Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sheƙi take se yar ramar fuska da tayi se fitinannan kamshi ke tashi a jikinta, kallo ɗaya zaka mata kasan ita ɗin Amarya ce. Rigar jikinta ta tattare tana murmushin mugunta ta riƙe wayarta gam ta iso dab da Mubina, ta ɗaga hannunta dirka ma Mubina duka abaya seda ta saki nishi ta zabura tace"Kan uba yau se naci gidan ku wlh tallahi." ta faɗa tana miƙewa. Amrah a guje ta nufi kofa da gudu tana cewa"uban wa yace kina zagar min mijina? ke idan na zagi wanan figagen Sageer ɗin me kamar ki zaki ji daɗi?" ta faɗa tana buɗe kofar ta wuce a guje. Mubina ta ko biyo ta daga ita se towel. Amrah bibiyu take tsallaka steps ɗin tana ihun kiran "Mamu zata dake ni wayyo Ablah..."Mamu da suke tare da Hajja lubah wacce shigo ba jimawa, ta miƙe tana tafa hannunwa tace"Amrah a siri zaki tona mana kike tsallaka steps bibiyu?" Bayanta Amrah ta laɓe tana shasheƙar gudu. Se ga Mubina da towel. Mamu tace" Baby hauka zaki fara ko me wai?" Mubina tace"Mamu Allah se na rama dukana tayi ban mata kome ba fa." Ta faɗa tana ƙoƙarin zuwa bayan Mamu ɗin. Hajiya lubah tace" yi hakuri baby wai ba makaranta zaku ba Basma yanzu direba ya kaita maza je shirya idan kin dawo kin rama." ta faɗa tana kama Mubina ta jata suka bar gurin tana gunguni. Se ga Ablah ta fito tace"Me yake faruwa anci zalinta ko?" Mamu tace" Amrah ce Mummy." Amrah tace" Yo ai mijina ta zaga ke da bakida aiki sai ɗaure mata gindi se kace mu ba jikokin ki bane." Mamu ta buge mata maki tace" zan barki da babyn raguwar banza , kanwarki kike gudu wannan figigiyar yarinyar me zata miki?" Ablah tace" an zaki mijin naki yaci gidan su kaji mara kunya kuma wlh se ta rama bugunta , Nusaibah keko meye abin guri haka Allah yayi ta me ake da ƙiba Allah na tuba." ta faɗa tana tokara sanda ta zauna ta ɗauki remote ta kamo tashar Aljazeera. Mamu bata yi mgn ba ta koma ta zauna. Lubah sai da ta raka Mubina sama ta dawo ta zauna tana gaishe da Ablah, Ablah tace" da kin barta ta rama ai haka kawai me aka gani na bugo a jikinta? haka ranar Nusaiba ta bugeta idan bakwa sonta wlh zan tarkata kayana mu koma Algerie wajan dangi..." Mamu tace"Mummy ayi hakuri bama sake ba..." Amrah ta bushe da dariya tace" ikon Allah humm..." Mamu ta bugeta ba shiri tabar gun ta nemi gun ɓuya har Mubina take barin gidan.

Mubina shiryawa tayi cikin wando jeas fari irin me bin jiki, ya yabi lafiyar kyakyawar fatarta, yabi ƴan kananun cinyoyinta ya fito mata ƴan matasan mazau nanta hips dinta ya fito sosai wandon ya mata kyau matuƙa kamar ƴar tsana, se rigar irin me dan tsayi ce kaɗan bata karasa guiwa ba tana da yankeken hannuwa pink ce gaban rigar igiyoyi ne farare masu adon duwatsu a jikinsu baƙake, sune tabi ta ɗaɗɗaure su yanda ta gani a pic ɗin ledar rigar dan yau ne zata fara sawa, yanda Mubina ta ɗaure din yayi masifa ma rigar kyau ya fito da asalin kyawun Mubina tayi ɗass tamkar ka sace ta ka gudu. Hadadɗan takalminta Basket fari ta saka, ta saka siririyar sarƙa na gold da ɗan kunne farare ne masu kyau sai abin hannunsu ta manna zoben su a zara-zaran yatsotsinta, ta fesa wani shu'umin turare mai shegen daɗin tsiya, ta sako jelar gashinta gaba ta ɗauki ƴar ƙaramar jaka fara ta ɗauki phone ɗinta, zata saka jaka kiran Basma ya shigo ta ɗaga da sauri tace"kiyi hkr ganinan zuwa Haladu zai kawo ni ki fito ma kofa ina zuwa se mu waske tin ɗazu laweesa take kirana taro yayi taro zamu cashe yau fa idan na aami shisha yasin se bata hayaƙi." tana faɗin haka ta tsinke kiran tana dariya, ta saka wayar ajaka ta fice cikin takunta me cike da nutsuwa ko ina jikinta motsawa yake kamar tarwaɗa abin gwanin burgewa gata dai ba wani jikiba amman akwai kyan diri.

Tin daga nesa Mamu ta ke kallonta tace"Me zan gani wai baby a haka zaki fita bazaki saka kayana na hausa wa ba? makarantar zaki a haka?" Ablah tace "Ai naga ita ba ɓahaus bace kuma ai makaranta zata ba wani ƙiba ce da itaba bare kice surata ta fito" ta faɗa tana kallon Mubina wace ta zumburo baki gaba tana bubbuga ƙafa. Ablah tace" Ki kula da kanki maza jeki Haladu na jiranki kin makara ma." Mubina tayi murmushi tace "yauwa Ablah nah wai yaya Kabeer bai zo ba ne?" Mamu ta kauda kanta tana mana lubah magana. Lubah tace"ai fa ƙawar tata ma wando tasa Allah dai ya tsare mana yaranmu , ai bakinsu cikin makaranta ne." Mamu tace" Wlh hakan dai baiba ni bana son saka wandon nan." Mubina ta karaso ta fado jikin Mamu ta shagwaɓe tace" Mamu ai bakin makarantane fa kawai kimun Addu'a kinji." ta faɗa tana mannawa Mamu kiss" a kummatu ta saketa ta rungume lubah ta manna mata kiss, ta miƙe ta rungume Ablah ta mata kiss ta fice da ɗan gudunta tana dariya tace" se na dawo." Ablah da Lubah suka ce"a dawo lfy." Mamu tace"Ameen"

Tana fitowa haladu ya bude mata mota ta shiga suka kama hanyar makaranta.

Kamal yana zuwa ya shiga Office ɗinsa ya jima yana nema takardun kafin ya samu, ashe wai ƙasan table ɗin suka fada. Tsaki yaja ya shiga toilet ya wanke fuskar shi ya fito. Ya dauki takardun sa ya nufi kofar tafiya yana kallon tsadaddan agogon hannunsa yaga 3:40 pm, tsaki yaja ya buɗe kofa ya fito ya murza key ya zare ya fara taka matattakalar benen a nutsu, karaf idanunsa ya sauka kan Mubina da take fitowa daga mota waya manne kunnenta tana sakin kayataccen murmushi dimple ɗinta na lobawa, siririyar wushiryata ta baiyyana. Idanu ya zaro ganinta da wannan shigar barin yadda halittar ta ta baiyyana, boobs ɗinta kamar su fasa rigar su fito, ga hips ɗinta sun fito. Idanu ya zuba mata ganin haladu ya juya yaga ta nufi Basma da gudu jikinta na dan motsawa barin boobs ɗinta, juna suka rungume suna dariya se yaga iyamu ta nufo gunsu tana murmushi. Kamal wayar sa ya ciro a aljihun wandan sa yay dailing ɗin number Amrah, bugo ɗaya ta ɗaga cikin ɗaga murya ya fara mgn" sweethear wai me yasa umpah ya sama yarinyar nan idanu take son lalacewa ne kin ko ga da kayan da ta fito yanzu?" ya faɗa da ɗan karfi. Amrah se da ta zabura tace" Wlh ba ganta ba ina bangaran Laure mai aiki dukanta nayi na gudu , amman naga su Mamu ai suna parlour ko basu ga fitar ta ba, dan Allah my hubbi ka korota ta canza kaya kuma nifa ina zargin gun party ne zasu dan na kamata tana waya cewar yau da yamma basu da lecture da tajini ta canza mgn." Kamal ya fesar da zazzafar isa waje yace"Ina zuwa sweetheart zan kiraki." ya faɗa yana tsinke kiran. Ya karasa saukowa ƙasa ya nufi gunsu Mubina. Mubina Tace Basma "kinsan wani abu yau so nake mu ƙure kausar anya ba da motar aro ba ake kawota makaranta ko ta makwafcin su ko saurayi? shegiya me zubin samudawa ai yau sai mun ƙureta muce zamu gidan su dan kara zumunci , kinga daga nan mun san gaskiya an ishemu d akaryar banza shegiya me zubin inyamurai..." Basma ta bushe da dariya tace" Wlh ba ruwana wannan idan ta kama mu ko har zawo mayi..." Iyamu ce ta isu wajan su tace"Wow baby Mubina wlh kin hadu fa Basma ma kinyi kyau sosai." Basma tace "tnx anty iyamu." Mubina ta haɗe face tace "Su Aunty iyamu gulmar me aka kwaso ne naga ba wani harkar juna muke ba?" Iyamu tace" Kai baby ke fa matsalata dake masifa kuma kuna zuwa partyn laweesa ne?" Mubina tace"yauwa ni nasan da walakin goro a miya , to eh muna zuwa se akayi me?" ta faɗa tana kama hannun Basma suka kama hanyar fita. Iyamu tace"Muje nima can zani shiyas naki shiga lecture , Leeza har ta tafi ga." Mubina ta murguda baki ta buɗe bakin zata yi magana kenan suna dab da fita daga get ɗin makarantar taji an fizgota da karfin gaske tayi tagal-tagal zata faɗi yay saurin tarota ta fado jikinsa ya ɗauketa da gigitaccen mari biyu wanda duhu ya baibaye mata ido ta rasa jinta da ganinta nan take. Wani gigitaccen ihuuuuu Mubina ta saki bata ganin kome sai baƙi cikin idanunta. Basma da iyamu suka ja baya da sauri suna neman hanyar guduwa....

Hkr da rashin Editing me kyau ina busy ne😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣9️⃣

Damƙar wuyanta Kamal yay yana huci cikin ɗaga murya yace"Ashe haka kika iskance? Kike yawo a haka? matsayin ki na ɗiyar musulmai kuma gidan mutunci , kowane jaki na kallon ki... Kina tallar kanki sbd da ke sangartacciya , taɓara ta miki yawa yau zan koya miki hankali ." ya faɗa yana damƙar gashin kanta ya jata ya nufi motarsa da ita. tana kwarara uban ihuuu tana tirjewa, tana kiran umpah. Ɗai ɗaikun ɗaliban makarantar da suke shawagi, suka zuba masu idanu cike da mamaki suna tamyar kansu, sanin Kamal bai fiye shiga harakar mutane ba, maybe itama ko dan tana ɗalibar sa ce tayi wannan shigar yake hukuntata...? Mubina tace "wayyo Umpah na makance bana ganin kome wai me na tsare maka arayuwa? Ina ruwanka dani ne? Me na maka yanzu ka makantani? Wallahi bazan taɓa yafe maka ba! Da duk wasa ne yanzu ne zan ɗauki fansa ta kirki , daman na raga makane darajar Aunty amman yanzu ba yafiya tsakanin mu , se na rama..." kara damƙe wuyanta yayi, ya sake ɗauketa da mari wanda ta kasa koda iya ihun sai wani guntun fitsari da taji na shirin zubo mata... Se lokacin ta fasa wani gigitaccen ihuuu ta tafi luuuu ya tarota jikinsa ta fada saman kirjinsa, ta sauke ajiyar zuciya da karfin gaske, kawai se numfashinta ya tsaya cak, ta langwaɓe a jikinsa bata ko motsi... Kamal baki ya taɓe ya ɗauketa cak kamar baby ya nufi mota. Ai Basma ta fashe da kuka ta riƙe iyamu, iyamu bakinta na rawa tace"Ki...ru...fa...ma...na...a...si...ri...kar...ya...dawo wajanmu mu gudu kawai."ta faɗa suka rumtuma a guje... Kamal duk abinda iyamu ta faɗa karaf a kunnen sa, dan iyamu akwai katuwar murya kamar kato. Ya buɗe motar set ɗin gaba ya kwantar da kujera ya kwantar da Mubina wacce take a sume. Ya waigo ya buga masu wata uwar tsawa, "Kai!! Kuzo nan yanzu ko jikin ku ya faɗa maku" da sassarfa suka ƙaraso suka zube a gabansa, iyamu ranta in yayi dubu ya ɓaci yanda take ji da kanta ya wani tozarta su... Kamal yace" Ashe Basma Isma'il haka kike kema kin lalace? ashe ba abinda iyayanki suka turo ki ba kike? Yanzu gidan uban waye zaku a haka? kuka ma iyayanku karyar kuna lecture kuka yi shigar ƴan iska ko kishin kan ku ba kwayi a matsayin ku na ɗiyan musulmai?" ya faɗa yana hararan iyamu ya nunata da hannu yace"Keko katuwar banza yanzu wannan yaran sa'o'inki ne? Ko kunya bakya ji uwa dake kin sako wando babu kyan fasali , kinzo zuwa yawo ina ne zaku?" ya faɗa yana ƙura mata tsumammun idanunsa masu shegen haske da wani irin abu a cikin su. Iyamu duk tana tsorace hakan bai hanata ganin tsantsar baiwar kyawun da Allah yama Kamal ba, ga kwarjini, kayan jikinsa suka tafi da imaninta yanda kwarinsa yake waje mai cike da gashi, kayan sun masa kyau matuƙa... Marin da Kamal ya zafga matane ya dawo da ita haiyacinta. Basma kuwa ta sake ruɗewa jikinta sai ɓari yake. iyamu taji zafin marin matuƙa a ɗan tsorace!! Tace"Sir kayi hakuri Laweesa ce take party shine ta gaiyyace mu." ta faɗa tana sadda kai. " Kamal yace" ba zaku ba tashi maza kiba mutane waje maza ki wuce gidan da kuke zaune , idan iyayan ki suka ajiye ki ki kama kan ki kiyi abinda ya kawo ki , kuma kika yarda a cikin makaranta na sake kamaki da irin wannan shigar hum ,get out." ya faɗa yana buɗe mota. A guje iyamu tabar wajan. Ai kuwa tsirarun ɗalibai na mata dariya ƙasa-ƙasa suna mamakin duk karyar tata ma ashe matsoraciya ce. Kamal ya shiga mota ya zauna ya waigo yace da Basma "Marasa kunya maza wuce ki shiga mota na maidaki gida na shiga har gidan naku na faɗi iskancin da kuke a makaranta , ba karatu kuke ba yawon party kuke yi." ya faɗa yana murza key jikin motar. Basma ta fashe da kuka tace"Sir ka rufa min asiri Abba yanka ni zaiyi kuma wlh bama zuwa yauma Mubina ta matsa min amman insha Allahu bazan sake ba na tuba." ta faɗa tana miƙewa ta shiga set ɗin baya ta zauna. Kamal ya fizgi motar ya nufi get a guje tin bai isoba megadi ya buɗe masa get ya sulala motar waje. Iyamu kuwa ta shiga gidan da suke zaune ta fada saman katifa ta kece da kuka tana buga kanta a bango, tace"Sir baka dubi irin sonka da Allah ya dora min naka ba kaci zara fina a filin makaranta ka tozartani sbd kanwar matar se kace nice na koya mata iskancin , to wlh yanda ka sani kuka se nasaka se na rama ta in da baka zato se na tozarta ka se kaji kunyar da tafi tawa baka san iyamu ba." ta faɗa tana shasheƙar kuka ta kira number Leeza se da ta kusa yankewa ta ɗauƙo gurin cike da hayaniya tace"Iyamu wai ya haka ne guri ya cika taro yakai taro fa..." Iyamu ta fashe da kuka tace" Leeza Sir Kangiwa ya tozar tani cikin ɗaliɓai ya wankamin mari ya kirani yar iska ana min dariya saboda wannan yarinyar wlh se na saka shi kuka da idanunsa..." Leeza tace"Jar uban can wai kina nufin a anan gaban kowa da kowa? Tab dijam ai kuwa se mun ɗau fansa ki share kawai ki fito zaki ji dadi a wajan." Iyamu tace"No kome baya min dadi bazan iya farin ciki ba ko nazo na hakura , idan kun gama kizo kawai muyi shirin ramuwa ta ruwan sanyi ni an min dariya ko shi ihu za'a masa." ta faɗa tana tsinke kiran ta miƙe ta shige toilet.

Kamal driving ɗinsa yake a nutse, Basma ko ta rufe bakinta banda kuka ƙasa-ƙasa babu abinda take, hankalin ta a tashe yake ganin Mubina asume kuma bai damu ba driving ɗinsa yake a nutsu. Muryar Kamal tajiyo yana cewa"Ki kama kanki ki min shiru ko jikinki ya faɗa maki wlh , ina ne gidan naku?" Basma ta haɗiye kukanta ta ɗago da kanta tace" Muna unguwa ɗaya ne da Mubina nan tsallake titi muke kwana ta farko." Tsaki Kamal yaja yaci gaba da tukinsa. Yana shigowa unguwar Basma ta rinƙa kwatanta masa har suka zo kofar gidan, yay parking. Basma tace"Sir na tuba kar ka faɗama Abbana wlh bazan kuma saka wando ba ko yinƙurin zuwa party wlh sir." ta faɗa tana shasheƙar kuka. Kamal yace"Ok naji share hawayen ki maza shiga gida." da sauri Basma ta goge hawayen fuskarta ,ta buɗe motar tana kallon Mubina tayi tsaye ta kasa tafiya. Kamal yace"Zaki rufe min mota na tafi ko ko ya ne na fito mushiga na faɗa ne?" Basma ta girgiza kai ta rufe motar tana share kwalla ta nufi get ɗin gidan su. Kamal ya fizgi motarsa yabar wajan a guje.

Amrah ce ta fito daga ɓangaran laure ta shigo parlon, ta isko Mamu da lubah a tsaye Ablah taba lubah abu a leda se godiya take, zata tafi. Amrah ta iso parlon tace"Don Allah Mamu me yasa kuka bar Baby ta fita da shigar banza daga gida? Wlh ko ban ganiba naji kunya sosai , a ce mijin da zai aure ni yaga abinda ba mai kyau bane har ya kira ya faɗa min haba dan Allah Mamu." ta faɗa ta zama. Mamu tace"Amrah ban son rainin hankali ni zaki ma faɗa ai daman nasan dole za'a zage mu wlh , Lubah muje na taka miki bakin mota." Ablah ta tafa hannunwa tace"Nusaiba tsine muku dai akayi ba zagi ba , shin meye a jikin Mubina na saka idanu? daman tace min yaron ya sa mata ido a makaranta." Mamu ba ta sake magana ba suka fice da Lubah Lubah na murmushi da mamkin rigimar Ablah, ga haskuya kiri-kiri ta hana a faɗa... Amrah ta miƙe tana hararan Ablah tace"Wlh kiji taoron Allah ki fasa wannan abinda kike sam bai dace ba..." Ablah ta miƙe da sandarta tana bin Amrah Amrah ta haye sama tana faɗa, tabar Ablah na bambami se kumfar baki take... Mamu kuwa ko da ta dawo daga rakiya ta isko Ablah na masifa ta bayan kujeru ta duƙe ta shige bedroom ɗin umpah na nan ƙasa ta ɗan kwanta kan a kira la'asar, tana me jin haushin Ablah dan ta san idan Mubina ta lalace ita za'a zaga ba kowa ba...!

Bai zame ko ina ba se gidan su yay horn megadi ya buɗe masa kofa ya shige da motar, nan harabar gidan yayi parking. Kallon Mubina yay yaja tsoki ya beƙa hannunsa ya ɗauki bottle ɗin water yaji akwai sanyi sosai, buɗewa yay ya matsa dab da fuskar Mubina, ya ɗaga bottel ɗin sama ya kwarara mata a fuskarta da kirjinta, zuwa shafaffan cikinta. Wata irin raunaniyar ajiyar zuciya Mubina ta sauke da karfi... Ta zabura jikinta na wani irin kyarrrrrma, ta fara ƙoƙarin bude idanunta wanda suka mata mugun nauyi, ga zafi tana girgiza kanta da karfi, amman ta kasa buɗe idanun kurma ihuuu tayi da karfi" Wayyo Allah na!! Umpah bana gani wlh bana gani umpah ƙishi nake ji ka bani ruwa." ta faɗa tana kecewa da kuka jikinta na karkarwa gag-gag. Kamal ya rankwafa yay mata rumfa da kirjinsa ya sanya tattausan hannunsa ya riƙo kafadunta, ya tallafo kanta ya sanya hannunsa ɗaya saman zara-zara gashin idanunta wanda suke kwance luf ya shafa, ya shiga hura mata iskar bakinsa ya meƙa hannunsa ɗaya ya janyo botteI ɗin water ɗin ya riƙota sosai jikinsa ya kafa mata bottel ɗin a ɗan karamin bakinta, da sauri ta fara haɗiyar ruwan ta dora hannunta saman nashi tana shan ruwan sosai. Kamal ganin batada niyar dena shan ruwan ya janye robar ruwan daga bakinta. Ta sauke ajiyar zuciya ta nitsa kanta kirjinsa tana maida numfashi, kuma sai tayi wata irin zabura, ya riƙeta gam itako se ƙoƙarin fizgewa take. Bakinsa ya kai dab da kunnenta Cikin ƙasa da murya yace"ke! maras kunya nutsu kisan da wa kike tare ko yanzu na sake tsinka maki lafiyayyun mari wlh , karamar ƴar rainin hankali." ya faɗa yana shafa idanunta da suke a rufe ruf, jikinta se rawar sanyin yake. Inajin murya a dodon kunnena sai naji wani irin mugun tsoron sa ya shigeni nan take ban taɓa tunanin zan ji tsoron mutum ba haka... Amman yau naji mugun tsoron sa fiye da kome... Sbd ni kadai nasan azabar da naji lkcn da ya tsinkamin marin karshe... Shiru nayi jikina na karkarwa ina jin wani irin sanyi yana shiga jikina se rawar sanyi nake na kasa kwakwaran motsi... Kamal ganin Mubina tayi shiru ta fasa hauka sai rawar sanyi take, yasa yaji mugun tausayin ta ya darsu a zuciyarsa. Jikinsa ya shigar da ita sosai yana shafa gashin kanta. Can ƙasan makoshi yay mata magana dab da kunnenta yace"kina jin sanyi ko?" ya faɗa yana shafa lallausan gashin kanta. Cike da tsoro na ɗaga masa kaina ina nitsa kaina cikin kirjinsa ina rawar sanyi. Murya sa naji yace"Am sorry my kanwar nine na mareki har kika suma ko?" tsintar kaina nayi da girgiza kaina ina kara ɓoye kaina kirjinsa, dan Allah ya gani bana son ko kallan fuskar shi ji nake banida makiyi a yanzu da ya wuce shi se dai a sannu zan rama cikin ruwan sanyi ta bayan gida, dan a yanzu bazan iya masa rashin kunya ba ya ɗarsa min tsoron! sa a zuciyata... Amon muryasa naji cikin kunnena yana cewa"Ok to waye ya mare ki idan ba Kamal ba?" ban iya bashi amsa ba hawayen baƙin cikin tunawa a tsakiyar makaranta yaci mutunci na! hawanye takai ci ke sauka kan fuskata... Ji nayi yana mgn cikin tsawa"Ke!! Maida hawayen ki yanzu nan." ya faɗa yana zaro handkerchief me wani irin daddaɗan ƙamshin sa me sanyaya zuciya, naji saman fuskata yana goge min hawayen. Shiru nayi nayi lamo jikinsa ina sauke raunaniyar ajiyar zuciya da karfin gaske, ina shaƙar daddaɗan ƙamshin sa. Hannunsa naji saman fatar idona yana shafawa yace"Oya buɗe idanunki maza." ya faɗa yana shafa gashin idona. Ƙoƙarin buɗe idanuwana da suka min nauyi na fara yi, amamn na kasa buɗewa... Muryasa na tsinto tsakiya kunnena ya kirani *Mubeena*" da sauri bakina yana rawa nace "Sir... na... Ka... sa... bu... ɗe... idon... na...wa" na fada ina hawaye. Kamal jin abinda Mubina ta faɗa gaban sa ya yake ya faɗi jikinsa na rawa ya ɗago da kanta ya riƙe fuskarta da hannu biyu ya kai bakinsa saman idanunta kawai sai ya fara lasar idanun nata ya shiga tsotsa a hankali yana shafa lallaunsa gashin kanta. Wani irin abu na fara ji na tsirgamin jikina tin daga ɗan yatsana zuwa tsakiyar kaina, nayi saurin ƙamƙameshi ina girgiza kaina nace"Sir ina jin zafi zan iya buɗe idanuna yanzu bari na gwada kaji Sir."na faɗa ina tusa hannuwana tsakiyar sumar kansa mai taushin gaske ina sauke ajiyar zuciya, ina ƙamƙameshi sosai jin yadda yake tsotsar min fatar idanuna, idan ya tsotsi na dama ya saki ya tsotsi na hagum. Kuka na sakar masa da karfi ina dukan kirjinsa. Kamal bakinsa ya janye daga idanun Mubina yana murmushi ya tallafo kanta murya can ƙasan makoshi yace" Ok *Mubee* oya buɗe idanun naki na gani kinsa gabana faduwa wlh." yafaɗa yana shafa fuskana yana huramin iskar bakinsa saman idona. Bakina na zumburo gaba, na fara ƙoƙarin buɗe idanuna amman sam na kasa kirjinsa an fada ina girgiza shi na kece da kuka nace"Sir Kamal wlh bana gani na kasa buɗe idanuna sam..." Kamal da sauri ya rufe mata baki jikinsa ya fara kyarrrma yace"Pls Mubeena ki rufa min asiri wlh buɗewa zaiyi , me zance ma Umpah da wani ido zan kalle su haba Mubee buɗe kinji."ya faɗa yana ɗaga min fatar idanuna na kara sakin kuka da karfi. Kamal yace" Ok yi hakuri yi shiru muje hospital ko?kai na ɗaga masa na tura kaina kirjinsa ina sauke ajiyar zuciya. Hannunsa naji tsakiyar bayana ya zagaye bayana ya dora kansa wuyana, yana gogamin habarsa a dede setin keyata, yana sauke ajiyar zuciya ajere a jere, naji bakinsa cikin gashin kaina, yana cewa"Mubeena ki daina min irin wannan wasan nasan lafiyar ki kalau dan ki rama ne, to pls kiyi hakuri na tuba me kike so yanzu na baki ko na saya maki ki hakura , muje na saya maki na kawo ki gida da kaina har gaban umpah da Mamu cikin ƙoshin lafiya yanzu zan maki ko meye amman pls bari min wasan ido kinji My Mubee kanwata?" ya faɗa yana bubbuga bayana, ya maido bakin sa dab da wuyana numfashinsa na sauka a wuyana ina jiyo bugon zuciyarsa da karfi tana bugawa... Duka na kai masa kirjinsa na saki kuka nace"Wlh Sir Kangiwa bana

Please Login or Register in order to submit comment