da su izuwa can
kololuwar sama ya kama tsala gudu yana keta
giza gizai tamkar gudun taurariwa mai wutsiya
A Dai dai wannan lokaci ne aljani Raugatul
Aguwanu yaji dan motsi a cikin kunnensa har ya
daga dan yatsansa guda zai cusa a cikin
kunnen yaji an fara masa susa
Page 149 zidane kd
180
TASKARNOVELS.COM.NG
Dan karen dadi daya ji ne yasa ya fasa sanya
dan yatsan nasa ya saki jikinsa cikin kwanciyar
hankali ya cigaba da tsala gudu: A Wannna
lokacin gimbiya Shalbirat ta kamu da tsananin
farin ciki takama murmushi: Boka sadusa ya
dubeya cikin mamaki yace ke kuwa mene ne ya
saki farin ciki haka har kike ta murmushi da
yake baki? Shalbirat tace gaba ai dolene na
kasance a cikin farin ciki, tunda rabona da
gannin fili haka ba a cikin keji ba yau shekara
goma sha tara kenan: Da jin haka sai tausayi ya
kama sadusa da Halyal har idanunsu suka ciko
da kwallah: A cikin kunnen aljani Raugatul
Aguwanu kuwa, Boka radiyan ya dubi Gimbiya
Hursiya ya ce bari na karasa miki Labarin da
dan uwanki sarki dujalu bai karasa miki ba
hakan zai debe miki kewa kafin mu karasa bakin
kogin bahar sufiya: Cikin tsananin mamaki
Hursiya ta dubi boka Radiyan ba tare da ta iya
furta masa komai ba: Boka Radinyan yayi
murmushi yace kada ki yi mamaki akan
lamarina domin na wucce dukkan tunaninki na
san abinda baki sani ba zaki gasgata hakan idan
kiyi la akari da abubuwan da suka faru
181
TASKARNOVELS.COM.NG
tsakaninmu tunda haduwarmu kawo izuwa
yanzu da muke cikin kunnen aljani Raugatul
Aguwanu
page 150 Gimbiya Hursiya ta gyada kai kawai
cikin tana sauraron boka Radiyan
Shi kuma ya cigaba da dora mata Labarin
Kamar Haka
: * * * MAZAN JIYA! (4) Kashi na sittin da
biyar (65) ABDUL'AZIZ SANI MADAKINGINI
(King ofAdventure Story) . LOKACIN da jarumi
SHADDADU ya cigaba da tafiya bisa wannan
tsuntsun tsafi, ga Mashin Galilul Haras daure a
gadon bayansa kuma gashi a cikin gagarumar
shigar Yaki, sai tsuntsun ya ci gaba da keta gizagizai a sararin samaniya ba kakkautawa. Sai
182
TASKARNOVELS.COM.NG
da suka shafe sa'a biyar da rabi suna tafiya
sannan tsuntsun ya sauko kasa-kasa da kansa,
ashe wani babban Birni suka tunkaro a
gabansu. Koda ya rage bai fi zira'i goma ba
tsakaninsu da Birnin sai tsuntsun ya sauko
kasa. Shadaddu ya sauko daga kan tsuntsun.
Saukarsa ke da wuya sai tsuntsun ya rikide ya
zama dan karami kuma ya tashi sama ya dira a
kafadar Shaddadu. Faruwar hakan ke da wuya
sai Shadaddu ya kunna kai izuwa kofar wannan
Birni ba tare da shakkar komai ba. Da isarsa
bakin kofar garin ya iske masu gadi wadansu
Dakaru samudawan karti kimanin su arba in a
tsaitsaye cikin shigar Yaki. Ko kallonsu
Shadaddu bai yi ba ya nufi bakin kofar Garin
wacce take a rufe. Su ma Dakarun sai suka yi
kamar ba su ganshi ba, domin ko kallonsa ba su
yi ba. Shi ma sai ya ki ya yi musu magana ya je
ya kwankwasa kofar domin a bude masa duk da
cewa ya ga daya daga cikin masu gadin a zaune
daf da bakin kofar bisa wata kujera rike da
katuwar Kuba. Shadaddu ya kwankwasa kofar
har sau uku, amma shiru ba a bude kofar ba.
Kawai sai ya ji masu gadin sun kama yi masa
dariya. Daya daga cikinsu ya dube shi ya ce,
183
TASKARNOVELS.COM.NG
"Ya kai wannan sakaran bako, shin ba ka da
da'a ne ko kuwa ba a koya maka ladabi ba ne a
gidanku? Idan haka halayyarka take a can
garinku to mu nan ba haka ba ne. Amma idan
kai Kurma ne sai ka gaya mana". Kawai sai
Shadaddu ya kalli mai maganar yai masa
murmushi ba tare da ya maida masa da
martanin maganar ba. Kawai sai ya ja da baya
kadan ya daga ya daki kofar garin wacce ta
kasance mai kauri da nauyin gaske ta zallar
bakin karfe. Nan take kofar ta jijjige ta fada ciki.
Al'amarin da yai matukar firgita Dakarun ke nan
suka zazzare mnakamansu amma kuma suka
kasa afka wa Shadaddu sakamakon ganin
wannan gagarumar jarumtaka da ya yi.
Shadaddu ya waigo ya dubi Dakarun ya yi musu
murmushi a karo na biyu sannan ya juya ya
shige izuwa cikin Birnin. Nan fa Dakarun nan
suka kama duru-duru suka rasa abin da za su yi
tsakanin su bi wannan bakon saurayi su yake
shi ko kuma su kai rahotonsa izuwa ga
Sarauniyarsu? Nan dai suka yanke shawarar
daya daga cikinsu ya ruga izuwa fada ya kai
labari. Nan take kuwa aka bi wannan shawara.
Lokacin da Shadaddu ya kunna kai izuwa cikin
184
TASKARNOVELS.COM.NG
wannan Birni sai ya zama abin kallo, duk inda ya
ratsa sai ya ga mutane har fitowa suke daga
cikin gidajensu suna binsa a baya, musamman
mata domin dimaucewa suka rinka yi. Abin da
yai matukar bai wa Shadaddu mamaki ke nan,
domin shi bai ga abin kallo ba a tare da shi.
Abin da Shadaddu bai fahimta ba shi ne
tsananin kyawunsa da kwarjinihsa ne ya sa ake
kallonsa. Koda ya ga kallon da ake yi masa ya
yi yawa, kuma jama'a dada karuwa suke ana ta
binsa sai ya juya ya kwarara uban ihu ya yi
kamar zai zare Takobinsa. Nan fa jama'a suka
tarwatse cikin firgita suka kama gudu. Kafin
cikar dakika biyar babu kowa akan hanyar.
Shadaddu yai dariya ya ce, "Ashe ma duk
matsorata ne a garin. Kawai sai ya ci gaba da
tafiya. Burinsa kawai shi ne ya ga kasuwa ko
inda ake siyar da abinci domin yunwa ta fara
damunsa ga shi bai taho da wani abinci ba a
cikin jakar guzurinsa sai tarin Dirhami mai
yawan gaske. Haka dai ya ci gaba da tafiya
yana kutsawa ta cikin lunguna da sako-sako na
Garin, amma kuma bai ga mutane sun daina
kallonsa ba, sai dai ba sa biyo shi a baya
sakamakon ganin rashin annuri akan fuskarsa,
185
TASKARNOVELS.COM.NG
kai da gani ka san cewa mutane suna shakkarsa
saboda ganin irin kirarsa ta manyan sadaukai.
Yana cikin dube-dube ne ya hango wani gida
wanda aka yi rubutu a jikin saman kofarsa
kamar haka. 'GIDAN ABINCI'. Koda ganin
wannan rubutu sai murna ta kama Shadaddu ya
kunna kai izuwa cikin gidan. Yana shiga ya iske
mutane da yawa a zazzaune bisa kujeru a
karkashin tebura suna ta cin abinci kala-kala.
Lokaci guda kowa ya dago kai ya kalle shi
sannan aka kawar da kai aka ci gaba da cin
abincin babu wanda ya sake dubansa.
Al'amarin da ya daurewa Shadaddu kai shi ne
gaba dayan mutanen da ke cikin gidan abincin
maza ne, kuma karti majiya karli, ababan
kwatance. Mace guda daya ce jal a cikin gidan,
kuma ita ce mai bayar da abincin. A can gefe
daya bisa wani dogon tebur mai dauke da
tukwanen abinci kimanin guda goma.
Shadaddu ya sake yin nazarin kartin da ke cikin
gidan ya ga kowannensu yana da siffa irin ta
mayaki duk da cewar babu makamai a jikinsu.
Nan take jikin Shadaddu ya ba shi cewar akwai
tuggun da ake son shirya masa amma sai ya
basar ya nuna ba ya tunanin komai. Kai tsaye
186
TASKARNOVELS.COM.NG
ya nufi inda mai bayar da abincin take. Da zuwa
sai ya bude jakarsa ya dauko Dirhami goma ya
ajiye a gabanta sannan ya nuna mata irin kalar
abincin da yake so. Kawai sai ya ga ta kura
masa idanu ko kiftawa ba ta yi har sai da ya doki
tebur din da ke gabanta sannan ta dawo cikin
hayyacinta. Ashe tsananin kyawunsa ne ya
dimautata ta sandare kamar Gunki. Koda ya
buga teburin ta dawo cikin haiyacintae ta ga ya
ajiye ma ta kudi akan tebur sai ta gan nufinsa.
Hannunta na karkarwa ta dauki cokali da faranti
ta zuba masa abincin. Shadaddu ya karbi
abincin ya je ya zauna akan wani tebur wanda
babu kowa akai ya fara cin sbincia. Yana cikin
cin abincin ne ya ga wadannan mutane da ke
cikin gidan sun fara mimmikewa tsaye suna
zaro makamai a jikin karkashin tebur din da
suke zaune. Ko motsawa Shadaddu bai yi ba,
da ma ta wutsiyar idanu ya kalle su, kawai sai ya
cigaba da cin abincinsa. Koda wannan mace
mai bayar da abinci ta ga an fara zaro makamai
sai tavyi wuf! Ta ruga izuwa cikin wani ɗaki ta
kullo kofa. A sannan ne aka rufo kofar shigowa
gidan gabadaya. Hakan ba ta sa Shadaddu ya ji
ko dar ba! Kawai sai ya ci gaba da cin abincinsa.
187
TASKARNOVELS.COM.NG
Lokaci guda gaba dayan kartin suka afkawa
Shadaddu da nufin su daddatsa shi. Cikin
masifaffen bakin zafin nama Shadaddu ya zare
tasa Takobin, ya yi wata irin katantanwa a
tsakiyarsu ya tarwatsa su da karfin tsiya. Nan
fa aka ruguntsume da Yaki, suka yi masa
rubdugu suka rinka kai masa sara da suka ta ko
ina. Shi kuma ya yi ta kare hare-harensu amma
sai ya dinga mai da martani da bugu da naushi
maimakon da makami. Nan fa ya rinka hada
musu jini da majina, amma saboda naci da
juriya irin na maza masu Jarumta ko sun fadi
kasa sai ka ga sun mike zumbur! Sun ci gaba da
kai masa munanan sara da suka, amma ba a
samu wanda ya sami nasarar koda lakutar
jikinsa ba. Shi kuwa Shadaddu sai ya nuna
tsagwaron sadaukantaka da fifikon yaki, ya ki ya
sari jikin dayansu da makami. Haka dai ya ci
gaba da gabza musu naushi da musu bugu
hannu da kafa har sai da ya bazar da gaba
dayansu a kas, bayan an kakkarya tebura da
kujerun da ke gidan, an lalata komai ya zamana
cewa komai ya ragargaje. á Sai ga shi karti
sama da mutum arba'in kwance kas sun yi lagalaga sun kasa tashi. A sannan ne wannan
188
TASKARNOVELS.COM.NG
mace mai siyar da abincin da ta ji an daina
kwarmazuwa ta bude dakin da ta shiga ta бuya
ta fito da sauri ta ga Shadaddu ya dauki tulun
giya ya kafa a bakinsa yana ta sha. Sai da
ruwan giyar ya kare kaf sannan ya wurgi da tulun
ya fashe. Ko alamar buguwa bai yi ba ya dubi
macen ya ce, "Ina cigiyar wata Jaruma mai suna
ZIYA'UL HAK ko kin santa?" Cikin alamun tsoro
matar ta dubi Shadaddu a lokacin da jikinta
gabadaya ya kama tsuma ta ce "Ba mu taba jin
ma mai irin wannan suna ba a garin nan ya kai
wannan bakon saurayı ma'abocin kyau da
jarumtaka. Wane ne kai, kuma daga ina ka fito?"
Koda jin wannan tambaya sai Shadaddu ya yi
mata wani guntun murmushi sannan ya ce, "Ni
kaina ban san amsar tambayar da kika yi min
ba!" Koda gama fadın haka sai ya sake bude
jakar guzurinsa ya dauko dirhami ashirin ya
mika mata ta karba sannan ya ce, yanzu
Makwanci nake bukata . Matar ta yi murmushi
ta ce, "Samari ka sami makwanci har ma da mai
debe maka kewa. Shaddadu ya yi ma ta wata
irin harara wacce ta sa zuciyarta ta buga da
karfi, ya dube ta a fusace ya ce, "Ba na bukatar
mace a kusa da ni". Cikin rawar jiki ta ja
189
TASKARNOVELS.COM.NG
Shaddadu suka fice daga cikin wannan gida
suka kunna kai izuwa cikin wani lungu. Ai
kuwa suna shigewa wannan lungun sai ga
Dakarun gidan Sarautar garin sama da mutum
dari biyu sun shigo unguwar a guje rike da
makamai suna neman Shaddadu domin tuni
labari ya isa ga Sarauniyar garin cewa ga wani
bakon Sadaukin saurayi can ya ɓalla kofar gari
da karfin tsiya ya shigo kuma har ya fara barna a
cikin gari. Bisa wannan dalili ne Sarauniyar ta
taso Dakaru domin su zo su kamo wannan
bakon Jarumi a mace ko a raye.. Lokacin da
Dakarun Sarauniya suka je wannan gidan abinci
suka iske wadannan karti arba'in a kwakkwance
mashe-mashe sun sha duka kuma suka ga
komai na gidan a ragargaje sai suka cika da
mamakin yadda za a ce wai mutum daya ne ya
yi wannan aiki. Nan dai suka shiga neman
Shaddadu amma ko alamarsa babu. Da suka
ga babu shi sai suka koma can fadar Sarauniyar
tasu suka sanar da ita cewa ba su ga wannan
bakon saurayi ba. Lokacin da Sarauniya
ZUBAINA IBINI LAIYARA ta ji cewar ba a ga
bakon saurayin ba sai ta bushe da dariya.
Al'amarin da yai matukar bai wa kowa mamaki
190
TASKARNOVELS.COM.NG
ke nan a fadar, aka zuba mata idanu kawai.
Daga can kuma sai ta tsuke bakinta ta murtuke
fuska ta ce, "Tabbas BABBAN GORO sai
MAGOGIN KARFE. Hakika babu wanda zai iya
tarar wannan bakon saurayi face ni. Da kai na
zan yi shiri na tafi farautarsa a cikin garin nan.
Na yi bincike a kansa na gano cewa yana da
matukar karfin sihiri da jarumtaka, to amma duk
abin da yake takama da shi ya zo gidansa. Tun
da na hau kan karagar wannan mulki a wannan
Birni namu na HADIYAS ba a taɓa samun wani
tsagera da ya zo mini Birnina babu izini yakarya
mini kofar gari kuma ya je gidan abinci ya yi wa
Dakaruna dukan tsiya. Hakika idan na kama
wannan bako sai na gana masa azaba mai
radadi har izuwa lokaci mai tsawo sannan na
yanke masa hukuncin kisa." Koda gama
wannan jawabi sai Sarauniya Zubaina ta mike
tsaye a fusace ta shige izuwa cikin gidan
Sarautar, a sannan ne fada ta watse kowa ya
tafi yana fadin albarkacin bakinsa. Wasu suna
cewa, "Lallai wannan bako ya tabo tsuliyar
Dodo". Wasu kuma suna cewa, "Ai saukin
wannan bako kawai ya samu ya sulale ya gudu
daga garin saboda kowa ya san cewa Sarauniya
191
TASKARNOVELS.COM.NG
Zubaina ta kasance BASADAUKIYA ta gaban
kwatance, kuma hatsabibiyar Bokanya ce
wadda babu kamarta a gabadayan Nahiyar.
Al'amarin Jarumi Shaddadu kuwa, lokacin da
wannan ma'aikaciyar gidan abinci ta ja shi suka
shiga cikin wannan lungu, sai suka yi ta wuce
gidaje har sai da suka je karshen lungun sannan
ta shige da shi izuwa cikin wani gida. Sai da ta
sa mukulli sannan ta bude gidan, suna shiga, ta
mai da kofar ta rufe. A cikin wani dan karamin
falo Shaddadu ya tsinci kansa mai dauke da
daki guda daya jal, sai kuma bandaki. Saboda
rashin yarda sai da Shadaddu ya leka cikin
dakin da bandakin ya tabbatar da babu kowa a
ciki sannan ya dawo ya zauna a falon. A
sannan ne matar wadda shekarunta ba za su
haura talatin da biyar ba, mai kyan diri da fuska
ta dube shi ta yi dariya ta ce. "Kana zaton za a
hada baki ne da ni a cuce ka? To ka sani cewa ni
karuwa ce, kudi ne kawai a gabana. In dai za ka
biya ni zan ci gaba da rufa maka asiri har izuwa
lokacin da za ka bar garin nan". Kafin
Shaddadu ya budi baki ya ce wani abu sai suka
jiyo an shigo lungun da gudu kuma alamar
mutane ne da yawa suka shigo.Cikin sauri
192
TASKARNOVELS.COM.NG
matar ta mike tsaye ta ruga izuwa bakin taga ta
yaye labule ta leka. Da sauri ta saki labulen
kofar la ruga izuwa wajen Shaddadu a gigice ta
ce, "Zo mu je na boye ka, Sarauniya ce da kanta
ta fito nemanka". Shaddadu ya dubi matar
cikin alamun matukar mamaki ya ce, "Akan me
za ki бoye ni an gaya miki ni ina shakkar wani
ne? Ki bari Sarauniyar taku ta shigo har nan ki
ga yadda za mu wanye." Matar ta dubi
Shaddadu kamar za ta yi kuka ta ce, "Ni dai ka
rufa mini asiri idan Sarauniya ta zo ta ganka
anan gidana kashe ni za ta yi". Koda jin haka
sai jikin Shaddadu yai sanyi. Ba tare da gardama
ba kuwa ya bi ta suka shige cikin wannan dakin
barci nata da sauri. Suna shiga sai ya ga ta
yaye dardumar dakin, ta daga wata kofar katako
sai ga matattakala izuwa cikin gidan kasa.
Matar ta dubi Shaddadu ta ce, "Shiga nan ka yi
zamanka". Cikin sauri Shaddadu ya shige cikin
gidan kasan, sannan ta mai da kofar ta rufe
sanna dardumar. Faruwar hakan ke da wuya
sai ta ji ana, bubbuga ma ta kofar gida. A guje ta
je ta bude, Sarauniya Zubaina ta gani tsaye a
gabanta cikin gagarumar shigar Yaki, ga wasu
manyan Dakarunta su goma suna take mata
193
TASKARNOVELS.COM.NG
baya. Zubaina ta dubi matar da kyau a cikin
nutsuwa ta ce, "Ya ke YALDISA ina wannan
bakon saurayi?" Yaldiṣa ta risina cikin
girmamawa ta ce, "Ya Shugabata, rabo na da
bakon saurayi tun da muka fito tare daga gidan
abinci ya tambaye ni hanyar kasuwa na nuna
masa anan muka rabu". Koda jin wannan batu
sai Sarauniya Zubaina ta yi murmushi mai nuna
alamun rashin yarda sannan ta hankade Yaldisa
ta fadi gefe guda. Kai tsaye Zubaina da
Dakarunta suka kunna kai izuwa cikin falon.
Sarauniya Zubaina ta zauna akan kujera sannan
ta umarci Dakarunta da su caje ko ina na gidan.
Lokacin da Yaldisa ta taso ta zo gaban Zubaina
ta durkusa tana mai sunkui da kanta kas ba tare
da ta nuna wata alama ta tsoro ba ko rashin
gaskiya. Zubaina ta sake duban Yaldisa ta yi
murmushi a karo na biyu sannan ta ce, "Ya ke
Yaldisa yau shekara bakwai ke nan kina aiki a
karkashina. Na san dukkan halayenki, ke
karuwa ce wadda in dai za ta sami kudi babu
abin da ba za ta iya yi ba. Ki gaya mini gaskiya
tun kafin lokaci ya kure miki. Idan na gano cewa
kina da hannu akan ɓoye wannan bako daga
baya, kin san halina, ba sani ba sabo. Ban san
194
TASKARNOVELS.COM.NG
tausayi ba kuma ban san hakuri ba, kashe ki zan
yi kawai". Yaldisa ta dago kai ta dubi Zubaina
ta ce, Ya Shugabata tsawon shekaru bakwan da
nake aiki a tare da ke ban taba yi miki karya ba,
wannan ya isa ki aminta da ni. Zubaina ta
jinjina kai gami da ajiyar zuciya ta ce, tabbas
abin da kika fada gaskiya ne, amma ai a wajenki
kudi su ne gaba da komai. Ni na abbatar da
cewa za ki iya siyar da iyayenki ma muddin za ki
sami kudi. Gama fadin hakan ke da wuya sai
ga Dakarun Zubaina sun dawo gabanta.
Shugabansu wanda ake kira SADAR ya risina ce,
"Ranki ya daɗe, babu kowa a cikin gidan nan".
Koda jin haka sai Zubaina ta mike tsaye ta nufi
bakin kofa, Dakarun nata na biye da ita. Har ta
sa kafarta guda a waje sai ta juyo ta dubi Yaldisa
ta ce. "A ko yaushe za mu iya kawo ziyarar
bazato, Kar ki manta hukuncin kisa ne a kanki
idan na kama ki da laifin boye mai laifi". Gama
fadin hakan ke da wuya sai Sarauniya Zubaina
da Dakarunta suka fice daga cikin gidan.
Yaldisa ta mai da Rofar ta rufe sannan ta jingina
bayanta a jikin kofar tana mai yin doguwar ajiyar
numfashi cikin tsananin tsoro. Ba ta matsa
daga inda take tsaye a jikin Rofar ba sai bayan
195
TASKARNOVELS.COM.NG
lokaci mai tsawo bayan ta tabbar da cewa su
Sarauniya Zubaina ba sa kusa sannan ta nufi
dakin barcin nata. Tana shiga sai ta iske
Shaddadu a kwance akan gadonta har ma ya
kama barci abinsa tamkar ba shi aka zo nema
ba. Cikin fushi ta girgiza gadon, Shaddadu ya
mike zaune ya dube ta cikin mamaki ya ce,
"Lafiya za ki katse mini barcina alhalin a cikin
gajiyar tafiya nake?" Koda jin haka sai Yaldisa
ta sake fusata ta ce, "Au! Kai ta barci ma kake
ba ta raina ba? To tsaya ka ji, ga kudinka da ka
ba ni, ba zan iya siyar da rayuwata ba a kan
dirhami ashirin kacal da ka ba ni". Koda jin
haka sai Shaddadu ya yi murmushi, nan take ya
janyo jakar guzurinsa ya bude ya sake debo
dirhami ashirin ya mikawa Yaldisa ya ce, ga
wannan ki kara. Ni dai ki kyale ni na yi barcina.
Yaldisa ta tankwaɓe hannun Shaddadu dinaren
ya zube kasa ta yı masa tsawa ta ce, "Ran nawa
zan siyar maka akan dinare arba'in? Ka ga ni ba
na bukatar kudinka kawai ka tashi ka bar mini
gida don ba za ka janyo mini hukuncin kisa ba a
banza". Maimakon Shaddadu ya yi fishi sai ya
yi dariya kuma ya dauko kullin dinarensa
gabadaya ya cilla wa Yaldisa ta cafe ya ce.
196
TASKARNOVELS.COM.NG
"Gashi nan gabadayan abin da na mallaka ke
nan in kin so ki kyale ni na kwana. Na yi miki
alkawarin babu abin da zai taɓa lafiyarki koda
asirinki ya tonu, kuma gobe da safe zan bar miki
gidanki". Koda gama fadin hakan sai
Shaddadu ya koma ya kwanta akan gadon yana
mai juya mata baya. Kafin cikar dakika dari da
ashirin ya fara munshari. Al'amarin da yai
matukar bai wa Yaldisa mamaki ke nan kuma ya
ba ta dariya. Nan dai ta sunkuya ta tsince
ragowar wannan dinaren da ya zube kasa ta
zuba a cikin kullin wanda aka ba ta ta boye,
sannan ta je ta ci gaba da dan aiyukanta na
gida. Har dare ya yi Shaddadu bai farka daga
barci ba. Lokacin da Yaldisa ta ji ta soma jin
barci har ma tana gyangyadi daga zaune sai
hankalinta ya tashi domin dama can tsoro ne ya
hanata zuwa ta kwanta, saboda tana ganin
cewa a kodayaushe Dakarun Sarauniya Zubaina
za su iya kawo ziyarar bazato. Da dai ta ga tana
jin barcin sosai sai ta mike tsaye ta nufi cikin
dakin barcin. Tana shiga ta ga har a sannan
Shaddadu barci yake yi. Koda ta kura masa
idanu ta dube shi sama da kasa ta ga irin
tsananin kyawun fuskarsa da kyawun surar
197
TASKARNOVELS.COM.NG
jikinsa, sai nan take ta ji ta kamu da tsananin
sha'awarsa. Sai a sannan ne ta gane cewa
ashe da can tsoro ne ya sa ta kasa yi masa
kallon nutsuwa bare ta san cewa kyakkyawa ne.
Nan dai Yaldisa ta kautar da tsoro ta cire tufafin
jikinta ta sanya na barci sannan ta kwanta a
bayan Shaddadu. Koda ta kai hannu ta tabo
Shaddadu sai ya mike zumbur! A fusace ya
dube ta ya daka mata tsawa da karfi. Yaldisa
ta razana ainun har sai da hantar cikinta ta
kada. Shaddadu ya ce. "Na gaya miki ba na
bukatar mace a kusa da ni. Ki sauka daga kan
gadon nan tunda dai biyanki na yi kudin komai a
gidan nan". Cikin alamun tsananin mamaki
Yaldisa ta sauka daga kan gadon ta dauki
matashin kai guda daya ta dawo falo ta kwanta
a kasa. Nan fa Yaldisa ta ci gaba da mamakin
wannan bakon saurayi har barci ya sace ta ba ta
sani ba. SHADDADU FA YANA DA GASKIYA.
DOMIN KOMAI TUMBATSAR SADAUKI MATUKAR
YA HADA SHAGALA DA MACE SAI AN YI
NASARA A KANSA. SADAUKI HANTARU IZINA A
GARE MU. Lokacin da gari ya waye sai Yaldisa
ta ji ana tashinta daga barci. Koda ta farka ta
bude idanuntasai ta yi arba da wata mace
198
TASKARNOVELS.COM.NG
tsohuwa tukuf! Zaune gabanta. Cikin alamun
tsananin tsoro ta mike zumbur! Ta koma jikin
bango ta takure jikinta tana mai kallon tsohuwar
a firgice ta ce, "Wace ce ke kuma yaya aka yi
kika shigo gidan nan? Shin kin samu wani ban
da ni a cikin gidan nan ne?" Koda jin wannan
tambaya sai tsohuwar ta bushe da dariya, nan
take ta rikide ta zama Shaddadu. Mamaki ya
sake kama Yaldisa ta ce, "Ashe ma kai ne?
Mene ne dalilin da ya sa ka rikide izuwa siffar
wannan tsohuwa". Shaddadu ya yi ďan guntun
murmushi a gare ta sannan ya ce, "Ai jiya bayan
kin yi barci ya yin dà dare ya raba sai na tashi na
rikide izuwa siffar wannan tsohuwa na ci gaba
da barcina. Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai
ga wadansu hadimai na Sarauniyarku sun shigo
cikin gidan nan da karfin sihirin tsafi, suka kama
bincike. Koda suka shigo cikin dakin barcinki
sai suka ga tsohuwa akan gadonki tana shara
barci har da munshari, sai suka juya suka fice
daga gidan gabadaya. Wannan shi ne dalilin
da ya sa na sauya kamannina don kada a zo a
gan ni na shafa miki kashin kaji. Sa'adda
Shaddadu ya zo nan a zancensa sai Yaldisa ta
cika da tsananin mamaki da murna. Shaddadu
199
TASKARNOVELS.COM.NG
ya dube ta ya ce, to ni yanzu nan zan tafi neman
abin da ya kawo ni garin nan don haka sai dai na
yi miki bankwana. Yana gama fadin hakan sai
ya koma cikin dakin da yai barci ya dauko
Mashinsa na GALILUL HARAS wanda ya rataye
shi a jikin bango sannan ya dauko karamin
Tsuntsun nan nasa na tsafi ya dora shi akan
kafadarsa. Koda ya fito falo Yaldisa ta yi arba
da Mashin da kuma wannan Tsuntsu sai ta dube
shi cikin mamaki ta ce, "Yaushe kuma ka sami
wanna Mashin da wannan Tsuntsun? Ni dai a
sanina jiya ba ka tare da su". Koda jin wannan
tambaya sai Shaddadu ya yi murmushi ya ce,
"Ai babu mai ikon ganin wadannan abubuwa
nawa face da amincewata." Yana gama fadin
hakan sai ya sake rikidewa ya zama wannan
tsohuwa wacce saboda tsananin tsufa sai da ta
rankwafa ta yi doro. Shi ma Mashin Galilul
Haras sai ya rikide ya zama sanda. Tsohuwar ta
dogara sandar ta nufi bakin kofa za ta fita, sai
Yaldisa ta ruga ta sha gabanta ta ce, "Haba ya
kai bako, yaya za ka kwana a gidana na ba ka
abinci kuma na ba ka makwanci duk da dai siya
ka yi amma za ka tafi ban san koda sunanka ba?
Ka yi sani cewa ina da wadansu 'yan tambayoyi
200
TASKARNOVELS.COM.NG
guda uku rak a gare ka wadanda na ke son
amsarsu kafin mu rabu.Tambayata ta farko ita
ce, Mene ne dalilin da ya sa kake neman wata
Jaruma mai suna ZIYA'UL HAK? Tambaya ta
biyu, ina son na sani idan kai namiji ne cikakke,
ko kuwa ba ka da lafiya? Tun da na fara
karuwanci ban taba haduwa da namijin da bai yi
sha'awata ba sai kai saboda kyawuna da
kyawun surata. Tambaya ta uku ita ce, Yaushe
za ka bar wannan garin namu?" Sa'adda
Shaddadu ya ji wadannan tambayoyi sai ya yi
murmushi mai taushi ga Yaldisa ya ce, Game da
tambayarki ta farko, amsarta ita ce, ina neman
Jaruma Ziya'ul Hak ne saboda ta kásance
babbar abokiyar gabata a duniya, muddin zan yi
arba da ita sai na hallaka ta. Amsar
tambayarki ta biyu kuwa, ni namiji ne cikakke
mai lafiya, amma mahaifiyata ta cire mini
sha'awar 'ya mace da karfin sihiri, kuma ta hore
ni da kaidinku tun ina karami don haka, a
rayuwata babu abinda na tsana kuma nake
tsoro sama da mata. Game da amsar
tambayarki ta karshe ita ce ba zan bar wannan
gari naku ba har sai na tabbatar da cewa
abokiyar gabata Jaruma Ziya'ul Hak ba ta
201
TASKARNOVELS.COM.NG
cikinsa. Na barki lafiya sai watarana idan da
rabon mu sake saduwa. Koda gama fadin
hakan sai tsohuwar ta je ta bude kofa ta fice
daga cikin gidan. Ita kuwa Yaldisa sai ta ji ta
kamu da tsananin damuwa da bakin ciki tamkar
wacce ta rabu da wani dan uwata shakikinta
kuma rabuwa ta har abada wacce ba za a sake
saduwa ba. Kawai sai Yaldisa ta ji idanunta
sun ciko da kwalla har hawaye
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 18