Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️9️⃣

.... Shin jama'ah wai su waye iyayan Mubina? ina ne asalin su?, *ABDULRAHIM KABEER ALGÈRIE* cika ken balarabe ne na asali. *KABEER NABEEL* balaraban Algèrie ne, Allah ya masu tarin dukiya me yawa, Kabeer Nabeel mutune shi wayayye ɗan son aji dadi, kuma shi ɗaya Allah yaba iyayansa, dan haka ya sami tarbiyya me kyau yayi karatu sosai, bayan ya kammala karatunsa ne ya kama aiki Allah ya haɗa shi da Jawahir, sukayi aure cikin so da kaunar juna, bayan auransu da sati biyu suka shiga yawo ƙasa daban-daban, wanda daga karshe suka yada zango a Niger a babban birnin Naimey, suka sauka a grand hotel, tsawon sati ɗaya suna cin duniyar su yawo babu inda basa zuwa Kabeer yaji duk duniya babu ƙasar da yake sha'awar zama kamar niger a yanzu... Nan akwai wani bazabarme me suna maiga da suka saba ma'aikacin hotel ɗin ne, yake faɗa masa buƙatarsa ta yana so ya dawo niger da zama se dai yana tsoron iyayansa bazu yarda ba... Maiga ya kwatanta masa ya koma ya bisu a sannu har su amince harakar mahaifa ba'a wasa da ita.
To daga nan yabar maganar bai sake neman shawara ba har suka koma ƙasarsu. inda kafin su tafi ya amshi number maiga.
Tinda Kabeer suka dawo yake ma mahaifinsa wayo da kwatanta masa su koma ƙasar niger mana da zama, rayuwar akwai dadi. Irin tsawar da fushin da Nabeel ya nuna ƙarara akan Kabeer da ƙyamar abinda ya faɗa, yasa Kabeer koda wasa be sake maganar ba ya barta ya rungumi aikinsa da matarsa suna soyewarsu... Cikin ikon har ta sami ciki, murna ba'a cewa kome wajan Kabeer da iyayansa da itama nata dangin. Har cikin ya girma ranar haihuwa tazo Allah ya sauki Jawahir lafiya ta haifo yaranta kyawawa mace da namiji, murna a dangi da iyayan yaran ɓata lokacin faɗi ne... Ranar suna ta zagayo yaran sukaci sunah Namijin Abdulrahim macan kakarta ta uba Sabeela.
Haka yaran suka taso cikin gata da kulawa dangi kowa na sonsu, suna shekara biyu Allah yama Nabeel rasuwa mutuwar ta girgiza Kabeer ba kadan ba, yayi kuka har ya gaji ya barwa Allah yaci gaba da kula da matarsa da yaransa da mahaifiyarsa... Bayan cikon shekarar Nabeel ne Sabeela mahaifiyar Kabeer take faɗa masa ita garin ya fice mata aranta! kamar ta koma tunis da zama... Kabeer najin haka ya bijiro mata da manufarsa ba yauba yana sha'awar komawa niger, nan tayi na'am da maganar. Ba a ɗauki lkc ba Kabeer ya kira maiga yana faɗa masa kome nan ya masa gaisuwa da tambayar sa garin da yake so a niger? Kabeer yace nan Naimey yake so zai zo ya sayi fili a maka masa gini irin nasu na larabawa... Ba ako jima ba Kabeer ya kwashi dukiya yaje niger inda suka fara fafutika neman guri me kyau nan ko a yantala ya samu filin da ya masa aka kafta masa maƙareran gida. Cikin wata uku aka gama kome ya damƙama maiga amanar kome koma ya riƙe amana har aka gama aka zuba kayan duniya tare da saukar AQura'ani mai girma. Suka tattara suka dawo ƙasar niger tare da dukiyar su wata kumana can ƴan uwa suna juyawa masu, suko suna rayuwarsu me dadi tare da yaransu biyu.
Haka suka kasance a niger Kabeer ya gina babbar asibiti domin temakon al'ummah duk da tana asibitin kudi amma akwai sauki sosai, haka jama ke tururuwar zuwa.
Akwana a tashi har su Abdulrahim suka girma sun sami tarbiyya me kyau da karatun book da na mahammadiya, tin daga haihuwarsu Allah bai sake ba Kabeer haihuwa ba, cuɗanya da suke da hausa da zabarmawa yasa suka iya hausa sosai hakama duk ma'aikatan gidansu daga bahaushe se zarma. Sabeela tana gama secondary school ɗinta aka mata aure ta auri wani buzu babban ɗan jarida me suna Saleem sabo a gidanta ta shiga jami'a, yayin da Abdulrahim ya maida hankalin sa kan karatunsa medicine, saboda yay aiki ana hospital ɗinsa me suna *Clinique Annur hospital*. Akwana a tashi babu wuya har ya gama ya fara aikin sa tare da mahaifinsa, watarana an kawo wani maras lafiya abin tausayi gasu talakawa likis, cikin ikon Allah Abdulrahim ne akan aiki shi ya masu kome kyauta sun bashi tausayi barin budurwar yanda take kuka tamkar mahaifinta ya rasu. Nan take yarinyar ta burge Abdulrahim duk da bayada ra'ayin auran bahausa. Dattijon kwanan sa uku ya warke ras zuwa lokacin Nusaiba ta shaƙu da Abdulrahim, duk tasan ba lallai ta sami balarabe ba. Nan yake tambayarta wane unguwa suke? ta faɗa masa su ba ƴan gari bane ƴan maradi ne, labarin irin temakon da ake a likitan yasa suka seda kadarasu suka zo ita da babanta da mamarta da yayanta... Kamar wasa kafin ake sallamar su suka kulla soyayya saboda Nusaiba kyakyawace son kowa kin wanda ya rasa fara doguwa me diri kawai de tallauci ne da ya masu cikas babu wadatar abunci me kyau da sutura shi ke boye kyanta.
Seda suka kwashe shekara guda suna soyayya ya wanke ƴan gidansu tass, yasa aka masu ginin zamani duk karshan wata se yaje maradi daga Naimey har yaji sha'awar zama maradi fiye da Naimey ɗin. Koda Abdulrahim ya gwadama iyayansa pic ɗin Nusaiba sunyi na'am da ita basu nuna kyama ba cewar se balaraba ƴar uwasa saboda tana da kome na mace da ake buƙata a tare da ita, dan haka basu yi ƙasa a guiwa ba wajan nemarwa ɗansu auran Nusaiba sukayi tattaki har garin maradi. Babu ɓata lokaci aka saka ranar aure, lokaci yazo akayi biki na kece reni, wanda har yanzu babu na biyun sa da aka taɓa yi a garin maradin... A ka ɗauko amarya aka kawota gidanta dake Naimey gida tamkar aljanar duniya, dangin Nusaiba fa sai buɗe hanci ake a garin maradi babu ta biyun jininsu ta auri balarabe. Soyayya me tsaf ake zubawa tsakanin Nusaiba da Abdulrahim tamkar zasuci junansu. Nusaiba tana bin surukanta sau da ƙafa da kakar mijinta rayuwarsu abin sha'awa nan da nan suka koya mata larabci. Shekara su ɗaya da aure ta haifo yaronta santalele kyakyawa aka saka masa suna Kabeer wanda hakan yama Kabeer kakansu dadi matuƙa, lele kam ya shashi gashi daman kamar su ɗaya da Kabeer ɗin. Seda Kabeer ya shekara biyar cif aka haifi Amrah zankaɗeɗiya kyakyawa da ita a ranar kuma Sabeela mahaifiyar Kabeer ta cika mutuwar ta girgizasu sosai sun jima kafin suke mantawa Lkcn Sabeela da mijinta ta yaransu biyu mace da namiji suka koma london da zama saboda BBC na buƙatar irin Saleem sabo . Amrah tana da shekara biyu aka sami cikin Mubina wanda Mamu taci wahalar laulayi kamar bazata rayu ba, har kuka take a cire mata cikin sbd bata iya ci bata iya sha se amai, umpah yace sam bai san zancan ba dan yana son cikin sosai tayi hkr dan Allah. Haka dai aka samu har yayi wata tara amma sam babu haihuwa idan ya dubata yaga da saura ana haka seda Amrah ta ahekara uku aka haifi Mubina, kenan seda ta shekara a cikin Mamu aka haifeta, wanda kyawunta ya kere na kowa a gidan gata katuwa aka haifota fara sul kallo ɗaya zaka mata kasan balarabar asali ce ga farin jinin jama'a tin ranar da aka haifeta amma se shegen kuka dan bata bar kuka ba se da akayi arba'in basa baccin kirki, amma cikin ikon Allah ana arba'in ta fasa kukan, se tsotsar nonon tsiya da son hannu dan ba'a ajiyeta, bata kwanciya se ahannun mutum ko baya, haka Ablah take fama da Mamu Kabeer yayi ta dariya da Amrah. Tin daga kanta har yau Mamu bata samu haihuwa ba, suka rungume yaran su uku suna basu tarbiyya haɗe nema masu ilim na addini da boko.
Umpah da Ablah da Kabeer sun ɗauki son duniya sun ɗorama Mubina, se sangarta da shagwaɓa, dan se abinda take so ake a gidan, Mubina itace ta dasama Abdulrahim umpah Nusaiba Mamu tin tana ƴar shekara uku idan kana son masifa da bala'i kace mata shekarara, to Allah zai rabaku da ita. Se dai fa akwaita ilimi sosai daga na book har na Qura'ani mai girma ɗin. Umpah ya zubama ƴaƴansa makudan kudi domin ne ma masu ilim, Kabeer farine kyakyawa me fara'a da son jama'a yana son kanninsa sosai tafiyarsa *Balgique* karatu ne ya raba su se ta waya. Tin a primary school Mubuna ita ce ke cin ta farko, har zuwa secondary school babu wacce ta shiga gabanta, ga farin jini duk masifarta dan lkcn tana primary kullum sai ta jibgi ƴaƴan mutane da cizo akunne, to har secondary ɗin ma bata daina fada da cizo ba, gata ƴar siririya in ta manne maka a jikin ka se an ɓanɓareta daket, kamar wahainiya take, ga ɗaukar magana tsokana kamar masifa, dan kafin Amrah take shiga university Mubina ke tsaye kanta ko kallon banza baka isa kama Amrah ka kwana lfy ba, seda ta shiga Jami'ar Abdou monmuni university nan Naimey suka rabu. Kuma lokacin ne Kabeer ya rasu mutuwar ta girgiza umpah AmrahdA iyalinsa, dan Mubina se da tai jinya sosai kafin take warwarewa daket. Ablah ma kamar tayi hauka miji ya tafi ya barta, anyi shekara kafin suke komawa normal, dan sunsan dai dole duk mai rai se ya ɗanɗani zafin mutuwa. Amrah matsagaiciya ce ita ba doguwa ba ita ba gajera ba me diri tana da ƴar ƙiba kadan, tana da dogon gashi sosai fuskarta doguwa me ɗauke da dogon hanci da faffadan lips da matsagaitan idanu, ba laifi kyakyawace. son kowa se dai Mubina ta kereta a kome gashi kawai Amrah tafi Mubina da jiki, amma suna kama sosai. Mubina doguwace kyakyawa fara sul ƴar siririya mai ɗauke da doguwar fuska me dan faɗi, me ɗauke da dogon hanci da dara-daran idanuwa lumsassu bakinta ɗan ƙarami kalar pink hakoranta sirisiri farare sul me ɗauke ƴar wushirya, tanada dimple a gefen damarta wanda ko magana take yana loɓawa, se kirjinta me cike da albarkatun fulani tantsam-tantsam jajur a tsaye suke kyam, kansu irin masu tsinine sosai duk da kasancewarta siririya tanada mazauna ƴan matasa gata ƙirar coca cola akwai hips, tana da gashi amma ba sosai ba ya sauka de har kafadarta yana da samtsi sosai ba baki bane yasa maroon, akwai ta laushin fata jikinta lallausa ne tamkar tarwada idan tana juyin rawa ko tafiya, jikinta mai taushi ne haɗe da samtsi, Mubina ta kasance ma'abuciyar tsafta ce da son kamshi gata da son gayu akwai daukan dreesing kuma dole duk namiji me lafiya ya kalleta dan tayi ba karya, se dai sangartatar yarinya ce shagwaɓa ɓa dan Ablah ta kasa ta tsare bata son abinda zai ɓatama mubina rai, bare uwa uba umpah ga son jiki tamkar mage bata iya bacci se jikin mutum, Ablah ta ɓatata idan bata ƙasar dole take dawowa wajan Amrah, dole Amrah ta saba da hakan Mubina akwai son jiki gata irin wannan matan ne masu wata irin muguwar sha'awa abu kaɗan zai sakata cikin halin buƙatuwa shiyasa bata kallon duk wani abun da zai sata cikin wani yanayi dan yanzu zaka ga tana mimmiƙewa tana matsar ƙafafu tana hawaye, ko Mamu tasan da haka shiyasa kullum take cikin Addu'a Allah ya kare mata yarta a duk inda take. Se dai Mubina bata kulla samari asali ma har yau bata ba kowane saurayi fuska ba duk farin jininta dan har manyan al'hazawa harinta suke ansha tinkara umpah da neman auranta yace sam ƴarsa karatu take, se ya cika mata burinta na zama cika kiyar Ƴar jarida. Dole suka hakura dan basu sami shiga gun umpah bare Mubina da ko kallo basu isheta ba. Amrah ma maza basa gabanta sam ta maida hankalinta gun karatunta na bank. Ranar da su Mubina suka gama secondary school ranar suka fara shirin barin Naimey komawa maradi. Mamu dan murna harda kuka tayi dan bata taɓa sa ran haka ba, ashe ba yauba umpah an can ana tamfatsa masu gidaje har biyu a maradi an an gina katon company da hospital ashe katsina hospital tashi ce ya hana ne duniya ta sani. Ranar da suka dawo maradi da zama abin ya burge Mubina dan dama kullun tazo gidan kakaninta hutu kamar karta koma take ji, duk da daman a maradi zata zo tayi university ɗinta. Ashe ko umpah saboda Mubina ya gwamma ce gwara su koma can da zama bazai bar ƴarsa wani gari ba tana karatu gwara ya haɗa kansu ita da Amrah dan haka amrah na 300 leve mataki na 3 umpah ya gyara mata takardunta suka dawo maradi ta karasa a Maryam abacha university. Gidan ɗaya suka zauna wanda yaji kome na rayuwar duniya kafin a gama wancan babban gidan. Mamu dangi se sunturi suke Mubina kamar wasa ta kwarama wata me sunan kuluwa da mijinta lawali basu da aiki kullum suna hanyar gidan ƴarsu ta zumu Allah kyauta. To fa daga nan suka yi sanyi se gulmar Mubina suke wai balaraba batada aiki se wulaƙanta baƙar fata, dan balaraba dangin Mamu suke ce mata. Baffa inusa kakanta kuwa yace tayi dai dai shiyasa yafi santa kaf jikokinsa.
Mubina ta shiga *Maryam Abacha American university of Niger* cikin sa'a dan sosai karatu take babu wasa tana karanta mass communcation. Yanzu Mubina na 100 level matakin farko a university, amma suna shirin jarabawa na shiga 200 level mataki na biyu wanda Amrah kuma tana dab da bankwana da makarantar dama matakin ƙarshe take gashi Lameer na damunta kan maganar auran su, duk da bata sonsa amma tana da niyar auransa, kawai ranar kamar a mafarki a fecebook taga wani me suna *KAK* ya turo mata invitation nan tayi confirmer ɗin sa, suke gaisawa se dai sam bata faɗa masa gaskiya ba tace ita ƴar dosso ce shiko ya faɗa mata yana maradi amman bai faɗa mata sunan sa ba ta haka ne har suka shaku. A kwananan. Kuma a wannan ɗan lokacin ne Kamal ya shigo makarantar Maryam Abacha wanda yake koyar dasu Mubina introduction too Business admin. Bayan an kammala gidansu na nan Ali ɗan tsoho an zuba masa uwar dukiya, suka baro can unguwar zaria1 suka dawo Ali ɗan tsoho haɗaɗiyar unguwa me kyan gaske ba ruwan wani da wani, barin ma ɓangaran su Mubina ta masu kudi ce zallah ba kamar sauran layin ba... Ablah bata gari ta tafi Algèrie anyi masu rashi tace se ta dan huta zata dawo. Kabeer ma yana nan tafe ya kammala karatunsa na engineering wannan shine cikaken tarihinsu Mubina, se kuma ku biyo ni jin waye Kamal a next page, kafin mu koma wasan......


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣0️⃣

.... *KAMALUDDIN ABUBAKAR ALIYU KANGIWA MAI NASARA*, shine cika ken sunan sa Alhaji Abubakar Ali kangiwa mai nasara, haifafan garin Kebbi ne cikin nigeria cikin garin kangiwa, su uku ne wajan iyayansu talakawane likis abinda zasuci se sun fita nema, shine babba bayan haihuwar kannisa biyu Safiyya da muhuseen, Allah yayi ma Aliyu rasuwa ta sanaɗin ciwon sugar, lkcn Abubakar yanada shekaru 13 a duniya, gashi ba wani dangi azo agani gare su ba, kasancewar Aliyun marayane gaba da baya. Haka suka rinƙa fafutika da Rumana mahaifiyarsa suna tallafawa kanninsa da kuma dangin Rumana ba laifi suna temaka masu, shima yana karatunsa cikin ɗauriya da jajircewa. A haka har ya gama secondary school sakammakon sa yayi kyau sosai cikin ikon Allah gwamnati ta ɗauki nauyinsa fita ƙasar waje karatu har tsawon shekara 7, amma Abubakar ya rufe idanunsa yace bazai bar marayun kanninsa ba, da mahaifiyarsa gwara yayi anan kusa dasu, ko kuma yaje niger Maryam abacha yayi, se yana ƙokarin zauwa ganinsu duk karshen wata. Haka ko akayi Abubakar aka haɗa masa kome daga gwamnatinsu ya tafi niger karatu inda yake karantar fannin business, yana ƙokarin zuwa kangiwa duk karshen wata yana kula da mahifiyarsa da kanninsa sosai, Muhuseen da Safiyya suna karatun su cikin kwanciyar hankali.
Abubakar ba karatun ya tsaya ba duk lokacin da basu da lecturer, zai tafi neman na kansa bayada girman kai kome yasa mu yi yake, kafin yake komawa kangiwa ya tarama kanninsa abubuwa sosai... Haka rayuwar Abubakar ta kasance a niger yana karatunsa, yana tare da abokaninsa yan niger, yana lura da yanayin yadda maradi ke harakar kasuwanci, ya yarda da ake cewa maradi cibiyar kasuwanci ce a Niger. Kwance tashi babu wuya har Abubakar ya gama karatunsa tare da sammakon sa me kyau, wanda yaji yana sha'awar zaman zuwa lokacin zaka sha mamaki irin yadda ya tara abin duniya har ya sayi fili a umguwar citè, nan maradi, dan ya gama yanke shawara zai tuntuɓi Rumana yaji idan ta amince su dawo nan da zama, dan sosai tasu tazo ɗaya da Alhaji munkaila. kuma a lokacin aka sanya auran Safiyya da wani yaro ɗan kebbi me suna Sabi'u. Abubakar da farko yaki yace bazai bar kaunwarsa ba, tinda Rumanar ta amince su koma, se da Rumana tace ya barta tinda tana son abinta dole ya hkr. Cikin ikon Allah. Abubakar yay ma Safiyya kome na daki anyi biki daidai misali ankai amarya gidanta dake can kebbi, Abubakar harda kuka tare dashi aka kai Safiyya lkcn Muhuseen yana A.B.U zaria karatu. Abubakar yaba Sabi'u amanar Safiyya ya amsa tare da alkawali duk bayan watanin zau kaita kangiwa ta gansu... Na ya sheda masa zasu koma niger ne da zama...
Baya auran Safiyya da wata uku Abubakar ya faɗa kasuwanci sosai shida munkaila maraɗawa Ana babbar kasuwar maradi babu irin business da basayi, kwance tashi har ya fara zuwa cotonou kawo motoci, a lkcn aka fara masa gininsa yaje ya ɗauko Rumana bayan sunje gidan Safiyya suka mata sallama, tare da ƴan uwansu... Masha Allah gidane madedeci me kyau ɗaki uku ko wannan da toilet ɗinsa a ciki, se kicin tsakar gidan na da fili sosai. Kuma a lokacin Abubakar Allah ya haɗashi da Fatima buzuwa ce ƴan taouha amman a maradi suke da zama mahaifinta yana da babban shago na siyar da kayan masarufi kome na abunci har sari yake badawa shinkafa mai macaron coscous madara da dai sauransu. Allah ya haɗa jininsu sosai Fatima kyakyawace sosai fara me gashi har gadon baya kasancewarta buzuwa duk inda kake neman kyau to ta kai. Abubakar kuwa baƙine amma kyakyawane sosai suna kama sosai da Muhuseen haka da Safiyya ma dan Ali mahaifinsu suka fito. Kamar wasa magana ta zama babba tsakanin Fatima da Abubakar magana ta kai ga manya. *Alhaji Sidi sidde* bai yi gardama wajan ba Abubakar auran ƴarsa Fatima ba, saboda suna harakar kasuwanci da yaron shike kawo masa shinkafa ƴar cotonou. Ba a dauki lokaci ba ƴan uwan baban Abubakar da na Rumana suka zo aka saka ranar biki... tin kafin auran Allah yake habbaka dukiyar Abubakar kafin kace me ya fara jiƙa, a lokacin ne kuma Rumana wani Alhaji ya takura mata wanda matarsa ta rasu gun haihuwa tabar yara uku amma manyane matan biyu an masu aure ɗayan kuma yana karatu se jaririn da ya rasu kafin arba'in ɗin uwar. Da farko takiya harda kuka se da Abubakar yasa baki cewar zai ji dadi ta koma ga Allah tana ɗakin mijinta. Se lokacin ta yarda, ba awani jimaba aka ɗaura auran ta tare a gidanta nan cikin cité ɗin... Auran Fatima da Abubakar ya kayatar sosai auran soyayya, jama'a dayawa sunyi mamakin yanda akayi Sidi yaba Baƙin mutum auran ƴarsa barin da suka san halin buzaye... Soyayya suke zubawa sosai a gidansu, kowa baya son yaga ɗan uwansa a damuwa, Fatima na girmama Rumana sosai a kullum se ta shiga ta gaisheta. Saida suka shekara biyu da aure Allah yaba Fatima ciki wanda suka ɗauki son duniya suka ɗora masa, dan Abubakar akwai son yara sosai, zuwa lokacin Safiyya ta haifi ɗanta namiji ta yaye har tanada wani cikin sosai suna zamunci da yayunta. Haka sukayi renon cikinsu har ya isa haihuwa ta haifo ɗanta katon gaske chocolet coulor kyakyawa ajin karshe, kallo ɗaya zaka masa kasan ruwa biyu ne kamarsa ɗaya da Abbu hasken fata kawai ya ɗauka na fatima, ranar sunah yaci sunan Kamaluddin, yaron da ya taso cikin gata da kulawa se bayan daya fara tafiya aka ga yana ɗingisa ƙafarsa, Abbu ya fara kaisa asibita ana masa massage amma ba abunda ya sauya likitocin sukace wannan baya kome ai inda ace tin lokacin da aka haifeshine aka lura ƙafar tana ɗanya da to zai iya dai daita, nan Abbu yace baya kome tinda ɗingisawa ce haka Allah yaso yaga abinsa sun amshi kaddara... Haka Kamal ya tasa har aka sashi makaranta sam idan ba ka lura ba bazaka ce yana ɗingisawa ba ma, sbd yin yana yaro akwai tsafta da kama jiki ga takun sa na burgewa, ɗingisawar ka ɗaukanma da gaiyya yake . Se da ya shekara 13 cif a duniya aka haifi Samha Kamal yaji dadi sosai samun ƴar uwa lkcn da baiyi zato ba, dan lokacin Muhuseen ma yayi aure amma shi yana Nigeria can Kebbi anan yake aiki, har ya haifi yara biyu maza a lkcn... Haka Kamal yaci gaba da karatunsa inda Rumana ma Allah ya bata ƴan biyu mata shekara biyu tsakani ta haifo wani namijin, kaji rabo Abbu murna yake sosai ya sami ƙarin ƴan uwa, Saifiyya murna take haka Muhuseen, daga nan dai bata sake haihuwa ba. Samha doguwace baƙa dan ita Abbu ta fito sak se gashin Fatima da ta samu kyakyawace tanada diri sosai na mata suna kama sosai da kamal haske kawai ya fita da girman jiki dan Kamal irin wannan murɗadɗin mazan ne masu ƙirar karfafa gashi dogo kyakyawa duk wani abu na ɗa namiji kama Allah ya bashi dan ɗingisawar nan bata dame shi ba yasan Allah ne yaso ya ganshi a haka. Bayan ya gama secondary school Abbu ya fitar dashi waje yay karatunsa kuma ba akan kome ba sai akan business, dan yaji daɗin business matuƙa. Kamal bai musa ba ya tafi tunis. Kamal ya karanci business adaministration degiri na 1, sai likita a degiri na 2 da na 3, Sbd Kamal mutun ne me Kishin bala'i yana kishin abinda yake so, yayi hakan ne wai sbd ko da yaushe ya duba matarsa ko yan uwansa A'A ba dan ya fito aikin ba burinsa yayi business ɗin da mahaifinsa yake so. Yana matakin Karshe ne Abbu ya tamfatsa masu gida a Ali ɗan tsoho, ya kuma fara gina masa companyn sa, dan yanzu babu irin dukiyar da basu tara ba, yan uwa daga kebbi da kangiwa kuwa se zuwa ake ziyara wasun ma Abbu ba wani saninsu yayi se da idan goggo Rumana tace ƴan uwansu ne zai masu shatara ta arziki yasa direba ya kaisu har Nigeria ɗin. Samha yanzu take secondary school nan a Mufeeda makarantar akwai karatu harda turanci amman madarissa ce anfi ba larabci karfi. Sun koma sabon gidansu da wata biyar Kamal ya dawo cike da tarin nasarori a rayuwarsa, Kuma lkcn akayi bikin buɗe Company ranar naga jama'a, Kamal ya zabi koyarwa ne dan burgewa da ra'ayi ba dan kudi ba, asalima dan jama'a su karu da abinda ya karu dashi ne shima, haka idan yayi niya yana zuwa hospital ya temakawa mata dan ba ƙaramin likitan mata bane. Kamal akwaishi da

Please Login or Register in order to submit comment