shirin
cake idonsa na hagu, koda Hasnalu ya goce sai
mashin ya wuce ta saman fuskarsa ya je ya
shige ta vikin wani katon dutse ya fice fit, kuma
ya dawo da baya da gudu ya yo kan Hasnalu.
Nan fa Hasnalu ya cigaba da yaki da wannan
mashi na galilur haras, shi kuwa aljani Raugatul
Agwanu sai ya tsaya cak yana kallon bakin
gumurzun da ake yi tsakanin mashin galilur
haras da kuma karumi Hasnalu ma'ana ya zama
dan kallo babu abinda Aljani Raugatul Agwanu
yake face kyalkkyala dariyar mugunta
musamman da yaga cewa mashin ya kuntata
Hasnalu. A daidai wannan lokaci ne su Imnal
suka farfado daga dogon suman da suka yi,
koda sukaga irin azababben yakin da ake yi
tsakanin mashin galilur haras da jarumi
Hasnalu sai suka cika da tsananin mamaki gami
da tsoro, domin basu taba ganin makami kamar
galilur haras wanda yake muguwar barna kamar
haka, barnar data ragargaza dajin gabadaya, ta
haddasa famtsamuwar narkakken dutse, b shiri
377
TASKARNOVELS.COM.NG
su jarumi Imnal suka mike suka ruga da gudu
izuwa can nesa kadan suka tsaya suna kallon
ikon Allah, domin idan suka tsaya inda ake
gumurzun narkakken ruwan dutsen ne zai dafar
da su. Sai da aka kara shafe wata sa'a guda ana
gumurzu tsakanin mashin galilur haras d jarumi
Hasnalu har takai cewa Hasnalu ya fara gajiya,
a lokacin ne kuma mashin ya kawo wa Hasnalu
mugun suka a ciki ya goce cikin matukar zafin
nama, amman duk da haka sai da mashin ya
huda rigarsa ya fice fit, take kuwa rigar ta kama
da wuta, cikin hanzari Hasnalu ya yaga rigar
tasa ya jefar fa ita, a lokacin ne kuma mashin ya
kara dawowa da baya ya saito kirjinsa zai
tsireshi, kawai sai su Imnal suka ga Hasnalu ya
mayar da takobinsa cikin kufe kuma ya runtse
idanunsa yana mai karanta wata addu'a.
Al'amarin da ya firgitasu kenan, gimbiya
Hursiyya ta kama kwala wa Hasnalu kira daga
inda suke labe cikin dimauta tana mai ce mashi
ya kauce kada mashin ya soke shi. Ko juyowa
ya dubeta Hasnalu baiyi ba, kuma sam babu
alamar tsoron wannan mashin a tare da shi.
Shiko aljani Raugatul Agwanu sai ya kama
kyalkyala dariyar mugunta saboda yana ganin
378
TASKARNOVELS.COM.NG
cewa tabbas wannan karon ajalin Hasnalu ya
zo, koda ya rage saura baifi kamu daya ba jal
tsakanin kirjin Hasnalu da mashin galilur haras
sai akaga mashin ya tsaya cak a sama, shi bai
gado kasa ba kum shi bai wuce ba, a sannan ne
jarumi Hasnalu ya bude idanunsa kawai sai ya
dafa mashin da hannunsa na dama take mashin
ya dagargaje kuma ya tarwatse yayi gutsugutsun kamar kwayar zarra. Koda ganin abinda
ya faru sai aljani Raugatul Agwanu ya kwarara
uban ihu cikin tsananin bakin ciki har kwallar
takaici ta zubo daga cikin idanunsa. Su kuwa su
sarki Maharaz koda ganin wannan nasara da
Hasnalu ya samu akan mashin galilur haras sai
suka kama kabbara gami da yiwa Allah godiya.
Nan fa aljani Raugatul Agwanu ya sake kwarara
uban ihu a karo na biyu, sannan cikin tsananin
fushi ya zare takobin Saiful Lujara ya afka wa
jarumi Hasnalu da dukkan karfinsa suka sake
kacamewa da azababben yaki. Wohoho!
Hakika wuya ba a sa mata rana, maza sune
maganin maza, kuma tabbas karfi yana da
ranarsa, haka ma kwarewa da sanin makama a
yaki tana da rana. Tabbas inba dan jarumi
Hasnalu ya kasance gwarzon mayaki ba wnda
379
TASKARNOVELS.COM.NG
ya saba gwagwarmaya tare da fafatawa a cikin
maza ba, kuma yana hadawa da neman tsari a
wajen Allah da tuni aljani Raugatul Agwanu yayi
masa kwab daya a wannan fafatawar da suka
fara, amman duk da haka sai da kai cewa aljani
Raugatul Agwanu ya zame masa alakakai, ya
rasa ta inda zai bullo masa, shima kuma Aljani
Raugatul Agwanu ya rasa hanyar da zai bi ya
samu nasara a kansa, sai gashi takobin tasa ta
Saiful Lujara da hular lamsara sun kasa tsinana
masa komai, a haka sai da suka shafe sa'a guda
suna wannan gumurzu. Kaico! Ance gobara
daga kogi maganinta sai Allah, ba shiri aljani
Raugatul Agwanu ya ja da baya ya tsaya yana
haki yana kum kallln jarumi Hasnalu cikin
tsananin al'ajabi, domin shi a rayuwarsa ma bai
taba gajiya a filin yaki ba dan yana iya kwana
arba'in yana yaki a filin daga cikin tsakiyar
miliyoyin abokan gaba, amman yau gashi
mutum daya jal ya gagareshi kuma ya gajiyar da
shi a cikin sa'a daya da rabi. Bayan anyi kallon
kallo tsakanin jarumi Hasnalu da aljani
Raugatul Agwanu na taawon dakika dari uku da
sittin, sai nan take hadari ya gangamo aka fara
wata Irin iska mai karfi amman hakan bata sa su
380
TASKARNOVELS.COM.NG
Imnal sun bar wanen da suke labe ba, saima
suka nemi mafaka suka labe, babban burinsu
kawai shine suga yadda karshen wannan fada
zai kasance. Nan take kuwa aka fara yayyafi
kadan-kadan yana mai sakkowa kasa, kawai sai
ljani Raugatul Agwanu ya cire hular lamsara ya
ajiyeta gefe guda, sannan kuma ya ajiye takobin
Saiful Lujara a kusa da hular, ya tada kwanjinsa
yayin da jijiyoyin jikinsa suka tashi suka yi
burdin-burdin nan fa kirarsa ta sadaukantaka ta
fito ainun, aiko sai ya takarkare ya kwarara uban
ihu mai tsananin firgitarwa, duk da irin
jarumtaka tasu Imnal sai da suka ji kamar su
arce da gudu, domin babu wanda bai motsa ba
harma da jan baya ba a cikinsu, duk da cewa
suna can baya nesa a matsayin yan kallo.
Shikuwa Jarumi Hasnalu ko gezau bai yi ba,
kawai shima sai ya gyara tsayuwa yana mai
dunkule hannunsa. Su zukatan su Imnal kuwa
cike suke da mamaki har suna tambayar
zukatansu cewa wai shin wacce irin dakakkiyar
zuciya jarumi Hasnalu ke da ita ne, ta yaya zai
tari wannan gansamemen sadaukin aljani yana
matsayin biladama. Aljani Raugatul Agwanu ya
dubi jarumi Hasnalu yace na ajiye dukkan
381
TASKARNOVELS.COM.NG
ababan dogaron nawa da dukkan tsafina, zan
yakeka da tsagwaron karfin damtsena, idan ka
sa kaima ka yakeni da tsagwaron karfin
damtsenka, kada kayi amfani da karfin
sihirinka. Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan
batu sai yayi murmushi sannan ya ce na yarda
xan yakeka da tsagwaron karfin damtsen da
ubangijin ya bani, kuma ina ka sani cewa ni bani
da wani sihiri face karfin ubangijina da yake
bani kariya daga dukkan sharrinku na aljanu...
Kafin jarumi Hasnalu ya gama rufe bakinsa tuni
aljani Raugatul Agwanu ya shammaceshi ya
daka tsalle sama yayi masa rotse fa gwiywar
hannunsa a ka, nan take Hasnalu ya sulale kasa
magashiyan mugun yananyi mai kama da suma
ko gushewar tunani. Nan fa hankalin su Imnal
ya dugunzuma ainun, kuma suka kamu da
tsananin tsoro, abinda ya basu mamaki shine
kamata yayi ace kan jarumi Hasnalu ya dgargaje
domin ko dutse aljani Raugatul Agwanu ya doka
da wannan gwiywar hannuntasa sai dutsen ya
farfashe, amman sai gashi babu abinda ya
samu Hasnalu, sai dai jini da yayi fitar burgu
daga cikin hancinsa gami da bakinsa. Nan take
Imnal ya yunkura zai falfala da gudu domin ya
382
TASKARNOVELS.COM.NG
kaiwa jarumi Hasnalu dauki, amman sai sarki
Maharaz yai caraf ya rikeshi tare da cewa ai
kada mage ba yanka bane tsaya dai muga
abinda zai faru. A wannan lokaci aljani Raugatul
Agwanu sai faman ihu yake gami da kuri da cika
baki, bisa ganin yayi wa jarumi Hasnalu kaf daya
ya baje a kasa yana neman shekawa barzahu,
koda yaga cewa Hasnalu ba zai iya tashi ba, sai
ya juya ya dauko takobin Saiful Lujara da nufin
ya dawo ya daddatsa Hasnalu yayi gutsugutsun da sassan jikinsa. Aiko yana daukar
takobin kafin ma ya juyo tuni jarumi Hasnalu ya
mike tsaye zumbur tamkar an ja zaren baka,
kawai sai ya dako tsalle sama daga inda yake ya
daki bayan aljani Raugatul Agwanu, kamar daga
cikin baka aka harba aljani Raugatul Agwanu
aka yayi tsalle sama yaje ya gwaru da wani
katon dutse, karar haduwar kirjinsa da dutsen
ta cika dajin gabadaya, dutsen ya farfashe
kuma ya fado kasa a matukar galabaice yana
mai yin aman jini ta baki da hanci kai harma ta
kunnesa ma jini ne ke bulbulowa, anan ya kama
shure-shuren mutuwa sakamakon cakudewar
jini da ƙwaƙwalwarsa. Cikin tsananin mamaki
da farin ciki su Imnal suka rugo da gudu izuwa
383
TASKARNOVELS.COM.NG
ga jarumi Hasnalu suka rungumeshi sun masu
yi masa jinjina bisa Wannan gagarumar
jarumtaka da ya nuna, shi kuwa Aljani Raugatul
Agwanu bai shafe dakika talatin ba yana
wannan shure-shuren ya zama gawa. Farin ciki
a wajen gimbiya Hursiyya da su sarki Maharaz
ba sai an fada ba,nan dai suka zauna
gabadayansu jarumi Hasnalu ya shiga koyar da
su yadda ake yin ibada kamar su; tsarki, wanka,
alwala da sallah, koma ya fara koya masu
karatun Alkur'ani mai girma, ya biya masu
suratul fatiha da falaki da nasi, bayan nan ne
yayi masu limanci suka gabatar da sallar
la'asar, da aka idar da sallar akayi addu'a sai
jarumi Hasnalu ya dubesu gabadayansu tare da
cewa to yanzu duk wanda yake jin yunwa sai
yaje ya ci, wanda kuma duk yke da bukata ya
kawar da ita, domin zamu cigaba da tafiya ne,
da izinin Allah zan cika alkawarina na kai
kowannenku zuwa kasarsa. Cikin matukar farin
ciki kowa ya bude jakar guzurinsa ya dauko
abinci ya kamaci, shiko jarumi Hasnalu sai ya
dauko tasbaha ya kama lazimi. Jarumi imnal,
sarkk Maharaz da gimbiya Mulaifa suka ware
waje guda suna cin abincinsu tare, Sadusa tare
384
TASKARNOVELS.COM.NG
da dansa Halyal da gimbiya Shalbirat suma
suka taru akan abinci guda. Ita kuwa Hursiyya
sai ta kasa cin nata abincin, sakamakon cewa
jarumi Hasnalu yaki yaci abincin kuma ya kama
lazimi, kawai sai ta dauki nata abincin taje ta
zauna gefen jarumi Hasnalu ba tare da ya lura
da ita ba. Koda Hursiyya ta danyi motsi sai
Hasnalu ya juyo ya dubeta, da dai yaga ta ajiye
abincin taki ci sai ya cika da mamaki ya dubeta
ya ce me yasa baki ci naki abincin ba? Da jin
wannan tambaya sai gimbiya Hursiyya tayi
murmushi tace ta yaya masoyi zai ji yunwa
alhalin masoyinsa baya ji, ina mai tabbatar
maka da cewa jina da ganina duk sun zama
naka, koda kaya ce idan ta sokeka a halin yanzu
nima sai naji zafin sukar a jikina, idan kaga naci
wani abu yanzu to sai dai idan yare da kai ne.
Sa'ad da jarumi Hasnalu yaji wannan bato sai
nan take yaji kaunar Hursiyya ta baibaye ilahirin
zuciyarsa kai da ransa ma gabadaya har bai san
sa'ad da ya maida mata da martanin murmushi
ba, kawai sai ya juyo ya fusknaceta sosai tare
da tsoma hannunsa cikin abincin dake gabanta
ya fara ci ya ce sa hannu muci tare, domin dai
dana barki da yunwa gwara na kawar da kunya
385
TASKARNOVELS.COM.NG
na saka hannu muci tare tunda a gaban mutane
ne, inda dai mun kadaita ne ba zan yadda na
kusanceki haka ba. Cikin tsananin murna gami
da farin ciki Hursiyya ta sanya hannunta a cikin
abincin ssuka fara ci tare suna masu yi wa
junansu murmushi mai nuna tsantsar so da
kauna. Bayan kowa ya gama kimtsawa ne sai
jarumi Hasnalu ya dubi gabadaya abokan
tafiyyar ya ce yanzu ina so kuyi mani affuwa mu
fara zuwa birnin su gimbiya shalbirat, domin ita
ce wacce aka raba da mahaifarta da iyayenta
tun tana da shekara bakwai, kuma ita ce take
da burin sake saduwa da mahaifiyarta idan har
tana raye. Koda jin haka sai kowa yayi kabbara
aka kuma aminci da wannan magana ta jarumi
Hasnalu, nan take kowa ya mike tsaye aka hau
kimtsawa, bayan kowa ya gama ne jarumi
Hasnalu ya shige gaba tare da falfalawa da
gudu yana mai karanta wasu Addu'o'i na
musamman a cikin zuciyarsa. Hakika Allah
shine mai yin yadda ya so, kuma shine mai
kunfa yakun, da yace kasance sai kawai abu ya
kasance take. A cikin rabin sa'a su jarumi
Hasnalu suka shafe tafiyar watanni tara, sai
gasu a kofar gidan sarautar gimbiya shalbirat,
386
TASKARNOVELS.COM.NG
duk da cewa an sauya tsarin fasalin gidan kama
daga katanga, da sauransu, kuma an kawata
gidan ainun ba kamar yadda yake a da ba
tsawon shekaru shekaru goma sha tara baya,
sai da gimbiya Shalbirat ta shaida gidan
sarautar, ta tabbatar da cewa nan gidansu ne.
Koda masu tsaron kofar gidan sarautar suka ga
su jarumi Hasnalu tsulum a gabansu kamar
aljanu, kuma basu ga ta inda suka taho ba,
sannan basuga durarsu daga sama ba, sai suka
kamu da tsananin tsoro jikinsu ya kama tsuma,
kafin su jarumi Hasnalu suyi magana an bude
masu kofa sun kunna kai ciki. Shalbirat ce ta yi
masu jagora wato ta wuce gaba su kuma suna
biye da ita a baya haka suka nufi fada kai tsaye.
Duk inda suk wuce sai dai kaga dakaru,bayi,
barori da kuyangin gidan sarautar suna ratsawa
gami da basu hanya, a haka har suka isa cikin
fadar inda suka iske Sarauniya Juzairat bisa
karagar mulki, koda Shalbirat ta kura mata
idanu sai ta shaidata, domin ita ce ta ci amanar
mahaifinta ta kawar dashi daga kan mulki, ta sa
masa cutar ajali, kuma itace tasa aljani
Raugatul Agwanu ya saceta ya kaita can dajin
darul hushushul maut. A wannan lokaci fadar
387
TASKARNOVELS.COM.NG
ta cika makil da fadawa da mutanen gari,
amman koda aka hango su jarumi Hasnalu sun
durfafi karagar mulki, sai fadawa da dakaru
suka kama mikewa tsaye suna masu ja da baya
cikin matukar tsoro da razana, ya zamana cewa
wannan sarauniya dake kan kujerar mulki
idanunta sun zazzaro, kuma ita jikinta na tsuma
kamar ace kyet ta fida da gudu. Gimbiya
shalbirat ta cigaba da tunkarar sarauniya, su
jarumi Hasnalu na take mata baya, a haka har
sai da suka iso daf da ita, yadda ita da Shalbirat
suna iya jin numfashin junansu. Shalbirat ta
dubeta ta ce nice gimbiya shalbirat yar
danuwanki, sarkin da kika kashe kika hau kargar
mulkinsa, sannan kika sa aljani Raugatul
Agwanu ya sace ni ya tafi dank can dajin darul
hushushul maut, ka rabani da uwata da ubana
tsawon shekara goma sha tara. Koda jin
wannan batu sai sarauniya Juzairat ta dada cika
da tsananin mamaki ta kura wa shalbirat idanu,
alokacin da ta dada kamuwa da tsoro jikinta da
baikinta suka hau rawa ta kasa cewa komai.
Shalbirat ta sake dubanta a karo na biyu ta ce ni
yanzu nazo maki da addinin gaskiya wato
addinin Musulunci, kuma na baki zafi ki karbi
388
TASKARNOVELS.COM.NG
addinin Allah ki tsira da rayuwarki, sannan ki
sauka daga kan matsayin da kike a yanzu ki
dawo talaka kamar kowa ko kuma yanzu ki rasa
rayuwarki? Koda jin Wannan batu sai sarauniya
Juzairat ta bushe da dariyar keta ta ce tsakanina
da addinin musulunci sai gaba.. Kafin ta gama
rufe bakinta gimbiya Shalbirat ta juyo cikin
tsananin zafin nama ta zare takobin jarumi
Hasnalu ta kuma juyawa ta fille kan Sarauniya
Juzairat, nan take jini yayi tsiri sama yayin da
kan nata ya gangaro daga kan karagar mulki.
Nan take Shalbirat ta kwala kabbara kuma ta
karanta kalmar shahada ta na mai umartar
gabadaya mutanen dake fadar da su biya
kalmar. Ba tare da wata gardama ba gabadaya
mutanen fadar suka maimaita kalmar shahada,
cikin tsananin farin ciki gimbiya Shalbirat ta hau
kan karagar mulki ta zauna alokacin da su
jarumi Hasnalu suka cika da tsananin mamakin
wannan gagarumar jarumtaka da ta yi. Zaman
Shalbirat akan karagar mulki sai idanunta suka
ciko da kwalla, har hawaye ya zubo mata a
lokacin data gama kare wa karagar mulki da
kuma fadar kallo. A sannan ne ta dubi wani
dattijo a fadar ta ce ya kai waziri Lamsanu mene
389
TASKARNOVELS.COM.NG
ne labarin mahaifiyata? Cikin tsananin mamaki
waziri Lamsanu ya dubi gimbiya Shalbirat ya ce
rankiya dade qshe ba zaki manta da kamannina
ba, kiyi sani cewa mahaifiyarki ta samu tabin
hankali, kuma tana can a tsare a kurkuku. Koda
jin haka sai bakin ciki ya turnuke Shalbirat har
hawaye ya sake zubo mata ta mike ta ce muje
ka kaini inda take. Nan take Waziri Lamsanu ya
wuce gaba Shalbirat dasu jarumi Hasnalu na
take mashi baya, haka suka yita tafiya a gidan
sarautar suna masu shiga lungu da sako na
gidan sarautar har sai da suka iso inda
kurkukun yake, aka kai su kofar dakin da
mahaifiyar Shalbirat take. Da zuwa sai suka
isketa a kwance tana bacci, gashin kanta yayi
buzu-buzu ba kyan gani, ga kuma furfura duk ta
rufeshi Hakazalika rigar jikinta ta yi dauda sosai
har tana wari. Su duka dai da suka zibar da
hawaye saboda tausayi, Shalbirat ta kira sunan
mahaifiyar tata har sau uku sannan ta taso
zaune tana mai kura wa Shalbirat idanu, kawai
sai ta bushe da dariya ta kama surutu irn na
masu tabin hankali tana mai kawo wa Shalbirat
duka. Koda ganin haka sai jarumi Hasnalu ya yi
sauri ya matsar da Shalbirat baya sannan ya
390
TASKARNOVELS.COM.NG
shiga karanta wata addu'a yana tofawa
mahaifiyar Shalbirat, aiko nan take wani
nannauyan bacci ya dauketa, jim kadan ta farko
tana mai tashi tsaye da kafafunta tana mai
binsu da idanu daya bayan daya, koda idanunta
suka yi arba da yarta Shalbirat sai ta kura mata
idanu har hawaye ya zubo mata, ta nuna
Shalbirat da hannu kuma ta kira sunanta tana
mai cewa Yata ashe kina raye a wannan duniya,
ashe zamu sake saduwa? Koda jin wannan
batu sai mamaki ya kama su Jarumi Hasnalu
suka yi kabbara a tare, nan take Shalbirat tasa
aka bude kofar dakin da mahaifiyarta ke ciki ta
ruga da gudu suka rungume juna ita da
mahaifiyarta tata suka fashe da sabon kukan
farin ciki. Suma su Imnal basu san sa'ad da
kukan ya kwace masu ba, saboda tausayi gami
da murna, a wannan rana aka kaddamar da
addinin musulunci a Birnin, gimbiya Shalbirat
kuma ta hau kan karagar mulki. Lokacin dasu
jarumi Hasnalu suka je yi mata bankwana sai ta
fashe da kuka, ta dubi Sadusa da dansa Halyal
ta ce kune farkon sanadin tsirata daga hannun
azzalumi aljani Raugatul Agwanu, bani da bakin
yi maku godiya face addu'ar Allah ya saka maku
391
TASKARNOVELS.COM.NG
da mafificin alheri. Ba tare da bata lokaci ba su
Hasnalu suka yi mata sallama suka tafi, ana isa
birnin sarki Dujalu nan ma aka kaddamar da
addinin musulunci amman gimbiya Hursiyya
bata karbi sarauta b sai aka ba Sadusa. Waziri
da jama'arsa kuwa suka bashi hadin kai. A
sannan ne aka shiga dakin tarihi na gidan
sarautar inda aka gano wannan littafin mai
dauke da tarihin kamannin mahaifin Hasnalu da
kuma inda kabarinsa yake, nan take aka
dunguma aka tafi wajen, koda aka tona saman
kabarin sai aka yi arba da fuskar mahaifin
Hasnalu lafiyarta sumul ko kwarzanewa bata yi
ba, kamar ma asannan ne aka binne shi, kuma
kamanninsu iri daya ne sak da jarumi Hasnalu
tamkar an tsaga kara, bambancinsu kawai na
shekaru ne. Koda jama'a sukaga wannan gawa
cikin koshin lafiya alhalin ta kusa shekaru
talatin a binne sai suka cika da al'ajabi aka
kama hailala da kabbara, aka kuma sallama Wa
Allah bisa ikonSa. Hasnalu ya kura wa
mahaifinsa idanu yana mai zubda hawaye ya ce
ya kai abbana ban taba ganinka ba sai labarinka
da mahaifiyata ta bani, rayuwarka gaba daya ta
gushe a cikin yada Addinin Allah, yau gashi
392
TASKARNOVELS.COM.NG
Allah ya cika mani burina naga fuskarka da
idanuna kafin mutuwata. Burina ya cika, fatana
nima Allah ya dau raina a irin wannan tafarki
naka, nan take ya mayar da kasar kabarin ya
rufe sannan yayi masa addu'a. Kamar yadda
aka kaddamar da addinin musulunci a birnin
Sarauniya Shalbirat da birnin sarki Dujalu haka
akaje birnin sarki Maharaz aka kaddamar da shi,
kuma duk d cewa jarumi Imnal da gimbiya
Mulaifa sun kasance yara a sannan aka daura
masu aure, akayi gagarumin shagalin biki a
gaban jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya.
Lokacin da Hasnalu da gimbiya Hursiyya suka
zo zasu yi wa su Imnal da sarki Maharaz
bankwana domin su tafi izuwa can nahiyar su
jarumi Hasnalu inda acan ne Hursiyya zata
karasa sauran rayuwarta ta duniya sai su duka
suka kama kuka saboda bakin cikin rabuwa da
juna, sarki Maharaz ya rungume jarumi Hasnalu
yana mai cewa ya kai jarumin jarumai, kaine ka
tsamoni daga cikin duhun jahilci ka haskake
mana wannan nahiya gaba daya da hasken
musulunci, hasken ilimi kuma haske na
gaskiya, tabbas har abada ba zamu taba
mantawa da kai ba, kuma har mu mutu zamu
393
TASKARNOVELS.COM.NG
rinka tunawa da kai muna alfahari da kai, idan
ka amince ina so tun gabanin ku barmu a daura
aurenka da gimbiya Hursiyya a gaban idanunmu
domin mu zama sheda kuma ku tsira daga
dukkanin wani tsautsayi na sharrin shedan
dana zuciya, tunda zaku kadaita a cikin wannan
doguwar tafiya da zaku yi izuwa nahiyarku.
Koda sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai
jarumi Hasnalu yaji matukar farin ciki, kuma ya
kama yin godiya ga sarki Maharaz bisa hango
masu abinda zai fiye masu alheri. Nan take aka
daura auren jarumi Hasnalu da gimbiya
Hursiyya bisa ka'idar addinin Musulunci, bayan
nan sai suka yi bankwana su sarki Maharaz
suna zubar da hawaye suma suna zubarwa, har
jarumi Hasnalu da Hursiyya sun juya zasu tafi
sai kawai sarki Maharaz ya kira sunan Hursiyya
ta juyo ta dubeshi ya ce da ita ya ke yata in da
tambaya a gareki? Tambaya ta farko ita ce
wane irin darasi kika samu a cikin hikayar
jarumi shaddadu, kuma wane ilimi kika gani a
cikin tamu rayuwar ni da fan uwanki sarki
Dujalu? Koda jin wadannan tambayoyi sai
hawaye ya zubo daga cikin idanun Hursiyya
domin babu wanda ya taba mata irin wannan
394
TASKARNOVELS.COM.NG
tambaya face sarki Dujalu. Hursiyya ta yi ajiyar
numfashi sannan ta ce ya kai abbana ka sani
cewa a cikin hikayar jarumi shaddadu na
fahimci cewar zalunci da son zuciya basa haifar
da komai face nadama da kaskanci gami da
dunbin wahala kamar yadda karshen rayuwar
sarki Laffaru ta kasance, tunda a farkon
rayuwarsa karfin mulki, dana jarumtarsa hadi
da na sihiri sun sa masa isgilanci har yana cin
zalin al'umma, ganin cewa babu wani da ya isa
ya taka masa birki, amma sai gashi ya mace ta
rabashi da mulkinsa, karfinsa da duk
daukakarsa, kuma ta jefashi a cikin tsananin
wuya da rashin kwanciyar hankali har izuwa
karshen rayuwarsa. Darasi na biyu a cikin
wannan labari shine abu ne mara kyau mutum
ya tsananta gaba a tsakaninsa da wani, kamar
yadda Sharlis da Laffaru suka tsananta gaba a
tsakaninsu har ga yayansu, wanda sai ga shi a
karshe yayan nasu sun kamu da son juna kuma
suka zabi su mutu tare dan kawo karshen gabar
iyayen nasu, abinda ya cusa wa iyayen bakin
ciki kenan suka kashe kansu, suka rasa komai
ba tare da burin dayansu ya cika ba. Dangane
da ilimin dana samu game da rayuwar dan
395
TASKARNOVELS.COM.NG
uwana Dujalu da taka rayuwar shine na fahimci
cewar wanda duk bai gode Wa Allah ba bisa
baiwar da yayi masa ta arziki da daukaka, har
yake harin ya samu wadda tafi wannan to
karshensa nadama gami da hasara, tunda gashi
kai da shi duk kunyi mummunar asara ta dukiya
da rayukan jama'a kuma burinku bai cika ba,
haka kuma na samu babban ilimi na kadaita
Allah, ikonsa da isarSa akan komai da kowa,
tunda gashi matsafa da aljanu sun kasa dauko
kayan yakin mazan jiya a cikin tekun bahar
Suffiya, amman sai gashi wanda yayi imani da
Allah ya kadaitashi ya dauko su salim alin,
kamar yadda ake cire silin gashi daga cikin
tandun mai, hakika ubangijin musulunci shine
buwayi gagara misali, wanda duk yayi imani da
shi ya kubuta kuma ya tsira daga dukkanin
sharri, wanda kuma ya bujire masa ya hadu da
masifa da halaka. Koda Hursiyya ta zo nan a
jawabinta sai sarki Maharaz ya cika da tsananin
murna gami da farin ciki, yace AlhamduLillahi
tabbas kin samu duk irin darasin daya kamata ki
samu a cikin wadannan labarai, albishir din da
zanyi maki shine kije ki nemi wani littafi mai
suna Tsatsuba tabbas zakiji labarin Sadauki
396
TASKARNOVELS.COM.NG
Hulkas na birnin Romaniya a cikinsa tunda dai
dan uwanki sarki dujalu bai samu damar baki
labarin ba ajali ya riskeshi. Koda jin haka sai
farin ciki ya lullube gimbiya Hursiyya ta ce aiko
in sha Allah duk inda Littafin Tsatsuba yake zan
nemeshi domin na karanta tarihin Sadauki
Hulkas mai hular lamsara n birnin Romaniya.
Nan take Jarumi Hasnalu da gimbiya Hursiyya
suka sake yi wa sarki Maharaz sallama suka tafi
suna masu waigensa har suka fice daga fadar
tasa, gabadaya suka nausa izuwa cikin daji
suna masu falfalawa da azababben gudu, cikin
yarda da huwacewa ta Allah suka nufi nahiyar
su jarumi Hasnalu inda zasu cigaba da rayuwa
bisa tafarkin addinin Muslunci.
AlhamduLillahi nanne karshen wannan littafi na
mazan jiya da fatan kunji dadin wannan littafi
wanda Abdulaziz Sani madakin gini ya rubuta ni
kuma Abubakar Saleh Alquyraemey na
jagoranci typing insa nake cewa mu hadu da ku
a wani littafin.
397
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 18