Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels TASKARNOVELS.COM.NG 1 TASKARNOVELS.COM.NG MAZAN JIYA 4 MAZAN JIYA Littafi na biyu 4 Part D Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey MAZAN JIYA! (4) Sai da sarki dujalu ya shafe sa.a shida cif yana baiwa hursiya lbrin sadauki shaddadu na birnin kufa, amma ba ta kosa ba da jin labarin har ya zamana cewa dare ya raba amma ko gyangyadi bata fara ba. Shi kuwa sarki dujalu a wannan lokaci bakinsa ya gaji da surutu kawai so yake yayi shiru don ya huta. 2 TASKARNOVELS.COM.NG Dama ga tsananin gajiyar yaki gami da tsamin jiki da radadin raunikan jikinsa sun dameshi. Kwatsam! Sai Hursiya taji sarki dujalu yai shiru ga barin zance.. Cikin tsanani damuwa ta dubeshi ta ce ya kai dan uwana ina dalilin yin shirunka? Ina mai rokonka bisa girman iyayenmu daka cigaaba da bani wannan lbr mai dadi domin ina son naji yadda karshensa zai kasamce kamar yadda na ji na JARUMI HANTARU. Koda jin wannan batu sai sarki dujalu yayi doguwae hamma gami da murmushi sannan ya dubi hursiyya yace haba yake yar uwata ai idan kika ce na ci gaba da baki wannan lbr har sai na je karshensa ba kiyi min adalci ba sbda koda zamu kwna muna yi ba zai kare ba. Ki sani cewa duk a cikin labaran uku babu Hikaya mai tsawonta tunda gashi dai har yanzu ba ta kammalu ba. Kiyi hakuri idan mun yi tsawon rai nan gaba bayan wanna yaki na karasa miki wannan labari. Lallai akwai bukatar na kwanta domin na 3 TASKARNOVELS.COM.NG sami isasshen hutu da bacci domin na sami kuzarin domin iya ci gaba da yaki. Idan gari ya waye. Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya kwanta akan shimfidarsa yaja mayafi ya lulluba. Faruwar hakan ke da wuya kuwa sai barci ya sace shi, koda ganin hakan sai itama Hursiyya ta kwanta akan tara shimfidar taja mayafi kuma ta rintse idanu domin ta yi barci, amma sai barcin ya gagara sakamakon tunani da fargabar yadda makomar wannan gagarumin yaki zai kasance idan anci gaba dashi a gobe ba ta sami damar rintsawa ba sai da suba ta kusanto.. Sai da gari ya waye rana ta take amma sarki dujalu da yar uwarsa gimbiya Hursiyya ba su farka ba daga barci... A wannan lokacin gaba dayan mutanen nasu da ke sansanin tuni sun farka daga barci an yi kalaci kuma an gama shirin ci gaba da yaki sahun aljanu dabam da na mutane.. A wannan lokacin manyan dakarun sarki dujalu matinu da ratiju sun tsaya a gaban rundunar tasu suna jiran fitowar sarki dujalu domin ya bayar da 4 TASKARNOVELS.COM.NG umarni.... Tsakanin rundunar sun sarki dujalu da ta su sarki Hamraz bai wucce taku dari biyu ba sbda dama dukkaninsu abakin kogin na bahar sufiyan suka yada sansani., kowanne bangare suna hango abokan gabarsu... Lokacin da matinu ta hango abokan gaba sun gama nasu shirin tsaf kuma sarki maharaz sadauki inmal da sadauki hibru na tsaye agaban rudunar tasu sun zobo ido izuwa ga nasu matinu kawai jira suke suga sarki dujalu ya baiyana agaba,,. Cikin tsananin damuwa matinu ya dubi dan uwansa ratiju yace ja ruga izuwa tantin sarki ko lpya.. Kafin matinu ta gama rufe bakinsa tuni ratiju yaruga izuwa can tanti sarki yake.. Yana isa ya dubi dakarun da suka Kewaye tantin don tabbatar da tsaron yace kuyi min iso a wajen sarki. Kafin daya daga cikinsu tace kala sai suka jiyo gyaran ,muryar sarki... Nan take sarki dujalu ya fito daga cikin tantin a cikin gagarumar shigarsa ta yaki kuma fuskaraa cike da annuri ya dubi rantiju cikin murmushi yace ya kai babban jarumi ka kwnatar da hankalinka kayi sani cewa yau ba rana bace ta gaggawa domin kuwa a yau ne za ayi tata kare! Ko dai muyi nasarar 5 TASKARNOVELS.COM.NG wannan yaki ko kuma mai abonka gabar mu su samu wata kila ayi ragas ina mai tabbar muku da cewa yakin da muka yi jiya share fage ne ko kuma wasan yara akan wanda za ayi yau.: (TAB IJAM! DUK BAKAR GUMURZUN DA AKAYI KUNJI PA WAI WASAN YARA YAKI CEWA TO KUBIYO NI MUJI YAWANNAN NA YAU ZATA KASANCE KENAN TIN DA YACE WANCAN WASA YARAN NE SULEIMAN ZIDANE KD.) Yaune maza zasu gane kurensu. Yau ne kasa da taiku zasu sha jini suyi gyatsa, kuma a yaune tarihin jarumta zai kafa kansa a bakin teku. Maza ka koma can bakin filin daga ka gayawa rundunarmu cewa gani nan tafe yanzu kuma ina zuwa za a fara wannan yaki. A jirani zan gana da yar uwata Hursiyya. Koda jin haka sai ratiju ya juya da sauri kuma ya falfala da matsanaicin gdu domin yaje ya isar da wannan sako. Tafiyarsa ke da wuya sai sarki dujalu ya juya ya fuskanci yar uwarsa Hursiyya suka kurawa juna idanu. Nan take duk biyun idanunsu suka ciko da kwlla. Hawayen sarki dujalu ne ya fara zubowa sannan nata. Sarki dujalu ya sa hannu ya share hawayen nasa yace yake yar uwata kiyi sani cewa wannan hawayen nawa bai zubo ba 6 TASKARNOVELS.COM.NG sboda tunanin zamu rabu ba. Tabbas ni na san ba zan mutu ba a wannan yaki to amma taki rayuwar ce bani da tabbacin zata tsira. Babu mamaki wannan gani da nake yi miki shi ne na karshe. Hanya daya ce nake zaton zan iya tserar da rayuwarki wato nasa a dauke ki yanzy a mayar da ke cikin birninmu domin ciki gaba da tafiyar da mulkin kasata. A hakan ma bani da tabbacin birnin nawa zai ci gaba da wanzuwa.. Koda sarki dujalu yazo nan a zancesa sai wani sabon hawaye yasake gangarowa daga cikin idanu Hursiyya ta dubeshi tace haba yakai dan uwana ashe har ka manta da bayanin da nayi ,maka kenan a jiya da daddare?? Nifa bazan iya rabuwa da kai ba a yanzu sai dai a ci gabada wannan yaki a gaban idanuna idan ma mutuwa zaka yi mu mutu tare domin muddin bana tare da kai ba zan taba samun sukuni da kwnaciyar hankali ba... Koda jin hakan sai sarki dujalu ya juyawa Hursiya baya a lokacin da shima hawayen ya sake subuto masa ya ce ai kuwa sai dai kiyi hkr domin rabuwarmu a yanzu ta zama dole.. Yana gama fadin hakan yaka tafiya ya nufi inda sansanin dakarunsa suke.. Koda ganin hakan 7 TASKARNOVELS.COM.NG sai goimbiya Hursiyya ta yunkura da nufin ta bishi ta gudu kawai sa taji an sureta an yi sama da ita tamkar shaho ya dau shirwa. Wata irin iska mai karfi taji tana busota a sama. Koda ta dga kanta sama sau ta ga ashe wani aljanu ne mai suna BARZARU ya dauketa wanda ya kasance babban hadimin sarki dujalu. Koda Hursiya taga barzaru ya juya da ita baya don barin sansanin yakin gaba daya sai ta kwlla ihu, ta fashe da matsanaicin kuka cikin sbda ta gane cewa dan uwanta sarki dujalu ya shammace ta ne ya sa a mayar da ita can gida domin ta tsira da ga masifar wannan yaki. Haka dai Hursiya ta ci gaba da ihu tama rusa kukan bakin cikin har aljani barzaru ya luluka da ita a cikin gajimare suka kule aka daina hangosu.. * * * ACAN Sansanin yaki kuwa lokacin da sarki dujalu ya iso filim dagar ya tsaya a tsakiyar matinu da ratiju sai aka fara kallon kallon tsakanin rudunar tasu da ta su sarki Maharaz. Kowanne bangare yana da jinsin mutane da na aljanu dukkaninsu a cikin gaagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini da ban tsoro. Wasu aljanun ma ko kallomsu mutum yayi nan take yake iya samin tabin hankali mai dakakkiyar 8 TASKARNOVELS.COM.NG zuciya zai tsure da gudawa ya cika wandonsa da iska. A dai dai wannan lokacin ne mulaifa ta matso gaban inmal ta tsaya tana mai rike da takobi, cikin tsananin mamaki inmal ta dubeta yace yake masoyiya mene ne yakawo ki nan filin yakin alhalin sarki ma yace ki yi zamanki a cikin tanti har izuwa karshen Yakin? Sa.adda mulaifa taji wannan tambayan sai tayi murmushi tace ai idan har na zauna a cikin tanti na bar masoyina yana fafatawa anan filin daga kuma na bar mahaifina yana gwagwarmaya ban cika jinin sarauta ba kuma ban yiwa soyayya adalci ba. Idan har a wannan yaki zaku mutu to ina fatan na mutu tare da ku. Koda Gimbiya mulaifa tazo nan a zancenta sai sarkin yaki hibru ya taho gareta domin ya rarsheta ya mai da uta can baya inda tantin sarki yake amma sai sarki Maharaz ya sha gabansa yace ka kyaleta. Ai yana da kyau ta nuna gadon gidansu. Cikin alamun tsananin mamaki da fargaba Hibru ya dubi sarki Maharaz yace haba ya kai abkna akan wane dalili za ka bar yarka gda daya jal a duniya tayi wannan yaki mai tsananin hadari alhalin ko sarrafa takobi bata iyaba? Kuma bata da wani sihirin tsafi da 9 TASKARNOVELS.COM.NG za ta iya kare kanta. Dajin wannan batu sai sarki Maharaz yayi murmushi gami da yar guntuwar dariya sannan ya ce abinda nakeso da kai ya kai abkna ka zuba ido kawai zaka sha mamaki. Sannan ina son ka gane cewa muddin mulaifa tana tare da inmal babu abinda zai sameta. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki Maharaz ya wucce gaban rundunar da kimanin tafiya taku goma sanan ya tsaya. Koda ganin hakan sai shima sarki dujalu ya wucce gaban tasa rundunar da kimanin tafiya taku goma sannan ya tsaya.. Ya zamana cewa tsakaninsa da sarki Maharaz bai wucce taku arba.in ba amma sbda karfin sihirinsu kowannesu na iya jiyo numfashin dayan. Nana fa suka fara yin kallon kallo na yan dakiku sannan sarki Maharaz yai ajiyar numfashi yace ya wanan sarki kayi sani cewa yakin da muka yi asarar Miliyoyin rayuka. A yau kuwa idan muka cigaba zamu iya kawar da dukkkaninmu a karshe duk mu tashi a tutar babu zamana cewa babu wanda ya sami nasarar dauko TAKOBIN SAIFUL LUJARA da ke karkashen wannan teku na bahar sufiya dake gabanmu. Wai shin me zai hana mu fito da wani tsarin dabam a 10 TASKARNOVELS.COM.NG wannan yaki wanda zai kawo karshen rigimar da ke tsakaninmu. Abinda nake nufi shi ne mu ware jarumai uku uku daga cikin mu su yaki juna. Idan nawa jaruman ne suka kashe naka sai ka hkr ka bar mini takokobin SAIFUL LUJARA. Idan kuma naka jarumai ne suka kashe nawa sai na hkr na bar maka. Ba don komai na yi wannan tunanin ba sai domin mu rage asarar miliyoyin rayukan da za ayi anan gaba. Sa'ad da sarki Maharaz yazo nan a zancensa sai sarki dujalu ya tuntsure da mahaukaciyar dariya kolacin guda kuma ya turbure fuska tamkar an aiko masa da sakon mutuwa yace ya kai maharaz na ji duk abinda kace kuma na aminta da shi. Amma bisa sharadi guda biyu. Sharadi nafarko shine jaruman uku uku da zasuyi wannan fafatawa ba zasu yi amfani da karfin sihiri ba kuma sai kowa ya rantse da abin bautarsa cewar ba zai yi yaudaraba sai dai ya yi amdani da tsagwaron karfensa da kwarewarsa ta yaki.... MAZAN JIYA Littafi na hudu 4 11 TASKARNOVELS.COM.NG Part B Na Abdulaziz Sani m gini Typing Abubakar Saleh AlQuyraemey Sharadi na biyu shine babu wanda zai zabi abkin gwaminsa da kansa sai dai ayi kuria a rubuta sunanyen jarumai shida a jikin duwatsu a gwamutsasu a zubar a kasa kowa ya dauki dutsen daya dauka shine abkin gwaminsa. Yayin da sarki dujalu yazo nan a zancensa sai sarki maharaz yai shiru yana tunani da nazari. A wannan lokacin gaba dayan jamaar dake sansanin yakin hakalinsu ya dugunzuma ainun sbda sun san cewa idan har aka bi wannan tsari wanda sarki dujalu yazo da shi dole ne ayi asarae manyan abban dogaro na kowanen bangare. Bayan sarki Maharaz ya gama nazari da tunani sai ya dubi sarki dujalu yace ina bukatar nayi shawara da mutanena.... Sarki dujalu yayi murmushi yace na baka har tsawon rabi sa a kaje jayi shawara bisa abinda zai fisheju jai da jama arka... Koda gama fadin hakan sai sarki dujalu ya juya da baya ya koma cikin ayarin rundunarsa ya ja sadauki ratinu da 12 TASKARNOVELS.COM.NG Matinu gefe daya domin suma su yi shawara. Sarki Maharazya durfafi inda su Hibru ke tsaye jikinsa a sanyaye fuskarsa cike da alamun tsananin damuwa. Da isarsa garesu sai suka kebe suka zauna a gefe daya suka shiga tataunawa sarki Maharaz dubi Hibru sannan ya dubi inmal yace me kake gani dangane da shawarar da nazo da ita bisa rage yawan a sarar miliyoyin rayukan da za a yi nan gaba? Hibru da inmal suka junansu suka sunkui da kansu kas sai ga mataimakin hibru ya taho gareshi barde KURSHAM. Kursham ya zauna daf da sarki maharaz ya risuna cikin girmamawa yace ya Shugabana ka zo da shawara mai kyau amma kuma itace mafi hadari idan ka yi la.akari da sharuddan da sarki dujalu ya kafa. Ka sani cewa kai kanka baka da wani abin dogaro wanda yafi karfin sihirin tsafi kuma gashi An ce baza ayi amfani da tsafin ba sai dai mutun yayi amfani da tsagwaron karfin sihirin tsafi kuma gashi ai amfani da tsagwaron karfin dantsensa, lallai kuwa in dau hakan za ayi to babu kai a cikin wanna fafatawan da za ayi mutum uku uku koda jin haka sai sarki maharaz ya dakawa barde kursham tsawa yace 13 TASKARNOVELS.COM.NG wnann wacce irin maganar banza kake yi haka? Ka sanin cewa yadda nake kishin jamaata da kasata bana kishin tawa rayuwar don haka lallai dani a cikin mutane ukun da zasu yi wannan fafatawa. Kafin sarki maharaz ya gama rufe bakinsa tuni sarkin yaki Hibru ya taru numfashinsa a fusatace cikin daga murya yace dakata ya kai abkna ka yi sani cewa wani lokacin ran mutum daya yafi na mutane dubunanai muhimmaci. Shin baka tunanin cewa idan aka kasheka a farko wanna yaki jama armu zasu sami karayar zuciya su kasa aiwatar da komai a wanna yaki? Shin baka tunanin cewa kai bango ne babban a filin yaki wanda idan ya fadi bamu da kwnacin hankali a can gida da nan waje. Kuma makiya zasu sami karfin guiwar daza su dada zage dantse akanmu domin ganin sun gagauta shafemu. Abin nake so da kai shine ka amince mana mu uku nan ni Hibru da Inmal mu wakilceka a wannan Gumurzu da za ayi. Koda jin haka sai sarki mahaza ya yunkura a fusace yace ba zan taba yarda ba ayi hakan ba. Ai mutuwa tace maza ta dada kara muku fishi da kwarin guiwa a wannan filin daga kuci gaba da ragargaza 14 TASKARNOVELS.COM.NG abokan gaba har ku karar dasu.. Da jin haka sai sarki yaki Hibru ya matso gaban sarki Maharaz ya kusanceshi ainu yadda har suna iya jin numfashin juna yace ya kai abkina ka sani cewa tsawon shekaru ina bauta a karkashinka kuma ina yi maka biyyya ban taba kin bin umarninka ba amma a yau baza ka bi umarnin naka ba kuma zan yi maka dole akan ka hakura da shiga wannan yaki idan kuma kaki to zan kashe kaina. Koda gama fadin hakan sai hawaye ya zubiwa Hibru aL.amarin da ya karya zuciyar sarki maharaz kenan nan da nan shima idanunsa suka ciko da kwallah ya rugunme Hibru yana mai cewa hakika yau ka nuna mini cewa bani da wani masoyi da ya fika a doron kasa don haka na janye nawa nunfi. Ku tafi ku ukun ku wakilceni a wannan yaki. Zan ci gana da hangenku daga nan inda nake. Ubangiji Durbuza ya baku nasara koda gama fadin hakan sai sarki maharaz ya janye jikinsa daga cikin na Hibru. Shi ku,ma hibru sai yadubi inmal da barde kursham yayi musu inkiyar su bishi izuwa can filin daga. Nan take kuwa suka bishi da sauri suka nufi can tsakiyar filin suka tsaya. Suleiman zidane kd) A sanna ne sarki dujalu 15 TASKARNOVELS.COM.NG Matinu da Ratiju ma suka tunkarosu. Sai ga ya rage saura bai fi taku goma ba a tsakaninsu sannan suka tsaya aka yi mugun kallon kallo yan dakiku. Nan take sarki dujalu yasa aka kawo tsakuwoyi guda shida masu dan fadi aka rubuta sunan kowannesu jikin tsakuwa guda sannan aka zuba tsakuwunyi duka shidan a cikin wani kurtu aka karkada suka hautsine a cikin sannan aka ajiye a kasa. Sarki dujalu ya bushe da dariya mugunta kuma ta turbune fuska yace kowannemu daya bayan daya zai zura hannusa ya dauko tsakuwa guda a cikin kuttun nan. Duk tsakuwar da mutum ya daulo to sunan wanda ke jikin tsakuwar shine abkin gwaminsa. Suwaye zasu fara zabar tsakuwar mu ne ko kuma kune? Sariki dujalu ya tambaya yana mai kallon fuskar inmal. Inmal yayi dan guntun murmushi mai nuna dakewar zuciya da jarumta ya ce kune zaku fara zaba sanna mu. Sarki dujalu ya bushe da dariya yace ai komai nisan jifa kasa zai fado. Yaro yau zan kasan cewa dujalu murucin kan dutse ne bai fito ba sai da yashirya kuma zaku san cewa kun tabo tsulliyar dodo. A yau ne zan karar da dukkanin wannan runduna taku sannan na shiga cikin 16 TASKARNOVELS.COM.NG karkashin kogin BAHAR SUFIYA na dauko TAKOBIN SAIFUL LUJARA daga nan naje na dauko MASHIN GALILLUL HARAS da HULAR LAMSARA wato na hada MAKAMAN da zan gagaru duniya gaba dayanta na zama sarkin ko ina da ina. Ka sani cewa birninku shi ne na farkon wanda zanje na mallakeshi. Waccan yarinyar kuwa Gimbiya Mulaifa wacce kake tsananin so zan masheta baiwa na wulakantata tamkar Akuya.. Kafin sarki dujalu ya gama wannan furuci tuni zuciyar inmal ta kufulo jikinsa ya kama tsuma don haka sai ya daka masa tsawa yace karyarka ta sha karsha yakai wannan sarki. Kayisani cewa nine mai yanka maka dukkan wannan burin naka kuma bani da wani buri wanda yafi ya zamana cewa kaine abkin gwamina ayanzu. Idan kowa ya dauki tsakuwarsa domin na yi maka kisan Gilla! Koda jin wnan batu sai sarki dujalu ya takarkare ya bushe da dariyar mugunta sannan yace ai ni da kai KAR TA SAN KAR ne tunda mun hada jiki ka ji. Ni babban bakin cikina shine rashin ganin sarki Maharaz a cikin ku ukun nan. Ko dayake na san bai isa ya shiga wannan gumurzu ba tunda shi jarimtakarsa ta karfin sihiri ce 17 TASKARNOVELS.COM.NG kawai... Na so ya zama abkin gwamina na yi masa mugun kisa a gaban yarsa da sirikinsa domin na kunsa muku gagarumin bakin ciki. Koda jin wanna batu sai Hibru da Inmal suka fusata ainun suka ji kamar su zare takubbansu su afkawa dujalu amma sai suka daure suka tsaya suna kallonsa kawai cikin hahara jikinsu na tsuma. Nan take sarki dujalu ya dubi Matinu wanda ke tsye a hannun hagunsa yace. Maza ka sa hannunka a cikin wannan kurtu ka zabo avkin yakinka. Cikin hanzari Matinu ta cika umarnu ai kuwa yana dauko tsakuwar sai aka duba aka ga sunan sarkin taki barde kursham. Matinu da kursham suka zubawa juna idanu suna yiwa kansu kallon raini sbda kowannensu gani yake zai iya gamawa da dayan a cikin kankanin lokaci. ABIN DA SUKA MANTA SHINE SAI AN GWADA AKAN SAN NA KWARA! sarki dujalu ya dubi su inmal yayi murmushin mugunta yace yanzu kuma kune zaku zaba ko mu? Da jin haka sai inmal ya yunkura domin ya sanya hannunsa a cikin wannan kurtu amma sai Hibru Hibru yai sauri ya sha gabansa yace dakata ya kai dana ai nine yakamata na zaba yanzu kuma da izinin ubangiji garzuba sarki 18 TASKARNOVELS.COM.NG dujalu zan zabo a matsayin abkin gwamina. Cikin alamun firgici da tsananin tsoro inmal ya dubi Hibru yace haba ya kai abbana ina kai ina tarar sarki dujalu alhalin ka sancewa ya fika jarumtaka nesa ba kusa ba? Page 18 ni kaina da nake da kuruciya a jikina na tsorata da shi bare kai da yanzy girma ya fara riskarka.. Yayin da yazo nan a zancensa sai Hibru ya numfasa yace yakai dana ai ni burina ke nan na kara da shi domin ya kasheni ba tare da naga yadda zai kashe kaba. Domin mutuwar tawa ta fiye mini sauki da ganin taka. Koda sarkin yaki Hibru yazo nan a zancensa sai Inmal yaji ya kamu da tsananin kaunarsa gami da matukar tausayinsa don haka bai san saadda hawaye ya subuto masa ba. Hibru yai sauri ya kau da fuskarsa ga barin kallon inmal don haka shima ya zubar da hawayen kawai sai yaje inda wannan kuttu mai tsakuwoyin yake ya zura hannunsa a cikin ya dauko tsakuwa guda koda ya fiddo tsakuwar aka duba sai aka ga sunan sarki dujalu ne. Nan fa sarki dujalu ya kamu da tsananin farin ciki yayi kururuwar murna. Shi kuwa inmal sai yakamu da tsananin bakin ciki ya cigaba da zubar da hawaye sbda ya sancewa lokacin 19 TASKARNOVELS.COM.NG rabuwarsa da mahaifinsa tazo. Bayan sarki dujalu ya gama kururwar murna gami da dariyar faran ciki sai ya dubi Rijiju sannan ya dubi inmal yace, ku kadai ne kuka rage baku dauki tsakuwoyin kuba don haka dole dai baku da sauyin abkin gwami don haka ba sai kun sa hannun a cikin wannan kuttaba. Yanzu mu bi ka idar wanan fafatawa domin a fara. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki dujalu Matinu da Ratinu suka hada baki suka yi rantsuwa da Girman Gunki da suke bautawa cewar baza suyi amfani da karfin tsafi ba ko yaudara a cikin wannan gumurzu da za ayi face tsagwaron karfin dantsen su da kwarewarsu ta yaki. Koda gama fadin hakan sai suma su inmal su ka hada baki suka yi irin rantsuwar da su dujalu sukayi suna kammalawa ne Matinu da Barde Kurshm na zare takubbansu suka buda suna masu kallon juna cikin nazari sannan kuma sai suka fara zagaya gama da dan uwansa cikin kankanin lokaci. Lokaci guda gaba dayansu suka yi kururuwa uku ruga kan juna suka kacame da azababben yki suna masu kaiwa junansu sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da jarumtaka kowannensu na kokarin 20 TASKARNOVELS.COM.NG yiwa dayan farat daya. Bisa mamaki sai aka ga duk suna amfani da da salon fada iri daya kuma sai gashi sun kasa cutar da juna. Haka dai suka ci gaba da fafatawa har izuwa tsawon dakika dari uku da tamanin amma babu yanda ya sami nasarar koda kwarzanar jikin dan uwansa. Hatta kaifin takubbansu sai da ya fara dusashewa sbda yawan goguwa da juna da kansu suka ja da baya suka yi cirko cirko suna haki kamar zakaru sbda gajiya gami da mamakin yadda aka yi salon fadan Nasu yazo iri daya. A bangare sauran dakarun yaki kuwa kowannen bangare sun zuba idanu ne suna kallo cikin fargaba gami da zakuwar sin ganin nasu ne ya sami nasara. Bayan Matinu da barde Kursham sun samu hutu na tsawon yan dakiku sai kowanensu ya yar da takobin hannunsa. Matinu ya zare wadansu gajerun adduna guda biyu dake kuibin cinyoyinsa a cikin kufe shi kuma Barde Kursham sai ya zare wata sharbebiyar wuka wacce tsawonta bai wuce kamu biyu ba amma tana da fadi gami da tsananin kaifi sannan ya kuya ya dubi jama,ar runfunarsa dake baya yana mai daga hannu. Nan take wani badakare ya rugo ya kawo masa 21 TASKARNOVELS.COM.NG garkuwa ya riketa da hannun hagu. . Yana karba garkuwar sai ya fuskanci matinu suka rugo da gudu izuwa kan juna. Ya yin da yarage saura baifi taku hudu ba sai kowannensu ya daka tsalle sama suka kaiwa juna mugun hari. Cikin sa.a Matinu ya dankarawa barde kursham sara a kan kafada. Shim kuma kursham ya sokeshi da wannan wuka a tsakiyar kirjinsa har sai da wukar ta bullo ta gadon bayansa. Duk su biyun suka tsanfara uban ihu a lokacin da jijiyar kafadar barde Kursgam ta tsinke jini ya kama tsartuwa a sama. Shi kuwa matinu jini ne ya kama bulbulowa ta cikin ramin da wukar ta yi a kirjinsa wanda inda za a tara yar kwatarniya sai ta cika fal da jini. Nan take du su biyun suka kama mata gun gun a tsaye har sai dasuka sulale kasa suka kama shure shure. Idan suka yunkura kamar zasu iya mikewa sai kaga sun sake bajewa. A haka dai duk su biyun suka zama gawa. Koda ganin wanan al mari sai kowane bangare sukakamu da tsananin bakin ciki sakamakon RAGAS da akayi. Har sarki yaji ya yunkura zai tari sarki dujalu sai shi sarki dujalu ya nole yace ai ni da kai manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda fadan kananun giwaye 22 TASKARNOVELS.COM.NG zai kasance sannan muyi namu a karshe... Manyan giwaye ne mu bari mu ga yadda fadan kananun giwaye zai kasance

Chapter 1 of 18