Ramlatul Siyam ya je wajen Aljani
Maruful Dauwaz ya ce, to yanzu ka zo ka sanar
da mu halin da 'yarmu ke ciki kuma ka sani
cewa babu wani taimako da za mu iya yi mata
tunda har yanzu ni ba ni da karfin jikina. Na
rasa jarumtaka tun daga lokacin da Sharlis ta
sihirce ni kuma na rasa dukkan karfin sihirina na
tsafi. Kai wanne hukunci ka yanke wa kanka?
Shin ka dawo ke nan ba za ka ci gaba da tsare
lafiyar 'yata ba? Koda jin wannan tambaya sai
idanun Maruful Dauwaz suka ciko da kwalla har
hawaye ya zubo masa ya dubi Sarki Laffaru ya
ce, ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa muddin
ina numfashi a doron kasa ba zan iya nisantar
'yarka ba domin a dalilinta ne kadai na yarda na
ci gaba da rayuwa a doron kasa saboda tana
matukar kama da masoyiyata. Babban abin
bakin cikina wanda zan mutu da shi a cikin raina
kuma wanda shi ne burina na karshe shi ne
rashin sanin inda wasiyyar masoyiyata take.
333
TASKARNOVELS.COM.NG
Inda zan ga wannan wasiyya ta isa ta debe mini
kewar rashin masoyiyata domin zan koma
Kogon Darul Ikisina na karasa rayuwata ya
zamana cewa kullum dare da rana ba ni da wani
aiki sai karanta wasiyyar tata har izuwa ranar da
wa'adina zai cika. Tun da dai yanzu ban ga
wannan wasiyyar ba dole na ci gaba da rike
alkawarina na kare lafiyar 'yarka da rayuwarta
iyakar karfina koda a sanadın hakan ne zan
sadu da ajalina. Ina so ka sani cewa na zo ne
na sanar da ku halin da ake cíki a matsayinku na
iyayen Ziya'ul Hak don kada mu riski ajalinmu ni
da ita ba ku san abin da ya faru ba a gare mu,
sannan kuma na yi tunanin cewa ku bil'Adama
kuna da hikima da basira irin wacce mu aljanu
ba mu da ita, babu mamaki kuna da wata
dabarar wacce za ta iya tserar da mu daga
sharrin Jarumi Shaddadu. Lokacın da Aljani
Maruful Dauwaz ya yo nan a zaneensa sai Sarki
Laffaru ya sunkui da kansa kas ya shiga tunani
mai zurti har izuwa lokaci mai dan sawo daga
can sai ya dago kai ya dubi Aljani Marutul
dauwaz ya ce, Masu ya magana sun ce faduwar
gaba asarar namiji ce, sau tari idan masifa ta
tunkaro mutum to bai kamata ya zauna jiranta
334
TASKARNOVELS.COM.NG
ba gwara ya je ya tare ta domin idan ya bari ta zo
ta riske shi har inda yake za ta yi masa kwaf
daya ne. Tabhas yanzu zan yi amfani da
shawarar matata, kuma akwai wata dama guda
daya wacce idan har na same ta a cikin gıdan
Sarautar Sarauniya Zubaina to ta karfin
dantsena da na sihirina zai iya dawowa. Koda
jin wannan batu sai mamaki ya turnuke Maruful
Dauwaz ya ce, yanzu kai dama ka san hanyar da
za ka iya dawo da martabarka amma ba ka bi ba
tun tuni? Sarki Laffaru ya gyada kai cikin
alamun takatci har kwalla ta zo masa sannan ya
ce, da ma Boka Muzaffar ya sanar da ni cewa
hanya biyu ce zan iya bi na sami waraka daga
sharrin Sharlis. Hanya ta farko ita ce, ta auren
Ramlatul Siyam mu haifi 'yar da za ta iya kashe
Shaddadu da mahaifiyarsa. Hanya ta biyu kuwa
ba zan taba samunta ba face a wajen
mashahuriyar Sarauniya wacce ta kasance
gagarumar matsafiya mai mulkin babban Birni
wanda ya kai Birni na Kufa. Bisa labarin da ka
ba ni na Sarauniya Zubaına na fahimci cewar
duk tana da wadannan abubuwa wadanda Boka
Muzaffar ya siffanta mini. Koda jin wannan
batu sai farinciki ya lullube Aljanı Marutul
335
TASKARNOVELS.COM.NG
Dauwaz ya ce, ai kuwa idan karfin dantsenka da
na sihirinka suka dawo shi ke nan mun tsira
daga sharrin Sharlis da danta, musamman idan
ba sa tare da Mashin Galilul Haras. Ka sanar da
ni hanyar da za ka bi ka dawo da komai naka
domin na san irin taimakon da zan iya ba ka.
Koda jin wannan batu sai Sarki Laffaru yai ajiyar
zuciya yace, ai da zarar na furtawa wani
al'amarın komai ya rushe domin ka'idar sihirin
ke nan. Yanzu dai bari mu yi shiri ni da matata
mu zo ka kai mu can Birnin Sarauniya Zubaina
domin a yi ta-ta kare. walau mu sami nasara
akan makiya ko kuma su sami nasara akanmu
kowa ya huta da fargaba. Koda gama fadin
hakan sai Sarki Laffaru ya juya ya nufi inda
Ramlatul Siyam take ya sanar da ita cewa ta
shiga cikin Bukka ta dauko musu kayansu
domin su tafi i zuwa can inda 'yarsu take. Koda
jın haka sai farinciki ya lullube Ramlatul Siyam
ta ruga i zuwa cikin Bukkar tasu ta debo musu
kayansu ta fito. Ba tare da bata wani lokacı ba
suka hau kan Aljani Maruful Dauwaz ya tashi da
su sama ya luluka a cikin gajimare yana tsala
azababben gudu. *** A can Birnin Sarauniya
Zubaina kuwa, Jarumi Shaddadu da Yaldisa na
336
TASKARNOVELS.COM.NG
labe a cikin duhuwar wadansu ciyayi da ke nesa
kadan da gidan Sarautar suna hangen Dakarun
da ke kai kawo a kofar gidan don tabbatar da
tsaro, suna tunanin hanyar da ya kamata su bi
su samı nasarar shiga cikin gidan Sarautar a
lokaci guda farat daya. Bayan sun shafe 'yan
dakiku suna tunanı sai dabara ta fado wa Jarumi
Shaddadu ya dube ta ya ce, abin da za mu yi
yanzu kawai shi ne, mu yi fitar burgu da gudu
mu afkawa wadancan Dakarun da ke bakin
kofar gidan Sarautar. Da zarar mun tarwatsa
su zan dawo da baya ki tsaya a gaban kofar
gidan Sarautar ni kuma sai na rugo da gudu, ki
hada tafin hannayenki biyu a waje guda na taka
su da kafa daya ke kuma sai ki cilla sama na
haye katangar gidan na fada ciki, ina fadawa
zan tarwatsa masu tsaron bakin kofar daga ciki
ki shigo ciki, a sannan ne za a fara wannan
gagarumin Yaki. Koda jin wannan batu sai
murna ta kama Yaldisa. Nan take su biyun suka
mike zumbur! A lokacı guda suka zare makamai
suka ruga da azababben gudu izuwa kan masu
gadin da ke kofar gıdan Sarautar. Kafin daya
daga cikin masu gadin ya dauki wata katuwar
guduma ya doka akan wani babban Bandiri tuni
337
TASKARNOVELS.COM.NG
Yaldisa ta daka tsalle sama ta doki fuskarsa da
guiwarta. Nan take yai sama ya fado Kasa
sumamme. Shi kuwa Shaddadu sai ya afkawa
sauran masu gadin wadanda adadinsu ya kai
goma sha daya a lokacin da suka yi masa
rubdugu. suna kawo masa sara da suka ta ko
ina. Maimakon shu ma ya yake su da makami
sai ya rinka kaucewa harin nasu cikin wani irin
bakın zafin nama na al'ajabi ya rinka gabza
musu naushi. Duk wanda ya nausa sau daya sai
ka ga ya zube kasa sumamme, Kafin cikar
dakika ashirin sun gama bazar da Dakarun gaba
daya Faruwar hakan ke da wuya sai Shaddadu
ya koma da baya ya rugo da gudu ya taka
hannayen Yaldisa ta cilla shi sama sai ga shi ya
haye katangar gidan Sarautar ya dirga ciki. Yana
dira ya tarwatsa masu gadin yai sauri ya bude
kofar Yaldisa ta shigo da sauri ta fara harbo
Dakarun da ke sama da kibiyoyinta suna
fadowa kasa suna ihu, shi kuma Shaddadu ya ci
gaba da gudu yana sara da sukar Dakaru a
lokacin da Dakaru suka fara tuttudowa ta ko
ina. Nan fa gidan Sarautar ya hargitse ya
yamutse da haniniya, ihun Dakaru gami da
karafkiyar karafa. Dabarar da su Shaddadu
338
TASKARNOVELS.COM.NG
suka yi ita ce, ba su yarda sun tsaya a waje daya
ba, suna Yakin ne suna gudu suna durfafar can
gidan Sarautar suna tarwatsa Dakarun da karfin
tsiya ba su yarda sun tsaya a waje daya ba. A
wannan lokaci ne Jarumi Shaddadu ya cika da
tsananin mamaki bisa ganin irin gagarumar
jarumtakar da Yaldisa ke yi. Nan fa kansa ya
daure ya kama zancen zuci yana mai cewa,
yaya aka yi Yaldisa ta zama gagarumar
mayakiya haka alhalin tana rayuwa ko yaushe a
gidan abincin Sarauniya Zubaina kuma ba ta
kasance daya daga cikin manyan garin ba?
Haka dai Yaldisa da Jarumi Shadaddu suka ci
gaba da ragargazar Dakarun gidan suna daďa
kutsawa can ciki, kuma Yaldisa ce akan gaba
tun da ita ce ta san hanyar da za a bi a isa har
can inda turakar Sarauniya Zubaina ta ke. Da
ma tun kafin su shigo cikin gidan Sarautar
Yaldisa ta gargadi Jarumi Shaddadu akan cewar
kada ya kuskura ya bari a kama su a tare ko
kuma su yi arba da Zubaina a tare tunda za ta
iya hallaka su farat daya da karfin sihrin
tsafinta. Bisa wannan dalili ne Jarumi
Shaddadu ya rinka bayar da 'yar tazara
tsakaninsa da Jaruma Yaldisa, burinsa kawai
339
TASKARNOVELS.COM.NG
shi ne ya yi arba da Ziya'ul Hak su bambance a
wannan rana tunda kowannensu sai dai karfin
dantsensa ya kwace shi ba dai karfin sihiri ba
saboda kowannensu sihirin tsafinsa ya daina
aiki. **** A can Turakar Sarauniya Zubaina
kuwa, tana cikin yin barcinta mai dadi har da
munshari sai ta ji hayaniya kamar a mafarki. A
firgice ta farka ta mike zaune. Ai kuwa sai ta ji
mafarki ya zama gaskiya domin gabadaya gidan
Sarautar ya cika da sautin ihun Dakaru da gujegujensu. A daidai wannan lokaci ne ta ji
Shugaban Dakarun tsaron na gidan Sarautar
yana kwalla mata kira kuma yana buga kofa.
Cikin hanzari ta sauko kasa daga kan gadon
tana sanye da rigar barci, kawai sai ta zaro
Takobinta wacce ke tataye a sama jikin bango
sannan ta je ta bude kofar, tana budowa ta yi
arba da Shugaban Dakarun a tsaye jikinsa na
tsuma. Shugaban Dakarun ya dube ta cikin
tsananin kaduwa ya ce, ya Shugabata yau dai
wadansu zakwakuran Jarumai ne guda biyu
suka kawo mana harin sumame gidan nan, duk
yawan nan namu ya zama na banza sai tarwatsa
mu suke, ga shi suna sanye da kayan Karle ko
mun saresu bama iya cutar da su kuma ga
340
TASKARNOVELS.COM.NG
dukkan alamu so suke su Karaso nan Turakarki.
Koda jin haka sai Zubaina ta yi murmushi ta ce,
tabbas babu wadanda za su vi wannan aiki face
Jarumi Shaddadu da Yaldisa. Abin da nake so
da kai shi ne, ka ruga can masaukin baki ka
dauke Jaruma Ziya'ul Hak da sauri ka boye ta a
wani wurin kada ka bar ta ta ce za ta tari su
Shaddadu ta yake su face na yi arba da su,
yanzun nan ni ma zan kimtsa na fito. Shugaban
Dakarun ya risina ya ce, an gama ya Shugabata.
Kawai sai ya ruga da gudu ita kuma Sarauniya
Zubaina sai ta shiga sanya kayanta na Yaki da
sauri, ta kawo damara ta bakin karfe da bakin
sulke ta sanya kuma ta zuba layu da gurayenta
na tsafi duka sannan ita ma ta fito da gudu daga
cikın Turakarta tana neman inda su Shaddadu
suke. Babban kuskuren da Sarauniya Zubaina
ta yi shi ne, ba ta dauko madubin tsafinta ba ta
duba ta ga a daidai inda Shaddadu yake bare ta
je ta tare shi. Al'amarin Jaruma Ziya'ul kuwa
tun da ta kwanta a masaukin nata a wannan
dare sai idanunta suka kekashe ta kasa yin
barci saboda tunani da zullumin halin da ta
tsinci kanta a ciki. Hakika zuciyarta ba ta
gamsu da cewar Sarauniya Zubaina za ta iya
341
TASKARNOVELS.COM.NG
taimakonta ba akan su kawar da Jarumi
Shaddadu kuma hankalinta bai kwanta da ita ba
tunda ta fuskanci cewar babu wani abu da ya
damı Sarauniya Zubaina face son ta mallaki
Mashin Galilul Haras. Nan take Ziya'ul Ilak ta ji
babu abin da take so sama da ta yi gaba da
gaba da Shaddadu domin su kawo Karshen
wannan muguwar kiyayya tasu. Tana cikin
tsakivar wannan tunani ne kawai ta ji gıdan
Sarautar ya rude da hayaniya. Nan take jikinta
ya ba ta cewa lallai su Jarumi Shaddadu ne suka
kawo harin sumame, kawai sai ta ji farın cıkı ya
lullube ta. Cikin hanzari ta mike tsaye ta dauki
makamanta na Yaki ta bude kofar dakin nata ta
ruga waje da gudu tana neman su Shaddadu
Duk inda ta fi jiyo ihun mazaje nan take yi amma
duk inda ta je sai dai ta yi arba da gawarwakin
Dakaru ko kuma ta ga wadansu Dakarun sun
taho da gudu sun wucewa ta suna neman su
Shaddadu. Al'amarin da ya fusata taa ke nan
ta cigaba da falfala gudu tana shiga sako-sako,
lungu-lungu. Kwatsam! Tana shigowa cikin
wata babhar haraba sai ta yi kicibus da Jarumi
Shaddadu ya sheko da gudu. Wani akasi kuma
da aka samu shi ne, babu kowa a wajen sai su
342
TASKARNOVELS.COM.NG
biyu kacal, sai kuma daidaikun Dakarun gidan
da ke gilmawa a guje ba su ma lura da su ba.
Lokaci guda duk su biyun suka yi tirjiya aka fara
kallon-kallo, kuma kowannensu jikinsa ya kama
tsuma, har tsawon 'yan dakiku Daga can sai
kowannensu ya fara kokarin zare makami,
kuma a yanzu ne duk su biyun suka sami damar
karewa juna kallo kamar yadda ya kamata
Koda kowannensu ya ga irin tsananın kyawun
da Allah Ya bai wa dan uwansa sai zuciyoyinsu
suka buga da karfi suka ji kamar su fasa yakar
juna amma kuma da kowannensu ya tuno da
irın labarin da aka ba shi akan irin kiyayyar da ke
tsakanın iyayensu da kuma yadda aka cusa
musu gabar juna ķtun suna yara sai dukkaninsu
suka rugo da gudu izuwa kan juna suna masu
daga makamansu sama suna kurma uban ihu
Ai kuwa suna haduwa suka kacame da
azababben Yaki suka rinka kai wa juna sara da
suka cikin tsananin zafin nama, juriya da bajinta
tamkar jikinsu ba na jini da tsoka ba ne, na karfe
ne. Sai da suka shafe kusan rabin sa'a suna
bakin artabu amma dayansu bai sami nasarar
koda lakutar jikin daya ba. Al'amarin da ya nuna
cewar karfi ya zo dava ke nan. Da kansu suka ja
343
TASKARNOVELS.COM.NG
da baya suka tsaya suna dan haki amma ko
alamar gajiya babu a tare da su. kawai sun
tsaya ne domin su yi tunanin irin salon fadan da
ya kamata su sauya. Ai kuwa sai suka sake
rugowa da gudu a káro na biyu suka sake
kacamewa da sabon masifaffen fada, Wannan
karon dai sai suka sauya salo suka hada da yin
alkafira a sama da kasa kuma suna kai naushi
hannu da kafa. Nan take kuwa fadan ya sauya
yanayi domin sun fara samun nasarar yi wa juna
illa sai dai wani abin mamaki shi ne, da zarar
Shaddadu ya samu nasarar naushin Ziya'ul Hak
a fuska sai ka ga ita ma ta samu nasarar
ramawa. Nan da nan cikin Kankanin lokaci
suka hadawa juna jini da majina. A sannan ne fa
suka fara jigata har kowannensu ya sami
nasarar yankar kowa sau uku. Ita dai Ziya'ul
Hak ta yanki Shaddadu ne a cinyarsa ta hugu da
ta dama, sai kuma a gefen kafadarsa ta hagu.
Shi kuwa ya yanketa ne a dantsen hannayenta
biyu da kuma bayan cinyarta ta hagu.
Kowannensu jini na diga a jikinsa har suna layi
amma saboda na ci gami da taurin rai ba su
daina ci gaba da kai wa juna hari ba. *** A
can wani bangare dabam na gidan Sarautar
344
TASKARNOVELS.COM.NG
kuwa Sarauniya Zubaina ce da Yaldisa aka yi
mugun gamo a lokacin da tazarar da ke
tsakaninsu ba ta wuce taku goma ba. Bayan
kowacce ta yi turus! Sai Yaldisa ta yi sauri ta yar
da Bakan da ke hannunta kuma ta cire jakar
Kibiyoyin da ke goye a bayanta ta yar da ita
sannan ta fuskanci Sarauniya Zubaina ta ce,
abin kunya ne Jarumar Sarauniya kamar ki ta
Yaki baiwarta da karfin sihiri ko makami, idan
har kin yarda cewar ke Sarauniya ce kuma
Jarumar da ta gaji jarumta da mulki ki ajiye
tsafinki da makaminki ki yake ni da tsagwaron
karfin dantsenki. Ki yi sani cewa na dade ina
jiran zuwan wannan rana da zan dauki fansa a
kanki da iyayenki domin ku ne sanadin mutuwar
iyayena, kuma ke ce sanadin lalacewar
rayuwata na taso a cikin rashin tarbiyya na
zama karuwa! Koda Yaldisa ta zo nan a
zancenta sai Sarauniya Zubaina ta bushe da
dariyar mugunta, lokaci guda kuma ta turbune
fuska ta ce, Ke yarinya tabbas yau zan nuna
miki cewa na gaba yai gaba, na baya sai labari.
Na rantse da darajar iyayena ba zan yake ki da
karfin sihiri ba ko makami ba, zan yake ki da
tsagwaron karfin dantsena. Sai na yi miki
345
TASKARNOVELS.COM.NG
dukan kawo wuka sanann zan murde miki wuya
ko kuma na shake ki har sai numfashinki ya
dauke kin zama gawa. Yaldisa ta ce, ai inda
babu kasa a nan ake gardamar kokawa, ga fili ga
mai doki sai a zuba a gani. Gama fadin hakan
da wuya sai Yaldisa ta kwabe kayan karfen da
ke jikinta ta zubar a gefe daya. Ita ma
Sarauniya Zubaina sai ta cire sulkenta da
dukkan kayan Yakinta ta watsar sannan ta cire
layu da gurayenta na tsafi ta dora su a kan wani
gini mai tudu. Nan fa kowacce a cikinsu ta
dunkule hannayenta suka gyara tsayuwa suka
kama tsuma, kawai sai suka tugo da gudu suka
ruguntsume da azababben fada, Ko dakika
goma ba a yi ba ido ya raina fata, domin nan
take Yaldisa ta gane kuskurenta ta san cewa
ruwa ba sa'an kwando ba ne, domin Zubaina ce
ta rinka hada mata naushi ba kakkautawa, cikin
bakin zafin nama. Tun Yaldisa na iya karewa har
ta kasa, nan da nan Zubaina ta rinka gabzarta,
kafin a jima ta fasa ma ta hanci da baki kuma ta
kumbura ma ta idanuwa. Tun Yaldisa na tsaye
sai da ta fara ja da baya tana layi amma saboda
juriya gami da taruin rai ba ta fasa kokarin kai
hari ba. Cikin fusata Zubaina ta kutufi Yaldisa a
346
TASKARNOVELS.COM.NG
ciki. Take cikin Yaldisa ya kulle ta rankwafa
kasa, ai kuwa sai Zubaina ta dage iya karfinta ta
yi mata wawan dundu a gadon baya. Kawai sai
Yaldisa ta kife kasa da rub da ciki ta kama
amana jini a cikin wani irin mugun yanayi har ta
kasa mikewa. Koda ganin haka sai Sarauniya
Zubaina ta kama kyalkyala dariyar mugunta ta
zo kan Yaldisa ta raba kafafunta sannan ta
kama gashin kanta ta fisgo baya. Yaldisa ta
kwarara ihu sakamakon tsananin zafi da zugin
da ta ji tamkar wuyanta zai karya. Zubaina ta
tofa Yaldisa yawu a fuska ta ce, Karyarki ta sha
karya ya ke 'yar talakawa. Hakika kin yi babban
kuskure da kika bijire mini kuma zuciyarki ta
yaudare ki da cewar za ki iya daukar fansa a
kaina. Yarinya tun kafin ki zo duniya na sami
gadon jarumtaka domin a nono na sha ta, ba
taka haye na yi ba, gado ne. Kafin Zubaina ta
gama rufe bakinta sai kawai ta ji Yaldisa ta doko
bayanta da kafarta guda. Saboda karfin dukan
sai da Sarauniya Zubaina ta yi tsalle can gaba ta
fado kasa bakinta ya gurzu da kasa ya fashe.
Kafin ta yunkura ta mike tsaye tuni Yaldisa ta
riga ta mikewa ta daka tsalle izuwa kan wannan
tudun gini inda Zubaina ta ajiye gurayenta da
347
TASKARNOVELS.COM.NG
layunta na tsafi. Cikin tsananin zafin nama da
hanzari Yaldisa ta suri layun ta daurasu a
wuyanta da hannayenta kuma ta daura gurayen
a kugunta. Faruwar hakan ke da wuya Yaldisa ta
ji wani irin gagarumin karfi ya shige ta. Koda
ganin abin da ya faru sai Sarauniya Zubaina ta
durkusa kasa bisa guiwoyinta ta shiga rokon
Yaldisa tana cewa, ya ke Yaldisa ki gaggauta
cire waďannan layu da guraye daga jıkınki in ba
haka ba kuwa komai da kowa da ke cikin gidan
nan zai narke yanzu take ya zama ruwa. Koda
jin haka sai Yaldisa ta sa hannu ta share jinin da
ke bakinta sannan ta bushe da dariyar farin ciki
ta ce, ya ke wannan tsohuwar azzaluma, ke ma
kin sani cewa babu abin da za ki gaya mini na
yarda da shi. kuma ke ma kin san na san cewa
kin fi ni Karfin dantse da jarumtaka nesa ba
kusa ba. kawai na yi ganganci ne na tare ki
domin na yaudare ki na sami nasarar raba ki da
layun sihirinki, sai ga shi kuma gangancin da na
yi ya yi min rana na sami dacewa. Yanzun nan
zan hallaka ki domin na dauki fansa ta tsawon
shekara da shekaru. Kafin Yaldisa ta gama
rufe bakinta sai Zubaina ta yunkura cikin
shammace da zafin nama ta juya da baya guje
348
TASKARNOVELS.COM.NG
domin ta gudu, ai kuwa sai Yaldisa ta yi nuni da
hannunta izuwa kanta, take wata irin iska mai
karfi ta daga ta sama ta rinka gwarata a jikin
gini. Kafin a jima duk gabobin jıkınta sun
kakkarye kuma jikinta ya farfashe ko ina jini ne
ke zuba. Sai da Yaldisa ta ga Zubaina ta daina
motsi ko kadan babu alamar rai a jikinta sannan
ta sauke hannunta ta zo kan gawar ta dube ta
da kyau ta tabbatar da gawar ce sannan ta ruga
da gudu izuwa cikin gidan Sarautar tana neman
Jarumi Shaddadu tana kwalla masa kira.
**********
********** A can bangaren
jarumi Shaddadu da jaruma Ziya'ul Hak kuwa,
fadansu yayi tsamari ainun ya zama abin tsoro
domin ta kai cewa kowannensu bai san sa'adda
makaminsa ya subuce daga hannunsa ba don
haka sai suka ci gaba da gabzawq juna naushi
da bugu hannu da kafa. Wani lokacin har gwara
fuskokinsu suke sai dai kaga sun zube kasa
magashiyan kamar sumammu. Daga can kuma
sai kaga sun mike sunyi gaba da kwarmazuwa
da kokawa. Su fada nan su wulkila can. A haka
ne suka ringa hawa kan wata matattakala
wacce ta kai su har can saman wani gini mai
tsawo gaske suka ci gaba da bugun juna Suna
349
TASKARNOVELS.COM.NG
cikin haka ne kafar Ziya'ul Hak ta gurde ta
subuto daga kan wannan gini mai tsawon gaske
zata fado kasa, har ta kwalla ihu saboda
tsananin razana sai kawai taji an cafo hannunta
tana reto a kasa koda tadago kai ta ga wanda ya
cafo hannun nata sai ta cika da tsananin
mamaki. Ba wani bane face abokin fadanta
jarumi Shadaddu . Kawai sai taga ya kura mata
idanu hawaye na zubo masa ya kasa sakin
hannunta ta fado kasa ta mutu. Cikin tsananin
mamaki ta dubeshi tace, ya kai abokin gaba
meyasa ka ceci rayuwata yanzu alhalin tun dazu
kake neman damar dazaka hallakani baka
samu ba? Sa,adda jarumi shaddadu yaji
wannan tambaya sai hawayensa ya digo akan
kumatun Ziya,ul Hak yace, yake ma,abociyar
kyawu da kwarjini, kiyi sani cewa tun a lokacin
da wannan fada namu yai tsamari naga muna
neman muyi RAGAS naji nadama ta shigeni ba
don komai ba sai don da na tuna cewa nifa
yanzu a duniya banda uwata bani da sauran dan
uwa ko dangi a doron kasa face ke tunda kin
kasance ya a wajen mahaifi na. Take a lokacin
naji sonki ya mamaye zuciyata amma sai na
kudurce a raina cewar da dai na kasheki gwara
350
TASKARNOVELS.COM.NG
muyi MUTUWAR KASKO. Wato mu mutu tare na
huta da takaici ko bakin cikin tunanin na kashe
yar uwata da hannuna. Yanzu kuma dana ga ke
ki mutu ki barni sai naga ba zan iya hakura ba
shi ya sa na ceci rayuwar taki na dagoki sama
izuwa kan wannan gini dana ke kwance a kai ko
kuma nima na biyoki kasa mu mutu tare kinga
shike nan mun kawo karshen gabar iyayenmu.
Lokacin da jarumi Shaddadu yazo nan a
zancensa nan take itama taji ta cika da tsananin
mamaki nan take itama taji ta kamu da tsananin
kaunarsa a matsayin dan uwanta na jini. Ba ta
san sa'adda hawaye ya zubo mata ba. A dai dai
wannan lokacine Sharlis ta iso daf da su bisa
Tsuntsuwan tsafi sannan kuma sai ga sarki
laffaru da matarsa Ramlatul Siyam bisa Aljani
Maruful Dauwaz sun bayyana an sa Shaddadu a
tsakiya ana kallon kallo. Gaba dayan jikin
Sharlis sai ya kama tsuma tana kallon danta
wanda ke rike da Ziya'ul Hak tana daka masa
harara kuma tana hararar Sarki Laffaru. Shima
sarki laffaru yana hararar Ziya'ul hak kuma yana
hararar Sharlis jikinsa na tsuma. Daga can sai
sharlis ta dakawa Shadaddu tsawa tace,
Saboda me zaka ceci rayuwar yar babban
351
TASKARNOVELS.COM.NG
makiyina a duniya. Maza ka saki hannunta ta
fado kasan wannan gini mai tsawo ta hallaka.
Kafin ta gama rufe bakinta tuni shima sarki
Laffaru ya dakawa Ziya'ul hak tsawa yace da ita.
Me kike jira da dan babbar abokiyar gabata? Ga
wuka nan a kugunki na hagu maza ki zareta ki
caka masa a kirji. Bisa mamaki sai Sharlis da
Laffaru suka ga yayan nasu sun yi buris da
umarninsu kawai suna kallon junansu suna
murmushi. Duk tsawon wannan lokaci
Shaddadu bai gaji da rike hannun Ziya'ul Hak ba
tana reto a sama. Shaddadu ya dubi
mahaifiyarsa yace, Yake Ummina kiyi sani cewa
ni yanzu bazan iya kashe Ziya'ul Hak ba domin
ina kallonta a matsayin yar uwata ta jini guda jal
a duniya. Tabbas bai kamata ace gabarku ta
shafemu ba. Yau dai gaki kuma ga abokin
gabarku saiku rabawa kanku gardama. Idan har
ya zama dole sai mun tayaku yin wannan gaba
to ni na zabi na mutu tare da yar uwata inyaso
ku mu barku a duniyar kuci gaba da gabarku.
Kafin Shaddadu ya gama rufe bakinsa sai itama
Ziya,ul Hak ta dago kai ta dubi Sarki laffaru da
mahaifiyarta Ramlatul Siyam a lokacin da
hawaye ke zubo mata tace, Yaku iyayena kuyi
352
TASKARNOVELS.COM.NG
sani cewa nima yanzu na gane kuskurena da
kuka cusq mini gabar dan uwana a zuciyata
tsawon shekara da shekaru kuma a halin yanzu
babu abinda nake kauna sama da shi a zuciyata
don haka nima nazabi na mutu tare da shi.
Tana gama fadin hakan sai ta dubi Shaddadu
tayi masa wani irin murmushi mai nuna tsantsar
so da kauna tace , Ya kai dan uwana idan har
son da kake yi mini na gaskiyane to kazo mu
hallaka kanmu yanzu take domin mutuwar mu
ce kadai zata kawo karshen wannan tsohuwar
gabar tw iyayenmu. Nan take Shaddadu ya
dago kaivya dubi mahaifiyarsa Sharlis a lokacin
da hawaye ya zubo masa yace, ki gafarceni yake
mahaitiyata wannan shi ne kallon karshe da zan
yi miki a duniya. Tabbas ba zan bi zancenki ba
sai dai nabi zancen yar'uwata. Yana gama fadin
hakan sai ya fado kasa dagga kan ginin ea yake
kwance, shi da Ziya,ul Hak suka sallamo izuwa
can kasan wannan gini mai tsawon gaske. Akan
wadansu cako cakon karafuna suka fado suka
tsire, ko shurawa dayansu bai yi ba. Koda ganin
abin da ya faru sai Sarki laffaru da Sharlis suka
kwarara uban ihu a lokaci guda kuma suka
fashe da matsanaicin kuka na bakin ciki. Ita
353
TASKARNOVELS.COM.NG
kuwa Ramlatul Siyam saboda tsananin bakun
cikin ganin mutuwar yarta a gaban idanunta nan
take ta hadiyi zuciya ta bingire kaea matacciya.
Aljani Maruful Dauwaz kuwa, kasa ya sauko yai
watsi da su Sarki Laffaru ya kama birgimq da ihu
yana matsanaicin kuka saboda ganin
mutuwarnZiya,ul Hak. Bai san sa,adda
yabkama sambatu ba yana mai cewa,
Rayuwata bata da sauran amfani a doron kasa
tunda na rasa mai kama
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 18