Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zai tashi sama, matar da take bayan napep ɗin tace"Haba yaru karka kashe ni mana kabi a sanun." niga yace"Humm mama karki damu nasan hannuna na iya tuki ki zauna kawi da kyau shine." ya faɗa yan kara gudu dan sam bai yarda da cewar Kamal bai biyo bayan sa ba. Matar nan na bambami, amman niga bai ɗaga mata ƙafa ba gudu yake sosai. Abinda ya faru kuwa ranar da Mubina ta saka niga fitsari, shine bayan Kamal ya ɗauketa niga yabar wajan a guje, kai tsaye gida ya nufa yana zuwa ya kare ma wayar kallo yaga babbar waya ce, ya fara murna yace wlh ruwa da iska bazai bayar da wayar ba yaci blus, nan aka fara damun sa da kira ya kasheta baki ɗaya ya cire layikan ya taune su a lokacin yasaka layikan sa, gashi dama ba security a wayar nan ya goge duka pics ɗin wayar da numbers kowa ya shiga ɗaukan hoto iri iri, ranar niga bai koma neman kudi ba, sabon wanka yayi yaci kwaliya ya fasa yawo a ƙafa. Umpah da suka gaji da kiran layin suka ji baya shiga dole yaje aka masa welcome back ɗin layinsa, ya sayi wata wayar ya haɗa da waccen, niga kuwa har yanzu yana cin duniyar sa da wayar. Kamal suna shuga gida ana kiran sallah magarib, a gaggauce yayi wanka ya zura jallabiya ya tafi masallaci.
Bayan sallah isha su Mubina suka shirya harda Basma tazo suka rankaya Airport tarba Kabeer. Bayan sallah isha Kamal da su Zakiyya suka baje cin dambun da gwaggo ta basu, se santi suke bugawa, bayan sun gama yasha lemon zoɓo suna santi Ummah sai dariya take masu. Yana gamawa yay wanka ya shirya cikin kananun kaya ya tafi can gidansu Ummah ya gaishe da tsoho Sidi.


Zaune suke a cikin Airport gurin da aka tana da domin zaman masu tarba baƙi. Mubina tana laɓe jikin umpah tayi kyau har ta gaji. Amrah ma tayi mutikar kyau sosai, Basma ma tayi kyau ba karya lass ne blue me ratsin fari ɗinki riga da siket ya mata kyau se hijab ɗan karami da ta saka. Haka Umpah da Mamu masha Allah dasu. Karfe 9:23 pm na dare jirgin su Kabeer ya sauka maradi. Mubina najin saukar jirgi ta ruƙumƙume umpah tana murna tace" umpah wlh su yaya Kabeer ne suka iso yanzu." ta faɗa tana murna. Amrah tace " Wayyo yau zanga brother nah..." Basma tace"Aunty brother ɗinmu dai ko Mubina?" Umpah yay dariya.
Wani hadadɗan gaye fari kyakywa ya haɗe cikin suit baƙaƙe masu matiƙar tsada da kyau, baƙin glass manne kan kyakyawar fuskar shi, kallo ɗaya zaka masa kasan balarabe ne. A nutse yake saukowa daga matatakalar jirgin yana riƙe da wata ƴar jaka mai masifar kyau.
Bayan sun gama saukowa an gama duk binci kar kayan su da posport ɗin, su Kabeer yana janye da katuwar akwatinsa ya nufi inda yasan ƴan gidan su na jiransa. Daga nesa ya hango su umpah da su Mubina tare da wata haɗaɗiyar yarinya kusan Mubina, kallo ɗaya mata ya gane Basma ce ƙawar Mubina dan tana yawan tura masa pic ɗin su tare da ita. Mubina tana hango Kabeer ta fasa ihu ta saki umpah ta ruga a guje tai kansa tana dariya. Amrah ma da Basma suka bi bayanta a guje. Kabeer yana hango Mubuna ta taho da gudu ya a jiye jakarsa ya ware mata hannayensa, tana isowa ta fada saman kirjinsa tana dariya, ya zagaye hannunsa bayanta yana juyi da ita yace" Wow my baby kanwas kin kara kyau da girma masha Allah iye babyn umpah." ya faɗa yana ɗagata sama kamar ƴar tsana, itako sai dariya take tana cewa"Wayyo my brother nah ka tsaya na maka sannu da zuwa mana." dariya yay ya ajiyeta. Dede lokacin su Amrah da Basma suka iso kusan su Amrah ta rungume shi ta baya tana dariya tace" Oyoyo my brother nah sannu da zuwa ka wani biye ma baby ko ta ni dasu umpah baka yi ko?" Kabeer ya saki Mubina ya rungume Amrah yace "Ayyah my kanwas sorry nayi missing ɗinku sosai fa." ya faɗa yana ɗagata yace" Aushhh kanwas kin fiye lukutanci ba kamar Baby ba sakwat ba nauyi..." Mubina ta bushe da dariya tace" Ai shine yaya wlh ni bana son ƙiba ko kaɗan ko na girma na isa aure an mini aure , ba zanyi ƙiba ba..." Basma ta bushe da dariya ta rungume Mubina tace" Aunty Amrah karki raga mata yasin dake take." Kabeer ya kalli Basma jin zazzaƙar muryata ya ƙura mata idanu yana kallon yadda take magana abun burgewa. Ɗagowar da Basma zata yi suka haɗa idanu da Kabeer, da sauri ta sadda kanta ƙasa cikin jin kunya tace"My brother sannu da zuwa ina yini." Kabeer ya janye Amrah jikinsa yace" lfy lau Basma yan mata ko?" murmushi tayi ta nufi gun akwatinsa ta sunkuya ta janyota. Su umpah ne suka iso yana cewa" Bari mu ma mu iso tinda kannin ka sun janye maka hankali..." Kabeer ya karasa yana murmushi ya rungume Umpah yace" i miss u my daddy na same ku lafiya?" ya faɗa yana sakinsa ya nufi gun Mamu ya rungumeta yana murmushi. Mamu ta shafi bayan sa tana murmushi. Umpah yace" Yanzu dai mu kara sa gida mu gaisa da kyau." ya faɗa yana kama hannun Mubuna da ta manne Kabeer. Basma na jaye da akwaitin Kabeer suka nufi kofar tafiya kowa ransa fari tass, suka dunguma gida. Ko a mota Mubina tana kusan Kabeer se sangarta take zuba masa.

Suna zuwa gida Mubina ta haɗa ma Kabeer ruwan wanka, daman itace ta gyara masa part ɗinsa, kome tsaf se gamshi ke tashi. yay wanka ya shirya cikin kananun kaya ya fito. Kamshi ya cika masa hanci dan Mubina tayi turare yafi kala biyar na wuta, kamshi har farfajiyar gidansu.
Zaune suke a parlo Mubuna tana jikin Ablah. Kabeer ya zo ya janyeta ya rungume Ablah yana mata kiss yace" i miss u Ablah nah." rungume shi tayi tana murna tace" Alhmdllh megidana barka da zuwa fatan dai an sami abinda aka je nema?" Kabeer yace"Alhmdllh Ablah." ya faɗa yana sakinta ya dawo wajan su umpah ya gaishe su suka amsa tare masa sannu da zuwa. Mubina tace"yaya muje kaci girke-girken da nayi maka."Mamu tace"kuji karyar banza yaushe kika iya girkin ma? Kullum ana abu ɗaya sangarta ta hanaki iya girki."baki Mubina ta zumburo, Basma na mata dariya. Ablah tace"Nusaiba wai kinga ta isa aure an mata bata iya girki bane?" Mamu ta zaro idanu tace"A'a Mummy" ta faɗa tana me jin haushin sangarta Mubina da akeyi kuma mutum bai isa yayi magana ba, da mamakin wai nufinsu ma bata isa bama aure amman ta isa shiga university? kana mgn Ablah yanzu zata fara kuka... Gabaki ɗaya suka rankaya kan dining are domin ciyar da bakon su haɗe dasu kan su.
Abunci ne kala-kala da girkin gargajiya da na zamani haɗe da nasu na larabwa, se lemuka iri iri na gargajiya. Mubina ce tayi serving ɗin Kabeer alkubus ta zuba masa da miyar niƙeƙen naman rago wanda akyita da alyahu da niƙaƙiyar gyada, se da ta zuba masa kala uku ta jera masa a gabansa, tana dariya ta zuba ma Ablah shurbah ta sa mata gasashan nama a plate ta zuba mata laban da shayi ta ajiye mata gabanta tace" Ablah nah ci maza ki koshi." ta faɗa tana zuba ma Kabeer fruit ɗin inibi, ta zauna. Amrah ta miƙe tayi serving ɗinsu tana cewa" Abin yar wariya ce ko? humm." Ablah tace" Amrah kina adawa dani ne ko?" Mubina ta murguda baki tace" barta Ablah ai su umpah ma ban zuba masu ba har Basma to meye a ciki?" ta faɗa tana sa hannunta cikin plate ɗin Kabeer sunanci tare. Basma ita da Amrah, duk ɗagowar da zatayi se sun haɗa ido da Kabeer se ta sadda kanta.
Bayan sun gama ciye-ciyen da taɗe-taden Kabeer ya fito da tsaraba yaba kowa tashi. Mubina tafi kowa tsaraba harda jeas masu kyau da tsada ya kawo masu da dogayan riguna da su sarka da ƴan kunne da su abin hannu takalma se launi kayan lashe-lashe ba'a magana. Mubina murna take sosai tana godiya, Basma ma ta sami rabonta. Basma se 11 pm suka tafi gida ita da iyayanta bayan sunzo sannu da zuwa. Abbu ma yazo ya masa sannu da zuwa yace su Ummah da safe zasu shigo suma.

Kamal tinda ya fita bai dawo gida ba se 10 pm na dare nan ya baje parlo ya fara aiki cikin laptop sbd wasu gadaje ne da za'a sarrafa su nan kamfanin sa yake aikin binci ke. Se 11:30 pm ya gama yaje yayi wanka ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta ya shiga neman number Amrah, kiranta yay ta fara ringing. Lkcn Amrah ta gaji da jiran sa har sako ta tura masa ba reply, bacci ya ɗauketa ta ajiye wayar kusanta. Mubina tana cikin hira da Sageer se ɓangala dariya take tana ɗaga ƙafa ta dorama Amrah, itaki Amrah akwai nauyin bacci. Mubina taga wayar Amrah na alamun kira ganin sunan *My Hubbina💋* Na yawo saman screen ɗin wayar yasa Mubina ta ɗauki wayar tai picking ɗin call ɗin, ta janye wayar da suke da Sageer ta tsinke kiran ta kai wayar Amrah kunneta cikin lankwasa murya tayi kamar Amrah ce sak ta kwaikwayi mgnr Amrah tace"Hello my hubbina ykk bakai bacci ba? Allah ni nayi fushi ma shine zaka wani shanya ni ina jiranka tin yaushe." ta faɗa cikin wata siririyar murya haɗe da shagwaɓa. Kamal sosai murya ta daki dodon kunnensa, se da ya lumshe idanunsa ya gyara kwanciyar sa yana sauke sansanyar ajiyar zuciya... Mubina jin baiyi magana ba ta cire wayar ta bushe da dariya tana rufe bakinta tace"kunji kwarto ko yazata Anty ce bari naga iyakar iskancin sa se na kamshi wlh idan dan iskana bazan bari ta aure shi ba." ta faɗa tana maida wayar kunnenta se ta tsinto muryarsa mai daɗin sauraro cike da rauni yana cewa"Wow my cutie angel i love u kiyi hkr wlh naje unguwa ne da na dawo kuma nayi aiki se yanzu na sami kaina , amman yau nafi jin dadin muryaki a waya fiye da baya Muahhhhh my angel tawan." ya faɗa yana kara sakar mta sansanyan kiss ta wayar. Mubina idanu ta zaro ta toshe bakinta ta janye wayar tace" Lah wlh ɗan iskane fa su Umpah basu da labari har auntyn ma , gurgu akwai jaraba wlh..." ta faɗa tana maida wayar kunnenta ta lankwashe murya tace" Uhm-uhm my hubbina ni kana zautar min da kwanyata kana hargitsamin lissafi , kana rikirkitani sosai kana sakawa naji duk maza maza matane , a fannin soyayya kana sakawa na kara dulmiyawa cikin tafkin kogin sonka da kaunar ka , Hubbina i love u woyyo ni angel ,irin wannan zazzafan kiss haka ni dai ka daina kar ka lalatani gaskiya My Hubbina." ta faɗa a shgwaɓe tana masa
wani ɗan kukan sangarta tana harba ƙafafunta saman gado. Kamal ya sake rumtse idanunsa yana jin wani irin abu na tsirga masa tin daga tsakiyar kansa har zuwa ɗan yatsar ƙafarsa, bai taɓa sanin angel ta iya shagwaɓa haka ba. Amon zazzaƙar muryata yaji ta daki kunnensa tana masa kukan shagwaɓa harda shasheƙa, tana kiran"My Hubbina banza kayi dani ko to sai da safe..." da sauri Kamal ya bude idanunsa cikin tattausan lafazi yace" Am sorry my cutie angel wlh yau duk kin canza mani ne ina sonki sosai wlh duk kin rikitani ne angel am nace faɗamin me yasa kika min karya baki faɗamin gaskiyar cewar kina maradi ba , kuma kika ki faɗamin sunan ki na gaskiya Oya my angel faɗamin" ya faɗa yana sauke mata numfashin sa cikin kunnenta ta cikin waya. Mubin taji wani zirrrr a jikinta ta lumshe idanunta tana fesar da numfashi mai dumi tana zumburo baki gaba.... Muryasa ta sake bugun dodon kunnenta, a hankali taji yana kiranta "My cutie angel tawan faɗamin mana pls bana son yaudara fa?" Mubina idanunta ta buɗe ta zaro su waje ta ciro wayar daga kunnenta ta ƙurama wayar idanu tana nazarin abinda zata faɗa masa, dan bata san maganar da suka yi ba da Aunty Amrah....... Afuwa ba Editing Sosai.


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣8️⃣

Amon daddaɗar murya Kamal na sake tsinta cikin dodon kunnena, cikin rauni yana ce min" My angel oya ki faɗamin me yasa da muka haɗu a fecebook kika min karya cewar kina dosso , kuma kika ki faɗamin sunanki na gaskiya amsa ina jira cutie nah...?" ya faɗa murya can ƙasa.
A jiyar zuciya na sauke da karfi... Se yanzu na gane Aunty daman da Kamal soke soyayya ta fecebook basu sani b...? lankwashe murya nayi na fara magana, ```"My Hubbi babban dalili na shine ina son na sami wanda zai soni domin Allah ta wannan hanyar, tabbas nasan idan ka soni ba tare da kasan kalar halittata ba , to ba shakka kai masoyine na gaskiya, haka zalika nima naji ina sonka tin ban ganka ba, da farko naso na bijire ma iyayena akan son da nake maka wanda nasan kaima kana sona , se naga babu ribar na bijirema iyayena akan namiji... Na gwammaci nayi biyayya na hakura dakai na rungumi wanda aka zabar min , se dai zuciyata ta kasa hakura na kasa jure rashinka , shine fa nace na faɗama gaskiya yaudara ka nake ashe wai kaine zabin raina... Kaga anfanin bin iyaye ashe ma mune masoyan yanar gizo na asali." na faɗa ina murmushi mai mutiƙar ƙayatarwa. ```

Kamal ya jinjina kai ya sauke sansanyar ajiyar zuciya, yana lumshe tsumammun idanunsa fesar da iskar bakinsa waje. Raunana muryasa yay yace"my sweetheart Amrah ina sonki naji daɗin kasancewar ki wacce zata zama uwar ƴaƴana tabbas ina sonki tin ban ganki ba , yanzu kuma ganinki da sanin halinki ya karamin sonki da kaunarki da kimarki a cikin zuciya na , insha Allahu nida ke mutu ka raba, yanzu kwanta ki huta u love u more." ya faɗa yana sakar min kyakyawan kiss mai ratsa jini da tsoka.
Baki na turo na shagwaɓe masa nace" My Hubbina" Kamal ya saki murmushi yace" Na'am My cutie angel menene?" sanin banida amsa nayi sauri cewa"Hubbina bacci nake ji ni sakani bacci to." nafaɗa a sangarce cikin irin murya Amrah. Murya shi na tsinto yana min sansanyar waka wacce ta sakani ƙamƙame jikina ina ina girgiza kai, ina murmushi idanuna a lumshe duk wakar buzanci ce ta Bonbino ce amman zaƙin muryasa tasa naji dadin waƙar sosai inajin wayata na ringing na kasa bude idanuna saboda baccin da ya fizgeni, na shige cikin jikin Aunty Amrah na manneta gam ina gyada kai. Ina haka ban ko san bacci ya ɗauke ni ba har wayar ta faɗi a hannuna se bacci. Kamal kuwa jin saukar numfashin ta yasa ya tsinke kiran yana murmushi, ya ajiye wayar gefen gado yana jinsa cikin wani irin farin ciki da wani nishadi, ya ɗago ya kara gudun Ac daman wutar ɗakin a kashe se ta gefen gado mara haske sosai, cikin blanket ya naɗe luf yana sakin murmushi. A haka har bacci ya ɗauke shi, Asuba tagari...

*************** ******** ***************
*Bayan sati hudu*
Masha Allah su Mubina sun gama jarabawar su lfy sakammako yayi kyau ita da Basma sun shiga 200 level mataki na biyu, Mubina tana karatu sosai ɗuk iskancin da ke damunta, dan yanzu kusan kullum se ta taɓo mgn a makaranta. Mubina da Sageer sun fara soyayya babu laifi tana kula shi sosai, sbd yana mata duk abinda take so yana riritata, Sageer yana mugun son Mubina ya mutu sosai a kanta, shiyasa take ji dashi dan bata kula kowane namiji se shi duk ko yadda maza suke mata dafifi bata ko kallan su, dan Lameer ma da yaji labarin za'a ma Amrah aure har bikin ya matso gun Mubuna ya dawo, tako masa fitsara tas tace bata sonsa. shiyasa Sageer ya zage ɗanze ya kara himma wajan kyautata mata, a yanzu har su umpah sun san son da Sageer yake ma Mubina umpah yace mutiƙar tana sonsa da zaran ta kammala karatunta zai aura masa ita ya bashi amanarta. Kamal kuwa zuwa wannan lokacin shakuwa me karfi ta shiga tsakanin sa da Amrah, dan suna kula da juna suna son junan su, se dai yayi mamakin bata sake masa irin wannan sangarta da shagwaɓar da ta masa ranar nan ba, shine ranar ya tambayeta akayi katari Mubina na manne jikinta, tana jin kome tama Amrah raɗa ta kawo ta tayata hira ɗa irin muryata, Amrah na dariya ta bata Mubina tako kashe murya suka fara hira da Kamal se sangarta take zuba masa, shiko yana lallaɓata yace tana masa mgn da wannan murya tafi zaki. To wannan shine sanaɗin shakuwar Kamal da Mubina ta waya ba tare shi yasan ita bace, dan har wayar take sacewa idan ta faki idanun Amrah ta kira sa suna hira tana wani lumshewa tana mimmiƙewa tana zuba masa sangarta, harda kukan shagwaɓa sji kuma Kamal duk ya gigice yana tambayata me take so? Amman har yau bai gano cewar ba Amrah bace, shiyasa idan suna hira Amrah se yana jin wani banbarakwai yace ta masa mgn da waccen murya mai daɗin sauraro, nan zata yi dariya dan ta gano iskancin Mubina ne, dole take zagewa tana lankwashe murya ba laifi tana masa irin tata. Mubina ta fita batun Kamal karatun ta take, se ta wayar Amrah kadai ne take kulashi tana masa iskanci ba tare da ya sani ba. Haka shima ko ya shigo gaishe dasu umpah bata masa magana se Mamu ta ƙaniyeta take gai shesa tana turo baki.
Kabeer bayan yazo da sati ɗaya ya huta sosai kullum suna tare da yan gidan su Mubina ko nan da can bata gusawa se idan tana makaranta. yana cika sati ya kama aikin sa a nan *BIA Bank* sosai sun shaku da Basma duk ba soyayya suke ba.
Zakiyya ta haihu sati uku da suka wuce, ta sami ƴarta mace taci sunan Ummah Fatima, sosai Kamal yaji dadi yarinyar nashan gata, yan kebbi sun zo suna sosai akai shagali, cikin dangi. Amrah da Mubina da Basma nan suka yini ranar sunan. Auren Kamal da Amrah ya gaba to saura 10 days sai gyara amarya ake ciki da bai ɗinta, sosai Mamu take tsuma ta da gyarata har an fara mata murza jikinta se sheƙi da kamshi da santsi yake, Mubina tace bata yarda har ita ake gyaran, amman baika na Amrah ba haka kayan shaye-shayen ma sata take tana bankama cikinta, ranar da Mamu ta kamata se ɗa taci duka ba kadan ba. Umpah ya fara masifa yana faɗa seda Mamu ta faɗa masa ilar abin idan ya ratsata ba tare da za'a mata aure nan kusa ba, dan na amare ne... Su Mamu da danginta se shirye-shirye ake kullum cikin siyayya ake, wasu irin kayan kitchen da gadaje umpah yasa aka ma Amrah odar su daga dubai ita ma... Haka wajan su Ummah ma se shirye-shirye ake odar Kamal ta iso daga dubai ta kayan lefe, wai akwaiti ne set 3 wanda su kadai ka kalla kasan bana kananan kuɗi bane ba! Kaya kuwa ba'a maganar dangi se son barka suke. Jibi za a kai lefen. Tamfatsetsan gudan sa wanda yake nan cikin *Zaria 2* kusa da Kalla transa mall, gidana na kece raini ya hadu ba karya, an gama fanti ɗin ruwan toka da fari wai gidan ya hadu ba karya Suwwing pool a gefen dama gabaki ɗayan gidan dauke yake da shukar plowers me ƙayatarwa iri iri masu bada wani irin launin kamshi na musamman, ga wani tafkeken lambu ga rumfar shan isaka gefe ta ajiye motoci se ɗakin megadi dana meba shuka ruwa suna haɗe da wanda zai rinƙa wankin kaya, ya tanadi duk masu masa aikinsa, saura masu girkin su dana ma'aikatan gidan kawai ya rage, gidan Kamal duk wanda ya masa kallo ɗaya se ya sake...

Misalin karfe uku na yamma Kamal ne zaune cikin hadadɗan Office ɗinsa na company, saman wata lumtsumemiyar kujera, sanye yake da 3qourter da rigarsa iri ɗaya ruwan kwai sun masa mugun kyau sai wani sansanyan kamshi ke tashi a jikinsa, gashin kansa iska na kaɗawa, farin glass manne kan kyakyawar fuskarsa me ɗauke da saja wanda ya zagaye fuskar, haɗe da ƴar ƙasumba hakan ba karamin kyau yay ba... Waye manne a kunnesa yana magana yana danna laptop alamar ana faɗa masa mgn yana rubutawa a jikin laptop ɗin. Kusan 20 munites ya cire wayar daga kunnesa ya ajiye saman table ɗin ya shiga duba takardu yana dube-dube, can ya dafe kai yace"Oh my god na manta a Office ɗin makaranta." ya faɗa yana miƙewa tsaye, wayarsa ta ɗauki ringing, ya ɗauka yana mgn,dayar ma ta ɗauki ringing ya ɗauka ya saka aljihun wandon sa ya fito. Sakatarensa ya miƙe yana cewa"yallaɓai kana da baƙi har biyu fa." Kamal ya murzawa kofar key ya tsinke wayar yace" Ok kace su dawo karfe biyar yanzu inada wani babban aiki banida lkc gsky na tafi na dawo yanzu." ya faɗa yana ficewa yana takunsa mai cike da dattaku haɗe da izza, se ƴar ɗingisawar da ta zame masa kamar ado. Yana fitowa ma'aikatan companyn suka fra kwasar gaisuwa yana ɗaga masu hannun ya buɗe zafgegiyar motar sa fara kal kirar venza 2020 ya shige yay mata key ya fizgeta ya fice a guje. Anutse yake driving wayar sa ta sake ɗaukan ruri ya cirota a aljihu, yaga Amrah ce, picking yay ya kara a kunne yana sakin murmushi yace"Uhm my sweetheart ykk ina driving ne zan shiga makaranta ki bani 30 munites na nutsu zan kira ki pls kina min mgn da waccen muryar shagwaɓar taki pls my angel amaryar Kamal." ya faɗa yana bata kiss me zafi yace "bye se na kiraki wasu takardu zan ɗauko a Office." Amrah ta narkar da murya cikin sanyinta tace" Angona kaga kullum cikin gyara ake min yau fa saura 10 days amman kamar yaune bikin ok Angona kar na cikaka da surutu a sauka lfy i love u se na jiki bye." ta faɗa tana shirin tsinke kiran yace"Sweetheart kiss me mana ke wlh kamar me jinnu wata rana ki narke min ki sani wani yanayi kina abubuwa masu dadi ko ban saki ba , watarana kuma kawai kina kauyanci kuma na faɗa maki ina son rayuwa ina son love fa" ya faɗa mata a shwgwaɓe. Amrah tace" My Hubbina wlh ba fa ni..." Ko me ta tuna se tace ba naki maka bane watara kunya nake ji fa." ta faɗa tana sakar masa kiss ɗin ta tsinke kiran tana dariya. Kamal ya girgiza kai yace" Sweetheart zan cire miki kunyar nan wlh muyi rayuwar mu." ya faɗa yana maida hakalinsa kan driving.

Mubina wacce take tsaye gaban dreesing mirror ɗaure da towel, handryer a hannunta tana busr da jiƙeƙen gashinta. Ta bushe da dariya tace"Kai Aunty yasin ina kwasar dariya wannan sakaran mijin naki ya kasa gane nice nake masa basaja fa ,hhhh wlh anji kunya jaki ya kada me shi." ta faɗa tana dariya, ta ajiye handryer ɗin ta shafama gashin ta mai ta kame shi da ribbon kamun gefe, ta zauna saman stool ɗin mirror ɗin ta shiga kwalliya tana wake-wakenta. Amrah kuwa da haushin abinda Mubina ta mata ya isheta ta sauko daga saman gadon sai lkcn na kare mata kallo tayi kara mulmulewa jikinta yayi kyau se

Please Login or Register in order to submit comment