Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki kuma hankain su ya dugunzuma sabo da burin da suke son cikawa tsawon shekara da shekaru ya rushe alhalin wannan ce kadai damar da suke da ita da zasu kawr da bakin zalunci da aka dade ana yi musu a nahiyar: a wanna lok Icin fadar tacika makil da mutanen gari da duk inda mutum ya duba sai dai yaga kawunnan bil adama rututu ako ina babu masakar sinke. ba komai ne ya janyo wannan cikowa ba face mutane sun ji cewar gimbiya hursiya ce kadai ta dawo daga can baki kogin bahar safiya don haka kowa yana son yaji halin da yan uwansa ke ciki wadanda suka tafi yaki. Bayan Gimbiya Hursiya ta zauna akan wannan kujera wadda ta saba zama akai sai aka buga mata tamburan sarauta gami da bushin algaita don girmamawa a gareta bisa matsayinta na kanwar sarki. Ana gama buga tamburan ne gimbiya hursiya ta mike ta fuskacin jamaar gari tace ua ku jamaata ina 47 TASKARNOVELS.COM.NG mai sanar da ku cewar wannan yaki da muka fita mun fita akan saa da nasara domin kuwa na baro jamaarmu suna ragargazar jama ar sarki maharaz doin haka akwai cikakakiyar alama tacewar mune zamu ci wannan yaki. Koda gimbiya Hursiya tazo nan a zncenta sai fadar ta rude da shewar mutane jama a su cika da dumbin farin ciki kuma suka sami kwanciyar hankali ba komai ne ke damub mutne ba facw tunanin yan uwansu wadanda aka tafi da su yakin suna ga nin cewa ba lallai bane su dawo ba amma jin cewar sune kesamu nasara a yakin sai suka sami nutsuwa sun san cewa da yawan jama'arsu za su dawo a raye. haka gimbiya Hursiya ta cigaba da kwantar musu da hakalin jama a cikin kalami na kara kwarin guiwar har suka sami cikakkiyar nutuswa da fahimta: a sannan ne ta sallami kowa a fadar ta watse kowa ya kama gabansa. * * * * lokacin da yan majalisar suka fice daga cikin fadar sai suka kewaye daya bayan daya a sirrince suka hadu acan gidan waziri sarki dujalu wanda ake kira MAZARUB IBINI HALSHAM kuma basu taru ba sai da dare ya raba saada gari yayi tsit ba a 48 TASKARNOVELS.COM.NG jin sauti komai face kukan tsuntsaye da nakarnuka. Zan ci gaba. MAZAN JIYA Littafi na Hudu 4 Part E Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey A cin wani babban falo na waxiri mazarub suka hadu, hatta barori da bayi na gidan a wannna rana tsaresu aka yi a wani daki dabam don kada su gazuwan yan majalisar ko su ji abinda zasu tatauna, dakarun dake tsaron gidan ne kawai suke kai kawo wadanda suka kasance aminatattun waziri mazarub : Bayan kowa ya gama hallara a cikin wannan falo sai aka janyo kofofi da tagogin falon aka rufee sannan wziri maharab yai gyaran murya ya kalli yan majalisar mutu tara shine cikon na 49 TASKARNOVELS.COM.NG goman wadanda gaba dayansu sun kasance dattijai babu dan kasa da shekara hamsin da biyar a cikinsu: waziri marzub yace yaku yan majalisa kun sani cewa shekara da shekaru tun zamanin mahaifin sarki dujalu muke fama da kunci bakin ciki gami da takaici bisa irin mulkin zalunci da ake yi mana babu sasauci ga basarke attajiri ko talakan gari: Gaba daya kasashen dake wannan nahiya a karkashin ikon sarki dujalu suke sai abinda yace shi akeyi: Yafi kowa dukiya karfi tsafi da karfin dantse amma dik da haka ya raina wanan baiwa daya samu kuma so yake ya mallaki duniya nan gaba danyata;; Shin haka za mu cigaba da zuba ido muyi ta zama a matsayin bayinsa yayanmu da jikokinmu ma su cigaba da yi masa bauta har abadan abidina, kuyi sani cewa mune makasantansa amma bai san darajarmu da kimanmuba, to ko mutuwa yayi haka yar uwarsa gimbiya Hursiya zata ci gaba da azabtar damu. Tunda yanzu sarki dujalu yana can sassann yakin da yafi kowanne yaki 50 TASKARNOVELS.COM.NG hadari a rayuwarsa mun sami dsmar da zamu kawo karshen bakin cikinmu Yanzu gashi yar uwarsa ta dawo tace wai mune muke samun nasara a wanna yaki ta yaya zamu iya tabbatar da cewa abin data fadi gaskiya ne: kumas ta ya ya zamu iya cimma burinmu mu yar da kwallon mangwaro mu huta da kuda? Sa adda waziri mazarub yazo nan a zancensa sai falon yayi tsit Tamkar mutuwa ce ta gifta gaba dayan suka kama muzurai suna kallon junansu aka rasa wanda zai ce kala daga can sai wani tsohon mafi shekaru a cikinsu wanda ya kasancve dan wada wanda tsawonsa bai wucce kamu shida ba mai suna SADUSA ya mike tsaye yana mai gyaran murya: Nan fa kowa ya Uba masa idanu: sadusa yai murmushi sannan ya shafi dogon gemunsa wanda ya sauko har kasan cikinsa yace yaku yan uwana yan majalisa ku yi sani cewa ga dade ina jiran zuwan wannan rana har mana fidda tsammanin zuwanta ama sai gashi tazo 51 TASKARNOVELS.COM.NG ina so ku sani cewa a duk fadin kasar nan da nahiyar nan bani da wani makiyi wanda yafi sarki dujalu domin a sanadinsa ne na rasa iyayena iyalina da dukkan dangina: A yanzu haka ni kadai ne na rage daga cikoin zuri armu hakam ya samo asali ne akan wani laifi da zuri armu tayi masa yasa aka rinka kamosu daya bayan daya ana yi musu yankan rago : A wannan lokaci ni bana wannan nahiyar na bazama cikin duniya neman ilmin tsafi: Ban dawo ba sai bayan sarki dujalu ya gama kashe gaba dayan zuri ar tamu gidamu mana iskeshi a kone kurmus ko tsinke guda daya ban samu ba, a bakin wani makofcinmu na sami lbrin abinda ya faru ga zuri ata gaba daya: Nan take zuciyata ta kama tafarfasa kamar zata kone sbda fishi 52 TASKARNOVELS.COM.NG Nan fa wannan makoci nawa ya shiga rarrashina yana mai bani shawarar na hanzarta na bar garin nan domin idan sarki dujalu ya sami lbr cewa ina dsga cikin zuri ar da suka yi masa wannan laifi tabbas kashe ni zai yi. A wannan lokaci ina ta faman rusa kukane na bakin ciki amma ko danaji wananan makofci nawa yace wai sarki zai sa a kasheni: Sai na bushe da dariyar takama na ce ai na wuce wannan matsayi: Kai dai kawai ka zuba ido ka sha kallo: Ba komai ne yasana yarda da kaina ba sai bisa tarin dumbin ilimin da na samo na tsafi don haka ina ganin cewa zan iya kare kaina daga dukkan masifa: Nan take na mike tsaye na yiwa makobcin nawa sallama sannan na bude jakata na debo dukkan gurayena da layu na tsafi na daddaurasu a jikina: Bayan na kammala shiri sai na durfafi fadae sarki dujalu kai tsaye ba tare da fargabar komai ba: Lokacin da na isa fadar sarki dujalu sai na isketa a cike makil da fadawansa da ;mutanen gari ana tafiyar da harkokin mulki, duk da cewar fadar cike take da dajaru a ko ina masu kwarjini da banTsoro amma ni dai ko gezau banyi ba na cigaba da tunkarar inda karagar sarki take:; Su 53 TASKARNOVELS.COM.NG kansu dakaru da zarar sun ganni sai ka ga suna buda mini hanya ina wucewa: koda sarki dujalu ya hangoni na durfafo inda yake zaune sai ya kura mini ido kawai yana sauraron isowata: kafin mutum ya isa inda aka ajiye karagar mulkin sarki dujalu akwai wadansu dardumai guda uku da aka shimfida kala uku: fara baka da ja: tunda sarki dujalu ya hau kan mulki aka shimfida wadannan dardumai amma ba a taba ganin ranar da wani mahaluki ya taba isa inda dardumai farko take ba wato wannan farar darduma ya take ba bare har ya taka ta biyu da ta ukun komai matsayin mutum komai jarumtakarsa da karfin sihirinsa ma baya iya zuwa ya taka wannan darduma ta farko Kawai sai na cigaba da tafiya ina durfafar sarki dujalu: A lokacin ne gaba dayan mutane dake fadar suka cika da mamakina kuma suka zubo mana idanu nida sarki dujalu domin su ga abinda zai faru: Saboda ba a taba ganin wanda yashigo fada ba a haka babu iso kuma babu sallama sannan kuma gashi ya durfafi inda 54 TASKARNOVELS.COM.NG sarki ke zaune an rasa badakare daya da zai tsayar dani Haka dai na cigaba da tafiya har na sami nasarar taka durduna ta farko: Al:amarin da yai matukar baiwa kowa mamki kenan: Shi kansa sarki Dujalu sai da Gyara zama Yana mai Al ajabina: Na ci gaba da tafiya sai gashi na taka darduma na biyu Kawai sai aka ga sarki dujalu ya mike tsaye ya zare takobinsa jikinsa ya kama tsuma har fuskarsa yana yi gatsine: Nima Sai na zare waya adda wacce ta fini tsawo tana sheki gami da wani irin walwali na tsafi Na cigaba da tafiya da nufin na taka darduma ta uku wacce ta kasance ja: Koda na iso karshen darduma ta biyu sai na kasa daga kafata na cigaba da tafiya: Nan fa na shiga karanta wadansu dalasimai na tsafi domin na 55 TASKARNOVELS.COM.NG wuce gaba amma sai nakasa; koda ganin abinda ya faru sai sarki dujalu ya bushe da dariyar farin ciki; lokacin guda kumkuma ya turbune fuska ya dubeni yace lale marhaban da sadusa ibn zaiyar T@bbas ban ga laifinka ba da kake kokarin kasheni tunda nine na kashe iyalinka danginka da duk zuri arka: A rayuwarta ban taba zaton cewa akwai mahalukin da ya sami sihirin tsafin dake daf da nawa ba tabbas na san cewa kasha bakar wahala kafin ka sami sihirin tsafin da kake da shi a yanzu samun kmarka a doron kasa a yanzu sai an sha wuya: Bisa wannan dalilin ba zan kashe kaba duk da cewar ya kamata na kasheka din sbda na san cewa ka tsaneni fiye da yadda ka tsani mutuwarka: zan kyaleka kuma daga yau ka zama dan majalisata amma busa sharadi guda daya; Sharadin kuwa shine idan har kayi wani yunkuri na cutar dani zan yi maka daurin rai da rai a kurkuku inda zaka karasa sauran rayuwarka ta duniya. Sa'adda tsoho Sadusa yazo nan a lbrinsa kowa yayi ajiyar zuciya a cikin falon sannan sadusa ya cigaba da bayani yace yanzu abinda ya kamata mu fara yi shine mu tabbatar da gaskiyar lbrin da gimbiya 56 TASKARNOVELS.COM.NG Hursiya tazo mana da shi: SHIN gaskiya ne mu muke samun nasara? Babu wata hanya da zamu iya sanin hakan face mu tashi aljni mai tsananin karfin gudun da zai iya zuwa bakin kogin Bahar Sufiya koda a cikin kwana bakwai ne yaje ya gano mana zahiri Al;amarin: Idan har su sarki maharaz ne ke samun nasara to tabbas akwai tuggun da zan iya shiryawa mu yiwa sarki dujalu juyin mulki yadda ba zai taba iya karba karagarsa bA: Amma fa idan mune muke samun nasara a filin yakin sai dai mu rungume kaddara mu cigaba da zaman hkri har ixuwa sa;adda ajali sarki dujalu zaizo: yanzu babbar matsalar ita ce gaba dayan aljanun dake wannan nahiryar tamu sarki dujalu ya tafi da su wannan yaki saura matansu tsofaffi da yaransu wadanda baza su iya wanan Aki ba: Sarauyin aljani mai tashen samartaka da kafin gudu data be ya rage a yanxu kua ba wani bane face aljani barzuri wanda yadawo da Gimbiya Hursiya daga CAN bakin Tekun Bahar sufiya: Barzaru ya kasance amintaccen sarki dujalu na gani kasheni don haka bazai taba yarda yayi mana wannan aiki ba sai dai maya tona mana asiri: Ya zama wajibi nayi shiti da kaina na bar 57 TASKARNOVELS.COM.NG wannan nahiya tamu na tafi nean aljanin dazai yi ana wannan aiki a cikin gaggawa. Sa'ad da sadusa yazo nan a zancensa sai hankalin kowa ya kara dugunzuma domin suna ganin cewa ai babu isasshen lokacin da za ayi wannan aiki: Cikin alamun tsananin damuwa waziri ya dubi sadusa yace yanzu a cikin kwana nawa kake ganin za ka iya zuwa kasamo aljanin da zai yi mana wannan aiki? Sadusa yai murmushi yace ku bani kwana uku rak Ai Al mari ne na tsafi: Koda jin haka sai farin ciki ya lullbe waziri da sauran yan majalisar: Nan take suka salami sadusa akan cewa za su jira dawowarsa nan da cikar kwana uku: Nan dai taro ya watse kowa ya sulale ya tafi gidabsa cikin wannan dare: * * * AL AMARIN Gimbiya Hursiya kuwa; tun sa;adda fada ta watse ta shige cikin gidan sarautar sai ta wuce izuwa cikin turakarta ta zauna a gefe gadonta ta shiga tunani mai zurfi. A dai dai wanan lokaco ne wata kuyagarta mai suna laziramat ta shigo cikin turakar dauke da farantin shayi: shi dai wannan shayi na ka:ida domin kullum sai lazimat ta dauko butar shayin ta tsiyaya a cikin wani dan karamin kofi na lu u lu u ta kaiwa Gimbiya Hursiya: Koda ta mikawa 58 TASKARNOVELS.COM.NG Gimbiya kofin shayin sai ga ashe Gimbiya kuka take yi hawaye na ta sartu kan kumatuwanta: Al amarin da yai matukar dugunzuma hankalin lazimat ke nan dubeta cikin tsananin damuwa ba mai ajiye kofin shayin akan faranti ta ce ya shugabata ki yafeni idan nayi miki wani abu wanda ya bata miki rai: koda jin wannan batu saI Gimbiya Hursiya ta sa hannu ta share hawayenta sannan tace ya lazimat kiyi sanicewa a iya zamana dake Tsawon shekaru baki taba yi mini wani abu ba wanda ya bata min rai Wannan hawaye nawa dakika gayana zuba bana komai bane face na tsananin bakin ciki bisa karyar dana yiwa mutanen garin nan a yau a fada: Maganar gaskiya ban san abinda ya faru ba a filin yaki domin ana daf da fara yakin ne sarki shammaceni yasa aljani barzaru ya sureni yai sama da ni kafin na ankara ya luluka dani izuwa cikin gajimare: Cikin abinda bai wucce kwanaki tara ba muka iso nan gida, ni yanzu babban abin bakin cikina shi ne idan sarki ya mutu bana son na gajesgi kuma yazama duniya 59 TASKARNOVELS.COM.NG babu wani mutum dana shaku da shi sai shi; Mene ne amfanin naci gaba da rayuwa a duniya bani da masoyi? Mulki daula da arziki duk shire ne a wannan duniya idan babu masoyi: Soyayya itace abar da take kawar da dukkan takaici da bakin cikin rayuwa: koda Gimmbiya Hursiya tazo nan a zanceta sai kunyaga lazimat takamu datsananin tausayinta har itama kwalla ya cika mata idanu ta dubeta tace ya shugabata to yanzu ke wanne irin hukunci kika yankewa rayuwarki? Hursiya ta ajiyar zuciya sannan tace ni yanzu bana bukatar koai face na koma can bakin kogin Bahar Sufiya domin naga yadda karshen wannan yaki zai kasance idan har sarki mutuwa zai yi to zanso na mutu tare da shi amma bana son ace sarki ya mutu ni nacigaba da sarauta anan sbda basan cewa kamar yadda mutne ke kin sarki haka nima zasukini: Nasani cewa dan uwana Azzalumi ne tsawon shekara da shekaru mutanen dake nahiryar nan basa jin dadi mulkinmu tun iyaye da kakani, kin sani cewa nima bana son irin wannan mulki da sarki ke yiwa jamaa amma ban isa na hanashe ba don haka ciwon ido sai hkri: Ni ina ganin cewa zai fi kyau ni da sarki duk 60 TASKARNOVELS.COM.NG mu mutu a wajen wannan yaki domin a sami sabo shugabanci a wannan nahiya mutane su huta da mulkin zalunci a sami na sauyin rayuwa mai dadi: Koda Hursiya tazo nan azancenta sai ta fashe da kuka Al amarin da ya kara jefa kunyaga lazimat cikin tsananin tsananin tausayinta kenan ta rungumeta ta na mai rarrashinta har tadaina kukan sannan ta ja jikunta daga cikin na tata debeta tace; Ya shugabata kiyi sani cewa a iyarayuwata ta duniya ban taba zama da basarake mai tunani da sani yakamata ba kamarki wanda yake da jin kai gama son talakawansa tunda gashi kin zabi ki mutu don kawai takawa su sami rayuwa mai dadi:Ya shugabata kiyi sani cewa rashinki a doron kasa ba karamar asara ba ce domin samun mace mai kyau da kyan hali irin naki sai an tona: Ya kamata a ce kin sami saurayi kyakkyawa kuma mai kyawun hali irin na ki domin yazma abkin rayuwarki ku haifawa baya abinda zasu amfanesu; yayin da Gimbiya Hursiya taji wannan sai murmushi ya subuce mata tace ai niban yaba yin soyayya ba kiuma ban zaton zanyi ta anan gaba har izuwa karshen rayuwata ban san maye SO ba: Tun ban taba 61 TASKARNOVELS.COM.NG kamani ba: KAUNA kawai na sani irin wacce ke tsakanina da dan uwana sarki dujalu da kuma mutane ire irenku wadanda nayi sabo da su sanadiyar zamantakewa;lokacin da Gimbiya hursiya tazo nan a zanceta sai itaa kuyanga lazimat Tayi murmushi tace ya shugabata kada kiyi kuri ko cika baki akan SOYAYYYA Domin kuwa shI SO abu ne wanda baya sallama bare ayi masa iso a duk yayin da yaga zuciya yake nean shiga cikinta Karfin gudunsa ya wuce na iska ko guguwa haka kuma DAFIN SO yafi na kibiya: A duk sa:adda ya soki mutum to fa babu wani magani da zai warka dashi face kasancewa tare da masoyinsa Dajin wannan batu sai Hursiya ta bushe da dariya sannan ta dauki wannan kofin shayi ta kurba sau uku tace daga yau mun kulla gasa nidake na ga wanda zai lashe gasar: Ni Hursiya na cika miki baki cewar KIBIYAR SO ba ta isa ta 62 TASKARNOVELS.COM.NG huda jikina ba bare ta samini dafin da zan rasa maganinsa Duk ranar da kika lashe wnnan gasa in dai ina raye nayi alkawari zan yantaki kuma zan baki dukiya mai yanwa gaske: Koda jin wannan batu sai kuyanga lazimat ta kamu da tsananin farin ciki tace tabbas zamu bambance tsakanin aya da tsakuwa kuma lokacin ne zai raba wannan gardaa dake tsakaninmu Hursiya ta yi ajiyar dogon numfashi a lokacin data ajiye wannan kofin shayi sannan ta kurawa lazimat idanu tace yanzu wacce hanya kike ganin zan bina sami damar komawa sansanin yakin nan a cikin yan kwanaki kadan kafin yakin yakare? Zan ci gaba. MAZAN JIYA Littafi na Hudu 4 Part G Na Abdulaziz Sani m gini 63 TASKARNOVELS.COM.NG Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Yayin da lazimat taji wannan tambaya sai hankalinta ya dugunzuma tayi shiru tana tunanun har izuwa tsawon wadansu yan dakiku kamar ba zatace komai ba. Daga can sai ta kawo gwauron numfashi ta aje sannan tace ya Shuganta akan bukatarki ta biya zan iya sallaa raina da jikina sbda kauna da aminci dake tsakaninmu don haka ki bani kwana biyu rak zan je na biwata hanya wucce nake gani cewa zata kaimu ga nasara Koda jin haka sai gimbiya Hursiya takamu da tsananin farin ciki nan take ta bude wata farar akwati ta debo dinare da yawa batare da sanin adadinsa ba cikin tafin hannunta ta mikawa lazimat tace ungo wannan ki tafi da shi sbda nasan cewa yanzu aiki wannan zamani babu wani wani aiki da yake tafiya ba tare da kudi ba: Lazimat tacce haba ya shugabata ai wannan kudn yayi yawa: Hursiya ta kada kai tace ai girman wannan aiki da nabaki yafi wannan 64 TASKARNOVELS.COM.NG dinare cikin turakar nan tawa duka: Hadarinsa kuwa dai dai yake da mutum ya sayi ajalinsa inda zan baki dukiya cikin gidan sarautar nan gaba daya ban biyaki ladan wannan aiki ba: Ki tashi ki tafi na sallameki sai nan da kwana biyu ki dawo mini da jawabi mai dadi sai ki wakilta wata daga cikin sauran kuyangina ta cigaba da yin irin aikin da kika saba yimini Amma lallai ki sami mai amana wacce zata iya rike sirrina: kunyanga lazimat ta risina cikin biyayya tace angama ya shugabata : WANNAN SHINE ABIN DA YAFARU A BIRNIN SARKI DUJALU BAYAN ALJANI BARZARU YA DAWO DA GIMBIYA HURSIYA DAGA BAKIN TEKUN BAHAR SUFIYA INDA AKE SHIRIN FAFATA YAKI TSAKANIN RUNDUNARSU DATA SARKI MAHARAZ : * * * ACAN Sansanin yaki kuwa awana na ukun da akayi ana hutun yaki kullum inmal da sarki mahazar suna zaune a gaban kabarin 65 TASKARNOVELS.COM.NG sarki yaki Hibru suna kuka dare da rana: Abinci a da kyar suke cin kadan idan Gimbiya Mulaifa ta matsa musu tana mai yi musu tuni da cewar idan fa basu ci abinci ba to fa bazasu sami damar cigaba da yakin ba tunda bazasu samu kuzari ba ajikinsu Wannan batu ne yasa suke daurewa su ci abinci kadan bayadda zasu koshi ba: A ranar dare na biyu ne sarki maharaaz inmal da sauran manyan daraunsu na Yaki suka zauna domin su tattauna akan yadda zasu bullowa wannan yaki a wannan karo na uku domin su sami nasara akan abokan gaba cikin kankanin lokaci: Wani barde da ake kira shamal shine ya fara magana yana mai duban sarki maharaz yace ya shugabana shawara ta ta farko dazna bayar ita ce kamata yayi ana fara wannan yaki inmal tare da manyan jarimanmu masu jarumtakar gaske su yiwa sarki dujalu rubdugu domin a kashe shi da wurin tabbas idan muka sami nasarar kashe sarki dujalu mun karya logon abkan gabarmu tunda a bangaren dakarunu na aljanu karfinsu yazo daidai da na 66 TASKARNOVELS.COM.NG dakarun aljanun su: koda jin wannan batu sai sarki maharaz ya dubi kowa yace ya ku dirkokin birnina kun ji shawarar da shamal ya kawo: Shin kun amince da ita ko kuwa akwai mai korafi akanta? Gaba dayansu sai suka yi shiru aka rasa wannan da zaice kala, sai inmal ne yai gyaran murya sannan ya ce ai ko kadan wannan shawarar da shamal ya kawo ba zata yi tasiri ba: dalilina na fadin haka shine masu iya magana sunce MASO ABINKA YAFI KA DABARA: kada ku manta cewa shi kansa srki dujalu zai yi irin wannan tunanin da shamal yayi don haka dole ne ya san dabarar da zaiyi yarufe wannan kofa: abu na biyu da nakeso da nake so ku gane shine: Dakarun yakinsa suna da bakin naci fiye da namu dakaru: Idan muka tattara hankalinu akan sarki dujalu kawai zasu sai damar daza suyiwa namu dakarun mumunar barna, kafin inmal ya gama rufe bakinsa tuni shamal ya tarin numfashinsa yace to wai shin kaanta ne cewar sarki dujalu ya zama masaki mai hannu daya: wannan lalura da ta same shi zata rage masa karfin da zafin nama: inmal ya girgiza kai ya ce ba haka bane ai kada mage ba yanka bane kuma ina so ka sancewa mazanjen kwarai suna 67 TASKARNOVELS.COM.NG yaki ne da zuciyarsu kafin jikinsu: Ma ana taurin zuciyarsu da karfinta yafi na hannayensu sbda haka wannan rashin hannu daya na sarki dujalu ba zai rage shi da komai ba face ma ya kara masa kuzari da mugun nufi akanmu: Sa adda inmal yazo nan a jawabinsa sai jikin kowa yayi sanyi aka yi shiru ana tunani : Jim kadan sai wani bardw shi KIMARU ya numfasa yana mai duban sarki maharazz yace ya Shugabana wai shi mezai hana goben da dazar an busa kohon ci gaba da yakin nan ka shammaci abkan gaba ka hallakasu da karfin sihirinka? Kafin kimaru yagama rufe bakinsa tuni sarki maharaz ya shara masa mari sbda karfin marin sai da kimaru ya tuntsure kasa ya mike zaune wuf, cikin firgici yana mai sunkui da kansa kas sauran dakarun kuwa duk sai suka firgita suka sunkuui da kawunansu kas don kada laifin wani ya shafesu. Sarki Maharaz ya dubi kimaru a fusace yace shin kai kurma ne a lokacin da nayi rantsuwa da sunan mai girma darbuza cewar ba zan yi amfani da karfin sihiri ba tun a farkon wannan yaki bisa yarjejiniyar da ke tsakaninmu 68 TASKARNOVELS.COM.NG da sarki dujalu? To ka sani cewa ni da sarki dujalu babu wandazai yi amfani da karfin sihiri har a gama wanna yaki tunda shima yayi rantsuwa da ubangijinu kamar yadda nayi: yanzu dai na fuskaci cewa gaba daynku babu, Wanda yake da wata dabara ko sabuwar hikima wacce zamu yi amfani da ita don ganin mun saminasara r wannan yaki. Abin da nakeso da ku kawa shine kowa yaje yayi shirin tunkarar wanannan yaki gobe idan aka fara yakin kowa yayi iya kokirinsa lallai sa a tana ga mai rabo walau garemu kukuma garesu. Koda gama wannan jawabi sai sarki maharaz ya mike tsaye ya tafi izuwa cikin tantinsa: a sannan ne su bardw kimaru a suka tashi suka tafi izuwa nasu tantunan aka bar sadauki inmal a zaune shi kadai a lokacin da yada cikin kogin tunani: A wannan lokaci wata irin iska mai sanyi ke kadawa: inmal na cikin wannan tunanin ne yaji an taba kafadarsa ta baya. Cikin dan alamun razana inmal ya waiga da sauri don a zatonsa aljanu ne keson tabashi, koda ya yi arba da wanda ke tsaye abayansa sai ya cika da mamaki ba wani bane face Gimbiya Mulaifa: Mulaifa da inmal suka yiwa juna murmushi 69 TASKARNOVELS.COM.NG sannan ta zauna a kusa da shi suka dubi gabas ba tare dayansu yace kala ba har izuwa tsawo yan dakiku. Inmal ne ya katse shirun yace menene ya hanaki yin barci har izuwa tsawon wannan dare? Mulaifa ta sake yin murmushi a karo n biyu sannan tace abinda ya hanaku yin barci kai da abbana shi ne ya hanani: Ya kai abin kaunata kayi sani cewa bamu taba tsintar kanmu a cikin halin bakin ciki irin na wannan lokaci ba sakamakon mutuwar mahafinka Sannan kuma bamu san yadda karshen wannan yaki zai kasance ba: Ni babban abin ma daya dugunxuma hankalina shine naga mahaifina jikinsa yayi sanyi gaba daya akwai alamar cewa bashi da sauran kuzari da sa ran samun nasara a wannan yaki: Koda jin wannan batu sai inmal yayi ajiyar zuciya ya ce ni kaina jikina yayi sanyi ba don komai ba sai sbda ina ginincewa karshen wannan yaki ba zai yi kyau ba: Za a yi asarar miliyoyin rayuka ko dai ayi ragas ko kuma ayi kare jini biri jini: Ni babban abinda yake damuna guda biyu ne: Abu na farki shine na tsaya nayi tunani na gano cewa damu 70 TASKARNOVELS.COM.NG da su sarki dujalu duk muna yin wannan yaki ne sbda son zuciya kawai kowanne bangare suna son su mallaki kayan yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya: Wannan duk al:amarin ne na zalunci: Ni ka zan fi son su mallaki kayan Yakin MAZAN JIYA don kawai su mulki duniya, wannan duk al amarin ne na zalunci: Ni ka zan fison na mallaki wadannan kayan yaki na MAZAN JIYA don kawai na bar abin tarihi na jarumtaka wanda baza ataba mantawa dani ba: Abu na biyu da yake damuna shi ne zuciyata tana rawa akan allolin da ake bautawa a wadannan nahiyoyo namu sbda na fuskanci cewar suna yin karya: Sau tari sukan fadi wani abun suce zai faru amma kuma sai aga sabanin haka: An ya kuwa ba kya ganin cewa akwai wani ubangijin wanda yafi dukkanninsu wanda shine ne mafi karfi da daukaka? Koda jin wannan tamabaya sai mulaifa tayi ajiyar zuciya sannan tace hakika duk abinda ka fada gaskiya ne kuma duk mai hankali dole ne yayi tunani akan hakan: To amma abinda nake so naki daga gareka shi ne shin kana da wata hujja ne mai karfi wacce tasa ka fadin hakan? Inmal yayi shiru yana mai daga kansa sama cikin alamun 71 TASKARNOVELS.COM.NG tunani sannan yace akwai wani lokaci a baya da marigayi mahaifina ya gaya mini cewa akwai wani ADDINI da ake kira ADDININ MUSULUNCI: YA tabbatar mini da cewa bai taba ganin mai karfinsa ba kuma yaji ajikinsa cewar shine addinin gaskiya sbda abinda ma abotansa suka sa a gaban koda jin wannan batu saijikin Gimbiya mulaifa yai sanyi tayi shiru har izuwa tsawon yan dakiku sannan tadubi inmal Inmal tace ni kaina yanzu naji a a cikin raina na gamsu da wannan addini domin ka karbi addininin mu sami taimakon ubangijinsa bisa wannan gagarumin yaki dake gabanmu: Inmal ya ja dogon numfashi yace hakika maganarki dutse ce amma tunda

Chapter 3 of 18