Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gamu kuna wane gefan ne?" umpah yace"muna sama room 11 mu kaɗaine guri na masamman Baby najin jiki sai cewa take yawu ya bata na rasa gane wannan lamari , anya ba mayu suka kamata ba?" Mamu tace" Ok ga munan tare dasu Alhaji fa." kitt ta tsinke kiran, tace " Bismillah suna sama." Abbu yace" Ok muje" nan suka rankaya Amrah kuwa duk ta duririce ga kunyar Kamal haka kawai takejin nauyinsa duk bai mata magana ba itama bata masa ba.
Jin ana knocking ɗin kofar yasa umpah jan bargo ya rufeta ruf ya janye hanunsa da ta damƙe gam jin zazzabin ya fara sauka, ya miƙe ya nufi kofar domin ya buɗe masu.... Yasin yau Phone ɗina ƙamewa take ƙam😌😌😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻




*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️6️⃣

....Yana buɗe kofar yaga harda su Abbu cikin farin ciki ya basu hanya suka shigo, ya rungume Abbu suka yi musabaha, ya sake shi ya rungume Kamal suka yi musahaba, Kamal ya gaishe shi cikin girmamawa. Umpah yana riƙe da hannun Kamal yace"Bismillah." ciki suka kara sa ciki suka zauna saman gadon ɗaya da yake kallon wanda Mubina take kwance. Abbu yace"ya jikin nata? Allah ya kara mata lfy , ashe harda drip aka ɗaura mata? sannu ɗiyata Allah ya baki lfy." umpah yace"bacci take da sauƙi jikin nata sosai , sai sambatu take dai." ya faɗa yana jinjina kai.
Mamu da Amrah suka nufi gadon suka zauna Mamu ta taɓa hannunta me ɗaure da drip taji da ɗan zafi kaɗan, ta janye bargon kaɗan ta shafi fuskarta tayi fayau abin ka da farin mutum har wani masara ta sa.
Amrah ta matsa ta riƙe hannunta tana kwalla, ta shafi kyakyawar fuskarta. Kamal har leƙe yake yaga wace yarinya ce wannan ake ta riritawa haka amma bai gani ba, sakammakon Amrah ta rungumeta gefen fuskarta, ya taɓe bakinsa dan shi ya tsani yaga ana lelen mace dayawa sangarcewa take. Mamu ta kira umpah gefe cewar ita fa bata yarda ba a faɗawa babban Dr a duba mata lafiyar ƴarta kar aje ko masu garkuwa da mutane sun taɓata, taki faɗane. Umpah bai musa ba ya amsa.

Su Abbu sun jima sosai amma Mubina bata tashi ba, nan suka masu ya jiki da Adu'ar samun sauƙi suka tafi, umpah ya rako su har harabar hospital yana godiya sosai, se da suka ta fi ya ya juya, direct office ɗin doctor ya nufa ya masa bayanin irin sambatun da Mubina take, da yadda tace masu garkuwa sun sace su, shifa bai yarda ba a duba masa ƴarsa kar aje an ɓata masa yarinya basu sani ba. Nan take Dr ya kira wata kwarara Dr su ka je aka fara bin cikar Mubina babu abinda aka mata, Dr yace suyi hakuri zafin zazzabi ne.
Se karfe 10 pm drip ɗin ya kare likita ya cire mata ya kara gwadata bata da kome zazzabin ya sauka, se yar damuwar da ta saka a ranta, yace tana tashi a bata magugunan bayan taci abunci.
Misalin karfe 12 pm Mubina ta farka, a hankali take bude shanyayyun idanunta tar ta ware su, ta fara bin ɗakin da kallo, Amrah kwance saman gadon da yake kallon wanda take kwance tana latsa waya se murmushi take, umpah kuwa na zaune kusan Mamu na rungume da Mubina ɗin tin bayan da aka cire mata drip.
Umpah ya matso ya kama hannunta yace"Baby sannu kin tashi ya karfin jikin?" cike da mamaki nake kallon umpah na kara shigewa jikin Mamu na nitsa kaina kirjinta banyi magana ba, saboda bakin ciki da yake adabar zuciyata yanzu wannan gurgune yay sanaɗin kwanciyata gadon asibita, tab ashe ko akwai ƙura babba wlh ko da hakan na nufi rasa raina mutiƙar zan saka shi cikin ƙangin rayuwa, to tabbas sai na rama, dan yanzu ma rayuwata rabi ce tin da na hadiye yawun sa a cikina... Mamu ce tace"Baby sannu bakya jin umpah na magana ne? Wai wane irin yawu kike faɗine baby ko masu garkuwa da mutane sun miki wani abu ne?" da sauri na dawo haiyacina, jikina babu wani kwarin kirki kasala nakeji sosai, na janye daga jikin Mamu na fada saman jikin umpah na shagwaɓe nace" umpah wai tin yaushe muke hospital ne?" umpah yay murmushi ya shafi kanta yace" Baby mun jima tin bayan sallah isha, oya tashi ki shiga toilet ki kurkure bakinki kizo na baki abunci." ya faɗa yana kamata ta miƙe... Amrah ce ta iso ta kama Mubina tana mata sannu suka nufi toilet.
Basu jima ba suka fito. Mamu ta haɗa mata lafiyayyan tuwon shinkafa da miyar taushe taji naman rago da man shanu, wanda Laure ta kawo masu duk basu wani ci ba sosai ma, girkin da Mubina take mugun so kenan, jikin Mamu ta zauna tana bata abaki umpah da Amrah suna masu dariya. Bata wani ci sosai ba tace ta koshi tasha lemon kwakwa kadan aka bata magaani tasha, taje ta wanko hannunta tana kisimawa a ranta bazata sake nuna damuwarta ba har ta dauki fansa. Likita bayan ya shigo ya basu sallama yana jama Mubina kunne cewar tabar sa damuwa a ranta, ta amsa da "To" kawai dan tasan mutiƙar bata ɗauki fansa ba to damuwar ce zata kasheta...

Bayan Sun je gida Mamu da umpah suka sakata gaba da nasiha tabar sa damuwa a ranta, ta saki jikinta tare da nuna masu kome ya wuce, Amrah taji dadin hakan, Ablah ta kira waya aka ba Mubina nan take faɗa mata nan da sati uku gatan zuwa, Mubina dadi harda ihuuu kamar ba ita bace aka sako daga hospital, nan ta kira Kabeer yayan su bata same shi ba, harda kukan sangarta Mamu ta lallaɓata taje ta kwanta, ai kuwa tana kwanci se bacci ko wanka ba tai ba. Suma basu jima ba suka shige ciki ita da umpah. Amrah kuwa se chart take..

Kamal bayan sun dawo gida Ummah da Samha suka tisa su gaba da tambaya ina suka shiga? Nan Abbu yay masu bayanin makocinsa ne wanda suka kauro kwananan *ABDULRAHIM KABEER ALGERI* ƴarsa bata da lfy suka je dubata hospital. Sai lokacin Ummah hankalinta ya kwanta, bayan ta masu jaje nan suka nufi kan dining are sukayi lunch, cikin kwanciyar hankali da wasa da dariya, bayan sun gama ne Kamal ya haye sama yayi wanka ya saka kayan shan isaka ya dauko laptop ɗinsa ya sauko ƙasa ya kunna ya shiga aiki gabansa. Nan Abbu yake faɗama ummah cewar yaga yarinya me nutsuwa ɗiyar Abdulrahim ta burge shi zai so su kulla zumunci. Ummah ma taji dadi sosai tace adai bi kome ahankali yanzu kai tsaye kar a masu maganar...

1:00 pm Kamal kwance saman makeken gadon sa, cikin shigar kayan bacci farare sul masu sulɓi, se sansanyan kamshin dadi yake fita daga cikin ɗakin.
A nutse yake magana yana sakin murmushi, can ƙasan maƙoshi ya furta"Lkc na tafe cutie angel amman kimin alkawalin duk munina zaki soni bazaki gujeni ba? Kuma inada nakasa fa." ya faɗa yana sakar mata sansanyan murmushi, wanda yay nasarar kashe mata duk wata gaba da take jikinta.
Lumshe idanunta tayi tana juyi tare da harba ƙafafunta cikin shaukin son da ya ɗebeta, har bata san ta ɗaga ƙafa ta harbi ta kusa da ita ba... Wacce ta miƙe cikin magagin bacci tana faɗi"kan wlh bazan yarda ba kuji Aunty idan ba jaraba tsakiyar dare kina waya se an kuya miki iskanci ta waya." ta faɗi ta dadagewa ta shirga ma Amrah dundu a baya, seda ta saki nishi wayar hannunta da take manne a kunneta ta faɗi saman bed, tace"kam uba wlh se na rama." ta faɗa tana ƙoƙarin kamo Mubina wacce ta miƙe tsam ta ɗiro daga saman gadan tana kwarara ihuuu tana cewa" umpah nah zo ka ceceni". Ta faɗa tana shigewa bathroom da gudu, ta murza key. Amrah ta sosa bayanta tana matsar kwalla dan ba karamin bugo ta mata ba. Phone ɗinta ce ta sake ɗaukan ruri ta ɗauka da sauri tai picking call ɗin ta kara a kunneta tace"Sorry wlh yarinyar nan ce ta kusa nakasa ni."Kamal yace"Wai ashe kinada kanwa kika ce rigimama ko? To kice mata zan kamata se na rama miki, yanzu ki kwanta pls karki biyeta kiyi bacci cikin salama my angel Ok?" Amrah cikin farin ciki tace"Ok my Hubby zan ma biyayya insha Allahu bazan kulata ba , amma duk ranar da kazo garinmu zaka ramamin ko?" Kamal yace "Yes cutie angel se na rama miki bye kiyi mafarkina fa." yana faɗin haka ya tsinke kiran yana sakin lallausan murmushi ya ajiye wayar saman dirowar gadan yana me karanto Adu'ar bacci yaja blanket yana luluɓe jikinsa...

Amrah dadi kamar ya kasheta ta shige cikin bargo tana juyi se wani irin murmushi take tana jin ruwa da iska se *K A K*... Mubina ce ta fito ɗaure da towel iya guiwa kanta na ɗigar da ruwa ɗan ƙara min towel ɗin dake hannunta tasa ta ɗaure kanta dashi tana zumburo baki, tace"Aunty kiyi hkr kinga banida lfy karki dakeni kinji"Amrah tace"Akwai me ramamin banda lokacin ki yarinya." tana faɗar haka ta lumshe idanunta.
Mubina ta galla mata harara tace"Yo wa yace ki harbeni ina bacci na wlh ki kiyayi kanki da maza fa aunty". Ta faɗa tana nufar wardrobe ta ciro rigar bacci me sulbi tana cewa"dan mugunta shine ko a tasheni nayi wanka." ta faɗa tana saka rigar ta yasar da towel ɗin nan ƙasa amman bata cire na kanta ba, ta nufi saman bed ɗin ta hauro saman bed ɗin ta kwanta ta matso jikin Amrah ta rungumeta gam. Amrah na jinta tayi murmushi bata dai tanka mata ba, a haka bacci ya ɗauke su.

************* ********* *************

Yau tsawon kwana *sati biyu* kenan, da faruwar rigimar Mubina da Kamal Mubina ta fita batun sa dan tasan se tayi masa shigo-shigo ba zurfi zata cinma burin ta, yanzu har ya shigo ajin su ya kammala abunda ya kawo sa bata ce masa gurgu sabgar gabanta take, haka shima kallon arziki bata ishesa ba dan mantawa yake da ita inda ba ya shigo class ɗinsu ba.
Iskanci kuwa da rawa da gwada tafiyar Kamal ta yanga ba abinda ta bari se karuwama abin yake, amma tana ƙoƙarin boyewa ta toshe duk wata hanyar da Kamal zai kamata, tana nan tana shirya ramuwarta.
Bangaran Kamal da Amrah kuwa sosai suke soyewa ta waya ya mata alkawalin zuwa karshen wata, tace ya faɗa. mata kafin yazo zata bashi mamaki. Haka Umpah Abbu sosai zumunci suke ummah da Samha sunzo suma su Mamu sunje amma har yanzu katari Kamal da Mubina ba su hadu ba...
Sageer na nan na ƙoƙarin samun kan Mubina ba laifi tana sauraran sa amma taki ta bashi haɗin kai yanda ya kamata, amma yasan watarana zasamu kanta. Misalin karfe 8 am Se kai komo yake cikin office ɗinsa yana neman hanyar da zaibi yau se ya sami number Mubina, se tsaki yake... Knocking ɗin Kofar akayi, ya nufi kofar da sauri! ya buɗe, Kamal ne tsaye cikin wani ɗanyen boyel milk colour yasha wani mahaukacin ɗinki me masifar kyau, yasha hula zanna bukar itama milk colour ce, se adon baƙi kaɗan da aka mata baƙin glass ne manne kan fuskarsa, yayi wani irin kyau sai uban kamshi yake zubawa.
Sageer yace "Bismillah mana irin wannan wanka se kace ba aji zaka shiga ba?" ya faɗa yana murmushi. Kamal ya bashi hannun sukayi musabaha yace"Eh ko ka manta yau juma'ah ce daga nan zan leƙa Company daga can nayi massalaci , meye naga kamar kana cikin damuwa?" Sageer yace"bari har zuwa yamma zamuyi magana".Kamal ya zubama Sageer tsumammun idanunsa masu shegen wani irin sinadari a cikin su, ya kaɗa kafaɗa yace"Ok no problem Allah kaimu , na shiga aji se na fito." Ya faɗa yana ba Sageer hannun sukayi sallama Kamal ya fita. Sageer ya kalli agogon hannunsa ya zaro idanu dan bai san har 8 ta gifta ba, da sauri yay waje shima ya murzama office ɗin key ya nufi class..

Kamal a cike da takunsa na izza yake tafiya cikin tsakiyar makarantar da ta haɗa ƙabila daban-daban ƴan ƙasa daban-daban, haka yake tafe cikin nutsuwa da kamala gwanin sha'awa, se ka lura zaka san yana ɗingisawa. Ɗaiɗai kun ƴan matan da basu shiga aji ba se kallansa suke cike da sha'awa, kowace na kisimawa a ranta ina ma zasu same shi... Wata naga ta bishi da kallo tana lasar baki a hankali ta furta"Allah ya kai damo ga harawa..." leeza tace" Ko bai ciba ya..." iyamu ta rufe mata baki tace"No karki karasa zaici ma.?
A tare suka bushe da dariya... Tsaye take tsakiyar ajin, Sanye take cikin ɗanyar shadda gizna baƙa ɗinkin riga da siket ya kamata sosai hips ɗinta sun fito tare da ƴan ƙananun mazaunanta, kirjinta dake cike dam da dukiyar fulani tamkar zasu fasa rigar su fito waje, ta saki gashin kanta wanda yasha gyara se kamshi yake har kafaɗarta, ya rufe mata fuska ta ɗaure ƙugunta da mayafinta tana cewa"Ku saurari abinda zan faɗa maku da kyau a matsayina na malamin ku ni *Kamal Kangiwa gurgu*..." Basma da Nazir ƴan tsaron kofa saboda shagala da sukayi da kallon tijarar da Mubina take zubawa a matsayinta na Kamal sam basu san cewar Kamal ya shigo class ɗin ba, har yazo dab da Mubina yayi tsaye, ya zura hannunsa cikin aljihun wandonsa ya kura mata shu'uman idanunsa, kunsan 1 minute ya janye idanunsa daga kallonta, ransa na masa suya, sauran ɗaliban yabi da kallo yadda suka shaga suka bada dukanin rayuwarsu wajan kallonta har basu san ya shigo ba... Basma da Nazir kamar a mafarki sukaji kamshin turaran Kamal. Ai kuwa ɗagowar da zasuyi daga can kofar sukayi ido hudu da Kamal yana tsaye dab da Mubina a bayanta, wacce ita ko ta saki jikinta tana abinda take so ita a dole Kamal ce.
Mubina tace Abinda nake so ku gane shine, neman ilimi abune me mutikar wahala dole ne ku jajirce ku tsaya tsayin daka domin kuyi abinda ya tara ku anan , domin kun fito daga ƙasashe daban-daban da garuruwa daban-daban , domin temakon kanku da kanku , kungan ni nan Kamal gurgu bana wasa da..." Nazir ne ya katseta ta hanyar cewa "Innalillahi wa'inna ilaihir'rajiun!! Mubina ki ankare fa an sami babbar matsala." Cikin rikita! Muniba ta fara ƙoƙarin since mayafin ƙugunta ta juyo a guje da nufin ta nufi gun zaman su, se jinta tayi ta fada saman kirjin mutum tayi kwance male-male a faffaɗan kirjinsa da sauri ta ɗago karaf suka haɗa idanu da Kamal, yo me Mubina za ta yi kuwa kawai se....


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻




*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️7️⃣

....Ta yi kicin-kicin da fuskarta duk da tsoro!! ya shigeta, amma ta dake ta kura masa manyan fararan idanunta, babu wani ɗar still tana saman faffaɗan kirjinsa, ta fara magana cikin taurin rai da dakiya, cikin zazzaƙar muryata me fitar da amon dadi, tace"Sir kayi hakuri wlh bada wata manufa nayi ba ina ƙoƙarin tunasar da su ne , abinda nasan zaka faɗa masu kuma wlh jin sunan da baka so wannan ba daga ni bane da bakina zaku ja shari'a , ba niba dan wlh ban san lokacin da yake faɗa ba , ni de ban maka kome ba bayan temaka maka da nayi wajan daliban ka amman duk da haka bakina na neman afuwa , saboda matar natuba bata rasa mijin aure." ta kai karshen maganar tana janye idanunta, daga jikinsa tana ƙoƙarin janyewar tana gunguni. Kamal bai ce mata ƙala ba, sai da tana dab da janye jikinta yay saurin damƙe siket ɗinta ta gaba kafin ɗalibai su farga ya zura hannunsa a marata ya shafo, ya tura karamar yatsar shi cikin ramin cibinta yana jujuya yatsar shi cike da mugunta. Mubina ta zabura ta saki wani uban ihu... Kafin take karasa ihun ya damƙi marata ya mintsineta iya karfinsa, se da ta yi saurin shigewa jikinsa tana cewa"Wayyo Basma Nazeer kuzo kunama ta cijeni ta shiga min riƙata Sir ka duba min..."ta idar da maganar tana ƙamƙame Kamal tana zuba uban ihuuu da kururuwa wanda kowa sai da ya miƙe yana mamkin ta ina? Kunamar ta shigo har ta shiga jikinta...?
Kamal cikin sauri yace Subahanallahi sannu, Malama daman kunama tana cizon malamai irinku?" ya faɗa yana ɓanɓareta daga jikinsa, dan ba riƙon wasa ta masa ba tana shirin tara masa malamai, yay saurin toshe mata baki, ya kalli Basma wacce jikinta har rawa yake dan tsoro saboda bata yarda cewar kunama ce ba se dai idan Kamal ne ya mintsineta. Kamal yace "Uwar me kike kallo zan kamaku ɗaya bayan ɗaya yanzu kamata kuje Office dina na dubata" ya faɗa ya hanƙade Mubina daga jikinsa, ya kalli Nazeer da yake cicira idanu babu gaskiya a tare dashi, yace "Maza muje ku jirani har na gama abinda ya kawoni badai kune tsagerun ba, harakar ku nake shiga ne?" ya faɗa yana tisa keyarsu gaba, Mubina kuwa ta tirje a kofa taki fita tana murza inda Kamal ya mintsineta. Kamal ya buga mata tsawa yace"Ki wuce muje za'a duba miki inda kunamar ta cijeki ne." Mubina tace "Bana son temakon ka ta kasheni kunamar ina ruwan ka kawai daga temakon ka , se kanemi cutar dani wlh se na faɗama umpah kuma..." bata karasa ba ya wanketa da gigitaccen mari! Ji kake fauuuu, Wanda ya ɗauke jinta da ganinta nan take, ya kuma kara tsorata ɗaliban kowa ya ƙame ƙam waje ɗaya, dan basu taɓa ganin ɓacin ra Kamal haka ba, fizgota yay yana huci ya fito da ita tana ihu tana cewa" Wlh ka linka fansar ka ka linkat na rantse da Allah se kayi da nasani marar anfani, ko zan rasa raina Na fadi Kamal gurgu se na ɗauki fansa me muni a kanka... Da sauri ya buge mata baki rufe mata bakin da hannunsa ɗaya yana janta ta karfi, kallo ɗaya yama Basma da Nazeer suka biyo shi a baya.
Basma wacce kaɗan ya rage batayi fitsari ba har wata zufa take keto mata, duk ilahirin jikinta rawa yake saboda tsoro! Tabbas tasan yau se Sir Kamal ya barsu a kwance, duba da yadda ransa yake ɓace da irin marin da ya zafgama Mubina.
Nazeer kansa ya sare dan yasan shima bazai barshi ba...
Suna zuwa ya buɗe kofar ya hankaɗa Mubina, wacce miƙe a guje tayo kansa gadan-gadan tana kururuwa tana faɗin" Wlh bazan barka ba , se kayi nadama ko da zan mutune burina na ɗauki fansa, wlh se nasa ka tsani duniya da abinda yake cikinta Kamal se kayi kuka amma ni tabbas baka isa ka saka ni kuka ba wallahi tallahi..." Kamal ya janyo kofar ya murza key.Ya juyo ɓangaran su Basma da suke duƙe gaban sa, Basma ta fashe da kuka tace"Don Allah Sir kayi hakuri wlh baza mu sake ba insha Allah , ka buɗe ta karta je ta ilata kanta mun tuba baza mu sake ba..."Kamal ya buga mata tsawa!! Wacce yasa Basma jin guntun fitsari ya taho mata kai tsaye, jikinta na rawa.
Kamal yace"Ke!! ba kune kuke biye mata ba na tsani maras kunyar mace ko da uwar mu ɗaya uban ɗaya da ita , natsani mace maras tarbiya da kamun kai , natsani raini bana raunawa bana son a raina ni... "Kai! kuma" ya faɗa yana nuna Nazeer da yake zazzaro idanu.
Yace"ka ɓata wayon ka ƙaton banza , kai gidanku babu mata ne? Da baka san kasa mace hanya ba se dai ka tunzura su? Oya maza ku fara sharar filin can kafin nake fitowa daga class ku amshi hukunci , dan nata yafi naku sakarkaru na tsani raini zan koya mata hankali tin da gidansu ba a bata tarbiyya ba." Ya faɗa yana barin gurin. Basma ta ɓarke da kuka tace"Mubina kin jamin masifa ni ko shara ɗaki bana yi a gidan mu , kome min ake amma zan zo nayi sharar filin makaranta tamƙameme irin wannan , ta ina zan fara? gashi yace a gaba wani horon, wayyo Allah na!!" Ta faɗa tana gun jin kuka. Nazeer yace"ke ko ni salon a raina ni a cikin makaranta amman ni wlh daga yau idan tana abinta ban kuma shiga , muje kawai kar mu ƙara laifi..." Ihuuun Mubina sukaji tana dukan kofar iya karfinta tana lailaya uban ashar... Basma tace" Nazeer muje kar ya dawo yace mune muka zugata." Nazeer bai yi magana ba ya ɗaga kai, suka sauko ƙasa. Suna saukowa suka fara share uban filin nan ɗaiɗai kun jama'a wanda basu shiga ɗakin karatu ba se kallan su suke suna dariya. Iyamu da leeza da suke tsaye kusan resstorant, Iyamu tace"kalli shegun yaran can ko me suka yi aka sasu sharar fili hhhh Allah ya kara , daman wannan me sufar aljanar aka saka fitsarara." ta faɗa tana dariya. Leeza tace" Hummm ba ruwanki ni bana son shiga harakar su dan bata da kunya Mubina zata iya ma mutum tsirara a kasuwa yasin." ta faɗa tana yamutsa fuska.
Iyamu tace" Tab ga wanda ta rena ni ma ina ruwana da ita." Leeza tace" Hakan shi yafi baki ga iskancin da tama Kangiwa ba ranar da a kayi taron nan , amma sam bai fahimci ita bace..." iyamu tace" Ai fa zanci uwarta idan tana masa rashin kunya harakar wa yake shiga , tabar gani munzo ƙasar su tsaf zamu koya mata hankali wlh." Leeza tayi dariya nan suka shiga wata hira duniyar suna jiran 9 ta buga su shiga Aji...
Kamal tin da ya shiga ajin su Mubina bai fito ba sai karfe 9:30 am, cif. Yana fitowa Sharifa ta biyo shi da jakar Mubina da Basma tana cewa "Sir ga jakarsu da wayoyinsu a ciki kar a sace..." Wani burki da Kamal ya taka ya watsamata wani mugun kallo ai a sukwane ta juya ba arziki.
Yaja tsaki ya tafi.
Har lokacin Nazeer da Basma na tiƙar shara sun hada uwar zufa Basma kuka harda majina, kallo ɗaya Kamal ya masu ya ɗauke kansa ya fara taka steps. Mubina kuwa jin tayi ta masifa ba'a buɗe kofar ba, tace "Kan uba lallai Kamal yana wasa dani bai san wacece ni ba bai san halina ba , banida kyau wlh se na saka yabar mahaifarsa da izinin Allah , wannan marin da ya karamin ya link fansar da zan ɗauka." ta faɗa tana juyawa tana shafa kyakyawar fuskarta wacce sawun yatsotsin Kamal suka fito radau kan fuskarta... Kai tsaye saman babban table ɗinsa ta nufa ta hau saman lumtsumemiyar kujera tana kallon uban tulin takardu da laptops manya guda biyu da wata fanka memiyar waya guda se turaruka uku masu tsada da kamshi se glass guda biyu fari da baƙi.
Bushewa tayi da dariya tana riƙe cikinta tace" Bazan taɓa takarduba na jama'a ne daban daban kuma nima ina cikinsu, so amman zanci

Please Login or Register in order to submit comment