Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
babu wani magani da zai iya bani na sha na warke daga wannan ciwo Koda na ji haka sai na fashe da kuka na dubi bokan nace yakai wannan boka kayi sani cewa ina yin wannan kuka ne ba don zan mutum ba ko don bakin cikin abinda yar uwata taui mini kawai inayi ne sbda zan mutu na bar yata gimbiya shalbirat. Ina mai rokanka da ka bani taimkon da zan iya kunbutar da rayuwar yata da mahaifiyata a bayan raina koda kuwa zasu gudu sukama wata nahiyar su cigaba da sabuwar rayuwa koda nazo nan a zancena sai boka yakamu da tsananin tausayina Har hawaye ya zubo masa sannan ya dora hannunsa a cikin aljihu ya dauko wani lailayayen dutse ya miko mini na karba sannan yace ka boye wannan dutse sai 129 TASKARNOVELS.COM.NG nan da Kwanaki casa in: a daren kwana na casa in dinne zaka mutu a lokacin dare ya raba tsakiya: Lallai kafin cikar wannan lokaci ka damkawa yarka wannan dutse dana baka yanzu sannan ka umarceta da taje ta janye mahaifuarta a cikin wannan dare su sulale daga cikin birnin nana: idan har wannan dutse yana hannin yarka shalbirat kuwa tana tare da mahairyarta babu wani tsautsayi da zai samesu har sun fice daga wannan nahiya: koda bokan yazo nan a jawaabinsa sai na kamu da tsananin farinciki: duk da cewar a kwance nake cikin jin radadin ciwo sai dana yunkura na mike zaune da kyar na kama yi masa gdya: kafin na kirawo hadimina nasa a baiwa bokan lada tuni ya bace bat: Ya nanemeshi sama da kasa ya rasa: Nan take na boye wannan farin dutse a cikin aljihun wandona bantaba yarda ani ya ganshi ba duk dacewar ina cikin halim cuta, daga wannan rana kullum sai yar uwata Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin cikina bisa lalura da nake ciki 130 TASKARNOVELS.COM.NG : daga wannan rana kullum sai yar uwata Juzairat tazo turakata ta zauna sai ta sani a gaba ta na ta kuka tana nuna matukar bakin cikina bisa lalura da nake ciki. : Dai dai rana daya ban taba nuna mata cewa nasan kaidin data kulla mini ba: Sai dai kawai idan na kalleta na zubar da hawaye takaici: ba komai ne yasa nake zubar da hawayen takaici ba face nayi matukar mamaki bisa yadda wacce nake kauna fiye da komai a duniya ita ce take son ganin mutuwata: Har izuwa wannan lokacin da nasan cewa ita ce ta samini wannan ciwo ban ji na tsaneta cikin zuciyata ba sbda tun muna yara kanana na taso da tsananin sonta: A dalilinta nayi yake yake ba adadi: Na bata da abkaina sarakai wadanda suka kasance aminena sbda sun nemi aurenta basu samuba: hakan ta faru ne sbda na bata damar tazabawa kanta miji: Muna yara juzairat ta taba taka dan aljani suka shafeta: A kokarin samo mata magani sai dana bar gida na shekara hudu a cikn daji har na kusan rasa rayuwata 131 TASKARNOVELS.COM.NG domin da na dawo gida sai da na shekara guda akwance ina jinya kuma an bata maganin da nakawo take ta warke daga cutar mutuwarrabin jiki Yau gashi an wayi gari Juzairat suk ta manta da wannan wahalar da na sha a dalilinta wai ita ce ma take neman rayuwata sbda kawai kwadayin mulki kuma har takeson ta sabauta iyalina. yake yata yanzu zan baki wanan fari dutsen wanda boka ya bani: Da zarar kin karbeshi sai ki ruga izuwa dakin mahaifiyarki ki labarta ma duk abinda na gaya miki yanzu domin ku gudu: Koda gama fadin hakan sai sarki ya zura hannunsa acikin aljihun wando ya dauko wannan farin dutsen ya miko mini: HANNUNAna karkarwa kuma ina kuka na karbi dutsen sannan na fada kan kirjinsa na kankameshi ina mai sake fashe wa da matsaicin kuka ina cewa ba zan iya rabuwa da kai ba ya kai abbana gwara na tsaya aljani ya kamani ya kaini inda bazan sake ganin komai 132 TASKARNOVELS.COM.NG da kowa ba har izuwa ranar ajalina tunda dai kaima mutuwa zakayi koda jin haka sai hankalina ya dungunzuma ya shiga rarrashina yana bani baki: sai da na shafe sa a biyu ina kankame da shi ina kuka da kyar ya shawo kaina na amince na sauka daga kan kadon rike da wannan farun dutsen na sihiri a hannuna ina waugensa ina zubar da hawaye shima yana daga mini hannun hawaye na kwararowa daga cikin idanunsa. . Nima nan take idona ya ciko taf da hawaye dan haka sai na tsaya cak da yin typing din ayi hak'uri jin MAZAN JIYA Littafi na Hudu (4) Part L Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Haka dai na daure na fice daga cikin turakar na ruga izuwa turakar mahaifiyata a cikin wannan dare. Duk inda na gifta a cikin gidan sai naga dakaru suna bina da kallo cikin mamaki. Haka dai na cigaba da gudu har na isa cikin turkar mahaifiyata na kunnan kai izuwa cikin turakarta: Ina shiga sai na iske mahaifiyar tawa zaune a gefen gado idanunta cike da hawaye kuma ko kadan babu alamar tayi barci 133 TASKARNOVELS.COM.NG a kwayar idanunta: Al amarin da yai matukar bani mamaki kenan na karasa gareta jikina a sanyaye: HAR NA BUDI baki zan yi mata bayanin abinda ke tafe dani sai ta rigani tace duk abin da ya faru yanzu tsakaninki da m Amahaiki naji kua na ganin domin ina labe a kofar dakin ina kallonku baku sani ba Yake yata kiyi sani cewa zuciyarta ta karaya domin nasan cewa abi ne mawuyaci mu tsira daga sharrin Juzairat: Ni kam na zabi na mutu tare da mijina yau a cikin wannan dare nan da cikar sa a guda inyaso ke ki tserar da kanki koda jin wannan batu sai na fada kan kirjin mahaifiyata na fashe da sabon kuka ina mai cewa ai kuwa sai dai nima na tsaya na mutu tare da ku din da dai na tafi wata nahiyar daban na zauna inda ban ssan kowa ba ba a sannani ba inda babu uwa kuma babu uba: Hakika rayuwar da babu masoyi ai ba ta da wani amfani a doron kasa Koda mahaifiyata taji wannan batu sai ta mike tsaye zumbur cikin 134 TASKARNOVELS.COM.NG firgici ta sureni da gudu muka fito daga cikin turkarta: Nan fa ta direni kasa ta kamo hannuna ta jani muka cigaba da gudu muka nudi kofar fita daga cikin gidan sarautar gaba daya: Har a sannan ina rike da wannan farin mulmullen dutse na sihiri wanda mahaifina ya bani: muka cikin gudun ne muka jiyo alamar wata irin gagarumar iska ta biyomu a baya tana kokarin cafkomu amma ta kasa: Sai da ya rage saura bai fi taku biyar ba tsakaninmu da bakin kofar wacce tuni masu gadi sun firgice sun budeta suma sun cika wandunansu da iska sun yi waje: Kawai sai muka ji wani irin gurnani mai tsananin ban tsoro a bayanmu. Cikin tsananin firgita ni da mahaifiyata muka waiga baya ai kuwa sai muka yi arba da aljani Raugatul Aguwanu: Nan takemuka razana ainun: Faruwar hakan ce tasa nayi tuntube na fadu kasa: ina faduwa sai wannan dutse dake tafin hannuna ya subuce ya gangare kasa can gabana: kafin na mike ba ruga inda dutsen yake sai kawai naji an figeni anyi sama dani ana ta kyalkyala wata dariya mugunta: Abinda idanuna kawai suka iya hangowa sa adda na kallo kasa shine: Haukacewar mahaifiyata tana 135 TASKARNOVELS.COM.NG ihu tana cisge gashin kanta kuma tana sambatu. Daga nan sai jinayi an lulaka dani izuwa can kololuwar samaniya a sannan ne jiri ya debeni: Lokacin fa na farka na bude idanuna sai na tsinci kaina a cikin wannan dan karamin keji da ke rataye a saman kogon aljani RAUGATUL AGAWANU: a firgice na mike tsaye na kama kai kawo cikin kejin: a sanan ne na gane cewa an asirceni na zama yar mitsitsiya: Nan take na kwarara uban ihu kuma na fashe da matsanaicin kuka: lokacin da Gimbiya Shalbirat ta zonan a Labarinta sai hawaye ya zubo mata ta dubi sadusa Halyal tace wannan shine labarina don haka ni na sancewa anan dajin zan gama rayuwata tunda ba zaku iya kubutar dani ba daga hannun wanan azzalumin aljani kuma ko dama kin kubutar dani bani da sauran sha awar cigaba da rayuwa tuda bani da sauran masoyi a doron kasa: Koda jin wannan batu sai tausayin shalbirat takama boka sadusa da dansa halyal har idanun su suka ciko da kwallah: kawai sai halyal ya dube shalbiyat yace yake wannan ma abociyar kyawu kayi sani cewa baki databbacin cewa mahaifiyarki tana raye ko ta mutu? Saboda 136 TASKARNOVELS.COM.NG haka bai kamata ki cire sha awar ci gaba da rayiwa b a doron kasa, bayan haka ina mai tabbatar miki dacewa mahaifina da muke tare da shi a yanzu zai iya kubutar dake daga hannun wannan aljani kua na yi miki alkwari komai dadewa sai na rakaki har izuwa birninku kin sadu da mahaifiyarki muddin tana raye: Haka kuma indai juzairat na nan a raye sai kin dauki fansa akanta: Sa adda Gimbiya Shalbiraat taji wannan bau sai ta girgiza kai tace wannan albishir naka daidai yake da tatsuniya a cikin kunnena ko kumma na kirashi da mafaarki da va zai taba zama gaskiya ba: Koda jin haka sai boka sadusa yayi dariya sannan ya dubi shalbirat yace ke yarinya abinda dana yafada miki gaskiyane amma bari na fara nuna miki karfin aikina tun daga yanzu Gama fadin hakan ke da wuya sai sadusa ya karanta wadansu dalasiman tsafi guda bakwai ya tofa akan tafin hannunsa na hagu sannan ya dafa kan shalbirat 137 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take Shalbirat ta dawo cikakkiyar surarta ta budurwa mai tsananin kyauwun diri da sura maimakon yadda ta kasance a da yar mitsitsiya: Shi kansa sadusa sai daya dimauce bisa ganin tsananin kyawun nata: Yayin da shalbirat taga ta dawo izuwa chakkiyar surarta ta mutum sai ta cika da tsananin farin ciki ta kama kyakyal dariya kamar bazata daina ba, sai daga can ta nutsu ta dubi boka sadusa ta durkusa har kasa bisa guiwoyinta takama yi masa gdya shi kuma sai ya kama kafadunta ya yasheta tsaye suka fuskacin juna yana mai yi mata murmushi yace wannan taimako dana yi miki ba komai bane face taimakon kaina domin kema akwai muhimmiyar rawa da zaki taka nan gaba bisa bukatar da ta fito damu daga birninmu A gobe ne zan rabaki da wannnan daji kuma idan mun isa can bakin kogin bahar sufiya za ki rabu da wannan azzalumin aljani har abada: yanzu sai kuzo mu cigaba da yawatawa a cikin wannan daji har izuwa lokacin da aljani Raugatul Aguwanu ya bukata: Koda gama fadin haka sai boka sadusa ya kunna kai izuwa cikin 138 TASKARNOVELS.COM.NG dajin cikin sauri shalbirat ta kama hannun Halyal suka taja shi suka bi bayan boka sadusa Haka dai su boka sadusa suka yi ta yawo a cikin dajin Darul HusHushul Maut; Shalbirat ta wucce gaba tana yi musu jagora har suna mamaki yadda ta lakanci hanyoyin dajin: Ai kuwa sai suka yi ta ganin abubuwan al ajabi wanda basu taba tsamamanin zasu gani ba: Abinda suka gani kuwa shi ne gaba daya bishiyoyin dajin na yan yan itatuwa ne iri iri sannan kuma bishiyoyin da ruwa ke zuba daga cikinsu mai haske da dadin dandano, gaba daya dajin a cikin ni ima yake kuma kowanne wuri irin tasa ni imar dabam data gaba: Duk inda mutum ya shiga ba zai ji zafi ba kuma ba zai ji sanyi ba sannan a duk inda zaka kwanta wata irin ciyawa ce a lullbe mai tsananin laushi kuma hankalo kwance mutum zai yi kwanciyarsa babu tunanin wani kwaro zai cijeshi ko kuma wata muguwar dabba zata kawo masa hari 139 TASKARNOVELS.COM.NG Nan take sadusa Halyal da shabirat suka tsinko yayan itatuwa kala kala masu dadi suka sami wuri suka zauna suka kama ci suna hira har sai da suka koshi sannan suka mike suka cigaba da yawo abinsu: Shalbirat Dai a wannan rana ji ta yi taamkar an tsamota daga cikin gagarumar wuta an sanyata a cikin ruwan sanyi sbd farin ciki Haka dai suka wanzu suna yawo har suka gaji suka kwanta suka kama barci: Al amarin aljani Raugatul Aguwanu kuwa tunda ya sha wannan giya yayi tatul kama barci bai farka ba sai da dare ya raba: A firgice ya farka zuciyarsa na dukan uku uku: Cikin hanzari ya mike tsaye ya dauko madubinsa na tsafi ya shafeshi: Nan take yaga Hoton Shalbirat Sadusa da Halyal a cikin dajin a kwance suna ta shara barci. koda yaga Shalbirat a cikin cikakkiyar surarta: ta mutum sai ya razana ainun ya kuma tabbatar da cewa lallai boka sadusa ya cika hatsabibi domin shi a tunaninsa baza a taba samun bokan da zai iya karya wannan asirin ba: Nan dai zuciyarsa ta kama sake saketana mai gaya 140 TASKARNOVELS.COM.NG masa cewa: AI KAWAI YANZU TUNDA SU BOKA SADUSA BARCI SUKEYI YAJE YA KASHESU YA DAUKE SHALBIRAT YA SAKE MAI DA ITA YAR MITSITSIYA YA SATA A CKIN KEJINTA: wata zuciyar kuma sai ta ce da shi TO IDAN KUMA KA KASHE WANNAN BOKA WAYE ZAI TSERAR DA KAI DAGA SHARRIN SARKI DA ZAI MALLAKI KAYAN YAKIN MAZAN JIYA? TABBAS IDAN KA BIYEWA SON ZUCIYARKA ZAKA YI CIN DARE DAYA NE KUMBURIN CIKI: ZAI FI KYAU KA TSAYA KA GA IYA KOKARIN DA WANNAN HATSABIBIN BOKA ZAI YI MAKA. haka dai aljani Raugatul Aguwanu yayi ta wasi wasi acikin zuciyarsa har dai daga karshe ya yanke shawarar ya jira abinda zai faru a gaba: Kashe gari da sassafe su boka sadusa suka farka daga barci kawai sai suka ga aljani Raugatul Aguwanu zaune a can gefe daya ya zura masu idanu: koda suka tashi zaune sai Raugatul Aguwanu ya risina ga boka sadusa yai gaisuwa sannan ya dubi shalbirat ya sake duban sadusa yace ya shugabana anya kuwa bakayi mini gaggawa ba? Ai ina ganin cewa bai 141 TASKARNOVELS.COM.NG kamata ka ai da shalbirat izuwa ainahin siffata ba tun yanzu tunda ban gamsu da cewar za ka iya warware mini matsalata ba Koda jin wannan batu sai boka sadusa ya murtuke fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa ya dakawa Raugatul Aguwanu harara yace shin kaine ka fini sani abinda yafi dacewa muyi ko kuwa nine? Raugatul Aguwanu ya sunkui da kansa kas ya ce ka gafarceni ya shugabana mantawa nayi boka sadusa yai murmushi yace yanzu nake son ka daukemu mu ukun nan domin mu tafi izuwa can sansani yaki wato can baki kogin bahar sufiya : koda jin haka sai idanun Raugatul Aguwanu suka zazzaro ya kamu da tsananin tsoro yace haba ya shugabana ya ya zaka ce na kaimu izuwa inda ajali yake? Ina mai tabbar maka dacewa masifar da ke bakin kogin bahar sufiya a yanzu babu kamarta a ko ina a cikin duniya 142 TASKARNOVELS.COM.NG koda jin haka sai boka sadusa yayi murmushi sannan yace ai ba wai ina nufin muje har inda ake yakin bane zaka sauke mu ne acan bayan kogin bahar sufiya nesa da inda ake fafata yakin sannan kaje kayi mana leken asiri bisa abinda ke faruwa abinfa nake bukata kawai shine nagane bangaren da suke samun nasara: Da zarar na gano hakan akwai a sihirin da zanyi daga inda muke mu dauko Takobin SAIFUL LUJA RA a karkashin kogin ba tare da su sarki dujalu sun sani ba mu bace daga wajen kaga kenan sun sha wahalar banza kuma sun kashe junansu a banza wato kura da shan bugu gardi da kwashe kudi koda boka sadusa yazo nan a zancesa sai aljani Raugatul Aguwanu ya kura masa idanu 143 TASKARNOVELS.COM.NG cikin alamun rashin yarda yai shiru yana tunani da nazari. Daga can sai ya ce kai boka nifa ina ganin cewa kazo mini da zance na rainin hakali: Yaza ai kace zaka iya dauko takobin saiful lujara da karfin sihirinka alhalin wadanda suka fika karfin sihirin nesa ba kusaba sarki dujalu da sarki maharaz tuntuni sun kasa daukota? Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda takobin take acikin karkashin tekun: Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi tsaron dake inda takobin take yafi gaban hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya gani kawai. Zan ci gaba. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. MAZAN JIYA Littafi na Hudu (4) Part M Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Koda ma dayansu ya sami nasarar wannan yaki sai ya sha bakar wahala kafin yagano inda takobin take acikin karkashin tekun. Kai ni ga yadda mana sami tarihi cewa aka yi tsaron dake inda takobin take yafi gaban hasashen mai hasashe sai dai abinda ido ya gani kawai. koda jin 144 TASKARNOVELS.COM.NG wannan batu sai boka sadusa ya murtuke fuskarsa yace to shikeanan idan har baka aminta da abin danake gaya maka ba sai ka yankewa kanka hukunci. kofa dai yanzu my yaki juna ni dakai wandaya kashe dayan yayi abinda yaso: ko kuma murabu salin alin kowa ya kama gabansa: amma kasani dace idan muka rabu salin alin har abada ka rabuda Gimbiya Shalbirat kenan baza kasake mallakarta ba: lokacin da boka sadusa yazo nan a zancesa sai hankali aljani Raugatul Aguwanu ya dugunzuma ainun fiye da ko yaushe yarasa abinda ke masa dadi a duniya, nan fa ya kasa zaune ko tsaye ya rinka kai kawo. daga can sai ya dubi sadusa yace ka bani sa a uku na koma can kogona nayi bincike. da tunani tukkunna: sadusa yai murmushi yace jeka nabaka tsawon sa a biyar ma: nan take aljani Raugatul Aguwanu ya bace bat tamkar kiftawar ido: A Sannan ne shalbirat ta dubi boka sadusa cikin alamun tsoro tace yakai abul halyal anya kuwa kana ganin cewa Raugatul Aguwanu zai amince ya daukemu yakaimu bakin kogin bahar sufiya? To wai shin ma meye hikimarka ta zuwanmu can din alhalin kasan cewa sansani ne na 145 TASKARNOVELS.COM.NG mutuwa? Sadusa yai ajiyar zuciya sannan yace kiyi hakuri yake wannan yar sarki: Ki tuna cewa mu bamu baki labarin mu ba kamar yadda kika ban mu naki sakamakon cewar babi isashen lokaci na yin haka: Ni dai kawai abinda na sani shine sau tari sai ka tari aradu da ka sannan kake fita daga cikin wata masifar: akwai abin da ya baromu da kasarmu kuma bukatarmu ba zata biya ba face mun dangana da bakin tekun bahar Sufiya inda ake yin wannan yakin: kuma ki rungumi kaddara har izuwa sa adda zamuje can dinko bakomai dai gwara ki mutu acan sansanin yakin da dai ki mutu a hannun wannan azzalumai alajni: kodajin wannan batu sai shalbirat ta jinjina kai tayi shiru bata kara cewa komai ba * * *: BIRNIN SARKI DUJALU: ACAN gidan sarautar sarki dujalu kuwa tundaga ranar da kunyaga lazimat ta tafi neman hanyar da Gimbiya Hursiya zata sami damar komawa sansanin yaki a cikin kwanki kadan bata dawo ba har kwanaki biyu da aka dirba mata suka cika: A dare kwana na biyun ne hankalin 146 TASKARNOVELS.COM.NG Gimbiya Hursiya ya dugunzuma ainun ta kasa zaune ko tsaye: fara zubar da hawaye domin ta saddakar da cewar har abada baza ta sake ganin dan uwanta ba sarki dujalu ba, babu abinda yake kara fusatata facw a duk sa adda ta leka wajen turakarta ta cikin taga sai ta hango aljani barzaru yana shawagi a saman turakae yana kewayeta don tabbatar da tsaro wato dai ta san cewa gadinta yake yi babu yadda za ayi wani ya iya zuwa yatafi da ita batare da yagani ba: Gimbiya Hursiya na cikin wannan hali ne ta jiyo alamar takun sawu an nufo kofar turakar Ta kawai sai ta zuba idanu akan kofar shigowar: abinda ta sani shine koma wanane ya taho in dai bai kasance daya daga cikin kuyangitaba ko bayinta aljani barzaru ba zai barshi ya shigo ba: Ashe ba wani bane ya durfafo turakar ta ba face kuyanga lazimat rike da wani jan fure mai kamshin gaske fisa faranti: yayin daya rage bai fi saura taku biyar ba tsakanin kuyaga lazimat da kofar turakar gimbiya sai kawai taga aljani barzaru ya fado juf a gabanta; ko Gezau batayi ba ta dubeshi a fusace yace meye haka zaka sha gabana alhalin kasanni na sanka ko kuwa ni 147 TASKARNOVELS.COM.NG bakuwa ce a gidannan? Aljani barzaru ya daka mata tsawa wacce tasa hanjin cikinta ya kada hannunta yakama karkaewa har farantin dake hannunta ya fadi kasa tayi sauri daukeshi: Barzaru yadubi wannan fure dake kab faranti da kyau sannan ya dubi kwayar idanun lazimat ko zai ga alamun rashin gaskiya a tare da ita sanna ya ce: ke tsohuwar makira: ni fa ban yarda dake ba ina kyautata zaton cewa akwai wani kullin boye da kuke shiryawa ke da gimbiya. shin baku san cewa ina lura da dukkan motsi ku ba? Yau kwanaki biyu kenan rabonki da turakar gimbiya alhalin kullum kuna tare baku taba rabuwa ba sai sa adda sarki ya tafi da gimbiya bakin tekun bahar sufiya: lallai akwai alamar cewa ta turaki ne kiyi mata aikin ne don haka ban yarda da wannan furen da kika kawo mata ba: bani shi na koneshi: Har aljani Barzaru ya yunkura zai dauke fure sai ya jiyo muryar gimbiya Hursiya tana mai daka masa tsawa; ba shiri ya janye hannunsa: nan take Hursiya ta dako kofar turakarta ta fito waje cikin tsananin fusata ta dubi aljani barzaru tace au sbda samun dama shine zaka wuce gona da iri a cikin aikin naka na gadinna? Shin ka manta ne 148 TASKARNOVELS.COM.NG cewar tun ina yarinya karama babu abinda nakeso sama da jan fure? Ka sani cewa labari ne yazo mini cewa an sami sabon samfarin jan fure a can birnin zandal shi ne na aikata taje ta siyo mini shi kuma ka san cewa dole ne mutum ya shafe kwana biyu kafin yake birnin zandal ya dawo ka dubi wannan fure da kyau kaga ni zaka ga cewa yasha bamban da irin sauran janjayen furen da ake kawomini: Koda jin haka sai aljani barzaru ya kurawa wannan fure idanu nan take kuwa ya ga lallai fure ne dabam domin bai kasance ja zallah ba akwai ratsin ruwan dorawa a jikinsa: koda ganin hakan sai ya zube kasa a gaban Gimbiya ya kama tuba; ko kallinsa Gimbiya batayi ba ta kama hannin kuyanga lazimat taja izuwa cikin turakar suka rufe kofa suka kulle: A sannan ne aljani barzaru ya mike tsaye ta bude fuka fukansa yai sama yana mai cigaba da shawagi yana kewaya saman turakar ta gimbiya don tabbatar da tsaro: ABINDA BAI SANI BA SHINE AN KULLE KOFA DA BARAWO KUMA BAWANI BANE BARAWON FACE 149 TASKARNOVELS.COM.NG WANNAN JAN FURE WANDA KUYAGA LAZIMAT TA SHIGA DA SHI CIKIN TURAKAR GIMBIYA: Lokacin da Gimbiya Hursiya ta ja kuyanga lazimat izuwa cikin turakarta sai suka shige har can cikin daki barcinta: Suna shiga sai lazimat ta rufe dakin gami da tagogi sannan ta fiddo wani turare wuta na tsafi daga cikinAljihun rigarta: take turarren wuta ya kunna kansa hakinsa ya cika dakin gaba daya tamkar hazo ne ya shigo dakin: faruwar hakan ke da wuya sai wannan jan fure da ke kan faranti wanda lazimat taxo dashi ya rikide ya zama wani dan wadan aljani mai kwalelen kai wanda tsawonsa bai wucce kamu biyu ba. Tunda gimbiya Hursiya ta zo duniya bata taba ganin mitsitsin wada kamar saba sai kace yar tsana: yana da kwala kwala idanu kamar na mujiya hancinsa kuwa wakakeke ne kamar na a zura kwai a ciki: yana da dan mitstsin baki tamkar kwallon dabino bazai iya shigewa ba: kafafuwansa kuwa yan dugul dugul ne kaman na agawagi: koda bayyaynar wannan aljani sai gimbiya Hursiya ta fadawa kainun taja da baya cikin sauri tana mai fadawa kan gadonta kamar za ta kwalla ihu: cikin tsananin razana ta dubi 150 TASKARNOVELS.COM.NG kuyanga lazimat tace sabda me zaki jeki nemo mini wannan aljani n mai ban tsoro haka? Koda jin ewannan tambaya sai kuyanga lazimata tayi murmushi sannan tace ya shugabata wannan aljani ba mai cutarwa bane kawai dai halittarsa ce haka: nantake dan wadan yadaka tsalee daga fartanti dayake ya dure kasa daf da gadon Gimbiya yai sujadda agareta yace sunana boka RADIYAL IBN ZAILUR: INA zaune a can nahiyar da ke kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina nazo domin na biya miki wannan bukata amma bisa sharadi guda?? ANAN ZANDAKATA SAI KUMA IN ALLAH YAKAIMU GOBE DASAFE DAFATAN ZAN IMIN AFUWA NA KWANA BIYU DA AKAJENI. Da fatan an tashi lafiya, sannan duk wanda yake son complete zai iya tuntubata ta wannan number 08138873799 kira ko whatsapp. INA zaune a can nahiyar da ke kudanci taku ne sako ya riskeni cewar kina neman wanda zai kaiki can sansanin yaki na teku bahar sufiya shiyasa na taso da kaina nazo domin na biya miki wannan bukata amma bisa sharadi guda:?? Cigaba: Page 125 Koda jin 151 TASKARNOVELS.COM.NG wannan jawabi sai Gimbiya Hursiya ta tashi zaune tana ;mai gyara zama sannan ta dubi boka Radiyan ciki murmushi tace ina sauraronka ya kai wannan babban boka: Radiyan yayi gyaran murya sannan yace a halin yanzu nayi bincike na gano cewa a duk fadin duniya babu wani aljani dazai iya zuwa bakin kogin bahar sufiya a cikin yan kwanaki kadan kafin a gaa gagarumin yaki da ake fafatawa acan face aljani daya wanda ake kira da suna Raugatul aguwanu wanda ke zaune a cn dajin darul Hushshul maut: Dajin ne wanda sama da shekaru bakwai baya mutane aljanu dabbobi da tsuntsaye da kwari suka daina shiga ko wanzuwa a cikinsa amma a halin yanzu wani takadarin boka dake nan garin mai suna sadusa ya karya kofin da ke dajin ya shiga har ya sadu da aljani Raugatul aguwanu zai daukeshi a gobe su tafi izuwa bakin kogin na bahar sufiya: zan iya kaiki can dajin Darul Hishushul maut a yau dinnan acikin abinda wuce sa a biyar ba kuma zamy shiga ne a sirrance ba tare da mun bari su aljani Raugatul aguwanu sun ganmu ba ko suji motsinmu ba: Nida ke zamu shiga cikin kunnen aljani 152 TASKARNOVELS.COM.NG Raugatul aguwanu ne muyi zamanmu a ciki a lokacin da yake barci: Ba zai taba sanin da zamanmu ba a cikin kunnen nasa muddin zamu jure yi masa susar kunne domin a duniya babu abinda yake sa shi yamanta da koai face susar kunne: Page 126 zidane kd A haka za a tadi dau izuwa bakin tekun bahar sufiya ba a sani ba: Sharadin dake tsakanina dake shi ne ba zan yarda na kaiki inda aljani Raugatul aguwanu yake ba face kinyi alkawari cewar idan dan uwakinki sarki dujalu ya sami nasarar cin yaki kuma ya dauko takobin Saiful Lujara zaki sa ya maisheni daya daga cikin manya fadawansa na hannun dama: lokacin da boka radinya yazo nan a jawabinsa sai hankalin gimbiya Hursiya ya dugunzuma tayi shiru tana tunani da nazari al amarin ta rasa abinda zatace: daga can sai ta dago kai ta dubi boka radiyan tace yakai wannan boka kayi sani cewa ina da wadansu yan tambayoyi a gareka kafi na aminta dakai: da farko dai ina son kaga mini dalilin da yasa boka sadusa yaje ya hada kai da aljani Raugatul aguwanu domin yaje 153 TASKARNOVELS.COM.NG sansanin yaki? Tambaya ta biyu itace ta ya kake tunanin zaka iya fitae dani daga cikin gidan sarautae nan har ka kaini dajin darul hushushul maut alhalin aljani barzaru na shawagi a saan turakata yana gadina? Tambaya ta uku wacce itace ta karshe yaza ayi muyiwa aljani

Chapter 6 of 18