Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a tulasu a gun, kowane abu da sharan sa.
Mubina ce tsaye ɓangaran kayan sawa na maza, sanye take da doguwar riga ta material pink coulor ne, me shegen kyau da tsada yana da adon duwatsu farare masu walkiya, ɗinkin ya kamata matuƙa wani hadadɗan takalmi ne pink a ƙafarta wacce tasha zanen kunshi wanda ja yafi yawa, takalmin akwau masifar kyau da tsini yayi ɗas a farar ƙafarta.
Daurin dan kwalinta ma yayi kyau sosai, jelar kitsonta ta zubo har kafadarta wuyanta da kunnenta sanye suke da wata siriryar sarka ta gold ƴan kunnen kananu sun mata kyau sosai, sai jakar hannunta itama pink ce, haɗe da siririn mayafin da ta maƙala a kafadarta shima pink ne... Dole idan ka kalli Mubina ta shiga ranka, ta kuma burgeka tayi kyau matuƙa ta hadu sosai.

Se Amrah wacce take sanye da Abaya baƙa mai shegen kyau da kudi, ta yane kanta da mayafin abayar, baƙar jaka a hannunta haka takalminta ma tayi kyau sosai sak balarabiyar take kunshinta yayi mata kyau sosai.
Mubina ta kalli Amrah wacce hankalinta ya tafi kan wasu kayan bacci tana dubawa. Mubina a shawaɓe tace" Aunty Amrah kizo mana kiga idan sunyi na siyawa my brother gobe nake so ya saka su." ta faɗa tana bubbuga ƙafa. Amrah tace "Don Allah baby ki saya kawai bari ina duba kayan baccin nan ne." ta faɗa tana ƙoƙarin ciro kayan.
Mubina tace " Ngd bari na kirawo Sageer ya tayani zaɓa." ta faɗa tana buɗe zip ɗin jakarta taga babu wayarta,tsaki ta saki tace"Oh she na barta a cikin mota Anty bani taki na kirasa pls kinji." ta faɗa tana isowa gun Amrah. Amrah tace" Wlh bazan baki ba kinga KAK yana hanyar zauwa maybe ma ya shigo , kinga ba dadi yakira kina amsa waya..."Mubina tace"Hamm naji bari na sauka na ɗauko tawa , duk baƙin cikin ki sai na sayawa yaya Kabeer kayanan wlh." ta faɗa tana tafiya zata sauka. Amrah dariya tayi tana jidar kayan. Tsaye suke a anan ƙasa ɓangaran kayan ciye-ciye, Kamal yace" Zakiyya gasu nan iri iri se kin zaɓa kuyi maza ku gama mu wuce bari na amsa kira." ya faɗa yana tafiya ya fara taka matatakalar bene, ya ciro wayar sa yay dailing ɗin numbert Amrah.
Tafe take tana kale-kale tana dab da matatakalar bene, har zata saka ƙafarta ta tsaya ta kalli wasu takalma suka ɗauki hankalin ta, baya ta dawo ta sake dubawa tana murmushi ta juya ta fara tafiya cikin nutsuwa se waiwayen su take tana murmushi, tamkar zarara. Kamal da ya hayo yana magana da Amrah yace" Ok fito gani nan na hayo zan duba wani takalmi ne , Allah yasa ba karya kike ba angel?" Mubina sam hankalin ta yayi nisa wajan kallon takalmin se kace yau ta taɓa ganin abinda ya burgeta sam bata ji maganar Kamal ba, bata masan tana dab da shiba. Kamal na shirin sake ma Amrah magana shima bai lura da Mubina ba gaban sa sam, se jin mutm yayi saman faffaɗan kirjinsa male-male a kwance.
A tare suka furta "Innalillahi" Mubina duk da tana tsorace!! Amma hakan bai hanata jin daddaɗan kamshin Kamal ba.
A ɗan firgice! ta fara ƙoƙarin janye daga saman kirjinsa, cikin jin kunya ta ɗago da kanta ta buɗe baki da niyar bashi hkr, karaf suka haɗa idanu da Kamal ya kafeta da tsumammun idanunsa, yana ƙoƙarin saka waya aljihun sa.
Mubina a ɗan tsorace!! ta ƙura masa idanu, yayi masifar kyau cike da rashin kunya ta daki kirjinsa da karfi tace"Tirrr yau ban fito da sa'a ba wlh , ina dalili duk inda naje se an bini." ta faɗa tana karasa janyewa daga jikinsa. Kamal kuwa yarinyar yayi missing ɗin rigimarta, kuma yaga tayi masa kyau sosai tamkar ka saceta ta ka gudu ta hadu ta ko ina, matsalar ta ɗaya bata ɓoye jikinta. Murmushi Kamal yay ya ciza lips ɗinsa, tana ƙoƙarin tafi yay saurin samata ƙafarsa, ai kuwa tayi tagal-tagal, luuuuuu tayi tai baya zata fadi ta kware baki ta zumduma ihu, tana cewa"Wayyo Antyna zo kiga zai kasheni wannan ba mijin aure bane wlh..." Kamal ya zaro idanu yay saurin tarota ta fado faffaɗan kirjinsa, tare da toshe mata baki da tattausan hannunsa mai fitar da ni'imataccen kamshi.

Waigawa Kamal yayi cikin ikon Allah babu kowa kusan su babu wanda ya gansu, tarai rayota yay cikin jikinsa ya mata kyakyawan makwanci saman kirjinsa ya rungumeta tsam-tsam a kirjinsa, yay saurin janta wata kwana layin gaɗaje babu alamun kowa a wajan. Yana shiga da ita, ya ɗago da kanta tana kiciniyar kwatar kanta, gashi ya rufe mata baki.
Fitinannun idanunsa ya zuba mata, ya kamo lallausan hannunta yana shafa kunshin hannunta, can ƙasa makoshi ya fara magana cikin raunaniyar muryasa me fitar da amon dadi, yace"Maras kunya a nan ma rashin kunyar zaki min ina matsayin mijin yayarki?" ya faɗa yana janyeta a jikinsa ya sakar mata bakinta. Dai-dai lokacin Amrah ta kwalama Mubina kira.
Mubina ta kware baki zata fasa ihu, da sauri Kamal ya riko ƙugunta ya tallafo kanta ya rankwafo yayi saurin dora bakinsa saman nata.
Ya jawota jikinsa sosai, yayin da suka game waje ɗaya gam, ya mata wata irin sihirtacciyar runguma, yana riƙe da ƙugunta yayin da kirjinsu ya haɗe ya manne waje ɗaya, zuciyoyinsu na wani irin bugo da sauri-sauri, wani irin sansanyan kamshine guda biyu ya haɗe a jikinsu se ya bada wani irin launin dadi mara musaltuwa.

Mubina a tsorace!! Ta kalli Kamal da rinanun idanunta yayin da taji lallausan lips ɗinsa cikin bakinta wani irin huci yake feso mata me fitar da dumi ga kamshi na musamman, wani irin taushi da kamshi ke yawo tsakiyar bakinta. Shima ita yake kallo still bakinsu na cikin na juna bai de tsotsa ba, ya zuba mata fitinannun idanunsa, tana jin bugon zuciysrsa da karfin gaske ga fitunannan kamshin sa ya cikata, ya adabi hancinta wata irin kasala ke ziyartata.
Cike da karfin hali me haɗe da tsoro! ta fara ƙoƙarin kwatar kanta da ƙokarin cire bakinta a nashi tana kallon kwayar idanunsa masu wani irin sinadari a cikin su.

Kai ta shiga girgiza masa kwalla ta fara taruwa cikin idanunta, tana damƙe bakinta cikin nashi.
Kamal ya lumshe idanunsa ya kara ƙamƙameta cikin jikinsa, ya shiga hura mata iska cikin bakinta wani irin dumi ne ya ratsa bakin su, ga yawu ya fara taruwa cikin bakin su saboda yadda Kamal yake jujuya harshensa a cikin bakinta amman bai tsotsa ba. Mubina wata irin kasala ce ta sabko mata haɗe da wani ɗan guntun bacci me haɗe da wani irin sanyi da ta fara ji a cikin jikinta, tsikar jikinta se mimmiƙewa take.
kur tama Kamal da idanu shiko ya lumshe idanunsa ya zagaye hannunsa tsakiyar bayanta ya haɗe goshinsu waje ɗaya.
Cikin jarumta Mubina ta fara yawo da harshenta tsakiyar bakin Kamal ta kamo lips ɗinsa na ƙasa yawu ya fara zuba, ta daddage ta gantsa masa cizo a lips, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa. Da sauri Kamal ya buɗe idanunsa yay saurin maida bakinsa nata yana girgiza mata kai alamu tayi shiru. Tsit ta haɗiye kunka tana damƙe bakinta. Da sauri ya zare bakinsa a nata ya janyata daga jikinsa, sbd wayarsa ta dame sa da ruri, janta yay suka sunkuya hannayensa ya sanya ya tallafo gefen fuskarta ya shiga goge mata hawayen fuskarta, ya sanya tattausan hannunsa saman fuskarta ya fara share mata hawayen fuskarta, fuskarsa dab da tata suna jin hucin juna, cikin tsantsar kulawa da raunaniyar murayasa me dadin sauraro yace"Am sorry jarabatu dan karki mana ihu ki tara jama'a ne yasa na dora bakina akan tsantsaman bakinki , yanzu haka tashin zuciya na damuna wlh ayi mace ƙazama bata iya kula da kanta ba!! banda wari ba abinda kike..." Mubina cike da masifa ta bugi kirjinsa tace"Sakeni kwarto kawai ni nafi karfin ka Allah ya isana a zalumi se na faɗawa aunty ka shamin baki ka sani tashin zuciya a banza ina ruwanka dani? Wlh nafi karfin ka kirani ƙazamar mace , sakeni ni na tafi." ta faɗa tana son miƙewa.
Kamal ya miƙe tsaye ya kamota soka miƙe tare yana riƙe da kafadunta yace" Ok naji Allah baki hakuri amman ai ban san dandanon bakin ki ba na dai dora ne dan karki tara mana jama'ah ta yaya zan sha bakin kanwar matata? , ina Amraya tawane maza kirata naji tana kiranki , amman wlh kika kuskura kika min rashin kunya a gabanta zaki gane kuranki ranar monday" ya faɗa yana kallon albarkatun kirjinta, dukiyar fulaninta wanda suke tsaye kam tamtsam-tamtsam, kamar zasu fasa rigarta su fito. Ya kauda kansa amman yaki sakinta, yace" kinsan yanzu na zama yayan ki fa Oya maza je ki kirawo min matata meye kika tsare ni da ido ne? me wari kawai busassa jiki ba tsoka." ya faɗa yana kallanta ya manna mata wani sansanya kiss a saman goshinta, da kumatunta ya sake ta tayi tagal-tagal zata fadi, ya tarota ta fado kirjinsa ta ƙamkameshi tace" Mugu kawai Allah ya isana se na faɗama umpah wlh Aunty karta aure ka kai mugune." ta faɗa a shagwaɓe tana wani nitsa kanta cikin tsakiyar kirjinsa tana shako ni'imataccen kamshin jikinsa mai dadin gaske. Murmushi ya saki ya janyeta jikinsa yace" Ai kin fini niko se na faɗa masu kin taɓa min fyade a Office ɗina se da Sageer yazo ya kwaceni daket." ya faɗa yana siririyar dariya mai dadin sauraro.
Mubina ta dago da kanta daga kirjinsa tana lumshe idanunta ta turo baki ta kwakwaɓe fuska ta duƙa tana ƙoƙarin cire takalmin ƙafarta tace" Wlh bazan yarda ba Allah kuwa *Kangiwa* se na fasa maka kai" ta fada tana shirin ciro takalmin taji tattausan hannun Kamal ya riƙe ƙafarta haɗe da hannunta yana murza hannun, yace"Ke bana son shirman ki na banza waye zaki doka da takalmi mijin yayar taki?" cikin rashin kunya ta murguda baki ta buge hannunsa tace" Eh kai ɗin wa yace ka shiga sabgata yo." ta faɗa tana kuciniyar cire takalmin. Cikin kakausar murya Kamal yace"Wlh kina cire takalman ki zan matseki na dura miki yawu , nasan duk shine kike so kike wannan babboƙara uwar jarababbu mijin yayarki kike kwaɗayin yawun sa dan bakida kunya ko?" Mubina saboda haushi kasa magana tayi ta fizge ƙafarta ta miƙe tsaye ta dauki jakarta ta buɗe ta fito da powder tace "Allah ya isana mugu ta kwada masa powder a kirjinsa nan ta fadi ta tarwatse, ta zunduma da gudu, ko tsoron faɗuwa bata yi tana ihu tana kiran"Aunty nah wayyo zai kamani." ta faɗa tana shan kwana taci karo ɗa Amrah tana kiran wayar Kamal. Jikinta Mubina ta fado ta ruƙunkumeta tana maida numfashi. Amrah tace "Baby ina kika shiga ne naje mota bakya nan ina kika shiga? duk kin bi kin hargitse haka?" Mubina tace"Aunty ba wannan mugun Kamal ɗin mijin naki bane haka kawai yaci zalina ban masa kome ba nide Allah ya isana wlh..." Amrah ta rufe mata baki tace " Haba Mubina babyn umpah amasa hkr ko saboda ni kinji." Mubina ta kwace jikinta tace"Allah kuwa aunty bazan ba mugu ne wlh kije yana kiran ki , yana tacan ɓarin kibi kuma asannu wlh nide ba ruwana Allah aunty." ta faɗa tana tafiya tace" bari na ɗauko wayar na kira Sageer yazo yamin shuwa." Amrah tayi murmushi ta girgiza kai ta nufi hanyar da Mubina ta nuna mata.

Kamal kuwa dariya Mubina ta bashi sosai ya bita da kallo yana girgiza kai yace"Tab amman mijin yarinyar nan na tausaya masa , wlh rayuwarsa na cikin kwale-kwale." ya faɗa yana cusa hannumsa sumar kanshi yana shafawa ya nufi gun takalman. Bai ɓata lokaci gun saya kala biyu ya saya ya biya kudin ya fito yana kiran number cutie angel. Bugu ɗaya tai picking ɗin call ɗin.
Kamal yace" hum me karya daman karya kike ko?" Amrah ta shagwaɓe kamar tana gaban sa tace"Haba Hubby wlh kiranka yafi dari baka ɗauka ba na zata wasa kake min baka cikin gurin , yanzu kana ina?" Kamal yace gani nan ina dab da kofar suka in dai gaskiya ne zo mu hadu." Amrah tace "Ayyah ka ɗan saukan ƙasa zan sauko yanzu mijin da zan aura ne yake kirana kaga kar ya ganmu yana ta layin nan pls Hubby kaji." Kamal yace" Ok nima ina tarw da wacce zan aura , amman daman tare kuka zo garin?" Amrah tace" Hummm dalilin da yasa kenan nake so mu hadu na baka hakuri akan yaudar da na maka KAK..." maganar ta ta maƙale ne sakamakon ido hudu da sukayi da Kamal shima ita yake kallo waya manne kunnensa. Yace "cutie ina jinki yi magana nima gani ga amaryata ko na baki ku gaisa?" Amrah ta zaro idanu tana kallonsa bakinta na rawa tace"Ba...na...ga...ne... Ko...me...fa." Kamal ya kura mata idanu yace" Ya ilahi wai dake ne nake wayar ko da wa?" Amrah cikin tsoro!! da murna ta kara matsowa kusan Kamal tace" Kaina daman KAK ne wayyo Allah naji kunya yau da na maka karya ashe abin sona ne iyayena suka haɗamu." Kamal ya tsinke kiran ya iso gabanta yana haɗe face yace " Ko zan iya sanin dalilinki na min karya?" Amrah ta isa kusan sa ta sunkuya gaban sa ta kai guiwowinta ƙasa tace"Na tuba Hubby zan maka bayanin kome wlh..." ya katseta ta hanyar rankwafawa ya kama kafadunta ya miƙar da ita yace" shittt bari har muje gida ki tabbatar kin riƙe kwakwaran hujarki bana son yaudara da kika ganni tabbas ina sonki angel amman zan maki hukunci idan hujarki bata gamsheni ba , Oya muje ki zaɓi abinda kike so." ya faɗa yana tafiya cikin takun sa na kasaita tafiya me cike da burgewa se ka kula zaka ga yana ɗan ɗnkisawa kaɗan. Ƙasa suka sauko tana ta zagaye ta kasa ɗaukar kome.

Mubina kuwa tana saukowa taje gun motarsu ta buɗe, haladu na zaune ta shiga ta zauna ,ta ɗauki wayarta ta kira Sageer bugo ɗaya ya ɗaga tare da cewa" Babyna ykk?" Mubina ta shagwaɓe tace"Sir pls kazo Kalla transa mall yanzu don Allah ka tayani zaɓar kaya zan sayama yayana suit ne kaji." Sageer cikin rawar jiki yace" Baby kinci sa'a kuwa gani a kusanta bari na karaso." cikin murna Mubina tace" tnx my one." ta faɗa tana tsinke kiran

Haladu yace " Auta nima a ɗan siyomin ko da ƴar choukulata ne mana na tsotsa." Mubina ta bushe da dariya tace" Haladu baka da matsala zan siyoma kuwa." ta faɗa tana fitowa daga motar. Bata cike 2 munites ba Sageer ya iso yay parking anan kusan motarsu Mubina ya fito ya haɗe tsaf cikin kananun kaya, ya nufo gunta.
Murmushi ta sakar masa, da sallama ya iso ta amsa tace" My one ngd fa muje to." Sageer yay murmushi suka jera suka shiga. Suna shiga suka ci karo da Kamal dasu Amrah da Samha se kaya suke jidama Amrah. Sageer ya rungume Kamal yana dariya, Kamal yay sansanyan murmushi ya bugi Sageer yace"Kai akwai labari ka smaeni bayan sallar isha." Sageer yace" Ok insha Allahu..." Amrah ta gaishe sa tare da Samha da Zakiyya. Sageer zaiyi magana Mubina ta kama hannumsa tana cewa" Pls my one muje mana." Sageer ya bita yana murmushin farin ciki, suka haura saman bene. Kamal ya basar ya kama hannun Zakiyya yace " ya dai ko tazo ne?" Zakiyya tace" uncle da saura mu tafi naga ji wlh." Janta yayi ya kara jido mata ice cream ita da Amrah su chocoulet alewa turare kaya niki.niƙi sukayi. Amrah kuwa kunya take ji sosai ɗaurewa kawai take wani gefen ga farin ciki ashe zaɓin ranta zata aura. Bayan sun Kamal ya gama biyan kuɗin ma'aikatan gurin suka kai masu kayan har mota suna biye dasu. Zakiyya ya zaunar gaba Samha na baya, Amrah ta masu sallama, Kamal ya rakata har gun motar su ya buɗe mata set ɗin baya ta zauna ya mata sallama yace" Cutie nah zan kiraki zuwa dare naji hujjarki tama masoyin ki wanda baki taɓa ganiba , kuma kina sonsa karaya bye." ya faɗa yana ɗaga mata kira ya nufi motar su. Yana zuwa ya shiga ya mata key ya gizgeta da karfin gaske, yabar wajan a guje yana hawa saman titi ya fara driving ɗinsa cikin kwarewa da nutsuwa, suna hira da kanninsa sama sama...
Mubina irin wanda ta zaɓa a farko sune Sageer ya zaɓa mata, taji dadi sosai kuwa se godiya take masa. Sageer ya hana tabiya kuɗin duk tsadar kayan shi ya biya kuɗin, ya ce kuma ta zaɓi duk abinda take so taki babu yanda bai ba taki karshema fushi tayi masa, dole ya dawo ya shiga lallashinta ga gurin da suke gun jama'a ne, se kallonsu ake soyayyar tasu abin sha'awa yanda yake riritata tana botsewa.
Daket ya samu ta amshi ice cream da chocoulet da ya saya mata tayi godiya cikin shagwaɓa, wacce ta sake dulmiyasa kogin sonta da kaunarta.
Har mota ya kaita yana riƙe da kayanta, ta zauna gaban mota Haladu se washe baki yake yace" Ah su auta sannu Yallaɓai ina yini." ya gaishe da Sageer. Sageer ya amsa yana cewa" Amryarmu allah huta gajiya a sauka lafiya." Amrah tayi dariya tace"Ameen" Mubina tace" My one bye" Sageer ya rufo masu motar yana ɗaga masu hannun ya nufi motarsa shima. yana zaune se da motarsu ta cira yay ma motar sa key yabar wajan cike da farin ciki maras musaltuwa, ji yake ba wanda ya kaishi sa'a a duniya...

Mubina ta jingina kanta da kujera ta lumshe idanunta, tace" Wai na gaji wlh wani irin bacci nake ji gashi magarib ta kusa ma." ta faɗa tana jan tsaki tana rungume jakarta gam a kirjinta, tana lumshe lumsassun idanunta. Amrah tayi dariya tace" Kanwata yau akwai labari amman sai zuwa dare idan mun dawo daga tarbar yaya Kabeer zan faɗa maki." Mubina ta turo ɗan karamin bakinta gaba ta shagwaɓe
tace" Allah ni Aunty se kin bani lbrn yanzu nan ko na maki karya wajan umpah nace tinda muka zo Super market tare kike da maza , baki sayi kome ba sune suka saya maki bayan kinsan an maki miji..." Amrah ta zaro idanu waje tana kallon Mubina. Haladu yace "Ikon Allah Auta waye ya kula maza tsakanin ke da ita? ita wanda zata aura ne ke fa? Ince har kiran kato kika yi a waya yazo ku ka hige ciki kika fito da kaya niki-niki a leda." ya faɗa kansa tsaye yana dariya yana driving ɗinsa... Mubina ta zaro idanu ta juyo cike da tsiwa tace" Kai kai kai Haladu nice zakama ƙage me kake nufi...?
Hkr dan zaku ga error typing😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻


```WANNAN PAGEN RANKATA KAF ƊINSA, SADAKARWA CE GA REKU MASOYAN WANNAN BOOK NA KAMAL NE... HAKIKA INAGA ZALLAR KAUNAR KU GA WANNAN BOOK, HAƊE DA RUWAN COMMENTS TARE DA SHARHI, DA KUMA ADDU'O'INKU GARENI, WALLAHI ABUN NA FARANTA RAINA MATUƘA BANI DA BAKIN YI MUKU GODIYA, HAKIƘA KUN CANCANCI NA BAKU KYAUTAR PAGE DUK WACCE TAKE KARANTA WANNAN BOOK TO TA SAKA ARANTA TANA CIKIN WANNAN KYAUTAR, NAGODE MAKU MASOYA ALLAH YA BIYA MANA BUƘATUN MU NA ALKHAIRI NI DAKU DA SAURAN AL'UMMAH MUSULMAI BAKI ƊAYA AMEEN DAN ALFARMAR RABIHIL RAHAMATIHI```


*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣7️⃣

"Kana nufin ni ƴar iskace ko me? Haladu?" ta faɗa tana riƙe baki, ta kafe shi da fararan manyan idanunta wanda suka fara rinewa suka bada launin ja, tana girgiza jiki. Amrah dariya abin ya bata amman ta gintse, tana kallon Haladu taji me zai ce mata.
Haladu yace"Niɗin banza na isa na faɗi wannan maganar ga yarinyar albarka , kawai dai naga kece kika kira rabin ranki yazo ya miki sayayya ba Amrah ba , amman tuba nake hajjaju." ya faɗa yana murmushi. Mubina ta kauda kanta ta gyara zamanta, tace" nazata kazafi zaka min ina bin maza wlh da umpah zan faɗama , ince kace wai mairo bata iya kome ƙazama ce kauye zaka maidata wai ya aura maka ni , Allah nasan yau umpah da ya kore ka." ta faɗa tana dariya. Amrah tace" mai karya dai dan wutane." Haladu yace" sosai ma Amrah ,Haba Auta ina zan iya dake ai wlh na yafe ko sadaka ma." ya faɗa yana dariya. Mubina hararasa tayi ta kauda kanta tace" abinda ba asamu ba ne daman." Amrah dai dariya take kawai...
Mamu ce tsakiyar parlo se kai komo take tsaka nin kitchen da kan dining table ana jera kayan abunci, itada da Laure. Da sallama suka shigo niki-niki da kaya, Haladu na biye dasu. Mamu tace " Sannu ku yaran kirki kun jima me aka sayo ma Kabeer ɗin?" Mubina ta cire takalmanta tayi jifa dashi da jakarta da ledojin hannunta tayi kan Mamu da gudu ta fada jikinta ta rungumeta tana dariya. Mamu tace"Baby ya dai an gaji ko?" kai ta ɗaga ta shige jikin Mamu sosai tana turo baki. Haladu ya ajiye kayan ya gaishe da Mamu ya juya zai tafi. Mubina ta janye jikinta daga Mamu tace" Haladu ga chocoulet ɗin fa." ta faɗa tana sunkuyawa ta kwance ledar ta kwaso chocoulet ɗin ta bashi, yayi godiya ya fice. Mamu tace" Me kuka kwaso haka ne?" Amrah ta karasa jikin Mamu ta rungumeta tace" Mamu kinga Hubbi Kamal ne fa yamin siyayya." Mamu tace "madallah Allah yayi albarka." Mubina ta zumburo baki gaba ta kwaso kayan da Sageer ya siya mata tace"Mamu kalli kayan da Sir Sageer ya siya mani malamin mu ne abokin gurgu mijin Amrah ta faɗa tana kwance ledar kayan Kabeer, ta ciro tana gwadama Mamu. Mamu tace" Auta karki sake cema sa gurgu ta ina yazama gurgun? Ko ba kome mijin yayarki ne fa." ta faɗa tana amsar suit ɗin blue coulor masu kyau, tana dubawa. Mubina kuwa fushi tayi ta turo ɗan karamin bakinta gaba tana bubbuga ƙafa ta faɗa kan kujera ta kwanta, ta juya masu baya.
Amrah tace " Kiyi fushin baza a faɗi gaskiya ba , wow Mamu kinsan kayan nan zasu ma Brother kyau." ta faɗa tana duƙawa ta ɗauki robar ice cream ta zauna tana sha. Mamu tace" Autata Kaya sunyi kyau sosai..." Ablah ce ta fito tana jan casbi tace" Auta Mubinat sannu ya gajiya?" Mubina ta miƙe zaune tana narai-narai da idanu tana langwaɓe kanta. Mamu na ganin haka ta sulale tabar gurin.
Ablah tazo ta zauna ta rungumo Mubina tace" Amrah ce ko?" Amrah ta bushe da dariya tace" ni me daɗin suna Ablah kalli kayan da mijina ya saya min." ta faɗa tana kai mata ledojin kayan gabanta, ta ajiye ta juya tana dariya. Ablah tace"ki rabu dasu maza amshi ice ceeam kisha kije kiyi wanka lokacin sallah magarib ya kusa. Ta faɗa tana ɗauko robar ice cream ta buɗe tana bata abaki. Ba ko kunya Mubina ta lafe jikin Ablah tana amsar ice ceam ɗin tana sha.

Kamal daga nan gidan goggo Rumana suka yadda zango, ta ko haɗa masu dambun shinkafa ya sha zogale da man kuli, ta zuba masu cikin kula tare da lemon zobo mai daɗin gaske, suka nufo gida. Danja tana tsayar dasu Kamal waiga war da zaiyi suka haɗa ido da harun niga, ai harun niga bai jira an basu hannu ba ya fizgi keke napep ɗinsa yay gaba a guje kamar zai tashi sama. Kamal ta tintsire da dariya yace"Ikon Allah wato nima ya shiga guduna kenan ko , tab Allah ka shirya fitsarara yarinyar nan." ya faɗa yana sakin murmushi. Zakiyya tace"uncle me akayi ne?" Kamal ya kalli gefenta ya zungure ta a kai yace, "gulma akayi." Samha tayi dariya. Dede lkcn danjar ta basu damar wucewa ya fizgi motar a guge ya wuce.

😀Harun niga kuwa sosai yake gudu kamar

Please Login or Register in order to submit comment