Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kin ceci rayuwata, ai babu bukatar kiyi mani godiya. Hursiyya ta yi murmushi sannan ta ce saboda me ba zanyi godiya ba ga abin kaunata ba, ya kai Hasnalu kayi sani cewa a rayuwata na fidda tsammanin cewa zan iya samun masoyi a duniya bbanda dan uwana sarki Dujalu, amman dana sadu da ki sai na gane ba haka bane, ina mai tabbatar maka da cewa a lokacin dana fara kyallara ido na ganka a take naji wani abu ya soki kahon zuciyata ban gane ko mene ne wannan abu 267 TASKARNOVELS.COM.NG daya soki zuciyar tawa ba sai bayan munci gaba da tafiya sannan na gane ashe so ne gami da haduwar jini, kaine namijin farko daya taba burgeni a rayuwata har naji na daina burin na bar duniya. Koda jin wannan batu sai jarumi Hasnalu yayi murmushi sannan ya ce yake wannan yar sarki kiyi sani cewa tundaga lokacin da kika ceci rayuwata kika tsaida jinin dake zuba a cikina, kuma naga kina hawaye saboda damuwa bisa halin dana shiga, kuma kika gode wa Ubangijina sakamakon farfadowata, sai naji nan take nim sonki ya shigeni, tabbas nayi matukar mamaki da har na kamu da sonki saboda acan garinmu naki yarda na baiwa kowacce ya mace soyayyata saboda na kudira a raina cewa sai na cika burin da mahaifina ya kasa cikawa na jaddada addini musulunci a wannan nahiyoyi naku, sannan zanyi aure kuma har sai bayan naga inda kabarin mahaifin nawa yake, ko kuma na samu labarin yadda aka yi ya mutu, ina ji a jikina cewa a sanadiyyarki zan cika burin nawa, kuma da izinin ubangijina sai kin zama matar aure bisa ka'idar addinina. Sa'ad da Hasnalu ya zo nan a zancensa sai gimbiya Hursiyya ta cika da tsananin farin ciki, ta 268 TASKARNOVELS.COM.NG dubeshi cikin murmushi ta ce ya kai abin kaunata ka yi sani cewa a halin yanzu ka cika sharadin dake tsakaninmu na ukun, tunda kayi gagarumin abin al'ajabi na kashe munafiki aljani Radiyan da taimakon ubangijinka, ni din nan ganauce na jiyau ba dan haka na bada gaskiya ga addinin musulunci, yanzu ba tare da wani bata lokaci ba in so ka shigar da ni cikin wannan addini naka na Musulunci. Koda jin wannan batu sai shima jarumi Hasnalu ya cika da tsantsar farin ciki, ba tare da wani jinkiri ba kuwa Hasnalu ya karanta mata kalmar shahada ta maimaita. Faruwar hakan keda wuya sai Hasnalu ya mike tsaye yana mai mayar da takobinsa daya kashe aljani Radiyan cikin kufenta suka nausa izuwa cikin daji da sauri kuma gudu-gudu tare da barin gawar aljani Radiyan anan. *********** Acan sansanin yaki kuwa lokacin da ttsanani yai tsanani sai labari ya sha bamban domin kowacce rundun dimaucewa ta yi, hankalinsu ya gushe banda kashe junansu babu abinda suke yi, kuma ragas ake yi a wannan aki dan ido bai isa ya tantance bangaren dake samun nasara ba. Acan bngaren sarki Maharaz da sadauki Himalu kuwa 269 TASKARNOVELS.COM.NG abin abu kyan gani domin kowanne ya sari abokin gwaminsa sau akalla bakwai bakwai, kowannensu jini ne ke zuba daga jikinsa, tun suna iya kaiwa juna hari har sai da takai cewa sun kasa, dan haka da kansu suka zubar da makamansu tare da sulalewa kasa cikin wani irin mugun yanayi wanda babu tabbacin zasu kai labari. A bangaren manyan zakuna kuwa wato sarki Dujalu da kuma jarumi Imnal abin ya kazanta fiye da na kowa saboda sai da suka shafe fiye da sa'a uku suna kaiwa juna sara da suka cikin matukar zafin nama juriya gami da bajinta ba tare da dayansu ya samu nasarar koda lakutar jikin daya ba, take a lokacin ajiya ta riskesu dan haka sai suka j da baya suna masu yin haki kamar zakaru, babban abin mamaki shine babu wanda yake iya kawo masu hari acikin mayan, kai ba wanda ma ya yarda ya rabi inda suke saboda kura ta san gidan mai babbar sanda. Bayan sarki Dujalu da Imnal sunyi kallon-kallo a tsakaninsu cike da harar juna gami da mugun nufi a cikin zukatansu har izuwa tsawon yan dakiku, sai suka sake rugowa da gudu suka kacame da sabon azababben yaki cikin sabon salo, a wannan karon kowannensu 270 TASKARNOVELS.COM.NG yana kai sara da suka cikin tsalle-tsalle gami da kwance-kwance, kuma suka dinga hadawa da kai naushi hannu da kafa. Faruwar hakan keda wuya sai rawa ta sauya tunda kidama ya sauya, nan take suka fara samun damar cuttar da junasu, a duk sa'ad da sarki Dujalu ya samu nasarar naushin Imnal a fuska, kafin ya sake kaima masa wani naushin shima imnal ya rama wannan naushi, nan da nan kuwa suka hada wa junansu jini da majina, suka fara luguiguita juna, ana cikin haka ne sarki Dujalu ya sammaci Imnal ya soka masa takobinsa a gefen saman kirjinsa, wanda har sai da takobin ta bullutso ta gadon bayansa. Imnal ya kwarara uban ihu saboda tsananin zafi da yaji, Dujalu yasa kafarsa ya doki kirjin Imnal jini yayi tsartuwa kuma Imnal yayi sama tare da fadowa kasa cikin tsananin galabaita yana numfashi gami da shure-shure kamar wanda ranshi zai fita. Cikin tsananin murna sarki Dujalu ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ta mugunta ya taho izuwa kan Imnal tarw da raba kafafunsa biyu akan Imnal din yana mai daga takobinsa sama da nufin ya cakata a cikin Imnal. Ba zato ba tsammani sai kawai yaga imnal ya tashi zaune, 271 TASKARNOVELS.COM.NG cikin zafin nama na gaban kwatance shima ya sokawa Dujalu tasa takobin a kirji a daidai inda shima ya sokeshi ya bullutso har gadon bayansa. Nan fa Imnal ya daddage iya karfinsa tare da naushin sarki Dujalu da daya hannun nasa, a take dujalu yayi sama a lokacin da Imnal ya zare takoninsa daga cikin kirjin sarki Dujalu aikuwa sai jini ya kama bulbulowa daga cikin kirjin, Dujalu ya fadi kasa magashiyan yana kakarin mutuwa. Imnal ya sake mikewa da nufin ya mike taaye amman sai jiri ya debeshi ya sake faduwa a kasa ya baje, nan fa aka rasa wanda zai iya sake tashi tsaye daga cikinsu, gashi dai suna cikin wani irin mugun hali na daf da mutuwa amman saboda naci gami da taurin rai kowanne a cikinsu burinshi shine ya tashi tsaye domin yaje ya kasara kashe abokin gabarsa amman sai gashi abu ya gagara. Ganin sun kasa mikewa tsaye ne yasa suka fara tafiya da jan ciki suna masu tunkarar junasu, sai da ya rage saura baifi taku uku ba a tsakaninsu sai duk su biyun suka sume a lokaci guda. A wannan lokacin gaba-daya dakarun dake a wannan filin yakin sun mutu babu sauran mutum daya daga cikin rundunonin wanda ya 272 TASKARNOVELS.COM.NG tsira da rayuwarsa. Adaidai wannan lokacin ne kuma jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka karaso filin yakin a guje,tun daga nesa gimbiya Hursiyya ta ga babu mutum ko daya a filin yakin, duk inda ta hanga sai dai taga gawarwaki fululu dan haka sai ta ringa duba gawarwakin tana neman gawar dan uwanta sarki Dujalu kuma tana mai fashewa da kuka, shima jarumi Hasnalu sai ya shiga duba gawarwakin dake a filin yakin ko zai ga wanda yake da sauran rai, sai da suka shafe rabin sa'a suna dube-dube sannan a lokaci guda suka zo kan Dujalu da Imnal, cikin gaggawa suka shiga kokarin ceto rayukansu, inda d farko suka fara tsayar da jinin dake zuba a jikinsu, sannan suka shiga dinke raunikan dake jikinsu tare da sa masu magani, kafin daga nan suka yayyafa masu ruwa suka farfado suna masu dawowa cikin hayyacinsu. A sannan nan ne Dujalu da Imnal sukaga jarumi Hasnalu da Hursiyya tsaye a gabansu kawai sai suka cika da tsananin mamaki kuma suka kmaa kalle kalle da hange-hange sukaga gabadaya filin gawarwaki ne babu sauran wani mai rai a cikinsa. Koda Hursiyya taga dan uwanta sarki Dujalu ya tsira da rayuwarsa sai ta rungumeshi 273 TASKARNOVELS.COM.NG ta fashe da kukan farin ciki, shi kuwa Jarumi Imnal a sannan ne hankalinsa ya dugunzuma ainun, ya fara kuka saboda ya hanga ko ina amman baiga gimbiya Mulaifa ba, kuma baiga sarki Maharaz ba, nan take ya takarkare ya kwarara uban ihu tare da fashewa da matsanancin kuka, haka yayita yin kukan yana mai dunkule kansa a kasa kamar ba zai daina ba. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka hango wani mutum daga can nesa ya mike cikin gawarwakin yana mai tunkaro inda suke yana tangadi. Su duka sai suka zuba masa idanu sai da ya kara matsowa kusa da su sosai sai sukaga ashe sarki Maharaz ne, a wannan gabadaya ya rine da jini, koda Imnal ya shaida cewa sarki Maharaz ne sai ya mike tsaye da kyar ya tafi zuwa gareshi, suna haduwa suka rungume juna tare da durkuwa a kasa. Cikin matukar karfin hali sarki Maharaz ya bude baki ya ce yayi magana a cikin kunne Imnal ya ce masoyiyyarka na can baya gawarwaki sun danneta, bani da tabbacin tana raye ko ta mutu. Koda jin haka sai Imnal ya saki Maharaz ya sake mikewa da kyar ya kara gaba. A lokacin ne sarki Maharaz ya yanke jiki zai fadi, kawai sai ga jarumi Hasnalu 274 TASKARNOVELS.COM.NG ya karaso gareshi a guje ya tallaboshi sannan nan take ya shiga ƙoƙarin ceto rayuwarsa. Imnal ya cigaba da tafiya yana tangadi sannan yana dube-duben inda gawarwaki suka danne gimbiya Mulaifa. A wannan lokacin gimbiya Hursiyya tana ta kokarin danne sarki Dujalu domin so yake ya mike tsaye ya je ya cigaba da yakar jarumi imnal, koda taga ya dage lallaı sai ya je ya kashe imnal din sai ta daka masa tsawa a karon farko a rayuwarta da shi. Cikin tsananin mamaki da takaici sarki Dujalu ya koma ya zauna a kasa dirshan sannan ya dubeta sa'ad da hawaye ya zubo masa ya ce yake yar uwata, yanzu yau kece da kanki kike daka mani tsawa akan ina son na kashe makiyinmu, ashe kin manta da duk irin halaccin da nayi maki kenan a baya, kuma kin manta da duk irin kaunar da na nuna maki, shin bakya kishin birninmu gami da jama'armu kenan, ko kuma kin makance ne baki ganin miliyoyin rayukan da muka yi asara da kuma dunbin duniyarmu data salwanta a filin yakin nan, yanzu kina nufin shikenan sai dai burina nason mallakar wannan duniya ya rushe, tabbas d dai haka ta faru gareni gwara ku kyaleni na mutu dan banga amfanin ceto 275 TASKARNOVELS.COM.NG rayuwata da kuka yi ba, wane ne wancan bakon jarumin dana ganshi a tare da ke, kuma ya aka yi kika dawo wannan filin alhalin nasa aljani Balzaru ya shammaceki ya daukeki ya tafi dake can birninmu? Hursiyya ta dubi sarki Dujalu a lokacin data share hawayen dake kan fuskarta ta ce ya kai dan uwana kayi sani cewa kayi mani tambayoyi masu yawa, amman kayi hakuri duk zan baka amsoshinsu nan bada jimawa ba, abinda yasa nayi maka tsawa a yau shine, a yau ne na gane da kai sarki Maharaz duk kuna kan tafarkin bata ne mabayyani, kuma kuna wannan yaki ne bisa zalunci da son zuciyarku kawai, gashi kun janyo anyi asarar miliyoyin rayuka ba tare da dayanku ya samu nasara ba, a yau kai da Maharaz zaku gasgata zancena cewar duk kuma kan hanyar bata domin a gaban idanunku wancan bakon jarumin zai yi abinda kuka kasa aikatawa da taimakon ubangijin gaskiya, koda ta zo nan a zancenta sai suka jiyo Imnal yana kwalla masu kira yana neman taimako. Hursiyya ta mike tsaye zumbur kawai sai ta hango Imnal yana ta kokarin ture wasu gawarwaki domin ya zaro gimbiya Mulaifa amman sai ya kasa, shi kuma a wannan lokaci 276 TASKARNOVELS.COM.NG jarumi Hasnalu nata kokarin ceto rayuwar sarki Maharaz. Koda ganin haka sai Hursiyya ta ruga da gudu izuwa inda Imnal yake, ta taimaka masa suka ture gawarwaki dake kan Mulaifa suka zarota, aikuwa sai suka isketa a raye tana numfashi kadan-kadan, cikin hanzari Hursiyya ta shiga ƙoƙarin ceto rayuwar Mulaifa ta fara tsayar da jinin dake zuba a jikinta ta hanyar saka masa magani, sa'ar m da aka yi shine babu manyan raunika a jikinta masu zurfi da yawa. Koda Imnal yaga Hursiyya ta dage tana kokarin ceto rayuwar masoyiyarsa gimbiya Mulaifa sai ya cika da tsananin mamaki bisa ganin kanwar babban abokin gabarsa ce take kokarin ceto masoyiyarsa. A wannan lokacin ne Imnal ya gama dawowa cikin hayyacinsa, ya juya baya ya hango sarki Maharaz a raye tare a jarumi Hasnalu kuma ya hango sarki Dujalu gefe daya zaune yana kallonsu, bayan kamar sa'a guda lokacin an gama yi wa kowa magani, aka samu nutsuwa sai gaba dayansu su shidan suka taru a waje guda, a lokacin ne Hursiyya ta kwashe labarinta ta zayyana masu, tun daga lokacin da ta hada baki da kuyangarta lazimat taje ta samo mata aljani Radiyan ya fito da ita daga gidan 277 TASKARNOVELS.COM.NG sarauta, kawo izuwa sa'ar da suka shiga cikin kunnen Aljani Raugatul Agwanu ya cigaba da tafiya da su har yazo dajin da suka hadu da jarumi Hasnalu, da dukkan abubuwan mamakin da jarumi Hasnalu yayi akan hanyarsa ta zuwa bisa taimakon Ubangijin musulunci, kawo izuwa lokacin da itama ta karbi addinin musulunci a hannun Jarumi Hasnalu har suka karaso bakin tekun. Lokacin da Hursiyya ta gama bada wannan labari sai jikin Mulaifa, Imnal da sarki Maharaz yayi sanyi, zukatansu suka yi sanyi suka fara ayyanawa cewa lallai wannan addini na Hasnalu shine addinina gaskiya. Shikuwa sarki Dujalu sai ya fashe da kukan bakin ciki, kuma cikin tsananin takaici ya ce yake yarbuwata hakika kin tarwatsa mani dukkanin shirina, yanzu duk irin tsananin wahalar dana sha ta tsawon shekara da shekaru ina shirye-shiryen mallakar duniya ina kuma mai yin tanadi ya zama na banza kenan? To bari in fada maki ni ban yarda cewa wannan addini shine n gaskiya ba, dan haka ina nan a kan bakana na cigaba da wannan yaki har sai na kashe abokan gabata na shiga cikin wannan teku na dauko takobin Saiful Lujara. Kafin 278 TASKARNOVELS.COM.NG Hursiyya ta kara budar baki ta ce wani abu sai sarki Maharaz ya tari numfashinsa ya dubi Dujalu ya ce ya kai wannan sarkin abokin gabata, ka sani cewa komai da yarjejeniya muke yinsa, mu yanzu mun janye maka wannan yaki mun hakura mun bar mka takobin Saiful Lujara, idn har zaka iya daukota to ga fili nan ga mai doki sai ka jaraba daukota mu gani, amman bisa sharadi guda Sharadin kuwa shine idan har ka kasa daukota kuma jarumi Hasnalu ya shiga ya daukota zaka bada gaskiya ga addininsa kamar yadda zamu bada gaskiya ga addininsa yanzun nan. Sa'ad da sarki Dujalu yaji wannan batu sai yayi shiru ya fada cikin kogin tunani, daga can kuma ya dubi sarki Maharaz ya ce na amince da wannan sharadi. Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauke takobinsa sannan ya dubi sarki Maharaz ya ce kafin na karbi addinin wannan bakon jarumin inason ka taimakeni na dawo da dukkan sihirin tsafina domin da shine zan iya shiga cikin wannan teku na yaki ljanun dake karkashinta masu gadin takobin na daukota. B tare da gardamar komai ba sarki maharaz yayi murmushi ya ce nasan cewa inba da taimakona ba babu yadda za'a yi 279 TASKARNOVELS.COM.NG sihirinka tsafinka ya dawo, lallai zan taimakeka b tare da naji shakka ko tsoron komai ba domin ni yanzu nayi imani cewa addinin Musulunci shine addinin gaskiya, kuma na yarda cewa kai ba zaka iya dauko wannan takobiba sai dai jarumi Hasnalu ya daukota. Koda jin haka sai Sarki Dujalu ya bushe da dariyar mugunta yana mai cewa aikuwa sai ka yi nadama kuma ka gane cewa kayi babban kuskure tunda har zuciyaka ta yarda da hakan, ina mai tabbatar maka da cewa indai sihirin tsafina ya dawo jikina to sai na samu nasarar dauko takobin Saiful Lujara, kuma kaine mutum na farko da zan kasheshi da ita. Sarki Maharaz yayi murmushi sannan ya ce na amince d hakan. Gama fadar hakan kedawuya sai sarki Maharaz ya mike tsaye shima sarki Dujalu sai ya mike tsaye suka tunkari juna, saura bai fi taku daya ba su hadu sai cikin sauri Hursiyya ta shiga tsakaninsu ta dubi sarki Dujalu idanunta na zubar da hawaye ta ce ya kai dan uwana na rantse da girman iyayenmu ko tsafinka ya dawo ba zaka iya dauko wannan takobiba... Kafin Hursiyya ta gama rufe bakinta tuni sarki Dujalu ya hankadeta ta fadi can gefe guda, kawai sai ya 280 TASKARNOVELS.COM.NG dubeta a fusace yana mai cewa kin bani kunya d har kika zabi abokin gabarmu kika gujeni, to kisani cewa har abada bazan yada Addinin iyayye da kakanni ba domin shine abin kunya na karshe da zanyi a rayuwata. Yana gama fadin hakan ne sai ya karasa jikin sarki Maharaz suka manne da juna, faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske mai karfi ya lullubesu, aka fara wata irin gagarumar iska mai karfi gami da taawa da walkiya a sararin samaniya, kawai sai sarki Maharaz ya janye jikinsa daga jikin na Dujalu tare da komawa gefe daya. Take wani irin jan haske ya taho daga sararin samaniya ya rinka shiga jikin sarki Dujalu har saida ya gama shigewa kaf, a sannan ne sarki Dujalu ya ji wani irin azababben karfi ya shigeshi, irin wanda bai taba jin irinsa a duniya ba, dan ji yake tamkar idan aka yi masa gammo zai iya daukar wannan duniyar a ka ya kuma yi tafiya da ita. Nan take sarki Dujalu ya kwarara uban ihu kuma y sunkuya kasa ya dauki takobinsa ya nufi bakin tekun bahar sufiya kai tsaye ba tare da shakkar komai ba, har ma yana ji a cikin ransa cewa cikin kankanin lokaci zai iya karar da duk aljanin da suke cikin wannan teku kuma ya dauko 281 TASKARNOVELS.COM.NG takobin Saiful Lujara. Nan dai y shiga cikin tekun ya nutse can cikin karkashinta. Faruwar hakan keda wuya sai Sarki Maharaz ya dubi jarumi Hasnalu cikin murmushi ya cw da shi ya kai wannan babban jarumi mai daraja, wanda ya fitar damu daga cikin duhu izuwa haske, maza ka shigar damu 2annan addini naka mai daraja, kamar yadda ka shigar da Hursiyya. Kafin jarumi Hasnalu ya bude bakinsa sai kawai suka ji wata irin iska mai karfi ta taso masu har tana neman wujijjigasu, sai da takai cewa sun rike hannayen juna dan kada iskar tayi sama da su, katsam kuma sai guguwar ta rikide ta zama wani gwabjejen aljani wanda girmansa ya ninka na aljani Raugatul Agwanu sau bakwai, gangar jikinsa ta rufe gabas gabadaya. Koda sarki Maharaz yayi arba da wannan aljani sai ya kamu da tsananin tsoro ya durkusa a kasa bisa gwiywoyin, ba wani bane wannan aljani face aljani darbuza, gunkin da ake bauta mawa acan birnin sarki Maharaz. Darzuba ya dubi sarki Maharaz a fusace ya daka masa tsawa ya ce ashe yanzu duk taimakon da muka dade muna yi maka tsawon shekara da shekaru ya zama na banza, mune muka doraka akan karagar mulki, 282 TASKARNOVELS.COM.NG muka baka arziki mai yawa, kuma muka daukaka amman kuma shine yanzu zaka yi mana butulci kadaina bauta mana ka koma bautar wani...? Kafin aljani darzuba ya karasa kalmar dake bakinsa tuni jarumk Hasnalu ya tari numfashinsa ya daka masa tsawa yana mai cewa kai tsohon kafiri, babban matsafi kuma mayaudari kayi sani cewa kai ba komai bane face bawan ubangijin musulunci domin shime ya halicceka, shekara da shekaru kana yaudarar sarki Maharaz da jama'arsa kana shiga cikin gunkin da suke bauta mawa kana magana da su a matsayin ubangijinsu, to ka sani cewa yau dubunka ta cika, kuma asirinka ya tonu, ina mai kiranka daka tuba ka daina kiran kanka a matsayin ubangiji ka mika wuya ga ubangijin musulunci wanda shine ubangijin komai da kowa. Koda jin wannan batu sai aljani Darzuba ya bushe da wata mahaukaciyar dariya wacce ta cika dajin gaba daha da amsa kuwwa, dan haka dole kowa ya rinka toshe kunnuwansa. Lokaci guda kuma darzuba ya tsuke fuskarsa yana mai daka wa jarumi Hasnalu tsawa yana mai cewa kai karanin kwaro, karyarka tasha karya, fiye da shekaru dubu ina fafawa da ire283 TASKARNOVELS.COM.NG irenka amma basu taba samun nasara akaina ba, saboda haka kalma yanzu zanyi maka kisan gilla a gaban wadannan mutane, domin su zama sheda akan cewa nine abin bauta mafi cancanta. Gama fadin hakan keda wuya sai aljani Darzuba ya wangame katon bakinsa ya frsa wa jarumi Hasnalu wata irin gagarumar wuta. Cikin bakin zafin nama Hasnalu ya daka wawan tsalle ya bar inda yake yana mai neman taimakon Allah, aikuwa sai wannan wuta ta zuba akan wata katuwar bishiya, wacce kaurinta ya kai kamu arba'in, tsayinta kuwa ya kai zira'i saba'in. Nan take bishiyar ta nake ta zagwanye kamar an tsom alumin a cikin ruwa, sai tiririn hayaki kawai aka gani na ruburbushin bishiyar. Koda aljani Darzuba yaga jarumi Hasnalu ya tsallake annan mugun hari nashi, sai ya taso masa a fusace da dukkan karfinsa, aikuwa shima Hasnalu sai ya tare shi rike da takobinsa suka kacame da azababben yaki mai tsananin ban tsoro, a duk sa'ad da takobin Hasnalu ta hadu da takobin aljani Darzuba sai kaji kara kal! Kal!! Tamkar karfe da karfe ne suka hadu, kuma tartsatsin wuta ya tashi, nan fa Imnal, Hursiyya, Maharaz da Mulaifa suka cika 284 TASKARNOVELS.COM.NG da tsananin mamaki bisa ganin irin jarumtakar Hasnalu, domin kwanjin aljani darbuza guda daya ma ya kai kaurin bishiyar katuwar kuka guda uku, amman duk sa'adda ya kai wa jarumi Hasnalu naushi ya kauce tofa duk abinda ya samu walau dutse ko bishiya take suke ragargaje, haka idan ya kai mashi sara ko suka da mugayen faratan hannayensa masu tsananin karfi da tsini kamar zabira to kome suka samu sai dai kaga abin ya dare gida biyu kamar an yanka tsakiyar tuffa, ko kuma kaga abin ya huje tamkar an hujeshi da mashi. Nan fa suka tayar da hankalin dajin gabadaya, kasa ta kama girgiza wuta ta dinga fallatsa tana dira a wurare da dama tana haddasa gobara, su kansu su Imnal sai da suka gama guje-guje suna neman wajen buya, saboda masifar takai masifa, amman duk da haka basu fasa leken su aljani Darzuba ba domin suga abinda ke wakana. Haka dai aka cigaba da wannan bakin artabu tsakanin jarumi Hasnalu da aljani Darzuba, har dare ya raba sosai amman daya daga cikinsu bai samu nasarar koda lakutar jikin dya ba, da kansu suka ja da baya suk yi cirkocirko suna haki gami da harar juna. Shi dai aljani 285 TASKARNOVELS.COM.NG Darzuba mamaki ne ya kamashi ainun yadda har aka yi yau ya hadu da shu'umin biladama alhalin tsawon shekara da shekaru yana cin karensa ba babbaka, duk mahalukin da suka yi gaba da gaba da shi walau mutum ko aljan, tofa a cikin abinda bai fi dakika goma ba yake gamawa da shi komai karfin damtsensa dana sihirinsa kuwa, amman yau gashi dan tatsitsin biladama ya gagareshi a kusan sa'a bakwai suna gumurzu. Shikuwa jarumi Hasnalu tunda suk fara wannan gumurzu addu'a yake yi a zuciyarsa ta neman tsari, dan haka a yanzu sai ya fra karanta addu'ar neman sa'a akan abokin gaba, a daidai wannan lokacin ne aljani Raugatul Agwanu ya iso bakin tekun dauke da boka Sadusa, Halyal da Gimbiya Shalbirat ya dauka a bayan wani katon dutse inda su Imnal suka buya, su duka sai suka fara leke suna hango inda ake wannan gumurzu, abinda suka iya hangowa kawai shine aljani Darzuba da jarumi Hasnalu a tsaye sun fuskanci juna suna kokarin sake kacamewa dda wani sabon fada. Su jarumi Imnal kuwa sun buyan wasu fogyen bishiyu dake nesa kadan da inda ake wannan fafatawar, suna masu kallon abinda zai faru. 286 TASKARNOVELS.COM.NG Koda su aljani Raugatul Agwanu suka hango aljani Darzuba da Jarumi Hasnalu su biyu kacal a bakin kogin bahar sufiya sai suka cika da tsananin mamaki, aljani Raugatul Agwanu ya jinjina kai cikin alamun tsoro ya dubi su Sadusa ya ce Tabdijan lallai yau abin babbane, tunda har takai cewa saura manyan mazaje kafai a filin dagar, shin ko kunsan wancan wane aljani ne a tsaye kuwa? Boka Sadusa ya dubeshi cikin ashin sani yace wane ne? Kuma wane ne biladaman dake fuskantarsa? Raugatul Agwanu yayi ajiyar zuciya sannan yace ai wancan aljanin shine sarkin sadaukai na dukkan aljanun duniya, kuma shine ubangijin da mutanen sarki Maharaz suke bauta mawa, kimanin shekaru dubu ashirin baya an taba yin yakin duniya na aljanu, wannan sarki na aljanu shine kadai ya baro filin daga a raye, amman sai da gabadaya mayakan sama da aljanu dubu dari tara suka mutu, a tarihin sadaukai da mayaka na duniya ba'a taba samun jarumi kamarsa ba, shi kuma wancan bil'adaman ban taba ganinsa ba, kuma ban taba jin labarinsa, ku duba da kyau gabadaya filin yakin can ciccike yake da gawarwaki, daga nan ma ina iya 287 TASKARNOVELS.COM.NG hango ruburbushin sassan jikin aljanu dukkaninsu sun kone, ai kawai ina ganin cewa mu tsaya anan mu cigaba da kallo domin muga yadda wannan fada zai kasance tsakanin Darzuba da wancan shaidanin biladama, na tabbata duk akan takobin Saiful Lujara suke fadan, babu mamaki suyi ragas mu kuma mu tsinci dami a kala. Koda jin wannan batu sai tunanin boka Sadusa ya sauya, shi dai burinsa kawai yazo yaga sarki Dujalu ya mutu ya koma can kasarsa ya sanar wa da yan majalisarsa a bashi babban mukami a masarautar, amman kuma yanzu da yaji batun samun takobin Saiful Lujara a saukake sai ya fara tunanin ya za'ayi ya mallaketa shi kadai, ya shammaci aljani Raugatul Agwanu ya halakashi tunda ya fahimci cewar shi sokone, nan dai ya kudurce a ransa cewa ya saurara yaga yadda karshen wannan gumurzu zai kasance tsakanin aljani Darzuba da bakon jarumin da baisan ko wane ne ba. Acan karkashin tekun bahar sufiya kuwa lokacin da sarki Dujalu yayi nutso zuwa cikinta yana mai jin tsananin karfi a jikinsa, yana ji tamkar zai iya yakar duniya kaf sai y kama lalube, nan fa ya dinga tafiya irin ta kifi a cikin tekun, da yayi 288 TASKARNOVELS.COM.NG tafiyar tsawon rabin sa'a yaga baiga alamar takobin Saiful Lujara ba, sai ya dawo da baya yayi yamma, haka dai ya cigaba da lalube har ya nufi bnagaren karshe na arewa, aiko yana cikin wannan gudu ne ya hango dandazon wadannan aljanu masu gadin Takobin Saiful Lujara a gaban wata katuwar akwatu ta zinare sunyi mata kawanya a sama da kasa. Koda sarki Dujalu ya hango ttsananin yawan aljanun nan da kuma kirarsu ta girma da sadaukantaka gami da irin mugayen makaman da suke dauke d shi sai zuciyarsa ta buga karfin gaske yaji tsoro ya darsu a cikin zuciyarsa, amman daya tuna irin shekarun daya bata yana shirye-shirye akan mallakar annan takobi ta Saiful Lujara da kuma tsananin wahalar da ya sha a wannan yakin har yakai ga wannan nasara ta matakin karshe, sai yaji dukkan tsoro ya gushe daga cikin zuciyarsa, yace ai rai ba a bakin komai yake ba muddin akwai biyan bukata, dan haka sai yayi kukan kura y ruga izuwa kan mugayen aljanun da nufin ya tsarwatsasu ya fasa wannan akwatu ta zinare ya dauko takobin Saiful Lujara daga cikinsa, a maimakon aljanun su taso masa gaba dayansu, sai guda daya ne jal ya taso masa suka kaure da 289 TASKARNOVELS.COM.NG zababben yaki, aikuwa suna fara yakin ne sarki Dujalu ya gane kuransa domin tsananin zafin naman ljanin da karfin damtsensa gami da na sihirinsa ya ninka nasa sau bakwai, sai da takai cewa sarki Dujalu baya iya kaiwa aljanin hari sai dai kokarin kare kai kawai d yake yi, gashi dai duk sa'ad da aljanin ya sari jikin Dujalu makamin baya tasiri amman fa jikin nasa yan tsami dan yana shan bugun tsiya. Koda wannan aljanin yaga Dujalu

Chapter 12 of 18