Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gani wayyo umpah kazo ya kasheni..." da sauri Kamal ya dora hannunsa saman bakinta yana murzawa a hankali, ta lafe luf jikinsa. Kamla yace"Innalillahi wa'inna ialaihir raji'un!! Mubeena muje hospital ko?" kai na ɗaga masa ina zubar da hawaye. Kamal ya goge min hawayen fuskata, ya kwantar dani saman kujera yace"Ok bari na shiga na ɗauko maki hijab nayi alwalla kinji Mubee." ya faɗa yana shafa fuska. Kai na ɗaga masa ina zumburo ɗan karamin bakina. Kiss ya rankwafa ya manna mani a agoshi ya buɗe motar ya fito ya murza key daga waje dan sam zuciyarsa bata yadda ba cewar idanunta sun ƙi buɗewa, kawai dai wahala take son bashi. Murmushi ya saki ya tura hannunsa tsakiya sumar kansa ya shafi tattausar sumar kansa, jiya yi ana kiran sallah la'asar. Anutsu ya nufi ciki yana ƙarƙaɗa makullan motarsa. Garba ya nufo Kamal da gudu yana washe baki yace"Yallaɓai barka da zuwa kaga namijin duniya , ɗa ɗaya tilo wajan Abubakar Kan Giwa Mai Nasara..." Kamal yace"Garba a yanzu dai ka barni na sami nutsu ina cikin wata yar matsala wacce idan ta girma zanji kunya a idanun duniya na makanta...." ko me ya tuna yay saurin cewa"Bari na nutsu sai kamin kiraranin Ok." yana faɗin haka yay cikin gida. Garba yayi dariya yace" to wa ya tabo mana Oga kuma?" kofar parlon ya danna ɗan madanin ya shege da sallama. Samha ta tarbe sa tana dariya tace"Yaya Kamal gwara da Allah ya kawoka zo na zuba maka kunun alkama da nama Zakiyya da kaina , wlh yayi dadi." ta faɗa tana dariya. Ummah ta kurba ta ajiye cup ɗin hannunta tana dariya tace"Kamaluddin ya naga kana gama fuska naga ai kana son kunun ko baka jin yunwar yamma?" Hafsat tace "my son ya dai kai dawa wai?" Kamal ya saki hannun Samha ya kara sa wajan Hafsat yace"Wlh momy an ɓata min raina ne amman nima naga abin bai kai ya ɓata min raiba, amman wlh ya ɓaci gashi kamar zan shiga cikin wata ƴar matsala , pls idan kunyi Sallah yanzu ku sani a cikin Addu'a kada Allah yasa wannan abun ya zama gaskiya, momy yaushe kika zo ne ina yini bari naje na dawo , Zakiyya saura ki shanye kunun nan kiga yanda zamuyi uwar ci ina Ummah tane?" ya faɗa yana haurawa saman bene. Ummah tace" gata nan kuwa tana bacci ai yanzu zan tasheta na mata wanka , Ai Addu'a kullum cikin yinta muke ɗan albarka babu abinda zai sameka na sharri se alkhairi." ummah ta faɗa tana miƙewa. tace" Zakiyya tashi maza tinda kin koshi aje asha ruwan zafi." Hafsat tace"lallai fa kam Samha ya dai anyi shiru yayanki zai sha yace ransa ne a ɓace wai." Hafsat ta faɗa tana kallon Ummah. Ummah tace"Kamaluddin kenan ya huce ai shida abokan kasuwanci ai su kullum burin su su kuntata ma wanda zai sauƙaƙa kayansa cikin sauƙi domin talakawa suji dadi , to basa so." Zakiyya ta miƙe tace" Allah ya fisu." Hafsat ma ta miƙe domin ɗauro alwalla se su Ameer kawai suna wasa, dan ganin yanayin fuskar uncle Kamal ta hana su bishi sama.
Kamal yana hawa sama bedroom ɗin Samha ya shiga ya sato hijab dogo har ƙasa ya saka cikin leda ti kun ya fito ya wuce bangaran sa se da yayi wanka saboda yadda yake kin zafi ya ɗauro alwalla ya fito, ya shirya ya saka wani yadi ruwan ƙasa me shegen kyau ƙaramin ɗinki ne mai masifar kyau ya fesa sansanyan turare ya kwashi wayoyinsa da makullan motarsa ya fice...

Yana fitowa parlo ba kowa se su Ameer da gudu ya fice dan karsu riƙe shi. Yana zuwa ya boɗe motar tana nan yanda ya barta, se dai tana rizgar kuka tana kiran umpah. Kamal ya shigo ya zauna ya ciro hijab ɗin a leda ya kamota ya saka mata yay ma motar key ya nufi get. Yana fita daga gidan, jin taki daina kukan ya janyota jikinsa bai yi magana ba ya shiga bubbuga bayanta da hannunsa ɗaya ɗayan yana driving, jin ta tsagaita kukan ta lafe jikinsa tana sauke ajiyar zuciya, yasa ya ɗan kara mannata jikinsa ya cire hannunsa daga bayanta, ya ɗauki wayarsa ya shiga neman layin Sageer. Bugo ɗaya Sageer ya ɗaga tare da sallama. Kamal ya sauke ajiyar zuciya da karfi yace"Sageer pls ina son ganinka yanzu da fatan kana hospital?" daga can Sageer ya bushe da dariya yace"Kangiwa ango me zan samu? Gani fa cikin makaranta..." Kamal yaja tsaki yace"To kazo hospital ɗinku yanzu yanzu mu hadu mu dubata." yana faɗin haka ya tsinke kiran, ya maida hankalin sa kan driving. Mubina ta fashe masa da kuka tin karfi. Kamal yace"Ya Salam me ye to kuma? don Allah kibar zuciyata ta huta haka haba ina dalili, ba hospital ɗin zamu ba ko idon ya buɗe ne? Mubina ta girgiza kai tana kara shigewa jikinsa tana sauke ajiyar zuciya. Hannunsa ya sanya yana buga bayanta...
Kai tsaye hospital ɗin da Sageer yake Kamal ya nufa. kusan tare suka iso da Sageer dan yana cewa su hadu su dubata yaji gaban sa ya faɗi. gashi yana kiran Mubina ba'a ɗauka, ya fito a guje ya shiga mota ya nufi hosfital ɗin. Kamal na parking Sageer na parking......


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



```Aslm masoyan Littafin Kamal ne... Dubun gaisuwa da fatan Alkhairi a gareku, nasan dayawa zasu shiga ruɗanin abinda zai faru a cikin wannan pagen... so abinda nake so daku 🙏🏻don Allah kar wacce ta bini pc dan ƙorafi ko shawara ko gyara nace a mafarki abin ya kasance, wlh bazan saurare kuba! Dan haka na tsara labarina kuma ina dalilina na yin hakan, dan haka don girman Allah tin wuri idan kinsa zaki saya domin ki dameni da jaje ko korafi, to na yafe ki riƙe kuɗin ki na riƙe book ɗina, se kuma ku wanda kuka biya kudi, don girman Allah kada ku cazamin kai ko isheni da korafi, kuyi hakuri ku biyo ni muje cikin labarin Kamal ne... Bayan wuya se dadi kuma mutum baya tsallake ƙaddarasa...````


*Daga yau pagen kyauta ya kare.*


*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Ƙarhen😅👉🏻 Free Page😉*


```Page biyu ne na haɗa```` 👉🏻 🅿️2️⃣1️⃣

Kamal yana gama parking ya fara ƙoƙarin janye Mubina daga jikinsa, ta wani tunzuro baki gaba ta saƙala hannunta wuyan shi, tana gujin kuka alamun bata so ya cireta daga jikinsa. Kamal ya zuba mata tsumammun idanunsa, ya fara mgn me cike da rauni yace"Mubeena mun iso hospital ɗin fa tsaya mana na sauka na kamaki mu shiga ciki ok." ya faɗa yana ɓanɓareta daga jikinsa, ya buɗe motar ya zuro kyakyawar ƙafarsa waje, ya hango Sageer na nufo gun motar sa, karasa fitowa yayi ya rankwafo ya kama hannun Mubina yace"Oya tashi muje" Mubina ta kwakwaɓe fusa tana shirin kuka tace"Allah Sir se ka ɗaukeni ni bazan iya tafiya ba bana gani salon na faɗa rami..." Kamal yace"Wane irin rami kuma? Ai ina riƙe da hannunki oya tashi muje." Mubina ta ɓangare baki ta saki kuka tana jijiga kanta tana diddira ƙafafunta... Kamal yace"Ok yi shiru bari na ɗauke ki shi kenan ko...?" Mubina ta ɗaga kanta. Kamal ya sunkuya ya cicciɓeta ya fito da ita ya rungumeta kirjinsa, ya fara ƙoƙarin rufe motar, Sageer ya iso gurin a guje ganin Mubina ce. Yana isowa yace"Subahanallahi me ya sami babyn my one kawota muje to" ya faɗa yana ƙoƙarin amsarta a hannun Kamal. Kamal ya kauce yana kallon Sageer fuskar shi ba walwala, yace"kuji ni da mutum kaine ka kawota ne zaka wani amsheta muharamarka ce?" ya faɗa yana ƙara manneta a kirjinsa. Sageer ya zaro idanu yace"Babban yaya harda gori? To afuwa muje."ya faɗa cikin yanayin damuwa. Mubina kuwa jin murya Sageer ta saƙala hannunta wuyan Kamal ta ƙamƙameshi ta fara magana dab da hancin sa, har tsinin hancin su na haduwa na gugar na juna, hucin numfashin su ya haɗe waje ɗaya, tana mgn a sangarce"my one Sir ne ya mareni bana gani..." Kamal yay saurin saka tattasan hannunsa saman bakinta ya rufe mata baki, suka nufi ciki. Jama'ah se kallon Kamal da Mubina suke yanda suka yi wani irin kyau suka dace da juna.

Suna shiga Sageer ya kai su wani room me kayan gwaje-gwaje komai akwai a ciki. Ya kalli Kamal yace"Wai Kangiwa me ya sami babyn tawa ne?" Kamal ya nufi gun gadan ya kwantar da Mubina yana jona mata wata na'ura, tako saki kuka ta riƙe hannunsa gam, Kamal ya riƙe hannunta gam ya zuba mata lumsassun idanunsa yace"To meye kuma? ba dub ki zamuyi ba pls daina kukan kinji kanwas." ya faɗa yana shafa fuskarta. Mubina ta damƙe hannunsa a cikin nata tace"Sir ni de my one zai duba ni bana so kai ka duba ni ko nayi ta kukan." ta faɗa tana ɓare baki zata saki kukan, Kamal yace"Ok shiru bari ya duba ki" ya faɗa yana sakin hannunta, ya juyo ya kalli Sageer yana tsaye dab dashi duk ya zama wani iri... Kamal yace" Abokina ka dubata da kyau karka biya sangarta ta pls." Sageer yace "Ok wai da gaske bata gani ne?" Kamal yace"ka dai jona mata na'urorin se mu tabbatar." ya faɗa yana lumshe tsumammun idanun da ya buɗe kofar ya fice. Direct masallaci Kamal ya nufa dan yayi sallah. Sageer ya jona mata na'ura a kanta ya haska mata wani abu a idonta, kamar fitila me hasken gaske gaban sa na faduwa yace"Babyna wlh ko da hakan ta kasan ce ina sonki ina kaunar ki , banga halin da zaki shiga bana na rabu dake zan kasance dake har abdan insha Allah , baby." ya faɗa yana cigaba da aikinsa kusan 1 hour. Kamal kuwa yana nan kofar room se kai komo yake gaban sa na bugun uku-uku kar abin ya zama gaske ina zai shiga da kayan kunya? Tabbas da yaji kunya ba karama ba.!! Se kiran sa ake a waya yaki ɗagawa, dan baya da nutsuwa.
Sageer ya sauke nauyaiyiyar ajiyar zucuya, ya cire ma Mubina na'ura da ya ɗaura mata ya zauna kusanta ya ɗagota ya zaunar da yace"Me yasa kika yi karyar idanu baby haba baby me ma wai ya faru ne?" Mubina ta buɗe idanunta tar ta dorasu kan Sageer tace"My one don Allah kamin alfarma karka cema Kangiwa ina gani so nake na rama abinda yamin cikin ruwan sanyi , nasa yaji kunyar da bai taɓa jiba a duniya na bashi wahala ya kasa sukuni ya rasa nutsuwar sa da kwanciyar hankalin sa..."Sageer yay saurin rufe mata baki da hannunsa yace"haba baby mijin yayarki ne fa to meye ya maki ma faɗa min naji idan ya cancanci hukuncin sai mu masa?" Mubina nan ta kwashe kome ta faɗama Sageer yanda abin ya faru... Ta dora da cewa "my one ka yarda ko da sati ɗaya ne na rama kaji." ta faɗa a shagwaɓe tana narai-narai da idanunta. Sageer ya riƙe hannunta, ya ƙura mata idanu yana girgiza mata kai yace"No baby ina sonki bazan so abinda zai cutar dake ba ko na rasaki , kina ɗaukan abin wasa zai iya zama gaske dan Allah babu ruwansa..." ta sakar masa kuka tana riƙe hannunsa tace"pls my one ka temakamin na ƙuntatama Kangiwa pls..."Sageer yace"ke ni fa ba ɗan iska bane najawo abinda nine zan kwana a ciki... Ta yaya zan ɗauki wuka na dabama kaina...? Ko baki san za'a iya cewa a fasa auran sa da Amrah ya aure ki tinda shine ya nakasa ki ba..." Mubina ta zaro shanyayyun idanuta wanda suka rine waje tana kallon Sageer tana turo baki. Sageer yace"eh wlh da gaske dan haka abar mgnr ki bari bayan auran sa se na faɗa maki abinda zaki yi ki rama cikin ruwan sanyi ai baza mu yafe ba tinda yaci zalinmu..." Mubina tace"my one ka tabbatar kuwa zamu rama?" Yes baby kibari se bayan auran yanzu ajiye ɗaukar fansar , kuma nima se na mare shi yayi fitsari wlh kangiwa ɗan iskane zai yi bayani ai." Mubina ta bushe da dariya ta kwanto jikin Sageer tana riƙeshi tace"Wayyo ciki ashe my one kaima mugune amman zan so naga fitsarin gurgu yasha mari wai niko kasan me? zan masa gobe a makaranta? Wlh karkashi zan zuba a roba na jiƙa shi naje saman bene nabi na zuba a matatakala ya fado nasan nan ma kara jirgewa zai yi."ta faɗa tana ruƙumƙume Sageer. Sageer ya janyeta jikinsa sbd yadda yake jin wani irin abu na tsirga masa, ga nonuwanta sai gugarsa suke. Ya bushe da dariya yace"wai baby A'A kibar kome a hannuna har ayi biki lfy zan baki shawara yanda zamu rama kuma bene a bashi ɗaya ba ke da office ko kin manta? Ai sai muyi barna dayawa kibar kome hannuna kinji" Mubina tace"Eh naji" Sageer yace"yauwa autar mata ƴar lelena yanzu dai ki hkr ok?" Mubina tace"Ai na yarda da kai bari nayi sallah." ta faɗa tana kama Sageer ta sauko daga saman gadon. Sageer yace"Au baki yi sallah ba?" kai Mubina ta ɗaga ta shiga toilet. Sageer ya miƙe yana jinjina kai irin rigimar baby darduma ya shimfiɗa mata, ya buɗe kofa ya fito.

Dudubawa yayi bai ga Kamal ba! Ya fito farfajiyar hospital ɗin, ya tsinkayo shi a mota ya nufi motar. Kamal kuwa tinda ya buɗe kofar room ɗin zai shiga yaji wane hali ake ciki, yaga Mubina idonta tar abuɗe tana hira, yaji iskanci ne Mubina take idonta ras wai dan ta ɗauki fansa ne, ya dawo mota yay kwancin sa yana amsa waya da abokan kasuwancin sa... Sageer ya buɗe motar ya shigo ya zauna yana tiƙar dariya harda tafa hannu. Kamal yace"Ok zamuyi mgn zuwa dare insha Allahu." ya faɗa yana tsinke kiran, ya kalli Sageer yace"kun gama gulmata?" Sageer yace"Wannan baby ina da aiki kar fa muyi aure duk abinda na mata tace se ta rama...?" Kamal ya taɓe baki yace "matsalar kuce yanzu dai Alhmdllh tinda lfy take jeka fito min da ita na kaita gida..."Sageer ya kai masa duka yace"Wlh bamu yafe ba kuma sai mun rama."Kamal yace"Ai nafi karfin ku wlh se dai ku rame... Ni jeka fito da ita mu tafi"Sageer yace"ka tafi zan kaita ai..."Kamal yace"ƙaniyarka kai ka kawota? bari idan na ajiyeta a gidan su kaje ka ɗaukota bai dame nuba , ai yarinyar ina tsoron sharrin ta." ya faɗa yana buɗe motar ya fito ya nufi cikin hospital ɗin.

Sageer ya biyo shi yana dariya. Kwance take kan dadduma ta gama sallah bacci ya fizgeta, ta ƙudundune cikin hijabi. Kamal ya buɗe kofar ya shigo kallanta yayi yaga kamar bacci take, sanin halinta na karya yasa yace"Ke!! Tashi mu tafi gida" yaji shiru bata motsa ba, Karasowa yayi ya sunkuya dab da ita yana leken fuskarta yaga tana fitar da numfashi a nutse, hannayensa ya sanya ya cicciɓeta yay sama da ita firgigit ta farka idanunta cike da bacci, amman ganin Kamal ne ta maida idanunta ta lumshe ta kara narkewa jiknsa ta zagaye hannunta bayansa take ta koma baccin daman sama-sama ne tashin. Kamal na buɗe kofa Sageer ya shigo ya kallesu yana dariya yace"baby ina sonki sbd bakya yafiya yanzu ma dakon kaita mota ne ko?" Kamal bai kulashi ba ya fice da Mubina tana rungume a kirjinsa har mota. Sageer ya rufe room ɗin ya biyo bayan su.
Kamal a gaban motar ya kwantar da ita, daman kujura na kwance take ya zaga ya shiga mazaunin direba, Sageer ya iso yana cewa"Se anjima mun haɗu ko?"Kamal yace"Yes insha Allah." ya faɗa yana ma motar key ya fuzgeta ya bar hospital ɗin. Sageer ma ya shiga mota yana dariyar Mubina, ya fuzgi motar ya nufi gida dan yayi wanka.

Kamal driving yake a nutse har yazo kofar gidan su Mubina, wacce take baccinta tsakani da Allah. Parking yay ya kalli Mubina, ya ɗan rankwafo dab da fuskarta ya hura mata iskar bakinsa ya sanya hannunsa kan kyakyawar fuskarta yana shafawa ya ja dogon hancinta, ya kai bakinsa dab da wuyanta ya dora habarsa kan wuyanta, ya shaki wani daddaɗan kamshinta, ya lumshe tsumammun idanunsa yana sauke tagwayan ajiyar zuciya, yaji numfashin sa na ƙoƙarin sauyawa yay maza zai janye, Mubina kuwa ta sanya hannunta ta zagaye shi a shagwaɓe tace"Uhm Kamal nah ni wlh bazan iya ba fa wayyo ni bana so ka bari pls." ta faɗa a shagwaɓe tana sakin kukan sangarta ta ƙamƙame shi sosai, har lips ɗinsu na gugar na juna. Kamal ya zaro idanun waje ya fara ƙoƙarin janye ta zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugo da sauri, a hankali muryasa mai cike da rauni ya furta" *Mubeena* me na miki me zan maki sorry yi shiri bari kuka kinji." ya faɗa yana ƙamƙameta kamar zai maidata cikinsa, fuskokin su na haɗe laɓɓansu ma na haɗe waje ɗaya har wani damshi-damshi yake badawa, yayin da bugun numshin su ma ya haɗe waje ɗaya suna shaƙar hucin junansu, kana jin bugun zuciyoyinsu yanda suke bugawa da karfi, se kukan Mubina marar sauti, har yawunta na ya fara shiga bakin Kamal , ta wani shige jikinsa sosai ta maƙaleshi. Kamal yayi saurin janye fuskarsa ya ɓanɓareta jikinsa, murya can ƙasa yace"Mubina kina mafarki ko?" ya faɗa yana kamota ya zaunar da ita, ya sanya hannunsa yana share mata hawayen fuskarta. Se lokacin ta buɗe idanunta ta kalli Kamal ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta zumburo baki, ta buge hannunsa ta matsa baya ta kalleshi zata masa rashin kunya cikin tsiwa tace"Wlh se na faɗama umpah na ganka a mafarki na zaka min fyade mugu ta Allah ba ta..." wani irin kallo da ya watsa mata yasa sauran maganar ta maƙale a bakinta tayi ƙasa da kanta ta beƙa hannun ta dauki jakarta tana gunguni. Kamal yace "karya kike wacce za'ama fyade ce take wani ƙamƙame wanda zai mata ba ma ta shiga neman kwatar kanta ba , wuce min a mota kiban guri maras kunyar banza kawai."Mubina bata yi masa mgn ba ta buɗe motar tana riƙe da jakarta ta fito ta tsaya tace"kuma Allah ya isana mugu gurgu kawai sai na rama bayan auran ku da Aunty mugu mai katon kai." ta faɗa ta zuba da gudu tana ihu se kace ya biyota. Kamal dariya yake harda riƙe ciki, ya ɗauki wayar sa ya kira Amrah bugo ɗaya ta daga da sallama. Yana dariya yace"My cutie angel ga rigiman ma nan mun dawo harda hijab nasa mata , yanzu ta gama min fitsara tas duk marin da taci har ta manta." ya faɗa yana dariya. Amrah tace"Au haba kace ka cimin kaniyarta? Yarinyar bata ji wlh Hubbina" Kamal yace"angel zan leƙa kamfani se zuwa dare zan shigo ok bye." Amrah tace "ok bye my Hubbi." daga can ya tsinke kiran yama motar key yabar layin, ko get ɗin gidan su bai kalla ba, dan sauri yake yanada baƙi a company.

Mubina tana shigowa cikin gidan, Haladu ya fara cewa"Ah Hajjaju hijab kuwa yayi kyau."Baba megadi yace"Haladu baka rabo da tsokana ko?" idi me bama plowers ruwa yace"Ai ya santa sarai ba raga masa zatayi ba..."Mubina bata juyo ba tace"Baba megadi baba idi ku barshi wlh yaci bashi zan kamashi."ta faɗa tana shigewa can ciki. Dariya suka yi, Haladu yace"uhumm kyaji dashi an fita da wando an dawo da hijabi yanzu haka Kamalu ne zai korota ya temaka ya suturtata yarinya se kace haihuwar jinnu..." dariya dai suka yi basu tanka masa ba ya kari mitarsa.
Parlour ta fado kamar an nasota tayi wurgi da jakar tana kiran"Mamu kina ina Mamuuuuuuu nah..." ta faɗa tana diddira ƙafa. Mamu ta kaɗo da gudu daga kitchen tana hadama Ablah shayi. Mamu tace "Mubina lfy ya nagan ki da hijabi?" Mubina ta afka jikin Mamu tana zumburo baki tace"yo wannan gurgun bane yayi ta marina ya samin hijab ya koroni gida Allah sai na faɗama umpah, Ablah kina ina zo kiji abinda akamin Mamu kalli fuskata..."Mamu ta rufe mata maki tace"don Allah yarinyar kirki karki faɗa yi shiru abinki muje na dafa maki indomie da kwai kici kayan ki , ga shayi nan me dadi ina dafawa." ta faɗa tana shafa fuskar Mubina tayi jajur alamar taci mari. Mubina ta shige jikin Mamu tana diddira ƙafa tace"to Mamu goyani ni wlh se kin giyani ko na faɗa masu" Mamu tace "Ok hau muje ai ba yauni gareki ba."ta faɗa tana sunkuyawa, Mubina tako ɗare bayan Mamu tana ɓangala dariya Mamu ta miƙe da ita babu wani nauyi atare da Mubina amman duk da haka Mamu se da tace"Woshhh baby."Amrah ce ta sauko tana riƙe baki, Ablah tana fitowa ta tsinkayo Mamu ta goya Mubina tana kyalkyata dariya, taji daɗi sosai tace"Yauwa Nusy ko ke fa yarinya karama agida ba'a kula da ita a gida." Kabeer yana sanyo kansa parlon yay tozali da Mamu ta goya Mubina, yace"Kai Mamu salon ta kashe mana ke katuwar budurwa zaki goya haka?" Amrah ta karasa ta kama hannun Kabeer ta masa mgn ƙasa-ƙasa, ya bushe da dariya yace"Au haka abin yake?" Ablah tace"Amrah munahirci ne zai kasheki ƴar banzar yarinya , yanzu wannan baƙin ciki kike yi ko?" Amrah ta murguda mata baki taja hannun kabeer suna bin su Mamu. Mamu a kitchen ta ajiye Mubina, laure na masu dariya, Mubina na manne jikin Mamu, Kabeer dariya yayi sosai ya wuce part ɗinsa dama ɗaukar wata laptop yazo. A haka Mubina na manne da Mamu har ta haɗa shayin ta bata ta kaima Ablah, ita ko ta haɗa mata indomie da kwai ta soya mata.
Jikin Ablah take a zaune tana cin indomien tana haɗawa da shayi tana zuba santi tace"Mamu ki koyamin irin wannan suyar idan nayi aure na ma oga ko ba haka Ablah nah?" ta faɗa tana ɗagama Amrah gira. Mamu tace"ke dai ci abinki ba wani surutu ba..." Basma ce ta shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta taro ta tana dariya. Basma ta zaro idanu tace"Ni inacan ina larura ashe ke ko a jikinki?" Ablah tace"Me ya faru ne.? Mamu ta ƙif tama Basma idanu. Basma ta kara so ta gaishe su tace"Ablah daman na zata bata iso ba daga makaranta dan direban mu ya riga nata zuwa." Ablah tace "Ai Haladu ya cika shiririta sakare ne." Amrah tayi dariya ta miƙe. Mubina tace"zo kici indomie tayi dadi" ta faɗi tana zubama Basma shayi ta beƙa mata. Nan suka baje suna ci suna hira Basma na mamakin taurin rai irin na Mubina... Umpah ne ya shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta tarbo shi da gudu ta ruƙumƙumeshi tana dariya. Umpah ya rikota yace"Baby ya naga fuskarki tayi ja lafiya?" zatayi magana Mamu tayi saurin cewa"yo ba dole ba goyo fa tasa na mata tana gurza fuskarta bayana." umpah yace"Ah lallai yau baby tasha bayan uwarta." ya faɗa yana janyo hannunta suka zauna yana gaishe da Ablah, tana murmushi ta amsa tana masa sannu da zuwa. Basma tace"umpah ina yini." umpsh yace"Basma ya gida dasu isma'il mun hadu dazu gun meeting." Mubina ta miƙe tana cewa"umpah bari na zuba maka shayi yayi dadi umpah kaji kuwa indomie da kwai da Mamu ta soya min wai dadi , wlh yau ko dan naji yunwa ne se naji tafi ta kullum." Amrah tace "umpah ni inata sannu anyi banza dani" hannu umpah ya bata ta ko kama ta zauna kusansa. Yace"to shikenan ko?" murmushi tayi. Mubina taba umpah shayin tace"Basma tashi muje sama muyi hira." Basma ta miƙe suka haye sama. Ai fa Mubina se da ta faɗama Basma kome... Basma tace"Tab yanzu da sai ki zauna a matsayin makauniya ki kawoma karatunki cikas?" Mubina tayi fari da ido tace"Ai Sageer yace bayan auran Aunty zai tayani na rama. Basma ta bushe da dariya

Please Login or Register in order to submit comment