin ga bakon Jarumi ki hanzarta zuwa nan inda muke zama ki zo ki sanar dani tunda kin ga ni na fiki kwarin jiki sai na garzaya fada na sanar da sarauniya. Na yarda ki sam mini ladan da Sarauniya za ta bayar ba sai mun yi raba dai-dai ba. Ni burina kawai shi ne, a kama wannan Saurayi saboda ya ci mutuncin garin nan kuma ya keta alkadarin Sarauniya. Sa'ad da tsohuwar Almajirar ta ji wannan batu sai ta numfasa ta ce. "Babu komai lallai zan yi kamar yadda ka bukala. Amma ina da tambaya a gare ka. Wai shin me ya sa dazu 207 TASKARNOVELS.COM.NG ka kare ni a wajen Sarauniya har ka fadi sunan wani kauye ka ce daga can na zo alhalin ni ban ma taba jin sunan kauyen ba?" Koda jin wannan tambaya sai tsohon ya numfasa ya ce. "Ai abokin barawo, barawo ne. Inda Sarauniya ta kama ki da wani laifi to da gabadayanmu laifinki ya shafe mu mu duka. kin ga ke nan, dukkaninmu 'yan uwan juna né daga yau mun zama abokai". Koda gama fadin hakan sai tsohon ya bushe da dariya ya mikawa tsohuwar hannu da nufin su gaisa, amma sai tsohuwar ta noke ta ki ta ba shi nata hannun. Kawai sai ta mike tsaye da kyar tana dogara sandarta ta dube shi ta ce, "Ka yi hakuri ba na taba jikin namiji, sai mun sake saduwa". Koda gama fadin hakan sai tsohuwar ta juya ta nausa cikin gari rike da dan kokonta tana mai ci gaba da bara. Shi kuwa tsohon sai ya bi ta da kallo kawai yana mamakin wannan kalma da ta gaya masa. Bai daina kallon tsohuwar ba har sai da ta bace masa da gani sannan shi ma ya mike tsaye ya kama hanya ya nufi can bayan gari. Tohon ya ci gaba da tafiya har sai da ya shiga daji ya iso gaban wata bishiya sannan ya rikiďe zama Jaruma Ziya'ul Hak. A daidai wannan 208 TASKARNOVELS.COM.NG lokaci Aljani Maruful Dauwaz ya fito daga cikin wata duhuwa da sauri ya dubi ziya'ul Hak cikin damuwa ya ce, Mene ne labari? Shin ba ki ga abokin gabar tamu ba ne?" Ziya'ul Hak ta yi ajiyar zuciya cikin alamun damuwa da takaici ta ce, "Ai na zagaya garin nan kaf ina neman Shaddadu amma ban gan shi ba. Kai a takaice ma dai ita kanta Sarauniyar garin nan nemansa take ruwa a jallo saboda ya aikata babban laifi ya shigo gari babu izini ya ɓalla kofar garin kuma ya yi wa Dakarunta dukan tsiya". Nan dai Ziya'ul Hak ta ci gaba da bai wa Aljani Maruful Dauwaz labarin duk abin da ya faru tun daga lokacin da ta ɓatar da kamanninta ta zama tsoho ta shiga cikin garin tana neman Shaddadu kawo izuwa sa'adda ta je ta zauna a gefen hanya cikin almajirai har wannan bakuwar almajirar ta zo, da yadda suka rabu da almajirar a karshe bayan tafiyar Sarauniya Zubaina." Koda jin wannan labari sai Aljani Maruful Dauwaz ya dafe kai cikin tsananin bakin ciki kamar zai yi kuka sannan ya dubi Ziya'ul Hak ya ce. "Kaico! Kin yi asarar babbar dama wacce yakamata ki yi amfani da ita wajen kashe abokin gabarki. Ai wannan tsohuwar almajirar da kika 209 TASKARNOVELS.COM.NG taimaka ba tsohuwa ba ne face Jarumi Shaddadu. Koda jin haka sai Ziya'ul Hak ta zazzaro idanu ta dubi Maruful Dauwaz cikin mamaki ta ce, "Yaya aka yi ka gane cewar tsohuwar Shaddadu ne?" Maruful Dauwaz yai ajiyar zuciya sannan ya ce, "Ai bisa binciken da muka yi ni da iyayenki kafin mu baro su mun gano cewa Sharlis ta cire wa Shaddadu sha'awa irin ta 'ya mace tun yana yaro karami, don haka ba zai taba yarda ya taɓa jikin 'ya máce ba. Duk da cewar kina cikin siffar namiji, kuma tsoho, ba zai gaisa da ke ba domin shi bai yarda da kowa ba a cikin garin. Yana daga cikin makarin sihirinsa idan har ya taba jikin 'ya mace da hannunsa. Wannan sandar da kika gani a hannun tsohuwar tana dogarawa ba sanda ba ce Mashin Galilul Haras ne wanda mahaifiyarsa ta ba shi. In da kin shammace shi kin soke shi da makami a wannan lokaci da take zai fadi ya mitu saboda in dai ya batar da kamanninsa na zahiri za ki iya yin tasiri a kansa. Koda Aljani Maruful Dauwaz ya zo nan a zancensa sai Jaruma Ziya'ul Hak ta yunkura da sauri a fusace da nufin ta ruga izuwa cikin gari, amma sai Aljani Maruful Dauwaz yai caraf ya ruko ta ya ce, 210 TASKARNOVELS.COM.NG "Ina kuma za ki je?" Ziya'ul Hak ta ce, "Neman Shaddadun zan tafi tunda na gane irin yanayin da yake". Koda jin haka sai Maruful Dauwaz ya bushe da dariya sannan ya ce, "Yaro man Kaza. Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce, "Wanda ya riga ka kwana dole ne ya riga ka tashi". Ina so ki sani cewa Shaddadu ya ri ga ki zuwa wannan duniya tunda ya girme ki da kusan shekaru hudu. Don haka dole ne ya fi ki wayo. Ina mai tabbatar miki da cewa yanzu dole ne ya sauya siffarsa don haka abu ne mawuyací ko kun hadu ki gane shi. Kada ki manta cewa farautar juna kuke yi kamar yadda kike nemansa haka shi ma yake nemanki ruwa a jallo. Ina mai dada yi miki tuni da cewar kada ki yarda ki Yaki Shaddadu muddin yana tare da wannan Mashi nasa na Galilul Haras. Idan kuwa kika yi gangancin aikata hakan ta farat daya zai sami nasarar hallaka ki." Lokacin da Aljani Maruful Dauwaz yazo nan a zancensa sai jikin Ziya'ul Hak ya yı sanyi ta yı shiru tana tunani, daga can kuma sai ta dago kai ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, "Ya kai babban masoyi yanzu mene ne abin yı? Ya za a yi na gane Shaddadu da zarar na hadu da shi?" Maruful Dauwaz ya 211 TASKARNOVELS.COM.NG numfasa ya ce, "Hanya daya ce, sai dai mu shiga cikin garin tare ni da ke, domin ni duk irin yanayin da zan gan shi sai na shaida shi, to amma kuma ni ma dole ne na juye izuwa kamannin Bil'adama. Koda jin wannan batu sai farin ciki ya lullube Ziya'ul Hak ta ce, "Ai shi ke nan ta kwana gidan sauki, sai ka zo mu koma cikin garin domin mu gaggauta gabatar da abin da ya kawo mu. Burina shi ne m, mu kashe Shaddadu kuma mu raba shi da Mashin Galilul Haras sannan mu tafi da iyayena can Birnin Kufa mu kashe mahaifiyar Shaddadu domin na kwatowa mahaifina Sarautarsa". Koda jin wannan batu sai Aljani Maruful Dauwaz ya shiga yi wa Ziya'ul Hak kirari yana mal cewa, "Haka ake son 'ya ta gaji ubanta wajen ra'ayi da taurin zuciya gami da jarumtaka". Ba tare da ɓata lokaci ba Ziya'ul Hak ta yi girgiza ta zama saurayi wanda bai fi shekara ashirin da biyu ba a cikin shigar mafarauta. Shi kuma Aljani Maruful Dauwaz sai ya yi girgiza, take shi ma ya rikide ya zama wani kyakkyawan Kare. Nan take saurayin ya ruga da gudu izuwa cikin gari, Karen ya rufa masa baya suna tsala zababben gudu tamkar za su tashi Sama. * Al'amarin Jarumi 212 TASKARNOVELS.COM.NG Shaddadu kuwa, lokacin da ya baro wajen Almajirai masu bara a gefen hanya ya zamana cewa ya yi nisa da su har ya shiga wani bangare daban inda babu mutane, sai ya rikida ya sauya siffa ya zama tsaleliyar budurwa cikin shigar Yaki, wannan sanda tasa kuwa sai ta rikide ta zama garkuwa kuma ga Takobi a rataye à kafadarsa. Budurwar na sanye da Hular karfe idanunta kadai ake gani. Tsawon budurwar da kaurin jikinta in daya ne sak da na Sarauniya Zubaira, kai hatta kayan Yakin irin nata ne. Bayan Shaddadu ya gama rikidewa izuwa cikin wannan siffa sai ya dauko madubin tsafinsa ya shafe shi da hannun hagu, ya shiga bincike. Nan take ya gano cewa ai tabbas Jaruma Ziya'ul Hak na nan a cikin wannan gari kuma ita ma tana farautarsa kamar yadda yake farautarta ruwa a jallo. Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan kuma ya dugunzuma hankalinsa domin ya fuskanci cewa shi fa yanzu ya shiga babban tarko tunda Sarauniya Zubaina na nemansa kuma Ziya'ul Hak na nemansa kuma kowacce a cikinsu so take ta hallakashi. Shaddadu ya ci gaba da bincike a cikin madubin tsafin nasa. Koda yai nisa a cikin binciken sai ya 213 TASKARNOVELS.COM.NG gano cewa ashe wannan tsoho da ya hadu da shi a wajen bara ba tsoho ba ne Jaruma Ziya'ul Hak ce. Al'amarin da yai matukar fusata shi ke nan ya ci gaba da bincike don ya gano a inda wannan tsoho yake a sannan amma sai madubin tsafin nasa ya kasa nuna masa komai. Shaddadu ya ci gaba da nacin binciken amma abu ya gagara. Bisa dole ya hakura ya mayar da madubin tsafin nasa cikin aljihu sannan ya kunna kai izuwa cikin garin. Duk inda ya gifta sai ka ga mutane na zubewa kasa suna gaishe shi domin gani ake Sarauniya Zubaina ce. Haka dai ya ci gaba da yawo kwararo- kwararo, lungu-lungu, duk inda ya hadu da Dakarunsa masu yawon farautar bakon Jarumi sai su ma su zube kasa su gaishe shi. Shaddadu ya ci gaba da zagayawa duk inda ya je ga Almajirai sai ya zuba musu idanu ko zai ga wannan tsoho wanda suka hadu a wajen bara amma bai gan shi ba *** Fada wacce ta karatu ainun da kayan alatu domin komai na cikinta an yi shi ne da zallar zinare da kuma lu'u-lu'u. Sarauniya Zubaina na zaune akan karagar mulkinta fuskarta a murtuke, kai da gani ka san cewa ranta a bace yake. Kawai sai ta mike tsaye ta 214 TASKARNOVELS.COM.NG kama kai kawo cikin fishi da kunan rai. Gaba dayan fadawanta da Bokayenta na zaune sun sunkuyar da kasu kas cikin alamun tsoro don kada laifin wani ya shafe su. Kawai sai ta dube su gaba dayansu ta ce, "Amma dai taron nan naku duk ya zama na banza. Yanzu ace mutum daya ya shigo garin nan ya zame mana matsala. Tun jiya ake neman wannan bakon Jarumi amma an rasa a inda yake alhalin kun yi bincike kun gano cewar lallai yana nan a cikin garin nan. To ku sani cewa idan har ba ku kamo wannan Jarumi ba a yau gaba dayanku sai na sauke ku daga kan mukaminku." Koda jin wannan batu sai hankalin gaba dayan 'yan majalisar ya dugunzuma suka kama rokon Sarauniya akan ta yi musu sassauci. Har Sarauniya ta dube su za ta daka musu tsawa sai kawai ta hango wani bakon saurayi a cikin shigar mafarauta tare da wani Kare biye da shi sun shigo fadar kuma sun tunkaro inda take kai tsaye. Har Dakaru sun yunkura za su tare saurayin sai Sarauniya Zubaina ta yi musu nuni da su kyale shi. Ba tare da fargabar komai ba kuwa wannan saurayi ya ci gaba da durfafar Sarauniya sai da zo daf da ita sannan ya zube kasa ya kwashi gaisuwa 215 TASKARNOVELS.COM.NG sannan ya dago kai ya dube ta ya ce, "Ya Shugabata ni mutumin kauyen JALRIS ne, kuma yanzun nan na shigo garin nan. Na fito daga daji domin yin farauta sai na sami labarin cewar wani bakon Jarumi ya shigo kuma ya karya dokokinki amma an kasa gane shi da gano inda yake. To ni ya Shugabata ina mai tabbatar miki da cewa a duk irin yanayin da wannan Jarumi zai shiga in dai zan yi arba da shi sai na gane shi kuma zan iya jagorar tafiya farautarsa". Koda jin wannan batu sai Sarauniya Zubaina ta kamu da tsananin farin ciki ta dubi Mafaraucin ta ce, "Ai kuwa idan har ka taimaka aka kamo wannan tsageran Jarumi sai na ba ka lada mai tsoka irin wanda ba a taɓa bai wa wani ba a masarautata. Yanzu Dakaru nawa kake bukata wadanda zan ba ka su yi maka rakiya izuwa farautar wannan Jarumi?" Mafaraucin ya ce. "Ai ba na bukatar Dakaru da yawa ko mutum arba'in kika ba ni sun isa domin na sanar da su dokokin farautar Jarumin su kiyaye, amma idan suna da yawa ba za a sami nutsuwa ba" Nan take Sarauniya Zubaina ta sa aka waro Dakaru mutum arba'in wadanda suka kasance zakwakuran Jarumai ta bai wa wannan mafarauci sannan ta dube shi ta 216 TASKARNOVELS.COM.NG ce. Nan da yaushe zan jira dawowarku tare da wannan bakon Jarumi?" Mafaraucin ya ce, lallai kafin faduwar rana za mu zo miki da wannan mai laifi. Zubaina ta yi murmushin farinciki sannan ta sallame su gabadaya suka fice daga fadar. Nan fa labari ya bazu ko ina a cikin garin cewar an tafi farautar bakon Jarumi kuma za a zo da shi fada kafin faduwar rana. Bisa wannan dalili ne jama'ar gari suka yi ta tuttuɗowa izuwa fadar saboda kowa yana son ya ga wannan takadarin Jarumi wanda ya zo ya gagari Sarauniya da Dakarunta. Hakika masu iya magana sun yi gaskiya da suka ce "Kifi na ganinka mai jar Koma". Ashe lokacin da ake ta yada wannan labari a cikin gari cewar wani bakon mafarauci ya je fada kuma ya tabbatarwa da Sarauniya Zubaina cewar zai kamo mata bakon Jarumi kafin faduwar rana har ma ta ba shi Dakaru sun bazama nemansa Shaddadu ya ji a daidai lokacin da ya zo zai gifta wani layi, wadansu matan aure ne guda biyu a tsaye suna hirar. Koda jin wannan batu sai jikin Shaddadu ya ba shi cewar lallai Ziya'ul Hak ce ta rikide izuwa wannan bakon mafarauci domin in ba ita ba babu wanda zai iya cewa zai iya yin 217 TASKARNOVELS.COM.NG farautarsa. To amma idan har za ta iya farautar tasa me ya sa wancan karon ba ta shaida shi ba a lokacin da suka yi ɓad-da-kama duk su biyun suka yi siffar Almajirai? Shaddadu ya numfasa ya ce, "Amma kuma ai idan ka ji Makaho ya ce a yi wasan jifa, to tabbas ya taka Hoge, don haka lallai akwai abin da ta taka." Wata zuciyar kuma sai ta ce da shi, "To wai shin me kake tsoro ne alhalin mahaifiyarka ta tabbatar maka da cewa in dai kana tare da Mashin Galilul Haras babu wani mahaluki da ya isa ya sami nasara akanka walau mutum ko aljan. Ai wannan wata babbar dama ce ka samu da za ka yi arba da Ziya'ul Hak tunda dole da ita za a fito wannan farauta. Kawai ka tsaya a yi fito-na-fito domin a yi ta-ta- kare. Koda gama aiyana hakan sai Shaddadu ya rikide ya zama dan karamin kwaron nan da ake kira Malam Buda mana littafi ya tashi sama ya tafi izuwa kan wata bishiya da ke gefen wata babbar hanya ya sauka ya zube kasa yana kallon kan hanyar. Ita dai wannan hanya babu wata babbar hanya sama da ita a duk fadin garin don haka Shaddadu ya tabbatar da cewa dole ne su Ziya'ul Hak su biyo ta wajen. *** Al'amarin bakon Mafarauci mai 218 TASKARNOVELS.COM.NG Kare kuwa, lokacin da ya baro fada tare da wadannan Dakaru mutum arba'in sai suka ruga da gudu izuwa cikin gari. Mafaraucin ne akan gaba da farko amma daga baya sai Dakarun suka ga Karensa ya wuce gaba yana musu jagora. Duk inda aka je sai Karen ya tsaya ya yi shinshine-shinshine a kasa da sama, kudu da arewa sanann a ci gaba da tafiya. Sai da suka shafe kusan sa'a hudu suna yawo kwararokwararo sannan suka iso wannan babbar hanya wacce ke dauke da wannan bishiyar wacce Shaddadu ya sauka akanta a siffar Kwaron Malam Buda mana littafi. Kalar jikin kwaron ta saje da kalar ganyen bishiyar saboda haka in dai ba kwaron ne ya yi motsi ba babu yadda za a yi mutum ko aljan ya gane akwai wani abu akan bishivat Tun daga nesa Jarumi Shaddadu ya karewa wannan mafarauci kallo ya gane cewa ba kowa bane face Ziya'ul Hak domin ya lura da layar da ke wuyansa wacce ta kasance baka ta sauya launi ta zama ja a daidai lokacin da yai arba da Ziya'u Hak. Da ma mahaifiyarsa Sharlis ta gaya masa cewa lallai in dai yai arba da Ziya'ul Hak sai layar da ke wuyansa ta sauya launi ta koma ja Duk da cewa Shaddadu na 219 TASKARNOVELS.COM.NG cikin siffar kwaro sai da jar layar ta nuna alama a jikin kwaron. Bayan Shaddadu ya gane Ziya'ul Hak sai kuma ya lura da wannan Kare da ke mata jagora ita da sauran Dakaru. Yana kallon Karen ya gane cewa ba dabba ba ce Aljani ne kuma tunda ya zo duniya bai taba ganin Aljani mai kwarjini irinsa ba. Nan take Shaddadu ya ji zuciyarsa ta buga da ƙarfi a karon farko a rayuwarsa. Al'amarin da yai matukar girgiza shi ke nan kuma ya ba shi mamaki. Kuma hakan ba ta taba faruwa ba a gareshi, kawai sai zuciyarsa ta ce da shi, Haba Shaddadu, wai shin tsoron me kake yi nes? Shin ka manta ne cewar mahaifiyarka ta gaya maka cewar in dai kana tare da wanann Mashi na Galilul Haras babu wani tsautsayi da zai same ka kuma babu wanda zai yi nasara a kanka?" Koda tuna wannan batu sai zuciyar Shaddadu ta kekashe ya yanke shawarar kawai a yi ta ta kare a wannan wuri.. Lokacin da mafarauci da Karensa suka zo za su gifta ta kasan wannan bishiya wacce Shaddadu ke zaune a kanta cikin siffar kwaron Malam buda mana Littafi sai Karen ya tsaya cak kuma ya ki ya wuce gaba. Koda ganin haka sai wannan 220 TASKARNOVELS.COM.NG mafarauci ya dakatar da Dakarun da ke bayansa yana mai tsayar da su da hannu, suka yi cirko-cirko sannan shi ma ya zare Takobinsa yana mai gyara tsayuwa. Karen ya zuba idanu akan bishiyar yana ta kallon kurilla amma sai ya kasa ganin wannan kwaro saboda kalar jikin nasa ta saje da kalar ganyen bishiyar iri daya sak! Kwatsam! Ba zato ba tsämmani sai suka ga kwaron Malam Buda mana littafi ya sauko kasa daf da wannan Kare. Ai kuwa sai Karen ya razana ya dawo baya a guje yazo daf da maigidansa wannan mafarauci ya tsaya. Koda kwaron ya sauka a kasa sai ya rikide ya zama Jarumi Shaddadu a cikin gagarumar shigar Yaki kuma rike da Mashin Galilul Haras. Faruwar hakan ke da wuya sai shi ma wannan mafarauci ya rikide ya zama Jaruma Ziya'ul Hak a cikin tata shigar Yakin. Shi kuwa wannan Kare sai yai girgiza ya zama Aljani Maruful Dauwaz. Koda wadannan Dakaru mutum arba'in suka yi arba da Aljani Maruful Dauwaz sai suka sulale kasa sumammu gabadayansu sabo da tsananin razana da firgita bisa ganin siffarsa. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin Jarumi Shaddadu da Jarumi Ziya'ul Hak, kowannesu jikinsa ya kama 221 TASKARNOVELS.COM.NG tsuma ana hararar juna. Cikin tsananin fishi Ziya'ul Hak ta yunkura za ta afkawa Shaddadu sai Aljani Maruful Dauwaz yai wuf ya riko ta kuma ya yi mata rada a kunne ya ce, "Ashe har kin manta cewa idan har Shaddadu na tare da Mashinsa na Galilul Haras ba za ki taba samun nasara ba a kansa. Koda jin wannan batu sai rán Ziya'ul Hak ya ɓaci ta dubi Maruful Dauwaz ta ce, to yanzu shi ke nan muna ji muna gani ga abin da muka zo nema sai dai mu kyale shi? Maruful Dauwaz ya sake yi ma ta rada a kunne a karo na biyu ya ce, "Ke yarinya ce kin cika gaggawa, ki tsaya mana mu jarraba dabarunmu na manya. Ai ita Saniya sai da shafa ake tatsar nononta. Gama fadin hakan ke da wuya sai suka ji Jarumi Shaddadu ya tuntsure da dariya. Lokaci guda kuma ya turbune fuskarsa ya dube su ya ce, Tabbas yau ne na yarda cewar idan Kere na yawo, Zabo ma yana yi, wata rana dole a hadu.Yau ramin karya ya kure babu ta inda za a bulle. Babu zancen бuya ko sauya siffa. Kun sani, ni ma na sani farautar juna muka fito, don haka yanzu sai a yi ta ta kare ko ni ko ku! Koda jin wannan batu sai Ziya'ul Hak ta tari numfashin Shaddadu ta ce, "Kai tsohon 222 TASKARNOVELS.COM.NG munafuki dan munafuka karyarka ta sha karya. A yau din nan zan yanke burin mahaifiyarka wanda ta dade tana tanadinsa shekara da shekaru. Yau zan kwatowa mabaifina 'yancinsa

Chapter 9 of 18